Showing 21001 words to 24000 words out of 113985 words

Chapter 8 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28452

suka fita shida matarsa. Itama hajiya Babban daga baya tabi su. Aunty maryama ta mike tana fad'in.

"Sannu Nanne, bari in had'a miki tea."

Dama abinda take shirin fad'a kenan, don yadda take jin jikinta shafal, ta tabbatar harda yunwa ke damunta, aikuwa Aunty maryaman ta hado mata tea mai kauri harda pepper soup din nama da dankali (irish) wanda da alama don ita akayi dama.

Ta cika cikinta fam! Sannan tayi wanka da ruwa mai zafi ta canja kayan baccin dake jikinta tun daren shekaranjiya. Aikuwa har yamma mutane shigowa suke ana duba ta, 'yan gidan kaf! ba wanda bai shigo ba, harda su ya Ahmad da ya ibrahim masu aure sai da suka zo da matansu bayan sallar maghriba.

Nanne taji wani b'angare na zuciyarta ya fad'a, bata zata kowa na sonta haka ba. Rahma kuwa harda kukan murna data ganta ta farka, a wajen su Aunty Nafisa taji ashe a gidan ta kwana a falonsu, sai da safe ne ta tafi gida saboda zuwa makaranta.

Duk wanda yazo dubiyar nan kuwa, sai inna ta labarta masa abinda ya faru tun daga farko har karshe, har sai da Nanne ta haddace kalma bayan kalma na abinda take fada. Sai dai kuma wani abin mamakin shine a duk labarin Inna bata ji ta danganta rashin lafiyarta da Aljanu ba, haka ma dukka 'yan gidansu da 'yan dubiyar babu wanda ya ambaci hakan, sai kawai fatan sauki da kariya suke.

Saboda haka itama ta ture duk wani tunani a ranta ta sake tana ta cin kayan dubiyar da kowa ke rik'owa in zai zo. Don hatta sadiq sai da yaje can wani bakery na hanyar makarantarsu ya siyo mata irin sandwich cake d'in da ya san tana so. Amma duk da haka saida ya dameta da tsokana, duk sanda ya shigo d'akin zai ta dariya yana cewa 'yanmata taji azaba idonta yayi wuri-wuri.

Da daddare mama halime ta kawo mata potate d'in dankali da alaiyahu, aunty amarya da mama rabi ma duk sun kawo 'yan fruits dinsu. Hajiya Babba kuwa manyan carton d'in madara da Bournvita ta kawo wai zasu sa taji kwarin jikinta. Inna sai washe baki take ganin yadda kowa ke nuna kulawarsa. Baffa ma sai da ya shigo da kansa da daddare yaga jikin nata.

Washegari da yamma Amina tazo, don sai a ranar Safiya ke gaya mata a makaranta, duk ta rikice tana ta tambayar jikin nata, Nanne tace ta kwantar da hankalinta don wasai take jinta, tsoronta d'aya ne in dare yayi bata son kwanciya, don a jiyan ma kusan a zaune tayi baccinta.

Aminah ta tambayeta abinda malaman suka ce tace itama bata sani ba, don tunda ta tashi, ba wanda yayi mata zancen, kowa ta ganin ta wartsake yake.

Sai da mutane suka lafa sannan Baffa ya kirata falonsa, yace da farko dukkansu sun danganta ciwonta ne da shafar aljanu, amma malaman da suka zo sunyi duk wani k'ok'arinsu basu ga alamar aljani a jikinta ba, Saboda haka ga magunguna nan sun kawo ta dage da shansu da kuma addu'o'i. Tun daga nan, Inna ta tsaya akanta a kullum sai tasha magungunan sannan zata kyaleta, ga litattafan addu'o'i da carbi har kala uku duk ta siyo mata.

Bayan sati d'aya ta warware sosai ta koma makaranta, sannan ta canja sabuwar islamiyya ta koma wata a hanyar gidansu Rahma, hakan yasa itama Rahman ba yadda ta iya, ta bita suka shiga tare.

A cikin sati biyu, rayuwarta ta koma kamar da, komai ya dawo mata daidai...tsiwa da rashin kunyarta ta d'ora daga inda ta tsaya, don har ya sulaiman saida ya zane ta wata ranar juma'ah. Da magribha ne ta lab'e a wajen barandarsu ta gama jin wayar da yake da girlfreind d'insa duka, sai a k'arshe da taji yayi k'asa da murya yana fad'a mata how much he loves her sannan bakinta ya sub'uce tace A'uzubillahi.

Ai kuwa karaf yaji a kunnensa, ya biyo ta har cikin d'aki ya mammake ta, bai ko saurari kwaroroton inna ba.

