Showing 33001 words to 36000 words out of 113985 words
ba abinda suka yi miki?"
"Ba abinda suka min, ta yaya ka san ina can? Me ya kaika wajen?"
"Na wuce ne ta hanyar sai na hango kamar ke, shine na dawo in tabbatar."
Idanunta suka hasko mata wannan motar da ta wuce ta gabanta. Har a lokacin da mamaki a fuskarta tace.
"Me ya kaika wajen toh?"
"May be ke ya kamata in fara tambaya, ni namiji ne zan iya zuwa koina kuma ina da mota, amma ke a daren nan, sannan wannan wajen...."
Taji idanunsa sun mata nauyi saboda haka ta juya sannan tace.
"Hanya ce ta b'ace min bayan na fito daga wani gida."
Ya gyada kansa.
"Okay, toh ta yaya kika zo unguwar ke kad'ai?"
Amsar da zata bayar ya tuna mata da Rahma, ta kalle shi da sauri.
"Ba ni kadai bace nida rahma ne, tana can tana jirana."
"A ina?"
"Ban san wajen ba, amma...." Ta juya ta kalli yanayin wajen.
"Ina tunanin mun wuce shi a baya."
Ya juya kan motar a hankali sannan ya sauka daga kan titi, suka koma baya tana ya zare ido har suka zo daidai shagon nan da Rahma ta tsaya.
"Ga wajen nan...amma kuma bata nan." ta k'arasa a hankali tana kallon koina a wajen. Tayi nufin bude k'ofar motar amma yayi saurin danna lock din gefenta.
"Ki zauna a ciki, bari inje in duba."
Duk da zuciyarta ba'a nutse take ba a lokacin amma ta kasa hana kanta kallon yanayin takun tafiyarsa da kuma yadda kafadunsa suke a k'ame kamar ba motsi yake ba. Ya k'arasa cikin kantin suka gaisa da mutumin ciki, tana kallon yadda mutmin keta masa bayani har sanda ya fito bakin kantin ya dauko waya ya kira sannna dawo cikin motar.
"Bata nan, ta koma gida."
"Kamar yaya? Ya akayi ta tafi?"
"Ta koma gidan da kuka je ta tarar bakya nan sai mutanen wajen suka ce mata watakila kin b'ace hanya ne kika tafi gida saboda haka ta tafi."
Nanne ta jingina kanta da seat din tare da yin ajiyar zuciya. Ta riga ta tsira daga koma me wadancan mutanen ke shirin yi mata amma zuciyarta ta kasa nutsuwa, tambayoyi da yawa ne ke yawo akanta na yadda akayi imran yaje wajen a lokacin, ta kasa yarda da abinda yace d'azu, don motar data wuce da farko ba itace wannan da take ciki ba sannan ita ko kad'an bata tsaya ba balle na ciki ya ganta.
Idonta ya kai kan titi, a lokacin ne ta lura da yanayin garin, kamar mutane sun fara raguwa sakamakon daren daya fara yi. Ta kalli agogon kan dashboard, karfe tara da minti goma sha biyu. Ta san dole Rahma ta koma gida yanzu kuma hankalinsu zai tashi.
Me yasa ne a cikin kwanakin nan take zama silar tashin hankalin kowa?
Kamar ya karanci damuwarta sai taji yace.
"Karki damu na kira sulaiman yanzun nan nace masa muna hanya."
Jin an ambaci ya sulaiman yasa ta juyo da sauri ta kalle shi. "Bai tambayeka a ina ka ganni ba?"
Haske fitilar wata motar ya haska mata fuskarsa sanda yayi murmushi a k'asan numfashinsa.
"Bai tambaya ba, watakila yayi tunanin ko na k'ara kade ki ne."
Abin yaso sata murmushin itama amma sai tace.
"Wannan ranar ma tsautsayi ne amma ko keke bai taba buge ni a hanya ba, sannan a lokacin ma na....."
Sai ta kasa k'arasawa saboda yadda idonta ya hango mata titin a wancan lokacin, sai da ta riga ta tabbatar babu mota a kusa sai wani babur daga can nesa sannan ta tsallaka, toh ta ina motarsa ta taho da bata ganta ba? Abin yaso yi mata shige da wanda ya faru yanzu.
"Ya kika yi shiru?" ya tambaya a hankali sanda taji suna k'ok'arin sauka daga kan titi.
