Showing 81001 words to 84000 words out of 113985 words
da aka sauke su mai sanyi, a haka ta k'araso har cikin d'an k'aramin gidan da Imran ya nuno mata a matsayin inda zasu zauna bayan ya fito daga reception d'in da yayi musu booking.
Tana tafe tana barin d'igon yashin a duk inda ta taka sannan tana kunna fitulun kowanne corridor, mamaki take na yadda gidan yake da girma fiye da yadda ta ganshi ta waje, tana ganin komai kamar a irin mafarki ko irin tunanin yadda take hango Aljanna a idonta, saboda haka yadda zuciyarta ke bugawa cike da d'oki yasa komai ya zama blurry a idonta.
Dogowar hanyar data bi daga inda yayi kama da falo mai d'auke da luntsuma luntsuman kujeru guda biyu da k'arama d'aya, ya kaita wata k'atuwar k'ofa data ganta 'yar mitsitsiya a gabanta, tasa hannunta a hankali ta tura ta sannan ta kunna switch d'in fitila dake jikin bango a gefe.
D'akin k'ato ne kuma komai na cikinsa fari ne tas! daga kan furnitures d'in har carpet din dake gaban gado, bedsheet, labulaye da kuma fentin komai fari ne, sannan bangon k'arshe dake gefen gado na glass ne gabad'aya dake nuna glistening view d'in waje, amma bata lura sosai da nan ba hankalinta yafi tafiya kan k'aton gadon dake tsakiyar d'akin, ta matsa ta tab'a lallausan bargon dake kai sannan ta danna hannunta ciki, she wanted to be sure everything was real!
Bata jin ko a hoto ta tab'a ganin waje mai kyau irin wajen nan, ta dinga zagaye d'akin tana tab'a komai cikin mamaki, akwai tarin kayan electronics harda wanda bata san amfaninsu ba, ta tura k'ofar inda ya mata kama da toilet ta shiga, toilet din ne kuwa, sai dai cikin wata irin haduwa da bata taba gani ba, drawers koina kamar kitchen sannan wai harda wani center carpet a tsakiya, abu d'aya idonta ya gane da wuri shine bathtub, amma sink ma da kyar ta iya lalubo shi tsakanin drawers d'in.
Akwai wasu irin dogwayen tagogi daga gefe, ta bud'e guda d'aya a hankali, hasken wata daga sama ya haske beach d'in dake can gabansu da kuma ruwan tekun, yashin wajen yayi wani haske a idon mai kallo sannan ga wata iska mai dad'i tana kad'awa.
A sannan ne ta jiyo maganganun Imran shida Room service d'in daya d'auko kayansu daga can reception din, ta rufe windon sannan ta fito daga cikin toilet d'in.
Daidai sanda shima ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo.
"Do you like white?" ya fad'a yana k'arasowa dab da ita, ta d'aga fuskarta kad'an tana kallon tasa.
"Kai kayi choosing colour?" Numfashinta ya busa a fuskarsa, tana ganin yadda ya lumshe idonsa kafin ya amsa.
"Na zata kina son fari."
"Ina son kowacce colour Ayunie, white is great, also this place is great."
Gefen kumatunsa ya lotsa alamun yaji dad'in maganarta.
"Baki ga komai ba Noory, zan nuna miki duk sauran abubuwan da nayi wancan karon."
"Ka tab'a zuwa dama?"
"Na tab'a zuwa lokacin dana d'auki hutu sau d'aya, amma tun a lokacin ba komai na iya yi sosai ba saboda tunaninki."
Sai ta sunkuyar da kanta k'asa tayi murmushi.
"Yanzu kije kiyi alwala muyi Sallah."
Magriba da Isha, abinda take tunani itama kenan, tunda sunyi azahar da la'asar tun a Nigeria da zasu taho. Kafin ta motsa taji ya lankwaso da kansa cikin wuyanta, lips d'insa suka yi brushing a gefen mak'ogwaronta daidai k'asan kunnenta, ta rufe idonta sannan ta damk'e yatsun k'afarta da k'arfi, kamar ya gani sai yayi dariya a hankali numfashinsa mai d'umi yana busawa akan fatarta.
Da sauri ta d'an ture shi ta juya ta koma cikin toilet d'in tayi alwalar, akwai dogwayen hijabanta guda biyu a cikin akwatinsa da tasa saboda nata ya cika, d'aya daga cikinsu ta d'auko ta saka yayi musu jam'in sallolin guda biyu .
