Showing 183001 words to 186000 words out of 280244 words

Chapter 62 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1085

ba. sallama sukayi ya nufi dakin da Baba malam din yake.
Lokacin da suka shiga har an shirya Baba malam cikin Kayan aiki.
Murmushi ya fara yi da yaga mahmud ya shigo.
Da sauri Shima ya nufe shi Bai taba jin karaya ba irin ta yau daya ganshi kwance sandam babu inda yake motsawa daga kugunsa zuwa kafarsa.
"Sannunka jarimin namiji, ubangiji yayi Albarka Mahmud ko yanzu Allah ya bani abunda bani dashi da namiji, kayi min komai Babu abinda zance maka sai godiya, idan Allah yasa na tashi falillahil hamdu idan Kuma lokacin komawar yayi to muna rokon Allah yasa mu cika da imani, ga Zainabu Nan Dan Allah a kula da ita, ga Kuma makaranta Nan Daman yanzu ni suna ne kawai na me makaranta, Amma kune ke dawainiya da ita, to kada a kasa ko bayan Mana Nan bamu San abinda ubangiji ke nufi da kawoka gurinmu ba shiya barwa Kansa sani, a kula da ibada da Kuma riko da gaskiya, Mai gaskiya baya tab'ewa kayi duk Mai yuwuwa ka koma mahaifarka Dan girman Allah a rage fushi kaji mahmud bashi da kyau ko alama ka Zama Mai yafiya kaima Allah ya yqfe maka kaji, Nima ka yafe min Zaman da mukayi Kona saba maka, Kuma ka rokarmin sauran jama'ar da muka zauna dasu Suma a fada musu na yafewa kowa Nima su yafe min, Abu na karshen da Zan fada maka ga yarinyar nan kaji tsoron Allah a Cikin lamarin ta nasha yin istikhara Ina ganinka a Cikin wata irin wadata Wadda na kan samu kaina da tunanin abun to duk yanda rayuwa ta juya ka kula da Amana ta Fadima marainiyar Allah ce".
Tunda Baba malam ya Fara Masa wannan magqngaun masu Kama da wasiyya jikinsa ke tsuma daga ciki Yana ta faman rokon Allah akan ya rufa Masa asiri kada bawan Allahn nan aikin ya Zama sanadinsa.
"Idon jajur da gani kukan zuci yake ya Kara rike hannun Malam.
"Baba in Sha Allah lafiya za'ayi aikin nan a Gama Kuma ka warke in Sha Allah saika taka da kafarka ka zagaya Asibitin Nan Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w, Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne ya bada nasarar aikin da za'ayi, ai sunce babu wata matsala Mai yawa dama mun zauna a Nigeria anyi aikin".
Kafin Baba malam ya fadi abinda yayi niyya ma'aikatan da zasu tafi dashi sun shigo da gadon da zasu tura shi zuwa theater room din, lokacin da zasu canza Masa gado ya ringa fadin.
"Wash!!! Allah kuyi a hankali bayana bana son ana motsani" .
Da sauri Mahmud ya karaso Yana musu magana da yarensu, da sauri suka mayar dashi suka fita.
Sannu kawai mahmud ke jerawa Baba malam Nan da Nan jibi ya rufe shi.
Kusan mutum bakwai suka shigo suka hadu aka Dora shi a gadon sannan suka tura shi a hankali suka fice daga dakin mahmud na biye dasu, har kofar karshe mahmud ya raka baba Malam Bai tsaya ba saboda dauriya kawai yakeyi Amma Yana Daf da zubar da hawaye.

Guri ya nema ya zauna Yana kallon yanda manyan doctors manya da kananu suke Kai kawo kafin time ya cika suka rufe kofar.
Yana Nan zaune har kusan one hour sannan Kiran Habib ya shigo Masa.
Cikin dari dari Habib ya Fara fadin.
"Yallabai ya maganar zuwa Asibitin ne munji shiru baka fito ba tun bayan da muka dawo daga sallar Asuba".
Tsaki mahmud yayi dama duk ransa ba dadi ga wani sabon salon da Habib ta tarka Wai yallabai.
"Wallahi ka Kara kirana da wani yallabai sai munyi uwar watsi a kasar nan da Kai,ba dai ba barci kuzoyi ba sai kuyi tayi, yanzu Baba malam ya samu good one hour a dakin tiyata, zaka wani ce min maganar Asibiti,kaima wallahi inaga saina kaika Inda zaka Kwana a tsaye kana aiki ko Abinci sai dai kaci a tsaitsaye sannan zaka fashinci namiji Allah yayi ka, ka fadawa dayan ya kawo ku yanzu Ni tun shida Ina nan".
Ya yanke Kiran ya dafe goshinsa da yake Sara Masa.

