Showing 84001 words to 87000 words out of 113985 words
wani azababben barci da kusan kullum bata san lokaci da kuma inda yake d'aukarta ba, wani lokacin suna cikin cin abinci, wani lokacin suna zaune a falo, wani lokacin ma a cikin toilet kafin ta gama brush, sai dai ta farka da safe ta ganta a d'aki. Sau da yawa zaice mata ta huta kar su fita, amma tsananin d'okin ganin sababbin abubuwa shi zaisa tayi ta rok'onsa da magiya har sai sun shirya sun fita.
A yanzu bata da matsalar abinci don Menu guda suka kaiwa can wajen dake kawo musu abinci na irin simple-simple abubuwan da suka san zasu iya yi wanda su kuma zasu iya ci, don haka a kullum warmers d'insu cike suke da cima kala-kala, wani lokacin ma har sai an koma da wasu.
*******
Wajen k'arfe uku na rana, dawowarsu kenan daga waje, bayan sun bawa cleaning crew d'in wajen awa biyu na gyaran cikin cabin d'in nasu.
Nanne ta shiga wanka ta wanke fatarta tas! data k'ara wani sulb'i da haske a cikin kwanakin, bruises d'inta sunyi sauqi a lokacin sai dai basu tafi duka ba, har a lokacin akwai alamunsu a wani wajen, sunyi shade d'in pink kad'an.
Bayan ta fito ta saka wata 'yar k'aramar riga mai kyau dark pink da d'an short da bai kai gwiwa ba, a yanzu ta riga ta saba da duka kayan nan, kullum su take saw kala-kala har gani take da ta taho da dogwayen rigunanta ba lallai ta iya sasu kullum ba, tunda wanda Imran ya bar mata ma amfaninsu in zasu fita ne kawai, amna duk inda suka je tattare abinta take tasha iska da dogon wandon da take sawa a ciki tunda ba wasu mutane a wajen.
Tayi k'ok'arin b'oye murmushinta sanda idanun Imran suka zare bayan ta fito daga toilet d'in, amma cikin wucewar second d'aya yayi k'ok'arin controlling fuskarsa sannan yayi gyaran murya kad'an.
"You look beautiful Noory, kinyi kyau da yawa, kamar kullum!"
Ya fad'i abinda take shirin tambaya.
"Awwn..." Ta dunkule hannayenta a k'irji sannan ta d'an turo bakinta tana kifta ido.
"Thank you Ayunie." Ta fad'a sanda ta hau kan gadon da yake kwance yana karanta wata bussines magazine, ya mik'o hannunsa ya jawo ta jikinsa tayi hamma kad'an sannan ta d'ora kanta a kirjinsa.
"Yaushe zamu koma gida?"
"Har kin gaji? ke da kika ce mu zauna anan har abada."
Tana murza idonta da hannu d'aya tace.
"Wajen da dad'i Ulfat, amma ina missing su Inna."
"Kullum fa sai kunyi waya."
Ta turo bakinta kad'an. "Yau bamu yi ba."
Sai ya mik'a hannunsa gefe ya jawo wayarsa yana fad'in bari a kira su toh, ta rik'o hannun nasa da sauri.
"A'ah ba yanzu ba sai anjima, bacci nake ji."
"Bamu ci abinci bafa...I'm afraid bana feeding dinki sosai."
"You're trying, ka bari sai na tashi sai muci, na gaji yanzu."
Ya ajiye magazine d'in hannunsa ya sake kwantar da kanta a jikinsa.
"Ofcouse you're tired, Sleep, Love."
Muryarsa can k'asa ya fara mata humming wani lullaby a hankali yana shafa bayanta.
"Ban san me yasa nake yawan baccin nan ba Ayunie..." Ta fad'a a hankali idonta na shirin rufewa.
"...I hope hakan bashi da alaqa da kasancewarka ba mutum ba."
Yayi murmushi kad'an sannan ya cigaba da humming d'in.
"Tunda nake ban tab'a irin wannan baccin mai yawa ba, kuma akai-akai haka."
Ta sake fad'a muryarta so low. Humming d'in nasa ya tsaya a lokaci d'aya.
"Nima I was wondering, baccin naki yaso yayi yawa habibty, ba don minshirin da kike ba, har zato nake ko kin shiga Coma ne."
Da sauri idanunta suka bud'e, ta d'ago ta kalle shi.
"Wallahi bana minshari."
Ya d'age girarsa duka biyun.
