Showing 90001 words to 93000 words out of 113985 words

Chapter 31 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28464

ta san sarai abinda yake nufi da yayi brushing hannunta a hankali, ta san wace kalma kowanne yatsansa daya tab'a ta yake nufi, kalmomin da suka had'u suka had'a sentence d'in da yake ta fad'a mata tun dawowarsu daga maldives har zuwa yanzu.

You will be fine!

****

"Ka tabbata da abinda muke shirin yi yarima? are you sure about this?"

Jaamil ya tambaya sanda suka zagaya bayan gidan suka zauna akan wasu kujeru dake cikin d'an karamin wajen shan iska, wajen da ana iya fitowa ta k'ofar kitchen ta baya.

Imran ya sunkuyar da kansa sannan ya fito da iska ta bakinsa.

"I don't know jaamil, wallahi ban san ya zanyi ba kome zai faru, kullum cikin magiya take min kala-kala ta safe daban, ta rana daban, ta dare daban duk akan a bar mata shi, ba irin bayanin da banyi mata ba tun muna can amma ta kasa fahimta ta, da farko ma zargi na ta fara yi akan wai zan kashe Babynta, yanzu kuma bayan duk taji komai tana ganin kamar ina underestimating d'inta ne, gani take kamar tana da k'arfin da zata iya."

"Baby? Tunani take Baby ne a cikinta?"

"Haka take gani saboda har a yanzu mantawa take ni ba mutum bane sai na tuna mata tukunnan, yadda ka san tatsuniya kawai na bata a baya."

"Tana matawa ne saboda baka nuna mata what you're capable of."

"Ba zan iya ba jaamil don koda ta yarda dani ita bil'adama ce, dole akwai tsoro irin nasu...ba zan iya dinga b'acewa a gabanta ba ko in dinga yin abubuwa da mutane baza su iya ba, ko in dinga baiyana mata ainihin halitta ta...I have to blend in for her sake!" (I tynk na amsa wanda ke tambaya ta me yasa Imran baya nuna powers dinsa.??)

"Haka ne." ya amsa curtly.

Suka d'an yi shiru na wasu seconds kafin jaamil yace.

"Bwama ta gaya min Naani ce kad'ai zata iya ganin ainihin abinda ke cikinta..."

"And she will never be involved!" Imran ya katse shi sharply.

Jaamil ya gyad'a kansa a hankali ba tare daya kalle shi ba, bayan wani lokaci ya sake magana.

"The good news...itama bwama bata so a rabata dashi."

Imran ya juyo ya kalle shi da sauri.

"Tana ganin cewa zai yiwu ne?"

"Ba zata tabbatar in zai yiwu ba sai ta gama ganinta yanzu, amma ta fad'a min ne k'aunar uwa ga d'anta wani abu ne da babu irinsa a fad'in duniya, tace kowacce uwa tana son jininta komai irin munin halayya da siffarsa, so inaga ta fahimci abinda Sa'adhan take ji ne a yanzu, shi yasa ta matsa min a lokaci d'aya cewa sai mun taho don taga irin halin da take ciki."

Imran ya had'e tafukan hannayensa sannan ya d'ora su akan lebb'ensa, kwakwalwarsa ta tuno masa hirarsa da ita jiya da yamma.

"Ina ji a jikina ulfat Babyn nan alkhairi ne a garemu, ba zai tab'a zama irin tunanin da kake ba...ina son shi sosai Allah, kuma kaima na gaya maka zaka zo ka so shi fiye da tunaninka insha Allah."

A lokacin suna zaune yana bata yoghurt a baki, abinda a yanzu suka gano cewa shi kad'ai cikinta ke d'auka ba tare da ta amayar daga baya ba.

"So habibty Babyn namiji ne?" Ya tambaya yana goge mata smudge na yoghurt d'in a gefen bakinta.

A lokacin d'aya kumatunta suka yi blushing zuwa pink... wata kala mai kyau, mai kyau sosai da yaji kamar an caka masa wuk'a a cikinsa, wata wuk'a mai tsini da kuma tsatsa saboda zuciyarsa ta kasa tantance wace irin k'auna Sa'adha ke masa, he'd hurt her in so many ways amma har tana iya wannan farin cikin around him.

"Yau ce rana ta farko daka fad'i wani abu good akan Babyn nan Ayunie..."

Kafin yayi magana ta cigaba.

