Showing 141001 words to 144000 words out of 280244 words

Chapter 48 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1048

Bata suyi magana Dan hankalinta ya kwanta".
"Ya salam Dan Allah ka bawa Amman mu hakuri laifi tayi min na karbe wayar, amma Zan Bata ita yau in Sha Allah, ai Zan shigo garin gobe ko jibi".
Tunda ta fashinci da Ya Abdul Hakeem yake wayar taji hankalinta gaba Daya yayi gida Jin cewa zeje Azaren bada ita ba sai taji duk ta shiga tashin hankali da gaske gida take son komawa, ta dauka da Wasa yake Mata lokacin da yace ze dauko Mata Rukayya idan zasuje Azare.
Wayar ya Mika Mata ya Mike ya fice daga parlourn gaba Daya.
Sallama tayiwa ya Abdul Hakeem din sannan ta gaishe shi.
Sannan ya dora da fadin "ga Ammah nason magana dake".
"Dan Allah Ya Abdul Hakeem ka Bata hakuri wallahi saboda bansan abinda Zan fada Mata ba na kashe wayar Allah ba yaji nayi ba, kaina ne yayi zafi gurin fa buduwarsa ta turoni Asibiti ita Kuma ta shiga wulakantani, Dan Allah ka rokarmin shi ya maidoni gida wallahi na gaji Ni tsoro nakeji bakaga irin gidajen da yake kawoni ba kamar baza'a mutu ba fa". Ta ida fada tana kuka.
Duk abunda ke wakana Ammah na zaune tayi tagumi tana Jin wani sanyi da tausayinta a Zuciyar ta, amman koba komai ta samu nutsuwa taji lafiyar ta sauran Kuma tasan shegantake ce kawai.
Wayar Abdul Hakeem ya mikawa Ammah ya tashi ya fice shima gara ya Basu guri su tattauna.
"Wai kukan Kuma na menene haka? ai kowa ya gyara ya sani kowa ya Bata ya sani, kiji tsoron Allah ki rike sirrin mijinki kinsan baqi kinsan fari keba karamar yarinya bace,saboda me Zaki tafi wani guri har ki nemi kwana bada izinin mijinki ba, haka kawai kin tashi hankakin jama'ar da suka daukeki da mutumci kin kyauta kenan? To wallahi kada na sake Jin wani Abu makamancin haka daga gareki ki nutsu ki rike aurenki kada na Kara Jin kin ambaci ya dawo dake nan, kinsan dai ba'a nan zaku dawwama ba ina cewa ya fada Miki garinsu wata Rana dole ze koma gida sai kice bazaki bishi ba? Akul na karajin magana makamanciyar wannan daga bakinki".
Tunda Ammah ta Fara magana Zahra ke shashsheka a hankali.
"Kiyi hakuri wallahi na daina bazan Kara ba, wallahi bansan laifin da nayi Masa ba ya dauke min wayar da passport dina har da kudi da ATM duka".
Salati Ammah ta dauka tana fadin "Ni Asma'u yanzu harda passport dinki Kika dauka dole ya kwashe wato guduwa kuka shirya zakiyi kibar kasar ko?"
Cikin gigita Zahra ta fashe Mata da kuka sosai tana Fadi "wallahi ba guduwa zanyi ba Daman suna cikin jakar fa".
Ji tayi an zare wayar daga hannunta Batasan lokacin daya taso ta shige jikinsa ba tana fadin "Dan Allah ka fadawa Ammah abinda take zargina dashi ba haka bane".
Ai Jin wannan furucin na Zahra yasa Ammah yanke Kiran cikin gaggawa.
Jin alamun yanke Kiran yasa shi Kara sakata a jikinsa baya son kukanta ko misqalazarratin.

AUREN HUCE HAUSHI.
(Maman Fateemah.


Page 51

=Ø‹??
___Dan murmushi Ammah tayi,koba ba komai ta Sami peace of mind, yanzu Bata da wata fargaba,zata Kira zilai ta fada Mata ta kwantar da hankalinta babu wata damuwa Zahra na Nan lafiya kalau ita dai tayi zamanta sai lokacin Daya bukaci su dawo sai su taho din kawai.
Tashi tayi da wayar a hannunta ta wuce Ciki tana Jin wata sabuwar nutsuwa tana shigar ta. Addu'ar da takewa yarinyar Allah ya Zama gatanta a dukkan al'amura.