"Ba komai." Ta fad'a sannan da sauri ta juya ta kalli window, sai dai sab'anin k'ofar gidansu sai taga sun tsaya ne a wani k'aton chemist mai cike da hasken fitilu. Ta sake dawo da idonta kansa.
"Me zaka yi anan? Dare yana yi ban koma gida ba."
Ya kashe motar nan sannan yace.
"Ke na kawo."
Ta kalli chemist d'in sannan ta sake kallonsa.
"Me ya same ni? Na fad'a maka lafiyata...."
Ta kasa k'arasa zancen sakamakon juyowa da yayi ya kalle ta, idanunsa masu kyau suka tsaida duk wani tunaninta.
"You don't look fine to me sa'adha, its like you are kind of distracted."
"Abinda ke damuna daban." Ta ayyana a ranta. Amma a fili sai tace.
"Dan Allah ka maida ni gida."
Minti uku bayan hakan, wata mace na tsaye a kanta a cikin chemist din. Daga ta zura mata wani abu sai ta gwale idonta kamar zata ciro tsakuwa a ciki. Duk abinda ake yi, idonta na kan agogo da kuma shi da yake ta zagaye a cikin wajen daga kanta zuwa kanta, yana kallon magungunan dake zube akai.
"Kina jin jiri?" matar ta tambayeta bayan ta zaro wani abu kamar tsinke data sa mata a baki.
"Ba abinda nake ji, lafiyata kalau."
Tayi murmushi tana kallonta.
"Kar ki damu madam, lafiyarki kalau."
Sai ta jawo wata 'yar takarda tayi rubutu sannan ta zagaya d'ebo magunguna. Daidai sanda imran ya dawo hannunsa d'auke da k'atuwar robar yoghurt guda biyu.
"Tace ba abinda ya same ni, mu tafi yanzu?"
Lebb'ensa ya motsa cikin murmushi.
"Ko in zauna ne a gwada ni a tabbatar miki cewa bana cin mutane?"
Kafin ta amsa matar ta dawo da 'yan maguguna a hannunta. Ta nufi inda yake tsaye.
"Yawwa ga wannan su zata sha, na duba na gani lafiyarta k'alau, kawai fargaba ce da kuma gajiya a jikinta."
Daga inda take zaune, Sa'adha ta san matar nan karya take, kawai dai tana son samun hanyar da zata ci kud'insa ne. Ya mika mata robobin yoghurt d'in yace ta had'a har dasu ta fadi kud'in. Ai kuwa abinda ta fad'a ko waye zaiji ya san ko kusa kud'in abubuwan basu kai haka ba.
"Zan iya ganinki gobe?"
Ya tambaya bayan sun koma motar.
"Me za'ayi?"
Itama ta tambaya a hankali idonta na kallon titi. Taji wani abu kamar k'arar murmushinsa kafin yace.
"Karki damu ba nan zamu dawo ba, akwai abubuwa da yawa da nake son in tambayeki ne."
Taji kamar ya karanci zuciyarta ne, don watakila ita tarin tambayoyin ma dake k'ulle a kanta game dashi sun ninka nasa. Saboda haka ba tare da tunanin komai ba tace.
"Allah ya kaimu."
"Ameen. Amma da yaushe zan same ki?"
"May be da yamma?" Ta amsa kamar tambaya.
Ya sake yin murmuushi yana kallon titin.
"Baki tabbatar ba?"
Tun lokacin da ta fara sabawa dashi a asibiti, ta lura yana da yawan murmushi, amma bata yi tunanin yawan ya kai haka ba.
"Na tabbatar. Allah ya kaimu."
"Ameen." ya sake amsawa.
Taji wani iri, yadda d'an wannan alkawarin yasa jikinta yayi sanyi bayan duk gwagwarmayar data sha a daren. Sun shigo layinsu a lokacin, komai yana nan kamar yadda yake, fitulun k'ofar kowanne gida sun haska tar! masu gadi na waje da 'yar rediyonsu sannan tsilli-tsillin mutane na wucewa.
Sai taji kamar duk abinda ya faru a mafarki ne, yanzu ta farka.
Yayi parking a k'ofar gate d'insu amma bai bud'e lock d'in ba. ya miko mata ledar magungunan.
"Ki tabbata kinsha maganin kafin ki kwanta."
Ta kalli ledar sannan shi, abinda ke idonta ya nuna masa tana shirin k'in k'arba ne saboda haka ya sauke muryarsa k'asa yace.
"...Don Allah."
