Showing 102001 words to 105000 words out of 113985 words

Chapter 35 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28477

then...

Bakinta ya bullutso da wani tarin jini daya tarwatse har cikin falon!

Matar dake tsaye daga waje tayi murmushi a hankali sannan taja k'ofar ta rufe!

¡ñ©n¡ñ

How many cliffhangers do you notice in the two chapters?

Meye k'arashen abinda ya faru tsakanin Imran da Naani a ranar da zai karbi Award din nan?

Shin ya ma karb'a tukunna?

Ina jaamil yake all this while?

Wacece Safiyya maman Hidaya?

Me Imran yayi sensing game da ita ya b'oyewa Sa'adha?

Me ya faru da Nanne?

Wacece matar da ta gani da ta bud'e k'ofar?

Me tayi mata?

Me ya tsaida Imran a ranar?

What will happen next?

Do you think the Baby is coming?

Allah ya sada mu da alkhairi!


WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

58


(¡î_¡î)


TARIYAR BAYA (FLASHBACK)

K'ARSHEN ABINDA YA FARU TSAKANIN IMRAN DA NAANI WATA UKU BAY'A.

"Me yasa?...

Muryar ta fito da kaushi kamar koyaushe, cikin amonta mai girgizarwa.

"Me yasa zuciyarka ta juya min baya?"

Imran ya d'ago da idonsa ya kalli manyan-manyan hallitun dake tsaye a gabansu basa bada ko karamin motsin da zai nuna cewa suna raye, a wancan lokacin d'akin da suke tsaye nasa ne shi kadai, amma a yanzu wannan d'akin da suke ciki mallakinsa ne shi da Sa'adha.

Sa'adhar dake rik'e cikin jikinsa a sume, tun bayan kallon farko da ta yiwa halittun tsananin tsoro ya d'auke numfashinta, tsananin tsoron ganin irin siffar da Allah bai halitta idanunta na bil'adama jurewa kallo ba.

Zuciyarsa a rikice take, yana fatan suman nata ya tsaya a iya suma kawai, kar ya lahanta jikinta ko kuma halittar dake cikinta, amma duk da haka idanunsa sun gagara d'aukewa kallon wannan dunkulallen hasken dake lilo a iska, hasken daya tarwatse ya baje ko'ina a cikin d'akin, hasken dake nuna tambarin irin na adon sarautar NAANI.

"Na dad'e da sanin cewa Bil'adama butulun mutane ne, amma ban taba sanin cewa butulcin nasu har zai iya shafar jinsin daba nasu ba don kawai kwaikwayon halitta ya shiga tsakaninsu... haka ban taba sanin cewa akwai ranar da umarnina zai zama abin wofantarwa gare ka ba yarima, ni din dana zama duk wani gata da tallafin rayuwarka, wane daraja kake dashi bayan tawa? wace rayuwa kake da ita bayan wadda na baka?

Nice zahirinka! nice sanadin duk wani abu daka samu a cikin jinsinka da kuma wannan rayuwar da baza ta taba d'orewa ba, na kawo ka cikinta ne don ka cika min burina ba wai don ka gina sabuwar rayuwar tare da wannan k'azamar halittar ba, k'azamar halittar da har zata sa ka iya yaudara...

"Yaudara...?"

Muryar Imran ta katse ta cikin kaushi da kuma tsananin b'acin rai, abinda ya haddasa motsin wad'annan halittun dake gabansu don hakan wani abu ne na farko da d'ayansu bai taba gani ba, in har akwai wanda ya tab'a yin katob'arar hakan, toh tabbas baya raye balle har ya iya bada labari.

Shi kansa Imran sai da yaji sanyin jikinsa lokacin da idonsa ke manne akan hasken daya tabbata tana iya hango shi ta ciki, shugaba kona kwaikwayo ne kuwa akwai kwarjinin da yake dashi, amma ya yak'i zuciyarsa da tunanin maganganunta na cikin habler nan ya fadi abinda yake ganin gaskiyarsa ne.

"Har zaki iya amfani da kalmar yaudara akaina? har zaki iya furta ta bayan kece abu na farko daya kasance a cikinta... rayuwar da kike tak'amar kin bani bata cike da komai face tarin yaudara wadda kika lullub'e don samun amfanin kanki, ba don tallafina ba kamar yadda kike tink'aho tsawo shekarun nan.

