Showing 207001 words to 210000 words out of 280244 words

Chapter 70 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1058

Gama bani zahra Alkhairin mu ce".
Kayansu aka dunga jida ana kaiwa mota Sameer sai mita yake yiwa Aunty Aishat akan sun lodo Kaya bayan Wanda suka turo jiya sukazo yauma ga wasu.
Kunnen uwar shegu tayi masa sufa sunfi son daga su sai kayan jikinsu, tunda suka dauko hanya zahra ke kallon garin, yayi matukar burgeta ba kadan ba tayi santinsa duk da hankalinta ba a kwance yake ba Amma ba karya sokoto tayi Mata =د?% sai dai Bata San meze biyo bayan zuwan nata ba, wata zuciyar ta fada Mata.
"Khairan in Sha Allah"
Take ta Fara addu'ar sauka a sabon garin da kaje ba garinku ba, Dan harga Allah ta manta.
"RABBI ANZILNI MUNZILAN MUBARAKAN WA ANTA KHAIRUN MUNZILIN".
Ta fada a zuciyarta tana rokon ubangiji ya dafa Mata a cikin lamuranta gata ta shigo garin da babu uwa ba uba ba dangin iya babu na Baba sai wannan bawan Allahn shi kadai ta sani, kallon garin taci gaba dayi daga kasan Zuciyar ta Kuma abubuwa ne rututu gasu Nan.
Wani katafaren gida taga Sameer ya dosa tamkar fadar shugaban kasa, Zahra hankalinta ta tattaro ta nutsu taga Nan kuma Ina ne Sameer ya kawo su Yana tsayawa a kofar katafaren gate din Mai Kama Dana kofar gari saboda girmansa wasu masu uniform suka taso su uku suka Karaso gurinsu Sameer kafin su Karaso sameer ya sauke glasses dan bada da baya,suna sameer ne suka gaisa sannan suka gaisa da Aunty Aishat da suke zaune a baya.
Katafaren gata din aka bude musu suka shige, " masha Allah".
Abinda zahra ta fada kenan a zuciyarta, wasu gine-gine take ganowa kamar a cikin film, an kawa gefen titin da flowes masu kyau da fitilu compound din ba mutane sosai sai 'yan tsiraru masu banruwan flowers har kofar part din Ammi na baya sameer ya kaisu ita dai zahra ba baka sai kunne Dan ba karya gidan gida ne tamkar dauko ginin akayi aka Dora a gurin a zuciyarta take tunanin meya yi zafi da har Wanda yake rayuwa a nan ze tsallake ya bar shi yaje yana rayuwar kwanan shago, ita dai saida Aunty Aishat ta Dan tabata ta dawo hayyacinta.
"Mu shiga ciki?"
Fitowa tayi dauke da Afnan a kafadarta tabi bayan Aunty Aishar wadda me rike da hannun Abulkhairi, numbers Auntyn ta saka ta bude kofar Dan juyowa tayi kadan tana fadin "Bismillah".
A hankali zahra tabi bayan wasu parlours suka ringa ratsawa na garari sai da suka wuce parlour biyar sannan Aunty Aishar ta cewa zahra ta Dan jirata tana zuwa ta nufi upstairs tana rike da Abulkhairin.
A kan center carpet zahra ta zauna tana wasa da Afnan wadda duk tayi laushi ta gaji danma yarinya ce mai hakuri, dogon tunani zahra ta shiga bata taba tunanin maganganun Hajiyar makwarari gaskiya bane sai Yau wallahi duk a lokacin shirbtun tsufa ta dauki zancenta Ashe batama fada mata gaskiyar zancen ba.
A sama direct bedroom din Ammi Aunty Aisha ta nufa knocking tayi daga ciki taji Ammin na fadin "shigo mana batool kinsan bana son yawan damu da safe"
A hankali tura kofar ta shiga da sallama, ai Abulkhairi na ganin Ammi ya Zane hannusa daga na mamansa ya ruga ya rungume Ammi wadda tayi tsaye kawai tana duban Aishar Dan ba karamin mamaki ta bata ba."surprise ko Ammina?"
Ta fada tana shgewa jikin Ammin tana dariya.
