Showing 111001 words to 113985 words out of 113985 words

Chapter 38 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28462

nan ne dai a gefen gado inda yayi nafila bayan tafiyar Hisham makaranta.

Ya dafe kansa cike da takaici sanda idanunsa suka koma suka lumshe, zuciyarsa ta dagule ta hasala kamar yadda hakan ke faruwa duk ranar da yayi mafarki da Sa'adha ya farka.

Wayar data katse a gefensa ta sake d'auka da wani ringtone d'in, ya zamo da hannunsa ya shafa kwantaccen sajensa sannan ya mik'a hannu ya d'auke ta.

"Hello mr. Siddiq?" Muryar baturiyar daga d'aya gefen wayar ta ambata.

"Yes." ya amsa cikin husky voice d'insa.

"There's an emergency about your son, we need to see you at the school now." ( Muna nemanka da gaggawa akan wata matsala data shafi d'anka.)

"Okay."

Hankalinsa a kwance ya amsa sannan ya kashe wayar, saboda hakan ba wai bak'on abu bane a wajensa, in dai matsala ce akan Hisham ya san yanzu suka fara, don makarantar da ya cire shi bayan dawowarsu daga madina, daga shi har malamar tasu sun riga sun saba da irin wannan wayar, tana d'auka zata ce.

'The usual.'

Shi kuma ya shirya ya tafi yaje Office d'in guidance and counselling yayi shiru yana jin dukkan k'orafinsu in sun gama ya basu hak'uri sannan ya d'auko shi su taho, a hanya shima ya bud'ewa Hisham nasa babin fad'an daga k'arshe kuma ya koma biya nasihar da dukkanninsu sun haddaceta.

Wannan shine kusan rabin yadda suke tafiyar da rayuwarsu a wani d'an karamin gari mai suna "Bottesford" dake k'ark'ashin birnin Nottingham a k'asar England. A zamansu na madina ne suka fuskanci k'alubale kala-kala saboda su da gaske hukunta Hisham suke yi duk ranar da yayi wani abu da ba daidai ba wanda hakan ya dad'a janyo baiyanar abubuwa mamakinsa saboda duk lokacin da ransa ya b'aci ko yayi fushi ne baya iya controlling kansa.

Dalilin da yasa har suka tafi dashi babbar headquarter d'in da ake hukunta masu laifi don yin bincike akan genesis d'insa saboda bayan sun d'ebe extraodinary possibilities d'insa, abubuwan da yake yi gabad'aya sun wuce irin abinda yara masu shekarunsa su kanyi.

Wannan dalilin yasa ba shiri Imran ya tattaro suka dawo England da niyyar zaiyi dedicating rayuwarsa wajen canja k'asashe da kuma garuruwa har zuwa lokacin da Hisham zaiyi hankalin da zai dinga b'oye possibilities d'insa, yayi wa kansa wannan alkawarin kamar yadda yayi wa Sa'adha alqawarin zai kula dashi har tsawon rayuwarsa.

Ya tuno rayuwar da yayi tsawon shekaru uku a hannun Bwama tana kula dashi kafin ya dawo hannunsa, rayuwar da yayi a cikin garin katsina kuma a cikin gidansu Sa'adha, rayuwar data sanya tsananin shak'uwa tsakaninsa da al'ummar gidan ya zama kamar ya maye musu gurbin mahaifiyarsa ne, rayuwar da Bwama bata tab'a barinsa ya baiyana wani abu daban nasa ba har ya gama zamansa tare dasu, bata taba bari ya bada wata kafar da zata kaisu ga sanin ainihin WAYE SHI ba. Abinda har yau har gobe ya kasa sanin da irin abinda zai gode mata, in banda tarin addu'ar da yake binta dashi a kullum.

A hankali ya mik'e ya ninke sallayar sannan ya shiga toilet yayi wanka sosai, bayan ya fito ya shirya cikin wata jacket mai kama da jallabiya data wuce gwiwarsa da kuma wandon jeans, ya taje gashinsa sannan ya d'auki key d'in motarsa ya fita, har ya kai waje ya tuna da wani abu, ya dawo ya shiga kitchen, ya d'auko robar lemo mai sanyi guda biyu sannan yayi locking gidan.

****

"Mr. Siddiq I just don't know how to explain but look at this and tell me how in the world can a 10- year old do this?"

