Showing 93001 words to 96000 words out of 113985 words
d'in da zai iya rik'e shi!
Amma a yanzu tana fatan cewa k'arfin zai iya rik'e shi har zuwa watannin da abinda ke cikinta zai fito, watannin da bwama ta tabbatar mata ba zai zamo d'aya dana mutane ba, don they grow so fast ba irin halittar d'an adam ba.
Ta tuno yanayin Imran sanda ya shigo gidan bayan tafiyar Bwama, ga mamakinta emotion d'in fuskarsa was weak! zata iya fassara yanayinsa da kamar na d'an karamin yaron a lokacin da yaga mamansa bayan ya b'ata na kwana biyu.
"Come here."
Ya fad'a a hankali yana bud'e hannayensa ba tare da ya bar tahowa wajenta ba, ai kuwa yana rufe baki ta ajiye sassak'en itacen da Bwaman ta bata ta tafi da sauri ta had'e distance d'in dake tsakaninsu, yadda ta cusa kanta cikin jikinsa ya tabbatar masa da kuka take shirin yi.
"Wani abu ya faru ne sweetheart?"
Ya tambaya daga saman kanta. Muryarsa kad'ai a lokacin ta tabbatar mata da dole akwai wani abu daya same shi a lokacin, akwai wani abu da suka tattauna jaamil bayan fitarsa, bata san ko meye ba amma taji zuciyarta ta sake tsinkewa, hawayenta ya k'aru har yana gangarowa kan kuncinta.
Ya jijjiga ta a hankali yana share hawayen da d'aya hannunsa.
"Me ya saki kuka?" Ya tambaya yana d'auke hawayen da yatsunsa masu taushi, amma raunin muryarsa da take ji yasa suka kasa daina fitowa.
"I'm so happy Ayunie, murna nake yi..."
Ta amsa muryarta a karye.
"...Bwama tace we can keep it!"
Ya fad'i abinda ya san zai zama next words d'inta, daga can saman kafad'arsa ta d'aga kai sannan ta k'ara rungume shi.
"Alhmdlilah."
His voice was low again, saboda haka ta d'ago ta kalle shi, a lokacin ne zuciyarta ta girgiza sosai don ganin wani abu da bata tab'a zata ba, wani abu da tunaninta bai kawo mata ba.
TEARS!
*********
HAWAYE.
Wani abu ne da Imran bai san ya d'uminsu yake akan fata ba, wani abu da bai tab'a using ba tun shigowarsa cikin mutane.
Amma a lokacin da yake rungume da Sa'adha bayan tafiyar Bwama, a lokacin yayi experiencing yadda mutane keji sanda suke fitar da kwallar farin ciki da godiya ga Allah kan wata baiwa da yayi musu...
Ya k'ara yarda cewa itace shi a yanzu, itace dukkan wani hope da zaisa ya cigaba da rayuwa mai kyau a gaba, Sa'adha k'addararsa ce da Allah ya shigo da ita don ta tallafe shi a lokacin daya rasa kowanne gata...kamar yadda jaamil ya fad'a ne zuciyarsa ta karye gutsi-gutsi ta dagargaje bayan muryar Naani da ya gama ji, muryar data fallasa dukkan wani zargi da zuciyarsa ta fara d'arsa masa tun lokacin da Naani ta d'auko shi a matsayin wanda ta 'yanta kamar d'anta, amma sai tarin alkhairinta suka ture masa komai a lokacin.
Sai a yanzu yake hasko dukkan abinda ya faru a baya tar! a idanunsa, kamar a da yana cikin wani d'aki ne mai duhu a yanzu kuma aka kunna fitila mai haske yake ganin komai a gabansa.
Ya godewa Allah da yasa komai ya baiyana a yanzu, a yanzun da abubuwa basu zame daga hannunsa ba, a yanzun da yake da Sa'adha... wata mace guda d'aya da ta san dukkan wani secrets d'insa but she still stood beside him, a woman who love and trust him da dukkan zuciyarta, wadda ta bashi hope d'inta 100% ba tare da ta tab'a zarginsa ba, macen data bashi wata irin kulawa da bai tab'a experiencing irinta a wajen wani mahaluki ba, a woman who had every reason d'in da zata guje shi amma bata yi ba, ta baro iyayenta da kowa tayi sacrificing rayuwarta da zata iya gyarawa a gaba and choose to stand by him!