"Kin kyauta kenan ki dauko jiki daga uwa duniya Amma bazaki fada ba ko Addu'a ayi muku sai dai ba ganku ba zato ba tsammani".
" Afuwan my Ammi nima bansan da tafiyar ba sai shekaran jiya waccan, kinsa dan gidanki baya jira".
"Ina kika ganshi ko kuma daman yana tare dake kika ki fada? Ina kuma Afnan din take?".
" suna master parlour da bakuwa mukazo fa".
"Bakuwa kuma?".
" Eh shigowa nayi na fada miki, to sannunku da hanya muje kasan a Samar muku abun break fast".
Suka nufo kasan takun takalmansu das das ya saka zahra dago kanta daga wasan da take yiwa Afnan tana bulbula dariya, caraf suka hada ido da Ammi nan da nan taji gabanta ya fadi, itama Ammi wani shock ta shiga babu ko tantama wannan fuskar take gani tare da Hussein dinta a mafarki yau gata a zahiri, tayi mafarkin yarinyar nan yafi sau shurin masaki me hakan ke nufi kenan.
Suna shigowa kamshin Ammin ya hade parlourn.
Zahra ba tayi tunanin haka zataga Ammin ba, babu Wanda zece ita ta haifi su Aunty Aisha sai dai ace yayarsu ce, 'yar gayu ce ta ajin karshe ga jindadin daya hana shekarunta nuna Kansu,a hankali take takowa idanunta na kan zahra wadda taji wata irin kunya ta rufeta, gurin da suke zaune Ammin ta karasa tana fadin.
"Sannunku da hanya, a kunya ce zahra ta bude bakinta tace.
" yauwa Ammy, ina kwana"..
"Lafiya kalau ya gajiyar hanya?".
Ta fada tana mika hannu zata dauki Afnan, makalewa tayi a jikin zahra alamar bazata zo ba.
Gaba Ammin tayi ta zauna tana fadin huta roro waken gizo yaqi 'ya'ya".
Aunty Aisha ce dubi Ammi tana fadin.
" Ammi ga zahra nan 'yar Amanar Hussein diyar mai gidansa ce bata da lafiya aka kaita India ganin likita shine yace na taho da ita Nigeria kafin yazo su 'yan jihar bauchi ne katagum local government sunanta Fateemah zahra".
Dan gyara zama Ammin tayi tana kara kallon zahrar from head to toe, haka nan taji wani Abu yana mata kai kawo a kasan zuciyarta.
"Sannu fateemah ya jikin naki?".
Kanta na kasa bata yarda ta dago ba ta amsa.
" Da sauki Sosai".
"Masha Allah, Hasana rakata sama dakin fake opposite da bedroom din ki bude Mata tayi wanka kafin a hada muku breakfast".
" To Ammi bari muje,ko kuma muje can gurina saita zauna tunda duk cikin part din nan ne".
Kaita girgiza "kaita sama inda sauran 'yan uwanta yara suka can gurinki ba zataji fadi ba nan kuwa gasu Batool nan kuma ba kince bata jin dadi ba sai saida babba a kusa maza kuje lokaci yana tafiya gara taci abinci ta kwanta ta huta tunda ba irin ujilarku ta iya ba".
A kunya ce zahra ta mike tana sabe da Afnan.
Saida suka bacewa ganin Ammi sannan ta dauke idonta daga kallon zahra.
" ya rabb kai kasan abinda ke boye da make nuna min yarinyar nan tare da Dana sauran sirrin kuma bani da masaniyarsa, ubangiji ka tsareni jin abinda ze zamar min tashin hankali".
Ya fada a cikin murya mai rauni.
Suna shiga dakin Aunty Aishat din tace "wow! Lallai matarmu you are special ai bansan haka Ammi ta hada wannan bedroom din ba, bari na sauka da wannan 'yar taki makale matar kawai"
Ta dauko ta tana kuka ta fice da ita, tana jin Zahra na magiyar ta dawo da ita tayi mata wanka Amma ta wuce kawai.
Lokacin da Aishat din ta sauko bata samu Ammi da Abulkhairi ba itama wata hanya ta nufa tana dan jijjiga Afnan.

