Showing 54001 words to 57000 words out of 113985 words

Chapter 19 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28479

iyayen daya gabatar a wajen Baffanta har zuwa matan da suka je a matsayin danginsa wanda duk babu su a gaske, ya rufewa mutane ido ne kawai sunga alamun siffarsu amma babu su d'in a zahiri.

Hallucination ne kawai yayi planting a cikin idanunsu. don da ace an samu wanda zai haska su a wajen da mudubi ba zai gansu a ciki ba. Shi yasa ma mai hoton nan ya kusa kawo musu matsala, ba don Allah yasa jamil ya....

Tunaninsa ya katse, sanda wani saurayi ya kwankwasa masa glass.

"Yawwa yallab'ai gasu nan gabad'aya ne, harda receipt d'in."

Ya fad'a yana zuro masa ledojin hannunsa, Imran yayi godiya sannan ya rufe glass d'in, ya tada motar ya cilla ta saman titi haka ma zuciyarsa ma ta cilla can inda ya nufa a yanzu wato gidansa.

Tsawon shekara d'aya kenan da uzirinsu ya shigo dashi wannan rayuwar, ya bar al'adarsa da komai ya canja yanayin halittarsa, amma duk tsawon wannan lokacin bai tab'a jinsa more human ba irin jiya da yau, watakila har gobe ma da jibi...har zuwa ranar da komai zai k'are.

Sau ba adadi ya sani aurensa da Sa'adha ba abu ne mai d'orewa ba, don ko a yanzu baya tunanin suna da abinda ya wuce karfin watanni, shi yasa a jiya bayan an gama d'aura auren zuciyarsa ta karye da ganin irin d'imbin farin cikin dake faruwa a gidansu, ya hango ranar da shi d'in da kowannesu ke yabo a yanzu, zai zama abin la'ana a wajensu, a lokacin da shi d'in baya nan kuma, baya cikin wannan jikin da mutane suka sanshi dashi.

Ranar da shi kansa zai ji haushin kansa, zai k'ara yin nadama da regreting abinda yayi sau ba adadi, mistake d'in da yayi tun farko na shiga jikinta, don da ba hakan ba, da komai dake faruwa a yanzu bai kasance ba.

Da Sa'adha na can na karatunta bata zama matarsa ba, da watakila shima ya gama abinda ya kawo shi ya koma nahiyarsu, can wajen gimbiyarsa Sareefa. Amma k'addara ba haka ta tanadar masa ba, ta shigo da sa'adha cikin rayuwarsa a wani irin yanayi da yafi k'arfin tunaninsa, don da gaske ne abinda ya fad'a mata jiya.

A yanzu, ya yardarwa kansa cewa da gaske yana son ta, zuciyarsa ta nutsu da ita kamar yadda ta amince da Sareefa a baya, shi yasa ya bud'e mata wani b'arin zuciyarsa da yake babu shi a tsarinsu shida jaamil, a lokacin tausayinta ne ya kamashi ganin tana kuka, ya san ya yaudareta ne ya rabo ta da iyayenta ya kawo ta cikin fake rayuwarsa, atleast she deserve to know something that is true about him, duk da cewa ma baya tunanin ta fahimci dukkan zancensa. ba lallai ne ma ta gane ba.

Sannan yayi ta nanata zancen nema musu zaman lafiya ne saboda zamanta dashi had'ari ne, ita d'in ba abokiyar halittarsa bace, dole ne yayi taka tsan-tsan da kansa a wajenta, dole ne in yana tare da ita hankalinsa ya zama fully a jikinsa don she's so fragile to him, kamar mutum ne ya rik'a wasa da circle d'in kwanduwar kwai a hannunsa, kuma ya na yi da zummar cewa ba zai fasa cikinta ba.

Saboda haka ba zai tab'a bari zamansa da ita ya samu matsala ba, zai iya k'ok'arinsa wajen nuna mata dukkan kulawarsa yadda ba zata fahimci rashin wasu abubuwa ba, don kamar yadda ya sani kuma jaamil ya dad'a fad'a masa a jiya, akwai abubuwan da ba zai tab'a bari su faru tsakaninsu ba.

Ya tuno d'azu da yazo tashinta sallar asuba, tana baccinta peacefully a lokacin, hular kanta ta zame gefe kad'an sannan strands d'in gashinta mai kyau ya kwanta smoothly akan filon, ta rik'e fuskarta da tafin hannayenta biyu a kowanne gefe kamar k'aramar yarinya, sannan bakinta slightly a bud'e.

