Showing 153001 words to 156000 words out of 280244 words

Chapter 52 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1025

a dawo Mata da tata Mai aikin babu amfanin zaman kashe Zane a can.

Bayan sun gama da Auta Amatu ta Kira Saida tayi kamar Kiran ze tsinke sannan ta dauka.
" 'yar rainin hankali da bazaki dauki Kiran ba?"
Zahra ta fada tana murmushi.
Wayar Amah ta cire ta duba number sabuwa ce ba wadda take da ita bace.
"Zahra! Irin wannan surprised haka? Na nemeki yafi sau goma bana samunki naje har gidanki na dubaki da naji labarin Baki da lafiya, sai Wani guy na tarar yace min kinje Asibiti Kano, ya jikin? Ga Aunty safiya ma tace a dubaki".
"Da sauki ciwon mara ne irin na period fa shine duk ya tashi hankalin mutane shi sai an duba anga menene, shine fa ya saka aka tarkatoni kano, kinsan abinda ya daure min Kai Amah?".
"A'a sai kin fada min".
"Hummm! Bari kawai Amah Kinga wasu mahaukatan gidaje da yake yawo Dani a cikinsu, wallahi Amah tsoron guy din Nan nakeyi ba Wanda muka zauna dashi bane a Nan wannan wani ne daban,ko dressing din da yake Amah... Bari kawai gashi yace bazan Kara zaman Azare ba Wai sokoto ze kaini garinsu".
Wani kallon kallo sukayi tsakanin Amatu da Auntu safiyya, Aunty safiyar na Mata kallon Mena fada Miki.
"To ke zahra meye naki na damuwa inda me Kai ya nuna ba a Nan ake masa shukku ba? Inda yakeso ku rayu ba Nan ze ajeki ba, kice sai munzo Kano ko sokoto suna".
"Amah! Bazaki gane ba, yanda kike daukar abin ba haka yake ba, yafi karfin tunaninki fa. Nina fadawa Ammah ta taikama min ta fadawa Abba yasa Baki na dawo Azare,kinsan cewa tayi nayi hakuri na zauna inda yake so".
Aunty safiyar ce ta karbi wayar duk da a speaker take.
"Kina jina zahra, karki kuskura ki koyi yiwa mijinki gardama duk abinda ya fada kiyi Masa biyayya nasan har abada baze citar dake ba, ki saka a ranki Allah ne ya duba lamarinki ya hadaki da Mahmud, na sanshi Dan garin mu ne duk da shi ba sanina yayi ba. Baki da tantama a Kansa har gidan iyayensa na sani Zan iya kaiki har dakin mahaifarsa, ki nutsu ki rike Aurenki sauran bayani sai mun hadu Amma yanzu dai ki sakawa ranki hakuri kawai ba lallai ya amince ya dawo dake nan ba gaskiya".. sallama sukayi da Amah.
Tana kashe wayar Amatu ta kalli Aunty safiyar.
"Me Kika fashimta Aunty?".
Amatu ta tambayi Aunty safiya.
"Mefa na fashimta Banda abinda nake hasashensa tun ganina dashi na farko a gidansu na Nan garin, amma nayi mamakin yanda akayi hakan ta faru gaskiya, MAHMUD DANGE a nan garin a irin wannan rayuwar? Amatu kinsan waye guy Nan kuwa wallahi multi million ne ke ko body guard dinsa kike aure a kalleki a Kara bare Kuma managers dinsa, gaskiya Allah yayiwa zahra wata irin sakayya wadda ita Kanta Bata San gatan da Allah yayi Mata ba sai Nan gaba wallahi makiyan yarinyar Nan sai sunyi kuka da idaniyarsu".
Amatu jinjina kai kawai take Dan abin girmamemata yayi kamar a Almara Dan kwanaki Saida Aunty safiya ta nuna Mata hoton zainab a parlourn gidanta a Nan taga duniya iya ganinta, to marasa wadatar family din Kenan inaga Mai gayya Mai aikin Kuma?.
Bayan Gama wayarsu sakato zahra tayi,Wai Aunty safiya tasan shi, to meyasa lokacin da dukazo gidana Bata nuna ta sanshi ba,to ai tace shi Bai Santa ba, kenan duk abinda yake fada Mata Babu Wasa a ciki da gasken dai basakkwacen ne.
Haka ta zauna har gurin biyu, tayi ta neman Ummee Bata samu ba ta hakuri.
Bata girka komai ba da tayi sallar azzahar kasan ta dawo coconut cookies dinta ta dauko taci Tasha ruwa,kallo ta kunna ko banza ta rage zaman shiru.