Kafin minti arba'in an hadawa su Aishat breakfast mai rai da lafiya, zahra tana fitowa daga wanka tayi tsaye a gaban mirror tana kallon kanta yanda tayi wani irin kyau na ban mamaki wato Inda ake gyaran jiki anayi dan tamkar anyi mata wankan inji,lotion din data gani ta Shafa tunda nata da take shafawa yana can cikin kayansu ba'a shigo dasu ba saida ta gama shafawa tayi turus Ashe bata da kayan sakawa kuma gashi towel din jikinta ma karami ne kusan Rabin cinyoyinta duk a waje suke, gefen gado ta koma ta zauna ita dai bazata iya mayar da kayan data cire ba, dan kwanciya tayi a jikin pillow dan tunda tayi wanka wata irin kasala ta saukar mata ba, tayi minti biyu ba barci yayi awon gaba da ita.
Jin shirun zahrar yayi yawa yasa Ammi tacewa Aishat ta bita ta kirata ko nauyin saukowa takeji tunda taga yarinyar akwaita da kunya.
Sau biyu tana knocking Amma shiru, kamar ba mutum a dakin a hankali ta murda handle din ta tura kofar ganinta tayi tana barci,komawa tayi a hankali dan bazata so ta gashi taga ta ganta a haka ba, haba dole bros ya rikice musu Ashe shi yasan sirrin kayansa Ashe a fuska wasa ne, tasan Allah ne yayi mass tukuicin kazafin da akayi masa ya bashi irin wannan yarinyar.
Sai data fara gangarowa ta tuna Ashe bata da kayan sakawa a tare da ita.
"Ya salam! Wallahi shaf ta manta tunda su basa dauko kayan sakawa suna dasu a nan.