Yana iya jin fitar numfashinta a hankali daga tsakanin leb'b'en nata, a lokacin yaji kamar ya matsa kusa da ita ya d'ora yatsansa akan leb'b'en, yaji irin taushi da d'umin da suke dasu amma ya hana kansa.

Yadda ya barta tayi baccinta hankali a kwance jiya ba zai so ya tashe ta da wani abu da bata saba ba.

Ya lashe gefen lebb'ensa sanda ya k'araso bakin gate d'in. Tun kafin ya danna horn maigadin ya fara k'ok'arin bud'e gate din. Sunansa Malam Aminu, wani tsohon dattijo a kamfaninsu da ya d'auko shi tun sanda ya siya gidan a matsayin mai gadi.

"Sannu da zuwa Alhaji, Sannu da zuwa."

Ya fad'a lokacin daya shigo da kan motar cikin gidan. Maimakon ya amsa sai yace.

"Ina kwana Baba, mun tashi lafiya?"

"Alhmdlilahi Alhaji, Alhmdlilah. Jiya ina taso in tuna maka zancen tankin nan na baya daya fashe kuma sai naga dare yayi."

"Ya salam, na manta ne amma da kayi magana ai, yanzu to babu ruwa a ciki ne?"

"A'ah ai da yake jiya na sami b'arin wasu robobi a can baya na aikin gidan, sai na k'ona su na manne shi, to ya ragu dai amma har yanzu ruwan na zuba."

"Toh shikenan Baba, zan fita anjima sai in taho da wanda zai canja shi....ga wannan."

Ya d'auko d'aya daga cikin ledojin gefensa ya mik'o masa, ya karb'a da godiya sannan ya k'arasa ciki, ya ajiye motar a daidai balcony k'ofar falo sannan ya fita, ya kwaso ledojin ya rufe motar.

Sai da ya tsaya a gaban k'ofar sannan ya fara k'ok'arin lalubo key d'in a cikin na motarsa. sai dai kafin ya kai ga budewa ya jiyo wasu 'yan k'ananan taku daga ciki, sannan hannu yana fumbling da k'ofar, a sakan d'aya k'ofar ta wangale Sa'adha ta tsaya a gabansa cikin shigar wata doguwar riga ta orange material, rigar ta haska kalar fatarta da tayi fresh sannan ga hannayen nan nata da suka sha kunshi d'as, ya illahi! ya had'iye yawu da kyar sanda ya lura da idanunta.

Me ya same ta?

Kuka take yi!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

36


(¡î_¡î)

Da sauri ya taka steps d'in ya shiga ciki, sai da yazo dab! da ita sannan ya tsaya.

"Sa'adha me ya faru? me ya same ki? wani yazo ne?"

Yayi tambayar duk a lokaci d'aya sanda hannunsa ya lalubo nata, jikinta ya d'anyi b'ari amma nan da nan ya saki sanda ya shiga murza babban yatsansa a bayan hannunta.

Cikin sheshshek'ar kukan ta girgiza kai.

"Ba wanda yazo, na tashi ba kowa a gidan sai ni kad'ai, kuma nayi ta jin tafiya kamar za'a shigo amma ba kowa, sannan...."

"Shshhh..." yasa d'aya hannunsa yana goge mata hawayen a hankali.

Zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya tuna cewa ba taba zama a gida ita kad'ai ba, ta tashi a gida mai mutane da yawa ne dole yanzu taji bata saba ba.

"I'm sorry habibty...kina ta baccinki mai dad'i sanda na fita shi yasa ban tashe ki ba, kiyi hak'uri dan Allah."

A lokacin wani gefen tunaninsa ya ayyana masa cewa shine Babban abin tsoron da ya kamata ta guda ma a yanzu. yasa hannunsa a bayanta yana zagaya shi a hankali sannan yana k'ara rada mata tayi hakuri har sai da ya tabbatar zuciyarta ta nutsu sannan ya d'an sunkuya da fuskarsa side d'in kunnenta yace.

"Ban tab'a dawowa gida wani ya bud'e min k'ofa ba Noory, this is my first time...Nagode!"

Tayi murmushi a hankali cike da kunya sannan ba tare da ta d'ago ba muryarta tace.

"Ina kaje?"

Yaji murmushin shima na shirin kub'uce masa, irin wannan courage d'in nata na burge shi, bata cika k'umbiya-k'umbiya ba.