Bayan sun idar order d'in abincin da yayi daga can reception d'in da suka fara tsayawa ya iso, akwai abubuwa da yawa amma in banda snack d'in samosa da fried naman kaza ba abinda Nanne ta gane a ciki toasted bread da ta gani guda uku.
Sai dai duk sauran abubuwan nan da bata gane ba, haka Imran yayi ta d'ura mata su yana cewa taci shima k'arin experience ne, wani ta had'iye da kyar wani kuma ta fito masa dashi, haka zai sa hannunsa ya k'arb'a bai ko damu ba.
Ita dai har a lokacin dad'a kallon wajen take tana gayawa zuciyarta cewa ta yarda ba mafarki take ba.
********
"No...!"
Nanne ta fad'a tana zare idanunta.
"Yes."
Imran ya fad'a tsaye daga bayanta, suna tsaye daga wani balcony da ya fito ta cikin falon inda akayi wani d'an karamin pool da aka jawo ruwansa daga cikin tekun sannan ga grass carpet mai taushi da kuma flowers da fitilu masu haske kala-kala a wajen, wajen yayi kyau it felt like a dream to her! Har yanzu gani take kamar ba da gaske itace a wajen ba, kamar zata iya bud'e ido a kowanne lokaci ace mafarki take yi.
Dazu taga k'ofar amma bata tab'a tunanin cewa wani wajen ne ba, tayi zaton toilet ne ko kuma d'an store kawai. Bata san sanda ta juyo da sauri ta kalle shi ba tace.
"Please Ulfat zamu zauna anan har abada?"
Ta fad'a tana kifkifta masa idonta alamun rok'o.
Yayi dariya mai zurfi yana kallonta.
"In kina so me zai hana, amma me zaki cewa su Inna?"
Inna. kiran sunan da yayi ya sata tuna cewa bata kira su ba.
"Ya salam! Ayunie ban kira su ba, ya kamata ace na kira su na fad'a musu inda muke tunda muka sauka."
Yayi saurin rik'ota sanda take kokarin komawa ciki.
"Kin san k'arfe nawa yanzu?"
Ta janyo d'aya hannunsa dake rik'e da wayarsa ta kalli agogon.
"K'arfe tara fa ai bata kwanta ba yanzu."
"Wannan setting d'in k'asar nan ne saboda na canja Sim amma k'arfe hud'u na asuba yanzu a Nigeria."
"Huh..?" Ta ware ido tana kallonsa.
"Ko so kike tayi tunanin wani abun?"
Ba tace komai ba ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta.
"Zamu kira ta first thing zuwa gobe, yanzu kin gaji da yawa Sa'adha, kije kisa ruwan zafi a jikinki kizo mu kwanta."
Ya Allah, kunya ta kamata sanyin iskar wajen gabad'aya yasa ta manta da wani abu wai shi wanka. Ta d'aga kanta a hankali ba tare da ta kalle shi ba.
A minute alone would be perfect!
"Ko muje ne in taya ki?"
Bata san sanda ta kalle shi da sauri tana zare ido ba, ya sake yin dariya cikin husky voice d'insa, sannan yasa kansa cikin wuyanta, wani waje dake fitting d'insa perfectly.
Ya rad'a mata wani abu da muryarsa data koma can k'asa yadda taji kamar yana lasar fatar jikinta ne, taji k'afafunta sun daskare a wajen kamar k'ank'ara, tunaninta ya gwamutse a lokaci d'aya kuma kwakwalwarta ta kasa tab'uka wani tunanin.
A haka yaja hannunta suka koma ciki har bakin toilet d'in.
"I'm waiting for you." Yaja saman hancinta sannan ya juya ya koma ciki.
Tabi bayansa da kallo kafin ta tattaro dukkan k'arfinta taja numfashi cikin k'irjinta, sannan ta kalli kafad'arta don taga ko ta kama ne da wuta, don hakan wani abu ne da Imran bai tab'a mata ba, kullum tana jikinsa amma tun lokacin da ta tashi da wannan marks, ya daina mata irin wannan abubuwan. Taji a cikin ranta cewa wajen zai k'ara kusanci a tsakaninsu.