(Ban san ta yaya zanyi maka bayanin abinda ya faru ba, amma ina so kalla sosai ka gaya min ta yadda yaro d'an shekara goma zai iya hakan.)

Mrs Judy, Malaysian-British Principal d'in makarantarsu Hisham ta fad'a tana kallon Imran dake zaune akan kujerar tsallaken teburinta.

Imran ya cije gefen lebb'ensa na k'asa yana kallon zungureriyar jelar kitson dake ajiye a gabansa, a gefensa na hagu, Wani ba'indiye ne rik'e da hannun 'yarsa wadda tasha plaster a gefen gashinta kusa da irin kitson da yake kallo a gabansa.

Daga d'aya gefensa kuma Malamin ajin su Hisham d'in ne da wasu Malamai biyu zaune suna jiran amsar sa.... Sannan hisham d'in kansa a tsaye daga gefe, wani kyayawan yaro mai kama da siffar mahaifinsa sak! in ka d'auke farin fatarsa da kuma da wad'annan manyan chocolate eyes d'in irin na Nanne sak! ya cije gefen lebb'nsa na k'asa shima kamar yadda mahaifinsa yayi sannan yana tsaye da wata irin tak'ama da kuma isa irin wadda ta wuce na yaro mai shekarunsa, yana sanye da wandon jeans da kema jar T- shirt, sai top mai had'e da hood wadda ya jawo hular ya rufe tarin gashin kansa da yake kar na jinsin jar fata, wanda duk da haka ya fito ta gaba perfectly styled dashi, girman jiki irin na yanayin abincinsu da weather ta can yasa zaka ce ya kai shekaru sha biyar.

Tun shigowarsa cikin office d'in, manyan idanunsa na kallon k'asa kawai ya zura hannayensa cikin aljihun wandon, ya had'e girar sama da ta k'asa yadda wani zai rantse ba akansa ake magana ba, yana jira ne a gama ya fad'i abinda ya kawo shi daban.

Cikon lallausan turancin nan nasa Imran ya bud'e baki yace.

"Ni kaina ban san me zan ce muku ba principal, ba san ta yaya yaro irin hisham zai iya aikata hakan ba, saboda haka sai dai mu danganta al'amarin da tsautsayi kawai, ina mai basu hakuri da kuma fatan zasu yafe masa sannan a gaya min tarar nawa hakan ya kama, zan biya yanzun nan."

Duk yadda principal din nan da mahaifin yarinyar suka kai ga jin haushin Hisham ba yadda suka iya haka suka hakura, aka fad'awa Imran tarar cire gashin ya fito da card d'insa nan take ya biya yana k'ara basu hak'uri, da haka ya bar office d'in Hisham na bin bayansa ba tare da ya ko kalli inda Malamansa suke binsu da kallo ba.

"How many times do we have to talk about this Rhea, I told you he's a single father."

(Sau nawa zamu yi maganar nan ne wai Rhea, na gaya miki bashi da aure.)

"I know, I knew! but I just can't control myself everytime he came into the view, and he's an african you said? oh my God! I swear Africa never look this beautiful and handsome an dashing and..."

(Na sani, Na sani! amma bana iya rik'e kaina ne duk sanda na ganshi, kince daga Africa yake koh? na rantse Africa bata taba min kyau irin haka ba, da shek'i da kyau da...)

"Hello Rhea, he's not Africa, he's from Africa! and you better be careful.. he's Emily's crush as well!"

(Kinga Rhea, bafa shine African ba, k'asar ce, kuma ya kamata kiyi hankali.. don Emily ma tana son shi!)

Imran ya tura main k'ofar fita daga makarantar ya fita, ya riga ya saba da jin irin wannan hirar daga wajen mata a kusan duk inda ya taka ya shiga cikin k'asar turawa, k'asa irin wadda kunya tayi k'aranci a cikinta, ire-iren abubuwan dake sawa yaji kewar arewacin Nigeria ta kama shi, wajen da yake cike fal! da tari al'adun Hausa-fulani masu tsananin kyau da burgewa, abin alfaharin duk wanda ya kasance a cikinsu.

Amma ba yadda zai yi ne, ya riga ya yiwa Sa'adha alk'awarin kula da Hisham tsawon rayuwarsa, kuma alk'awarin ya had'a har fa bashi kulawa ta gari da kuma d'ora shi akan hanyar da zata fi karkarta ga rayuwar bil'adama, shi yasa yake bin makarantun turawa dana larabawa, wad'anda suka fi Nigeria wajen bada ingantaccen ilimi boko da kuma na addini, don duk wani abu da zai bawa Hisham a duniyar nan, sai ya tabbata mafi kyau ne!