"Baki ga note d'in dana ajiye miki ba."

Ta girgiza kai.

Ya rufe k'ofar da k'afarsa sannan ya
d'ago mata ledojin hannunsa.

"Naje samo miki abinda zaki ci ne."

Idanunta suka kara girma da tambayar abinci ya siyo.

"Come on, na san jiya da za'a kawo ki anyi ta fad'a miki cewa ki kula dani koh?"

Bata amsa ba ya cigaba.

"Nima haka kowa yayi ta fad'a min, to ta yaya zan fara barin ki da yunwa da sassafen nan?"

Ta d'ago ta kalle shi da jik'akk'un idanunta da kuma d'an mitsitsin murmushi a lebbenta. Kwayar idanunta farare tas suka d'auki hankalinsa, yaji kamar zai fad'a cikinsu ne ya nutse. Subhanallah! ya fad'a a ransa.

She's so beautilful...very stunning and deadly gorgeous!

Ba tare da wani dogon tunani ba ya ajiye ledojin sannan ya kai hannunsa ya shiga tab'a doguwar jelar kitsonta da suka fito ta gefe, a lokaci d'aya kuma yana k'ara sunkuyo da fuskarsa saitin tata, ya lura ta ki'fta idonta a hankali tana kallonsa, sai da ya matso da kansa dab! da ita sannan ta rufe idanunta gabad'aya.

A hankali lebb'ensa ya sauka akan cheeks d'inta, wani waje just a mere inch from the side of her lips. Sannan a hankali yaji wani abu da bai tab'a experiecing ba a rayuwarsa, wani abu daban, wani abu sabo da babu shi a register kwakwalwarsa.

Cikin kiftawar ido jijiyoyin jikinsa suka daina aiki sannan jikinsa ya k'ame kamar dutse, yaji zuciyarsa na bugawa da k'arfi kamar zata tsaga kirjinsa ta fito, ya kasa koda kwakwaran motsi, Hannunta d'aya dake rike da nasa shine kad'ai wani abu dake rike da jikinsa, jikinsa da ya tsaya a k'ame kawai, frozen! kamar mai jirin wani abu, wani abu da zai dawo dashi duniyar zahiri.

Ring Ring Ring Ring Ring.

Wayarsa dake gaban aljihu ta zama wani abun daya janyo shi zuwa senses d'insa.

********

BAYAN KWANA UKU.

Imran bai tab'a tunanin cewa akwai wani farin ciki a duniya da ya kai wanda yake ji a yanzu ba, ya yarda cewa duk wani farin cikin duniya ya taru ne a gefe guda sannan farin cikin aure ma ya tattara a gefe guda.

Ya k'ifta dogwayen gashin idonsa a hankali yana kallon fuskar Sa'adha dake kwance a gefensa tayi pillow da kafad'unsa tana baccinta hankali a kwance, tunda yake bai tab'a ganin wanda ke bacci so innocent kamar ita ba.

Ya tuno yadda ta dinga dariya jiya da daddare lokacin da tasa rigarsa, tana cewa tayi kama da irin masu film d'in abinda dariyar nan, amma shi a idanunsa ba haka ya gani ba. she look so flushing and radiant!

A cikin kwana uku kawai yayi mugun sabawa da ita kamar yadda ya san itama ta saba dashi, don ko bata fada ba kyallin farin cikin idanunta da kuma yawan murmushinta zai shaida masa hakan, sannan ko daga yanayin maganganunta ta sake dashi saboda tana iya masa doguwar hira har ta bashi labari, wani lokacin ma tana indicating da hannunta cikin tsiwarta. Matarsa mai tsiwa ce, ya riga ya sani, Shine farkon abinda yaja hanakalinsa game da ita.

Bayan hakan ya kula ta fara sabawa da yadda koyaushe hannusa ke cikin nata, good morning kisses d'in da kullum yake raining a fuskarta da kuma sauran abubuwan da kullum yake iya k'ok'arinsa wajen daure zuciyarsa akanta, don ko sau d'aya a rayuwarsa bai taba experiencing irin feelings d'in dake nukurkusar zuciyarsa game da ita ba, wasu irin feelings ne kamar electricity suke yawo a kowacce jijiya ta jikinsa duk sanda yake tare da ita.