Hakan ya tuna mata da ranar daya fara mata magana, lokacin da yake tambayar ta sunanta. Sai ta sauke gashin idonta kan ledar sannan ta karb'a.
"One more thing...." ya katse godiyar da bakinta ke shirin yi. Muryarsa ta canja, ta zama so serious.
"Zaki iya min wani alkawari?"
Ta gyada kanta, a lokaci d'aya kuma tayi dana sanin hakan, ta san me zai tambayeta ne? in kuma wani babu ne da bazata iya ba fa?
"Kar ki sake zuwa inda baki sani ba ke kad'ai."
Ssi tayi ajiyar zuciya, wannan ai ba wani abu bane.
"Insha Allah, sai da safe."
"Allah ya kaimu." ya amsa sannan ya bud'e lock d'in.
Ta juya ta bud'e k'ofar motar, sai dai tana zura k'afarta d'aya waje, ya sake tsaida ita.
"Sa'adha...."
Me yasa ne muryarsa ta saba fad'ar sunanta, watakila don bai san yadda hakan ke sawa taji bane. Ta juyo da sauri ta kalle shi. Saboda shirme wani b'angare na zuciyarta na fatan zaice kar ta tafi ne.
"Sleep well."
Amon muryar tasa ya amsa a kowanne lungu da sako na jikinta, taji zuciyarta ta buga kamar tana neman hanyar fitowa daga kirjinta. Ba shiri ta fita daga motar ta tura k'ofar gate d'in ta shige.
Babu kowa a harabar compound d'in amma duk fitilun d'akunan mazan a kunne suke alamun ba wanda yayi bacci. Da sauri ta shige ciki kar wani ma ya fito ya ganta. Akwai 'yan aiki da d'an yawa a kicin din amma bata bari kowa ya ganta ba tayi hanyar sama da sauri.
Tana shiga d'aki ta tarar inna na zaune akan sallayarta.
"Alhmdlilahi, har kin dawo?"
Ta fad'a bayan ta amsa sallamarta. mamaki ya kamata.
"Inna har ne? Ban dad'e ba?"
"A'ah baki dade ba, yanzun nan fa sulaiman ya bar d'akin nan yake ce mana wai kin b'ace hanya ne, amma kin had'u da d'an albarkar yaron nan zai maido ki, itama rahman fitarta kenan ta tafi gida."
Nanne ta juya ta kalli agogo, karfe tara da minti ashirin, tun kafin su tsaya a chemist d'in nan taga k'arfe tara da minti goma sha biyu, ta yaya za'a ce duk sauran abubuwan da suka faru a minti takwas ne kawai?
"Inace ba dai abinda ya same ki koh?"
Ta girgiza kanta da sauri.
"Ba komai inna, dana koma gidan ne sai na fito ta wata k'ofar, na kasa gane hanya, sai Allah ya had'ani dashi ya dawo dani."
"Toh Alhmdlilahi, ai baki ji yadda naji ba da Rahma tazo min da zancen wallahi, wannan bawan Allah dai Allah ya saka masa da alkhairi..."
Tayi cikin d'aki ta bar innan nata sa masa albarka. Ta ajiye ledar hannunta a kasan gado sannan ta shiga toilet, ta tara ruwan zafi tayi wanka, ta fito tasa kayan bacci tayi sallah sannan tayi wa inna sai da safe ta kashe fitulun ko'ina sannan ta dawo d'aki.
A yanzu ita kad'ai take kwana don Inna ta koma da shimfid'arta falo, ta jawo ledar nan ta fito da magungunan, guda uku ne daga wani pain reliver sai paracetamol da vitamin C, ta san ba abinda take ji a jikinta amma ta d'auko ruwa ta tura su bakinta, sannan ta sa vitamin C d'in a baki.
Idan bata sha ba, zata yi ta tuno muryarsa ne sanda ya miko mata ledar. Ta d'auko robar yoghurt din nan tana juya ta, abubuwa da yawa game dashi suna d'aure mata kai, amma gobe ta san komai zai warware, don in har zai mata tambayoyi, itama zata yi masa tambayoyin da zasu sa ta san WAYE SHI.
Ba zata b'oye komai ba, zata tambayeshi gabad'aya abubuwan da bata fahimta ba, tun daga ranar data fara ganinsa har zuwa yanzu. Ta koma cikin bargon ta dunk'unk'une jikinta rik'e da robar a hannunta.
