Showing 12001 words to 15000 words out of 113985 words

Chapter 5 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28447

tabbata."

"Ba irin bayanin da banyi masa ba a lokacin amma ya kasa fahimta ta, na fada masa 'G&M' ba kamfani bane da za'ayi trusting d'insu da makudan kudi haka, amma ya samu wannan yaron yana gaya masa kawai adadin hundreds din da suke biya per week, gashi nan yanzu just in a half year budget d'inmu yayi kasa da 20%, who knows me zai faru nan gaba?"

"Ni naji fa ana cewa zai janye ne, kawai a maida contract d'in ya zama iya rabin shekara.

Imran ya girgiza kansa.

"Wallahi ba zasu yarda ba, ai yau ko karamin kamfani ne akayi wannan yarjejeniyar dasu baza su taba yarda da haka ba, kuma we can't force them tunda an riga an rubuta komai da sa hannu."

Sunyi kamar minti goma suna tattaunawa kafin mr. Marvin ya mik'e.

"Akwai wasu files da zanyi compling, sai na ganka anjima."

Bayan fitarsa, Imran ya cigaba da ayyukansa, sai da yayi nisa sannan wata mak'ociyar office d'insa maryam ta shigo, ya d'an ja tsaki a k'asan numfashinsa, ko kad'an baya bukatar surutun ta a lokacin. Don a cikin mutane masu irin zuciyarta ma daban ne, yayi tunanin zata daina shiga hanyarsa tun lokacin da ya gaya mata kiri-kiri cewa abinda take tunani tsakaninsu ba zai taba faruwa ba. Amma sai ya zama kamar ba'ayi ba.

"Good afternoon dear, aiki ne da kai yau haka?"

Muryarta mai sanyi ta shiga kunnensa.

"Afternoon." ya amsa a gajarce ba tare daya kalleta ba.

Ta tsaya daga karshen bencin ta dafa hannayenta da suka sha kunshi akai.

"Akwai wani project na oil company da shamsu yace min zamu yi aikinsa tare, an kawo maka ne?"

"No, banyi signing akai ba, so yanzu ke dashi ne kawai zaku yi handling."

"Amma saboda me? Zaka bamu guidance fa." ta marairaice murya.

"kinga maryam..." ya d'ago da kansa.

"In the next 3 months ma bani da aiki dake, kuma kina iya gani yanzu wani abin nake yi, so if you will excuse me."

Ya nuna bayanta hanyar kofa. Da yake 'yar duniya ce ko a jikinta, sai kawai ta gyara zaman d'an mayafinta tace.

"Okay, lets discuss something then...nayi zaton baka da relation a kusa kamar yadda yake a file dinka da komai, amma yau sai Allah ya had'a ni da brothernka."

Ya had'e kakkaurar girarsa waje daya yana kallonta, itama ta nutsar da idanunta cikin nasa sannan ta kiftasu a hankali.

"I'm serious Imran har kama kuke."

Jin haka yasa gabansa ya fadi, don daga yanayin muryarta ya tsinci k'anshin gaskiya a ciki. Sai dai ya riga ya san halinta, sai ta gama juyashi kafin ta gaya masa gaskiya, kuma bashi da wannan lokacin da zai iya jiranta saboda haka a lokaci d'aya ya tsaida duk wani abu dake motsi a cikin office d'in sannan ya mik'e ya isa wajenta, jikinta ya sandare kamar a k'ank'ara ga hannayenta a iska, sannan bakinta slightly a bud'e alamun tana shirin yin magana ne, bugun zuciyarta ne kadai abinda ya rage mai motsi a tare da ita.

Imran ya tsaya cak ya kalli cikin idanunta, nan take ya shiga ganin abinda ya faru da ita tun daga tashinta a yau har zuwanta office, ya dinga wuce mutanen data hadu dasu kala-kala da abubuwan data yi har zuwa sanda ta koma wajen motarta dauko wani flash, yaga sanda ta juya ta kalli wani kyakkyawan matashi dake mata murmushi daga gefen mota a dai parking lot na office dinsu, bai tsaya yaji maganar da suka yi ba yayi sauri ya nufi kofa, har zai bud'e ya tuna ya murza hannunsa, take komai ya dawo daidai.

"Ko kana tunanin karya nake..."

Maryam ta zarce da maganar data makale a bakinta.

"Idan kin gama ki rufe min office din."

Yana fada yayi ficewarsa. Ta juyo a kid'ime ta kalli kofar da tsananin mamaki sannan kuma kujerarsa.

