Showing 6001 words to 9000 words out of 113985 words

Chapter 3 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28446

karbe.

"Me ko zata yi masa banda tsananin azaba irin tasa."

"Nace me tayi maka?" ya muhammad ya sake tambaya.

A dak'ile ya amsa.

"Yaya kayana na shanya a courtyard ta d'ebe."

Kafin a tambayeta nanne ta k'ara rushewa da kuka tana fadin wallahi tallahi k'arya yake ita ba abinda ta dauka.

"Kai dama tana d'aukan kayan ka ne?" yaya Ahmad ya shigo zancen.

"Ba wai tana d'auka bane, na san ita ta d'auka don ita kadai ce a wajen lokacin da aka shanya."

"Toh ai hakan baya nufin ita ta dauka...ke kuma kar in sake ji kince k'arya yake, tashi ki tafi."

Dama abinda take jira kenan, saboda haka yana fad'a ta mike tayi ciki.

"Guda nawa ne kayan?" Taji yana tambayar suraj bayan ta shiga d'aki.

Ta wanke fuskarta sannan ta yafa d'an karamin mayafi lightbrown akan doguwar rigar, ta nufi wajen kayan wankinsu ta janyo kayan suraj d'in dake can k'asa ta cusa su a bak'ar leda tana fadin..

"Kai da kayan nan har abada wallahi."

Ta fito har a lokacin suna hayaniyarsu ana ta dariya, kanta a mik'e ta fita, Allah yaso idon inna bai hango ta ba lokacin ta juya tana ganin adadin abincin da yaya ibrahim ke zuba mata.

Tana sauka k'asa ta tarar Rahma na jiranta a bak'in k'afar bene.

"Me tace?"

"Tace dai kar mu dad'e, don wai an tafi markad'en Alala zamu yi k'ulli."

"Ai dama ba dad'ewa zamu yi ba, abinda ya kaimu kawai zamu yi."

Ko dai abinda ya kai ki. Rahma ta fad'a a zuciyarta.

Don inda zasu je d'in gidan wata 'yar islamiyarsu ce Hafsa, a sati biyun da nanne bata je makaranta bane hafsan ta tada ballin cewa nanne na neman kwace mata saurayinta, wanda kullum aka tashi zai zo ya raka ta gida. Ta dinga masifar cewa wai duk sanda aka tashi sai ta dinga binsa da kallo wani lokacin ma harda murmushi.

Abin ya zama topic d'in ajin nasu kullum sai an tada zancen da za'a zazzage ta, ganin ma taki dawowa yasa suka rubata takarda aka gaya mata bak'ak'en maganganu sannan aka bawa safiya ta kawo mata shekaranjiya da yamma, jiya kuma ta titsiye rahma sai da ta gaya mata dukkan abinda yake faruwa da bata nan.

"Zamu biya ta shagon khalid kafin muje."

"Wane khalid?"

"Mai shagon bakin titi mana."

Khalid irin 'yan karyar samarin layin nan ne da ba abinda suka sani sai d'aukan wanka, iyayensa masu rufin asiri ne daidai nasu, amma shi inda yake kai kansa yafi haka, shagon da yake dashi ma na soft drinks da recharge card wani Alhajin layinsu ne ya bud'e masa. Dalilin haduwarsu da nanne kenan wajen siyan lemo.

Suna isa kuwa ya tsuke bakinsa yana murmushi, kafin ya fito ya fara shafa sumar kansa irin ta fulani.

"Kin b'uya fa, kwana wajen shida kenan ban ganki ba."

"Shida?"... Ta zare ido tana kallonsa.

"Har wani kirgawa kake?"

"Sosai ma, ke d'in ai ta daban ce."

Ta tab'e baki kafin ta mika masa ledar hannunta.

"Kaga rik'e, kaya ne na kawo maka ban sani ba ko zasu yi maka?"

"waww! Ai ko nagode sosai zasu yi ma insha Allah..."

Ya d'ago ya kalleta, idonsa d'aya a kanne.

"Thank you, har na hango ni a ciki."

"Wai me yasa kika damu da Khalid d'in nan ne."

Rahma ta tambaya bayan sunyi gaba.

"Saboda bashi da matsala, kuma yana yin duk abinda nace."

Ta amsa kanta tsaye wanda kuma hakan ne, in dai mutum zai jure halinta ya kuma dinga yi mata biyayya toh fa zasu yi shiri dashi.

Rahma bata kara cewa komai ba, tunda ita ta san abinda khalid ke tunani daban ne, don har ya fara yad'awa a unguwa cewa nanne sonsa take yi, zaiyi auren jari.

