Showing 57001 words to 60000 words out of 113985 words
me tayi missing da kuma bayanin yadda komai yake dalla-dalla.
Tayi masa bayanin yadda fasalin gidansu yake tun asali kafin azo a canja abubuwa daga baya, yadda wajen baffa yake, yadda kitchen d'insu yake da tarin 'yan aikinsu da kowanne sai da tayi masa bayanin nasabarsa da gidan tun asali, sannan ta dawo kan jerin d'akunan yayyenta har zuwa kan bene, hawa na farko, na biyu da kuma barandar can sama, ta dinga kwatanta masa yadda wajen yake da yamma, cike da iska mai dad'i da kuma yadda mutum ke iya ganin yadda rana ke faduwar a yamma.
Ta dinga bayanin tana kwatance da hannunta, yadda yayi shiru yana saurarenta ta cikin dim hasken tvn, yasa ta zama freely tayi ta magana. Daga k'arshe ta k'are da bayanin yadda setting d'in dakinsu yake, d'akin kwanansu ita da Inna.
Murmushi tayi a hankali data tuno cewa yau kuma ranar tace, daga yau nata tambayoyin zasu fara, jerin gwanon tambayoyin da tara akansa fal! gasu nan kwando-kwando zube a kowanne lungu da saqo na zuciyarta.
Tun daga lokacin data daina ganinsa a k'ofar gidansu d'in nan har zuwa yanzu, ta k'ara ta jera su perfectly akan wanda ta tsara kwanakin baya, wancan lokacin daya maido ta gida da daddare yace mata zaizo washegari, wancan lokacin da ya zama mafarin rayuwar da take ciki yanzu.
Excitement raced through her at all the thoughts she would unlock today.
Ta mike ta nufi toilet, idonta na kaiwa kan reflection d'inta a mudubi mamaki ya kamata, wani k'aton tabo ne jazur dashi ya fito a gefen kumatunta, tasa hannunta da sauri ta tab'a wajen, babu tudunsa akan fatarta sai jan kawai, kamar irin bruise d'in dake fitowa in mutum ya buge ko jini ya taru a wajen.
Ta wanke fuskarta da sauri sannan tayi brush, anan taga wani mark d'in a gefen wuyanta da k'asan kunnenta, ta tuno yadda Imran yayi kissing d'inta a wajen jiya.
Matsalar jikinta kenan, very sensitive yake akan komai, a gida ko kurjewa tayi sai wajen gabad'aya yayi jawur. Tayi tunanin concealer zata shafa duk su b'ace amma kuma duk a cikin kayan kwalliyarta yanzu bata da ita, sannan na cikin lefe ta gansu duk masu duhu ne, in ta shafa zaiyi daban da farar fatarta.
Ta koma cikin d'aki ta tsaya a gaban full body mirrow d'in dake gefe, tana binciko su d'aya bayan d'aya, akwai da yawa a wuyanta da k'asan hab'arta, ta zame hannun doguwar sleeping dress d'inta nan ma akwai su da yawa, abin ya fara bata mamaki yadda suke da yawa haka, kamar wani abu na ciwo.
A lokacin taji k'arar bud'ewar kofar d'akin.
Tana juyawa idanunta suka ci karo da Imran rik'e da breakfast tray a hannunsa, singlet ce kawai a jikinsa sai wando three-quarter, lallausan gashin kansa a barbaje har yana saukowa goshinsa sannan fuskarsa d'auke da wannan murmushin dake dulmiyar da tunaninta, taji kamar ta d'auke shi ta kaishi can k'asan zuciyarta ko zata samu sauk'in abinda take ji duk sanda ta ganshi a ranta.
"Good morning Habeebty!"
Ya fad'a yana lumshe dogwayen lashes d'insa akanta. Hancinta ya jiyo mata daddad'an had'in wani abu kamar scrambled egg da fries, sannan ga sandwiches tana gani a bowl da kuma had'add'en Oats a mug guda biyu.
Ta maida hannun rigarta a hankali sannan ta k'arasa gabansa. Sai dai kafin tace wani abu idonsa ya hango masa tarin bruises d'in dake jikinta, idanunsa suka zare da tsantsar mamaki ya lalubi kan dressing mirror ya ajiye tray d'in sannan ya matso ya shigo jikinta.
"Me ya same ki? Meye wannan?"
A hankali tace.
"Nima ban sani ba, yanzu na tashi na gani."
