Showing 174001 words to 177000 words out of 280244 words

Chapter 59 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1070

bada Abincin suzo, Mahmud Yana addu'a masu bashi abincin suka shigo tare da wasu doctors biyu da nurses biyu suma, ba laifi yaci abincin da Dan dama tunda abincin mu na Nigeria aka cike lokacin da Sameer ya cike komai, da suka Gama bashi suka dauki jininsa za'ayi gwaji sukaci Baga da sauran bincike binciken su kafin daga karshe suka cewa Mahmud zasu shiga dashi dakin bincike na musamman sai Nan da awa arba'in da takwas.

A gadon mararsa lafiya aka gungura shi zuwa dakin da za'ayi bincken, har kofar dakin Mahmud ya raka Baba malam Yana masa Addu'ar samun lafiya, hannun Mahmud baba malam ya riko.
"Mahmudu ubangiji yayi maka Albarka ya amfani nemanka ya Kara maka budi na Alkhairi yanda ka jikaina kaima Allah ya dawwama maka farin ciki, ko ban tashi ba kayi kokari ka sada Fadima da iyayenka ka basu hakuri bisa yin gaban kanmu gurin aura Maka ita".
"Babu komai Baba Allah ya bada nasara, in Sha Allah sai kaje Sokoto da kafarka".
Murmushi yayi.
"Kayya gamu dai sai abinda Allah ya hukunta".
"Alkhairi in Sha Allah".
Yana tsaye suka shige dashi ciki, sai kuma yaji wata irin karaya a cikin zuciyarsa.
"Ubangiji ka duba niyyata ka bawa wannan bawan naka lafiya, ka tashi kafadunsa yanda mukazo kasar Nan kasa na mayar dashi Lafiya".
Sai kusan biyu da rabi na dare Mahmud ya samu taxin cikin Asibitin ya nufi gida.
Lokacin Daya shiga ba kowa a parlourn, Mr Ajey ya Kira a waya kukun gidan ne, fada Masa yayi ya dafa Masa coffee ya kawo Masa daki.
Yaso ya Kira precious Amma ya gaji hutu yake bukata dole ya hakura wanka yayi yasha coffeen da Mr Ajey ya kawo Masa.

Tun bayan da zahra suka Gama waya da mahmud da safe ta rasa sukuni, data san haka kewarsa zata dameta da Bata bata lallabashi ba a Kan ya hakura su tafi, Batasan wani jigo bane a rayuwarta saida yayi nesa da ita tayi missing dinsa ba kadan just in one day kawai taji tana nema gazawa, Dan ko cikin barcinta shine.
Da kyar ta tashi tayi wanka ta saka rigar Atampha purple Mai manyan flowers farara da ratsin yellow simple make up tayi ta yafa karamin farin gyale ta fito parlourn farko, ba kowa an gyara shi da sai kamshi yake yi ga sanyi ko Ina ya dauka, a hankali ta ratsa parlourn tana tafiyarta a nutse tamkar tana counting steps dinta ta nufi kitchen inda take jiyo motsin Aunty zilai.
Kwanukan da tayi amfani dasu take wankewa, tsayawa tayi da wanke-wanken tana fuskantar zahrar dake shigowa tare da sallama.
Sallamar ta amsa tare da fadin.
"Barda da Asuba uwar dakina, yanzu nake tunanin naje na duba ko lafiya Baki fito ba kada abicinki ya huce.
Zama tayi a Kan kujerar kitchen din tana fadin.
"Lafiya kalau wallahi kawai dai bansan meya sameni ba duk bana Jin dadin garin".
Dan murmushin manya Aunty zilai tayi tana fadin.
Ko canjin yanayi ne kinsan bazara tana da saka kasala, ga abincin ki nan a Kan dining ko Nan Zan kawo miki?"
"A'a barshi a can kawai naje naci Wai me Kika dafa need? Allah yasa Zan iyaci ni har cikina bana Jin dadinsa tun jiya".
"Allah ya saukake ko Asibiti zamuje ne?"