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

04


(¡î_¡î)

An kawo lefe kamar yadda kowa ya zata, akwati goma sha shida da kuma bayanin cewa bayan auren a can nijar jamilan zata zauna, anci an sha a gidan kamar gidan biki sannan kuma an tarbi mutanen nijar cikin girmamawa kafin su tattara su tafi wani guest inn dake bakin titin unguwarsu inda baffa ya kama musu d'akunan kwana. Su mama rabi an samu abinda ake so, wato lefen 'yarta yafi na kowa, don na Aisha guda goma sha biyu ne, nasu maryam da nafisa kuma takwas-takwas. Saboda haka sai washe baki take yi anata hidima.

Duk wannan abin ya faru ne bayan an gama tashin hankali da bala'i a gidansu hafsa, inda nanne ta rufe idonta ta zage ta tas! a gaban 'yan gidansu, ba don rahma bama da abin ya kaisu harda kokawa don sun tarar maman su hafsar da kishiyarta basa nan sai 'yan matan gidan kawai, amma duk da yawansu ba wanda nanne ta kyale a cikinsu, sai da rahma taga abin zai koma kokawa sannan ta jata da kyar suka bar gidan.

Suna zaune bayan sallar isha a barandar dake kofar kicin itada Rahman dake b'arar maggi, ta sake yin kwafa tace.

"Na rantse da Allah rahma don dai ba zan iya kula wannan jagwal din yaron bane, amma wallahi da sai yarinyar nan ta zama 'yar kallo tsakanina dashi sai na mayar mata da tunaninta ya koma gaske."

"Dan Allah ki bar maganar nan, tunda dai kinje kin ja mata kunne ai komai ya wuce."

"Ba abinda ya wuce, in dai bala'i ne yanzu aka fara, saboda da sai wani satin nake tunanin komawa makarantar, amma wallahi ranar asabar d'in nan zanje muyi ta da sauran 'yan iskan k'awayen nata da suke biye mata, sai naci mutuncinsu d'aya bayan d'aya."

"Kin san fa malam murtala ya dawo, wallahi aka kai masa ku kuna fad'a ba zai muku da sauki ba, don ranar litinin d'in nan kusan bulala talatin yayi wa su Anisa."

"Ko d'ari zaiyi min wallahi sai nayi musu kacakaca a ajin nan..."

Ganin bata da niyyar sauka yasa ta karkato da farantin kan cinyarta tace.

"Allah ya kaimu asabar d'in toh....yanzu dai d'an taya ni b'arar maggin nan."

Suna cikin yi, rahma ta sako mata zancen saurayinta daya nace akan zai turo iyayensa, ita kuma ta dage sai ta gama makaranta tukunna tunda dama ss3 zata shiga yanzu, tare dasu nannen.

"Toh wai meye? Tunda dai mamanki ta yarda dashi ki bari ya turo mana."

Rahma ta kalleta da murmushi.

"Kalli wadda take cewa ba wani abu bane, ke da har yanzu ba wanda kika taba saurara...kuma kin san in dai za'ayi auren zainab baffa dake zai hada tunda ba dole sai kun fara jami'a ba, gashi ita tana da wani."

Nanne ta tabe baki.

"Nifa na gaya miki harkar samarin nan duk wahala ce, ni in zanyi auren ma cewa baffa zanyi kawai ya zabo min babban mutum mai hankali, don duk samarin nan 'yan duniya ne."

"Haka dai kike gani don baki taba tsayawa kin saurari wani ba, ga masu son miki magana da yawa."

Da jin haka, idonta ya hango mata fuskarsa, wani mutum guda daya da ta kasa cire shi daga tunaninta, tun ranar data fara ganinsa har yanzu da baya nan, yanzu da take jin kamar tana kewarsa, kewar yadda take ganinsa tsaye a kofar gidansu duk sanda ta dawo daga islamiyya, a saman mota yana danna waya ko tare da abokansa.

Yawanci iya haduwarsu kenan, sai ko da safe wani lokacin in zasu makaranta ta hango shi ya dawo daga morning training, ita ko sanin gabadaya 'yan gidansu ma bata yi ba don bata taba shiga ba, duk da cewa yanzu zasu yi kusan wata hudu da dawowa, kuma wata k'anwarsa ma sun saba da safiya don ta shiga islamiyarsu.

"Wai tunanin me kike?" Rahma ta katse ta.

"Ba komai, me kike cewa?"