***


Sun Jima a yanda suke ita Bata janye ba shi Kuma be saketa ba, ajiyar zuciya kawai take saki a hankali.
"Wai me kika yiwa Ammah ne haka da zafi har kike neman bayi Miki shaidar zur".
Tsuntse idanu tayi sai wasu hawayen. "Ya salam! Pls bana son kuka sam, ki adana abinki Mana Yana da lokaci, ai kin gane?".
Shiru tayi masa, me zata fad'a Masa tace Ammah tace Mata niyyar guduwa take yi.
"Pls ki fada min Mana ko saina Kira na tambayeta laifin da kikayi Mata sannan zanji Kan maganar?"
Da sauri ta shiga fadar "wai fa Dan naje gidan su bestie shine take min fadan me yasa nayi yaji, shine na fada Mata ba haka bane".
Dago fuskarta yayi yaga yanda idanunta suka sauya kala daga farare zuwa ja.
"Shi kenan ai komai ya wuce tunda Nina janyo akayi yajin tunda na turaki gurin Haseena, nayi zaton zuwa yanzu ta aje maganar soyayya a tsakanin mu sai zumunci kawai, kiyi Hakuri nayi Mata last warning akan shirmen da tayi".
"Ni dai dan Allah ka maidani gida na gaji da garin kwata kwata".
Ta fada tana turo baki.
Baice Mata komai ba ya nufi one seater ya zauna ya dorata a cinyarsa suna facing din juna.
"Ki cire ranki da komawa Azare Saida ganin gida daga Nan sai Sokoto birnin shehu, kina tunanin Zaki koma can ne? Ai shi yasa nace a hadoki da house maid wadda take da Amana tunda a yanda Naga takunta zatayi amanar, shine dalilin da ze kaini can na fadawa Abban mu da malam Zan koma gida tunda the game is over, na samu a binda nake nema ai saina koma ayi wadda za'ayi ko?".
Ya fada yana dage Mata girarsa ta dama.
Wani ruwan idanunta suka kawo alamun zatayi masa halin.
Bata fuska yayi ya Zama serious din nan.
"Wallahi naga digon hawayenki saina sakaki kukan gaske, kuji min yarinya sai shagwaba, ai Naga kin Fara sallah gara na cire Miki yarintar Nan ko kin nutsu ki fuskanci aurenki, dan Naga alamar har yanzu Baki yarda da igiyar aurena ba a kanki tunda na kasa banbance Miki tsakanin Aya da tsakuwa ko?".
Mukus ta hadiye kukan tana qiqqifta Idanu, Jin ya b'aro magana, to a Ina yaga tana sallah har yake fada Mata hakan?.
Kafin ta samu zarafin magana wayar da take jikinsa ta dauki wani kidan larabawa Mai Dadi.
Dagawa yayi Yana fadin "ok gani Nan Amma ka tabbata komai ya Zama ready kafin na shigo, dan Allah kace mommy ta bani aron Rukayya ta shigo Nan Hausawa Bawo road ta Taya 'yar rigimar Nan Zama zuwa yamma, ka Bata address din gidan".
Ya fada yana sauketa daga jikinsa ya Bata light kiss ya manna Mata a saman goshinta Yana fadin "Zan dauki Aron motar ki na fita da ita kinji my previous, anyi min izini?
Kai ta gyada Masa tana fadin.
"Allah ya tsare".
Harya juya ya nufi hanyar barin parlourn ya dawo ya Mika Mata wayar hannunsa,.
"Kiyi amfani da ita sabon sim ne a ciki Sameer kawai nake Kira da shi kafin a kawo Miki Taki tunda na fadawa yayan mu yau Zan Baki wayarki".
Hannu ta saka ta karbi wayar iPhone 16 plus ce da sauri ta dago ta kalleshi alamar mamaki fal cike da fuskarta da kallon tuhuma Dan ba da ita tayi ways da Amma ba.
"Ya akayi Kika tsareni da kallo ko batayi miki ba".
Ta bude Baki zatayi magana ya daga mata hannu.
"Bari na dawo saina amsa tambayoyinki a nutse ai cewa nayi Miki aro bi kyauta ba ko?".
Ya fice da sauri, da alama uzurinsa Mai girma ne, tun bayan fitarasa take juya wayar a hannunta idan ba bataga daidai ba a mbc taga tallarta 1.48 million naira ne kudin ta in Nigerian Price.
To wai waye shi ne Dan Allah? Duk lokacin da wani Abu irin haka ya gitta a tsakaninsu baya yarda ya tsaya yayi Mata bayanin komai.
Ajeta tayi a gefen da take zaune ta Zuba uban tagumi da hannu biyu tana nazarin wasu abubuwan da take gani tun shigowar su Kano abun ya canza salo gaba Daya, ta rasa Wanda zasu tattauna da dashi Aunty Hussina ce to babu waya a hannunta ta mayar da kanta kurma.