Daga yanayinsa ta lura ya tsorata sosai, sai faman dubawa yake yana shafa wajen, saboda haka yace.
"Ba ciwo bane bafa, may be wani abin ne ya same ni, I easily get bruises like this... amma ina shafa concealer zai tafi."
Sai a sannan taga reaction d'insa ya d'an kwanta. Ya lalubi kunnenta a hankali ya rad'a mata.
"I'm sorry!"
Maimakon ta amsa sai tace.
"Zamu je mu siyo anjima?"
Taji sautin murmushinsa kafin amsar ta biyo baya.
"Zamu je mu siyo kwalayensu da yawa Sa'adha, don zasu mana amfani sosai."
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
38
(¡î_¡î)
Nanne ta taho da sauri daga cikin d'aki don bud'e kofar main falonta da ake ta knocking, Wani dad'i ya kamata sanin cewa bak'i tayi, bakinta na farko a gidanta da tayi sati d'aya a ciki.
Don ta san cewa ba Imran bane tunda basu fi minti talatin da gama waya ba, kuma ya gaya mata sai yamma zai dawo, yauce ranar farko daya koma aiki, ranar farko data fara rabuwa dashi ta fara zama a gidan ita kadai.
Dazu da tana gyara d'aki ta d'auki filonsa ta shinshina k'amshinsa dake jiki, awa uku kad'ai amma tayi missing d'insa kamar kwana uku, tayi missing muryarsa mai taushi da babu ita a gidan, tayi missing yawan bibiyarta da yake yi a komai, tayi missing tambayoyinsa da har yanzu basu k'are ba, God...! tayi missing hannunsa ma da kullum ke cikin nasa.
Kwanakin shidan da tayi tare dashi gani take kamar shekara shida ne saboda yadda ta saba dashi sosai, He's the best husband anyone could ever wish for! Dukkan irin rayuwar da tayi mafarkinta a baya tare dashi ta same ta har ma fiye da hakan, Imran was caring, loving and showers her with so much affection.
A iya tambayoyin data ware a yanzu wanda taga su ya kamata ta fara sani game dashi, ta fahimci mutum ne mai saukin kai sosai, baya tab'a d'aukan abu da zafi a rayuwarsa kuma ra'ayinsu da yawa yazo d'aya wajen so da k'in abubuwa.
Sannan bai cika complain ba, rana farko da suka fara yin girki a gidan kusan k'onewa yayi amma haka ya zauna ya cinye baice komai ba, sannan komai tace masa za'ayi ko tana so zai biye mata suyi da dukkan iyawarsa sau da yawa tana jin kamar tana ordering yaro k'arami ne, (D'aya daga cikin abubuwan da take so a rayuwarta.)
Sannan in har abu nada matsala zaiyi mata bayani in a simple way da zata gane ba tare da taji haushi ba.
Tun a cikin weekend d'in nan yake bata hak'urin komawarsa wajen aiki wanda a lokacin ita bata ga komai, ba sai a yanzu da ta jita a gidan tsit tukunna! Ta tuna yadda yayi ta kissing cheeks d'inta da safen nan yana gaya mata zaiyi mata misssing d'inta da yawa.
Taji tarin abubuwa sun tsaya mata cak a lokacin, ta rasa wanne zata fara tunkara, ta riga ta saba komai tare dashi take yi, komai k'ank'atar abu kuwa, da kyar ta tsaida ranta ta fara share gidan tas! sannan tayi mopping, kafin ta gama taji bayanta na shirin k'agewa kamar ta share wani waje mai tarin datti.
Ta gyara kitchen ma sannan taje tayi wanka, tana komawa kitchen d'in ta sake tunowa dashi, kullum sai su shafe lokaci mai yawa ana debating me za'a dafa, in ta tambaye shi me zai ci, shima sai ya tambayeta me zata ci yana yi yana wasa da gashinta da a yanzu ta manta yaushe rabon data d'aura d'ankwali, don ko tasa ba zaifi minti biyu ba zai cire shi.
Da kyar ta tsaida ranta akan me zata dafa, ta duba fridge taga lemukan da suka hada jiya wajen kala uku suna nan, ta ciro wanda aka had'a da gwanda, ayaba, madara da kuma sugar ta dawo dashi k'asa don ya rage sanyi.
Sai da girkin ya kusa gamawa sannan ta koma d'aki d'auko kud'in da zata bawa malam Aminu ya siyo mata Slippers d'in da zata saka a toilet d'in cikin d'aki, a sannan ne taji bugun k'ofar falon.
