Showing 219001 words to 222000 words out of 280244 words

Chapter 74 - AUREN HUCE HAUSHI complete

07 Feb 2026

1035

tanka tsakanin Aishat da Aunty Surayya, ba'a daukesu daga parlourn ba sai da Abbie ya shigo shida uncle Mustapha sukaga kayan Aishat taso ta bude musu uncle ya Hana Yana fadin.
"Haba Hasana sai kace Mata zamu zauna muna bude kayan sakawa muna kallo, Allah ya Sanya Albarka ya hada kawunansu ya kare fitina".
"Allahumma Amin"

Suka fada gaba daya, Aunty Surayya bata bar gidan ba Saida suka Gama duk abinda ya kamata suyi na shirye-shiyen Baki Dan Ammi taci alwashin sai ansan danta yayi Aure.

Saida Aunty Surayya ta taya su Aishat shiga da kayan wani daki kusa da Wanda Mahmud ya kwana a ciki, Amma Dan Karamin kit din da sarkokin gold ke ciki dakin Ammi aka kaisu.
Washe gari aka tashi da rabon IV na dinner da yini abinda ya girgiza duk wata yarinya data kwana ta wuni a family din dake kokarin cusa kansu gurin mahmud Kota halin Yaya ne.


****

Su Aunty Badi'a basu samu gaisawa da Abbansu Zahra ba sai da safe, yaji dadin abinda Ammin tayi sosai yayi godiya.
Bayan sun dawo sunyi break fast ne Ammah tazo musu da bayanin Abba ya sallami drivern tun dare sukayi sallama ana yin sallar Asuba ya dauki hanya yace Bauchi za'a kaiku kubi flight zuwa sokoton.
Godiya suka yiwa Ammah kamar wasu kayan duniya aka Basu, sai da zasu tafi Mama ta shigo shima Abba ne ya turota su gaisa da bakin Ammah, Amma batayi niyya ba duk da sahura ta kaimata tsegumin bakin ita abinda ya dameta shine a gabanta Lamarin salma wadda da kyar aka Zubar da Cikin tamkar bazata rayu ba Dan ta Suma yafi sau goma da kyar aka samu ta farfado, jini kuwa an Kara Mata shi yafi Leda bakwai Dan Zuba yake tamkar lalataccen famfo.
Ammah ce tayiwa su Aunty Badi'a bayanin wacece mama a gidan da kuma Matsayin su na iyayen mijin zahra.
Har dakin da zahrar take Aunty Badi'ar taje ta samu zahrar tana karatun Alqur'ani mai girma.
Tana Kai aya zahra ta rufe Qur'an din.

Shigowa tayi tana kallon Zahra wadda ta saka rigar wani material da Aunty Fateeha ta bawa tele ya dinka Mata sai tayi wani mahaukacin kyau, gefen gadon Mummy badai'a ta zauna ta nuna mata kusa da ita, Bata zauna kusa da ita ba saita zauna a Kan carpet din dake kusa da kafarta.
"Zamu tafi diyata me Zaki bamu mu kaiwa Dana kafin ki isko shi?".
Sadda Kai zahra tayi,duk kunya ta rufeta.
"Kina jina".
Kai zahrar ta gyada Mata alamar eh.
"Ki kwantar da hankalinki kada ki jewa yarona da rama, babu abinda ze rabaku in Sha Allah,mun kawo ki ne Dan Kara nema miki mutumci a idanun 'yan uwan mijinki idan aka wayi gari kawai suka ganki bazakiyi daraja da kima ba a idanunsu sai ayi muku wata fassara ta daban kinji, ki yiwa Amminku biyayya yana sonki sosai wallahi tun kafin ta ganki Allah ya nuna Mata ke a Cikin mafarkanta sau babu adadi tare da mahmud Kuma a zahiri ma Kuma ke dince dai ba wata ba, zata turo matanenta suzo har Cikin gidan Nan su daukeki su danka ki Amana a hannunta gadan dangin mahaifinsa da nata dangin, kuma duk jarabawar da tayi Miki a zaman kwana Daya daikayi da ita ba'a samu matsala ba haka muma a namu bangaren babu kuskuren da aka samu Sai ma abinda babu shi da muka samu Karin haske a cikinsa,Dan haka ki fadawa kawayenki na kusa zasu rakaki dakinki na dindidin duk sauran Wasa ne ai ya fada min yanda kukayi ta gantali kamar mararsa mafadi,Dan Allah kiyi Masa biyayya ki kula dashi jariri ne a gurin soyayya ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kece mace ta farko Daya taba so a tarihin rayuwarsa da bakinsa ya fada min wannan yace min ya fara sonki tun Yana dan shekarar farko a university lokacin ya Dan Fara business Sameer Yana raka shi, Bai dai bude min maganar ba to kinji dai da sonki ya rayu Dan haka ki Zama jaruma a dukkan al'amuransa kinji diyata".
Kai ta gyada Mata alamar to.
Bayan tafiyar bakin ne Ammah ta dawo Cikin a parlour Ammah ta Sami zahra tana fada Mata yanda ta yaba da halin surukarta ba kadan ba.