* *

Karfe bakwai da rabi dai dai Mai a dai daita ya sauke Salma a kofar katafaren gate din gidansu,kudin dake hannunta ta Mika Masa ta wuce da sauri ta shige ciki, ba kowa a harabar gidan ko Mai gadi ma ya shiga sallar insha'i.
Wuf tayi ta shige part din Mama cikin sa'a babu kowa a cikin parlourn directly master bedroom dinta ta wuce, can ta hango Mama ta Zuba tagumi tana zaune duk tayi zumu ba wannan gayun da kwalisa, tunda ta rasa tudun dafawa a Kan sakon da za'a kaiwa Zahra ta shiga halin ha'ula'i tunda Saida aka gindaya mata sharadi ta amince gashi kuma kwabarta na neman yin Ruwa.
Ganin shigowar Salma ko sallama babu yasa Mama ta wani zabura ta taso tana fadin.
" Ke!!! Salma lafiya? Daga Ina kike da wannan tsohon daren? Ina Hameeda Kuma?".
Zama tayi a gefen gado tana sadda Kai kasa tayi shiru.
"Wai ba magana nake Miki ba Dan ubanki kin mayar Dani banza".
Kuka ta fasa Mata Mai cin Rai, Wanda ya firgita 'yar sauran nutsuwar Mama.

*AUREN HUCE HAUSHI*

Naman Fateemah


Page 66.