Ya rantse da ubangijinsa zai so Sa'adha ya kula da ita, ya kare ta da dukkan wani iyawarsa a duniyar nan, saboda ya fahimci cewa iya abinda zai iya yi mata kawai kenan!
***
A cikin mota lokacin da yaje d'aukarta bayan ya shiga gidan ya karb'o godiya kala-kala a wajen kowa, Nanne tayi ajiyar zuciya mai nauyi, ya mik'o hannunsa da baya kan sitiyari yayi squeezing nata a hankali.
"Me ya faru? how did it went?"
"Ba abinda ya faru Ulfat, Inna ta fahimta tun kafin ma in bata slightest hint...kuma kowa da yaji yayi farin ciki komai ya tafi daidai."
Ya gyad'a kansa ba tare da ya kalleta ba idonsa na kan titi.
"Komai zai tafi daidai insha Allah Noory."
"Insha Allah." Itama ta amsa.
Ta san cewa ya fahimci akwai 'yar damuwa a tare da ita amma bai tambaya ba, and she was glad that ya barta tayi keeping abun a cikin zuciyarta, in ba haka ba bata san ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta a tsinke take na ganin irin farin cikin da inna ke ciki game da Babynta ba alhalin ita tana b'oye mata wani babban abu da ya kamata ace ta sani, ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta ta dagargaje kamar irin yadda tasa tayi ranar da aka d'aura musu aure, ranar da yaga irin tarin al'ummar daya d'ora akan fake labarinsa.
Maimakon ya kaita gida a lokacin sai ya canja hanya zuwa wani k'aton mall dake d'auke da wajaje da yawa a cikinsa, watakila ya fahimci damuwar da take ciki ne a lokacin, ya fahimci yanayinta ya canja kamar yadda itama take gane komai nasa da duk wani slightest bit na motsinsa, cikin sa'a kuma sai frozen vanilla yoghurt din da suka siya ya taimaka wajen lifting spirit d'inta, taji sanyinsa har yana barin wani danshi a can k'asan zuciyarta.
Kusan minti talatin suna zaune a d'aya daga cikin kujerun park d'in wajen ba tare da sunyi magana ba, shiru da sanyin bishiyun wajen ya saukar da wani peace of mind a zuciyar kowannensu.
Sai da Nanne ta d'aga robar yoghurt d'inta taji ya k'are tas! sannan ta yar da ita a gefe, ta juya ta kalle shi sannan tace.
"Ayunie we need to talk... akwai abinda kuka tattauna da jaamil lokacin da Bwama tazo, You need to tell me, ina son inji me ya faru."
Imran yayi squeezing robar chocolate ice-cream d'in da ya gama sha shima, he'd seen this coming...ya riga ya san Sa'adha ta fahimci damuwar da yake ciki tun wancan lokacin kuma ya dad'e yana jiran zuwan tambayarta dama, tambayar da ya riga ya shirya amsarta daki bayan daki.
Sai dai kafin yayi magana, idonsa ya hango masa text d'in da ya turawa jaamil a d'azu.
Komai zai cigaba da tafiya kamar yadda muka tsara jaamil, ba abinda zai canja ko ya tsaya, zanje in karbo dutsen Nil....zan kare Sa'adha dashi kuma zan d'auki fansa akan Naani dashi!
¡ñ©n¡ñ
Revenge guys!
What do you think?
****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
55
This page is yours! My amarya freind..It's your day SHAMSIYYA ADO MA'AJI...Happy Birthday dear! ??
Chill Out Mrs. Abdullahi...we love you!
(¡î_¡î)
"Naani ce ta dawo kuma ta san da dukkan abinda ya faru amma bata san da zancen cikinki ba...so mun tattauna yadda zamu b'oye mata sanin hakan ne har zuwa lokacin da zaki haihu, saboda in har ta sani ba zata yarda ba Sa'adha, ba zata yarda muyi abinda baya cikin tsarinta ba."
Imran ya fad'i k'aryar da zata lullub'e ainihin gaskiyar da yayi niyyar gaya mata a da, ainihin gaskiyar da zata sa ya daina barinta a duhu game da al'amarin Naani, don a yanzu yana ganin ta cancanci ta san ko wane gutsiren al'amari game dashi, he can't hide anything fom her! amma sai kalaman da Bwama ta fad'a masa suka hana shi furta mata ainhin gaskiyar...