Babu wutar a kafad'arta, atleast babu a fili sai ta cikin fatarta da take jin wajen kamar an d'ora gaushi, ta lalubo jakar toiletries d'inta sannan ta koma toilet d'in, sai dai tana bud'ewa taga ta manta brush dinta, saboda haka ta shiga bud'e drawers din anan wani mamakin ya kamata, akwai komai da aka san d'an adam na iya buqata a harkar toilet, brands kala-kala masu kyau bama irin na Nigeria ba.
Saboda haka ta zuge jakarta ta ajiyeta a gefe, don ba ta yadda za'a had'a kyan kayan da nata, ta d'auko wani shampoo mai ainihin k'amshin extract d'in strawberry ta wanke gashinta tsaf sannan tayi wanka, shi kansa ruwan wani irin santsi ne dashi akan fata, bayan ta gama ta d'auko wani katon towel a cikin drawer ta nannade jikinta sannan tasa wani karami ta tsane ruwan kanta, ta jona hand dryer ta taje gashinta, yayi d'umi ya kwanta smoothly har gadon bayanta.
Sanda ta fito ta bud'e akwatinta, wani mamakin ya kamata, gabad'aya kayan da ta san ta jera da hannunta babu su, instead kayan da bata tab'a gani bane, k'ananan riguna da three-quarter skirts da wando, bayansu sai kayan bacci kala-kala masu mutuk'ar kyau.
Undies d'inta da kuma wasu dogwayen riguna uku na material sune kad'ai abinda ta sani nata. Ta fiffito da kayan, gabad'ayansu sababbi ne da tag d'insu, bata san yaushe ya siyo ba kuma bata san yaushe ya canja su da kayanta ba, ita kad'ai amma kunyar kayan ta kamata, ta tuno da abinda ya fad'a mata a gida.
"...bana jin ma duk wannan kayan zasu yi miki amfani sosai a can."
Da kyar ta iya zab'ar wata rigar mai gajeren hannu kalar Pitch da kad'an ta wuce gwiwa ta saka, Ta juya wajen mirrors d'in dake kan wani dogon counter a gefenta, ai kuwa tana kalla ta juya da sauri ta juyawa mudubin baya, gaskiya ba zata iya fita a haka ba, ita da ta saba kullum cikin dogwayen rigunan barcinta...ta koma cikin akwatin ta d'auko doguwar rigar material d'inta guda d'aya, toh ai kuma yanzu dare ne, ta yaya zata zumbula wannan rigar ta kwanta?
Numfashinta ya shiga fita kamar tayi gudu sannan hannunta ya fara rawa, sai kawai ta zauna akan sassayan tiles d'in d'akin ta cusa kanta a tsakanin k'afafunta, Zuciyarta ta shiga addu'ar kar ya gaji da jiranta yazo ya ganta, ta san in har ya ganta a haka shima hankalinsa zai tashi ne.
Zai yi tunanin she's freaking out saboda tsoronsa ne, ba zai yarda cewa she's freaking out saboda bata san ta yadda komai zai fara ba, ba zai yarda cewa shes freaking out saboda bata san ya k'addararta zata kasance ba lokacin da ta fita daga cikin d'akin nan.
Tana ji ne kamar zata fita cikin dubunnan jama'a wad'anda suke jiranta ba tare da ta san me zata fad'a ba.
Ta yaya ne mutane suke iya had'iye tsoro da kuma taraddadinsu su tunkari wani abun? ta yaya zata iya zuwa wajen Imran a yanzu?
Saboda kina son shi.
Zuciyarta ta amsa, Da ace ba imran bane ke jiranta, Da ace zuciyarta b
ata riga ta amince dashi ba, da ace kowanne particles na jikinta basu san cewa yana sonta unconditionaly ba, ba zata tab'a iya daurewa zuciyarta ba, amma Ayuninta ne ke jira saboda haka ta rad'awa kanta cewar kar taji tsoro.
"Don't be a coward."
K'ofar d'akin ta bud'e a lokaci d'aya, lokacin da itama ta juyo daga kallon kanta da take a mudubi.
"Sulaiman ya kira ni yanzu, I don't know ke da inna wa yafi..."
Maganarsa ta katse lokacin da idonsa ya gano ta, kyawawan idanunsa suka sauka akan nata, sannan a hankali suka soma sulalewa zuwa jikinta, ya tako a hankali ya k'araso gabanta, sannan yasa hannayensa ya nannad'o ta cikin jikinsa. Tana kallon yadda mak'ogwaronsa ya motsa alamun ya had'iye wani abun.
"Kinyi kyau." Ya rad'a cikin kunnenta.
"Kinyi kyau sosai Mine!"