"Har da rantsewa? ni da nake tare dake kullum? To ranar da muka zo nan da kika ji iska sosai, a firgice na farka na zata wasu ne suka tayar da inji."
Wani haushi ya cika mata wuya, bata san sanda ta wawuro pillon gefenta ba ta shiga maka masa, yana ta kyalkyaka dariya yana fad'in tayi hak'uri wasa yake yi!
****
BAYAN SATI BIYU.
"I'm sorry!" Jaamil ya sake fad'a karo na biyu yana kallon yadda tekun gabansu ke tambal-tambal cikin wani salo mai ban sha'awa.
Ganin Imran bashi da niyyar amsawa yasa ya juyo gefe ya kalle shi, suna zaune a wata kujera dake facing bakin tekun.
"Yarima." Ya kira sunan sa a hankali, maimakon ya amsa sai ya gyara zamansa ba tare da ya kalle shi ba yace.
"Ta yaya ka san muna nan?"
"Saboda na sanka, na san duk wani possibilities d'inka."
"Amma ka ture wannan sanin kake son biyewa plan d'in Naani? kake kokarin yin abinda ka san zai cuce ni?"
"Karo na uku kenan da nake maka bayanin cewa daga ni har Naani bamu yi wannan zancen don cutar da kai ba sai don kawai abinda muka tsara tun farko ya tafi daidai sannan a lokacin baka tsaya kaji ra'ayina ba yarima, ina fitowa ka shak'e ni da tambayoyinka."
Imran yayi ajiyar zuciya sannan yace.
"Naani ta sani?"
"I never told her, ta cigaba da tsarinta na yadda duk lokacin da ka kawo yarinyar zata raba ruhin da jikinta, a kwanakin baya ma ta kirani da saqon cewa in gaya maka zata nemeka nan gaba, saboda da farko ta gaya maka zata kira ka ne bayan sati d'aya."
"Ba zan taba kawo ta ba." Muryarsa ta fito kai tsaye.
"Na sani, amma ta yaya zaka iya karb'ar dutsen in lokaci yayi? tunda ka san b'arinka d'aya ba zai taba iyawa ba."
"I'm figuring a way out Jaamil, ban san wace hanya zan samo ba amma definetly zan samo hanyar da zan kare Sa'adha, I will, surely!"
Jaamil ya juyo ya kalle shi kamar mai karantar wani abun sannan ya koma da kallonsa kan tekun.
"Sooo..." yaja maganar yana kallon yatsunsa.
"Ta yarda dani." Imran ya fad'i amsar tambayar da bai furta da dogon kalamai ba.
"Na gaya mata komai kuma ta yarda dani jaamil, tace it doesnt matter ko ni meye, zuciyarta ta riga ta amince kuma zata zauna dani."
Jaamil ya d'aga kansa kafin yace.
"Kuma ka fad'a mata abinda Naani tace?"
"Ba zan iya fad'a mata wannan ba, ba zan iya karya zuciyarta bayan yardar data riga ta bani ba, saboda haka na gaya mata Naani bata dawo ba, kuma kota dawo zan san hanyar da zan kare ta."
"Insha Allah, zamu samo mafita yarima."
Sai a sannan Imran ya kalle shi cike da mamaki. shima ya juyo yayi focusing sosai yana kallonsa.
"Tun tasowarmu tare muke komai yarima, bamu tab'a banbanta wani abu namu ba, sannan tare muka fara wannan abin, tare Naani ta turo mu yin aikin nan, tare muka samo mafitar waccan matsalar, me yasa kake tunanin don wani abu ya faru yanzu hakan zai canja?"
Imran ya had'iye yawu kafin ya maida kallonsa kan tekun, a hankali muryarsa ta fito.
"Thank you."
Jaamil ya juyar da kansa shima sannan suka yi shiru. Zuwa can yace.
"And I like your wife, tana da kirki."
Imran yaji murmushin jin dad'i ya cika bakinsa, ya kasa daurewa har saida hakan ya fito.
Daga nan suka shiga tattaunawa akan yadda zasu b'ullowa lamarin ba tare da Naani ta sani ba, sun dad'e sosai kafin su fitar da wani kwakwaran plan wanda babu makawa shi zai zame musu mafita. Kafin su rabu hirarsu ta dawo daidai kamar ba abinda ya tab'a had'a su, dama haka yake kowannensu baya iya fushi da d'an'uwansa.