"Kar ka tab'a bari ranta ya b'aci har ta shiga damuwa yarima, dole ne ka dinga b'oye duk wani abu da kasan zai takura zuciyarta...oum veri nah kour menku rajern! (stress will only make her more ill.) irtou nah kalabg daer waqatu harvil jourda gnawyer bayadda ferl...(Zuciyarta da duk wani k'arfin jikinta sun ta'allak'a ne yanzu akan abu guda, she can't be distracted.) hazar fumerbe ferl don sartu nah, gzarde ser tah ngam! (You have to he composed, you can't make it harder for her.)
Wad'annan kalaman su suka hana shi fad'a mata ainihin yadda zuciyarsa ta dagargaje da kuma irin ciwon da take yi bayan yaji kalaman Naani daga cikin Habler nan, Amma kwakwalwar Sa'adha was so sharp than tunaninsa.
Ta tsuke idanunta kad'an sannan tace.
"Ayunie ka tabbata ba wani abu da Naanin take shiryawa da zai cutar dani ko kai?"
A lokacin data fad'i hakan wani abu a k'irjinsa ya tarwatse sannnan harshensa ya k'ulle... ta ya zai fara gaya mata cewa he just found out cewa Naani bata tab'a nufinsa da alkhairi ba, ta d'auko shine kawai don ta gyara rayuwarta daga k'arshe shi kuma ta tsaida tasa...
Daga yanayin fuskarsa Nanne ta fahimci cewa ba zai bata amsa ba, saboda haka ta kwantar da kanta a kafad'arsa sannan ta zuro hannunta ta cikin nasa.
"Koma meye Ulfat, na san I'm safe with you!"
Matsalar kenan! gabad'aya tunaninta akansa were all backwards... bata tab'a gane hatsarin da rayuwarta ke shiga akansa, a koyaushe tana bashi wata yarda ne da shi bai cancanta ya samu daga gare ta ba, maimakon guduwa tana k'ara cusa kanta ne wajen da yake da hatsari...watakila kuma laifinsa ne da tun farko bai nuna mata hakan ba.
Amma ta yaya zai kare ta daga kansa alhalin dukkan zuciyoyinsu basa son hakan?
Sai ya jingina kansa shima a saman nata a hankali, idanunsu na kallon k'ayatattun lilukan park d'in dake can gabansu!
****
BAYAN WATA UKU.
"Kina da popo pos?" Hidaya ta tambaya zaune daga kujerar island na kitchen d'in.
Nanne ta k'ara d'auraye bakinta daga d'an guntun aman da tayi a sink sannan ta juyo ta kalleta da murmushi, wani murmushi da ya fad'a can cikin ramin kumatunta kamar yadda idanunta da suka d'ashe suka yi zurfi a can cikin lungunsu.
A cikin watanni uku kawai wanda ya san Nanne a baya zai yi mutuqar wuya ya gane siffarta a yanzu, wata siffa da a kullum innarta ke kira da kwarangwal... don d'an karamin jikinta ya yamushe sosai cikin abinda za'a iya kira fata da k'ashi kawai, fuskarta ta sirance sosai ta yadda k'ashin gefen hab'arta ya fito k'arara yana haska idanunta da suka d'ashe tas!
Gashin kanta mai cika a yanzu duk ya yamushe ya kuma wani d'an yalolo sai tsawo ne kawai dashi...sai dai duk wannan canjin babu shi a cikin zuciyarta... zuciyarta da take b'ul-b'ul cikin k'oshin lafiya kuma cike da murnar sanin Babynta yana raye cikin k'oshin lafiya, don a kullum in banda k'ara girma ba abinda yake yi, girman dake tada hankalin 'yan uwanta ganin yadda ita take k'arewa kullum a tsaye.
Sai dai tunda har bata jin wani ciwo ko kad'an sai inna ta kashe bakin kowa da cewar ko wacce mace da irin yanayin cikinta, ita nata laulayin a haka yazo mata... amma duk da hakan tana ganin tashin hankali kwance a k'asan idanun innar ko yaushe taje gida, tashin hankalin da duk girmansa bai kai na Imran ba, shi da a kullum suke kwana da tashi tare, ya san cewa bata cikin wani ciwo in banda rashin tak'amaiman abincin da bata iya ci...duk kuwa da duk irin k'ok'arin da Bwama ke zuwa bata na magungunansu kala-kala amma bata iya cin wani abun kirki, abinda ke bata mamaki kenan na ganin yadda kuma babyn ke ta girma a cikinta.
