Showing 126001 words to 129000 words out of 280244 words

Chapter 43 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1067

ba, yo wannan ai Bai kama kafar gidajensa na sokoto da Abuja ba, ni duk naje Kinga na Abujan,? ganin likita naje lokacin Ina ciwon kafa, na sokoton Kuma bikin kanwarsa wadda take a can Germany mukaje, wannan mutane da karamci suke, gashi kinyi sa'ar suruka Hajiya zainab Bata da damuwa ko kankani" .
Tsai Zahra tayi da ranta Kenan da gaske shi Dan Sokoto ne kamar yanda ya fada Mata sannan da gaske sunan Babar tasa zainab din Kennan lokacin da take fadar iya Abu yace ta daina fada gatsal sunan surukarta ne ta dauka Wasa yake Mata wallahi kenan duk abinda ya fada ba joking a ciki.
"To ai shike nan nayi zaton ko gidan na wani ne muka Mike kafa a cikinsa"..
'Ko alama ranar dasu Hajiya Inna sukazo ai nayi zaton fa a Nan zasu kwana gurinki sai Kuma suka juya surukar Taki ce Bata samu zuwa ba sai ita kakarsa da matar kanin mahaifinsa, ki yiwa Allah ki taushi zuciyarsa yayi hakuri ya koma gida tunda Naga alamar kece Zaki iya wannan jahadin, wani irin fushi yayi da kowa har Amminsa abin ya shafa ranar da nace Miki su Hajiya innar sunzo Saida Tasha kukanta a dakina, wallahi Banda idan na Fadi ga inda yake abin ze iya shafar tarensu da Sameer da saina fada musu kodan samun kwanciyar hankalin Ammin tasa tafi kwanan watanni Bata gidan ubansa saboda rikicin da akayi a gidan yanda mijinki ya fice yabar gidan itama ta fice ta bar musu gidan, abunfa Babu dadi kiyi wannan aikin ladan Dan Allah ko an samu kwanciyar hankali a zuri'ar su.
Ita dai zahra Banda gyada Kai babu abinda takeyi, Dan ji tayi abin yafi karfin dan karamin tunaninta.

('('('



AUREN HUCE HAUSHI.


MAMAN FATEEMAH

Page 46.


_______Sun Jima a gurin suna hira da Hajiyar tana Kara Bata labarin taren Sameer da Mahmud, anan tasan mamansa 'yar Niger ce Kuma cewa shi din da gaske twins ne su kamar na Ammah mace da namiji.
Suna nan suna hira har aka Kira sallah, da sauri Zahra ta tashi tana fadar "Hajiya Kinga guri Yana neman kurewa ban Dora miki abinci ba ko".
"Kinga dawo ki kaini inda zanyi alwala nayi sallah Banda kinibibi ki wani ce Zaki dafa min abinci, to Wanda Rahane da wannan yarinyar Dana gani akace tare kuka taho da ita Wanda suke faman aikinsa kuma ayi iri dashi? Ina fada Miki ki nutsu mijinki yawa ke garesu Kuma duk cikinsu mijinki daban ne sai kin koyi kamewa da gaske sannan Zaki fuskanci yanayin kowa Ina ke Ina wani dorawa Baki abinci banqiba dai in mijinki Zaki ringa yiwa wannan ba laifi,amma ba kowanne karabiti ba kice Zaki wani kama rawar jikin yi Masa, mujeni ki nuna min nayi dahara kafin a shiga sallah".
'yar Jakarta ta hannu ta daukar Mata suka nufi bedroom din da suka kwana.

Saida ta rakata har cikin toilet din ta nuna Mata duk abinda ya kamata sannan ta fito, sallaya ta shimfida Mata sannan ta karasa gyaran gadon da Bata Ida ba dazu ta saka freshner ta Daki ta rage karfin A/C din dakin. Hajiyar ce ta fito tana fadin "Ina dalili komai ya Zama na tab'e tab'e sai mutum yasha wahala kafin ya tantance yanda za'ayi"

Dan murmushi Zahra tayi "Haba Hajiya me yake da wahala saboda Allah?"
"Babu Miko min gyalena nayi sallah naji kamar an tada sallar"
Hijabin ta Mika Mata tana fadin "Bari naje na dawo ta nufi kofa ta fice.

