Showing 1 words to 3000 words out of 130717 words

Chapter 1 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

118

🌑 *DUHU....*🌑
( *sark'akiya*)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)

DAGA MARUBUCIYAR
🦎 *K'ADANGARUWA*🦎

*SLIMZY*✍🏻
Wattpad slimzy33

*1*

Gida ne da ya amsa sunansa gida na alfarma, daga yanayin gidan zai nuna maka kamar irin family house ne wanda ko family house din nan kasan wannan gidan ba gidan talaka bane.

Zaune take a tafkeken bedroom ɗinta wanda babu abinda babu na kayan more rayuwa. Bedroom din ya ƙawatu sosai gwanin birgewa da ban sha'awa, duk wannan girman gida da kyawun ɗaki bai hana ya nuna maka irin tsananin damuwar da take ciki ba, huci ta fuzar mai zafin gaske tana miƙewa tsaye duk da mutane a gidan amma idan mijinta baya nan bata samun natsuwa da kwanciyar hankali, plate ɗin da taci abinci a daki ta dauko da niyyar ta kai shi kitchen ta fito kenan ta hau saukowa kasantuwar dare ne, tana taka kafar ɗaya akan step ta taka na biyu da na uku zata taka na huɗu kenan gidan ya gauraye da wani ihun duhu mai tsananin gaske. Wani ihu ta saka a gigice tana sakin plate din tangaran din dake hannunta wanda ya faɗi ƙasan tiles ɗin step ɗin ya ƙara bada ƙara bai ban tsoro ta sake sakin ihu a karo na gaba tana ambatar sunan "Mamaaa! Abraham....
wani haske tagani mai kalar blue nan da nan taga cikin gidan ya koma ruwa matakalar da yake kai tanayin sama da kasa da ita jin ta takeyi kamar zata tsunduma kogin datake gami a gabanta wanda take ganin tartsatsin wuta cikin sa da k'urgumin duhu ta saki razananniyar kara a karo na biyu wani sauti taji mai ban tsoro da taku da sauri ta bude idanuwanta gilmawar inuwar mace tagani batare da taga ko waye ba tayi baya zata fadi ganin yadda ruwa yakeyo kanta da wata irin halitta mai manyan idanuwa da kahonni guda biyu tasa hannu ta toshe kunnuwanta dake jiyo mata wata kararrawa dakin na juya mata ta sake kwalla razananniyar kara tace "Abraham"tayi baya ji tayi an tallabota an rukota sosai jikinta sai kyarma yakeyi ta bude idanuwnta tanabin cikin dakin da kallo ta kalli matakalar da take kai bataga wanan abun tsoro da ruwa dayake kokarin shanyeta ba gumi ya gama jikata ya kallesa yana rike da ita idanuwansa kyar akanta....."Alhamdulillah kazo gareni"ya shafa fuskarta narjisu ce ta bullo batare da taga ta inda ta bullo ba kallon narjisu takeyi cike da mamaki wato narjisu tana cikin wanan sashen tanajin yadda aka tsoratata tana ihu ya kasa kawo mata dauki?narjisu ta d'aga mata gira daya tace "lafiya kika tsareni da idanuwa husnah?"husna kallon narjisu takeyi tana mamakin yadda take nuna mata kiyayya dikda husnah tasan narjisu ta mutu akan mijintq,
Abraham yace "ke narjisu lafiya kinzo kina wani mazurai?"ta kallesa tayi narai narai narai da ido tace "momy ce tace inzo in duba ko kana nan in kira mata kai"yayi kwafa sarai yasan karya takeyi tazone dan kawai taji husnah na ihu husnah ta dubi mijinta cikin wani irin yanayi tace "ka fita kabar gidan amma ya akayi kazo ka kawomin dauki a cikin matsanancin halin dana tsincu kaina na d'an lokaci?"tambayar da tayi masa kenan ta tsaresa da ido murmushi yayi yace "ina tare dake akoda yaushe kece dai bakisan hakan ba"tadan matsa daga jikinsa a razane yayi dariya yace "karkiji tsoro wasa nakeyi miki aidana fita nasake dawowa nayi mantuwa shine najiyo ihunki nazo"ya rike kwankwasonta narjisu kuwa tana tsaye sai tsaki take ja,
ajiyar zuciya husnah ta sauke tace "har naji sanyi kabani tsoro furucin da kayi,kasan har fargaba nakeyi idan ka fita kabarni ni daya saboda yadda ake tsoratani cikin gidan nan"ya shafa fuskarta yace "koda an tsorataki saidai ya tsaya a tsoron amma babu wanda ya isa ya cutar dake indai ina raye"yayi kwafa.....tayi murmushi yace"yanzun me kikeso?"ta yatsina fuska "nadanji yunwa ne nadauko plate zani kitchen din kasa in zubo abinci"ya jinjina kai ya kalli narjisu ya hada rai yace "jeki zubo mata abinci"shiru narjisu tayi wani irin wulakanci ne ya Abrahm zaice ta zubowa husnah abinci salom ta kara raina mata wayau?amma sai kawai ta juya ta nufi aikata umarninsa ya ruko hannun husnah ya kaita bedroom a sama ya zaunar da ita har yakai kofa cikin tsoro take har yanzun zuciyarta bata daina bugawa ba tace "kadawo da wuri"ya gyada mata kai yace "karkiji komi babu abinda zai sake faruwa"ya fice ya rufo kofar ta shiga kalle kalle cikin dakin a matakala ya hadu da narjisu da abincin a hannunta da ruwa ya rike kunnuwanta tace "ashhhhh to menayi maka"cikin shagwaba tayi maganar ya harareta yace "raini kikewa matata a haka zan aureki?"zatayi magana ya wuceta yana takunsa mai cike da kasaita da sarauta.....tana zaune a gefen gado a d'arare take cikin tsoro taji an turo kofar babu ko sallama tadan razana zatayi ihu taga narjisu,tabe baki narjisu tayi tace "aikin banza kiyita wata shagwaba waike ana razanaki kwalba uwar sharri"ta ajiye mata abincin ta fice ta banko kofar......
ta dauki abincin yunwa takeji sosai ta rike cokalin zataci taji ansa hannu an kab'e abincin daga hannunta ta razana ganin plate din ya fad'i kasa babu kuma abincin a kasan ya bace har ruwan da aka kawo mata sai kawai ta fashe da kuka tana rera kuka....k'arar kofar toilet din dakin taji tayi sauri ta bude ido taga kamar ana budewa ana rufewa ta kwanta ta takure ta runtse idanuwanta ruffff......