"...ban sani ba ko mace ne ko namiji
, amma ni a mafarkina namiji nake gani."

"Har mafarki kike yi da Babyn?"

A lokacin da ya fad'i haka zai iya rantsewa yaga giftawar wani abu cikin idanunta, kamar akwai wani sauran bayanin tattare da mafarkin nata da take k'ok'arin b'oye masa amma sai ta sake yin murmushi tace.

"Zanso in iya nuna maka shi a mafarkin, yana da kyau sosai saboda da kai yake kama!"

Kafin fuskarsa ta iya rik'e wani reaction d'in ta rik'e hannunsa dake shirin kai mata wani spoon d'in baki tace.

"Kaci abinci?"

Ya langwab'ar da kansa kad'an irin abin tausayin nan yace.

"Noory ba abinda naci."

"Awwn...I'm soory na barka da yunwa, kaine kuma kak'i bari na in tashi."

Ta fad'a tana cupping fuskarsa a cikin hannunta, a lokaci d'aya kuma ta tashi ta nufi kitchen, bai b'ata lokaci ba shima ya rufe robar yoghurt d'in yabi bayanta. A gaban deep freezer ya same ta ta bud'e tana kallon kayan ciki, ya matsa a hankali ya juyo da ita, hannunsa d'aya zagaye da waist d'inta, d'aya kuma ya karb'e bowl d'in markadadd'en kayan miyan data d'auko.

"Me zaki yi?" ya tambaya fuskarsa dab da nata.

"Abinci zan dafa maka."

"Yaushe nace ina jin yunwa."

Ta d'age girarta d'aya.

"Kace baka ci komai ba."

"Amma bance ina jin yunwa ba." Ya fad'a yana kallon bakinta da idanunsa masu d'auke da emotions kala-kala da take hango su ta cikin maik'on idon.

"Toh ai zaka nemi abinci anjima kuma sai mu zauna ba'ayi girki ba don ni ba zan..."

Kafin ta k'arasa kawai ya had'e lips d'inta da nasa and just like that...ta manta k'arshen zancenta, kwakwalwarta ta tafi cloud 9 ta nutse can cikin duniyarsa.

Ya k'ara manna ta a jikinsa yana jin kamar ya cusa ta cikin zuciyarsa ta gano yadda yake mutuqar k'aunarta, ita kuma ta rik'o wuyansa kamar tana tsoron zata fad'i.

"Kasha tea Ayunie, bakinka na k'amshin madara." Ta fad'a breathlessly sanda ta d'an ja baya kad'an.

Yayi murmushi so soft idanunsa kusan a rufe, kafin ta k'ara magana ya sake sunkuyowa yana k'ara kissing d'inta, wannan karon itama ta taya shi, k'arar heartbeat d'insu ya had'e waje d'aya.

"I want to tell you something, abinda zan gaya maka yana mutuk'ar muhimmanci."

Muryar jaamil ta jawo shi daga tunanin da yayi tafi, ya juyo a hankali ya kalle shi.

"Mene ne?"

Kamar bai ji ba, sai da yayi shiru kafin yace.

"Ban san ta ina zan fara maka bayani bama."

Ya sake fad'a ba tare da ya juyo ba, Imran ya d'an tsuke gira yana kallonsa.

"How about the begining?...ka fara ta farko."

Maimakon ya amsa, sai ya d'ora hab'arsa akan hannayensa duka biyu sannan yace.

"Yaushe ne lokacin da Naani take jira?"

"Jiya na koma company, sunyi fixing date nan da kwana goma sha shida, atleast dai sati biyu, so i was thinking zamu iya samun mafita kafin nan."

Jaamil ya girgiza kansa har a lokacin bai juyo ba.

"Babu wata mafita da zamu nema yarima, Allah ya riga ya kawo mana sauk'i."

"Ka samo wata hanyar kenan?"

"Ban samo ba, kuma ba abinda zan samo, hasalima ba zaka je karb'ar award d'in ba, wannan dutsen ba zai tab'a shigowa hannunka ba."

"Ban gane ba..." Da tsananin mamaki Imran ya furta reaction d'in dake kan fuskarsa.

"Me kake nufi jaamil? ka san wannan dutsen shine dalilin duk abubuwan dake faruwa yanzu, shine dalilin shigowarmu cikin bil'adama kusan shekara guda kenan..ta yaya sai yanzu da komai ya kammala, Dr. turaki ya gama amincewa dani a matsayi wanda za'a bawa award d'in sannan zaka ce ba zan karb'a?