Babyn da har yanzu bata san ya yake ba, don taje asibiti sau d'aya, a wata rana da ya zama ya zama silar fad'uwar wani jigon a rayuwarta, taje gida ta had'u da ya Ahmad sunzo shida matarsa da 'ya'yansa, tunda cikinta ya fara baiyana bata ganshi ba sai a wannan ranar...inda yayi mamaki ganin yadda duk ta k'are saboda haka yace zai dubata don bai tab'a ganin ciki irin nata ba, inna kuma ta bada goyon bayanta da cewar itama a lokacin taga ramar tata ta fara yawa, Ba irin hanyar da bata bi ba don ta zille masa amma sai da inna tasa ya d'auketa ya tafi da ita can asibitinsa. Inda wani al'amari ya faru daya jijjiga tunaninsa, gabad'aya injinan ultrasound na asibitin suka k'i aiki a jikin Nanne, ba abinda suke nunawa sai tarin wasu alamomi da suke fad'in...
The membrane is too hard!
Wato fatar dake lullub'e da babyn tayi karfin da ultrasound d'in ba zai iya ratsawa ya haska cikinta ba. A lokacin ne ya karb'i wayarta ya kira Imran da cewar yazo ya same su a asibitin, wanda kafin zuwansa ba irin magiyar da bata yi masa ba akan ya fad'a mata abinda ya gani amma yayi shiru kawai yana kallon hawayen da take yi, hawayen da ya kasa tantance na tsoro ne ko kuma na son kare abinda take b'oye musu.
Lokacin da Imran ya k'araso cikin asibitin a d'an k'ank'anin time, lokacin ya Ahmad ya bud'e baki ya fad'i abinda Nanne bata tab'a zata ba.
"Imran ka san cewa abinda ke cikin matarka ba mutum bane?"
Zata iya tuna yadda fuskar Ayuninta take hard a lokacin, wani emotion da ya tabbatar mata cewa abinda take tsoro ya faru, baiyi magana ba ko sau d'aya har sanda ya Ahmad d'in ya sake tambayarsa.
"You need to tell me, wane asibitin kuke zuwa suna yaudararku tun farkon samun cikin nata?"
"Ya Ahmad dan Allah...."
"Shshshsh...." yayi saurin katse ta idonsa cike da b'acin rai da kuma wani abu kamar tashin hankali.
"Da mijinki nake magana, kar ki sake kisa min baki.!"
Daga yanayin idanunsa da muryarsa ta riga ta san what he's capable of a lokacin, ta san halinsa sarai, ta san babu abinda zai hana shi tunkarar Baffa a ranar da zancen, saboda haka ta juya wajen Imran dake zaune kamar gunkin da aka sassak'a ta rik'o hannunsa sannan ta kira sunansa... sunansa direct don ya san cewa abinda zata gaya masa da gaske take, hakan kuwa yasa ya juyo da kansa ya kalle ta, idanunsa were so dark! alamun feelings kala-kala a tare dashi amma bata kula da wannan sosai ba, abinda zata fad'a a lokacin shine priority... a hankali muryarta ta fito ta cikin fuskarta dake shab'e-shab'e da hawaye.
"Wipe his memory please!"
"What? Me kika ce?" Muryar ya Ahmad tayi ihu daga gefensu.
"Ka goge tunaninsa Ayunie dan Allah, in ba haka ba komai zai ruguje mana ne...za'a illata Babynmu." Ta sake fad'a idanunta akan Imran.
"Nanne kina da hankali kuwa? me kike cewa? me ya same ki? me zai yi..."
He trailed of cike da tambayoyi kala-kala, amma bata juya ta kalle shi ba, idanunta na kan imran da take rok'o da dukkan wani senses na jikinta akan ya taimaka yayi hakan, daga yanayin idanunsa kad'ai ta tabbatar baya son aikata abinda ta fad'a amma kuma ba zai iya mata musu ba, don shi kansa ya san basu da wata mafitar data wuce hakan, ya Ahmad ya riga ya san wani b'ari na sirrinsu da ba zai tab'a rufuwa ba saboda haka ya gyad'a kansa a hankali sannan ya mik'e ya juya wajen ya Ahmad dake k'ok'arin lalubo wayarsa a lokacin.