"Wannan purple jakar ta lefen aunty jamila tayi kyau sosai, kinga d'an flat takalminta kuwa?"

Daga nan ta shiga santin abubuwan ciki, wanda a lokacin da ake d'agawa ita nanne hankalinta ya tafi wajen zirawa Aunty nanah (k'anwar mama rabi) fara cikin rigarta, don sun kusa yin karo da ita a hanyar bene ta zageta har tana fad'in tayo halin rashin mutunci irin na Nuratu mahaifiyarta.

Ai kuwa ba'a gama ganin kayan ba, ta hau make-make a jikinta, kafin ta tashi da gudu tayi d'aki.

***** *****

Sati d'aya bayan haka rayuwar gidan ta cigaba da tafiya tare kuma shirye-shiryen biki daga kowanne b'angare, don kuwa kowa ya dage wajen ganin bajintarsa tafi ta sauran saboda wata guda ne kawai ya rage ayi bikin, baffa ya saiwa kowacce amarya dank'ara-dank'aran gadaje guda biyu da kuma furniture saitin kujeru suma guda biyu, sai manyan-manyan tvn plasma da sauran kayan saitinsu.

Sauran abubuwa irin na kitchen da kuma k'arin wasu abu na ado wannan duk na iyayensu mata ne, sannan ya bawa kowacce a cikin matan nasa dubu d'ari tasa gudunmawar don yaga take-takensu na cewar bayan events d'in daya had'a za'a yi gabad'aya, kowacce na shirin kama waje tayi wani bikin da 'yan uwanta. Hatta Aunty amarya saida ya bata dubu hamsin yace tayi d'inki itama da 'ya'yanta. Don haka a kowacce rana gidan cike yake da mutane na 'yan uwa dake zuwa anata faman hada-hada tsakanin gidan da kasuwa.

A lokacin an koma makarantar boko daga dogon hutun da akayi na sabon zango, wanda su nanne suka shiga aji shida itada sadiq da zainab, safiya kuma na aji uku, surrayya ce kad'ai a ajin na k'arshe a primary. 'yan biyu kuma sun sami abinda suke so sunyi candy, sai aikin baccin safe kamar baza su tashi ba, da yamma kuma su tafi ball ko yawon eatery da abokai.

Da safe nanne na zaune a falo ta hard'e k'afa d'aya kan daya tana shan tea, uniform d'in makarantarsu ne a jikinta na farar riga da bak'in wando, ba d'ankwali a kanta sai jelar manyan kalbar da rahma tayi mata sun zubo har k'asan kafad'arta.

Inna ta juyo ta kalleta daga kan sallayarta data gama lazumi.

"Yanzu nanne baza ki dubi girman Allah da magiyar da nake miki ki tsefe kalbar nan ba? Tafi sati biyu fa akanki."

Ta yamutsa fuska.

"Inna na fad'a miki sai na wanke kan ne kafin in sake kitson kuma wankin wahala yake bani, so nake in samu lokaci inje saloon tukunna."

"Ai shikenan. sai kiyi ki gama kafin su fara jelan kiranki."

Tana rufe baki kuwa safiya ta shigo falon, ta durkusa har k'asa ta gaishe da innan sannan tace.

"Nanne tun d'azu fa muke jiranki, kowa ya fito kuma yaya umar ne zai kaimu yau."

"Yaya umar?...ina idris d'in?"

"Wai ya aiko bashi da lafiya."

"Toh maza tashi, don kin san halinsa." inna ta fad'a da sauri.

Ta zura hijabi sannan ta dauki jakarta tare da safa da dankwali tabi bayan safiya, tun daga waje sadiq dake zaune a gaban sienna da ake kaisu ya langwab'e kai yana mata murmushi, hakan ya tabbatar mata sun dad'e suna jiranta kenan.

Suna isa safiya ta shige baya sannan ta zauna a kujerar gefen surrayya ta rufe kofar motar, umar ya ajiye tab d'in da yake dannawa a gefe sannan yayi magana ba tare daya juyo ba.

"Ke kina jina?"

"Eh." Ta fada kanta tsaye.

"Idan kin dawo kije wajen mama Azumi ki karbi key din d'akina, ki gyara shi tas! Ki wanke band'akin, sannan kuma for the whole week ni zan dinga kaiku makaranta, idan kin ga dama ki bari kullum in dinga riga ki shigowa motar nan."

Yana gama fad'in haka yaja motar suka yi gate, ta had'a ido da sadiq ta cikin mudubi ya sake sakar mata murmushi motsin fatar bakinsa na fad'in 'yan mata! Ta gallara masa harara kafin ta sunkuya saka safarta.