Dan yatsina fuska zahra tayi.
"Kai haba daga dan rashin dadin ciki sai mu Kama tafiya Asibiti".
"To na sani uwar dakina ko Allah ya kawo Mana abinda muke nema, ai bazamuyi Wasa ba".
Rufe Baki Zahra tayi da hannu tana dariya.
"Kai Aunty zilai! Ki rufa min asiri ni ai ban isa wannan sabgar ba".
Itama dariyar tayi tana fadin.
"Bangane Baki isa wannan sabgar ba? kina nufin kallonki yake shi yallaban?".
"Gaskiya dai kam, to me Zan masa".
Kafin zilan ta Fadi abinda tayi niyya sukaji Karan door Bell, da sauri zilan ta fita ta nufi kofar,zayyan ta gani lokacin data bude Yana tsaye, sannu yayi Mata tunda sun gaisa lokacin data Kai Masa break fast dinsa.
"A fadawa madam ta duba wayarta oga Yana kiranta".
Ya fada Yana juyawa, ya koma bakin aikinsa.
"Da sauri Aunty zilai ta koma kitchen din tana fadin.
"Uwar dakina kije ki duba wayarki yallabai yanata Kira bakya kusa sai mutumin can ya Kira ya fada Miki ki duba Yana Kira, Dan Allah ki ringa tahowa da ita idan Zaki fito tunda kinsan mijinki baya kusa ai Kullum ta Zama ta katararki duk lokacin Daya Kira kinya samu" .
Tashi tayi tana fadin.
To in Sha Allah Zan kula nagode Aunty zilaina".
Ta fita ta nufi bedroom din.
Tana shiga bedroom din wani Kiran Yana shigowa, video call ne tunda gidan nasu suna da Wi-Fi.
A cikin wani irin shauki ta dauki wayar ta dauki Kiran.
"Amincin Allah da Rahamarsa su tabbata a gareki".
Ya fada yana Mata wani shu'umin kallon Daya sakata Jin wani irin Abu a ilahirin jikinta.
Lummm tayi da idanunta tana Masa kallon kasa-kasa, sannan ta bude Dan bakinta Wanda yake ta walainiyar lips glow a hankali ta furta.
"Tare da kai".
"Nagode, meye labari? Naga alama previous ba kiyi missing dina ba dubi fa yanda Keke Kara wani fresh dake Kamar wadda..... Bari dai kada na Bata show din,me Kika dafa Mana?".
"Nifa yanzu na tashi bana Jin Dadi fa tun jiya da dare cikina ne Sam bana Jin dadinsa, bana Jin Zan iya cin Abinci ma kwata-kwata".
Dan tsareta yayi da idanunsa da suke sakata nutsuwar dole.
"Wane irin ciwon ciki kikeyi? Irin Wanda kekeyi suk ending din month ko Kuma wani ne daban?".
Dan narai-narai tayi da Ido tana Masa wani kallon Nima ban sani ba.
"Please precious kada ki daga min hankali wane irin ciwo ne wannan da baya tashi sai bana nan".
"Bafa shi bane babu ciwo ko kadan, kawai dai cikin ne babu Dadi".
"Are you sure?".
Kai ta gyada Masa tana jujjuya masa golden sexy eyes dinta.
Sun Dade suna hirarsu wadda ta saka kowannensu cikin nishadi da son Jin Dan uwansa a kusa dashi, Koda zahrar ta fito Aunty zilai taga canji sosai a tare da ita, ba dai tayi magana ba.
Nan cikin parlour aka kawowa zahrar abincinta na Breakfast taci.
Suna zaune suna Hira aka Kira Aunty zilai a waya sunan sahura ta gani, dauka tayi tana Mata sallama.
Daga can bangaren sahura ta tambayi zilan Ina ne unguwar da Zahra take Hajiya Mama ta bada sako a kawowa zahra.
Dan shiru Aunty zilai tayi kafin tace

Wallahi ban San sunan unguwar ba Amma ki nemi magaji ya kawo ki tunda yazo sau biyu.

Sukayi sallama Aunty zilan ta cewa zahra "uwar dakina wai Hajiya Mama ce ta bada sako sahura ta kawo miki wai nayi Mata kwatancen gidan shine nace ta nemi magaji tace ya rakota".
Shiru zahrar tayi tamkar Ruwa ya cinyeta, take gargadin mahmud ya dawo Mata a cikin kwakwalwarta.
"Kada ki yarda da kowa a gidanku idan ba Ammah ba, ba ruwanki da Mama Koda shiga dakinta da gaisuwa ban amince ki mu'amalance ta ba duk abinda ta Baki kada kiyi amfani dashi ko kici"
Da sauri ta Tashi ta nufi daki tana ayyana Bari ta Kira magajin tace masa kada ya kawo sahura idan ta nemi ya kawo ta yace sun koma kano, tun jiya da aka tafi da Baba malam.
Ta rasa meta tsarewa Mama a gidan duniyar Nan taki jininta ba kadan ba, to ko da abinda meu Amor ya sani ne akan Mama Wanda ita Bata sani ba yake ja Mata dogon warning akan kowa Dan har Aunty zilai Saida ya shata Mata wasu layuka yace kada ta wuce su a mu'amalarta da ita.