Idan har matsalar b'arin ruhina dake jikin Sa'adha ne na san zamu iya samo wata mafitar kafin sati biyun, amma ba zamu tab'a k'in cikawa Naani alk'awarin da muka d'auka ba..she has sacrificed alot don a kawo wannan lokacin saboda haka zamu k'arasa komai ba tare da saninta ba, na san in dai har na iya karb'ar dutsen na kai mata, ba zata takurani akan matsalar Sa'adha ba tunda ta samu abinda take so...sai dai kuma in nemi yadda zanyi da sareefa don Allah jaamil a yanzu ba zan iya rabuwa da Sa'adha ba."

Har ya kai k'arshen zancen jaamil bai katse shi ba, sai da yayi shiru sannan yace.

"Ban san ta yaya zan fara maka bayani ba yarima, amma abinda kake shirin ji yanzu zai karya zuciyarka."

Imran yayi focusing idonsa sosai yana kallonsa kwakwalwarsa na son tsinto yanayin da fuskarsa ke nunawa, yasha ganinsa cikin fushi, cikin b'acin rai, tashin hankali, mamaki, rud'ani da kuma ciwo...

Amma yanayin fuskar tasa a yanzu wani abu ne daya girmewa tashin hankali ko rud'ani, a cikin idanun bil'adamansa yana iya hango ainihin kwayar idonsa da tayi jawur duk da cewar baya kallonsa, ya tsirawa wata 'yar k'aramar flowerpot d'in dake gabansu ido ne kamar an cinna masa wuta, duk zagayen tunanin Imran ya kasa gano dalilin da zaisa jaamil cikin wannan yanayin.

"Naani ta yaudare mu yarima... bata turo mu samo dutsen nan don kariyar nahiyarmu ba kamar yadda ta fad'a."

Imran ya k'ifta ido jin hakan, kwakwalwarsa ta maimaita zancen ta k'ara maimatawa amma ya kasa gane me suke nufi.

"Kamar yadda kaji zancenmu da Naani, haka nima naji zancensu da Sareefa jiya bayan ta kira ni da saqon cewa in gaya maka ka kai Sa'adha wajenta gobe.

"Gobe? Ta gama dukkan shirin da tace zata yi kenan na cire ruhin daga jikinta?"

"Ba wannan ne mai muhimmanci ba." Jaamil ya fad'a yana ciro wani dunk'ulen abu daga aljihunsa, Imran ya riga ya san mene ne...HABLER, wani abu da suke recording murya dashi.

Ya bud'e shi a cikin tafin hannunsa, take wasu abubuwa kamar fuka-fiki biyu suka fito ta kowanne b'angare suka shiga kad'awa, a lokacin muryar dake ciki ta shiga fitowa.

Wannan muryar mai cike da kaushi da kuma k'arfin amo mai girgizarwa, kamar koyaushe Imran yaji sautin ta yana tab'owa har k'asan zuciyarsa. don yana iya jin yadda zuciyar tasa ke amsawa.

"Na fahimce cewa zuciyarki ta fara karkata akaina sareefa, kina ganin kamar bana sonki, kamar ina fifita su yarima fiye dake...a yau zan shaida miki wani abu da babu mahalukin daya sani...ina amfani da yarima da jaamil ne kawai don cimma manufar da zata gyara rayuwarmu ni dake, shi yasa na d'auke su na nunawa al'umma su na fifita su duk don zuciyarsu ta amince dani suji zasu iya sadaukar da rayuwarsu don yi min komai...!

Kamar yadda tun tasowarki kike ganin suna yi min aiki kala-kala, haka a yanzu ma na tura su yin aikin da shine dalilin d'auko yarima da nayi daga kwararo na gyara rayuwarsa na bashi dukkan wata kulawa daya rasa a baya.