Sai dai bayan sati biyu, komai ya fara dawowa sabo...

Maganganun da take ji a cikin kanta suka dawo tare da yawan kiran sunanta da kuma alamun wani abu na tsaye a bayanta.

Sannan ga azababben ciwon kan nan da kuma yawan tsoratar da take yi.

Wannan kwankwasa kofar ma na cikin dare ya dawo...!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

16

(¡î_¡î)

Ya d'ago da kansa a hankali sanda aka rufe main kofar shigowa falon.

"Watarana idan na gaji, zan shak'e wuyanka ne kowa ya huta."

Imran ya juyo daga cire takalmansa da yake ya kalli jaamil dake zaune daga kujerar dining na falonsa.

"Yaushe kazo? Ka dade kana jirana ne?"

"Tun sanda ka bar wajen aikinka ka tafi yawon zagaye gari nake zaune anan."

Imran ya k'araso da murmushinsa.

"Toh me yasa kawai baza ka dawo nan bane, kaga ka huta zirga-zirga, kuma akwai spare d'aki...biyana kawai zakayi ka shiga."

Jaamil bai saurari k'arshen zancen nasa ba ya kalli ledar daya ajiye akan table din.

"Meye wannan kuma?"

"Abinci ne nayi takeaway, don har yanzu bana jin k'arfin jikina, ba zan iya girki ba."

"Wai me yasa ka damu kanka da abincinsu ne?"

Ya d'aga kafada kad'an.

"Saboda yana min dadi."

"Ranar da komai zaizo karashe zanga yadda zakayi."

"Me kuwa zanyi, zan cigaba da zuwa ne ina siya."

Har jaamil zai bashi amsa suka tsinci knocking daga k'ofa. Ya juyo ya kalleshi.

"Meye kake kallona? Gidanka ne fa."

Yaja k'aramin tsaki.

"Ba sai ka tuna min ba ai, ban taba yin bak'i bane thats why."

Yana bud'e k'ofar, yaci karo da wasu 'yanmata biyu a balcony d'in. Ya d'an bude baki saboda mamaki sanda kowaccensu ta fad'ad'a murmushinta.

"Ina wuni." suka fad'a a tare.

"Uhm...lafiya kalau."

"Dama mu mak'otanku ne, tunda aka tare ne bamu shigo ba shine muka ce bari yau muzo mu gaida matar gidan."

Imran ya d'anyi shiru sannan ya cusa yatsunsa cikin sumar kansa yace.

"Mungode...sai dai kuma ba mata a gidan."

Suka zare idanunsa sannan d'aya ta kalli daya.

"Oh sorry, bamu sani bane wallahi...sai anjima."

"Its nothing, sai anjima."

Ya rufe k'ofar ya dawo ciki. Jaamil yana dariya k'asa k'asa yace.

"Yanzu a kawo maka ziyara ka hana su shigowa? Bayan kaine matar gidan?"

"Wallahi k'arya suke, ina ganinsu fa in na dawo sun san babu mace a gidan."

"Kaima ka san me suke nufi ai."

Bai saurare shi ba yayi hanyar d'aki kawai. Bayan kamar minti talatin ya fito sanye da wasu kayan, ya jawo kujerar gefen jaamil ya zauna ya fara cin abincinsa.

"Meya faru?"

Ya tambaya ba tare daya kalle shi ba.

"Ciwon yarinyar yana shirin dawowa."

Da jin haka imran ya saki cokalin hannunsa.

"Tun yanzu...? Jaamil gaskiya dole mu sami wata hanyar, ba zan iya ba wallahi nayi losing k'arfi da yawa kuma i'm still picking up."

"Na sani."

"Na san ka sani mana, I'm asking me ka samo? Don ba abinda zan iya nan gaba idan dai ni zan cigaba da controlling d'inta."

"Da ace ban samo komai ba yarima, bazaka ganni anan ba."

"Okay ina jinka."

Jaamil yayi ajiyar zuciya mai nauyi yana kallon set d'in cokula da table knife d'in dake jere a cikin gidansu na katako daga tsakiyar table din.

"Wai taya ka iya tsara komai na gidan nan ne ma?"

"Wani Decoration company na biya suka had'a min. Ina jinka me ka samo?"

Jaamil ya sake yin shiru, abinda zai fada nauyi yake masa, kuma shi kansa har yanzu ya kasa yarda cewa hakan shine kad'ai a hanyar samun saukinsu, wani abu da babu shi a tsari ko tunaninsu.