Suna isa makarantar ta tarar har malami na farko ya shiga, wata malamar biology mai tsanani rashin son surutu ta juya kan allo tana rubutu, bata bari ta ganta ba ta shigo a hankali ta wuce bencinsu ita da Amina, dukkan 'yan ajin na kallonta ba wanda yayi magana, don duk da cewa ba tsoronta suke ji ba kowa yana d'an shakkar surutun ta, irin dai karar da akewa mutum mai baki.

Tana zama Amina tasa hannu ta cusa mata jelar gashinta da ta fito ta gefe. In da akwai abinda ya banbanta halin nanne da Amina to rashin kunya ce, saboda ita magana ce kawai da ita amma bata da rashin kunya irinta nanne.

"Ya akayi yau kika zo da wuri?" ta tambayeta a hankali.

"Azababben yaya umar ne ya kawo mu wallahi."

"Ina idris d'in?"

"Wai bashi da lafiya."

"Kice kin daina missing first period."

Taja guntun tsaki.

"Wai a tunaninsa ma fa haka na makara ban fito ba."

Amina ta d'anyi dariya kafin tace.

"Zaki saka mai wani sabon tunanin ne."

"Ke bari a fita break, akwai maganar ma daza muyi."

"Haba? Ko munyi first catch ne?"

Ta juyo daga kokarin d'auko littafin da take, ta gallara mata harara.

"Ke dai 'yar iska ce, baza a taba wani abu a duniya ba sai saurayi."

A daidai nan malamar ta juyo ta kalle su.

"Surutun me kuke yi?" Ta tambaya da turanci.

Kai tsaye Amina ta d'ago tace.

"Malama rasuwa aka mata ne shine nake mata gaisuwa."

"Ajin nawa ne gidan gaisuwa?"

Ta sake gyara murya tace.

"Ma, ai yadda mutuwa take zuwa ko'ina haka gaisuwarta ma ana iya yi a koina."

Ta kalle ta da mamaki kafin ta nuna musu hanyar kofa.

"Toh ku fita waje kuyi zaman makokin."

Inda sabo dama hakan yasha jawo musu fitowar bakin aji, don Amina irin mutanen nan ne da basa taba rasa amsar fad'a, ko waye mai tambayar kuwa.

Har sun kai k'ofa ta tsaida su da tambayar waye ya rasu, Nanne tayi rau! da ido kafin ta amsa da kazar da take kiwo ce, abinda ya jawo dariyar gabadaya ajin kenan wanda ya jawo musu kneel-down a gaban aji, next period ma english ba suka shiga aji ba, tunda malaman k'awaye ne haka suka zauna har aka fita break.

Da break d'in ma basu samu damar maganar ba saboda haduwa suka yi da 'yan click dinsu akayi ta hira kala-kala, wata maryam tayo musu dan malele ana sha ana cafta. Bayan an kada kuma suka tafi wanko farantan da suka aro a kicin din makarantar, suna dawowa kuma aka tafi physics lab, suka ci uban note sannan aka fara practical, last period ya kasance geography ne, wani malami mai azabar dictation shima.

Sai da aka tashi sannan suka tsaya daga k'asan wata bishiya a harabar parking lot din inda ake d'aukarsu. Nanne ta kalli Amina sosai tace.

"Ta yaya aljanu suke shiga jikin mutum?"

Amina ta d'an had'e girarta.

"Ban gane ba, nifa ba malama bace."

"Dalla ina nufin kamar yanzu ni in inaso aljanu su shiga jikina me zanyi?"

"Sa'adha aljanu? Me zaki yi dasu?"

"Wani malami nake so na waskawa mari a islamiyarmu."

"Me yayi miki?"

"wai kawai daga cacar baki ta had'a mu da wasu mahaukatan yara a aji, ya kama ya mana bulala ashirin-ashirin."

"Toh kiyi na k'arya mana, me zai sa ki jawo wa kanki bala'i?"

"Malamin ne mugun d'an izala ne, yanzu sai ya iya ganewa."

"Wallahi ba ta yadda za'ayi ya gane tunda aljanu dai ba ganinsu ake ba, kuma a yadda na sanki zaki iya, kawai abu d'aya ne kar ki tab'a bari ya dake ki da sunan ruk'iya tunda kin san ke za'a jibga."

Ta d'anyi shiru tana tunani.

"Kuma fa hakane, ba dai ihu ake ba da zare ido?"