Gaba Daya ta fice daga part din, ta cikin barandar Nan tabi ta shiga babban part din, ko Ina tadal sai sanyi da sansanyan kamshi ke tashi Nan ma wani bangaren ne daban da gyar ta gano inda ta kwana saboda duk gurin shine parlourn da yafi kankanta Amma yafi sauran tsaruwa, a hankali ta bude dakin ta shiga yana nan yanda tabar Shi direct bedside din ta janyo wayar na Nan yanda ta ajeta Saida kudin America dollars data gani a ciki shiya Bata mamaki Daman dasu a ciki ta saka ko Kuma daga baya aka aje Dan tab'e Baki tayi tunda ba matsalarta bace, gurin mirror taje ta dauko kayan da Aunty Rukayya ta saya Mata ta dauko luggage dinta ta zuba kayan ta duka ta fito daga ciki, a nan parlourn ta aje luggage din ta wuce ta ratsa duk parlours din Shiru ba motsin kowa, ta nufi inda su Aunty zilai suke Nan ma shiru, ta dawo kitchen Nan ma shiru abin ya Bata mamaki to suna Ina ne? Hanyar fita ta nufa sai Kara jinjina maganganun da sukayi da Hajiya takeyi abin yayi matukar daure Mata Kai shin abinda Hajiyar makwarari ta fada haka yake ko Kuma rudun tsufa ne kawai.
Cikin sa'a tana fitowa ta hango iya Rahane ta bullo ta bayan wani gini da wani babban basket a hannunta, ganin zahra yasa ya tsaya tana fadin "ai Daga can nake nayi zaton ko tare kuka fita Maida Hajiyar makwarari da shiga naji Shiru a gurin naku".

"A'a Iya Ina nan Hajiyar ma tana nan sallah takeyi Ina wuni? Wallahi tun dazu naso fitowa to saiga Hajiya ita ta zaunar dani sai data shiga sallah na fito".
'yar dariya Iya Rahanen tayi "Lafiya kalau ya jikin naki? Sai Kuma ga Uban gidan mu yayi Mana zuwan bazata ko? Masha Allah, ai Hajiyar sai ku kai almuru Bata gaji ba kin Sha labari dai Kam".
"Lallai kam nasha hira, Wai Kuna Ina ne? Na duba banganku ba a can".
Rike Baki tayi kamar yarinya " ke! 'yar Nan ki rufa Mana asiri, Banda dalilin wadalilatan Ina mu Ina kwana a bangaren yallabai, tun sassafe muka dawo nan kafin Rukayya ta tafi, Bari na yiwa zilan magana ko?".
"A'a mu shiga kawai".
Tare suka karasa shiga cikin bangaren. Masha Allah guri ne Mai kyau tamkar gidansu na Azare abinda ya banbanta su kalilan ne tunda wancan Renovation ne,wannan Kuma haka aka tsara shi sai banbancin furnitures kawai, nan ma question mark tayiwa abun.
Jin sallamar zahra yasa zilai fitowa daga kitchen din tana fadin "Masha Allah, wallahi jiya ban samu kwanciyar hankali ba Saida Rukayya ta shigo tace min kin wuce Daki kin kwanta har Ammah na Kira na fada Mata Baku dawo ba, tace min na kwantar da hankalina ba komai tunda bake kadai Kika fita ba, Kuma sai muka wayi gari da zuwan yallabai? Ai ya shigo shida oga Sameer mun gaisa".

"Eh wallahi muna cikin gari gidan Hajiyar makwarari kakar oga har dare, kunyi waya da Ammah kuwa yau?"
Saita share zancen Mahmud din.

"Eh mun gaisa tun wurin karfe shida na safe har take tambayar ya jikin naki tunda wayarki Bata shiga, nace mata da sauki amma dai kun wuni a Asibiti Dan sai wurin Sha biyun dare kuka dawo".
"Ok.ba damuwa Bari na bude wayar na kirata sai yanzu na dauko wayar, Bari na koma na baro Hajiya tana sallah inaga yanzu ta Gama kada ta jini Shiru amma dai Zaki zo can din ko?".

Ta fada tana mik'ewa tsaye.
Zaro Ido tayi Kamar wadda taga abin tsoro.
"A'a wannan fa Daya ai jiya ba yau ba, sai dai In da abinda za'ayi Miki ki fada min ta waya sai nazo nayi Miki".