Munji komai daga gare ki lokacin da kike gayawa Sareefa sirrin da kika dad'e kina b'oyewa, babu sauran wani abu da zaki kara rufe mu dashi, maganganun da duka fito daga bakinki sun haska mana duhun da kika dad'e da samu a ciki don amfanin kanki da kuma diyarki , ba don kariyar al'umarmu ba kamar yadda kike ikirari, Allah ya sani na soki kuma na girmamaki da dukkanin zuciyata, ina ganin cewa kin maye gurbin duk wani dangi nawa dana rasa, ban fahimci cewa kina sani hak'a ramin dake ta yin k'asa dani bane... kuma abin mamaki harda d'an 'yar'uwarki, wadda ta sadaukar da abubuwa da yawa a rayuwarta saboda cigaban ki, amma kike tanadin sa mata bak'in cikin da zai tsaida zuciyarta, ki kashe d'anta saboda samun cigabanki.

Farin ciki na daya ban taba d'ora raina akan kwadayin samun sarautar da kika yi ta mak'ala min ba, balle har in d'ora raina wajen son d'iyarki, saboda haka a yanzu bana tunanin tsakani na dake akwai wani abu kuma da yayi saura.

Da gaske ne, na karbi dutsen NIL a yau, dutsen da kika d'auko ni kika 'yanta ne saboda shi, dutsen da kika sadaukar da abubuwa da yawa akansa, sannan dutsen da a yanzu ya zama mallakina zan iya sarrafa shi ta hanyoyi masu yawa, hanyoyin dana yanke shawarar baza su taba giftawa ta gabanki ba.

Na riga na san amfanin dutsen nan a yanzu, na san irin kariyar da yake bawa duk mamallakinsa, irin kariyar da duk karfin iko da tsafinki ba zaiyi tasiri akansa ba, shi yasa kike nemansa ido rufe... don ki k'ara girma da martabar sarautarki yadda ba mai iya ganin bayanki, saboda haka tsarin da muka yi tun farko ya wargaje Naani, ba zan taba baki dutsen nan ba kuma kema ba zaki tab'a iya tunkarata ba, na zabi in zauna a wannan rayuwar fiye da rayuwar k'aryar da kika d'ora ni akai.

Wannan shine zahirina Naani, saboda haka godiya d'aya zan miki, ta jikin bil'adaman da kika iya sarrafa min!"

A wannan lokacin Imran ya tabbata in har Naani tana jinsa toh tabbas mamaki da rud'anin maganganunsa sun lullub'e kwakwalwarta, saboda kowacce kalma daya fad'a.. every single word abu ne da bata taba zata ba, bata taba zaton sunji kalamanta da sareefa ba sannan bata taba zaton akwai ranar da zasu san b'oyaiyiyar manufarta game dasu ba.

Sunfi karfin awa d'aya zaune a hakan ba tare da ta sake magana ba, Imran ya riga ya sani, ita din a koyaushe ba mai tada hankalinta bace, duk yadda abu ya kai ga rikicewa da kuma hargitsi, zata bishi ne a sannu har ta sami lagon da zata ci galabarsa, Abu d'aya dake burgeshi game da tsarinta, sannan kuma abu d'aya da yasa ta sami sarauta akan 'yar'uwarta!

A cikin tsawon wannan lokacin, Imran ya san ba don k'arfin radiation d'in dutsen Nil dake fita daga hannunsa ba, babu abinda zai hana wad'annan halittun kawo k'arshen rayuwarsa shida Sa'adha dake rike a jikinsa, don suna fahimtar umarnin Naani ba tare da ta furta ba... sai dai a wannan karon daga ita har su d'in basu da karfin karasowa kusa dashi.

"Zamu gani yarima, lokaci zai baiyana abinda alkalami ya riga ya bushe akansa!"

Ya lumshe idonsa a hankali lokacin da daga hasken har halittun suka b'acewa ganinsa, ya san sarai me maganganunta suke nufi, zata nemo jaamil ta hukunta shi akansa, bata san cewa nasu tsarin yafi gaban tunaninta ba, yadda yayi wa kansa katanga daga gareta, haka ma bazata taba iya tunkarar jaamil ba.

A hankali ya ware tafin hannunsa d'aya, rabin dutsen Nil ya baiyana akansa, rabi kuma yana tare da jaamil da Bwama.

****

Jikin Nanne wanda gabad'aya ya baci da jinin dake fitowa daga bakinta ya shiga jijjigawa tare da d'agawa kamar wutar lantarki na janta sannan idanunta dake zare basa d'auke da wani emotion. They were pale and blank!