Kuma a yanzu tare suke yin komai na gidan, tare suka gyara setting d'in d'aya falonsu da tace baiyi mata ba sannan tare suka gyara kitchen d'in gidan, suka mayar da dukkanin kayan da aka jera cikin kwalinsu suka bar iya na amfani kawai, ya fahimci bata fiye son tarkace da kaya da yawa ba, she prefferd everything plain and simple! kamar yadda nature dinta take itama.

Tare suka zauna suka yi lists d'in dukkanin abinda suke buk'ata na gidan sannan suka fita suka ciko boot da bayan motarsa dasu, a kwana uku kawai rayuwarsa ta canja, yaji kamar duk zaman da yayi a da cikin wani kango yake sai yanzu ya shigo gida.

Murmushi ya sub'uce a kumatunsa amma bai motsa ba, ya kwanta very still yana kallonta, Sai wajen karfe biyu suka yi bacci jiya, ba zai so ya tashe ta tun yanzu ba, don ko da asuba, sai da ya d'auketa ya kaita har cikin toilet d'in sannan ta bud'e idanunta.

Kullum baya iya barinta tayi bacci da wuri, in suna tare lokaci tsaya masa yake yi yaga kamar ba wani sauran abu mai motsi a duniya sai su biyu, sai yaga idonta ya fara rufewa sannan yake fara rage tambayoyin da a kullum yake cika ta dasu, ya dinga jefo su d'aya bayan d'aya a hankali yana tracing k'unshin hannunta, k'unshin da a yanzu in za'a sake irinsa ya san ko mai k'unshin da tayi baza ta kaishi yin mai kyansa ba.

Ta gefen idonsa ya kalli agogon dake mak'ale a d'akin, lokaci ya nuna masa karfe sha biyu saura na rana, a yau ya kamata ya koma office don kwata-kwata bai d'auki hutu ba, sai iya 2-days leave d'in kawai da ya zama dole na ma'aikata, amma baya jin daga yau har zuwa satin ya k'are zai koma office, he wanted to spend his time with her, akwai abubuwa da yawa game da ita da bai gama sani ba. he wanted to know every single detail of her life.

Tun daga kan abubuwa masu muhimmanci har zuwa silly-silly abubuwan da bata d'auke su a komai ba.

Ya riga ya tanadi tarin tambayoyin da yake son yi mata dama, amma a kullum ya tashi ya kalli fuskarta, sai jerin tambayoyin list d'insa su k'aru. ya rayuwarta take kafin ya had'u da ita? Wadanne irin mutane take mu'amala dasu? Me take so me nene bata so?

His list grew. Koyaushe cikin tambayarta yake yi, in suna wani aikin, in suna cin abinci, in suna girkin da a yanzu tare suke yi ko kuma mafi yawan lokutan da zai jawota jikinsa yana absorbing duk wasu information d'inta. Amsoshin da take bashi, tun daga kan yanayin fuskarta da body language d'in da yake fahimta su suka bud'e kwakwalwarsa ya fahimci halayenta da yawa bayan iya wanda ya sani.

Sa'adha wasn't just good, she was perfect! kamar wani box guda ne da aka had'a complete set na duk abinda d'an adam zai buk'ata a rayuwarsa. Kuma tun a yanzu tsoro ya fara kama shi, tsoron ranar da lokacin tambayarta zata zo, ranar da zata fahimci shi d'in ba komai bane mai daraja, don ya san k'aryar da duk zai had'a ba zata tab'a tashin wani abu mai daraja irinta ba.

"Wane irin chewing gum kika fi ci?"

Ya tuno tambayoyin daya mata na k'arshe jiya kafin tayi bacci.

A lokacin tana kwance a jikinsa yana janye wani strand d'in gashinta da ya shiga bakinta. Ta d'ago da idonta ta kalle shi, yaji d'umin jikinta yana fitowa directly akan fuskarsa, k'amshin turarenta ya cigaba da nannad'e kowanne senses na hancinsa, ya k'ifta idanunsa a hankali sanda tunaninsa ke sulalewa kan plumpy lips d'inta da yake facing.

"Kowanne... banda d'an goma dana biyar."

Yayi murmushi a k'asan numfashinsa kafin yace.

"Na Ashirin fa?"

"In ka bani zanci."

"Wane colour kika fi so?"

"Suna da yawa."

"Fad'a min first daya fara zuwa ranki."

"lemon green."

Ya sake yin wani murmushin, ba tun a lokacin ba ya fahimci Sa'adha tana da ra'ayin kanta, bata tab'a yin wani abu don wai hakan ya zama zab'in mutane da yawa.

