Showing 108001 words to 111000 words out of 113985 words

Chapter 37 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28465

wannan d'an kyakyawan Babyn na k'udundune cikin hannun Bwama dake zaune daga can wani b'angare na d'akin, rikicin ganin gawar Nanne ya hana mutane da yawa biyowa ta kansa, kuma 'yan k'alilan din dake zuwa ganinsa, ba wanda take mik'awa don ta kafa sharad'in cewa shima ba cikakkiyar lafiya ce dashi ba don haka ba'a d'aukarsa, sai dai duk da haka tsananin mamakin irin kyawunsa ya fara zagaye cikin al'ummar gidan.

Wajen k'arfe goma na safiyar juma'a aka gama shirya gawar Nanne tsaf cikin farin kyallen dake jiran duk wani mai rai! Mama Halime, Aunty Maryama da wata malama zahra'u su suka wanke jikinta da babu ko kwarzane sai alamun warkewar ciwo a k'asan mara da gefen cikinta, suka tufke dogon gashinta cikin tufka biyu, wadda tasa fuskarta ta koma kamar ta k'aramar yarinya saboda kyau, Aunty Maryama ta fashe da kuka sanda suke nannad'eta cikin likkafanin, gani take kamar jiya ne suke shiryata cikin kwalliyar aure yayin da taron gidan ya kasance na farin ciki, gashi ko shekara bata zagayo ba suna yi mata shirin tafiya kabari, yayin da taron gidan ya kasance na makoki.

A wannan lokacin Inna ta farka daga suman ta, kuma abin mamaki wannan karon bata rikice irin d'azu ba, rarrafowa ta sake yi cikin tsakar falonsu da aka sake dawo da gawar don yi mata addu'a kafin a fita da ita.

Ta durkusa a gabanta daga gefen Baffa wanda ya bud'e tafukan hannayensa yana ta zubo addu'o'in neman yafiyar ubangiji da gafarsa akan ruhin d'iyar tasa, Idon Inna baya iya gane kowa ne a lokacin amma zagaye da ita ta kowanne gefe 'yan gidansu ne kaf! daga mazan har matan su ashirin da uku, jaamila dake can Niger ce kawai bata nan, sai ko mahaifiyarta Nuratu da a lokacin suke kan hanyar tahowarsu, Kowannensu na zubo kalar addu'oinsa, wasu kuma amsawa Baffa... daga bayansu ne 'yan uwa na kusa irinsu Aunty Maryaama ke tsugunne suma suna nasu addu'o'in.

Zuciyarta na zafi jikinta na girgirza tasa hannu ta janye likkafanin da yayi mata katanga da fuskar Nanne, fuskarta dake cike da annuri kamar wadda ke cikin tsananin farin ciki, kamar wadda ba taba fuskantar wani b'acin rai ba a cikin 'yar gajeriyar rayuwarta.

Yafiya har yafiya, albarka har albarka, neman gafarar ubangiji da neman Rahmar ubangiji ba wanda Nanne bata samu daga wajen Inna ba, tun tana fadar addu'oin cikin hankalinta, har komai ya kai k'arshe ya zamo maimaci kawai take yi.

Allah ya sani, zuri'arsu irin mutanen nan ne da basa mutuwa da wuri, kafin kaji mutuwa a danginsu toh ka tabbata ta tsoho ce ko wanda ya bawa hamsin baya, Saboda haka mutuwar Nanne ba k'aramin girgiza su tayi ba, kamar wata katanga ce daga wani b'angare na gidan ta fad'i ta rugurguje har garinta!

Nanne mutum ce mai d'imbin kirki da alkhairi, tana da mutuk'ar kyautayi da son 'yan uwanta, tana hak'uri da tsananin biyayya ga iyayenta, tana da kuma tsanani kulawa kan duk abinda take so a rayuwarta! tana iya sadaukar da komai nata don samun farin cikin wani... ita d'in mai nasibi ce da faffad'ar zuciya, ga duk wanda ya fahimci halinta, toh tabbas zai so ya zauna da ita tsawon rayuwarsa!

A lokacin da aka zo fita da gawarta daga gidan a lokacin komai ya sake rudewa da cakudewa, Inna ta rik'e k'afarta ta shiga yiwa Baffa magiya akan kar su tafi da ita, a bar mata ita haka ita zata iya zama da ita, rantsuwa take har cikin ranta cewa zata zauna da Nannenta a haka koda ba zata iya komai ba, duk wanda ya ganta a wannan lokacin sai ya zubar da hawayen tausayi, domin komawa tayi kamar k'aramar yarinya tana rik'e da k'afar Nanne tana rok'on Baffa dake tsaye daga bakin k'ofa.