Hargitsin dake faruwa a cikin cikinta shine jigon girgizar jikin nata, don daga kowacce kusurwa ta k'aton falon kana iya jin k'arar karyewar wani abu da kuma ruk'urkushewarsa.

A cikin k'arar, muryoyin Bwama, jaamil da kuma Imran ke amsawa cikin k'arfi da kuma ihun da baza ka iya rarrabe kalmomin da suke fad'a ba.

"lazzu nah se ka our tad to jikal vanmbiyarda jo! (Ka rik'e ta sosai yarima, kar ka bari ta fita daga hannunka, we can do this!)

Muryar Bwama ta fad'a tana kallon Imran wanda ke rik'e da Sa'adha a jikinsa tana jijjigawa da wani irin k'arfin dake neman gagararsa, ba zaka iya tantance cewa k'arfin abinda ke cikinta ne kusan d'aya da nasa ba ko kuma raunin dake mamaye dashi ne na ganin Noorynsa cikin wannan mummunan halin, idanunsa na manne da nata dake a zare hawaye na zirara ta kowanne gefensu, don ba zai iya kallon sauran jikinta ba, sauran jikinta dake cikin azaba... sauran jikinta da k'arar karyewarsa ta cika kunnunwansa, he was afraid to save the memory in his head!

"Babu iska a cikinta... jijiyar dake bada iska ta tsinke!" muryar Bwama ta sake ihu a cikin kunnensa.

Somewhere in the lost zone, Nanne ta dawo haiyacinta a wannan lokacin tayi magana da wata irin murya mai k'arfi da bata yi kama da tata ba.

"Ku cire shi!" Ta fad'a da k'arfi!

"Do it now! ku fito dashi zai mu..."

Kafin ta k'arasa wani tarin jinin ya bullutso daga bakinta ya fallatsa a kowanne direction, da sauri Imran ya d'ago da kanta kad'an yadda ragowar na bakinta zai fito.

"Wourjuoni!"

Muryar Bwama ta fad'awa jaamil da karfi cikin abinda baifi kiftawar ido ba ya mik'o mata wani dogon abu mai kama da allura, a cikinsa wani koren ruwa ne irin nasu dake kashe zafin waje, Imran na ganin haka ya k'ara rik'e ta yayin da Bwama tasa hannu ta yage kusan rabin doguwar rigar jikinta, jaamil ya juyar da kansa gefe.

"Ka samo mata iska... ka samo mata numfashi, lour ni biryam!"

Muryar Bwama ta sake bashi wani umarnin.

Imran ya sunkuyar da fuskarsa kan tata da sauri, yayi pressing lebb'ensa akan nata masu laushi sannan ya shiga hura iska cikin mak'ogwaronta da dukkan k'arfin da zai iya, zak'in ragowar jinin dake bakinta ya gauraye a nasa bakin, yana iya jin yadda zuciyarta ke bugawa a hankali daga can k'asan k'irjinta.

Keep it going!

Ya ayyana da k'arfi a cikin kansa.

You promise Sa'adha, kin min alkawari! Stay with me, kina jina? Stay! keep your heart beating!

Ya tsaya da hura mata iskar sanda Bwama ta zura abun cikin fatar hannunta, zafin wannan koren ruwan da ya shiga bi cikin jijiyarta yasa jikinta k'ara girgizawa da k'arfi, Imran yasa karfinsa ya k'ara damk'e ta sosai cikin hannunsa, Sai da ya gama shiga duka sannan Bwama ta zare abun da sauri, a lokacin ne kuma wata k'arar karyewar wani abun tayi cracking daga cikinta sannan jikinta ya bar girgizawar, k'arar data sa kowannensu ya tsaya cike da tsananin tsoro, sannan idanunsu suka k'ame akan nata cike da tsabar hanqoro da kuma rok'o, rok'o kar tunaninsu ya zama gaskiya wajen fatan samun wata alama daga gareta, any single thing! ko da kuwa motsin gashin idonta ne amma ba abinda ya biyo baya...

Jikinta ya tsaya cak! kamar wani abu ya daskarar da ita ne a lokaci guda.

"Me ya faru??" Muryar Imran choked in horror sanda ya juyo yana kallon Bwama da tsananin fargaba.

"Lakarta ta karye... Ba abinda jikinta zai iya yi yanzu!"