dakin momy mahaifiyarsa ya shiga yw tarar da ita zaune da lullubi da carbi a hannunta kamar koda yaushe ya tsugunna har kasa yace "barka da Rana momy"ta jinjina kai tasa hannu ta shafa kansa wata matashiyar yarinya da bazata wuce shekara sha biyar ba ta shigo dakin tana tsalle "yaayah yayah yanzun nake cewa zani ganin anty husnah"yayi murmushi cike da kasaita yasa hannu a plate din da ta shigo dashi hannunta farfesu ne na kayan ciki yasa cokali ya dauki daya yana taunawa yace "jeki zauna da anty husnah "momy tace "ka barota ko tanacan tana ihun nata ko ni bansan meyasa takeyin haka ba sai tace ana razanata to waye zai razana ta?"narjisu dake shirin shigowa tace "sharri mana"momy batace komiba kannen abraham biyu maza suka shigo juraid da junaid yace "ku kuma fa?"dayan su ya sosa keya yace"kai muke jira zamu bika"ya kada kai kawai yace "fitinarku yawa gareta kuje waje ku jirani"suka mike suna dariya abrahm yace "saina dawo momy"....tace "allah ya tsare" Abraham ya fita kanwarsa dake zaune ta ajiye plate din data gama cin pepe soup tace "zan tafi wajen anty husnah"kai kawai mahaifiyarsu ta daga mata ta fice ta rufo musu kofa narjisu ta durkusa gaban momy tace "momy yaushene zaayi aurena da ya Abraham tunda anyi aurensa da wanan yar tsuntuwar momy kun kasa gane irin son da nakeyi masa wallahi zan iyayim komi akansa"momy tace"nasan zaki iya amma sanin kanki kinsan yadda Abraham yakeson husnah kinsan yadda ya reneta a gidan nan tun tana yarinya kin kumasan yadda bayason abinda zai tabata"narjisu ranta ya baci ta sakejin masifaffen kishi ya taso mata momy tace "kuma kinsan nida mahaifinsa abinda yakeso shi mukeso in dabadan haka ba bazamu barsa ya auri wacce ba jinsin mu ba"narjisu bata sake magana ba ta fice kicibis sukai da wata budurwa wadda suke kai daya dukkansu yaran yayyin baban Abraham ne dik gidansu daya babban gida ne bangazar juna sukayi dayar ta fizgo narjisu tace "ke kin isa ki bangajeni akan masoyina bari kiji ko matarsa bazata iya dani ba ballantana ke"idanuwan narjisu suka sauya kala sukai jajir tace "nidake zamuga wanda zai aureshi mata ta biyu "ta wuceta tana huci tayi dakin mahaifiyarta tana shiga ta zube a kasa ta fashe da kuka mahaifinta na dakin wanda wa yake a wajen mahaifin abraham ganin kukan narjisu yayi masifar daga masa hankali mahaifiyarta tace "abun guda daya ne dik akan Abraham ne bayan ya gabatar da zabinsa ya aureta kuna haukar banza"mahaifinta yace 'ba hauka bane kisa ranki a inuwa kin auresa kin gama'ya fada jikinsa tana kuka yana huci yace "zan sami mahaifinsa shin mune yayyinsa koko shine yayanmu abinda dansa yakeso shi zaiyi?ya fice cikin bacin rai har yana bugewa a kofa....