Wanda ganin mahaifiyarsa cikin wannan halin ya sashi kasa daurewa kukan dake nuk'urkusar zuciyarsa, sai kawai ya saki labulen yayi hanyar waje ta cikin dimbin jama'ar da suka cika gidan a lokacin.

K'arfe Goma sha d'aya daidai na ranar juma'a aka fitar da Nanne daga gidansu a matsayin gawa, gidan da ta taso tun yarintarta, gidan da mahaifiyarta ta tafi ta barta a cikin sa, gidan da Inna ta raine ta da dukkan kulawarta, gidan ta fara gina rayuwarta a cikinsa, gidan da ta fara haduwa da Imran a k'ofarsa, sannan gidan da aka d'aura mata aure a cikinsa!

Da da gaske ne da ake cewa duniya ba matabbatace, Lalle ne komai mai k'arewa ne... can d'in shine gida na gaskiya!

***

Imran na sahun gaba hannayensa cikin na jaamil dake jansa tamkar rak'umi da akala, don da ace zai sake shi, ba zai iya cigaba da tafiya ba, zai tsaya ne kawai saboda kwakwalwarsa ba abinda take ganewa a wannan lokacin sai abu d'aya, abu d'aya da Bwama da jaamil suke gwagwarmaya akansa tun daga jiya, abu d'aya da ya zama dukkan fata da burinsa a halin da ake ciki, abu d'aya da yake ganin sai ya yishi sannan kwakwalwa da tunaninsa zai iya karb'ar labarin mutuwar matarsa.

Don komai dake faruwa ganinsa kawai yake yi yana wucewa kamar a shirin wasan da aka zauna aka tsara shi, baya yarda da dukkan abinda idanunsa da kunnuwansa ke d'auko masa, har kuwa sanda ya kama gangar jikinta shida Baffa suka zura ta a cikin ramin kabarinta, da sanda ake jera tukwane a kanta, da sanda ake zuba k'asa akan tukwanen, har saida ta shafe hasken farin likkafanin dake lullub'e da ita, da sanda k'asar tayi tudu aka kafa allon alama akanta.

Da sanda aka kusan shafe awa guda ana jero addu'o'i a gefen kabarin, da sanda jaamil ya sake jan hannunsa suka koma cikin motar da suka zo, da sanda kowanne motsin tayar motar ke k'ara nesanta shi da Ayuninsa, da sanda suka dawo cikin layin gidan nasu, da sanda suka fito daga mota saboda cunkuson mutane da ya fara yawa, da sanda suka iso daidai jikin wannan tsohuwar container data raba gate din gidajen biyu....

Sai kawai ya zame hannunsa daga na cikin jaamil ya tsugunna har k'asa a wajen, wajen da ya zama mafarin had'uwarsa da Sa'adha, ranar da ya fara ganinta sun dawo daga islamiyar nan, gashi wai a yau yaje ya raka ta cikin kabarinta ya dawo, ya dawo daidai wannan wajen dake cikin duniyar da babu Noorynsa!

Sai ya kifa kansa cikin tafin hannunsa ya shiga rero kuka tamkar karamin yaro, jikinsa na girgizawa tare da zuciyarsa, jaamil na shirin sunkuyawa ya bashi baki, Baffa ya tsaida shi ta hanyar d'aga masa hannu, ya yarda cewa duk duniya ba wanda ke da hurumin hana Imran kukan da yake yi a lokacin... Matarsa ce ta mutu, irin matar da ba'a koyaushe Allah ke azurtar bawa da ita ba, don haka hakk'insa ne yayi makokinta!

Zai iya yiwuwa mintoci, ko kuma awanni, irin wanda suke dunk'ulewa cikin jimla, jikin Imran bai bar girgizawa tare da kuka ba, Abu d'aya kawai da ya sani kuma yake ganewa a wannan lokacin shine zai kashe NAANI!

Zai kashe ta dukan iyawarsa!

¡ñ©n¡ñ

Ehem Ehem Ehem!

Did I do you wrong?

A yafe min albarkacin ranar idi!

Ina son inji ra'ayinku dai... me kuke tunani da wannan aika-aikar da nayi?

Enough votes, and i will post the last chapter zuwa dare Insha Allah!