"Yarima abinda na samo mai girma ne, ni kaina na san ba zai yiwu ace duk bayan sati biyu kana k'arar da k'arfinka wajen controlling d'inta ba, amma ka yarda dani ba yadda zamu yi ne."

"Nima na san da hakan, saboda haka ka fad'a min kawai me ka samo?"

"Hanya d'aya da zai sa ciwonta ya tafi gabad'aya shine in yarinyar tana kusa da kai!"

Imran yayi shiru yana kallonsa, hannunsa rik'e da cokalin daya d'ebo abincin. Sai kuma ya sake shi cikin plate d'in sannan ya gyara zamansa sosai.

"Ban gane me kace ba..."

Jaamil yayi ajiyar zuciya, yana jin shima kamar abinda ya fad'a ba daidai bane.

"D'aya b'arin jikinka ne kad'ai zai iya controlling wanda ke jikinta, saboda haka idan kuna tare a kullum d'aya b'arin zai dinga jin alamun d'ayan a kusa dashi saboda haka ba zaiyi k'arfin da zaiyi tasiri ba, kamar dai sanda duka biyun suke jikinka.

Amma in har d'aya yayi nesa da d'ayan, ciwonta zai ta taruwa ne ta yadda duk sanda ka tashi zuwa kwantar dashi, sai kayi amfani da k'arfi mai yawa. Wanda in kuma kana yawan yin hakan toh k'arfinka zaita tafiya kullum ka zama baka da kuzari."

Imran ya tsura masa ido, yana jin kowacce kalma tana bi ta kan fatarsa tana nutsewa cikin kwakwalwarsa. Amma kuma ya gagara fahimtar ma'anarsu. zuwa can ya daure yace.

"Jaamil ban gane ba fa, ta yaya yarinyar zata zama a kusa dani? Ka san dai ba zan iya zuwa inda take kullum ba?"

"Na sani."

"Toh ta yaya hakan zai yiwu? Kuma ka san ba zamu iya sace ta mu cigaba da zama a garin nan ba, dole za'a nemo mu ko kuma yarinyar ta gudu...sannan in muka bar gari kuma zan samu matsala da wajen aikina. Wajen da saboda shi muka shigo rayuwar nan kuma nayi abubuwa da yawa ba zai yiwu mu b'ata komai ba...mu bar abu mai muhimmanci don gyara kuskurena."

"Nima duk nayi wannan tunanin yarima, kuma na ga hakan ba zai yiwu. Shi yasa na ture komai na samo hanya d'aya kawai da zata fitar damu, mu sami komai kuma a sauk'ake."

"Wace hanya kenan?"

Kai tsaye jaamil ya amsa.

"Shine ka AURE TA!"

*****

Jikinta kwata-kwata ba kwari, yayi wani irin shafal kamar fallen paper, ta rufe idonta tana sauraren maganar Inna, tana ta gaisawa da amare, zainab ce a kusa da ita tana kira mata su d'aya bayan d'aya, kowacce sai ta tambayi jikinta kasancewar duk sunji labarin.

Ji take yi kamar zata yi bacci amma kuma yak'i zuwa, ko sallar azahar d'azu da kyar tayi tana jin layi, abinci ma bata ci ba saboda ko kad'an bata jin sha'awar komai. Ta cusa yatsunta cikin gashinta tana rokon baccin ya d'auketa.

"Zainab mama na nemanki." muryar safiya ta shigo d'akin.

"Ta dawo ne?" zainab d'in ta tambaya.

"Eh yanzun nan da zamu hawo suka shigo."

"Toh bari in kira wa inna jamila tukunna."

Nanne ta bud'e idonta a hankali sanda safiyyan ta k'araso wajen kujerar da take kwance. A gefenta wata yarinya ce da a lokaci d'aya ta cilla zuciyarta cikin tunani, tunanin wannan fuskar da ta kasa fita daga ranta....IMRAN.

Tun ranar da ya shigo cikin gidansu da daddare, bata kara jin labarinsa ba balle ta ganshi. Sannan rashin lafiyar da tayi ta kwanan nan ta ture duk wani abu dake zuciyarta, dalilin da yasa bata k'ara tunawa dashi ba kenan.

"Wai bacci kike yi?" safiyya ta fad'a tana zama a hannun kujerar.

"A'ah wallahi kawai jikina ne ba dadi."

"Sannu, ya jikin?" yarinyar ta tambaya, ta juya ta kalle ta sosai sannan ta amsa.

"Walida ce take son style d'in doguwar riga, shine nace bari muzo wajenki kece mai su."

"Ta kuwa yi sa'a jiya aka kawo min wanki, ki d'ebo mata suna wardrobe."

Bayan safiyya ta d'ebo wajen kala goma suna d'agawa ne ta kalli walidan tace.