*****
husnah na d'kunkune cikin daki taji motsi ta kara takurewa kanwar Abraham ta girgiza kai tausayin husnah ya kamata a sanyaye tace "anty husnah"da sauri husnah ta mike ta fito da fuskarta data jike da gumi ta sauke ajiyar zuciya tace "kece zahraliyya?"zahraliyya t"nice"ta kallu plate din dake ajiye a gefen gado da abincin tace "ah ah ya bakici abincin ba har yayi sanyi?"husnah tace "abincin da ya zu......"shiru tayi ganin abinci a plate a gefen gado shedar yadda aka kawo mata ta shiga girgiza kai kamar zararriya tace "ah ah....wallahi an kabar mun da abincin ya zube"zahraliyya ta dauko abincin ta mika mata tace "ci anty babukomi kin tsorata ne"bakim husnah na d'aci ta karba har yanzun a tsorace take ta soma ci zahraliyya ta zura mata ido tana karantarta tanayi tana mata hira dan ta mantar da ita tsoro da furgicin da take ciki.....tausayi anty husnah take bata musamman yadda ta taso a cikin gidansu batasan ita waceceba sai yadda akayi da ita gashi ba kowa ke sonta ba sai dan tsoron mijinta da akeyi kallon husnah kawai takeyi yadda takecin abincin tace "anty husnah ki saki jikinki babu abinda zai sameki kawai kin tsoratane kuma ai gani a gabanki ko?"

jinjina mata kai tayi hade da yin ajiyar zuciya husnah ta gama ta dire plate din tace "ki jirani inyi wanka mana"jinjina mata kai tayi ta gyara zamanta tace "jekiyi sai mutafi sashen goggo kande"murmushi tayi ta nufi toilet ta cire towel dake jikin kofar toilet din ta tube kaya zahraliyya tana kallonta ta shiga toilet din ta rufo kofa ta tara ruwa kenan ta kalli madubin jikin toilet din taga ba fuskarta take gani ba tayi saurin kawar da kai jikinta na rawa ta wawatsa ruwa ta fito ta sauya kaya riga mara nauyi tasa doguwa har kasa pink da hularta tace "muje zahrali...."ta mike suka fito tana taka matakalar a hankali har suka sauka gani takeyi kamar zata sake ganin abinda ta gani dazun sun fito mutane cike da gidan kasantuwar babban gida ne duka suka zuba mata idanuwa suna magana kasa kasa wadda batason ganice suka hadu da ita tana matukar tsoronta batasan daliliba dik rashin mutuncin narjisu Gara ira akan zabariyya sukai ido hudu gabanta ya fadi kallon da zabariyya tayi mata yasa ta sadda kanta kasa suka wuce.....a kofar shiga sashen goggo kande ta jadu DA abrahm dasu juraid ya mata wani kallo ta sakar masa murmushi ji takeyi kamar ta rungumesa yayi mata kyau sosai ya rad'a mata a kunne yace "ina zuwa?"tace "sashen goggo kande"sai kawai ya ruko hannunta yana murzawa wani yarrrrr taji ta kallesa wata irin muguwar shaawarsa taji ta kamata gashi har yau ya kasa kusantarta dik sanda zatayi masa magana saita kasa haka suka juya suka jero tare kishiyar momynsa ce tace "saki hannunsa mara kunya kin ruko hannunsa kun ratso mutane saboda bakida kunya shi kuma ya biye miki" da sauri ta saki hannuwansa tayi kasa da kai tayi gaba har tana hardewa ta wuce sashen momy ya wuce a fusace sam bayason yadda hajiya babba keyi ma matarsa sam bayaso fiuuu ya wuce wani kallo tayiwa zabariyya sukai murmushi tare zabariyya tabi bayansa,