BARKA DA SALLAH


WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

60


(¡î_¡î)

MURFI.


Har zuwa ranar da aka shafe zaman makokin Nanne da kwanaki bakwai, Bwama na cikin gidan a matsayin mai kula da Babyn nan, domin har a lokacin hankula da yawa baya kansa, sai bayan sadakar uku ne ma su Aunty maryama suka fara karb'ansa don yi masa wanka da kuma bashi abinci, wanda ba komai bane face tatacciyar madarar shanun da ake kawowa daga gonakin Baffa, wanda shi da kansa ya bada umarnin hakan, a cewarsa mahaifiyarsa ma da abinda ta rayu kenan.

Sai dai abinda basu sani ba shine, a duk sanda aka kawo madarar, Bwama na fakar idonsu ta zuba garin wani abu mai suna 'jerul' a ciki, abu ne da suke amfani dashi ne wajen dakushewa irin halittunsu possibilities d'insu a duk sanda suka yi laifi don a samu a iya hukunta su, saboda haka a yanzu da bata san irin abinda Babyn zai iya ba wanda ta san zai fi k'arfin hankalin bil'adama, yasa take amfani da jerul wajen dakushe koma wani irin abu ne ke tattare da jininsa.

A ranar sadakar bakwai ne, Baffa ya kira taro a gidan gabad'aya wanda ya hada harda Nuratu da itama take kwana da tashi a gidan ita da 'yan uwanta, Nuratun da basa shiri da Inna a yanzu tana d'aya daga cikin mutane mafi soyuwa a wajenta, don duk sanda ta kalleta sai taga kamar taga wani b'ari ne na ragowar Nannenta da ya rage, saboda haka kullum tana gefenta suna karb'ar gaisuwa tare... gaisuwar tarin mutanen da cincirindonsu baya tab'a raguwa a gidan, don har daga can Niger ba'a daina zuwa ba.

Hakika mutuwar Nanne ta girgiza duk wani mahaluki a gidan, ta guntule farin cikinsu, ta wargaza tunaninsu kuma ta k'ara sanya musu tsoron Allah a zukatansu. Don haka fuskar kowa na falon in ka kalla a wannan lokacin d'auke take da alhini irin na rashi.

Bayan doguwar addu'a daga bakin Muhammad, Baffa ya fara bayanin cewa ya kira taron ne don ya gaya musu cewa anyi rad'in sunan Babyn da asubahin ranar kuma Imran ya rad'a masa sunan mahaifin Inna wato HISHAM. Anyi yanka kuma su mama Azumi har sun gama suyar naman.

Yanzu abinda ya rage shine inda rik'on yaron zai kasance, za'a barshi anan wajensu ne, ko kuwa Inna tana ganin a bawa dangin Imran su rik'e shi. Daga yadda ya fad'a kowa ya san cewa ya fad'i hakan ne kawai don a kwatanta adalci a kowanne b'angare, amma ba ta yadda za'ayi Inna ta bari d'an nan ya matsa daga kusa da ita.

Ai kuwa yana rufe baki, tayi tsalle ta dire cewar ba inda za'a tafi dashi, ai hakk'in dangin uwa ne kula d'a karami yaro irin haka, saboda haka yadda ta raini Nanne, a bar mata shi zata raine shi da dukkan iyawarta. Aunty maryaama kuma tace Inna ta tsufa, d'awainiyar yaro k'arami zata yi mata wahala a wannan shekarun saboda haka ita a bata shi, ta san mijinta zai amince, amma bata k'arasa ba Inna ta hau sababi wanda ya had'a da kuka tana fad'in bata yarda a matsa koina dashi daga cikin gidan ba, saboda haka Nuratu ma dake shirin magana tayi shiru da bakinta.

Sai Aunty amarya tace ita zata karb'e shi amma Inna tayi saurin katse ta tun kafin ta k'arasa.

"Kar ki kuskura ki k'arasa zancen nan, Hadiza, kar ki kuskura ki k'arasa, yau har kece mai bakin cewa a baki d'a? Duniya makaranta! Shekaru ashirin kenan baya muka yi irin wannan zaman a d'akin nan, ba irin yadda bawan Allahn nan bai rok'e ku ba akan ku taimaka ku rik'e masa marigayiya ke da Halime, amma kuka k'ek'ashe idanunku kuka ce baza ku raini 'yar kishiya ba, shine kike da bakin magana a yau? yo me kuma zaki yiwa d'anta a yanzu? me...."