***
Mafarkin ya fara ne a wannan wajen, wannan filin mai tarin bishiyun da ta san cewa abinda tazo nema yana cikinsu, sai dai a wannan karon babu muryoyin su inna dake kiran sunanta daga can nesa.
Sannan kamar wancan lokacin Imran ya fito daga cikin bishiyun nan yana kallonta da lumsassun idanunsa, kamar koyaushe yayi wani irin kyau sanye da light kaya, fuskarsa ta haska, sannan kyakkyawan murmushinsa ya kwanta sosai a gefen fuskarsa, sai da ta shagala da kallonsa sannan ya d'ago yatsansa guda d'aya yayi mata alamun ta biyo shi sannan ya juya ya koma cikin bishiyun.
Taku daya kawai ya shigar da ita cikin duhun bishiyun, amma sai wajen ya zama sab'anin tunaninta kamar wancan karon, a maimakon duhu wajen mai haske ne da kuma kyau, korayen ciyayi da fulawowi sun baje a koina, ga wani dutse daga can gefe yana zub da ruwa.
Taji wani ya rungumeta ta baya, hannayensa sun zagaye k'ugunta sannan ya d'ora hab'arsa a daidai lungun wuyanta, ko bata juya ba ta san Imran ne kuma zuciyarta ta riga ta nutsu dashi, saboda haka ta cigaba da tsaiwa ba tare da ta juya ba tana jin d'umin jikinsa akan fatarta da kuma yadda numfashinsa ke busawa a k'asan kunnenta.
A lokacin ne abin ya faru, taji an caka mata wani abu mai tsini a wuyanta, abin ya huda tun daga farkon wuyanta ya fito ta d'aya gefen.
Numfashinta ya tsaya cak, sannan jini ya shiga gangarowa kan fatarta, tayi k'asa ta fad'i da baya sannan zafi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta, taji ruhinta na barin jikinta a hankali sannan idonta na shirin rufewa.
Amma kafin komai ya d'auke mata, fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye kamar lokacin baya akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sai dai wannan karon a gefensa akwai wani d'an karamin yaro fari tas! mai mutuk'ar kyau dake ta b'angala mata dariya, a hankali idonta ya dawo kan hannun Imran wanda ke ta faman d'igar da jini!
Ta mik'e da wani irin sauri lokacin data farka daga baccin. D'akin yayi duhu sakamakon yamma data yi sosai kuma an saki curtains d'in gabad'aya harda na jikin glass wall din an zuge shi, akwai sanyi air condition kad'an, amma taji gumi na gangarowa ta cikin gashinta.
Ta kai hannunta jikin bango ta kunna fitila, haske ya dallare koina, hasken daya nuna mata cewar Imran baya d'akin, a sannan ne kuma Idonta kan tarin takardun dake baje kusan koina a d'akin.
Kan drawars, gado, mudubi, da duk wani abu da yake da space a d'akin, ta mik'a hannu ta d'auko guda da'aya dake gefenta akan side-drawer.
I'm hoping ba zaki karanta takardar nan ba saboda ba dad'ewa zanyi ba, amma in har kina karantawa yanzu, wani abu ya rik'e ni kenan...but I 'll be back very soon, kiyi sallah kici abinci sannan ki koma baccinki kinjii...? Zaki ganni lokacin da kika sake tashi insha Allah. I love you...
...like crazy!
"I love you too."
Ta fad'a a hankali sannan ta maida ninkin paper ta rufe, ta mik'e ta tattaro dukkan sauran na d'akin da abu d'aya suke fad'a ta zuba su a handbag d'inta. Ta shiga toilet tayi alwala tayi sallar La'asar data nemi ta kub'uce mata sannan ta sake wanka, kamar wancan karon bata sa mafarkin nan a cikin kanta ba, abu d'aya ne kawai ya tsaya mata a rai...wannan kyakkyawan yaron dake tsaye a kusa da Imran yana b'angala mata dariya.
Bayan ta shirya ta fito don samun abinda zata ci kamar yadda Imran yace, ba wai yunwa take ji sosai ba amma tunda ya fad'a dole ne taci, tana tafe tana kunna duk switches d'in data san shi ya kashe da zai fita.
Ta k'ara jin gidan ya mata shiru fye da koyaushe sannan ta dinga ganin koina wani iri. Different somehow.