"Wai kowacce kice tayi miki, toh guda nawa zaki d'auka ne?"

"Ko duka ne fa ni d'auka zanyi, sauran sai in karbi na riga da skirt a wajenki."

"Kaya nawa zaki d'inka ne wai?"

"Goma sha hudu ne, ummah tace harda na sallah amma ni wallahi duk d'inke su zanyi."

Safiyya ta gyad'a kai tace.

"Gaskiyane, dama ke kad'ai 'yarta dole kiyi abinda kike so."

Kamar a mafarki Nanne taji kalmar, saboda haka ta bud'e idonta da sauri ta kalle su sanda walida ke fad'in.

"Kowa wai sai yace don ni kad'ai ce, kuma wallahi abubuwa da yawa ba haka bane, kinga yanzu fa na d'an kwana biyu banyi d'inki ba."

Kafin safiyya ta bata amsa, Nanne ta riga ta magana.

"Baki da yayye dama?"

Walida ta gyada mata kai tana murmushi.

"Ita kad'aice fa a gidansu daga ita sai mamanta da babanta, 'yar gata ce ai."

Nanne taji kanta k'ulle, komai ya tsaya mata cak! Kamar yaya? Dama Imran ba wanta bane? Toh ya akayi kullum take ganinsa a k'ofar gidan duk tsawon watannin nan? Idan ba anan yake ba toh daga ina yake zuwa. Ta sake kallon walidan tace.

"Akwai wani da yake zuwa gidanku Imran?"

"Imran? Kai anya kuwa na sanshi? Ganinsa kika yi a gidan?"

"Ina yawan ganinsa ne a k'ofar gidan naku."

Ta kalli safiya tace.

"Kin gane wa take nufi?"

"Ta yaya zan gane, nina san duka 'yan uwanku ne?"

"Toh ai kina yawan zuwa."

Safiyya ta jiyo ta kalli Nanne tace.

"Waye shi?"

Ganin dai da gaske basu gane ba yasa kawai ta rabu dasu ta cigaba da kwanciyarta, suka d'ebi kala takwas sannan safiyya ta mayar mata da biyu suka fita.

Har dare tunanin Imran bai bar cikin kanta ba, mamaki take yi in ba gidansu walidan yake zuwa ba me yake kawo shi? tunda dai bayan gidan nasu ba wani gida a gefensu duk kangwaye ne. Ta tuna kuma yace mata wani lokacin yana zuwa wajen ya umar, amma in har wajensa yake zuwa ya kamata ace ta tab'a ganinsa a cikin gidan nasu ba sai ranar ba kawai, tunda duk wasu abokan yayyunta masu zuwa ta sansu.

Sai kuma ta tuna a cikin samarin nan dake yawan zama akan wata mota take ganinsa, in har hakane su zasu sanshi kenan, saboda haka tayi niyyar tambayar sadiq gobe.

Sai dai har ta kwanta bacci a ranar, kwakwalwarta tambaya d'aya take nanata mata.

WAYE SHI?

¡ñ©n¡ñ

*****

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

17


(¡î_¡î)

Imran ya shigo kicin ya dauki 'yar kettle d'in da yake had'a coffee ya nufi jikin despenser ya fara tsiyayo ruwa a ciki.

"Wai ta yaya ne zanyi ta binka tun jiya akan magana d'aya?"

Muryar jaamil ta fad'a daga bayansa.

"Wai ta yaya ne zanyi ta maka bayani guda d'aya tun jiya?"

"Yarima ya kamata ka zauna muyi bayanin nan sosai, ka fahimci abinda nake nufi."

Ya juyo ya bud'e cabinet d'in sama ya d'auko containers guda uku, na coffeee powder, madara da kuma sugar, ya zuba kowanne sannan ya maida kettle d'in jikinta ya kunna socket.

"Na fahimce ka tun jiya jaamil kuma na gaya maka cewa ba zai yiwu ba."

"Bamu da wata hanya bayan hakan yarima, saboda haka ba abinda zai hana shi yiwuwa."

"Okay then, let's talk."

Yaja kujera daga jikin island d'in ya zauna.

"Zauna." ya fad'a ganin jaamil d'in bashi da niyyar zama. yaja kujerar a hankali shima ya zauna.

"Ka saurareni da kyau don Allah....sanda kayi wannan tunanin Auren a cikin kanka, na san kayi la'akari ne da abubuwan da suka faru a baya, so lets make things clear, Bana son yarinyar nan kuma ban taba sonta ba, kawai da farko ne kafin in san rayuwar nan, yanayin maganarta ke burgeni shine har ka tab'a ganina a wajenta.