Wani irin dad'i da fresh take ji a jikinta, kamar an sauke mata nauyin wasu abubuwa, ta manta da halin da take ciki, ta manta da maganganun Baffa, ta manta da abinda ke shirin faruwa da ita, ta manta da wa'adin da Baffa ya bata, ta manta da duk wani zumud'in Inna.
Ta janyo tunanin Imran da duk abinda ya faru a yau da kuma fatan ganin gobe kawai tasa a ranta, goben da take fatan sanin...
WAYE SHI?
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
24
(¡î_¡î)
Bai san me ya same shi ba, bai san me yasa tunda ya dawo zuciyarsa ta kasa nutsuwa ba. ya san ya riga yayi kuskure tun a jiyan, kuskuren fad'a mata cewa zai ganta a yau, abinda ya san ba zai tab'a faruwa ba. Watakila ko don ganin yadda ta tsorata da mutanen nan ne.
Shi kansa har yanzu da ya rufe ido su yake hangowa, musamman d'ayan, wanda yafi matsawa kusa da ita sosai yana dariya. Da ace Allah bai kawo shi a daidai wannan lokacin ba, baya jin zai iya tsayawa abinda zai faru.
Daga office ne suka je gidan wani abokin aikinsu daya takura musu da gaiyata tun wajen watanni uku a baya da yayi aure, sai a jiyan Allah ya k'addara zasu je, kuma ya riga sauran da suka je tare tahowa, ganin dare ya fara yi amma su basu da niyyar tashi.
Saboda haka yayi musu sallama ya taho, sai dai tunda ya shiga motarsa ya fara jin gabansa na fad'uwa sannan zuciyarsa tana bugawa, ya rasa dalilin hakan tunda ya san ba abinda ya same shi kuma ciwon Sa'adha a lokacin bai isa ya tashi ba.
Abin ya cigaba da k'aruwa bayan ya fita daga layin yabi hanyar da zata kaishi titi.
A hanyar ne idanunsa suka hango masa wasu mutane daga gefe sannan bugun zuciyarsa ya k'aru a daidai wannan lokacin saboda haka ya juyo da kan motarsa ya dawo.
Anan ne ya hangi abinda ya sashi mutukar mamaki, wasu maza biyu suna kokarin ritsa Sa'adha a jikin wata kantanga, mamaki ya kamashi na ganinta a wajen, kenan abinda yasa shi fargaba kenan? Saboda daya b'arin jikinsa na cikin matsala? Bai san lokacin daya k'arawa motar gudu ba yayi kansu gabadaya.
Abu d'aya ne ya hana shi bin bayan matasan nan lokacin da suka gudu. Idanunta. wad'annan idanun nata da suka cika da d'imbin tsoro, yaji ba zai iya tafiya ya barta ita kad'ai a wajen ba, don bai yarda cewa in har ya tafi wasu irinsu baza su sake zuwa ba.
A zahiri da kuma yadda ta fad'a masa, ba abinda suka yi mata amma har suka hau titi fad'uwar da gabansa yake da kuma bugawar zuciyarsa basu canja ba, alamun har a lokacin tana cike da tsoro, saboda haka yayi tunanin ko sunyi mata wani abun ne ta b'oye masa. shi yasa a lokacin daya tabbatar k'awarta ta koma gida yanke shawarar tsayawa a wannan chemist d'in.
Sannan bayan matar ta gama dubata ta zagaya d'ebo magunguna, ya tsaida duk wani abu dake motsi na cikin chemist d'in ya isa gurinta ya kalli idanuwanta, ya lalubo cikin tunaninta daga sanda suka shigo chemist d'in har zuwa lokacin da ta gama duba ta.
Babu wani abu data gani a jikin sa'adhan, hasali ma tunaninta baya cike da komai sai k'ok'arin ganin meye a tsakaninsu. Tayi tunanin sa'adha k'anwarsa ce ko cousin, don a cewarta ba zai yiwu ace ita matarsa bace, he's too classy for her. (ya girmewa ajinta.)
Yayi murmushi sanda ya tuna hakan.
Daga baya kuma sai ta koma tunanin yadda zata karbi kud'i da yawa a wajensa, tana tunanin idan ta k'ara akan wanda take dasu zasu isa ta samu ta kai 'yarta asibiti gobe.
Ganin ta bar zancen sa'adhan yasa ya juya ya nufi can k'arshen ginin, wajen da aka jera fridges sannan ya murza hannunsa komai ya dawo daidai.