........... Ai kukan da Salma ta fasa sai ya Zama kamar rura wutar bala'i akayi a zuciyar Mama, nan da nan tayo Kan Salma da manya manyan zagi kamar diyar maguzawa.
"Kukan uban me ki kazo Kika sakani gaba kina mini ko wata jaraba Kika kwaso min Ina zaman zamana".
Ita dai kukanta take ba kakkautawa.
"Wallahi Zan Miki dukan bala'i yanzun nan dan kin raina ni sai ki sakani gaba kina min kukan babu gaira babu dalili".
"Na shiga uku mama ciki ne daniiiiii...."
Ai ita kanta mamar batasan yanda akayi ta doro gaban Salma ba jikinta kamar ana kada Mata gangi sai mazari take tamkar Wadda jaura tabi ta kanta, wata irin Shaka ta kaiwa Salma tana fadin.
"Wallahi gara na kasheki na huta da inga wannan bakin cikin".
Kakari Salma ta Kama nan da nan idanunta suka firfito daman ga jiki ba kwari Kullum Zazzabi.
Cikin Rahamar Allah Hamza ya shigo daman ita ta aike shi tace Idan ya dawo ya shigo tana ciki ya kawo mata, badan haka ba zati iya yiwa Salma mummunan lahani.
Da sauri ya nufo Mama Yana fadin.
"Mama Lafiyar ki kuwa? Me tayi Miki haka? Yaushe ma tazo garin? Meta kawota?".
Lokaci Daya ya shiga Jero Mata wadannan tambayoyin.
Ganin kamar Bata cikin hankalinta yasa shi saka karfi ya banbare hannun Mama daga wuyan Salma. Faduwa tayi sharab a sume Nan da Nan hankalin Hamza ya tashi da gudu ya fita kitchen ya dauko ruwa Mai sanyi ya kwara mata, ya Kara Zuba Mata sannan ta kawo numfashi a wahale, har lokacin jikin mama Bari yake, kamata Hamza yayi ya zaunar yana tambayarta meya faru zata dauki doka a hannunta kome Salma tayi Mata ai bazayi Mata irin wannan danyan aikin ba da Allah baisa yazo ba da Allah kadai yasan abinda ze faru kenan.
Kuka ta fasa Masa tana fadin.
"Wallahi gara ta mutu da wannan abun kunyar data dauko mini, yanzu ina Zan saka kaina Ni Rabi'a shike nan duk wata fuffuka ta Kuma ta Kare a gidan nan kin tozartani kin wulakantani".
Ta saki wani gunjin kuka.
"Wai nifa har yanzu Baki fada min me tayi Miki ba Ni wannan zancen ba gane shi nakeyi ba fa".
Ido jazur Mama ta dago ta kalli Hamza.
"Cikin shege jake tayo a makaranta"..
Hamza jin maganar yayi tamkar saukar aradu a Cikin Kansa.
"Cikin shege Kuma how comes?"
Ya fada yana kallo Salma Wadda ke fidda numfashi da kyar ga ruwan hawaye tamkar an bude lataccen famfo.
"Bazakiyi magana ba Saina Ida aikin da Mama ta fara?".
Cikin galabaitacciyar murya Salma tace wallahi Ya Hamza Nima bansani ba lokacin da naje Jos ne Ya Mukarram din Mama Ladi yace nazo na rakashi duba abokinsa a Asibiti da mukaje Asibitin bamu ganshi ba shine ya kirawosa a waya yace ai suna gida tun safe shine yace muje ya duba shi tunda ya riga ya sayi kayan dubiya, da mukaje gidan bamu samu kowa ba Daya kirasa a waya sai yace mu zauna yaje allura ne chemist, shine muka shiga mun Dade sosai baizo ba sai Ya Mukarram din ya Ciro Mana freshyo biyu yace musha tunda ko ruwa babu a gidan, wallahi daga lokacin Dana Sha zuwa yin barcina baifi minti biyar ba daga nan wallahi bansan meya faru ba sai tashi nayi na ganni a wani yanayin Yana ta bani hakuri Wai aikin shedan ne".
Ta karasa tana sakin wani kuka.
Dafe Kai yayi ya tafi taga-taga ya zauna a Kan sofar dake dakin.
"Innailaihi wa innailaihi raji'un, wannan wace irin masifa ce? Shi yasa har Raina bana son zuwan da sukeyi Jos din Nan saboda gudun irin haka yanzu Dan Allah wa gari ya waya? Kin lalata future dinki totally Baki da sauran wata Qima ta Diya mace kin Bata record dinki har jikan jika wallahi".
Yayi tsaki ya tashi har ya Kai bakin kofa ze bar dakin Dan idan ya tsaya saiya yi Mata fiye Dana mamar, ganin idan ya fita ba tare ta yiwa tubkar hanci ba ze iya zuwa ya Kira abbansu ya fada masa.
"Kai dawo ka zauna zanyi magana da Kai"
Ba musu ya dawo ya zauna yana bin Salma da Ido wadda ta takure guri Daya tana sauke numfashi kadan-kadan.
"Kanaji ba wannan maganar ta tsaya iyakacin mu ukun Nan idan najita ko a bakin Abban mu ban yafe maka wallahi Dan fasa maganar Nan tamkar ka dauko wuka ne ka dabi min a cikina kaji abinda na fada ko? yanzu idan an fito sallar asuba kazo ki wuce Jos ka kaita gidan murja Zan shigo Nima zata fito ta kofar baya sai ka dauketa bana son wani yasan da zuwanta gidan nan".
Sadda Kai kasa yayi yana nazarin maganganunta.
Kada Abba yaji me kenan? Tana nufin baza'a fada Masa yasan halin da ake ciki ba ko me?.
Take ya aro jarumta ya yafa, ta tako ya shigo ciki sosai sannan ya zauna Inda ya tashi.
"Yanzu Mama menene hikimar hanawa a fada Masa wannan ba Karamar magana bace fa kiyi tunani Mana".
zaburo Masa tayi tana zare masa manyan idanunta

"Wallahi naji maganar Nan sai ranka yayi bacin da Bai taba yiba yanda nace haka za'ayi, tashi ka bani guri Wanda baya kishin 'yan uwansa yanzu kai ko cewa nayi kaje ka fada ai ka nuna ba haka ba abun ya Zama sirri".
Tashi ka bani wuri saura Kuma ka Bari wannan munafikin Mai gadin yaga salmar ya fadawa Abbanku ka dauki motarka ita ce me glass Mai duhu".
tana Gama fada ta tashi ta nufi toilet tana zabgawa Salma harara.