Ba jimawa Hajiya Kaltum ta shigo suka kule da Ammah bed room din.

Zahra ma Bata koma ciki ba zamanta tayi a parlourn ita kadai tana kallon girkin larabawa.
Wurin Sha biyu da rabi Ya Abdul Hakeem ya shigo Yana fadin.
Ina Zahrar tazo tayi bako".

*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH
(Maman Fateemah)

09061432330
Or
08055362975


Page 79.


...........
Maganar data sauka a kunnen Ammah kenan, wani kallo Ammar ta yiwa Abdul Hakeem na ina tunaninka yake da lissafinka yake.
"Me naji kana fada tayi bako Kuma kamar yaya?".
Dawo yayi daga fitar da yayi niyya.
"Ammah bafa wani bane da ban Sameer ne abokin mijinta Ina ganin sako ne ze Bata fa, ya za'ayi nazo kiranta idan bansan waye ba tubda da aurenta shima ganin na hannun Daman mijinta ne Kuma ga bayanin da Kika yi min nasan da abinda ya kawo shi girinta".
"Ah to yanzu naji magana, turo min magaji ya bude Masa falon baki.
"Haba basai na turosa ba bani kawai na bude masa".
Gurin dinning Ammah ta nufa ta dauko Masa keys din ta bashi ya fice, Alawiyya Ammah tasa ta Zuba abinci da drinks ta Kai Masa.
Sai da Zahrar ta bashi a kalla minti talatin tasa dai zuwa lokacin ya Gama komai sannan ta leqa ta fadawa Ammah zataje gurinsa.
Lokacin da tayi sallama ta shiga Sameer Yana tsaye da waya a kunne Yana fadin.
"Dan Allah ka koyi hakuri Mana haba kamar a kanka aka Fara Aure duk ka tashi hankalina nace maka Ina Cikin gidan abincin tarba aka kawo min kafin ita madam din ta fito.....yauwa gata Nan ta fito".
Ya fada Yana mikowa Zahra wayar wadda ke fadin.
"Barka da sauka oga Sameer".
"Yauwa sannu amarya, ungo mijinki ya hanani sakat Saida ya tasoni daga aikin daya sakani a garin nan Wai nazo na gani da abinda yake damunki".
Dan murmusawa tayi.
"Ni lafiya ta kalau kawai dai baya son ka huta ne, Ina baby na?".
"Baby sun dauki hanyar sokoto acan zaku hadu, harda su Rukayya da mommy da mutuniyar ki ai Rukayya na fada Mata tayi tsallen albarka tace tafiya ta tashi".
Ya fada yana nufar kofa.
Wayar ta duba Yana Kan layin Yana jinsu.
"Karawa tayi a kunne tana fadin.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
A zuciyarsa ya amsa sallamar Amma a zahiri sai yace Mata
"Haba precious kunyi min adalci kenan? me yasa Zaki yarda a maida Mana hannun agogo baya, Wai Dan kada mutane suyi surutu sai a dauke min ke? Nifa nayi zaton koma menene a iya sokoto Nan ze tsayaKema na kiraki Dan na samu relief sai kik'i daga wayar sai ace min wai kuka kikeyi wato so kike na nuna musu raunina a kanki ko?
Shiru tayi ita ta rasa mema zata ce Masa Umarnin mahaifiyarsa zata tsallake, da kunnanta fa taji Yana fadar Ammi ze bawa zabi ta zabar Masa Mata, to Kuma tace ta tashi tabi yan uwanta su tafi to musu zatayi Mata tace bazata ba ko Yaya?shi me yasa ya Bata zabin tayi abinda ya dace, ita Bata kullace shi ba sai ita zega laifin ta taho wato shi yayi biyayya ita kuma ta nuna ba haka ba ace kwadayin dukiyar su take yi kenan,duk da itama a Cikin wadatar ta tashi gaba da baya Amma ai ba kowa ne ya san hakan ba.
"Kinyi shiru precious".
"Me kake son na fada bayan biyayya na yiwa Ammi cewa fa tayi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na tashi mu tafi kawai lokacin banma San inda zamu ba Saida mukazo Kano Naga mun dauki hanyar Azare na gane Ina zamu,ai Ina ganin kawai mu hakura mu yiwa Iyayen mu biyayya kaga Nima biyayyar nayi lokacin da aka bani Kai bansan Koda waye aka daura min aure ba,Amma na hakura nayi biyyyar iyaye kaima kayi biyyyar idan Ammi bani bace zabinta muyi hakuri haka Allah ya nufa zaman takaitaccene kabi abinda takeso bazaka tabe ba in Sha Allah".
Cikin tashin hankali ya Fara magana.
"Me kike fada haka preciousss? Kina son heart attack ya sameni? Waya fada Miki Ammi Bata Sonki? Soyayyar tasa ta raboki da gidanta badan Bata sonki ba Kinga yanda ta kasa zaune ta kasa tsaye duk fa kunyar Dan fari Ammi ta aje a gefe hidimarta takeyi babu Kama hannun yaro, Ina gama da sakon data bawa Sameer ya kawo Miki, na Ammah Ina Jin sai gobe za'a taho dashi, ki shirya dake za'a taho min fa a Mika min kayana daga cikin daki Nima naji abinda 'yan uwan sukeji na gaji da gararamba gara na tsuguna Nima na Fara hada nawa family din, in sha Allah da biyu Zaki Fara min ko 'yar gidana".
Runtse idanu tayi ita fa idan yana ambatar irin wadannan kalaman na haihuwa tuno yanda sabgar take kafin samun abun haihuwar shine damuwar ta da gasken gaske tana hasaso ranar da alama Kuma an dauki hanyar zuwanta.
"Dan Allah ya mahmud ka Bari ba kyau fa irin wannan maganar"