Tana bud'ewa idanunta suka ci karon da tarin mutanen da bata san tayi missing d'insu kamar hauka ba irin yanzu. Ta daka wani irin tsalle tare da ihu.
"Na shiga uku, Nanne yaushe zaki yi hankali ne wai?"
Aunty maryama ta fad'a sanda ta d'ane kanta, ta sake ta ta koma kan Aunty Nafisa sannan Aunty zainab, ga Rahma, ga wata 'yar uwarsu Sadiya... idonta ya ware da taga harda Amina, Ta sake daka wani tsallen kafin itama ta rungumeta.
"Anya Nanne k'alau kike kuwa? sai kace kin shekara baki ganmu ba, kwana shida ne fa kawai."
Ta juyo da bakinta a washe tana kallon aunty maryaman da suka yiwa kansu masauki a cikin falon. Tayi missing fad'anta ma kamar me.
"Haba Aunty toh yaushe na tab'a zuwa wani waje na kwana shida, sannan bani da ko waya fa balle in kira gida."
"To sai kiyi kuka yanzu..."
Aunty zainab ta kwaikwayi muryarta, dukkansu suka fashe da dariya.
Basu ko gaisa ba ta fara tambayar.
"Inna inna? tace a gaishe ta? yaushe zata zo? muryarta ta washe yanzu? jikinta bai mata ciwon gajiya ba? ya k'afar tata? ta koma asibiti bayan bikin..."
"Mu nan duk ba mutane bane ai da bama zaki bari mu gaisa ba."
Sai kuma 'yar kunya ta kamata, ta fara gaishe su d'aya bayan d'aya, Aminah tace.
"Rufa min asiri ke yanzu ai Aunty ce, matar Aure guda."
Ta juya idonta tayi magana yadda Aminan ce kadai zata ji.
"Kamar kuwa kin san dama in nayi waya da Aunty Sa'adah zance kiyi saving numberta."
"Ai in baki fad'i haka ba, ba zan tabbatar ke d'in bace.
Rahma dake gefe hankalinta na kansu ta kyalkyale da dariya. Ta tashi taje kitchen ta kashe girkinta sannan ta d'auko musu lemon data fito dashi da ruwa sannan ta had'o da ragowar cupcakes d'in daya siyo.
"Mu fa yanzu zamu wuce, kasuwa zamu kar rana tayi mana."
Ta kalli Aunty Nafisan sanda ta mik'a hannu ta k'arbi 'yarta Shukra.
"Kasuwar ina?"
"Ta can k'ofar gabas, gobe duk zamu koma gida."
"Wayyo, zaku bar inna ita kad'ai."
"Ke ba tafiya kika yi kika barta ba."
Kafin ta amsa Aunty maryama tace.
"Ke ni kamar ba haka kujerun d'akin nan suke da farko ba koh?"
"Eh, mun canja tsarinsu ne, wancan style din yasa sun had'e a waje d'aya."
"Ke da wa?"
"Nida shi, shi ya taya ni."
Amina ta kalleta baki a sake sannan tace.
"Gaskiya Aunty nima aure zaku min, yarinyar da muka bari tana kuka kamar ranta zai fita ita ke wannan bayanin..."
Nanne ta d'aka mata duka a bayanta. Suka yita hirarsu ana dariya, kasancewar su Aunty Nafisa basu fiye d'aukan kansu da girman kai ba ganin su Nannen ba sa'anninsu bane.
Sai da zasu tafi Aunty Maryama ta jata d'aki tana tambayarta game da zancen 'yan uwan mijinta da basu ga ko d'aya ba ranar kawota.
"Wallahi Aunty nima banga ko d'aya daga cikinsu ba har yanzu, ya dai ce min ne dukkansu sun koma saboda wai basu da wajen zama anan garin sai kuma ranar da muka gaisa a waya da matar k'anin baban nasa daya bani labarin ta taimake shi sosai a rayuwarsa, amma bayan ita ni ba wanda na sani."
"Toh dole ne kuwa ki dinga tambayarsa game dasu, tunda a yanzu dole danginsa kema sun zama naki, kuma shi mutumin kirki ne Nanne kinyi sa'ar miji dole ki san yadda zaki dinga kula dashi, ince dai kin rike duk abinda na gaya miki ranar nan koh?"
Ta had'iye wani abu a makogwaronta, don ko kalma d'aya baza ta iya tunawa a tarin zancen da akayi ta d'ura mata ranar ba, don a lokacin abinda ke gabanta daban ne, amma sai ta d'aga kanta da sauri tace.
