Showing 42001 words to 45000 words out of 113985 words

Chapter 15 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28469

kyau me yasa ta d'auko mata.

Kamar tayi magana taga yanzu sai inna ta fassara zancen da wata ma'anar, saboda haka ta cukwuikuye ta mayar, ta d'auko riga da skirt na atamfa coffee da milk da kuma dogon hijabinta mai hannu milk.

"Su zaki sa?"

"Inna meye laifinsu to dan Allah, shifa bata shigata yake ba, tunda har zai iya zuwa neman aurena ba tare da amincewata ba na tabbata shigata baza ta sa ya fasa ba."

Ta saka kayan kamar gaske sannan tayi waje, ta tsakanin k'ofar gate d'in ta hango shi.

Yana tsaye daga jikin motarsa yana danna waya, sanye cikin wani milk yadi wanda ya kwanta akan fatarsa sosai, yana da d'an shara-shara kad'an don har ana iya hango layin singlet d'insa dake ciki, sannan yasa hula mai kyau kalar brown shigen aikin dake jikin kayan da kuma takalmi k'afarsa, zata iya rantsewa a rayuwarta tab'a ganin halitta mai kyau irinsa ba,

Zuciyarta tayi nauyi da tunanin cewa wannan jiran da yake nata ne, abinda tayi mafarki da tunaninsa fiye da cikin k'irga a baya, sai gashi a yau yake faruwa, yau d'in da komai ya cakud'e mata.

Tunaninta ya tsinke, taji kamar baza ta iya bin shawarar data yanke ba, amma in har bata yi ba, ta san sai tayi regretting hakan daga baya sau cikin carbi.

Tayi baya ta koma ciki sannan ta kira wani hanif d'an wata mai aikinsu dake wasa a gefe tace masa.

"In ka fita gate d'in nan zaka ga wani mutum a jikin mota kaje kace masa wai ance sa'adhan bata nan."

"Yaron ya d'an kalleta.

"Wace ce Sa'adha?"

"Nima ban santa ba a gidan nan take kuma bata nan, kaje ka fad'i abinda naka gaya maka."

Ta tsaya tana kallon tafiyar yaron, kowanne taku d'aya da yake ji take kamar taje ta jawo shi tace ya koma ta fasa ta fita wajen imran d'in dake jiranta. Amma kuma tunanin ya danne-danne abinda zuciyarta ke so, saboda haka tana gani har yaron ya fita ya rufe gate d'in sannan ta juya ta koma cikin falon da akace ta shigo dashi.

Bata tab'a tunanin cewa hannun mutum zai iya gyara d'akin ba tunda kusan kodayaushe a k'ulle yake cike da ku'ra, amma a yanzu yasha gyara tas! harda carpet aka shimfida da kuma wasu manyan tin-tin guda uku, sannan daga gefe turaren wuta mai dad'in k'amshi yana tashi a kaskonsa.

A tsakiya wannan farantin ne da ta hango a hannun lami cike taf! da duk irin snacks d'in da take so, a lokaci d'aya taji yawunta ya tsinke.

Ta koma gefe guda ta jingina da bango sannan ta cusa hannunta cikin lallausar sumarta kamar zata tsinto duk wata damuwarta waje. Har a lokacin kanta na ciwo sama-sama.

Komai ya cakud'e mata, kuma ta san ba sai ta fahimce su duka ba, abu d'aya ne kawai ya kasa shiga kwakwalwarta har yanzu, cewa Imran shine k'arshen duk wannan k'addarar tata.

Ta tuno da mafarkin data yi a jiya, mafarkin da su inna ke kiranta kar taje wajensa, a yanzu kuma su ke k'ok'arin had'a ta dashi, sannan wannan jinin hannun nasa sanda ta fad'i k'asa. sai tayi saurin ture wannan shi kuma, mafarki k'arya ne, ba zai tab'a zama gaskiya ba.

Ta dad'e zaune a d'akin kafin daga k'arshe ta janyo plate d'in nan ta cika cikinta dam, sannan ta kulle d'akin ta shigo cikin gida.

*******

Bayan ta idar da sallar magriba, ta cigaba da zamanta akan sallayar tana lissafo dukkan damuwarta ga jalla wata'ala, ta bud'e zuciyarta sosai ta rok'e shi akan Allah yasa duk abinda ke faruwa da ita ya zame mata alkhairi, tunda wani abu ne da baza ta iya canjawa ba.