"Kam bala'in waye yayan naki Allah ki iya bakinki babu hadin Zuma da guna,ki nemi yayanki tun dare be Miki ba,Ni ki barni a your love dinki kawai ko kin manta meu amor dinki ne...? Pls Dan fada min irin tanadin da aka yiwa meu amor a wannan special day din?".
"Wayyo.... Dan Allah ka rufa min asiri.. ni wallahi wannan zancen yafi karfina pls Kan bariiii..?
Ta fada da sigar data yamutsa Masa jam'iyya nan da nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa.
"Ya salam! Previousss Anya Zan iya hakurin kwana uku nan gaskiya tahowa zanyi na daukeki mu wuce Dubai inda a tanadar Miki Dan amarcinki alkawarin nayi azumi uku kawai bazan iya ba"
Ya fada Yana Mata wani irin numfashi a kunne, da sauri ta cire wayar daga kunnenta tana fadin "nashiga Tara me kuma nayi Masa?
Da sauri ta mayar da wayar tana Masa magiyar ya rufa Mata asiri kada ya jawowa mahaifiyarsa abun fada Cikin kishiyoyi.
Ba Karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin ya hakura, da gaske tuburewa yayi shi baya son bidi'a ansan tun yaushe suke tare da za'a wani tarki bikin babu gaira babu dalili, tana samu ya Dan sauka tayi Masa sallama tace Ammah tana kiranta anyi Baki,yasan neman guduwa takeyi kawai Bai barta ba saida ya jaddada Mata ze Kira da dare.
Lokacin data fito Sameer baya kusa tasan suna tare da ya Abdul Hakeem part dinsu ta nufa Ya imam ta gani ta tambaye shi ko su Ya Abdul Hakeem suna nan? Tabbacin hakan ya Bata Kira shi a wayar ta tace tana jiran oga Sameer.
Ba jimawa suka fito ya Mika Masa wayarsa, tana fadin .
"Gashi nagode".
Karba yayi yana fadin..
"Bari na dauko Miki sakon Ammi Wanda ta bayar a kawo Miki"..
Wata Leda Yar madaidaiciya ya Miko Mata Yana fadin.
"Gashi Aunty Aishat tace zakuyi waya".
"Ok Nagode, bazaka shiga ku gaisa da Ammah ba?"
Yar dariya yayi.
"Na nawa kuma? Na shiga mun gaisa".
Dan murmushi tayi ta nufi Cikin gida.
Ba zato tayi arba da Aunty Hasana da gudu ta shige jikinta tana fadin.
"Aunty kin manta Dani wallahi, laifin me nayi Dan Allah".
"Kuji mun yarinya ! Sai Kuma nayi ta kiranki a waya har mijinki ya Raina ni ya daina Jin 'yar kunyar tawa da yakeji ai yawan damun kani ko d'a da Kira a waya bini-bini Yana kawo raini da rashin ganin kima a tsakani gara a ringa daukar lokaci yanda duk lokacin daka Kira ya Zama ana marmarinka ku rabu ana kewarka da Jin ba'a gaji da Hira da Kai ba".
"Wannan maganar taki bisa hanya take, haka ake son Babba yaja girmansa".
Hajiya kaltume ta fada.
"Ah to Mamma fada Mata dai so take girma ya Fadi a gurin kanin nawa yanzu kuwa Aunty sama Aunty kasa duk bayan kwana biyu saiya kirani ya gaisheni".
"Aunty Ina zuwa".
Zahra ta fad'a tana nufar bedroom din data yiwa kanta masauki, Bata Jima ba ta fito da abinda Ammi ta Bata ta mikawa Aunty Hasana tana fadin.
"Gasu Nan na manta dasu Ammi ce ta bani jiya da zamu taho".
Bata zauna ba daki ta jiya tana rike da hannun Autar Aunty.
Aunty Hasana ce ta cire rapping sheet din na madaidaicin, white gold din ne yayi musu maraba, da sauri Hajiya kaltume ta matso tana fadin.
"Masha Allah girma sai Dan girma wani kayan sai amale wane jaki,lallai babban goro sai magogin karfe, irin wannan kyautar girma haka, 'yan biting bude sauran muga abinda ke ciki".
Wata ubansun Alkyabba ce baka da ratsin zare golden sai turarika masu azabar kamshi a ciki.
Jim maganar Hajiya kaltume yasa Ammah fitowa daga daki taga menene ake dagawa murya haka?
Sarkar Hajiyar ta mikawa Ammah.
"Duba kiga Karamar arziki irin wannan daga uwar mahmud, Ashe dasu tazo gidan ta aje ta shiga tata sabgar, inga fa sarkar Nan ta tasamma wajen fifty millions wallahi Dan kwanaki mun siyar da wata Bata Kai wannan ba wurin forty seven milion aka sayar".
Ammah rasa abin fada tayi saboda abin ya Bata mamaki to su wane irin dukiya garesu mutanen nan?.
Nan suka zauna suna ta maida yanda akayi har kusan la'asar duk abinda ya kamata sunyi yi an bada aikin kayan garar da za'a Kaiwa Zahra Dana Iyayen mijin duk wata al'ada da ake a sokoton Ammah ta tambaya an fada mata, da yammaci suna zaune Abba ya shigo Yana fadin.
"Asma'u ku tanadi abun tarbar Baki gobe in sha Allah bakin sokoto na Nan tafe yanzu ba dadewa Kanin Alhaji Muhammad ya kirani yake fada min zasuzo naso na hanasu duba da nisan dake tsakanin Bauchi da sokoto Amma ya nuna min a'a idan ma yafi haka zasuzo godiya ce zasu zo tunda ba aure za'a sake daurawa ba inaga ko maza ne ko kuma Mata da maza ne ban sani ba dai sai ayi dai abinda ya kamata nace Abdul Hakeem suje da magaji a debo zabi sai a Kara Dana gidan idan yaso sai a kawo sabo Naman na gida.
"To Allah ya kaimu, ya Kuma maganar furniture's din da za'a tafi dasu daga nan?".
Sai goben insha Allah za'a had a da kayan da kikace za'a kawo daga Bauchi Sai a tafi dasu gaba daya ai inaga hakan yayi ko?"