Sallama ta yiwa Iya Rahane suka fito tare da Zilan, Saida sukayi nisa sannan zahra ta tsaya itama Zilan tsayawa tayi.
"Aunty zilai me Kika fashimta daga lokacin da mukazo zuwa yanzu?"
Zahra ta jefa Mata tambaya.
"To abin ne da yawa gaskiya, Dan ni lissafina ya kwance gaba daya wallahi na rasa tudun dafawa Amma dai komai rintsin mijinki shine ke Jan ragamar gidan nan Dan dazu lokacin da oga Sameer ya kawo Hajiya naji suna magana da wasu ma'aikatan gidan Nan akan oga yayi zuwan bazata, sai Kuma lokacin Daya fito a can gurin Naga ya Tara su yana magana dasu oga Sameer Yana gefe harya gama oga Sameer ya rarraba musu kudi muma har ya aiki wani Wanda Naga ya shigo da waccen babbar motar ya kawo Mana dubu ashirin ashirin nida iya Rahane".
Ajiyar zuciya zahra tayi tana duban bangaren motocin hango motarta tayi a cikin parking lot din, kenan a Nan ya ajeta ko kuma jiyan yazo da ita Nan Dan kamar Bata ganta ba jiya, rausayar da Kai tayi tana wani tunani kafin tace.
"Muje kawai Aunty zilai mu zuba idanu a hankali gaskiya zatayi halinta, nifa duk hankalina ya koma gida Amma naji yana fadin zasuje Azare jibi za'a dawo min da Aunty Rukayya, Kinga ba zancen komawar mu kenan, ni Kuma abinda bazan yarda ba kenan ya ajeni a wannan gjdan da bansan asalinsa ba gashi Nan Kashi-kashi kamar gidan marasa gaskiya".
"A'a kada kiyi haka ki Bari kiga iya gudun ruwansa Mana nasan dai baze cutar dake ba, to kiyi Masa biyayya a duk abina ze umarceki matukar Bai sabawa shari'a ba,kiyi hakuri wata rana ma garinsu ze koma sai kice bazaki bishi ba? ai shi aure ba inda baya Kai mace, ki duba Maman Akwanga kin taba cewa tayi rayuwar Azare".
Haka zilai ta dunga tausar zahra har suka shiga part din da suka zauna Zahra ta dauki luggage dinta Zilan ta karba suka shiga ta ciki suka fito barandar nan zilai sai mamakin abin take Bata taba tunanin da wani ginin a bayan wannan ba, Bata Gama sarewa da lamarin ba Saida suka shiga ciki, a parlourn farko suka tarar da Hajiya ta rabsa uban tagumi ta zubawa kofa idon suna shigowa ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "Haba 'yar Nan daga Bari na dawo Kika nemi gurin Zama Kika manta Dani saboda Allah kin kyauta min kenan? duk sanyi ya game min jiki har attishawa na Fara nasan mura Kuma sai abinda hali yayi kawai".
Da sauri zahra ta karasa kusa da Hajiyar tana fadin "Ayya wallahi nayi tunanin ko zakiyi nafilfili ne fa shi yasa na fita dauko wayata da kayana Dana Bari a wancen dakin, taso muje kici abinci kinji Hajiyarmu insha Allah bazakiyi mura ba, Aunty zilai Naga da kaji a can bangaren inda muka fito kiyi Mata irin pepper soup din da Naga kin yiwa Inna maimuna lokacin tana mura, ko a soya Mata ta tafi gida dashi".
"To in Sha Allah Bari naje ai kayan dazu wani mutum ya debesu ya mayar kitchen din part din da muka koma harma an karo wasu kayan masu yawa mun shafa'a mu nuna Miki su".
Ta fada tana mik'ewa ta nufi kofa ita Kuma zahra ta nufi dining ta daukowa Hajiyar abinci.