Bata k'arasa ba Baffa ya katse ta da girman Allah akan tayi shiru, abinda ya faru a baya ya riga ya wuce. Bayan ya gama 'yan koke-kokenta da rantsuwar baza a bawa Aunty Amarya ba, Baffa ya tambayi Imran game da ra'ayinsu, a karon farko cikin kwanaki bakwan nan ya bud'i baki yayi magana, don hatta jaamil ba yadda baya yi dashi ba wajen tambayarsa abubuwa amma baya tab'a cewa komai, ko wajen karbar gaisuwar baya zama, a kullum yana can cikin dakin Baffa inda yake kulle kansa yayi ta kukan da har hawaye sai sun daina bin kumatunsa, don Allah ya sani daya zauna a waje wani yace masa.

Ya hakuri?

Gwara ya shafe yinin ranar bai ga kowa ba, yana faman yi mata addu'ar da bata k'arewa! Tun lokacin da karfin rabin ruhinsa da ya bar na Sa'adha ya dawo jikinsa yake fatan k'arshen zaman makokin yazo don ya sami damar yin abinda Bwama da jaamil keta hana shi tsawon kwanaki.

So yake yaje Muzaffar ya gayawa Naani cewa abinda dake fata ya dawo jikinsa, dama tace ruhinsa ba zai taba barin jikinta ba sai in har ta mutu, zai gaya mata tayi nasara ta kashe ta, b'arin ruhinsa ya dawo jikinta kuma zaiyi amfani dashi itama ya kashe ta!

Amma Bwama da jaamil sunce alamar tambaya zata d'arsu akansa in har ya bar gidan zaman makokin ya tafi Muzzafar a wannan lokacin, sunce yayi hakuri ya daure wad'annan kwanakin don ya rufe asirin sanin WAYE SHI daga dangin Sa'adha, sunce bai kamata ya bada wata k'ofar da zata sa su fahimci wani abin ba kamar yadda ta rufa asirinsa da dukkan iyawarta, shi yasa jaamil ya sake dawo da wad'annan tarin mutanen a matsayin 'yan uwansa suka zo suka yi gaisuwa kamar yadda kowa yake zata.

Yayi gyaran murya kad'an lokacin da hankalin kowa ya dawo kansa.

"Baffa duk abinda Inna ta fada gaakiyane, a yanzu wajenta ne mafi cancanta da yaron ya zauna, sai dai kuma abinda Aunty maryama ta fada itama gaskiyane, bai kamata a d'ora mata d'awainiyar jariri a shekarunta ba, tunda kuma bata yarda da kowa ya rik'e shi ba ina rok'on alfarmar ta bar 'yar uwata (yana nufin Bwama) a wajenta ta taya ta rainonsa."

"Wallahi na amince, ko su nawa suzo, idan har zaku bar min shi a gabana." Inna ta amsa kai tsaye.

Cikin wannan tattausar muryar tasa mai zurfi, Imran ya cigaba da magana.

"Sai dai ina rok'on ya dawo wajena daga lokacin da shekarunsa suka kai na shiga makaranta, na riga nayi mata alk'awarin zan kula dashi."

Ba sai ya fasa ba, kowa ya san yana nufin Nanne ne, yayi wa Nanne alkawarin cewa zai kula da Babynta/Hisham tsawon rayuwarsa!

"Wannan ba wani abu bane Imran, kai ubansa ne kana da hakkin karb'arsa a duk sanda kaga dama, saboda haka ko bayan raina kowa ya shaida nayi alkawarin zamu baka shi daga lokacin da ya shekara uku."

Da wannan alkawarin taron ya tashi, Inna bata ja da hakan ba saboda itama ta san yana da hakki akan d'ansa kuma ko ba komai an had'a da cewar alk'awarin da aka yiwa Nannenta ne.

Da hakan kuma Imran da jaamil suka had'a bangarorin dutsen Nil suka dank'a a hannun Bwama a matsayin abinda zai cigaba da bata karfin da zata iya maintaning jikin bil'adama a cikin shekaru ukun da zata yi na kula da Hisham, da hakan kuma aka yi sadakar bakwai aka share zaman makokin Sa'adha, gidan ya sake shiga sabon yanayi na alhini, kewa da kuma k'unci.