Yana isa parking lot d'in ya hango wannan matashin dai tsaye jikin motar nan kamar yadda ya gani a idanun maryam.

"Wallahi na raina haukan yarinyar akanka, na zata tun sanda ta ganni zata je ta fada maka amma kusan mintuna talatin ina tsaye."

Imran ya bashi amsa yana k'arasawa wajensa.

"Waya sani ko tana tunanin canja shek'a ne tunda ta ganka."

"Kuma ka san har number wayarta ta bani."

"A ina ka samu waya?"

Ya d'ago masa tsinken dake hannunsa.

"Shi ta gani a matsayin waya."

Ya girgiza kansa yana k'are masa kallo.

"Wallahi daka san yadda kayi kyau, da kayi sujjada a wajen nan ka ta rokon Allah ya maida kai haka."

"Bana son wannan zancen, kaima ka san ba don abu mai muhimmanci ba, babu abinda zaisa inzo nan."

"Meya faru?"

"Tafiya ce ta dole ta kama ni zuwa k'asar Nepal, kuma zan d'auki kusan wata guda don maganin da zanje karb'owa sai an hada shi tukunna."

"Maganin waye?"

"Bwama ce ke fama da ciwon b'arin kai."

Imran ya girgiza kansa.

"Ya salam, Allah ya bata lafiya...amma da kun gwada panadol yana aiki sosai." jaamil yaja tsaki.

"Bani da lokacin rainin hankalinka yarima, abu d'aya ne ya kawo ni nan..."

"Na sanshi..."

Bai saurareshi ba ya cigaba.

"Naani bata san da tafiyata ba, ka dubi girman Allah, ka tafi da komai daidai har na dawo, zuwa sannan na san baifi wata biyu ba mu huta da duk wannan wahalar."

Imran ya cigaba da kallonsa gira d'aya a d'age, kamar akwai wani abu da bai fada ba yake jira. Jaamil yayi ajiyar zuciya sannan yace.

"Kar kaje wajenta."

****

Ranar Asabar tunda ya tashi yake gida yana ta harkokinsa, kwana biyu kenan yana rayuwar 'yanci tun tafiyar jaamil ranar alhamis, a yanzu bashi da wani mai takura masa ya san yayi nesa daga duk wani idon sani, jinsa yake kamar a farkon watanni hud'un da suka wuce, watannin da ya canja rayuwarsa gabadaya zuwa wata siffar da har yanzu ya kasa yardarwa kansa cewa hakan ba zai d'ore ba.

Wajen karfe uku yana kitchen, ya gama cin abincin daya dafa, ya wanke kayan da yayi amfani dasu ya kife a dryer, sannan ya wanke sink din, yana aikinsa ya sauraren cool wakokin da yake so daga cikin bluethoot a gefe.

Sai da ya kimtsa komai sannan yayi wanka ya shirya cikin wani light blue yadi mai kyau, d'an fitted dinkin kuwa ya zauna daidai a jikinsa, ya gyara sumar kansa sannan ya feshe jikinsa da turare, wanda ko bai sa ba kanshinsa baya taba barin kayansa. Kafin ya gama shiryawa ya kunna wayarsa tare da data, messages suka dinga kokawar shigowa kota'ina harda voicemail, yana danna na farko muryar maryam ta karad'e dakin.

"Imran na kira ka several times wayarka bata shiga, please if you got this message call me, na kasa nutsuwa da abinda ya faru ranar thursday..."

Ba bari ta k'arasa ba ya danna na biyu, muryar wani ta maye tata, ya cigaba da saurarensu d'aya bayan d'aya kafin ya fito falo, ya kashe Tvn dake nuna tashar football da duk wasu switches na gidan sannan ya fita. Bai d'auki mota ba don strolling kawai yake son yi yaga unguwar sosai.

A wani masallaci dake can gaba da gidansa yabi jam'in sallar la'asar, ya dad'e ma a ciki yana addu'oinsa kafin ya fito ya nufi hanyar gida ta cikin wani layi mai yawan bishiyu. Sai dai me? yana shan kan kwanar yaji gabadaya duk wata jijiya ta jikinsa ta shiga aiki da sauri.

Tar! idanunsa suka hango masa sa'adha ta fito daga wani k'aramin gida, fararen hannayenta sun sha jan k'unshi mai kyau, sannan ga bak'i a sama tana ta hura shi da iskar bakinta, tana yi tana wa k'awarta mitar zaman bin layin da suka yi, wanda duk da tazarar su yana jiyo komai.