"Eh hakan yayi Allah ya saka da Alkhairi ya jikan mahaifa".
Ameen su Hajiya da Aunty Hasana suka fada ciki ya shige Aunty Hasana ya tashi tabi bayansa.
Aiki su Ammah suka Fara babu kama hannun yaro auta Ammah ta turo makota tace ya fada musu su shigo gobe za'a karbi Kaya Kuma ya fadawa mamansu mujiba idan Abbansu yana gidan ta tambaye should ta shigo zasuyi aiki.
Hajiya kaltume Bata bar gidan ba sai kusan Tara na dare, taso a Kara yiwa Zahra gyara Amma Aunty Hasana tace a karba a tafar Mata dashi tunda Hasanarsa ta kaita gurin masu gyaran Amare a India a barta haka Nan tunda Abu ne a duhu ba'asan yanda abun yake ba".
"Eh to kema da gaskiyar ki Naga 'yar tawa har yanzu zubin 'yan Mata gareta babu kamar cikakkiyar mace a tare da ita".
Da haka suka rabu haka Nan taji Bata son a Kara Bata komai idan ba fruits ba gaskiya Bata son wannan tonon sililin duk da bata da tabbas na wani Abu be shiga tsakani ba duba da tun lokacin da akayi bikin to sai dai a yanda zilai ta fada Mata bayanin da likitar Nan tayi Mata Lamarin abun dubawa ne kwarai, ita fa tausayin Zahra takeji yanda taga anyi Mata wannan gyaran tasan sai yanda Hali yayi kawai Amma da Qura a gaba.