Bata Jima da Zama ba taji ana Danna bell din kofa tashi tayi ta bude.
"Lah Aunty Rukayya Daman da gaske Zaki dawo?"
Zahra ta fada tana Bata hanyar shiga, Su biyu ne Ashe tare suke da wata buduruwa kamar sa'ar Zahrar.
Tunda suka shigo take kallon Zahrar da parlourn, Saida suka zauna sannan zahra ta gaishe da Aunty Rukayyar sannan suka gaisa da wadda sukazo tare.
Kitchen zahra ta shiga ta dauko musu abin motsa Baki da drinks.
Tana dawowa taga Aunty Rukayya na dariya harda hawaye. Ita Kuma dayar tana ta rokon Aunty Rukayyar da alama akwai abinda ta fad'a da yasa Aunty Rukayyar dariya.
"Meya faru ne Aunty, Naga kina dariya?"
"Bari kawai matar big bro, wallahi Asma'u ce ta bani dariya, Wai Daman ke bahaushiya ce, Kuma Dan tsabar kauyanci Wai ya akayi taga hadari da wata da taurari a saman rufin dakin Nan gashi ba dare bane Amma tana shigowa taga dare yayi".
Ta karasa fad'a tana kwasar wata dariyar.
"Kai haba Aunty wallahi Mai sunan Ammah bazatayi haka ba gaskiya ko Mamana? Ai ba kauyanci kikayi ba ki sake Nan gidan diyarki ne kiyi yanda kikeso ba kwab'a".
"A to Aunty Ashe ma mune masu gidan".
"Gaskiya kam ki mik'e kafa sai abinda kikeso za'ayi".
Zahra ta fad'a tana aje musu tray din a Kan coffee table.
Saida suka huta ana ta hira, sannan Aunty Rukayya ta cewa Zahra.
"Ga fa mai gyaran gashin nan da kunshin".
Bata fuska tayi.
"Gaskiya bana son kunshi sai gyaran gashin dai".
"Ok ba damuwa sai ayi gyaran gashin kawai, sama suka haura a can akayi Mata gyaran, Asma'un kamar ta mayar da gashin Kanta sai santinsa takeyi, har gurin magariba suna gidan, da zasu tafi Sha Tara ta arziki Zahra ta hadawa Asma'un har gurin mota ta rakosu sannan ta koma, har akayi sallar insha'i babu labarin Mahmud, Wasa Wasa har Sha Daya babu labarinsa a gidan, duk sai taji tsoro ya kamata ko ba komai namiji karone a gida duk da akwai Mai gadi.
Tashin hankali be gama samunta ba Saida taga Sha biyu ta wuce Daya ta kawo jiki.
Ta kasa zaune ta kasa tsaye, hankalinta In yayi dubu to ya tashi Ina ya shiga? ko Kuma ya gudu yayi tafiyarsa ya barta a gidan haya azo ayi bolinta da safe.
Ita dai barci Sai barawo Kiran sallar farko ta tashi figigit tana salati Dan mafarki tayi da Mahmud din a cikin wani yanayi Wanda ya tada Mata hankali.
Alwala tayo ta Fara jera nafila har akayi Kiran assalatu sannan tayi sallah ta zauna tana Addu'oi, har gari ya waye babu ko motsinsa a gidan, ko kasa kasa saukowa tayi ko break fast Bata sauko tayi ba, ta rasa wa zata Kira ta tambaya wayar Daya Bata ta dauko da sauri ta duba yace Mata Sameer kawai yake Kira da layin cikin ikon Allah taga number sa, da sauri tayi dialing number sai dai an fada Mata baya arear da yake da network.
Da kyar ta samu Tasha hollandia da biscuit's Wanda suka taho dasu jiya tunda a fridge din daki ta zubasu dazu da safe duk da an Sha dabi jiyan Kayan kwalama dai ba'ayi zuciya dasu ba.
Abu kamar Wasa har yamma babu labarin Mahmud ko a waya, zulumin duniyar nan ya Turu ya rufe Zahrar, taso ta Kira Ammah ta fada Mata sai Kuma ta fasa kada ta Zama marar sirri komai saita fada, tasan tana fada Mata zata tayar da hankalinta.
Har dare shiru number Sameer din ma taqi shiga, gashi Bata da number Fateeha a ka duk suna Kan layinta Wanda ya karbe.
Bata gama sarewa ba Saida taga Wani Daren ya Kara zuwa harya raba tsakiya, kukanta Tasha Dan nafilar ma kasayi tayi har kusan Asuba tana zaune ta Zuba uban tagumi ta rasa ta inda zata bullowa lamarin taga alama rufa-rufa ba zata yuwu ba saita fadawa wani halin da ake ciki.