****

A wannan lokacin, azabar da Nanne take ji ya maye gurbi da wani irin rad'ad'in ciwon baya wanda yasa taji numfashi ya tsaya a makogwaronta, taji kamar kowanne k'aramin particles na jikinta yana b'angarewa ne daga jikin d'anuwansa... slicing apart!

Zafin ya cigaba da blazing a jijiyoyinta, taji kamar ta mike ta tafi a guje ko zata oya barin ciwo anan inda take amma ta kasa motsa koda hannayenta, wani irin nauyi ya manneta a jikin Imran dake rik'e da ita, kamar an dora k'aton dutse akan kirjinta, wanda nauyinsa ya binne ta cikin azababben ciwon dake tafiya yana mamaye sauran gab'ob'in jikinta, spreading with impossible pain through her shoulders and stomach!

Me yasa jikinta ya bar girgizawar da yake yi? me yasa ta kasa motsi? me yasa take jin nauyi a jikinta? Tunaninta a fik'e yake da azabar da take ciki saboda haka kwakwalwarta was so clear da ta fahimci abinda Bwama ta fad'a a daidai wannan lokacin, kamar mai amsa tambayarta.

"Lakarta ta karye... Ba abinda jikinta zai iya yi yanzu!"

This was'nt part of the story, ta san tasha gaya wa kanta irin mutuk'ar wahalar da zata sha duk sanda da wannan ranar tazo amma bata tab'a kawowa wai abubuwa zasu rincab'e haka ba, Lakarta ta karye? Ta yaya lakarta zata karye? Kenan shikenan yanzu ba zata iya motsa jikinta ba? Ta yaya kenan Babynta zai fito... da wane karfin zata iya kawo shi duniyar da take ta tanadar masa tsawon lokaci?

A sannan hankalinta ya d'aukar mata cewa babu muryoyin da a d'azu take iya ji sun zagayeta suna k'okarin ceto ransu, ransu ita da babynta... saboda bayan wannan maganar da taji komai ya d'auke, ya d'auke gabad'aya.

Ina Imran yake? me yake tunani alhalin yaji me ya faru, ance jijiyar dake bawa Babynsu iska ta tsinke me yake jira? jiran me ake bayan Babynta yana mutuwa... Babu shiri ta yunk'ura da dukkan iyawarta ta kira sunansa, sunansa direct don ta janyo hankalinsa.

Sai dai rabin harafan suka fito k'arashen kuma ya koma sakamakon wani sabon ciwon daya dawo ya soke ta a tsakiyar cikinta, ta tattaro dukkan k'arfinta ta daure hakan kuwa yasa idonta ya sake cika da duhu, ta kasa ganin komai amma kunnenta na iya d'auko mata sautin muryoyin da a yanzu suka cigaba da fafutuka da kuma ihu akanta sakamakon alamar data basu cewa tana raye, fuskar imran ta sake sunkuyowa sannan iska ta cigaba da shiga cikin huhunta, tana busawa da zafi a ki'rjinta.

"Stay Sa'adha, dan Allah... you promised!"

Muryar tasa ta busa a cikin bakinta, so weak yadda bata tab'a jinta ba.

I'm trying...!

Taso kwarai ta iya gaya masa hakan, ta gaya masa cewa tana kokartawa da dukkan iyawarta wajen cigaban bugun zuciyarta ba don kanta ba sai don ta raya abinda ke cikinta har ya k'arasa fitowa kar burinta ya tashi a banza... sannan kuma don tarin mutanen da tasan zata ruguza wani b'angare na rayuwarsu in har babu ita. Imran a farko, mijinta da rayuwarta da tasa ke nannad'e jikin zare d'aya, in har babu ita bata san ya duniyarsa zata kasance ba.

Sannan Inna-- tsohuwar data raine ta lokacin da ta rasa duk wani gata da tallafin UWA, tsohuwar dake mutuk'ar sonta fiye da kowa da komai a rayuwarta, Would she hurt her again? bayan b'oye mata sirrin Imran da tayi?

Ga Baffanta ma, bawan Allah dake ganin ya cuci rayuwarta wajen aurar da ita da wuri, me zai yi tunani a yanzu in har babu ita? Ta san kuma ko yaya ne Nuratu ma zata azabtu da rashinta, bata da shak'uwa da ita amma akwai k'auna da Allah ya halitta a tsakaninsu irinta d'a da mahaifi.