Tana shafawa wayar inna ta shiga ringing, ta juya ta ga har a lokacin bata idar ba saboda haka ta d'auka ta kai kunnenta.

"Assalamu Alaikum."

A lokaci d'aya, taji tunaninta ya tsaya cak!

Wannan muryar, wannan muryar mai taushi ta cika kunnenta. taji tayi kewarta kamar ba'a jiya ne taji ta ba.

Calm down Sa'adha! just calm down!

B'arin zuciyarta mai hankali ya shiga bata warning.

"Waalaikum salam." Ta amsa a hankali.

"Sa'adha kina lafiya?"

Bani da lafiya kuma hankalina a tashe yake imran, komai ya cakud'e min a lokaci d'aya, sannan ga al'amarinka da na kasa ganewa, ka san irin halin dana shiga a baya? kace min zakazo na jiraka har dukka hope d'ina ya kare ban ganka ba, me ya hana ka zuwa? me yasa baka fad'a min kana sona ba? me yasa ka tafi wajen baffa kai tsaye? sannan tsawon lokaci baka neme ni ba? in kowa yak'i fad'a min halin da ake ciki atleast i deserve an explanation from you, amma kaima ka share ni, sai a jiya kawai ka kirani, babu tambayar lafiyata balle wani explanation kace zaka zo wajena, ni kuma banyi tunanin komai ba na biye maka, sai a yanzu ka damu da sanin halin dana ke ciki? me yasa ma zaka damu? bayan ka riga ka samu go ahead akaina? a yanzu ko da yardata ko babu ka san ba zan iya fasa aurenka ba, saboda ko ba komai nima na san har yanzu wani side d'in zuciyata yana sonka...

Maimakon duk wannan sai tace.

"Ina lafiya, Alhmdlilah."

This is clumsy. ta fad'a a ranta

"I'm sorry, ban tambayeki haka jiya ba."

Huff. wannan kuma ya wuce.

"I'm so sorry sa'adha, na san ban kyauta miki ba, na san nayi abubuwa da yawa wanda ba haka ya dace ba..."

"Me ya hana ka zuwa ranar da kace min zaka zo?"

Tayi saurin katse shi, in har zata saurareshi gwara ayi komai tun daga farko, tana bukatar bayani da yawa.

Ya danyi shiru kafin a hankali yace.

"Sulaiman ne ya hanani zuwa wajenki sa'adha, ba'a ranar kad'ai bama harda duk sauran lokutan da ban nemeki ba."

Taji wani k'aton abu ya fad'a daga zuciyarta, ya sulaiman kuma? ta ina ya shigo zancen?

"Tun ranar dana fara ganinki a k'ofar gidanku rayuwata ta canja, duk wani tsari da nake dashi ya ruguje, na zama ba abinda nake iya yi ba tare da tunaninki ba, tun ban fahimta ba har nazo na gane cewa sonki nake yi, irin son da zuciyata bata taba yiwa kowa ba.

Zan so in iya fad'a miki kuma ki fahimci irin son da nake miki sa'adha, duk sanda na rufe idanuna ke nake gani, in na bude su kuma sai inji ke d'in kawai nake son gani, duk da bana iya samun ganinki kullum amma i always feel your presence around me.

Every second, every moment, every hour, my eyes search for you only, call this love, craziness or the beat of my heart... it is all same for me.

I love you very very much Sa'adha and i don't want to lose you, ever!

Shi yasa a ranar dana ce miki zanzo naje na sami yayanki sulaiman na gaya masa damuwata, shi yace inje wajen baffa sa'adha, shi yace kar in neme ki na tsawon lokacin nan sai na samu yardar baffa tukunna. a duk tsawon lokacin ba mantawa nayi dake ba, ina ta fad'i tashin neman amincewar baffa ne har na samu ya saurare ni, don da farko yace min yayi maganar ki da wani d'an abokinsa ne.

Da Sulaiman da umar su suka yi ta min kokari a wajen baffa har na samu ya saurare ni, daga nan kuma yace zan iya turo magabata na, ko a lokacin na so zuwa in sanar dake komai amma sulaiman yace in bari inji me zasu tattauna tukunna.