*** *** ***



Tunda garin Allah ya waye Mama ke faman Kai kawo a cikin Daki ta Kai gwaro ta Kai mari, tun bayan wayar da sukayi da Aunty larai hankalinta Bai kwanta ba sai yarfe gumi takeyi baji ba gani, ta Kira wayar Asabe yafi Shurin masaki amsar Daya ce switch off.
Wannan wane irin Abu ne Kullum tana tubkar gaba baya na warwarewa, Wai ita wannan Matar meta taka ne, duk abinda takeyi ya tashi a banza Kenan?
Tun bayan kaiwa Mai gadi sakon Nan Basu Kara samun damar shiga gidan Nan ba ko kofar ma tafi karfin zuwansu gashi yanzu Kuma aunty larai tazo Mata da wani Abun d'aga hankalin ga sako Amma isar dashi shine aiki ga wayar Asabe Bata shiga da sai ta Kai ko ta bayan gidan ne ta jefa abin bukatar dai ya shiga gidan ga sakon ya taho daga Jos din Kuma ance ba'a son ya kwana ba'a aiwatar dashi ba, akwai matsala Dan ze iya warware duk ayyukan baya, kuma wani aikin ze iya yin kome a Kanta ko 'ya'yan ta shine ta tada hankalin ta, tunda tasan idan tayi sake kwabarta ce zatayi ruwa, tayi tunanin ko sahura zata aika Tasha ta karbo sakon idan yaso sai tayi Mata bayanin yanda zatayi da sakon idan ta Kai can gidan zahrar, tayi tunanin ko zilai zata Kira tace Mata ta fadawa Zahra sahura zata je tayi musu share-share kafin su dawo, Nan ma taga abun ba lallai ya yuwu ba. Kara Kiran Asaben ta gwada still dai a rufe, dangwarar da wayar tayi duk abin duniya ya taru yayi Mata yawa.
Duk iya tunanin ta ya Kare ta rasa Ina ne mafita dole ta tashi ta fice daga dakin tana tunanin dole ta tura sahura taje ta Kirawo Mata Asaben in ba haka ba tasan watan Jin kunya ne yake neman Kama Mata.
Wannan kenan.

Tunda Ammah ta fita daga bangaren Abban take kokarin neman zahra Amma Shiru har bayan Azzahar inda taji Dadi da zilai tace Mata zahrar a gidan ta kwana Kuma Mai gidan ma yazo, tasan kome ne ne zezo da sauki. Banda kada yaron Nan Sameer yaga Kamar ta raina abinda yakeyi da yanzu ta tsufa a Kano, sakon text ta turawa zahrar ta tashi ya nufi bedroom dinta.




**** **** ****


Tun bayan fitar zilai zahra ta wuce bedroom tabar Hajiya nacin abincin ta, a gurguje ta sake wanka ta gyara jikinta Bata wani Bata lokaci ba ta shirya cikin wata doguwar Rigar lace cotton Mai kalar blue black, anyi touching dinsa da silver ash yayi Mata kyau sosai.Bata daura dankwalin ba rolling tayi da ash din gyalen ta feshe jikinta da turenta ita abin har mamaki yake bata, ta rasa yanda akayi duk inda take sai taga turaren da take amfani dashi a gurin. Dan watsa hannu tayi irin baka gane Abu ba din nan.
Parlourn ta koma gurin Hajiya dai dai lokacin da su Sameer da Mahmud suka shigo.
"Bakin Hajiya ne yaki rufuwa data hango zahra ta nufo ta Fadi take "Masha Allah! Haka ake so wwnnan 'ya naga alama bazakiyi saken da za'a karbe miki miji ba, ki Kama abinki ki rike wallahi sonsa akeyi kamar goron hannun sarki ki matse kayanki tunda Allah kadai yasan gwagwarmayar da yasha kafin ki shigo hannunsa..."
Sameer ne ta katse Mata hanzarin zancen data dauko ya Fara fadin "ki tashi na mayar dake gida garin Zan Bari yanzu Banda kina Nan da nayi nisa a Hanya".
Shi kuwa Mahmud Banda kallon zahra ba abinda yakeyi gani yayi ta Kare Masa wani sanyin kyau a idanunsa, Kuma fir Taki yarda su hada Ido dasu duk kowa da kalar kunyar da takeji tasa.