=؞?
* AUREN HUCE HAUSHI *



Maman Fateemah



Page 63.



............ cikin sa'a zahra ta Sami magajin a wayar, tsokanar ta ya fara.
"Dan Allah ka tsaya ka isheni da magana, kanaji Wai sahura ce zata tambaye ka Ina na koma kada ka fada Mata kace Mata bana garin kawai".

"An Gama yallabiya, kinsan bazata Fara ma tunkarata da wannan maganar ba, ba sakar Mata fuska nakeyi ba tunda na gane ita munafuka ce"
Tsaki zahra tayi.
"Can ta matse musu duk munafurcin mutum sai dai ya koma Kansa babu abinda ze sameni sai abinda Allah ya hukunta min, Wai sako to sakon me? har wani abun arziki Mama zata taso mutum ya kawo min wadda ko kallon arziki baya hadani da ita saboda tsabar kin jinina da tayi".
"Share kawai bakin ciki ne taga Allah yayi halitta a Nan take hasaada saboda nata 'ya'yan Kamar ka yanka ka boye wukar, Ni bansan wace kaddara ta Kai Abba Aurenta ba, duk matan jihar Nan Saida ya tsallake ya dauko ta Dan ma Allah yasa Basu da yawa da ansha kwantai".
Ya fada Yana wata dariyar rainin wayo.
Zahra ce ta katse shi tana fadin.
"Amma wallahi baka da kirki magaji 'yan uwanka nefa kake fada musu haka".
"Kema dai ai kinsan gaskiya na fada duba fa ki gani, kawai dai abar kaza cikin gashinta".
"Allah ya shiryeka wataran sai ka fada a gabanta, ta sauke maka ajja".
Tana Gama fada Masa ta yanke Kiran tasan sai su Kai minti goma shi ba gajiya zeyi ba.

Zahra Bata koma gurin Aunty zilan ba a Nan daki ta zauna, karatun Qur'an tayi sosai Dan Saida tayi surori da yawa, sannan ta shafa Addu'a ta tashi.

*
Sahura ce ta shiga dakin Mama Jiki ba kwari, ganin ta shigo yasa Mama tashi zaune tana fadin.
"Meya faru Kika dawo? na dauka yanzu kinje can din?"

"Eh naje Amma gidan babu alamun da mutane a cikinsa gaskiya. Dan idan ba idona ne bega dai dai ba babu wata alama data nuna giccin mutane ma a nan kusa a cikinsa, sai na Kirawo zilai nace ta fada min suna Ina ne, sai cewa tayi Wai ita Bata San sunan unguwar da suke ba tunda ba fitowa tayi ba tunda ta shiga gidan, Dan tsabar munafurci".
Ta fada tana aje kunshin kayan da za'a Kaiwa zahra.
Wata shariya Mama ta lafta tana fadin.
"Har yaushe raini irin wannan ya shiga tsakanina da zilai? Har ta Isa ta nuna min wuyanta ya Isa yanka, wallahi idan tayi Wasa saina yi mata sanadin barin aikin kwata-kwata, ai dama matsiyaci be iya cin arziki ba".
Hakuri sahurar ta ringa ringa bawa Mama ganin Nan da Nan ta ture sai masifa takeyi bakinta har kumfa yake fitarwa saboda bala'in da take kwasa .
Ita dai sahura sai abin ya daure Mata Kai, to menene najin zafi haka, dan zanyi maka Alkhairi anje ba'a sameka ba, ba sai nabar abuna ba ko na bawa wani tunda Inda nayi niyya ba rabonsu bane.

Cikin bacin Rai tace kije ko magaji ne ya rakaki Mana Zaki zo kiyi tsaye Kamar baki da wayo da dabara Dan Allah wuce a gurin".
Kayan ta dauka ta nufi kofa tana fadin.
"Bari naje na gani ko Yana nan din".
Ta wuce ta fita.
Zugum Mama tayi tana nazarin yanda abubuwa suketa lalace Mata, Wai yarinyar Nan me take takama da shine? duk abinda za'ayi da sunanta sai ya lalace,ko da tsiya-tsiya yau sai sakon Nan ya shiga gidanta duk Inda ta koma ma saina lalubo shi Dan wallahi bazanga bakin cikin da ze hanani barci ba.