Kamar an tsikareta ta Mike ta nufi upstairs da wayar a hannunta tana fadin Bari na Kira bestie musha hurar yaushe gamo da ita".
Duk yanda zahra taso ta fada Mata wani Abu Daya shafi Mahmud saita kasa fada Mata Kuma da alama Ummansu Bata fada Mata taje gidan ba koda wasa, saima wani abun mamaki da sajidar ta fadawa zahrar cewar Mahmud yace zasuzo har syprus gurinta tare Amma yace kada ta fada Mata, sun dauki lokaci suna wayar har sajidar ke tsokanar Zahra tana fad'in "ke Kullum canza layi kamar wata marar gaskiy".
Dan nisawa Zahra tayi kafin tace "ki Bari bestie kawai wallahi ba laifina bane shine yake kwace min wayar Kuma idan ya tashi Kuma ba ita Ze bani ba sai dai ya bani wata, jiya fa da muka fita unguwa ya shiga sahad na Nan zoo road muka hadu da Musbahu bakiga yanda ya yi, ba Banda Allah ya Soni ba da inaga sai yayi min duka ma da Allah yasa nayi tsautsayi munyi magana dashi".
Dariya sajidar tayi tana fadin Namijin duniya kenan Wanda ke kishin iyalinsa, nifa Daman harga Allah musbahun nan ba wani yi min yayi ba, kawai dai baka hana nutum abinda yakeso ne, Amma Ina hadin be hadu ba ko alama wallahi,ban qara sanin haka ba Saida sarkin yaqi ya bayyana".
Ta fada tana kyalkyalewa da dariya.
"Wallahi bestie Baki da kirki ki ringa Jin tsoro Allah, musbahun ne haka? Amma Ina cewa harda ke a masuyi Masa campaign a wancan lokacin"..
"Manta kawai bestie ya zaman past, yanzu ta Wanda Allah ya zaba Mana mukeyi, yauwa munyi magana da Baffa yace akwai saukar Alqur'ani da ake Miki in Sha Allah babu wani Abu daze sake tasiri a cikin rayuwarki in dai sihiri ne yace kiyi ta Hakuri mijinki Mai jama'a ne".
"Hummm! Bari kawai bestie nifa mutumin nan tsoro yake bani".
"Tsoro kuma? Kamar Yaya?"
Tsaki tayi kadan.
"Ba Zaki gane ba kwata kwata ba Wanda Kika zani bane wannan wani ne daban, kinsan ya maidoni Kano daga zuwa ganin likata yace nida Azare sai ganin gida, Kuma Kinga wasu mahaukatan gidaje da yake yawo Dani a cikinsu Kamar baza'a mutu ba wallahi, Kinga wannan wayar dake hannuna yanzu wallahi iPhone 16 plus ce ya bani Wai ga aro kafin ya kawo min tawa. Allah Lamainsa Yana damuna Kuma yaki yayi min bayanin komai sai sabgar gabansa yakeyi kawai"..
Tunda Zahra ta shiga bayani sajida ke murmushi Dan tasan za'ayi haka Ya Abba ya kirata dazu ya fada mata waye mijin da zahra ta aura kawai ya bada kafa ne wanda shima baisan dalilinsa na yin hakan ba.
"To ke meye naki na sai kin San waye shi yanzu kiyi Hakuri Mana ai yau da gobe tafi karfin Wasa ba dai Kuna tare ba, ai wata Rana gaskiya zatayi halinta abinda nakeso kiyi kawai ki saka a ranki mijinki ba macucin da ze cutar dake bane, Kuma bata haramtacciyar hanya yake samun kudinsa ba,Kika sani ko wani mashahurin Dan kasuwa ne Allah ya Baki".
"Kin jiki aikin fa NGOs fa yakeyi Dan dai wata tsohuwa ta fada min wasu maganganu Wanda ta sakani a confusing sosai".
"Ki manta kawai ki fiskanci zahiri tunda gashi gaki bada labari Kuma ai ya Kare keme reality a gabanki,kawai dai ki zama Mai lura da lamarinsa da kyau, kiyi kokarin Kare Masa Sha'awarsa kada ki zama lusara mijinki yaro ne Mai jini a jika Wanda Mata irinsa suke rububi Koda aure ko Kuma ayi shashanci gaskiya sai kin dage in ba haka ba garin kallon ruwa kwado yayi Miki kafa".
"Kamar Yaya?"
"Au Baki gane ba to ki ringa bashi hakkinsa Dan Naga alama kamar zakiyi son jiki ta wannan fannin Ni Kuma yanda nake ganinsa ba ragon namiji bane".
"Inna fatahana laka fatahan mubina! Bestie yaushe Kika Zama haka wallahi badan nayi Miki farin sani ba da cewa zanyi kina wata sabgar a bayan fage, to wallahi Ni har yanzu in nan yanda nake shi ba yanda kike tunani yake ba a Nan dai sai nace kinyi failed tunaninki ya kasa.."
Wata irin dariya tayi tana fadin Dan Allah mu koma video call Naga idanunki su kadai Zan kalla na tantance maganarki"