"Sannan ki cire d'ankwalinki ki tsaida idonki tar! ko waye yazo kar ki nuna kin sanshi ma balle wani tsoronsa, ki zagi duk wanda kike so kuma."

Nanne ta tsaida idonta waje d'aya, tunaninta na hasko mata ita a hoton da Amina ke zanawa.

**** ****

BAYAN SATI BIYU.

Da maghriba ta dawo daga bayan layinsu gidan wata hajiya talatu, ta karbowa inna tarin adduwa a cikin bakar leda wai ta gaji da cin goro. Tana tafe tana cilla ledar a hannunta, layin ko'ina da haske saboda wuta da aka kawo a lokacin kuma babu mutane da yawa, daga tsillin masu wucewa sai masu gadin gidaje da suka fito waje da 'yar rediyonsu.

Cilla ledar da zata sake yi sama sai kawai ta yage a daidai sanda ta karyo kwanar layinsu, gabadaya adduwar ta tarwatse wasu ma suka shiga gangarawa cikin kwalbatin dake gefenta, taja karamin tsaki.

"Ai wallahi dama na san sai ledar nan ta yage, matar nan tana tab'a bada wani abin arziki ne?"

Ta tsaya tana kallonsu kamar su zasu kwashe kansu kafin ta tsugunna ta shiga bin wadda bata fada kwalbatin ba tana sakawa a hijabinta.

"ledar bata da kwari ne?"

Kamar a irin tunanikan da take yi kunnenta ya jiyo mata wannan muryar, wannan muryar mai taushi daga bayanta, ta juya da sauri daidai sanda yake kokarin tsugunnawa. Yana sanye da farar t-shirt da kuma farin wando, ya kara wani fresh akan yadda ta sanshi a baya.

Bata san lokacin da ta d'aga kanta ba.

"Ina jin dama ta fara yagewa."

"Ko kuma kin cilla ta sama da yawa."

"Cillawa sama ba zai sa ta yage ba."

"Inji wa? Bayan da nauyi a cikinta."

Ta mike tsaye rike da karshen hijabinta.

"Watakila baka san adduwa bane, amma bata da nauyi."

Ya karaso gabanta hannayensa cike da wandanda ya tsinto.

"Na san adduwa mana harda sauran 'yan uwanta, su taura, magarya, d'inya da kuma d'ayan mai kwallo da yawa a ciki."

Ta daga siririyar girarta d'aya.

"Kad'anya...?"

"Right! Kad'anya."

Ta girgiza kanta alamun ta gane sannan ta kalli hannayensa tace.

"Nagode."

Maimakon ya zube mata a ciki, sai ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya zuba a kai, sannan ya kwashe na hijabinta ma sannan ya fara tafiya, ta kalli bayansa kafin ta bishi.

"Sunana Imran, baki taba gaya min naki ba."

Tayi shiru kamar baza ta amsa ba.

"Baka taba tambaya ba."

"Baki taba bani damar tambaya bane."

Ta kalle shi da gefen ido.

"A ina kake ganina?"

"In dai ina garin nan kullum ina ganinki, da safe in zaku tafi makaranta, da rana in zaki je islamiyya, da yamma in kin dawo...ko kuma sau da yawa in kin fito keda k'awarki."

"Ta yaya kasan duk wannan abubuwan?"

"Abubuwan da na sani naki sun fi cikin kirga, d'azu ma kin raka inna asibiti wajen gashin k'ashi."

Daidai sannan suka iso kofar gidansu, ya mika mata handkerchief din ta karba.

"Zaki fada min sunan...?"

Ta sauke gashin idonta kan hannayenta dake rike da adduwar.

"...Don Allah" muryarsa a hankali ta fito.

"Idan ka san duk wadannan abubuwan, sunana ba zai maka wahala ba, sai da safe."

Tana fadin haka ta tura gate d'in ta shige gida. A ranar ko inna ta shaida cewa cikin farin ciki take.

Sai dai kuma me? Ta kwana da wani matsanancin ciwon kai!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

05


(¡î_¡î)

"Inna wai ina cokulan, nifa bangansu akan tray d'in ba."

Nanne ta tambaya daga falo bayan ta dawo daga makarantar boko ta saka kayan islamiyya. Inna ta amsa daga cikin d'aki.

"Toh watakila basu sako ba, don yau ance ba azumi bace akan rabon, iyami ce."

"kuma a rashin hankalinta haka zamu ci abincin da hannu?"

Don a yadda tsarin abincin gidan yake, duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login