Hannunsa ya koma gefen fuskarta ba tare da amincewar zuciyarsa ba, ya sake janyo wasu tarin gashin nata, idonsa akan lips d'inta yana jin kamar ya d'ago da fuskarta sannan ya sunkuyo da tasa, zai iya had'uwa da bakinta halfway...

Enough!

Yayi saurin dakatar da kansa, in har hakan ta kasance, zai iya losing controll d'insa yaji mata ciwo.

"Meye last music d'in da kika ji?"

Her lips twisted, alamun tunani daga can tace.

"Last wak'ar da akasa ranar bikin mu."

Ya dage girarsa d'aya.

"Seriously? wacce kenan?"

"I beleive in you."

Yayi murmushi a hankali.

"I beleive in you too Noory!"

"Kai wanne ne last da kaji?"

"Mhm-mhm..."

Yayi saurin dakatar da ita.

"Har yanzu time d'ina bai kare ba, sai gobe turn d'inki zai fara."

"Zuwa yaushe toh?"

"Wannan ma tambaya ce, ki bari sai goben yayi tukunna sai ki tambaye ni."

Tayi murmushi mai fad'i tana lumshe idonta a kansa... Her smile was infectious to him!

Imran yaji duk wata kafa a jikinsa ta tsaya da aiki, sannan dauriyarsa ta k'are, a hankali ya sunkuyar da kansa cikin ramin wuyanta.

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI

AYSHA SHAFI'EE

37


(¡î_¡î)

Hannun Nanne ya mik'a zuwa d'aya b'angaren gadon, babu kowa kamar yadda tunaninta ya bata, ta bud'e idonta a hankali, babu Imran a kwance a wajen sai alamun imprint d'in kansa a jikin pillown daya kwanta.

Tayi murmushi a hankali sanda ta tuno event d'insu jiya da daddare, a yanzu ta k'ara yarda cewa Imran yana sonta har cikin zuciyarsa kuma ba abinda zai canja hakan. Tana ganin soyayyarta fal a cikin idanunsa duk sanda ya kalleta, sannan ko kad'an baya jin nauyin fad'a mata how much he loves her tun tana kirgawa a rana har sai tazo ta b'ace k'irgar.

Rayuwarta ta canja a iya kwanaki uku kawai da aurenta, Imran ya kaita wata duniyar daban mai cike da d'imbin kulawarsa da tarairaya. Ta riga ta saba dashi sosai a yanzu, ta saba da hirarsa sannan ta saba da jikinsa, yadda yake yawan tab'ata da yadda hannunsa kullum yake cikin nata.

Sannan baya taba barinta tayi abu ita kad'ai, komai tare suke yi cikin hirarsa, hirarsa ta tambayoyi kala-kala da suka had'a da dukkan wani insignificant detail of her existence, films d'in da take so da wanda bata so, wajajen da taje a rayuwarta, wajajen da take son zuwa, sannan tambayoyi game da ita...endless tambayoyin da suka shafe ta.

Ba zata iya tuna lokaci na k'arshe da tayi magana mai yawan wadda tayi a kwanakin nan ba, don ta tabbata in za'a tattaro jarabawoyin data amsa a rayuwarta kaf! a had'a dana Imran a yanzu nasa zasu fi yawa. Sau da yawa jikinta yana ta bata cewa zata dame shi da yawan maganarta, amma absolute yanayin fuskarsa da kuma yadda baya tab'a tsayawa da tambayoyin, suke bata kwarin gwiwar cigaba da magana.

Yawanci tambayoyin nasa masu sauki ne, 'yan kad'an-kad'an ne suke sata tunani ko kuma murmushi kafin ta amsa, kuma duk sanda tayi murmushin sai an sake new sets na wasu tambayoyin.

Akwai lokacin da fita ta kamashi kai wasu takardu office jiya, baifi minti goma ba yaje ya dawo, amma a lokacin taji ba dad'i, gidan ya mata wani iri da girma, bata san ta saba dashi har haka ba sai da ya dawo sannan taji komai ya koma mata daidai.

Da daddare suka zauna a falo da Tv a kunne, suna zaune a k'asan carpet da tulin eatries d'in daya siyo amma hankalinsu baya kan tvn, tambayoyi yake ta mata akan gidansu, da duka 'yan gidan, yana son ya san me da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login