Ya sawa hadaddiyar motarsa k'irar 'Venza' key suka juya suka fita daga harabar makarantar suka cilla kan titi, hasken ranar da yayi tar! a lokacin ya haska kyawawan fuskokinsu su duka biyun, wadda banbancinsu ya kasance abu biyu, na farko fuskar Imran cike take da kwantaccen saje da gashin baki wanda a yanzu suka k'ara yawa fiye da lokutan baya, yayin da na Hisham sid'ik take, in banda lallausan gashi kad'an da ya fito har wajen hab'a, alamun nan gaba shima sajen ba zai masa wahala ba.

Sai kuma banbancin yarinta da ta alamun matashi d'an shekara talatin da takwas. Imran ya janyo wani bak'in space ya saka saboda hasken ranar da ya masa yawa, sai ya k'ara wani kyau kamar yana shirin gabatarwa da kamfanin space d'in talla ne, ya d'ago robar lemon nan guda biyu da har yanzu ke d'igar sanyi ya mik'awa Hisham d'aya.

"Ina jinka." Ya fad'a ba tare da ya d'auke idonsa daga titi ba.

"Daddy cewa tayi tana sona."

Sai da Imran ya kware a lemon da yake sha kafin ya rage gudun motar ya juyo ya kalle shi.

"What?"

Hisham ya d'aga kafad'unsa shima ba tare da ya kalle shi ba.

"Ai ba ita kad'ai ce bama, ita nata abin ne yafi bani haushi tayi ta zuwa wajena, wallahi da an barni sai na cire gabad'aya gashin kanta."

Imran ya buga kansa da jikin kujerar sannan ya tura hannunsa cikin gashin kansa.

"Hisham for goodness sake! shekarar ka fa goma, kana grade 4... me mamanka zata ce in taji haka?"

Ya riga ya saba masa, suna maganar Nanne ne a kullum kamar zasu koma gida su same ta, don ya yarda in ba da hisham ba babu wanda zai iya hirarsa da ita, kuma shima ya kamata ya san wani abu na mahaifiyarsa.

Hisham ya kurb'i lemonsa kafin yace.

"Cewa zata yi duk wanda ya sake cewa yana son Babyna, kabi su duk mammare su sai sun koma ja kamar tomato."

Imran ya d'anyi murmushi kafin shima yace.

"Sannan kuma tace dukkansu ka had'a musu da Allah ya isa!"

Hakan yasa suka kyalkyale da dariya gabad'ayansu kafin kuma dariyar ta mutu a hankali, yadda suka saba duk lokacin da suka tuna cewa babu ita d'in. Kusan a tare suka cusa hannunsu d'aya cikin gashinsu sannan hisham yace.

"Yaushe zamu je Nigeria?"

"Yaushe zaku yi hutun Summer?"

"In the next three weeks."

"Then ka had'a kayanka!"

Suna isa gida Hisham wayarsa ya fara lalubowa ya kira number Sadiq, bugu d'aya biyu ya d'auka.

"Man, ya akayi ne?"

Cewar Sadiq daga d'aya b'angaren, wanda shigarsa d'akin Inna kenan bayan ya dawo daga wajen aikinsa, tunda a lokacin har ya gama masters dinsa a b'angaren economics. A yanzu sune samarin gidan Baffa shi da 'yan biyu, duk sauran yayyen nasu sunyi aure da 'ya'yayensu. Aunty Amarya ta sami abinda take so, 'yayanta ke juya kusan komai na harkar gidan tunda tsufa ma ya kama Baffa baya iya abubuwa da yawa.

Cikin irin hirar da suka saba Hisham yake gaya masa zai zo Nigeria nan da sati uku, daga k'arshe kuma ya bawa Inna dake ta mik'o hannu jin ance Hishaam ne ke wayar.

"Hey, Baby girl! ya k'afar taki?"

Imran na tsaye daga jikin dining hannunsa d'aya a aljihu d'aya kuma rik'e da mug din coffee yake kallon Hisham, yana iya jin magiyar Inna ta cikin wayar wadda a kullum bata gajiya da ita kan suzo taga Babanta, koda kuwa a yau suka je suka dawo in an sake waya sai tace su taimaka su dawo, a yanzu tsufa ya kamata kwarai! don ko tafiya bata iya yi sai an kamata.