AUREN HUCE HAUSHI.

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinqai salati da daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w .w.

Maman Fateemah.


Page 56.



_____Tunda garin Allah ya waye Zahra Bata sauko kasa ba tana sama snack kawai taci sai chocolate da Madara ta shiga hada kayan da mommy ta Bata da Wanda Fateeha ta hado Mata da duk abinda tasan tana da jibi dashi ta shirya tsab tana ayyana yau Kota halin Yaya saita bar gidan Nan Kano ai ba bakuwar ta bace,zatayi nisa da duk inda ake tunanin za'a ganta,daga Nan direct branch dinta zataje na bank tayi requesting din ATM sannan ta Ciro kudi tunda ya Maida ita faqarahun dole.
Doguwar rigar ta saka Egyptian tayi rolling ta dauki Jakarta ta hannu sannan ta dauko wadda ta Zuba kayanta saboda da gaske ba nan kusa zata Zauna ba Dan ya dauke Mata passport ai ba Yana nufi ze hanata abinda tayi niyya bane.
A hankali take saukowa daga saman har ta sauko kasa Wanda yayi daidai da Danna door bell din kofar falon jakar kayan ta aje taje ta waye yake kofar.
Tana budewa tayi arba da Zayyan Dan ta gane shi Sarai yanzu, gaisheta yayi, sannan ya Dora fa fadin.
"Oga ne yace bazo na mayar dake Nasarawa".
Ya fada yaja bakinsa yayi shiru.
Shirun itama zahra tayi gaba daya budget dinta ya rushe kenan? Ba yanda za'ayi tace ba zataje ba ina taga wannan courage din ita da aka sakarwa kare a gabansa wace fuffuka zatayi kuma.
"Ok ba matsala".
Ta fada tana juyawa gurin data ajiye jakar ta dauko ta fito, Ashe su biyu ne da sauri dayan ya karbi jakar hannunta lokacin Zayyan din ya koma mota ya dauko Wani Abu a Leda ya nufosu.
Madam bari na aje wannan sakon na kashe kayan wutar na fito mu tafi ya fada Yana shigewa da sauri, Wanda ya karbi jakar ya bude Mata bayan wata Mercedes Benz blue black sai sheki take a Rana da alama ma sabuwa ce.
Sai ta daidaita zaman ta sannan ya rufe ya koma ya saka jakar, Zayyan ne ya fito da sauri ya rufe kofar parlourn ya gangaro steps din ya nufo seat din driver ya bude dayan ma ya shigo, ya tada motar suka nufi gate, da sauri malam musa ya bude musu suka fice fit Yana fadin.
"Allah ya tsare".
Ita dai zahra lamura sun tsaya Mata ba haka taso ba, Saida suka fita daga layin na kusa da Zayyan din yayi magana.
"Kasan na hadu da Sauban last week a kaduna kuwa?"
"Kai haba dai"
"Wallahi a unguwar sarki suna siyar da breads".
"Siyar da bread Kuma".
"Wallahi kuwa kasan har hawaye yayi Daya ganni Wai Dan Allah na bawa oga hakuri ya daina abinda yake wallahi sharrin shedan ne ya tuba ya Dena".
Wata dariyar mugunta Zayyan yayi kafin yace.
Waya fada masa lahira ana Dan wake fada da
"Amma baka da man Kai na Fadi sakonsa ko?", "kace Nima ayi waje Dani kenan yanda oga ya tsani Zina ko sunanta baya sonji ai nasan daga ranar Nima zece halinmu Daya dashi".
"Ai Idan kana son ganin bacin ran oga kazo Masa da maganar matan banza yanzu zakuyi uwar watsi dashi ko yaya kuke dashi kuwa, katuna karonsu da oga Sameer? Ai wallahi nayi zaton da wasa yake Masa a Kan Fateeha Ashe da gaske yake Sai da aka ce an daura aure na Kara sarewa da lamarinsa".
Dariya Aliyu yayi.
"Ai lamarin oga ba sauki fa, Wai meya faru ne naji sagir nata bawa oga Sameer sakon bada hakuri gurin oga?".
Tsaki Zayyan yayi Yana kwafa.