Ta k'ifta idonta hankali tace.
"Yaushe ka siyo kayan?"
Maimakon ya amsa mata sai ya d'ago hannunsa zuwa gashinta ya warware Bun d'in data k'ulle shi.
"I preffered your hair loose!" Ya fad'a cikin husky voice d'insa, muryarsa mai taushi dake d'auke hankalinta.
Zuciyarta ta buga da k'arfi sanda ya sunkuyo daidai fuskarsa yayi pressing lips d'insa a gefen bakinta.
Ya Allah!
Tunaninta ya d'auke gabad'aya, taji bakinta ya bushe sannan numfashinta ja fita da sauri, kamar zai janye gabad'aya ta suma, a cikin haka kwakwalwarta ta jiyo masa sanda ya fad'i wani abu, bata tabbatar ba amma taji kamar yace ne "Please" Sannan ya d'an tsaya kamar mai jiran wani abu, amma ta gaza yin komai, ta tsaya cak kawai hannayenta rik'e dashi ba tare da ta san me zata yi na, bayan wani d'an lokaci taji yana shirin d'aga kansa.
No! not so soon...!
Duk wani sauran tunaninta babu shi a lokacin, saboda haka tasa hannayenta dake rik'e da rigarsa ta janyo shi ya dawo...daga nan ta daina gane komai, magana d'aya kawai daya fad'a kwakwalwarta ta iya fahimta.
"If you feel something wrong...If I hurt you, ki gaya min at once."
Hasken ranar dake shigowa directly ta cikin windon shi ya tashe ta da safe. can safiya koma tsakar rana ne bata sani ba, Idonta ya bud'e tar tana ganin komai clearly, kuma ba sai tayi wani tunani ba ta san ina take, wannan farin d'akin mai k'aton farin gado, wajen tsit! k'ara d'aya ce kawai ke yawo, na kad'awar tekun dake waje.
Taji zata iya kwanciya a haka tsawon lokaci tana jin dadin yanayin, amma ba abinda ya dace kenan ba, a wani waje suke mai cike da d'imbin abubuwan da take d'okin gani, She'd to get up nd face all the wonders that awaits her!
Imran ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo a daidai lokacin, sanye da wasu kayan bana jiya ba, annurin fuskarsa ya dawo mata da dukkan memories d'in da suka faru jiya, taji alamun kumaunta sunyi ja like she's blushing, and she wondered dalilin da ya kawo tsoronta da farko jiya, it seem silly a yanzu tama yi tunanin tsoro game dashi.
A lokaci d'aya ya k'araso kan gadon.
"Ka tashi lafiya" Ta fad'a a hankali tare da yin murmushi, maimakon ya amsa, sai ya kwanta a gefenta sannan ya jawo hannunsa yayi stroking a hankali.
Nanne ta kalli cikin idonsa, kalarsu ta canja daga bright zuwa wannan dark d'in alamun damuwa. Damuwa? me zai kawo masa damuwa a yanzu?
"Ayunie me ya faru?" Muryarta ta sake fitowa a hankali fiye da d'azu.
"Baki san me ya faru ba?" Sautin muryarsa was so deep sanda ya tambaya yana tracing hannunta kamar mai bin layin wani abun.
Ta k'ifta idonta a hankali tana kallonsa, sanda tunanin ko laifi ta masa yazo cikin kanta. kwalkwalwarta ta shiga lalube akan duk abinda ya faru jiya amma bata ga komai ba, ta shiga tace kowanne single memory da take iya tunawa amma ta kasa ganin wata tangard'a ko 'yar k'arama kuwa, to be honest komai ya tafi ne cikin sauqi ba kamar yadda ta zata ba, ita dashi sun dace ta hanyar data k'ara yardarwa kanta cewavana halicci kowannensu ne a matsayin abokin rayuwar d'aya, they fit together perfectly ta yadda har yanzu ta kasa gano abinda zai sa shi cikin wannan damuwar.
A hankali taji hannunsa yana tab'a tattarewar da fatarta tayi a tsakanin girarta..
"Tunanin me kike yi?"
"Tunanin abinda zai saka damuwa.."
"Wane irin ciwo kike ji a jikinki?" Yayi saurin katse ta.
"Ciwo...?" Fatar goshinta ta k'ara tattarewa lokacin da tayi focusing idonta akansa.