Kamar yadda aka fad'a miki nima haka naji zancen sa'adha, bayan tattaunawarsu, sun yanke mana rana zuwa nan da wata guda kuma wallahi duk da bani na tambaya ba i'm more than happy.

Shi yasa jiya dana kira ki na kasa cewa komai...nace miki laifina da yawa sai nazo zan fad'a miki duka reasons d'ina, kuma nazo kika ce min bakya nan."

Ya k'arashe zancen muryarsa can k'asa kamar k'aramin yaro.

Nanne taji duk wata jijiya a jikinta tayi sanyi, gabad'aya fushin da take ji game dashi yabi iska, maganganunsa kamar sun sa hannu ne sun yaye rabin duhun da take ji game dashi, bakinta ya k'ulle ta rasa me zata ce. sai ta jingina kawai da jikin gado ta dunk'ule jikinta waje d'aya.

Shiru ya biyo baya ba tare da yayi magana ba.

"I'm sorry Sa'adha, i'm reeeeallly sorrry, dan Allah kiyi hak'uri if i've hurt you in anyway."

Yadda muryarsa ta fita a hankali da kuma zurfi, yasa taji kamar zata narke gabad'ayanta.

I'm so sorry nima da na kasa fahimtarka a baya, i'm sorry da duk wahalar da kasha akaina, i'm so sorry dana kore ka d'azu.

Ta ayyana hakan duk a zuciyarta, sannan ta sake k'ank'ame wayar a hannunta ba tare da tace komai ba.

"Sa'adha..."

Sai da zuciyarta ta buga da k'arfi jin yadda muryarsa ta nannad'o sunan kamar tun asali shi ya bada shawarar a rad'a mata.

"Na yarda kiyi punishing d'ina duk yadda kike so amma dan Allah kar kice kin fasa."

"Na fasa me?"

"Aure na."

Kalmar tayi mata nauyi sosai, don duk sauran dauriyarta ta tattare ne wajen yadda muryarsa ke shiga kowanne lungu da sak'o na jikinta.

"Na san ba zaki fad'a ba koh?"

A hankali ta daure tace.

"Baffa ya riga yayi magana ai ba zan iya masa musu ba."

"Saboda Baffa ne ba saboda kema kina sona ba?"

Ta damk'e k'arshen hijabinta da k'arfi sanda sallamar sallar inna ta shiga kunnenta. jin tayi shiru yasa yayi murmushi sannan yace.

"Karki damu, zan koya miki yadda zaki so ni, for now wanda nake miki ma ya ishemu mu biyu."

Taji maganganun suna shirin yi mata yawa a rana d'aya kawai da komai ya kwance mata saboda haka tace.

"Sai da safe."

"Zaki kore ni? dan Allah sa'adha kar ki d'auki fushin nan da nisa, so nake mu sake komai afresh, in sanki sosai kema ki san ni."

Tayi shiru tana cije lebb'enta na k'asa.

"Kinjiii....?"

Da sauri tace.

"Naji, sai da safe."

"Ya na iya...sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya."

"Ameen."

Tana shirin d'auke wayar daga kunnenta taji abinda ya d'auke numfashinta gabad'aya.

"I love you!"

¡ñ©n¡ñ

Next chapter zamu ji yadda akayi imran ya iya tsara duk wad'annan abubuwan.

Sannan zamu ji yadda zata bashi damar da zai gaya mata WAYE SHI.

Kuna tunanin zai gaya mata gaskiya?

Ko rabin gaskiyar?


****

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

30


Assalamu Alaikum...i can't beleieve we are up to chapter 30 already! ya Allah kamar jiya ne fa kawai naci na qoshi na rasa me zanyi na jawo wayata na fara typing...gashi har mun fi rabi na cikin labarin nan.

Kuma Allah ba don ku ba, da tuni na jefa shi a dustbin d'in da nake tara irinsu, cox i have lots of uncompleated stories kamar meh?

Nagode da dukkan support d'inku...dix shapta is dedicated to o laf yuuu!...(lol??) I mean all of you!

Enjoy!??

(¡î_¡î)

"Nanne...?" muryar Rahma ta kira ta.

"Mhmmm." ta amsa halfway cikin barci ba tare da tunanin komai ba.

"Yau baccin me kike yi haka, sha d'aya fa ta wuce."

Jin haka yasa ta bud'e idanunta da sauri ta kalleta.