Na taba gaya miki a baya cewa ina neman dutsen Nil, wani dutse da zai bani k'arfin da zaisa zuri'ata ta d'ore wajen mulkar nahiyar nan...toh daga baya mun samo dutsen a cikin bil'adama, wad'anda basu san amfaninsa ba sai kawai kyau da yayi musu suke ado dashi a matsayin kyauta, a lokacin yana wajen wani mutumi dake shugabantar wani kamfani saboda haka nayi niyyar d'aukowa amma sai farme ya shaida min cewa kona d'auka dutsen ba zai tab'a min amfani ba, k'arfinsa yana aiki ne kawai ga duk wanda ya same shi ta hanya mai kyau, ma'ana sai in har mai shi ya bani da yardarsa inba haka ba ba zai tab'a min amfani ba.

Tun a lokacin nayi niyyar tura dalak (Babban bawanta) a matsayin bil'adama yaje kamfanin mutumin har yayi aikin da zasu yarda dashi a bashi dutsen amma sai muka sake ganowa cewa ba kowa ne zai iya rik'e shi ba, sai irin d'aid'akun halittun cikinmu masu k'arfin ruhi, saboda haka nasa farme ya shiga nemo min irinsa.

A sannan ne ya gano wani bawa dake can nahiyar Sabeel, saboda haka mu karkata zuciyar mai shi ya taho muzaffar da niyyar saida bayinsa ya samu kud'i, bana so ko kad'an matashin bawan ya san inada hannu a cikin lamarinsa don haka muka shirya komai ya tafi a tsare, Farme ya kashe ubangidansa a daren da suka shigo Muzaffar sannan ya taimaka wajen kwance sark'arsa ya gudo. Sai bayan sati d'aya da shigowarsa cikin muzaffar sannan na shirya had'uwa dashi, shine a ranar da muka fita cikin kasuwa har dake ya taimaka wajen cetona daga fad'awa rami da Farme ya shirya komai, ni kuma nayi amfani da wannan damar na 'yanta shi na kawo shi cikin masarauta.

Ban tsara komai da jaamil ba saboda bana son cutar dashi a matsayinsa na d'an 'yar uwata, amma daga baya na fahimci alaqarsu tayi karfin da ba zan iya raba su ba saboda haka na barshi a matsayi mai taimakonsa nake tura su yin abubuwa kala-kala duk don su saba da hakan, sai da na fahimci zuciyar kowannensu ta yarda dani sannan na bijiro musu da buqatar samo min dutsen Nil, kuma ba wanda yayi musu a cikinsu duk da cewa basu tab'a wani abu makamancinsa va wato canja siffarsu su shiga cikin bil'adama.

Na tsara komai ba tare dana gaya musu ainihin manufata ba, sannan na tura su da dukkan wani abu da zasu nema yadda komai zai tafi daidai su samo dutsen kuma su danqa minshi da yardarsu! sai dai gabad'ayansu sun sab'awa umarnina a yanzu sunyi wani abu da babu shi a cikin tsarinmu...wani abu da zan d'auki mataki akansa duk ranar da suka gama abinda na tura su.

Saboda haka ki kore dukkan wani tunanin dake cikin kanki game da ina fifita su yarima akanki, K'arshensu ya kusa zuwa kwanan nan , daga lokacin da suka kawo min dutsen Nil, daga lokacin zan shafe tarihinsu daga tunanin al'ummar nahiyar nan gabad'aya, don hatta aurenki dashi na yarda da baikon ne wai don in k'ara samun yardarsa game damu ba wai don hakan zai kasance ba.

Ke kad'ai ce d'iyata Sareefa, ke kad'ai ce zan iya sadaukar da komai akanki...kuma saboda ke kad'i nake duk wannan tanadin!"

¡ñ©n¡ñ

So i can recall wata ta tab'a cewa Anya Naani son da take wa Imran na gaske ne ba wai don yana da wani abu ba?....so whoever you are nayi saluting d'inki! u guess right!...??

My humble readers, what do you think of this chapter ...?

And me kuke tunani Bwama zata ce game da cikin Nanne?

******

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

54

(¡î_¡î)

"Toh kin gansu nan, kala biyu ne...wannan da nono zaki samu ki dama shi wannan kuma da ruwa kawai in kinga dama ma ki watsa shi a bakinki haka, cikin cokali d'aya ya isa."

Nanne ta d'age hanci da gira tana kallon k'ullin magungunan da inna ke nunawa a gabanta, ita tunda aka bud'e k'ullin wani yellow taji cikinta ya juya, yoghurt d'in data sha na safe na shirin fitowa.

"Wai daga ina ma aka samo su?"

"Tun zuwan da nayi Niger na taho dasu a wajen malam na vonni."