"Ba zanyi ba sai anjima tunda kin Zama abinda Kika Zama sai neman sauki gaskiya Ya Abdul Hakeem ya gamu da gamonsa a Ido kamar saliha nasan idan Kika shiga gidan sai yayi Dan wuya tunda Naga alama kina cikin.... Allah dai ya kyauta kawai".
"Kai! Sharrin da zakiyi min kenan shi kenan Zan rama".
Sun dauki lokaci suna Hira har sajidar ke fada Mata Hameeda ta kirata tana kuka akan abunda tayi Mata Wai Mama da Salma ne suka sakata, Bata gane kuskuren da tayi ba Saida ta dawo gida, abinda yasa suka samu sabani da Salma kenan har ita Hameedar tayi tafiyar ta Jos Saida zasu koma Jigawa sannan ta koma gida.
"Lah ki fada Mata Ni a gurina ya Dade da wucewa wayace lokacin babu a hannuna Dana kirata tuntuni Amma idan nayi waya Zan nemeta ai karo Daya masu magana sukace Koda kusa ai yi akeyi, Hameeda tawa ce".
"Kiyi dai taka tsan-tsan da lamarin ta kinsan ance jini yafi ruwa kauri duk rintsi ba zataqi uwarta a kanki ba, ko Zaki Kara karbarta kisan irin zaman da zakuyi da ita, Ni garama Daya daukoki daga can yayi maganin abubuwa da yawa wata qila Kuma da abinda ya lura dashi yasa ya yanke wannan hukuncin".
Shigowar su Aneesa dakin sun dawo daga lectures yasa suka canza akalar hirar sun gaisa da Zahrar suna ta korafin taji dadin aure ta manta dasu ko wayarta ba'a samu saboda tayi nitso cikin kogin soyayya, ita dai saikokarin Kare Kanta takeyi sajida na tayata.
Da haka sukayi sallama.
Aunty Husaina ta Kira itama tayi Mata nata fadar rashin samunta a wayar sannan ta Kara dubata da jiki tare da tambayarta yanda sukayi da Asibitin? ta fada Mata fada har yanda sukayi da doctor din, da Kuma maganin da Hajiyar makwarari ta Bata, sannan ta fada Mata abinda yake faruwa da ita a Nan kanon Bata rufe Mata komai ba, tayi mamaki kwarai sai dai tun farko Daman ta yiwa lamarin sa question mark, tun ganin irin kudin da aka narkar a kankanin lokacin gyaran gidan da aka bashi a nan Azaren.
Kamar hadin Baki itama Aunty Husainar cewa tayi ta Zuba Masa Ido ta Kuma yi masa biyayya, sannan sukayi sallama.
Kusan awa Daya da tafiyar Mahmud Zahra taji bell na Kara alamar anyi bako.
Saukowa tayi ta nufi kofar ta bude Aunty Rukayya ta gani a tsaye da basket din abinci a hannunta dayan hannun Kuma da karamar jaka irinta matafiya.

AUREN HUCE HAUSHI.

(Maman Fateemah)