"Da gaske kike sha d'aya?"

"Na gaya miki ma fa ta wuce, inna har ta fita asibiti nima shigowata kenan."

Ta mirgina a hankali ta juya kan bayanta.

"Ni kaina ban sani ba, na dad'e banyi bacci irin haka ba."

"An kawo miki sak'o yanzu wani yaro ne ya kawo daga waje, shi yasa ma na tashe ki."

Nanne ta had'e girarta waje d'aya.

"Sak'o? meye a ciki?"

"Sak'o fa nace miki, ta yaya zan bud'e."

Ta matsa jikin dressing mirrow ta d'auko wata brown leda k'atuwa mai logo d'in hannaye biyu.

"Kamar wani kwali ne a ciki."

Nanne ta mik'e sosai akan gadon ta karb'i ledar, tana bud'ewa taci karo da wani pink box medium size a jikinsa akwai large prints d'in flowers purple.

Ba tare da tunanin komai ba ta bud'e cikinsa, idanunta suka ci karo da ledoji na different kinds of chocolate, tun daga kan wanda ta sani harda wanda bata tab'a gani ba, gasu nan fal! a ciki.

"Lallai kayan dad'i ne ashe, daga ina haka?"

Rahma ta fad'a tana zama akan gadon, ita dai tayi turus! da murfin a hannu tana kallon su, daga can gefe idonta ya hango mata wata takarda ta janyo ta a hankali ta bud'e.

Sa'adha....!

Yau ina tashi da safe naji a News wai sugar yana kwantar da anger dake
jikin mutum, zaki taimaka kisha wannan ko zamu samu fushin da kike dani ya ragu?

Bata san lokacin da wani d'an guntun murmushi ya sub'uce daga fuskarta ba.

Bayan ta fito daga wanka ta zauna a gefen gado tana shafa mai tana kallon fuskarta ta cikin mudubi, akan mudubin wannan box d'in alawar yana facing d'inta.

Wayar da tayi da imran a jiya kawai ta wanke abubuwa da yawa a cikim kanta, idan ta tuno cewa duk tsawon lokacin nan ba share ta yayi ba yana ta neman hanyar da zai same ta ne sai taji wani dad'i ya wanke zuciyarta, sannan idan ta tuno kalaman daya gaya mata cewa shima yana sonta sai taji kamar tana daya daga cikin wadanda suka fi kowa sa'a a duniya, don Imran daban yake daga irin mutanen data sani kuma take gani.

Ance mutum baya taba zama cikakke, amma ita gani take shi komai nasa perfect ne! komai da ta sani a yanzu, kamar ice cream mai dad'i ayi topping d'insa da m&m's...

Ta ina za'a sami matsala a cikinsa?

Ta kalli box d'in ta tuno da d'an short text d'in nan, wani dad'i ya ratsa ta, kamar an saka k'ank'ara a cikin zuciyarta.

Da gaske Imran yana sonta.

Da gaske ne ba mafarki take ba.

Yace yana so suyi starting komai afresh, kenan zai gaya mata waye shi da duk sauran details d'in rayuwarsa, kamar yadda ya fad'awa baffa har ya yarda ya bashi aurenta, in ma bata san duka a yanzu ba, ta tabbata zata sani nan gaba.

Tunda k'addararsu ta riga ta zama d'aya.

A lokacin ne taji wani abu a gefenta yace zut! tana juyawa taga ashe tana zaune ne kusan akan rabin wayar inna, aikuwa idonta ya gane mata number da taje tana kira, number Imran ce da yake itace ta farko akan call log d'in.

Da sauri tasa hannu ta katse kafin ya kai ga shiga, me zai kaita kiransa a yanzu? tace masa me?

Ta mik'e ta nufi sa kaya, sai dai kafin ta zak'ulo kayan da zata saka k'arar shigowar message ya shigo.

A wayar inna dai ta san banda layin gidan waya babu masu turo da text, sai ko wani lokacin wrong number, amma kawai sai ta samu kanta da matsawa ta d'auko wayar.

Da gaske text d'in ne kuwa, kuma ba daga layin waya ba balle wrong number ba. Daga number Imran.

Missing me already?...ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d'inki Habibty...

...like crazy!