Nanne ta juyar da kanta zuwa kallon k'ofa hawaye na bin idonta daidai sanda Imran ya tsaida duk wani abu dake motsi a cikin office d'in cak! har kuwa da nata tunanin.... Sannan irin abinda ya faru ga masu hoton nan ya kasance ga ya Ahmad, memory d'in abinda ya faru tas! ya d'auke daga cikin kwakwalwarsa.
Daga wannan ranar kuma suka tattara komai nasu suka bar cikin garin katsina zuwa Abuja, Nanne ta bar cikin mahaifarta don kare abinda take ganin shine rayuwarta a yanzu, kuma hakan yazo musu da sauqi tunda a yanzu Imran ya riga ya bar aiki a kamfaninsu, abinda ya kaishi ya riga ya k'are kuma ba zai tab'a iya cigaba da zama ba tun bayan abinda ya faru tsakaninsa da Naani.
Wani abu da ya zamo.....
"Baki da popo pos d'in?" Muryar 'yar yarinyar d'azu ta janyo kwakwalwar Nanne daga tunanin data tafi, ta k'ifta idonta da sauri sannan ta kalleta sosai, tayi tagumi da hannayenta akan island table d'in kamar sanda take tunanin ita kuma ta tsaya ne tana kallonta. Sai data d'anyi gajeren tunani sannan ta gane me yarinyar ke nufi.
"Coco pops kike so?"
Ta d'aga kanta da sauri.
"Eh nawa ya k'are kuma Daddy bai shiyo ba."
Yadda tayi maganar tana turo d'an plumpy lips d'inta ya burge Nanne ta shafa kumatunta ta hannunta d'aya sannan tace.
"Karki damu hidaya zaki sha coco pops yanzun nan, amma zaki yi game kafin a kawo?"
"Yey! kina da candy crush?" Ta tambaya with pleading eyes.
"Oww...bani da candy crush amna akwai garden scapes, yana da dad'i."
"I'm in!"
Ta fad'a da sauri tana d'aga hannayenta, Nanne tayi dariya ta koma falo ta d'auko mata tablet d'in Imran, ta nuna mata yadda zata yi gane d'in sannan ta d'auko wayarta ta kira shi, zuciyarta na fatan ya amsa kafin ta tsinke, don wajen sabon aikinsa na yanzu, aiki yake sosai fiye da wancan tunda suka gano irin kwarewarsa a harkar advertisiment d'in nasu, abinda take gani ya taimaka wajen lifting spirit d'insa da bashi kwarin gwiwa wajen manta abinda ya faru tsakaninsa da Naani.
Wani abu da ya zamo....
"Hello! sweatheart ta tashi?"
Muryarsa ta silalo ta cikin speaker wayar, tayi murmushi kad'an.
"Na tashi Ulfat, kuma gidan ba dad'i, na saba da kai a cikinsa, kana tunanin weekend d'in nan ya b'ata ni?"
Taji sautin murmushinsa kafin yace.
"Ina tunanin ni na b'ata ki baby."
Ta ciji gefen lebb'enta tana danna hannunta cikin shinkafar data d'ebo a wani bowl zata wanke.
"Tell me how much you miss me Noory...ina nan inata ganin fuskarki akan screen d'ina, I kept checking time kowanne minute a wayana don inga fuskarki, (Picture d'inta was his wallpaper) And beleive me it's getting out of hand don na kasa ko gama project d'aya.
So tell me naki storyn."
Ya Allah! wai yaushe ne zata saba da irin wannan kalaman na Imran, maimakon ta biye masa sai tace.
"Dan Allah zamu samu Coco pops in zaka dawo?"
"Coco pops?"
Tana iya jiyo mamaki a cikin muryarsa.
"Are we talking Babies?"
Murmushinta ya k'aru, ta sake nutsar da hannunta cikin shinkafar.
"Ni dai in za'a samu dan Allah ka taho dashi."
"Sure Babe kar ki damu... your wish my command."
Ta gyad'a kanta a hankali kamar yana ganinta sannan tace. "Come back soon!"
"I will habibty."
Tana ajiye wayar ta koma kan girkin da take yi, tun dawowarsu gidan bata tab'a d'ora wani abun arzik'i ba, kullum girkinsu 'yan kame-kame ne kawai, saboda haka a ranar tayi niyyar zama ta yiwa Imran girki sosai tunda ita ba