zama husnah tayi a parlour ranta a bace tana jiran shigowarsa shiru shiru bai shigo ba ta dauki remote ta kunna tv ta maida hankali akan tv dan ta mance da yadda hajiya babba tayi mata tsawa amma har yanzun amsa kuwwar maganarta takeji a kunnuwanta ji tayi an rufe kofa da sauri ta juyq bataga kowa ba ta gyara zama tana waige waige ta juya kenan abinda ta ganine ya razanata ta mike aguje tayi hanyar kofa ji tayi ta fad'a kirjinsa ya rungumeta sosai ya tura kansa cikin wuyanta Yana kissing dinta yana shafa bayanta ta sauke ajiyar zuciya.......

ya rukota suka nufi parlor suka zauna yana rungume da ita tace "inaso inje kasuwa"gabansa ne ya fadi nan da nan ya sauya fuska tana kallonsa tana lura dashi dik ta bukaci fita cikin gari baya barinta sai ya canja fuska shagwabewa tayi tace "manshafawa nane ya kare"

"ok akwai kasuwa ai a cikin gidan nan gobe zamuje"tayi shiru tana mamaki "kasuwa kuma?"ya jinjina mata kai sai kawai ta kinkimeta ya nufi sama da ita yana rungume da ita magriba tayi gari yayi DUHU gashi babu wuta daki ya shiga da ita ys rungumeta yana kissing dinta yana shafa jikinta gabaki daya jikinta ya saki ya barbaza gashinta a fuskarta ya rungumeta sosai yana shafa sassan jikinta nan da nan taji bacci ya dauketa cikin tsakiyar dare ta Tashi yau ma kamar ko yaushe babushi a kusa da ita tunda sukai aure batasan inda yake zuwaba daddare a fusace ta mike ta fito samm ta mance da wani tsoro ta fito arba sukayi da mace doguwa mai tsayi a gabanta gashinta har kasa yana jan kasa kalar jikinta kalar kayan ta wato ruwan toka wani haske ne yake fitowa daga cikin idanuwanta husnah ta soma ja baya tana tahowa jikinta na karkarwa haka take tsallake matakala da baya da baya har ta cinma jikin bango bata ganin inda take takawa duhu ya gauraye ko ina wata kara da iska ke kad'a kofofin cikin sashen fitulun dake sama suka shiga kunnuwa suna mutuwa ta surare ta fadi kasa sumanmiya......


DOMIN MALLAKAR WANAN LITTAFIN KI BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT DIN

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHEDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08036953516 KO 07042277401

DOMIN KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08036953516.....



*SLIMZY*✍🏻
🌑 *DUHU....*🌑

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(home of expert and perfect writers)