******

Saida Mahmud yayi barcinsa mai isarsa ya tashi, sau uku Hajiya Inna tana zuwa ta buga masa daki tana jinsa a rufe, wanka yayi ya fito cikin yadin filtex mai laushi fari tas, a parlour ya samu Hajiyar da Aminiyarta Innoni suna hira, kusa da Hajiya Innar ya zauna yana gaishe da innonin, kama haba tayi.
" kai kuma yaushe ka dawo garin namu?".
Tabe baki Inna tayi "kin gashi nan saida malamai suka?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? gama karbar nasu rabon ya mula ya Mile ya dauko jiki sinkin fakiti ya dawo, yazo kuma ya zaune min yaki ko leka kofar gidan nan, kofa gidan iyayen yaki zuwa ni naga ta kaina kasan da irin wannan ranar amma ka tsallake kayi naka guri sai yanzu zaka zo kana daddofar na kaika gidan".
Wata dariyar da bai shirya ba ta kubce masa.
" Amma wallahi matar nan kin gama dani ni zaki cewa ina kamun kafa fake ki kaini gida,ni kadai na fito ni kadai zan koma kuma kinyi da dan halak idan na fice sai kin shekara baki sakani a idanunki ba".
Ya mike ya nufi kofa, nan da nan Hajiya inna ta rude.
"Idan ka bawa Annabi daraja ka dawo wallahi wasa nake maka ga abincinka can kazo kaci".
Ya tsaya Amma bai juyo ba.
"A aje min idan na dawo zanci lokacin magariba ya karato masallaci zani".
Yana gama fada ya bude kofa ya fice.
" miskili kawai idan ba haka nayi masa ba ko gidan baze leka yau ba duk kuwa yanda yake da kawa zucin uwa".
"Ai mutumin naki sai ke".
Saida ya gaisa da masu gadi sannan ya shiga motar da yazo a ciki ya nufi unguwarsu tunda babu nisa daga unguwar su Hajiyar, yana shiga ana kokarin tayar da sallah da sauri ya shiga cikin masallacin gidan nasu tunda da alwalarsa.
Sahun bayan su Abbie dinsa yayi sallah da aka idar masu fita suka fita shi daman a dabi'arsu yawanci basa fita sai sunyi insha'i zirillahi yaci gaba dayi Abbie din bai juyo ba shima bai matsa ba sai Babban yayansu Ibrahim da yake daga jikin ginin masallacin ta kudu yake mamakin yaushe Mahmud din ya dawo kuma uncle saminu ya dawo dazu yace Mahmud ya gudu daga India, uncle mustapha ya bazu nemansa to ga Mahmud kuma a sokoto ga uncle mustapha ya sauka a abuja ze biyo jirgin karfe bakwai na dare zuwa sokoto to me kenan hakan ke nufi? Shifa daman ya dade yana zargin uncle saminu da wasu abubuwa marasa kyau a tsakaninsu.
Ana idar da insha'i Mahmud ya tashi ya fice kafin Abbie din su ya tashi, hannu kawai ya dagawa securities din ya wucesu suna faman murna dan sunsan kakarsu ta yanke saka mai yiwa dawa ruwa bare gashi a karkara,koda bayanan sakonsa yana iskesu to bare gashi ya dawo.
Ya dan jima a parking lot na gurin Ammi yana Karewa harabar gidan kallo ko ina haske ne tar ga wata iska mai dadi da take busowa cikin motar tare da kamshin furanni mabanbanta, abubuwan da suka faru suka dunga dawo masa daki-daki lumshe idanu yayi baiyi aune ba yaji ruwan hawaye suna bin kumatunsa abinda baiyi ba kenan duk badaqalar da aka sha a gidan nan a lokacin, kansa ya kifa jikin sitiyarin motar baiji alamun tafiya ko wani Abu sai dai jin hannun mutum yayi a bayansa bai dago ba, bubbuga kafadarsa yaji an fara kafin ya tsinkayi muryar Abbie dinsa yana fadin.
"Haba! namiji baya kuka tunda ka iya jure kwaramniyar baya baka nuna rauni ba yanzu lokacin fuskantar gaba ne taso mu shiga ciki kada kannanka suga kana kuka, su raina min kai".
Da Saudi ya dago jin furucin da bai zata ba daga bakin Abbie idan yayi la'akari da lokacin da guguwar abun ta tashi tsine masa ne kawai baiyi ba Amma yayi masa wata irin tujara ta Ala tsine uwar mai karya.
Jikinsa ya fada yana fadin.
" wallahi Abbie ban aikata ba! Ban taba zina ba, ka bani Qur'ani zan rantse da Wanda ya halicceni idan na taba zina a rayuwata Allah yayi min abinda yaso na azaba, ka yarda dani ka fadawa Ammi banyi ba sharri ne akayi min na fada Amma Baku yarda ba...kum..."
Sai jikinsa ya langabe ya saki.
Da sauri Ya Ibrahim dake tsaye a gefe Wanda shima hawayen yakeyi ya zaburo yana fadin .
"Suma yayi Abbie bari na samo ruwa"
Ya tafi da gudu ya haura steps din part din Ammi, suna zaune ya bude kofar afujajun baiko kalli su Ammi ba da saura yaran yayi kitchen da gudu ya dauko ruwan sanyi da sauri Ammi da Aishat da Batool suka rufa masa baya Ammi na tambayarsa menene? Bai ko juyo ba yayi gaba,suma gurin daya nufa suka nufa turus sukayi ganin Abbie a tsaye rungume da mutum Ya Ibrahim yana bulbula masa ruwan sanyi.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da shashsheka abinya yake fada yaci gaba da fada.
Ka fadawa Ammi ni ba nazinaci bane ban aikata ba".
"Pls kayi shiru mana ta sani ka kwantar da hankalinka bama zarginka kaga Amminka tana jinka fa".
Da sauri ya juyo sai kuma jiri ya kwashe shi ze zubar Ya Ibrahim yayi saurin rike shi suna faman jera masa sannu, juyawa Ammi tayi idanunta fal hawayen tausayin dan nata kenan duk tsawon lokacin nan yana fama da wannan damuwar wadda sai yau ya fasata gashi zata janyo masa matsala a lafiyarsa.
" Allah ka biwa yaron nan haqqinsa".
"Allahumma Amin".
Taji su Batool sun fada sai lokacin tasan a fili tayi addu'ar.
Su zahra na tsaye tana dauke da Afnan tun shigowar Wanda ya dauki ruwa ya fita su Ammy suka bishi taji gabanta yayi wata irin faduwa, ta mike tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kuma taga an shigo da Mahmud din a rirrike yana layi kamar Wanda ya bugu da kayan maye.
Ai bata San yanda akayi ba ta dira a gabansa jikinta yana wata irin tsuma cikin rufewar idanu da manta a ina ma take ne ta fara fadar
" Na shiga uku meya sameka meu amor...? Me akayi maka fada min dan Allah..."
Hannu Aunty Aishat da Dora a bakinta data bude tana fadin.
" kai? Wonderful...! the game is over".

* AUREN HUCE HAUSHI *

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.


Page 76.