Mamaki ya kamata, ta saki baki kawai tana kallon inna, ta kasa yarda cewa tun sanda suka je Niger da zancen aurenta inna ta karb'o mata maganin ciki.

"In zaki sha tea da safe ma kawai ki saka shi a ciki tunda na san baki fiye son nono ba."

"Inna nifa bana jin zan iya shan wannann abubuwan, ba komai ma nake iya ci ba."

"Haka kuwa zaki sha, ko kina sha zasu dawo baza a rasa mai amfanin da zai tsaya ba, wad'annan d'in da kike rainawa sune masu amfani amma ku kunfi ganewa kwayoyin turawa da zaku yi ta sha ana haifar 'ya'ya da cututtuka."

Ta fad'a tana janyo manyan ledojin da aka shigo dasu na tsarabar kayayyaki masu kyau da Nannen tazo dasu, komai a rabe yake don kowa a gidan saida ta d'auko wani abu da sunansa, hatta 'yan aikin gidan su lami sai da ta d'auko musu mayafai irin na mutanen can, inna ta shiga warewa tana fad'in kuma ya biye miki kuka yita kwaso kaya haka, amma can k'asan ranta farin ciki ne fal! na ganin tarin alkhairin da kowannensu baisa rai dashi ba, ta riga ta sani tun da Nanne bata da rowa ko kad'an, abin hannunta bai dame ta ba don bata k'i tayi kyauta da komai nata ba har kuwa ga wanda ba shiri suke ba, rashin kunyarta iya ta baki ce kawai.

"Ki d'auki fa magungunan kisa a jakarki."

Ba yadda ta iya haka ta d'auka tasa a handbag d'inta ba da niyyar sha ba, don tun zuwanta a yau da inna fahimci cikin dake jikinta tayi ta tambayarta game da zancen sunje asibiti da kuma yadda take jin jikinta, ba sai an fad'a ba ta san murna ce tsantsa a can k'asan ranta don tana iya hango kyallin hakan daga cikin idanunta sanda take gayawa Mama Azumi data shigo.

Zuciyarta ta karye da tunanin yaya zasu ji a lokacin da suka san irin sirrin da take b'oyewa, kafin zuwan Imran cikin rayuwarta bata taba tunani akwai wanda zuciyarta zata amince har tayi sharing sirrinta dashi bayan Inna ba, sai gashi a yau innan take b'oyewa sirrinta, sirrin wani abu da take ganin ya zama jigon rayuwarta...take kareshi da karya kala-kala a wajen innar tata.

Don ko awa d'aya bata rufa da zuwa gidan ba ta fara tambayarta game da zancen 'yan uwan Imran, ba yadda ta iya haka ta bud'i baki ta fad'i k'aryar cewa ai daga dawowarsu can bauchi suka fara sauka, sai da suka suka kwana biyu aka zagaya da ita cikin danginsa sannan suka taho. Jin haka yasa hankalin innan ya kwanta ita kuma nata ya karkasu waje da yawa.

A cikin wajajen harda wani waje mai kama da damuwa ganin cewar dukkansu basu san irin cikin dake jikinta ba kuma basu kawo zaton komai a ransu ba, mama halime ce kawai data shigo tace mata in ta koma asibiti tayi complain akan idanunta don k'asansu yayi rami kad'an, basu san cewa ko sau d'aya bata bi hanyar asibiti ba, kuma bata jin har lokacin haihuwarta zata nemi asibitin.

Bwama ta riga ta gama yi mata duk wani therapy da take buqata kuma ta gaya mata abinda a kwanakin baya take jin zata iya saida ranta don ta ji shi, Abinda ya zama dukkan wani fata da burinta a lokacin da Imran ya dasa ayar tambaya game da cikin nata.

Allah ya sani a lokacin da yake gaya mata b'arin ruhinsa yana tare da ita, taji tsoro kad'an don bata son sake experiencing abinda taji a baya, har wani part na zuciyarta yayi fatan dawowar Naani don a cire shi, amma daga sanda bwama ta dubata, ta ganocewar wannan b'arin ruhin shike rik'e da cikin nata, ta mik'a godiyarta ga Allah da har a lokacin ya kasance a jikinta, don tace ba don shi ba, babu ta yadda za'ayi cikin Imran ma ya iya zama a jikinta kona 'yan mituna...jikinta is too weak

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login