"Na rik'e komai Aunty."
"Toh madallah, ga numbobin wayoyin mu nan duk jna rubuta a wannan paper, harda tasu inna da sauran 'yan gidan naku, duk randa kika samu waya ki kira kowa ku gaisa kafin ki samu zuwa."
Kanta tsaye tace.
"Ai watakila ma a cikin satin nan zani gidan, tunda tun ranar da aka kawo ni yace zamu je."
Aunty maryama ta d'auko salati tun daga farko har k'arshe ta dire.
"Ai na san zaki aika uwar san yawo...wato har kin fara tambayarsa zuwa gida ko sati baki gama rufawa ba, toh kar ki fasa...yi ta tambayarsa ya kaiki gidan, in kinje bayan fad'an Baffa na inna ma kad'ai ya ishe ki."
Ta had'e rai a lokaci d'aya.
"Toh dan Allah meye dan naje gida yanzu, gidanmu ne fa ba wani waje ba, daga tafiyata da kwana shida har sai a fara korata?"
Bata kai amsa mata ba Aunty Nafisa ta shigo d'akin.
"Daga kitchen d'inki nake Nanne, komai tsaf-tsaf an zama matar gida, amma tun yaushe kika fara girki?"
"Tun washegari muka je muka siyo komai."
"Danginsa basu kawo muku komai ba?"
Ta girgiza kanta.
"Da safen ma sai da ya siyo abinci."
Aunty maryama ta karb'i zancen.
"Yanzu nake gaya mata ai, dole ne a hankali ta dinga tambayarsa game dasu gar ta gano wani abin in akwai."
"Gaskiya dai, idan matsala ce yake dasu dole ne ki gano ta ki kuma san yadda zaki gyara tsakaninsu, in ba haka ba ke kanki bak'in jini zaki yi a wajensu da kuma 'yayan da zaku haifa, saboda haka dole ne ki gyara bakin zaren tun yanzu."
Nanne tayi shiru kawai tana jinsu, a tunaninta dangin Imran ba matsalarta bace, dasu da babu su duk uwarsu d'aya ubansu daya a wajenta, indai har tana tare dashi kuma yana cigaba da nuna mata kulawar da a yanzu suka fara.
Zancen Aunty Nafisa na farko ya d'auki hankalinta, da tace 'ya'yan da zasu haifa, Ya Allah! Zuciyarta ta narke da tunanin 'yan little babies d'in da zasu zama combination d'inta ita da Imran. Zasu yi kyau sosai ta san, musamman ace su d'auko kammanin Imran sosai.....
"Kina jin mu wai kuwa?"
Muryar Aunty maryama ta katse tunaninta. Da sauri ta kalleta tace.
"Aunty Naji komai, kuma insha Allahu zanyi yadda kuka ce."
Da haka suka yi ta cika ta da wasu shawarwarin suka tafi bayan Aunty maryamah ta mata dogon kashedin daura d'ankwali. Aka bar Rahma da Amina kad'ai.
"Wai ta yaya kika biyo su, ko har yanzu kina gida."
"Haba dai na koma tun washe-gari, Rahma ce ta kirani jiya tace zata biyo su Aunty Nafisa yau ko zanzo, shine naje muka taho tare."
"Kin kyauta wallahi, baku san yadda nayi missing d'inku ba kamar me?"
"Ni ban gani ha, kinga wani irin fresh da kika yi?"
"Dan Allah? ni kuwa ban gani ba."
Ta kalli Rahma da tayi kwanciyarta akan kujera tana facing Tvn dake nuna tashar Bollywood tace.
"Wai kin koma islamiyya?"
"Eh ranar laraba kawai naje."
"Yawwa ai dai kinje, ko bakya so kuwa sai kin bani labarin irin gulmata da aka kafa a makarantar nan, don na san tabbas za'ayi."
Rahma tayi murmushi tace.
"Kema kin san wannan dole ne, don yanzu maimakon mijinki ke kika koma General topic d'in islamiyyar."
"Dan Allah, me da me suke cewa?"
"Ina zuwa dai su maryam suka hau ni da zancen wai dama ni da ke mun san shi zaki aura muke jinsu suna ta b'ab'atu akansa.
Su kuma su Aysha suka dame ni da tambayar wai in gaya mata ta yaya kuka had'u, a ina ya ganki yace yana sonki, da wasu tarin tambayoyi dai."