"Hajiyarmu ya zaman guri Daya nasan kin gaji sosai ko".
"Mahmud din ta kalla Wanda ya nufo ta.
"A'a ban gaji ba ai wannan yarinyar da Abun gari take, jiya ma dai an Bata Mata Rai ne yasa na ganta Kamar marar wayo Amma yau ai ka gani sai Ina taka saka Dani takeyi".
"Dan Allah ki taso bana son nayi dare a hanya ke Kuma kin tsaya sai maimaita zance kikeyi, abinda ya wuce ai ya wuce".
Da sauri Zahra ta juya ta koma ciki ta barsu Sameer nata yiwa Hajiyar Dan zance, turarika da sabulai ta daukowa Hajiyar ta fito, lokacin Hajiyar na gyara lullubin gyalenta tana fadin "ai Zan dawo ne tunda ban karbo Mata dawa'in Dana saka ayi Mata ba a sanka, Kasan duk wannan jidaliyar ta jiya Bata Hana da almuru Saida Tofeek ya kaini Sanka naje na fadawa Malam karami ya taimawa jikata da maganin tsarin jiki Dana Baki, yo anyi sake Baki ya Kamata dubi fa yanda take tubarkalla, yo tunda ya fito da ita Nan ai magana kuma ta gare haka ze dunga reto da ita,to kasan wani idon da bakin ba masu kyau bane, shi yasa gara a dafata daga Nan" shi dai mahmud ban kunshe dariya ba abinda yakeyi yasan kadan da aikin Hajjaju ne hakan, shi Kuwa Sameer ya cika yayi fam shi yayi Dana sanin kawota gidan nan Dan Allah kadai yasan abinda ta fada Mata tunda kanwa Bata jiqa a bakinta.
"Wallahi Zan tafi na barki a gidan nan haba saboda Allah kin kama zance kamar an saka Miki batir".
Dakuwa tayi Masa ungo Nan. Dan nema kake wani zaro min Ido to tsoron ka zanji kome? wato gaskiyar ce baza'a fada ba".
Juyawa yayi ya nufi kofa da hanzari Hajiyar tabi bayansa itama zahrar da sauri tabi bayan Hajiyar, ji tayi an riko ledar da hannunta gaba daya ya dawo da ita jikinsa.
"Precious ba irin huge din Nan na welcome saiki wani shareni"
Ya fada Yana Dan goga Mata sajensa a gefen kumatunta cikin wani irin low voice.
Wani yar taji a jikinta.
Cikin shagwaba tace "Dan Allah ya Bari na rakata kada su tafi ban Bata komai ba, Kuma na saka Aunty zilai ta dafa Mata nama".
Juyota yayi suna facing din juna. "Baze tafi ba kawai ya gaji da surutun Hajiya ne itafa Bata gajiya da magana, kawo na gani dame-dame za'a bawa kakar tamu?"
Ya fada Yana duba cikin ledar.
"Inye ashe dai da wayonki irin wannan Abu haka? jazakumullahu khairan. Bari na Kara gyara Miki kudi ya Ciro daga aljihun wandonsa ya saka a ledar Yana fadin sai kice ta sayi man shafawa ko kice ta sayi goro, bari mu dawo ki bani abida ya samu, Kuma idan anjima Zaki rakani gidan su Sameer na gaishe da mommy sannan muje muga Mai sunana"
.
Bai saki hannun nata ba, a haka suka nufi kofar fita.
Taso ta zame hannunsa daga cikin nata tasan ba Karamin aikinsa bane su fita harabar a haka, kuma taga alama gidan da mutane da yawa ga kuma Hqjiya da Sameer.
Ganin kada ya Bata kunya yasa ya saki hannun ya rike ledar kawai kafin taje gurin motar ta shiga gurin su Aunty zilai ta gani ko angama.
Cikin ikon Allah ta samu an Gama soya Mata cikin roba, Ashe Daman tun safe suka dafa aka saka a fridge yanzu soyawa kawai sukayi, a ciki babban warmer aka zuba zilai ce ta dauko suka fito suka nufi gurin da suke tsaye suna jiran zuwansu.
Saida Motar tabar harabar gidan sannan suka juya suka koma, Saida suka wuce idanun jama'a ya janyota jikinsa Yana shagar kamshin jikinta, a haka suka shige ciki zame jikinta tayi tana Dan dubansa. "ga abinci Nan na kawo maka nan ko can table Amuje".
Dan bakinta ya shafa kadan ka Yana kwaikwayon maganarta..
"Bari nayi wanka sai muzo muci abincin nasan kema bakici ba ko?".
"Kai ta gyada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login