"Bari kawai Aliyu wallahi sagir ba karamin marar tunani bane Wai kawai daga oga yace ya sako su little zasu yi masa gadi wai ashe shi dauka yayi irin masu kawowa oga kansu ne yake so ya koya mata hankali, tunda a bude take kowa ya sani oga ba mazunaci bane duk damar daya samu Yana da karancin shekaru kuwa yafi gane yayi azumi, idan Kuma abin Yana neman fin karfinsa yasha magani kawai, shi lokacin of a interrview zeyi da wata 'yar shegiya Dana kamo daga can Azare tana Zuba tsubbu a gidansa ta baya, wallahi naso a ranar ya barni na lakada Mata shegen duka, Amma kasan halinsa karshe ma kudi ya bada a Bata masu kauri amma da sharadin tabar garin in dai Dan babu take wannan aikin taje tayi sana'a, kasan Allah Aliyu Idan nine sai nasaka barbar yayi Mata katsa katsa yanda a gaba idan taga Wani zeyi ta irin abinda tayi ta bashi labarin abinda akayi Mata sanadin munafurci".
Ita dai zahra tunda suka Fara labarinsu taji hankalinta yayi matukar tashi kenan abinda take zargi ba haka bane, to wacece aka kamo daga Azaren kenan baya so taga ko wacece yasa aka sakar Mata karnuka, ji tayi wani jibi ya rufeta.
Take ta Fara wata irin nadama tayi Masa cin fuska na karshe akan abinda wataqila saboda ita yake yakin, ita Ina hankalinta ya tafi a lokacin. Innailaihi!.
Wato hikimar Ubangiji da yawa take, su hirarsu sukeyi ita kuma ta zamar Mata mabudin abinda ya shige Mata duhu ne, ya tsani ko Mai yin zina Yana raba jaha dashi ko sunanta baya kaunar ji to kenan ranar data dubi tsabar idonsa tace Masa FASIQI Yaya yaji a zuciyarsa? Kenan shi yasa yayi tafiyarsa ya kyaleta?.
Har sukazo Sultan road din Bata sani ba tayi zurfi a tunani, Saida taji anyi horn sannan ta ankare da sun karaso.
Har kofar sabon gurin Zayyan ya kaita ya Parker motar ya fito da sauri ya bude Mata, jiki ba kwari ta fito da sauri Zayyan din yaje ya bude Mata parlourn ya dawo Yana fadin.
"Bismillah, oga yace a fada Miki ki bude wayar hannunki".
"Ok in Sha Allah, nagode kwarai".
Tayi gaba da sauri ta shige tana Jin takun Zayyan din daga bayanta ya shigo da jakar. A Nan ta Zauna Kamar kazar da kwai ya Mace Mata a ciki, tasan maganar ta bude waya kawai ba da kafa ne kada Zayyan din ya Dora alamar tambayar rashin fada Mata zezo daukarta.
Tana shiga parlourn ta tsaya cak Dan Wani irin gyara akayi Masa na fitar hankali, ba Dan taga gurin daga waje ba zata taba yarda inda ta Zauna bane, mamakin duniyar Nan ya rufeta Wai shi wane shine Dan Allah? tana bukatar ya magantu kafin kwakwalwarta ta samu matsala, ita dai tasan mijinta Almajirin malam ne, Amma wannan Bata gane waye ba.
Bata Jima da Zama ba taji alamun taba door bell din kofar, tashi tayi take ta bude Aunty zilai ce a tsaye, tayi wani tas da ita a 'yan kwanakin da tayi Bata ganta ba.
"Masha Allah uwar dakin Kinga yanda Kika Zama kuwa? Kai Alhamdulillahi! Allah na gode maka yau ga 'yar da mahassada suka tauye a baya yau ta zama sararin samaniya wadda tayiwa yaro nisa sai dai ya tada Kai ya gano, kin zama murucin Kan Dutse Baki fito ba sai da Kika shirya, Ubangiji ya tsare gabanki da bayanki ya yiwa rayuwar Aurenki Albarka ko yanzu na koma ga Allah baurina ya ciki Allah ka dubi maraicin yarinyar nan".
Sai hawaye.
Matsa Mata hanya Zahra tayi, ta shigo tana share hawaye.
"Haba Aunty zilai meye na kuka Kuma ai ba Bata nayi ba Nima kina raina wallahi wayar tawa ce ya karbe tana gurinsa".
"Ba kukan takaici nake ba, kukan Dadi ne yanda Allah ya rufa Miki asiri nake godewa Allah Kinga yanda Kika Zama kuwa? Wallahi kamar kasar Kika Bari ai Allah ya sakawa Alhaji da malam da Alkhairi ya biya musu bukatunsu na Alkhairi Dan su suka kulla wannan Alkhairin, kinsan kuwa yanda mijinki ke sonki? Jiya wuni guda ana aikin cikin bangaren Nan sai da aka canza komai, Ni nayi zaton ma ko yau zasu dawo daga Niger din Ashe ke akewa hidima".
Ta fada tana Zama a Kan center carpet Mai laushi.
"Haba Aunty zila ki tashi daga kasa ki Zauna magana zamuyi dake wadda ko Ammah Bana son taji".
"Ba komai ba Saina hau sama ba Ina saurarenki".