Page 52



______

Cikin Jin dadi Zahra tayi zarya ta karbi jakar hannun Aunty Rukayya tana fadin. "sannu da zuwa Aunty Ni harna cire rai da naji shiru ga babu Wanda ze tabo min ke a waya tunda number ki tana Kan waccen wayar". Ta fad'a tana Bata hanyar shiga.
"Wowooo! Masha Allah, gaskiya Ya Mahmud Yana shagwaba ki yarinyar nan, irin wannan babbar harka haka".
Ta fad'a tana karewa parlourn kallo, handbag din dake hannunta ta aje tana fadin Ina zuwa ta juya da sauri ta koma waje, zahra na tsaye Aunty Rukayyar ta dawo da basket Babba fal Kaya a cikinsa ta shigo.
"Kai Aunty daga ina haka da wadannan Kaya?.
Zama tayi tana Kakabin haduwar gurin. Itama Zahrar zaman tayi kusa da ita.
"Bari kawai wallahi aikin mommy ne, daman ko Ya Mahmud be kirani ba Mommy zata tasoni takanas ta garin Nan na kawo Miki sakon nan, ai jiya Kuna barin gidan naji ta Kira Hajiya Salima 'yar Sokoto tana Mata wani bayanin dayasa na sulale nabar parlourn".
Ta fada tana dariya.
"Kamar ya Aunty?"
Wata dariyar tayi tana fad'in "ji nayi fa tana Kiran a Kara gyara Mata diyarta tasan Shirin wancen yayi sanyi tunda ta fuskanci diyar tata Bata Fara Amarci ba, Kinga kuwa ai Zama Bai ganni ba a gurin, Wai hadi za'ayi Miki bana Wasa ba"..
Hannu zahra ta saka ta rufe fuskarta wata irin kunya ta rufeta.
"Dan Allah bude idonki ni zakiji kunya? Ni nan Nima zuwa bayi na Dora Miki karatu Naga kin fiye Sanya ba wani abubuwa masu zafi da kikeyi ko wannan shigar batayi min ba, ki zage kina tsula fitinannun shiga wadda Zaki gigita Masa lissafi, humm wallahi Naga alama bakisanta true colour din ya Mahmud ba".
Da sauri zahra ta bude Ido tayi wuri-wuri tana duban Rukayya.
"Aunty waye shi dan Allah? Dan duniya ne ko?".
Wani sakaran duba Rukayya tayi Mata. "Amma ke wallahi anyi marar wayo, meya hada magana ta da bariki kuma? Allah yayi masa tsari da wannan sabgar, Kinga mubar maganar tunda kin Bata zancen sai wani jikon Kuma".
"Dan Allah Aunty kiyi Hakuri kiyi min bayani, a'a wallahi Naga alama sai an qara gasa Miki bakinki".
Ta fad'a tana janyo basket din gabansu.
Abincin da mommy ta bayar a kawo ta cire suka Kai Kan dining suka dawo wasu food flask ta Ciro guda biyu Daya kazace wadda aka dafa da saiwar Malmo sai kamshin spices ke tashi ga habbahan Nan guda guda a ciki.
Sai dayan wani irin romone na kwai da Albasa da wani Abu a ciki kamar hanta.
Sai Kuma wasu madaidaitan robobi masu kamar girman na swan medium, had'in Zuma ne pure da magunguna,sai wasu Kuma na tsimi da robobin gumbar aya da dabino, a hankali Rukayya ta shiga Yi Mata bayanin yanda zatayi amfani dasu wata Leda ta Mika Mata wannan Kuma da bayaninsu a cikin kowanne.
Ta karasa tana dariya.
"Wani bayanin sai a takarda ki duba koni ba'a fad'a min ba".
Rufe fuska zahra ta karayi tana fad'in, "nagode Allah ya sakawa mommy da Alkhairi".
"Allahumma Amin, wato su Mommy ana gyarawa d'a Mata yanda..... Umhh ".
Ta rufe bakinta tana wata dariyar.

Hannu Rukayya tasa ta dauko wayar da zahra ta aje a tsakaninsu ta Fara juyata tana kallon zahra.
"Mrs Dange! Masha Allah yaushe ya gwangwajeki da wannan me zafin?".
Dan warrr tayi da ido tana duban Aunty Rukayyar..
"Ba tawa bace aro ya bani da ya dauke min tawa" .
"Kamar ya?".
Labarin abinda ya faru ta Bata.
" Ke ai gobarar Titi a Jos, ba gashi kin samu waya daga sama ba".
Baki ta bude tana fad'in. "Kai Aunty Ina Akuya zata da Kayan Cali, wallahi wannan tafi karfina".
"Naki wasa ne yarinya kinsan waye mijinki kuwa Naga alama anyi Miki lillibin biri, bazakiji mutuwar sarki a bakina ba Amma ki zaman very curious a Kan duk wani motsinsa da lamuransa da kanki Zaki bani labari".
Dan narainarai tayi da ido.
"Wallahi na kasa gane komai a Kansa Kuma an rasa Wanda ze min cikakken karatun da Zan fahimta".
Wayar Aunty Rukayyar ta aje a kusa da Zahrar tana fad'in.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login