Hisham nata dariya cikin wayar kamar bashi ba yana tsokanarta, Imran yaji wani sanyi a kasan zuciyarsa daga yadda yake kallonsa daga nan. Kaf! duniya yanzu baya tunanin akwai abinda yake k'auna sama da d'an nasa, dama Sa'adha ta riga ta fada.

"Ina ji a jikina ulfat Babyn nan alkhairi ne a garemu, ba zai tab'a zama irin tunanin da kake ba...ina son shi sosai Allah, kuma kaima na gaya maka zaka zo ka so shi fiye da tunaninka insha Allah."

"That's true Noory!" ya fad'a a hankali yana kub'ar coffee d'insa.

"So true!" Muryar jaamil ta amsa a gefensa.

Yayi saurin juyawa ya kalle shi sannan yaja tsaki.

"Jaamil don muna k'asar turawa fa haka baya nufin an daina sallama kenan."

"Ko kuma ya kamata mutum ya daina tafiya zurfin tunani yana amsa sallama in anyi ba."

Ya fad'a yana karbar mug d'in hannun nasa.

"Me ya kawo ka ma ne wai? it's less than a week fa da kazo? An gaya maka haka ake shugabantar al'umma?"

Jaamil ya d'age kafad'unsa yana zama akan dining d'in.

"Ya zanyi, kewarku nake kullum kamar me... can din ba wani abu mai gamsarwa daga hukunci sai zartarwa! inaga ya kamata in canja tsarin abubuwa da yawa wallahi."

"Ko kuma ya kamata ka sami wadda zata canja ka ba, nasha gaya maka it's high time wata ta shigo cikin rayuwarka, ya kamata kayi aure."

Imran ya fad'a yana zama shima akan kujerar dake fuskantarsa.

Shekaru goma kenan baya, da jaamil ya kasance shugaban nahiyar Muzzaffar! sakamakon kashe Sareefa da Imran yayi, don a lokacin da ya isa Muzaffar bai tarad da Naani a raye ba, Sareefa ta kashe ta bayan dukkan abinda ta tanada saboda ita, bayan dukkan d'awainiyar data yi mata, ta kashe mahaifiyarta sakamakon tsananin k'ullatar ta da tayi da kuma son mulkinta, wanda a lokacin kuma take fafutuk'ar ganin yadda zata ga bayansa shi da jaamil.

Saboda haka a lokacin da ta ganshi, bata b'oye masa komai ba na yadda ta kashe mahaifiyarta saboda ta fahimci bata da niyyar d'aukar fansa akansa, sannan ta shiga ganin bayan matarsa kafin ta k'araso gare shi. Ta gaya masa dukkan abinda yaji daga cikin habler nan Naani ta fad'a mata ne saboda ta kwantar da hankalinta ba wai don haka komai yake a zahiri ba, Tace da gaske ne tun farko Naani ta d'auko shi ne saboda wannan aikin da take so yayi mata, amma daga baya zuciyarta taso shi tsakani da Allah, So irin wanda ita da take d'iyarta bata taba mata.

Saboda har a lokacin da ya hana ta dutsen Nil, zuciyarta ko kad'an bata da nufin cutar dashi, tace mata ne kawai zata kyale shi don ta san bayan wani lokaci zai dawo gareta shi d'in mai tsananin biyayya ne, Saboda haka a tunaninta na son farantawa Sareefa itama, sai ta bata kusan dukkan karfin jikinta, sannan tayi murabus ta nad'a ta a wanda da wannan damar Sareefan tayi amfani ta kashe ta bayan kwanaki biyu.

Sannan ta shiga kokarin ganin bayan matarsa, don tayi rantsuwar sai ta guntule farin cikinsa tukunna kamar yadda suka hana ta itama kafin shima ta kashe shi, sannan tazo kan jaamil da mahaifiyarsa Bwama. Sai dai a lokacin bata da ikon kusantarsu saboda karfin dutsen Nil dake cikin gidan da suke, saboda haka daga nesa ta karanci halayen Sa'adha tsaf! da kuma mutanen da take mu'amala dasu.