Washe gari da sakkon aiki suka tashi Dan tun shida Maman mujiba ta shigo ita da Aina'u makociyar itama suna gaisawa sosai da Ammah din, duk bidirin da akeyi Mama Bata fito ba ko kuma tace me akeyi babu Daya,itama Ammah ta bawa banza ajiyarta.
Karfe Tara Mai kyau su Inna maimuna sun shigo gidan a Bauchi suka kwana saboda sunyi dare bana Wasa ba dole suka hakura suka kwana a can.
Wasu dunkuna ne aka kawo wanda Aunty Hasana ta bayar aka dinkawa Zahra express laces ne na manyan Mata Wanda suke ji da Kansu na manyan kudi ta saya saboda yau masu kawo Kayan walau maza ne ko Mata ya Zama dai babu raini duk da babu inda makusa take ta ko ina kawai dai idan kana da kyau ka Kara da wanka ne.
Karfe sha biyu ta gota wasu lafta laftan motoci suka tsaya a kofar gidan Alhaji Jafar Mai yadi wa
Bata lokaci Mai gadi ya bude musu tunda Alhaji ya fada Masa za'ayi Baki a gidan to Yana ganinsu yasan bakinne.
Gate baba sani ya bude musu suka Sanya Mai cikn harabar gidan.

A can Kuma Zahra ce tayi make up simple ta saka fitted gown na rigar lace sai ta fito da ainihin structure din jikinta yake. Su dai su Hajiya kaltume dasu Inna mainuna suna zaune Basu yi aune ba sukaga an Fara shigowa da Kaya, tun suna girgawa har suka zubawa sarautar Allah Saida aka zube set goma Sha biyu, sai kuma mata suka shigo bisa jagorancin magaji su kuma mazan suna gurin su Abba da jama'arsa.
Sannu da zuwa aka Fara jera musu mutanen Cikin parlour din tare da Basu girin zama, Aina'u ce ta ware murya ta zankada guda uku a jere abinda ya fito da su zilai da sahura daga Ina suke zaune a gidan, Mama ma fitowa tayi da Dan sauri tana fadin.
"Menene akeyi a gidan nan haka da uwar Rana ake ta rafsa guda.
Part din Ammah ta nufa da sauri su zilai duna biye da ita a baya, turus tayi ganin Iyayen akwatuna a zube a parlourn,kasa daurewa tayi.
"Wannan kayan fa na waye haka?" Inna Maimuna ce ta Bata Amsa "na Amarya Zahra ne kin san mijin nata ya koma gida shine iyayensa suma zasuyi nasu bikin".
Taku biyu tayi sai ganin ta akayi a kasa ta fadi jikinta na wata irin karkawa Nan da Nan aka yo kanta da sauri Dan Bata taimakon gaggawa.


*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

08055362975

Or

09061432330

Page 80.


.....& .& .. Subhanallahi mutanen dake parlourn suka dauka, da sauri Ammah da Aunty Hasana suka matso gurin da Mamar ta Fadi Ammah tana fadin..
"Ikon Allah har yanzu jikin ne kenan da Baki fito ba, Hasana maza Nemo Abdul Hakeem ko Hamza aje asibiti"O.
"Gaskiya dai Kam tunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login