Saura kad'an yayi wani abu daya kusan manta shi a rayuwarsa, saura kad'an ya sulale yabi jikin bishiyar bayansa sanda idanunta suka d'ago suka kalle shi.

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

08


(¡î_¡î)

Da sauri ya janye idanunsa daga cikin nata sannan ya d'auke kansa yayi kwanar dake damansa, ya zaro wayarsa ba tare da ya ko juyo ba ya b'acewa ganinta.

A lokaci daya nanne taji guntun murmushin da take shirin yi yabi iska, wani abu mai kama da mamaki ya maye gurbinsa, ta rufe idonta ta sake bud'awa ta kalli inda ya tsaya sannan kwanar da yayi, tabbas ba karya idanunta suka mata ba ya ganta, ya ganta ya kalleta sannan ya d'auke kansa yayi gaba.

"Me kike kallo ne wai? Kizo muyi gaba baza mu sami abin hawa ba anan."

Ta tsince muryar rahma daga nesa kamar ba'a kusa da ita take ba, ta juyo da sauri tace.

"Rahma kinga mutumin daya wuce yanzu?"

"A ina?"

"Anan wajen, wanda yayi can kwanar da light blue kaya."

"Anya? kin san na sunkuya d'auko kudin mota....waye shi?"

"Wani ne." Ta fada a hankali idonta na kallon hanyar, kamar tana jira ya dawo ya fada mata dalilinsa na kin mata magana, Toh amma saboda me? Ta tambayi kanta, bata da wata alak'a dashi, me yasa in ya ganta zai mata magana? Don kawai ya taimaketa sau d'aya kuma ya tambayi sunanta a ranar?

"Nanne muje mana la'asar fa ta wuce, ko sallah bamu yi ba."

Ba yadda ta iya haka tabi Rahma da hannayenta a d'age suka yi titi.

Har bayan magriba wani iri take ji a jikinta, ta rasa kuma dalilin hakan, ko don zuciyarta ta damu da son sake ganinsa ne a baya, yanzu kuma ta ganshi ya d'auke kansa.

Ta dafe kanta sanda take zaune a kan kujera tana hango tarin 'yan aikin da suka baje a tsakar gida anata packaging sabulun salo dana magarya a roba wanda za'a rabawa mutane jibi ranar wankan amare. Tayi tunanin tashi daga wajen amma bata san inda zata ba, don koina a gidan cike yake da mutane, hatta dakinsu yanzu tarin 'yan niger ne fal, 'yan uwan inna tsofaffi sun had'u anata hirar yaushe gamo, inna ta basu labarin abubuwan da suka faru da ita, suma su bata nasu na can.

Rahma ta d'ago mata hannu daga tsakiyar matan wai tazo ta zauna amma ta girgiza kanta. Abu na karshe da zata so yanzu shine ta shiga cikinsu duk da cewa anata irin hirar da take so ana dariya, don sun samu taimakon wasu 'yan niger masu barkwanci, amma zuciyarta ba dadi a lokacin.

"Ko zaki taimaka mana da kujerar nan dan Allah kitso zamu yi."

Ta juya taga wata mata tsaye akanta da kibiya a hannu. Ta san ta sarai daga cikin 'yan uwan mama halime take, su da suka fara zuwa tun cikin sati masu aurar da 'ya'ya biyu.

"Gaskiya ba yanzu zan tashi ba."

"A'ah uwata..." mama Azumi da zata wuce ta katseta.

"...Taimaka ki basu mana, gidan ne yayi albarka duk kujerun an zaune."

Kamar baza ta tashi ba, don dai kawai mama azumin ce yasa ta mike.

"Ko kefa, zo muje ta kicin akwai abinda na ajiye miki."

Dama yunwa take ji, don sun dawo daga kunshin ta tarar jollof akayi tun rana tayi shape din flask, ita kuma taki ci don babu ko zob'o tunda yanzu yawan gidan ya kai intiha.

Ta tarar cake ne k'anana wajen guda takwas, ta karb'a da murna ta dauki ruwa sannan tayi wajen compound, ta samu k'arshen barandar d'akunan mazan ta zauna, ta zame dankwalinta saboda zafi da ake d'anyi a lokacin.

Bata ci ya kai uku ba sanda taji Alamar an turo gate din gidan, wannan k'iii! din k'ofar ya shiga kunnuwanta, ta rufe idonta gami da d'an jan tsaki, don ta san in d'aya daga cikin su ya sulaiman ne yanzu za'ace ta shiga gida, musamman ace da wani abokinsu suka shigo.