A kan stool d'in jikin counter ta zauna tana ta kallon abincin dake cikin warmers d'in, haka kurum take jin bakinta ba dad'i saboda haka tayi tagumi tana tunanin me zata ci. Da kyar ta tsaida zuciyarta ta janyo wani bowl dake cike da potato soup yasha yankan vegetables round kala-kala.
Yawu ya taru a bakinta tun kafin ma ta fara ci saboda haka ta ajiye cokalin data d'auko tasa hannunta ta fara, tana ci tana lashe hannu kamar wadda aka sanmata. Sai dai bata kai ga ko ci da yawa ba ta fara rage taunarta a hankali... Me ya same shi? wani irin k'amshi yake, ko dai ya fara lalacewa ne? Ta kai hancinta ta shinshina, ai kuwa wani irin k'amshi ne ko wari ya daki hancinta, bata san sanda tayi wulli dashi ba ta matsa da sauri jikin sink ta shiga kwara amai.
Sai da ta fito da duk wanda taci sannan ya tsaya ta d'auraye bakinta a hankali ta had'a har da fuskarta, tana d'agowa taji kuma kamar jiri ya kamaya, gidan ya fara juya mata saboda haka ta lalubi kujera ta dunk'ule akai, a can d'aya side din kujerar akwai wani blanket, amma kafin ta iya d'auko shi ta lullub'a wani sabon baccin yayi awon gaba da ita.
Sanda ta sake farkawa duhu yayi sosai, kuma Imran na zaune a gabanta, gaban kujerar da take kai.
"I'm sorry, ya fad'a yana shafa fuskarta a hankali.
"I'm sorry na barki ke kad'ai, wani uzurin ne..."
Bata ji k'arshen zancensa ba ta ture hannunsa da sauri sannan ta tashi da gudu tayi d'aki, ta banka k'ofar toilet din ta nufi sink ta shiga kwara wani sabon aman kamar zai had'o da hanjin cikinta.
"Noory me ya faru? me ya same ki?"
He was there in an instant! ya rik'o ta yana janye gashinta daga fuskarta. sai da numfashinta ya dawo daidai, sannan ta kalle shi, idanunta sun ciko da kwalla tace.
"You don't need to see this, dan Allah kaje, amai fa nake yi."
Bai ko kula ta ba ya mik'ar da ita tsaye, ya bud'e fanfon aman ya wuce sannan ya d'auraye mata baki suka fita.
"Abinci naci ya fara lallacewa."
Ta fad'a sanda ya zaunar da ita akan gadon.
"Wane iri ne?"
"Yana nan akan counter."
Ya mik'e da sauri ya koma falon sai ta maida kanta kan pillow ta sake dulunkunewa. Bayan kamar minti ashirin ya dawo d'akin, ya tsugunna a gabanta ya d'ora hannunsa akan goshinta.
"Ya kike ji yanzu?"
Ta daure tayi murmushi tana kallonsa.
"Lafiya k'alau."
"Zan kira likita yanzu ya duba ki."
Da sauri tace.
"Amai ne fa kawai Ayunie, ba wai ciwo bane I'm fine, dan Allah kar ka kira su."
"Allura kike tsoro?"
"Harda magani ma bana so."
Yayi shiru yana kallonta, ba yadda ya iya saboda haka yace.
"Nasa an fitar da duk abincin an kawo sababbi, ki taso muje kici tunda ba komai a cikinki yanzu."
Da kyar ta samu taci meatpie guda uku sanda ya d'auke ta ya maida ita falon, yana bata a baki yana tab'a jikinta da k'ara tambayar yadda take ji, tunda tana bashi amsar cewa ba komai, har in ya tambayeta sai ta lankwasar da muryarta ta fad'o wani k'aton ciwon, hakan ke sawa su kyalkyale da dariya.
Bayan sunyi sallar isha, ya kunna t.v suna kallon wani funny American film na wasu teenagers, don shelf guda ne cike da movies kala-kala harda cartoons, tana zaton ma wajen yafi wani gidan saida CD's d'in yawansu. Tun ita kad'ai ke dariyar yana karanta bussines magazine d'insa har dai ya ajiye shima ya biye mata.
Kafin su kwanta, she was so happy da har ta manta da jirin da take d'anji.
Sai dai k'arfe biyun dare, ta tashi da wani irin ciwon cikin da yasa ta amayar da dukka meatpie d'in nan.
"Sa'adha...."
Imran ya fad'a yana kwankwasa k'ofar toilet d'in don ta k'ulle wannan karon.
"Open the door, ki bud'e min."