DAGA MARUBUCIYAR
🦎 *K'ADANGARUWA*🦎
*SLIMZY*✍🏻
Wattpad slimzy33

*2*
A hankali husnah ta bude idanuwanta tana kalle kalle cikin dakin yana rungume da ita a kirjinsa babu riga jikinsa ta janye jikinta ta fashe masa da kuka mai ban tausayi tace"inaso insan inda kake zuwa daddare dik kabarni bacci ya daukeni idan nafarka bana ganinka a kusa dani"ya janyota yana shirin rungumeta ta kwace ta zuba masa ido tana hawaye yasa hannu yana share mata hawaye "niko ina zani daddare bayan anyi dare ne dan ko wani bawa ya huta?"wani kallo tayi masa lallai ma Abraham ya raina mata wayau haka ma zaice?kallonsa kawai tayi ta gyara zama ta had'a kai da gwiwa ya dagota ya rungumeta ta fad'a jikinsa tana ajiyar zuciya shiru tayi tanaso ta tuno abinda tagani dazun shin mafarki ne ko gaske ne gamo tayi?tambayar da tayiwa kanta kenan shiko kallonta kawai yakeyi yanajin kaunarta can cikin zuciyarsa yanaji bazai taba Iya rayuwa babu ita ba,shafa sumar kanta yayi,ya kissing dinta a goshi ya gyara mata kwanciya shima ya kwanta yayi mata rumfa da kirjinsa......shiru tayi ba bacci takeyi ba tanaji ana kiraye kirayen sallahr asuba ta Tashi ta zame jikinsa daga nata ta shiga toilet tayi wanka sanan tayi alwala ta fito gaban madubi ta zauna motsinta yaji ya bude idanuwansa gashinta yake kallo bakinkirin yana lilo a bayanta ta shafa turarruka kala kala kamshi kawai katashi sanan tasa doguwar rigar atamfa ta tada kabbarar sallah shima mikewa yayi ya fad'a toilet tana idar da sallah ta fito sanye da hijab jikinta a hankali take taka matakalar abinda ta gani jiya ya fado mata taji tsoro sosai ta dake sanin mijinta na gida ta fito....maaikatan gidan keta hada hadar girke girke daya daga jikinsu ta tsugunna tace "barka da Tashi ranki ya dade"murmushi hunah kawai tayi mata ta wuce a hanyar shiga sashen momy ta hadu DA zahraliyya tana ganinta cikin faraa tace "ina kwana anty husnah"husnah ta amsa cike da kulawa tace "lafiya kalau zahrali...."sosai zahraliyya kejin dadin yadda matar yayanta ke kulata a babban parlorn gidan ta tsugunna gaba hajiya babba ta gaisheta wani mugun kallo tayi mata cikin tsawa tace "kim taba gaisheni na amsa?tsintacciyar mage kinzo cikin gida kim aure d'an gida"tayi kasa da kai ta mike jiki babu kwari ta karasa gaban sirikarta ta gaisheta ta amsa mata babu yabo babu fallasa ta mike tace "ina kika baroshi ko kin hanashi fitowa ne?"..husnah tace "ah ah nabaroshi a daki ne yana wanka"kamshin turarensa ne ya gauraye wajen dukkansu kowa ya shiga hankalinsa husnah ta fice daga parlorn ta nufi dakin marikiyarta wato goggo kande yar mahaifin mijinta wadda bata taba haihuwa ba,

"mahaifinka nason ganinka Abraham "shine abinda momynsa tace ya amsa da "ok"ya Tashi zabariyya Tasha ado dikda safiya ce ta fito daga sashensu ta taresa "yaya"tace cikin wata irin murya mai daukar hankali yayi saurin ganin waye dikda jikinsa ya basa tace "dama inaso idan zaka fita ka saukeni a makaranta mana "ya jinjina mata kai "fatan kim shirya"ta gyada masa kai farin ciki ya lullubeta lallai hak'arta ta kusa cinma ruwa shawarar hajiya babba tayi narjisu na lab'e tana kallonsu ji tayi kamar ta mutu saboda kishi babu yadda zaayi ya fita da zabariyya tana cikin gidan nan,

zabariyya kuwa bin bayansa tayi tana yauki tare suka jera zuwa sashen goggo kande tana zuba masa surutu,a zaune ya tarar da husnah a carpet ta tankwashe kafa goggo kande tace "ah ah ka biyo matarka ne?"murmushi yayi kasantuwar bashida son magana ya kalli husnah ta dauke kai ganinsa da zabariyya ji tayi kamar an watsa mata rushin wuta a zuciya wani irin kishi ne ya turnuketa taki kallonsa yace "sammakom fita zanyi hussy akwai abinda kikeso ne?"batare data kallesa ba tace "Babu allah ya tsare".....yayi shiru jimm kadan yace "ameen"zabariyya tace 'goggo kande saimun dawo zamu fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login