*****


Cikin lafiyayyan Turkish bed Zahra ce kwance tayi lif a Cikin blanket sanyi da kamshi freshner suna ratsata, a hankali ta dauko wayarta tayi dialing number dinsa harta tsinke ba'a daga ba. Kiran ta sake Nan ma the same thing, sai taji hankalinta ya tashi ta tashi zaune ta kunna wutar dakin ta zuro kafafaunta kasa tana Kara Kiransa.
Tana kokarin Kara Kiran nasa Kiran ya shigo.
"Alhamdulillahi"
Ta fada a hankali tana sauke numfashi sannan ta daga Kiran.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
Ta fada Yana gyara zamanta, sallamar ya amsa Mata a kasalance sai taji hankalinta ya tashi ba haka ya Saba Mata ba.
Meu Amor, meya faru? naji kamar baka cikin mood me Dadi pls menene? Dan Allah fada min ko jikin Baba Malam din ne?"
Saida ya danja fasali kafin yace mata.
"Precious Ina cikin damuwa sun shiga da Baba Malam za'ayi Masa aikin sunce twelve hours Amma har yanzu fourteen hours ba'a fito dashi ba, ba kuma wani information da muka samu sai dai shige da fice da yayi yawa a dakin mun tambaya sunce babu wata damuwa suna Kan aikin ne,Kinga ta Ina Zan same peace of mind ne?".
"Au yau ne Daman za'ayi aikin da ba cewa sukayi sai wurin jibi zasuyi ba?".
"To ai da abinda suka gani ne shi yasa suka rage kwanakin aikin".
"Allah ya bashi lafiya,dan Allah kada kayi abinda ze karya masa gwiwa, you have to be very strong fa, ka ringa bashi courage akan ze tashi".
"To ki tayani addu'a yanda na kawo shi Allah ya taimakani na maido shi gida lafiya, preciousss.. Baba Malam ya karya min zuciya da yawa, nayi rashinki kusa dani nasan da kina kusa dani ko dumin jikinki kadai ya Isa ya saka min nutsuwa bare nasan za'a taimaka min ai ko?"
Ya fada da wata murya Wadda ta motsata.
"Kaiiii... Meu amor pls ba kyau fa".
"Meye ba kyau din? Lallai nayi sa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ke da yawa fa yanzu da kina dauke da babyn mu da baki Fadi wannan maganar ba, yarinya ki shirya soon komai ze daidaita, ai kin gane?".
Shiru tayi masa.
"Oya Yi magana Mana".
"Me kake son na fada...?".
Komai ma ki fada min Ina so?"
Bata Kara tanka Masa ba,yayi nacinsa ya hakura, "kina jina"
"Eh..." ta amsa masa.
"Gobe in Sha Allah kije gidan Ammah kiyi Mata yini sai ku dawo gida,inaga Sameer zezo kuje kano".
Dan Jim tayi kafin tace "
"Plssss... Dan Allah meu amor ka barni na Kwana a gurinta Ina so naji duminta?".
"Ban fahimta ba? Kamar Yaya kiji duminta? Goyaki zatayi?". Ya jefa Mata tambayar. Jin tayi shiru ya sake cewa
"Baki da damuwa akan wannan ki Bari kizo sai kiji Mai dalili, Amma dai maganar Kwana babu ita".
"Plssss... Dan Allah fa".
"Ok zuwan ma a hakura bazaki sakani a tension ba bayan Wanda nake ciki, wallahi idan na barki Kika Kwana ai ko barcin kirki Bazan iya ba kinsan riskyn dake cikin zamanki a gidan kuwa?".

"Risk! A gidan namu?".
"Yessss..."
Ya Bata amsa Kai tsaye.
Saita rasa abin fada Kuma, duk mamakin duniyar Nan ya cikita Wai akwai hatsari a zamanta cikin gidan, to hatsarin me?.
"Ok shikenan, na hakura tunda gidan namu kake zargi".
"Ba gidan nake zargi ba, wasu daga cikin mazauna cikinsa nake zargi, kuma wallahi badan darajar Abba ba Saina ladabtar da duk wanda ya shiga gonarki Amma a juri zuwa rafi wata Rana za'a fasa tulu ne".
Das ya yanke Kiran daga Jin yanda ya gama maganar kasan ya tuna wani Abu Daya taba dagula Masa lissai.

Ta Jima tana nazarin maganganunsa, kenan dai da gaske ne ya Kama wata rashin gaskiya daga gidan nasu Idan tayi la'akari da ranar Daya sakarmata su barbar suka hanata fita wato yayi haka ne kada taga ko wacece aka Kama a gidansa din.
"Ubangijina ka Kara bani kariya".
Ta fada a hankali tana gyara kwanciyar ta.