"Yaya za'ayi ki Samar Mana hanyar fita daga gidan Nan wallahi Ina Jin kunyar haduwa dashi idan ya dawo nayi Masa rashin kirki ba kadan ba Wanda har tasa yace min baya Sona kunya kawai tasaka ya barbeni a matsayin Mata shine nake son nayi nesa dashi nasan ko yaci gaba da Zama Dani sai don kunyar su Baba malam badan so ba, tun ranar da abun ya faru ban Kara ganinsa ba har yanzu ko waya baya mini bansan ma inda ya tafi ba sai yanzu a bakinki".
Nan da Nan idanunta suka ciko da ruwa.
Shiru Aunty Zilan tana kallon zahra abinda ta gani a ranar da sukaje gidanta da sahura ya fado Mata a Rai ko dai Bata yarda dashi bane har yanzu?
"Zahra ki nutsu ki bi mijinki kowa da haka ya girma, ko dai har yanzu Baki bashi hadin Kai bane, har Kika tunzura shi yayi Miki kaura?".
Ita kunya ma maganar Aunty Zilan ta Bata ta rasa me Zata ce Mata kuma.
"Ba Wai so nake naji meke faruwa ba Amma dai ki canza tunani Ashe bazaki godewa Allah da tukwaicin da yayi miki ba idan na fitar dake kije ina? Da kike fadar kina Jin kunyar haduwa dashi bakin da yayi tsiwar shi ze bada hakuri, ai macece ke kinsan yanda Zaki gyaro kayanki baya sonki ya taso mutum daga jihar TAWA Dan kawai ya daukoki daga wata unguwar zuwa wata nasan ko rantsuwa nayi babu kaffara gyaran da aka yiwa gurin Nan ba kananun kudi aka kashe ba ki duba Nan, ki kalli can ki shiga dakunan barcin kiga duniya a baya sonki yake wannan rawar jikin a kanki eyeh?"
"Aunty Zilai bazaki gane ba nifa har yanzu bansan waye nake aure ba sai dai nayi ta Jin jita-jita a bakin mutane, yace min wannan gidan abokinsu ne Hajiya kakar oga Sameer tace min gidansa ne, tace Sameer yaron Mahmud ne to ta Yaya Zan samu nutsuwa yace min shi Dan Sokoto ne, Hajiyar ma haka ta fada min,gara muje gida yazo yayi musu bayani da bakinsa tunda Ni dake abinda muke gani daban abinda muka baro daban".
"Haba u????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
war dakina ai ba sai anyi Miki wannan aikin ba a dare Daya Zaki Gama abinki ta Ina Allah ya rageki ai ke kadai gayyace haba kada ki bani kunya Mana,ai yakin ko yafi haka nasan Zaki iya, Kinga yanda yake mini Ni kaina da yasan matsayina ba kowa bace face 'yar aiki, kinsan Kullum sau biyu yake Kiran Ammah Yana gaisheta, duk cikin rashin son ne?".
Rasa abin fada zahra tayi, jakar da Zayyan ya aje Aunty Zilan ta dauka tana fadin tashi na shigar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login