Ance sabo akewa kuka ba mutuwa ba, duk da auren da tayi, d'aukacin al'ummar gidan kaf! sun saba da Nanne, don ita d'in mai tsokana ce da karamniya, ko mutum bai shiga shirginta ba, dole zata nemi abinda zai had'oka da ita, wanda daga baya za'a zo ana dariyarsa, hatta su Lami da ba shiri suke ba sun sha kuka da idanunsu akan rashinta, saboda haka dole alhini ya shafi wani b'angare na walwalar gidan.

Da hakan kuma Imran ya shirya tsaf! ya d'auki hanyarsa ta zuwa Muzzaffar!!

****

BAYAN SHEKARA GOMA.

Yamma ce, amma gari yayi duhu sosai alamun bak'in had'arin dake manne a sama na iya narkewa ya sauko a kowanne lokaci.

Imran ya bud'e k'ofar cikin d'aki da saurinsa ya fito... Nanne ta biyo bayansa da gudu ta cikin corridon da ya kawo su main falon gidan, tana sanye da wata 'yar k'aramar vest kalar ja da kuma da d'an blue short da bai ka gwiwa ba, hannuta rik'e da wani k'aramin towel yayin da Imran ke sanye da dogon wando da singlet kawai, lallausar sumar kansa na d'iga da ruwa.

"Ayunie dan Allah mana sau d'aya."

Ta fad'a tana turo d'an bakinta alamu shagwab'a. D'aya daga cikin manyan abinda Imran baya so shine a goge masa gashi in ya wanke shi, ita kuma tunda ta fahimci hakan shikenan ta samu hanyar tsokanarsa.

"Dan girman Allah kiyi hak'uri, wallahi ba dad'i ne."

"Dan girman Allah nima ka barni inyi sau d'aya.."

Ta fada tana k'okarin zagayowa ta bayan kujerar da yake tsaye, aikuwa yana fahimtar haka ya fara matsawa shima.

"Toh kije ki d'auko hand dryer, amma ba da wannan ba."

"Saboda me?" Ta d'age girarta d'aya.

"Towel d'in nan yana da laushi, zaka ji kamar massage nake maka."

"A'a Noory, ki hak'uri dan Allah."

Ta matse kafad'arta d'aya.

"Allah ba zan hak'ura ba."

Da haka ta fyalla da gudu ta nufe shi, suka shiga zagaye kujerun falon da gudu tana ta kyalkyala dariya, shi kuma yana ta rokonta don har ga Allah baya so, a haka yayi tuntub'e da wayar extension ya fad'i k'asa, ai kuwa ta d'ane kansa ta shiga murza towel din a cikin gashinsa, da kyar ya iya cafke hannayenta ya wullar da towel d'in.

"Ba kya jin magana you sweet little dickkins!"

Ya fad'a yana ware tufkar gashinta itama, ta dinga dariya sanda yake hargitsa shi da hannayensa har saida ta fad'a kan jikinsa tana fadin.

I'm sorry!

Muryar ta mai sanyi ta ratsa dukkan jijiyoyin jikinsa, it was so real da yaji ko kad'an baya son ya bud'e idonsa ya koma wannan zahirin da babu muryar.

"Noory...

Ya kira sunanta a hankali, ta d'ago ta k'ifta chocolate idanunta masu d'auke da kwalla a hankali, so slow ta yadda yana ganin yadda dogwayen lashes d'inta suka had'e dana k'asa kafin ta sake bud'e su, gashinta a hargitse kan kafadunta wani ma ya zubo kan fuskarta... the way he always wanted it! the he always missed it!

"I've missed you, I'm always missing you..."

Muryarsa ta rad'a mata a hankali sannan ya k'ara da.

"... like crazy!"

Sai tayi wani guntun murmushi da ya k'ara fito da yawan kwallar idonta, sannan a hankali ta ware hannunsa d'aya dake rik'e da ita, ta d'ago shi sama sannan ta lankwasa yatsunta a tsakanin nasa, ta juya kanta da wani irin slow motion ta kalli hannayen nasu sanda shima ya lankwasar da nasa yatsun a cikin nata, amma bai bar kallon fuskarta ba.

"I miss you too Ayunie!"

Lallausar muryarta ta fito kamar rad'a, Imran ya kalli yadda kwallar ke gangarowa gefen fuskarta a hankali tana shigewa cikin sassalkan gashin kanta, yaji zai iya nutsewa cikinsu ya manta da duk wata damuwarsa.

Ring. Ring. Ring. Ring. Ring..!

K'arar wayar dake ajiye a gefensa ta farkar dashi zuwa zahirin da yake gujewa. Ya kalli inda yake, kan sallayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login