Mahmud na yanke Kiran ana fitowa da Baba Malam, a kalla ya samu good fifteen hours, da dan sassarfa yabi bayansu, wani bangare suka nufa dashi nan ma VIP section ne dakin harya fi wancan tsari da komai tamkar gida, Saida suka kwantar dashi suka kara karfin A/C sannan suka Fara yiwa mahmud bayanin yanda ya kamata a ringa yi masa sannan ze dauki kaman thirty days a haka ba tare da an daga shi ba ko kwakwkwaran motsi.sannan suka fice daga dakin, zuwa yayi ya saka shi a gaba yana jinjina Lamarin ubangiji, tsoron Allah ya Kara shigarsa ganin yanda Dan talikin Nan ya Zama sai yanda akayi dashi, idan ma fa da kwanan ya Kare shikenan, wani Abu ya gani kamar rigar roba an saka Masa a kirji ga wasu Abubuwan a kugu Suma Yana kwance baya ko motsi Nan da Nan yaji hawaye sun cika masa Idanu, Rabon da yayi kuka harya manta duk cimadadin da aka Sha a baya Bai taba zubar da hawaye ba, amma yau dai zuciyar ta karye, ya godewa Allah da yasa su Habib basa Nan ya sender su gida tunda yaga Hankalin Habib ya tashi ganin lokacin da aka ambata ya wuce da awa daya ya shiga rudu,Saida mahmud yayi masa fada sosai sannan yadan Sami nutsuwa ganin hankalinsa ya kasa kwanciya yasa dole suka bar Asibitin.
Saida mahmud yayi kukansa sannan yaji Dan dama-dama, shi duk Lamarin rayuwa ya kwance Masa daga kansa, Bai taba jin abinda yayi Bai kyauta ba sai yau yayi Dana sani yafi sau shurin masaki, wani irin fushi yayi Wanda ba ragin daka sai da ya shafi kowa, a nan ya yanke hukuncin Kwana duk da lokacin Sha daya ne na dare Amma sai yaji ko Nan da can baze iya matsawa yabar Baba Malam a haka ba Yana fatan idan Allah ya nufi ya farka to ya Fara arba dashi a gabansa, tunanin Amminsa Yana damunsa kwanan nan idan da Wanda yake ganin ya batawa Bai wuce ita ba duk rintsi ai uwa-uwa ce amma sai itama ya hada yayi musu kudin goro, duk da yasan shirunta kusan shiya kawo Karin lalacewar abun Amma dai dole yaje kada alhakinta ya Fara Kama shi fa.
Kiran wayar Abubakar yayi, lokacin suna zaune a parlour tun dawowarsu yake faman bawa Habib Baki akan ya dangana yayi Masa Addu'a.
"Bazaka gane bane Abubakar nifa Baba Malam na sani a matsayin uwa da uba duka duk wani gata na duniyar Nan babu Wanda bai min ba, dole na shiga tashin hankali Mana idan ya mutu Yaya zanyi?".
Sosai ya bawa Abubakar tausayi.
Yana kokarin hada kalaman da zeyi amfani dasu gurin nuna Masa abinda ya kamata sai Kiran mahmud ya shigo.
Da sauri Habib ya dago Yana kallon Abubakar.
"Shi...ne yaaa kiii..ra ka ko?".
Ya Fadi maganar a rarrabe kamar sabon Dan koyon Karatun hausa.
Gyada Masa Kai yayi Yana amsa Wayar.
"Yes sir, to shikenan Allah ya bashi lafiya, eh gani nan"
Ya fada Yana mikawa Habib wayar.
"My man ka samu nutsuwa kaji, sun fito dashi tun dazu anyi aikin cikin nasara in Sha Allah".
Wata irin nutsuwa ta shigi Habib, Alhamdulillahi kawai yake fa.

Bayan anyone sallar Asuba Abba ya shigo ya samu Ammah ta Idar da sallah tana ninke hijabin,
"sannu da dawowa"
Ta fada sannan ta gaishe shi.
"Yau fa barci nakeson yi sosai da safen Nan saboda na zaunu a mota yanayin hazo ya hana jirgi tashi kwata-kwata, ko Zaki tayani barcin tunda kin kawoni gurin da babu Mai takura Miki ki dama daddawarki da moda babu Mai gani, Au Kinga Zan manta danki dai ya kasa hakuri matarsa yake so, d
Jiya ya kirani muna hanya yace an shiga da baba Malam aiki, sannan yace min yau Zahra zatazo ta wuni a gurinki gobe su wuce kano zata bishi India din, Amma bana Jin ya fada Mata, na fada Miki dai Koda abinda zakiyi Mata"
Gyaran murya Ammah tayi tana fadin.
"Yanzu Abban Yara bazaka bincko Mana asalin yaron Nan ba kadafa ya gudar mini da 'ya saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login