Jikinta k'alau yake in banda gajiya kad'an da take ji a wajen gab"ob'inta ba komai, sai ko damuwar da take yi a yanzu na yadda yake son b'ata safiyar da tafi kowacce a wajensu.
"Lafiyata k'alau Ulfat, ba abinda ya same ni I'm..."
"Shashshsh..." Ya katse ta tare da rufe idonsa.
"I'm sorry Noory, I made a mistake...Nayi laifin da nake jin na tsani kaina, dan Allah kiyi hakuri, I'm so sorry fiye da yadda zan iya fad'a miki."
A wannan lokacin tasa hannayenta duka biyu tayi cupping fuskarsa.
"Dan Allah ka gaya min me ya faru, me ka min? hak'urin me kake bani?"
Bai bud'e idonsa ba har a lokacin kamar baya son ganinta.
"Ayunie..."
Ta kira shi cikin wata irin murya kamar zata yi kuka. A hankali ya tattaro ta cikin hannunsa sannan ya mik'e tsaye, bai tsaya koina ba sai gaban mudubin nan ya dire ta cikin carpet d'in har a lokacin fuskarsa take kallo, a sannan shima ya bud'e idonsa da suka k'ara rinewa suka koma so dark sannan ya juya kafad'unta hankali tayi facing mudubin.
"Look at yourself Sa'adha."
Cikin umarnin idanunta suka tafi cikin mudubin sannan bugun zuciyarta ya tsaya a lokaci guda.
Marks, Bruises....bruises koina jikinta fal! ja jawur dasu kuma manya, gasu nan fal har wani na had'ewa da wani yadda ba wani sauran space da babu su.
Tayi burd'in-bird'in da ita!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SH?
AYSHA SHAFI'EE
51
So wannan itace longest chapter da na fara rubatawa a labarin man, hope you will enjoy it!??
(¡î_¡î)
"Kayi shiru, I want to watch it quietly."
Nanne ta fad'a a hankali idanunta na kallon can gabansu, inda rana ke shirin fad'uwa, Tana kwance a jikinsa daga k'asan wata dogowar bishiyar kwakwa a bakin tekun dake ta ambaliya wani har yana tab'o kafafunsa dake mik'e.
A can gabansu rana ce ke shirin fad'uwa, wani abu ne da bata tab'a gajiya da gani tun zuwansu wajen, wani abu dake k'ara mata jin kamar ba'a cikin duniya take ba sannan wani dake k'ara k'arfin imani a zuciyarta...ranar tayi wani irin ja sannan brightness d'inta yayi reflecting a kowacce kusurwa ta yadda ya bada hasken rainbow, tana kuma yin k'asa a hankali kamar tana lumewa cikin makeken tekun dake gabansu.
A sannan satinsu biyu kenan da zuwa wajen, wani lokaci da Nanne tayi wa tambari a matsayi ranakun da suka fi kowanne farin ciki a rayuwarta, the most happiest days of her life!
Rayuwa ce ta kwanciyar hankali da nutsuwa, ba ruwan kowa dasu don wajen ba mutane sosai...saboda haka yadda zasu farantawa junansu rai shine kad'ai a gabansu.
Sun ziyarci wajaje da yawa har da wasu island d'in dake kusa da nasu cikin irin speedboat da suka zo, a yanzu Nanne ta riga ta kware a shiga jirgin don har rige-rigen wajen zama suke ita dashi wajen da a karshe dai su biyun ne zasu zauna, har cikin ruwan sun shiga amma ba can zurfi ba, gefe kawai inda 'yan k'ananan kifaye da kuma kunkurun ruwa suke amma sai da suka sa snokel tukunna, (Wani glass d'in ruwa dake rufe ido da hanci saboda shak'ar iska.)
Har da wani paddle na ruwa da ake tafiya a tsaye, abubuwa kala-kala yadda kullum suka fita sai rana ta fad'i suke komawa cikin cabin d'insu. Bayan fad'uwar rana kuma har fitowarta suke gani, Inran ya saka alarm a duk lokutan sallah saboda haka bayan sun idar da sallar asuba kullum zasu fito da overnight mat din da suka samu a cikin gidan su shimfidaa wannan balcony din na wajen pool, mat din na da laushi kamar katifa anan zasu kwanta suna facing fitowar ranar, yadda haskenta ke fitowa a hankali yana canja kalar duhun sama zuwa kamar royal blue da kuma shade d'in golden da kuma orange.
Sai dai a cikin kwanakin nan, Nanne ke fuskantar