Duk iya kokarin sahura na taga magaji abun ya gagara wayar zilan ma an rufe ta, ko Kuma network yaki bada hadin Kai.
Wata dabara ta fadowa sahura, da sauri ta nufi gurin Bala driver tana fatan samun mafita a gurinsa saboda Bata fatan ta rasa abinda Mama ta kwadaita Mata zata Bata.
Yana aikin goge mota da alama fita zasuyi da Abba, sallama tayi Masa suka gaisa sannna tace Masa.
"Dan Allah malam Bala ko zaka taimaka ka kwatanta min gidan da yarinyar Nan zahra suka koma naji ance sun tashi daga Nan hayin banki,Kuma na nemi duka lambobinsu ban samu ba".
Ta fada tana fatan samun abinda take so.
Tunda ta fara Kora bayani malam Bala ya dakata da aikin da yakeyi Yana kallon ta Saida ta Kai aya sannan yace Mata.
"Haba sahura yaushe Zan dunga bin diddigin yarinyar da take gidan mijinta, ai wannan rashin lissafi nema ma wallahi ai da kunya ki fito neman gidan Zahra a Nan gurin mu alhalin ga uwarta can a cikin gida, to ke me zakiyi a can Wanda Baki son uwarta ta sani".
Cikin rashin yarda da Kai ta Fara fadin.
" A'a wallahi kasan wani abun alherin idan mutum zeyi baya son a gani sai dai shi yaron ya fadawa uwar tasa daga baya".
"To shiga ciki ki nemi bayani dole"
Ya juya yaci gaba da aikinsa ya bawa banza ajiyar ta, it's Kuma ta koma ciki da ledarta a hannu, mita yake shi kadai.
"Haba mutane sai halin tsiya, Nan gaba kadan wallahi wannan mijin nata ze shayar da mutane mamaki Dan naji Alhaji Yana wani furuci jiya bansan dai dawa yake waya ba Amma Ina ganin da bincken da yake yi akan yaron Nan Kuma jiya Wanda ya saka shi ya dawo Masa da amsa".

Shi kadai yaci Baga da Yan maganganunsa.
Duk iya dabara Mama tayi Amma babu wani cigaba dole ta nufi bangaren Ammah.
Cikin iya makirci Mama tayi knocking a kofar falon Ammah.
Autane ya taso ya bude mata kofar, parlourn yasha gyara sosai sai kamshi ke tashi da sallama ta shiga, duk sai ta Raina nata dakin Dan babu karya ko yanayin gyaran da banbanci.
"Mama Ina yini".
ba zato Mama taji muryar magaji yana gaisheta daga bayanta.
Da sauri ta juya tana fadin.
" A'a Magaji! Daman kana gidan Nan tun dazu nake nemanka na rasa, Dan Allah tashi ka taimaka ka raka sahura gidan Zahra akwai wasu Kaya Dana saka a kawo Mata Amma shiru basuzo ba sai yau da safe shine nake son a Kai Mata su banso ko Ammah ma ta sani ba, sai dai zahrar ta Bata labari, to anje ance Wai basa gidan".
Zama magajin ya gyara, Yana kallon Mama Ido cikin Ido.
"Wai Mama kina maganar zahra ne?".
"A'a to da maganar wa nake maka".
"To ai Bata garin nan tun jiya suka wuce Kano, kinsa mijin nata baya kasar suna tare da Baba malam a India, to yafi son ta zauna a ca gaskiya, kin San manya Basu fiye son zaman gefe ba gara gurin da yake da kyakykyawan tsaro"
Rasa abin fada tayi, ta rasa zancen wa zata Kama na magaji Kona zilai data ce Bata San unguwar da suke ba, kenan ba'a garin Nan ba kenan take nufi,ai da mamaki Daman Ace Wai zilai Bata San sunan unguwa a garin Nan ba, to Wai waye ma babban da taji magaji ya fada shi yaron ko Kuma waye?.
Tunda magaji ya Gama fada Mata abinda zahra ta fada masa ya koma yayi kwanciyarsa, yaci gaba da latsa wayarsa.
Fita tayi daga parlourn ta koma nata part din duk dabara takwance mata Kuma Bata taba zaton wankin hula ze kaita dare ba sai yanzu, tana fita Ammah na shigowa.
Magaji Ammah ta kalla tana fadin.
"Waye ya fita yanzu?"
Tashi zaune sosai magaji yayi haka Musaddiq ma matsowa yayi tana fadin.
"Ammah Wai Ya magaji yaje ya raka sahura gidan Adda Zahra".
Gyara Zama magaji yayi sosai Yana fuskantar Ammah.
Kinsan wani Abu Ammah Anya zahra Bata San wani abu ba game da maganar zuwan da sahura ba zatayi ba? saboda ina zaune Zahra ta kirani ta kada min warning akan kada na kuskura na kawo sahura inda take, tace min na fada mata Bata Nan sun koma Kano, to yanzu magamar ce ta kawo ta wai na dauki sahura na kaita gidan zahra zata kai Mata sako shine nace Mata ai sun koma Kano".