Ya lura har suka koma cikin mota, bata da nutsuwa sosai, tunaninta ya rabu kashi-kashi sannan hankalinta ya tafi gida, kamar tana ganin wani abu zai faru in bata nan,
Yayi tunanin yi mata magana don hankalinta ya kwanta ko shima ya sami nutsuwar zuciyarsa.
"Zan iya ganinki gobe?"
Bai san abinda ya tambaya kenan ba sai da tace
"Me za'ayi?"
Yayi murmushi a hankali saboda yadda muryarta ta fita kamar tana tsoron zai sake dawo da ita chemist d'in ne, saboda haka yace mata kawai yana son yi mata tambayoyi ne.
Kuskuren da yayi kuma kenan, na neman kauce tsarin da suka yi shida jaamil. Don a yadda suka tsara ba zai k'ara ganin ta ba sai nan da wani lokaci, lokacin da zata shigo cikin rayuwarsa ya k'arasa daga inda jaamil ya tsaya.
Tsarinsu ya tafi ne a cewar ta riga ta fara sonsa, don haka zata yarda dashi in har komai yazo a k'urewa amma shi bai yarda ba. Ya san Kawai tana cikin Delusion ne irin na mata da yawa da yake gamuwa dasu. Bata san WAYE SHI ba, bata san komai game dashi ba, toh ta yaya zata so shi?
Soyayya shine a lokacin daka yarda ka kuma amince da mutum a kowanne irin hali na rayuwa. Don haka baya tunanin akwai wanda zai so shi, SHI d'in dake bayan wannan fuskar.
Ya san zata shiga damuwa a yau d'in na rashin zuwansa amma ba yadda zaiyi, yayi kuskure da yawa a baya ba zai so ya cigaba da lalata musu abubuwa ba, alhalin jaamil yana iya k'ok'arinsa wajen gyarawa. Ko ganinta a jiyan ma, ba zai taba bari ya sani ba.
Ya kalli had'dd'en agogon dake facing d'insa a saman TV.
K'arfe hudu da rabi.
*******
"K'arfe hudu da rabi." Sa'adha ta fad'a tana mikawa inna wayar. Inna ta karb'a ta kara a kunnenta tana fad'in.
"Toh ni kuwa ina suka tsaya haka? ace kasuwa tun safe har yamma..." Tayi saurin katse maganar sakamakon d'aukar wayar da akayi daga d'aya gefen.
"...Maryama yanzu Allah baza ku taho ba sai wannan ruwan ya sauko a kanku, kuna ganin wannan hadari haka..."
Nanne ta mik'e a hankali ta isa jikin taga inda iska ke kad'owa ciki kamar zata taho da labulen, garin yayi bak'ik'irin kamar da magariba sakamakon hadarin daya game sararin sama baki daya.
A kusa da tagar akwai fridge, sannan a cikin fridge d'in akwai wannan robobin yoghurt d'in guda biyu, ta bud'e ta d'auko d'aya, sannan ta jingina da tagar tana wasa da ita a hannunta, babu d'ankwali akanta sakamakon 'yan k'ananan kitson da Rahma ta gama yi mata wanda ya dameta da zafi, saboda haka iskar ta shiga d'aga gashinta tana turo shi kan fuskarta.
Ta tuna murmushin da yayi lokacin daya rik'o robobin a hannunsa.
"Ko in zauna ne a gwada ni a tabbatar miki cewa bana cin mutane?"
Taji kamar itama zata yi murmushin amma ya mak'ale daga wuyanta, akwai abinda yake ba daidai ba yau, duk da ta saba a kwana biyun nan bata da walwala amma yau tana jinta ne kamar tana tsaye a k'arshen wani abu mai tsawon gaske, k'arshen da zata iya fad'owa a kowanne lokaci.
Ta sake hasko gabad'aya tambayoyin data shirya tun jiya a cikin kanta. Bata da matsala ta riga ta had'a komai da zata tambayeshi amma ita bata san me zai tambayeta ba kuma ta matsu taji ya nasa tambayoyin zasu kasance.
Ba irin tunanin da bata yi hasashensa ba tun daga jiya har zuwa yau. Ta hasko cewar imran zai zo wajenta, kuma zai cigaba da zuwa har su saba. Watakila ma har suyi sabon da zai iya neman aurenta kafin adadin lokacin da Baffa ya d'ibar mata.
Don in bashi ba, bata tunanin zata tab'a saurarar wani, balle har