"Ni ba wannan na tambaye ki ba, negative d'in zancen nake son inji."
Rahma tayi shiru tana murmushi, Nanne ta tashi daga gefen Amina ta koma wajenta.
"Ai na rantse ko ba kya so sai kin fad'a min."
Ta cafki hannayenta ta murd'e su ta baya, ta kwallara k'ara had'e da dariya tana fad'in ta sake ta.
"In kina so in sake ki fara bayani."
Rahma ta dinga k'ara tana neman taimakon Amina wadda ke ta kyalkyala dariya tana kallonsu. Sai da taga da gaske Nanne baza ta sake ta ba sannan ta lallab'a tace zata gaya mata.
"Ina jinki toh."
"'Yan ajin malam isma'il ne suke yad'a zancen wai k'ila wani abu kika yi masa ya aure ki tunda har kika shigo islamiyyar baki sanshi ba, kuma kowa ya san ba wadda yake kulawa a unguwar tun zuwansa."
Nanne tayi kwafa tace.
"Toh me kika ce musu?"
"Me kuwa zan ce musu? masu fad'a fa da yawa ba wai mutum d'aya bane kuma nima tsintar zancen nayi."
"To ba kince daga ajin malam isma'il aka fara ba, nan zaki je kici mutuncinsu gabad'aya."
"Kema kin san ba zan iya ba, da dai kina nan ne."
"Yanzu ma ai bai wuce duk ranar da zanje gida sai na tabbatar ranar makaranta ne, inje inci uw*rsu wallahi, yadda suka fara zancen nan haka zasu san yadda zasu tsaida shi."
Ta sake yin kwafa.
"Wato ma wani abu nayi masa, toh zanje in gaya musu asiri nayi ba wani abun ba kuma gwara ni nawa yaci akan nasu."
"A'uzubillahi..." cewar Amina.
"Wannan wace irin magana ce?"
"Ke baki san yaran nan bane Aisha, tun da haushinsu nake ji wallahi." Rahma tace.
"Wato Nanne yara, duk fa sun girme mu."
"Ke kuwa yanzu tayi aure ai muma duk kallon yara take mana."
Nanne ta kalleta da gefen ido tace.
"Ga ku nan 'yan matasa dai haka."
Amina ta jefo mata d'aya daga cikin throw pillows d'in gefenta, suka yi dariya gabad'ayansu.
Bayan sunyi sallah, Nanne ta zubo musu abincin da ta dafa sannan ta mik'awa malam Aminu ma nashi, suka ci suka k'oshi sannan aka sake dasa wata hirar, Nanne tayi ta dariya tana jin dad'i, ji take a yanzu kamar duk sanda Imran ya fita suzo suyi ta hira.
¡ñ©n¡ñ
Thank you so much for reading this far!
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
39
(¡î_¡î)
"Tunda kazo garin nan baka da abokai ne? Su waye freinds d'inka ? ban tab'a ji ka fad'i sunan kowa ba, ko baka dasu?"
Muryar Nanne ta wancan lokacin ta dawo cikin tunanin Imran, yana zaune a cikin office d'insa a lokacin amma ya kasa k'arasa ayyukan dake gabansa, tunanin tambayoyin da tayi masa kwanaki uku keta yawo akansa.
Kafin lokacin yasha tunanin yadda zai amsa mata su a cikin kansa, ta yaya amsarsa ya kamata ta kasance? da k'arya mai ma'ana ko kuma da k'aryar da baza tayi kama da gaskiya ba?
Sai gashi tambayoyin sun fito a yadda bai zaci zasu kasance ba, don duk cikinsu ba wanda ke da alak'a da nasabarsa, nasabar da zata kaita ga sanin WAYE SHI..? sun ta'allak'a ne kawai akan sanin intrest d'insa akan abubuwa da kuma Habit d'insa, kuma masu sauk'i ne, they gave away nothing! sannan shima duk amsoshin daya bata masu tsafta ne, suna dacewa da labarin k'aryar daya d'orata akai tun farko, k'aryar da ya fad'awa Iyayenta suka amince da bashi aurenta.
Bai bada ko k'aramin hint d'in da zaisa ta fahimci wani abin daban game dashi ba, sai dai ma shi daya gane inda tunaninta ke tafiya akansa, and it was nowhere close to suspense!
Kwakwalwarta a goge take game al'amuransa, babu wani abu koda d'igo na zarginsa a cikin kanta, son da take masa ya lullub'e hakan, ta riga ta yarda da