Bata ko motsa ba, idonta na kan cikin toilet sink d'in wanda ya rine jawur da jini, aman nata ya had'o da wani rin jini mai yawa da har dunk'ulewa yake, kamar wani abu ya fashe a cikin ta, ta mike da sauri tayi floushing, da ragowarsa har a lokacin saboda haka ta sake dannawa sanda taji hannun Imran ya rik'o ta.
Ta juya da sauri ta kalle shi, sannan k'ofar wadda handle d'inta yake a karye.
"I'm calling a doctor now."
"Ayunie amai ne fa..."
"I don't care..." ya katseta.
"...Baki da lafiya shine kad'ai abinda na sani."
Ta d'ora kanta akan k'irjinsa shi kuma yasa hannunsa ya rungume ta.
"Aman da nayi harda jini." She finally admit a hankali. taji yadda k'arar bugun zuciyarsa ya canja a lokaci d'aya sannan rik'on da yayi mata ya d'an saki, daga can yayi ajiyar zuciya sannan yace.
"Abin yayi yawa Noory, dole ne muga likita...yawan bacci, tashin zuciya amai kuma har da..."
Sai dai kafin ya k'arasa kwakwalwar Nanne ta ta tsinci wani abin, ta d'ago kanta da sauri tana kallon fuskarsa, kamar me shirin d'auko wani abu nata daya fad'i.
"Me ya faru? Tunanin me kike?"
Bata ce komai ba ta cigaba da kallonsa blankly, fatar goshinta na tattarewa alamun tunani. Ya d'ora hannunsa akan goshinta.
"What's wrong?"
Maimakon ta amsa masa sai ta sake shi da sauri ta fita daga toilet d'in, ta kunna fitilar d'akin haske ya dallare koina, a jikin mudubi ta lalubo wayarta, hannayenta na rawa ta shiga
k'ok'arin bud'ewa.
"Sa'adha, I'm loosing my mind...me yake faruwa ne?" Muryarsa ta biyo bayanta.
Tana bud'e application d'in da take nema, wayar ta sub'uce daga hannunta ta daki tiles din k'asa. Ya k'araso gabanta ya rik'e hannayenta da suke rawa.
"Sa'adha...."
Kafin ya k'arasa muryarta ma dake rawa tace.
"Yau wane Date?"
"25th...gida kike son tafiya?"
Ta girgiza kanta da sauri sannan ta had'iye wani k'aton abu a makogwaronta.
"Period d'ina yayi latti da kwana bakwai!"
¡ñ©n¡ñ
Zan muku alqawari saura couple of chapters mu rufe labarin nan!??
*****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
52
(¡î_¡î)
"Is it possible? zai iya yiwuwa?"
Abinda Nanne ta iya fahimta a cikin kalaman Imran dake waya kenan kawai, wayar da yayi kusan awa d'aya yana yi da wani irin yaren da bata ganewa, bayan wannan hausar da yayi ta farko, sunanta kawai ta iya tsinta wanda ya had'o tare da gwamutsin kalmomin da bata san ma'anarsu ba.
Mamaki take na shi dawa yake waya haka? me yake son tabbatarwa bayan likitan da ya kira yazo ya tabbatar musu cewa da gaske ne tana da ciki.
CIKI.
Ciki wai...
Ta rufe idonta a hankali, tunda take a rayuwarta tunaninta bai tab'a hango mata kanta a matsayin UWA ba, ta san dai cewa tunanin 'ya'yan da zata iya haifa da Imran yazo cikin kanta, amma d'aukar cikin da haihuwarsa wani abu ne da babu shi a register kwakwalwarta.
Ta kai hannu ta shafa saman cikin nata a hankali, a yanzu halitta ce a jikinsa, halittar da take combination dinta ita da imran, halittar da zai girma zuwa wani lokacin ya fito a matsayin d'an baby, irin babies d'in da take hangowa a hannun mutane, itama zata samu nata...nata na kanta da zai zama cikin ikonta sannan nata itada Imran!
A hankali kwakwalwarta ta shiga imagining yadda kammanin babyn zai kasance, ko mace ce ko namiji zata fi so ya d'auko kammanin Imran sosai, yadda duk sanda ta kalle shi zata ga abinda zuciyarta ke k'auna guda biyu awaje d'aya, don duniyarta ta canja daga lokacin da likitan nan ya furta cewa taba d'auke da cikin Imran, taji kamar zuciyarta ta k'ara girma ne ta