"Sa'adha..!"

Wannan muryar mai zurfi da taushi ta shiga kunnenta, tana juyowa taci karo dashi tsaye daga d'an gaba da ita. Bakinta ya bud'e saboda mamaki, a lokaci daya taji zuciyarta da tayi sanyi ta shiga bugawa da karfi.

Tayi saurin jawo mayafinta ta rufe gashinta.

"Yaushe ka shigo? ta ina?"

Ganin gashinta da yasha gyara dakuma hanbayenta masu kunshin nan yaso dauke hankalinsa, don sai da yayi shiru sannan ya amsa a hankali.

"Yanzu na shigo ta gate."

"Dama kana shigowa gidan nan?"

"Wani lokacin ina zuwa wajen umar." ya nuna kofar d'akin dake gefenta.

Ta mike da sauri kafin tace.

"Ina ga baya nan yanzu." Bata jira komai ba ta juya tayi hanyar komawa ciki.

"Sa'adha..!"

"Ba wajensa nazo ba, ke nake son gani."

Bata juyo ba ta girgiza kanta.

"Ba zan iya tsayawa ba, in wani ya ganka za'a min magana."

"I'm sorry, d'azu na ganki bamu gaisa ba ina sauri ne."

Kanta yayi duumm! Ta kasa gasgata abinda kunnuwanta suka ji, da gaske shi din ne? Ya shigo har compound d'insu don kawai ya bata hakuri? ta juya a hankali rik'e da plate d'in cake d'in. Yana tsaye kuwa, ya d'an biyo bayanta kad'an.

Dogo ne sosai, ba fari ba sai dai yana da hasken fata irin ta murjewa, sumar kansa a dunk'ule take kamar ta jinsin larabawa, ta taho tun daga saje ta zagaye bakinsa, Ga wani irin k'anshi dake tashi mai dadi wanda tabbas daga shi din ne, Taji bugun zuciyartu ya karu akan da, kamar yana barazanar tarwatsa kirjinta.

"Ba komai, sai da safe." muryarta da kadan tafi rada.

Imran yayi ajiyar zuciya sanda ta b'acewa ganinsa, bai san me yake shirin faruwa ba dashi ba, amma zai daurewa koma menene tunda yanzu ya sauke wannan nauyin, nauyin daya dame shi tun lokacin da ya ganta d'azu yayi tafiyarsa.

A lokacin ya dake zuciyarsa ne cewa zai cika alk'awarin daya d'aukarwa Jaamil da Naani, na cewa ba zai bari wani abu ya shiga gabansa ba, zai tafi da tsarinsu kamar yadda suka shirya komai a farko, amma tunda ya koma gida ya kasa wannan dauriyar, ya kasa cire fararen idanunta daga ransa, yadda ta bishi da kallon mamaki sanda ya juya, da yadda take ta kallon hanyar da yabi, yana iya ganin zafin dake cikin idonta tunda daga nesa.

Rauninsa kenan a duniya, baya taba son ya zama sillar bacin ran wani, ya shigo cikin rayuwarta da salama ba zai so ace hakan ya zama rabuwarsu ba.

Da wannan tunanin ya samu kwarin gwiwar zuwa wajenta. Ya gayawa kansa cewar abinda Naani da jaamil ke tunani ba zai taba faruwa ba don yazo wajenta sau d'aya, yana da enough focus d'in da ba zai taba zama distracted ba, sai dai ma ya zama distracted in wani abu na damunsa.

Yayi saurin yin baya sanda wasu mata suka fito daga cikin gidan rike da kaya niki-niki, ya matsa wajen duhun rumfar adana motocin dake gefe, sannan ya bar wajen, a tunaninsa ya barshi kenan har abada.

Sai dai kuma wata kaddarar bata ma soma ba!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

09


(¡î_¡î)

"A daidai ina muka tsaya wancan karon?"

Muryar da kaushi ta fita, cikin wani irin amo mai girgizawa, don yana iya ganin yadda 'yan k'ananan decor's d'in dake kan center table na gabansa ke jijjigawa.

Imran ya d'ago da idonsa ya kalli manyan-manyan hallitun dake tsaye a bayan kujerar falonsa, basa bada ko karamin motsin da zai nuna cewa suna raye.

A tsakiyarsu akwai wani dunkulallen haske dake lilo a iska, haskensa ya tarwatse ya baje ko'ina a cikin d'akin, daga kasa kuma jikin inuwarsa, wani tambari ne ya fito, tambari irin na adon sarautarta.