.............. Aunty Aishat ce tayi sauri tazo gurin zahrar saboda kowa a gurin wutarsa daukewa tayi barema Abbie da Ya Ibrahim da Basu da masaniyar da wata bakuwar fuska a gidan, itama zahrar sai data fada ta dawo Cikin hayyacinta, wata irin kunya ce ta rufeta taji kamar kasa ta tsage ta shige Dan kunya, me tayi kenan shike Nan tayi abun kunyar da zata Dade Bata hada Ido da Amm bai wallahi.
Kan kujerar dake kusa dasu su aje Mahmud Wanda tun dirowar Zahra gabansa yaji wata irin Rahama ta saukar Masa a zuciyarsa badan a gaban iyayensa bane saiya Bata hot kisses na nuna godiyar nauyin data sauke Masa Cikin kankanin lokaci ta isar da sakon Daya Dade Yana tunanin ta Ina ze bullo musu Sai gashi in some minutes tayi musu aikin.

Aunty Aishat na rike da hannun zahra suka shige Cikin wani parlourn har lokacin jikinta Bai dawo normal ba, Afnan Auntyn ta karbe daga hannunta suka zauna.
"Ki nutsu babu fa abinda ya same shi inaga farin ciki ne ya sakashi sumewa, kinsan mutumin naki da kwakawar son iyaye kinsan kuwa haduwar ai Daman za'a iya samun irin haka".
Ita dai Zahra kasa daga Ido tayi ta kalli Aunty Aishar wannan abun kunya har Ina da farawa da iyawa ranar data sauka a ranar ta baza abin fada to Wai ita meye ya shiga kanta ne ta kasa controlling kanta a gaban mutane?.
Itama Aunty Aishat Bata dameta da yawan magana tasan tana Cikin Jimamin abunda tayi Wanda ya bude wwani murfin da suka kasa budewa sai gashi wadda aketa kunbi kunbiyar bayyana wacece ita tayi ta bude aiki da kanta ba tare da itama ta sani ba, ta Kara girmamawa girman Allah buwayi gagara misali Dan wani connection din idan aka hada shi sai dai kayi kallo kawai, tashi tayi fice ta koma can main parlour din.
Da Ido Ya Ibrahim yabi su Aishat har suka fice daga parlourn Yana kissima abubuwa masu yawa a cikin Zuciyarsa "kafa fa a gudu ba'a tsira ba".
Yayin da Ammi da Abbie suka dubi juna da alamar tambaya a fuskarsu, Ammi nayi masa wani duba na Mena fada maka?.
Aishat na shigowa Hajiya Inna na shigowa atfujajan uncle Mustapha na biye da Auncle Autan Hajiya Inna.
" Muhammadu Rasulullahi! Ni Hadiza Naga abunda ya isheni Ashe haka ka dunga gararamba yaron Nan a cikin kasar nan kamar marar gata? saida ubangiji ya tallafeka da mutanan kirki bayin Allah masuyi Dan Allah yanzu Nan Mustapha yazo min da wannan labarin daya jiyo gurin bawan Allahn Daya tsinceshi a yashe a kasa ko takalmi babu a kafarsa ko magana fa yace baya iya yinta a lokacin, wannan Dan taliki Ubangiji yayi Masa sakayya da gidan Aljanna, duk Kuma Wanda yake da hannu gurin neman tagayyara min rayuwar jika Allah ya wulakantashi tun anan duniya Kuma wannan yaron KAINUWA ne dashen Allah ba dashen mutane ne ba, ita Kuma sameera mun barta da Allah suje suji da abun kunyarsu munafukarkar banza da Ido kamar an rutsa mazuru a dakin tantabaru na godewa Allah da 'ya'yan da take haihuwa basa Zama da yanzu ta tafi tabar mana mugun irin".
Ammi CE ta matsa kusa da Hajiya Innar tana fadin.
"Ayi hakuri Hajiya ai komai ya wuce ki daina tada hankalinki saboda lalurarki Bata son yawan bacin rai".
"Yo bacin rai na nawa Kuma zainab ai saidai kada a Kuma".
Shi dai Abbie ya yayi shiru Yana jujjuya Lamarin a zuci.
Gurin Zama Ammi ta raka Hajiya Inna ta zauna kusa da inda mahmud yake zaune idanunsa a rufe.
"Kai Kuma menene haka ta wani kike Riga sharaf ka kuma Kama ido ka rufe sai qif-qif kake dasu kamar wani sabon makaho".
"Trouble

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login