Hannayenta suka shiga rawa, dama kiran ya shiga kenan? ya salam! yanzu me zaiyi tunani akanta? zaice har ta fara kiransa kenan? ta ya zata ce masa bata san ta kira ba?

Ta ajiye wayar ta koma wajen wardrobe ta jawo kayan da hannunta ya fara kaiwa kansu, ta saka rigar amma kafin ta zuge zip ta koma ta d'auko wayar ta sake karanta text d'in.

Habibty. Ta fad'a a hankali.

He just call her habibty!

*******

"Toh ina jinka...sai kuma kayi me bayan nan?"

Jameel ya tambaya yana kallon Imran dake zaune a study room d'insa yana signing wasu papers. shi kuma yana zaune ne akan wata couch dake jikin glass wall na d'akin. D'akin triangular ne mai bango uku, bangon k'arshe shine aka yishi da glass gabad'aya inda daga ciki kana hango d'an k'aramin garden d'in gidan mai d'auke da flowers.

"Na kira ta a waya, na bata hak'uri kuma nace mata nima ina sonta kamar yadda itama take sona, sannan nace mata zanyi mata bayanin ko ni waye saboda ni da ita mu fahimci juna."

"Yarima...."

"Na sani jamil..." yayi saurin katse shi.

"...Ba sai ka tuna min ba, na san bamu tsara haka ba, na san na dawo yanzu ne saboda ciwonta yana shirin dawowa sannan na san bamu yi da kai zan kulata ba har lokacin da za'ayi auren.

Amma idan har muna tsarinmu dole ne mu dinga duba yanayin rayuwarsu suma. ba zai yiwu don iyayenta sun yarda da auren ba kawai ace babu wata alak'a da zata shiga tsakaninmu a yanzu, a tsarinsu dole ne a samu fahimtar juna tsakanina da ita wanda in babu hakan, ba yarinyar kad'ai ba har iyayenta zasu fara suspecting wani abu, kuma babban abinda zai fara rusa mana shiri, shine in har wani ya fahimci cewa akwai wata manufar da yasa nake son aurenta.

Saboda haka dole ne jaamil sai nayi acting cewa da gaske ina son ta ne. kamar yadda ka fada a baya ka gama naka aikin saura nawa, don haka ba sai anyi auren zan fara zan fara part d'ina ba, zai fara ne tun daga yanzu."

Jaamil ya d'anyi shiru yatsunsa akan lebb'ensa yana nazari, daga can kuma yace.

"In dai zaka tafi da hakan akan tsarinmu ba matsala bane yarima, I'm just afraid kar ka zama so close da ita nan gaba...."

"Na gaya maka bana sonta jaamil, abinda ya faru tun farko ya riga ya wuce, har yaushe zaka yarda dani ne wai?

Sannan ni kaina ina da hankalin da zan san cewa Sa'adha ba abokiyar rayuwata bace, halitta ta da tata daban ce, ko banzo cikin mutanen da wannan manufar ba, ba zan tab'a fad'awa wannan kasadar ba.

Rayuwata daban ce da irin tasu kuma na san a kowacce halitta aure shine cikar rayuwa, to ta yaya zan k'arashe rayuwar da ban fara anan ba?"

Jaamil yayi shiru baice komai, hakan ya bawa imran tabbacin cewa ya d'aure shi ne da jijiyoyinsa.

***

K'arfe sha biyu saura na rana, Imran na cikin office d'insa yana harhad'a takardun da ya gama signing, sha biyu daidai zasu shiga meeting da wani sabon company da suke son fara bussiness dasu.

Wayarsa tayi haske, wani d'an mitsitsin haske da ba don idonsa na kusa ba zai gani ba. ya mik'a hannu ya jawo ta gabansa, mamaki ya kamashi ganin number Sa'adha, ya sake kallon agogo, yau friday...bata je makaranta ba kenan?

Ya tuno da fuskarta a jiyan nan, sanda ta lek'o tana kallonshi daga cikin gate din gidansu. a lokacin yaji kamar ya shekara ne bai ganta ba, duk da cewa bata canja ba, amma wad'annan fararen idanun nata cike suke da damuwa wanda ya tabbatar masa da cewa abinda ya karanta da ita a sanda yaje don kwantar da ciwonta gaskiyane kenan.

Zuciyarta tana cikin damuwa, damuwa mai yawa kuma rabi akansa ne, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login