"A ina muka tsaya yarima...?"

Muryar tasa kowacce tsigar jikinsa mik'ewa, A kullum girmanta da matsayinta karuwa suke a wajensa.

"Ki min gafara Naani, abinda kike tunani ko kadan ba haka bane, a wancan lokacin kinyi fushi ne dani sosai shi yasa na kasa miki bayani, amma an samu sab'anin fahimta ne tsakanina da jaamil, don kinfi kowa sani na a duniya, kinfi kowa sanin cewa ba zan taba yin abinda zai bata ranki ba."

Maganarta ta fito a gajarce.

"Ina saurarenka."

Ya gyara Gwiwoyinsa dake zube akan tattausan carpet d'in sannan yace.

"Farkon zuwana garin nan, na had'u da ita ne a layin da nake tunanin zama, daga baya na fahimci wajen yana da yawan jama'a sai na barshi, kuskurena na farko shine ban rabu da ita ba, na cigaba da bibiyarta bayan nan, kuskurena na biyu shine a lokacin da jaamil ya gane, sai na maida abin kamar sigar tsokanarsa, har nayi mata magana don ya gani, amma babu komai a raina game da ita, kuma tun a huduwarmu a baya nayi miki rantsuwa cewa ba zan kara zuwa kusa da ita ba."

Shiru mai yawa ya biyo kafin murya ta sake fitowa.

"Me ake ciki game da tsarinmu?"

Ya lumshe kyawawan idonsa sannan ya amsa.

"komai yana tafiya daidai, bana tunanin zamu kai watannin da aka d'iba don YA RIGA YA FARA YARDA DANI YANZU!"

****

~_~ Ta zama tazama...ta zama d'auko riga, tazama d'auko wando, ta zama tazama...ta zama dama furar nan...! ~_~

Wak'ar ta karade katon filin farfajiyar gidan su Nanne, wajen ya tsaru sosai kamar bashi ba, yasha ado da kayan al'ada na gargajiya kala-kala. Rumfar da amaren ke zaune a tsakiya akayi ta kuma ba'a shimfida komai a k'asa ba saboda 'yan kujeru ne irin na tsakar gida guda hud'u inda kowacce amarya ke zaune akan d'aya, a gefenta da katuwar roba da aka cika da ruwan d'umi, duk wanda yazo gaban amarya zai d'ebi ruwan ya watsa a jikinta, sannan ya ajiye gudunmawarsa a k'asan k'afarta wanda ake kira da 'kudin sabulu.'

Amaren gabadaya farin zanin da inna ta sak'a sukayi d'aurin k'irji dashi sai da kowacce tasa farar t-shirt daga ciki kuma sunyi yafen farin mayafi. Sannan gabad'aya 'yanmatan da suka sa anko daga kowanne b'angare na amaren, ankon plane zani suka yi suma da riga buba.

Nanne na zaune ita da Amina daga can kujerun baya suna cin gasasshiyar awarar nono wadda aka raba a wajen da kuma fura. Itama irin ankon 'yanmatan ne a jikinta, sai dai ba ko hoda a fuskarta kuma ta cokala d'auri gaban goshi.

"Wallahi da kin fada min da nazo munje gidan kunshin nan tare, yaushe rabon hannuna da lalle."

Nanne ta juyo daga kallon wasu 'yanmata a gefensu tace.

"Nima rahama ce ta takura min, kwata-kwata banyi niyyar kunshin ba, kuma in gaya miki gidan d'an banzan layi kamar da sallah, tun wajen goma fa muka fita bamu muka dawo gidan nan ba sai bayan la'asar."

"Ai baku yi jiran banza ba, ta iya wallahi."

Nanne ta kalli hannunta sannan tace.

"Kuma lallenta nada kyau, tunda fa tun ran asabar, gashi kamar yau akayi."

"Ai gaskiya zanzo bayan bikin nan ki raka ni."

Har Nanne zata ce wani abu wata murya ta tsaida ta.

"Kinga dan Allah tambaya muke."

Ta juya taga d'aya daga cikin 'yanmatan dake gefensu ce ta d'an juyo da kujerarta saitinsu.

"Naga kamar kin san 'yan gidan nan ne?"

Nanne ta d'aga kai tana kallonta.

"Dan Allah kin san wannan?"

Ta miko mata hadaddiyar wayar hannunta, Nanne na juyo da fuskar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login