Amma tun daga ranar da na yiwa Naani alkawari cewa ba zan k'ara zuwa kusa da ita ba, na goge duk wani abu daya shafeta a zuciyata, kuma tun daga wannan lokacin i try my best to keep away from her. So abinda kake tunani ba zai taba yiwuwa ba!"

Jaamil yayi shiru na kusan minti d'aya yana kallonsa, sannan yace.

"A yaushe aka tsara cewa zamu yi iya abubuwan da kake so ne?...nayi tunanin muna yin duk abubuwan da zasu samo mana mafita ne."

Bai amsa ba ya cigaba.

"Ya kamata nima ka saurerini da kyau yarima, sanda ka shiga jikinta baka yi wani tunani ba balle shawara, kayi abinda ka san cewa kuskure ne, yanzu kuma da matsala ta b'ullo me yasa kake zaton zaka sami zab'i a cikin kuskurenka? Dole ne ka hak'ura ka karb'i duk wata dama da muke da ita hannu biyu.

Sannan dama bai kamata ka so yarinyar ba, saboda gabad'aya auren zai zama cikin abinda baifi wata biyar bane kawai, duk lokacin da Naani ta fito zamu ciro d'aya b'arin naka ba tare da ta sani ba sannan ka rabu da ita, mu k'arasa abubuwan da zamu yi mu koma rayuwarmu.

A ina kaji dole sai da zancen so abin zai yiwu?"

Imran yayi shiru yana saurarensa, abu d'aya kawai ya fahimta tun farkon zancen, shine duk wannan abin laifinsa ne bana jaamil ba, saboda haka da gaske ne bashi da zab'i, bai kamata ma ya samu ba, don in har ya samu d'in za'a iya kiran hakan da son kai.

Abinda yayi wani kuskure ne da babu shi a lissafinsa, bai ma tab'a tunanin abu makamancinsa ba, a rayuwarsa yana taka tsan-tsan da komai mai muhimmanci, baya tab'a bada k'ofar da wani abu zai kawo masa cikas!

Watakila shi yasa jaamil d'in ma yaji haushinsa a baya, yayi tunanin ko ya canja ra'ayi ne akan abinda suka tsara tun farko. Kafin daga baya shima ya gane cewar tsautsayi ne ya fad'a masa, ko kuma k'addara wadda bata wuce kan kowa.

Cikin tunaninsa ya tsinto muryar jaamil yana cigaba da magana, ba yadda zaiyi, dole ne ma ya yarda da shawarar nan, in ba haka ba zai cutar dashi ne, shi d'in dake ta fad'i tashi wajen ganin komai ya tafi musu daidai, komai kuwa...komai d'in da ba laifinsa bane.

Ya lumshe ido yana sauraren k'arar tafasar coffee d'insa daga baya. Ya riga ya yarda da duk abinda yake fad'a, saboda haka babu amfanin sauraren, sai da yaji ya kai k'arshe sannan yace.

"Ta yaya aure tsakaninmu zai yiwu?" ya tambaya daidai sanda kettele d'in ta kashe kanta da k'arar k'assss! Alamun tafasa.

"Yarima, na fad'a maka na tsara komai kafin na tunkare ka da wannan zancen, in har ka amince insha Allah komai zai yiwu cikin k'ank'anin lokaci."

Lokaci. Kalmar lokaci ta d'auki hankalinsa, ya bud'e idonsa sosai sannan yace.

"Jaamil aurensu yana d'aukan lokaci, ta yaya zanje har ta sanni na aureta kafin wata biyar kawai?"

*****

Sulaiman ya shigo cikin falon baffa da sallama. Babu kowa a ciki don haka ya samu waje ya zauna, don a lokacin k'arfe goma ne saura na safe.

Kusan mintuna goma kafin Baffan ya fito daga cikin d'akinsa.

"A'ah ashe kaine..."

Ya fad'a sanda ya taho kan kujerarsa ya zauna, a lokacin sulaiman yayi saurin saukowa k'asa.

"Nayi zaton ai Ibrahim ne yayi sammako, don yau zamu je wajen commissioner dashi akan maganar kwangilar nan."

Ya zauna sosai, sannan sulaiman d'in ya gaishe shi ya amsa.

"Dama wad'annan malaman da suka duba Nanne jiya ne suka zo, da tun jiyan ma suka so ganinka sai kuma baku k'araso da wuri ba."

"Toh...toh suna nan ne yanzu?"

"Eh, suna tsaye a compound."

"Toh shigo dasu mana, jeka ce dasu su k'araso. Koda kuma Ibrahim d'in yazo kace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login