Ta haka ta gano cewar hankalinta yafi karkata ga Safiyya maman yarinyar nan Hidaya, ta gaya masa cewa matar bata tab'a zama muguwa ba kamar yadda yayi tunani a baya, kawai bai yarda da ita bane saboda jikinsa ya bashi alamar da bai iya ganewa ba a lokacin, alamar cewa rayuwarsa zata hargitse ne ta dalilinta, saboda da ita tayi amfani, ta shiga jikinta taje har kofar falonta, ta bugawa Sa'adha 'Kambun Turaz' a cikinta, wani abu da suke hukunci dashi wajen karya gab'ob'in irin halittarsu.

Sai a lokacin Imran ya fahimci Sa'adha ba karamin k'ok'ari tayi ba na iya tsaida bugun zuciyarta har sanda Hisham ya fito duniya, don in har za'a bugawa irin halittarsu wannan kambun gab'obinsa su karye inaga an bugawa halittar bil'adama wadda take mai rauni?

Mummunar kisa irin wadda in ido ya gani zai rikice, kwakwalwa ta hargitse hankali ya tashi, ita yayi wa Sareefa a lokacin da take ganin tayi k'arfin da ba zai iya galaba akanta ba, ya kashe ta amma bai cigaba da farfasa halittar jikinta ba har saida jaamil ya janye shi da k'arfin tsiya.

Bayan nan kuma bai k'ara zama cikin hankalinsa ba tsawon watanni, jaamil shi yayi fafutukar kula dashi a duk lokacin nan, alhali ya karbi sarautar nahiyar Muzzafar! domin shai kad'ai ne jinin sarautar da ya rage a cikin zuri'ar Naani.

Damuwa da depression kala-kala ba irin wanda bai shiga ya tafi ta gaba ba, saboda ba don d'aya b'arin ruhinsa dake jikinsa ba ya tabbata da tuni zuciyarsa ta dad'e da bugawa ya mutu! don sai a shekarar da rik'on Hisham zai dawo wajensa ne sannan ya samu ya fara dawowa haiyacinsa... amma Allah ya sani, ya azabtu fiye da tunanin mai tunani!

"Kar ka damu, zanyi aure kwanan nan yarima."

Imran ya zare idanunsa a lokaci d'aya, sannan ya matso da jikinsa ta kan table d'in.

"Kace min mafarki nake yi jaamil, kaine yau kake fadar kalmar aure da bakinka? ya salam! you seriously need to tell me this, wacece haka?"

Kafin jaamil yayi magana Hishaam ya taho da wani irin sauri da yafi k'arfin ganin idanun d'an Adam ya d'ane kan jaamil yana ihun murna.

"Hishaam sau nawa zan gaya maka ka daina irin wannan saurin?"

Imran ya fad'a da k'arfi amma Hishaam bai ko saurare shi ba, ya dinga kyalkyala dariya yana jijjiga jaamil har sai da ya suka sauka daga kan kujerar suka shiga birgima a k'asa.

Sai yayi murmushi kawai sannan ya janyo wayarsa ya kunna ta.

Hoton Sa'adha tar! ya baiyana akan screen d'in, ta lumshe idanunta tana murmushi, shima ya lumshe nasa idon a hankali yayi murmushi.

"I love you so much Nanne!"

Sunan da baya tab'a jin ya kirata dashi a tsawon rayuwarta!

"Allah yayi miki gafara!"


KARSHE.

***

Alhamdlilah! Alhamdlilah!! Alhamdlilah!!

A yau mun kawo k'arshen labarin WAYE SHI? munji komai kuma ina k'ara baku hak'uri da ta'aziyya akan rashin Nanne da muka yi.

Ba yadda muka iya ne, k'addarar labarin tafi soyayyar da muke yi mata!

Nagoode! Nagoode!! Nagoode!!

For all d love u guys show me along the way. Allah ya faranta muku da d'imbin alkhairi????

A big shout out a to all wad'anda zasu zo bayan mun gama labarin nan, na gaishe ku kyauta! Allah ya saka muku da alkhairi!??

Kuma kuyi min dropping ra'ayinku game da labarin nan ta wannan number, 08067794315 zan dinga samun lokaci ina dubawa don in dinga baku dukka amsoshinku Insha Allah.

Allah ubangiji yasa zamu sake had'uwa a next labarina, wanda nake ganin zai ma fi WAYE SHI dad'i saboda I'm becoming a better writer now!????

Contact me via dat number for more Information, Allah ya sada mu da alkhairinsa.!??

Thank you guys!??????






































Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login