Jinjina Kai kawai Ammah tayi tace.
"Allah ya kyautata".
A binda ta iya fada Kenan tayi gaba abin ta, ita lamarin Mama har ya daina ma Bata mamaki tausayi take Bata hassada ai mugun ciwo ce.

*



Sai kusan Sha biyu na agogn kasar India Habib ya tashi, yayi mamakin yanda lokaci yayi gudu haka, da sauri ya nufi toilet Yana yiwa Kansa fadan me kenan yayi shida ya biyo marar lafiya Amma ya bige da dogon barci irin haka, "ko Yaya Baba malam din yake?" Ya yiwa Kansa da Kansa tambaya.
A gaggauce yayi wanka ya fito, Bai wani Bata lokaci ba ya shirya ya fito yana ayyana Allah yasa Mahmud ya dawo Dan jiya sun Dade suna dakon zuwansa Amma shiru dole suka hakura suka kwanta.
A parlour ya iske mahmud Yana ta faman aiki a cikin computer desktop wadda take girke a parlourn, daga gefe Kuma wasu indiyawa ne su biyu Yana musu magana da harahen indianci suna amsa masa, da alama Kamar Umarnin wani Abu yake basu, har Inda yake zaune Habib ya Karasa yayi Masa sallama ga mamakinsa sai yaji gaba Daya sun amsa masa, Shima Mahmud barin abinda yake yayi ya juyo Yana sakin murmushi ya mikawa mahmud hannu sukayi musabaha, sannan ya mikawa bakin mahmud suka gaisa, ganin Kamar Habib na dari-dari dashi dan Yana kula da yanda yake tsare shi da ido, sai idan yaga zasu hada Ido yayi saurin janye nashi, tashi muhmud yayi daga Kan computer ya riko hannun Habib Suma sauran biyun suka rufo musu baya.
"Bakon india, nasan ka gajine shi yasa na Hana Abubakar tashinka nace ya barka kayi barcin gajiya tunda ka gaji da yawa".
Ya fada suna Zama a kujera two seater,
"Bari kawai ni kaina nayi mamakin barcin da nayi, Ina Abubakar ne?".

"Sun fita da Mr Ajey kasuwa, inaga sun kusa dawowa ma yanzu, ga abinci nan kaci idan ka gama zaku fita dasu Mr Salman zasu rakaka kuje a Sami kayan sakawa tun dazu suke jiran ka fito ku tafi baka tashi ba, ga abincin can ka duba Wanda zaka iyaci sai ku wuce, nima Zan shiga naga doctors din dake kula da Baba malam yanzu suka nemi ganina tunda tun jiya suka shiga dashi dakin bincike na musamman sai gobe za'a fito dashi, kasan tsare-tsaren Asibitocin su da banbanci da namu na Nigeria"..
ATM mahmud ya mikowa Habib na bankiya juya Kuma yayiwa su Mr Salman maganar da Habib besan me aka fada ba, ya wuce ciki Yana fadin.
"Kada ka dauko kaya kadan Dan bamu San how long samu zauna a Nan ba sai yanda Hali yayi".
Shi dai Habib kasa cewa komai yayi Dan ya gama Shan ruwan mamaki ba kadan ba, Mahmud din da suke kwana su tashi tare ne wannan? ko a mafarki be taba kawo haka ba".

Cikin abinda be wuce minti latatin ba Mahmud ya fito cikin kananun Kaya yayi fresh dashi ya fice daga gidan, har lokacin su Abubakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login