Ga tarin 'yan gidansu ma, Rahma, Mama Azumi, Sadiq da duk wasu ahalinta... she'd to survive for them, in ba haka ba a wannan azabar da take ji her life means nothing to her! ciwon da take ciki mai tsananin azaba ne da take jin kamar zata iya sakin komai ta sallamawa duhun dake shirin lullub'e idanunta, ta barshi yaci galaba a kanta, yaci galaba wajen tura ta zuwa wannan k'arshen da ta san zata rabu da duk wani ciwo... Mutuwa!

Amma wannan tunanin shi ke sawa ta tattaro duk ragowar k'arfin jikinta wajen rik'e Babynta, don duk yadda ta kai ga son rayuwa saboda ahalinta, it was not the same as the gut- wrenching terror da take ji wajen tsoron rasa shi, dole ne ta sami hanyar da zata cece shi ko da kuwa hakan zai zama abu na k'arshe a yanzu da zata iya yi... Don shine Babban fatan zuciyarta, zata iya hakura da duk wata wahalar da zata sha amma banda rasa Babynta.

It was the only thing she had to save!

Sai dai ciwon dake yankar k'irjinta a daidai wajen saitin zuciyarta felt so real... tayi k'okarin ture shi tare da sake lalubo tunanin Babynta... abinda ta san cewa dashi zata iya yak'ar kowanne irin ciwo a jikinta.

Zafinsa ya cigaba da k'aruwa. Sosai da sosai, Sosai data kasa tantance ko yanka wajen akeyi ko kuma ruhinta ne ke kokarin fita, the pain was too much!

Taji kamar ta mik'a hannayenta ta danne wajen ko zata ji sauk'i... but there was nothing a jikin hannayen nata, not a single twitch! su d'in a yanzu ba komai bane face wasu matattun abubuwa dake rik'e cikin hannun Imran, hannunsa da baza ta iya sake shafawa ba har abada!

Ciwon ya cigaba da d'agawa-- yana k'aruwa yana d'agawa har saida ya shafe duk wani ragowar k'arfin jikinta! A lokacin ne kuma abun ya faru, abinda ya zamo fata da kuma jigon rayuwarta tsawon wani lokaci... abinda ya zamo sanadin dukkan wata gwagwarmaya da kuma k'addarar rayuwarta!

THE BABY!

Kicking her ribs apart! yana b'alla duk wani abu na cikinta da ya zama a hanyarsa ta fitowa lokacin da wani abu mai kaifi ya yanka fatar cikin nata hanya ta bud'e, hanya mai fad'i data zama mafarin fitowar halittar dake cikinta tsawon watanni bakwai!

****

Imran ya runtse idonsa lokacin da k'arar yankawar fatar Sa'adha ta cika kunnensa, ya damk'e hannayeta sosai a cikin nasa wajen tsaida kansa kokarin hana Bwama tsaga jikin nata da zuciyarsa ke tursasa shi yayi... ya san its for their own good babu wata hanyar bayan haka, babu wata hanyar da zasu raya abinda ke cikinta bayan a bud'e cikin nata don a yanzu ko yatsanta baza ta iya d'agawa ba, balle ayi zancen karfin da zata iya haihuwarsa da kanta. Ya cije lebbensa na k'asa har sai da hak'oransa suka datsa ciki yayi zurfi.

Bayan wannan k'arar yankawar fatar cikinta, wata k'ara ce ta biyo baya... wata k'ara da ta firgitashi yaji kamar an jona wutar lantarki ta cikin jijiyoyinsa, it was terryifying and unexpected! k'arar b'allewa da dagargajewar abu daga cikinta, alamun koma meye a cikin nata yana fighting hanyarsa ne ta fitowa a yanzu da ya sami hanya.

Don hana kansa ganin hakan da kuma k'ara bawa jikinta k'arfi, ya sake sunkuyar da bakinsa kan nata ya cigaba da hura mata iska cikinta, hakan yasa tayi wani d'an guntun tari idanunta dake kusan a rufe suka juya blindly kamar mai k'ok'arin lalubo wani abun.

"You stay with me now Sa'adha!" Ya fada da k'arfi sanda k'arar fitowar Babynsu daga jikinta ya cika kunnensa.

"Kina jina? stay! Ba zaki tafi ki barni ba... keep your heart beating! kinyi alqawari!"

Idanunta suka sake juyawa, kamar tana so ta lalubo shi a cikin blankness d'insu, duk da bata ganinsa ya tsaida nasa a cikinsu sannan ya k'ulle su bada niyyar daina kallonta ba.

And then, sai jikinta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login