Showing 96001 words to 99000 words out of 113985 words
iya ci take ba, sai dai tunda ta fara zuciyarta ke tashi tana ta yin k'ananan amai akai-akai, amma bata fasa ba don ta dake zuciyarta cewa zata yin.
Kusan minti talatin tana aikin suna 'yar hirarsu jefi-jefi da hidaya tana mata tambaya game da kewayen unguwar da kuma makarantarsu, wata amsar ta gane, wata kuma ta had'e cikin jagwalgwalon gwarancinta...
Bayan wani lokaci ta tsinci muryar Imran daga k'ofar kitchen d'in lokacin ta gama sauke abincinta, tana had'a samosan da take yi, kafin ta k'arasa amsa sallamarsa taji hannayensa guda biyu sun zagaye k'ugunta.
"I'm back!" Muryarsa mai taushi ta fad'a dab da kunnenta, numfashinsa ya busa akan fatarta, taji tsigar jikinta ta tashi.
"Sannu da zuwa." Ta fad'a a hankali.
"Mhmhmm." Ya amsa softly yana grazing fuskarsa a cikin wuyanta, taji k'afafunta sunyi sanyi amma duk da haka ta karkata kanta kad'an don ta bashi more space.
"You feel warm habibty..."
Abu ne mai mutuqar wuya idan Imran na tab'a ta ta iya wani tunani mai kyau, saboda haka it took her a minute of scattered concentration kafin ta iya tuna cewa Hidaya na zaune a bayansu, da sauri ta juya game da d'an ture shi amma ga mamakinta ba kowa a zaune wajen island d'in nan, sai tablet dake kan table.
"Ayunie Hidaya tana ina?"
Girarsa biyu ta had'e waje guda.
"Hidaya? Wace ce ita?"
"Baka ganta ba, tana zaune fa anan."
Kafin yayi magana ta kwance hannunsa dake rik'e da ita sannan ta bazama cikin gidan tana ta faman kiran sunan Hidaya.
Imran yabi ta da kallo cike da mamaki, wace ce kuma Hidaya, a ina ta samo ta? A ina ta sami wata yarinya mai suna Hidaya? yaji gabansa ya fad'i wani abu mai kama da zargi ya d'arsu a zuciyarsa, tun bayan abinda ya faru tsakaninsa da Naani, zuciyarsa bata tab'a hutawa ba, don wani abu ne da ya zamo....
"Hidaya...kina ina?"
Muryarsa ta katse tunaninsa, yana iya jiyo yadda bangwayen saman gidan ya d'auka da sound d'in muryar tata. Ba shiri ya ajiye ledar Coco pops d'in daya shigo dasu har guda uku yabi bayanta.
¡ñ©n¡ñ
So wacece Hidaya?
Me ya faru tsakanin Naani da Imran a cikin watanni ukun da muka tsallake?
Just hang in there...muna ta gangarawa dai! ??
Waye ya iya karanta yaren su Imran a muryar Bwama???
@Shamsiyer, The Gardenscapes game is dedicated to you...!??
*****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
56
I'm so sorry na san nace zanyi updating jiya but Allah bai bani dama ba!
@RashidaMuhammad4...??
(¡î_¡î)
TARIYAR BAYA! (FLASHBACK)
ABINDA YA FARU TSAKANIN IMRAN DA NAANI WATA UKU BAYA.
"Duk sanda kake tare da ita wannan b'arin na jikinta yana mstsowa dab da gab'ar nata ruhin, yadda wanda ke jikinka zai iya sensing nata, saboda haka in har tana kusa da kai... zaka iya karb'a ba tare da wanda ke jikinka yayi raunin da zai maka illa ba."
Imran ya gyara zamansa yana kallon zanen taswirar bayanin da jaamil ke nunawa a gabansa, idonsa ya kai kan zanen wani dunkulen abu dake tarwatsewa kamar yana fitar da wani hayak'i, ba tare da ya tambaya ba jaamil ya bashi amsar da yake nema.
"In har aka samu matsala, ta haka ruhin dake jikinka zai fara k'onewa."
"Bai kamata mu saka matsala a cikin lissafinmu ba, insha Allah komai zai tafi daidai, sai dai abinda nake tunani kayi wannnan binciken ne tun kafin mu san da cikin Sa'adha, a yanzu kuma baka tunanin k'arfin dutsen zai iya shafarta ta wata hanyar?"
Jaamil ya d'anyi gajeren tunanin kafin yace.
"Ai d'aya b'arin ruhinka yana jikinta, kuma karka manta a zuciyar Dr. Turaki kai ya nufa da zai bawa, saboda haka bana ganin wani abu zai faru tunda har da wanda ke jikinka da nata kusan d'aya ne, saboda haka k'arfin dutsen ba zai illata ta ba ko kad'an."
Imran ya gyad'a kansa alamun ya fahimta, yayin da idanunsa ke nuna zurfin tunanin yadda komai zai kasance kamar yadda suka tsara.
"Har yanzu bata fara susupecting komai ba?" Muryarsa ta tambaya sanda jaamil yake nannad'e takardar.
"Ba abinda tunaninta ke kawo mata, zuciyarta ta riga ta yarda damu cewa baza mu tab'a fasa bin umarninta ba kamar yadda a baya ta sa mana yardarta, shi yasa da na gaya mata cewar sai nan da jibi zaka kawo ta ba tayi tunanin komai ba, ta yarda cewa bama son a samu wata hanyar da mutane zasu zarge mu ne... shi yasa zamu bari ta fara rashin lafiya tukunna kafin a fitar da ita daga haiyacinta."
Imran ya d'ora tafin hannayensa da ya had'e waje d'aya akan lebbensa sannan ya huro iska ta cikinsu, dogwayen gashin idonsa suka had'e da 'yan uwansu na k'asa sannan muryarsa ta fito cikin kaushi.
"Zata sha mamaki jaamil, I will make her pay!"
****
Taron kamfanin ya fara gudana ne da misalin k'arfe hud'u na ranar Alhamis a watan August, a wani open park dake can hanyar barin gari waje ne k'ato da aka cike shi da shuke-shuken bishiyoyi masu cikar ganyayyaki kuma cikin wani tsari mai ban sha'awa, sannan k'asan wajen gabadaya grass carpet ne mai taushi anyi cutting dinshi so low ga kuma shukar flowers kala-kala a zube ko'ina da suke serving as fragrant!
Daga farkon inda zaka shigo wajen ma wasu tarin fulawoyin ne da aka rataye su daga can sama cikin haruffan da suka bayar da...
ORZ AT 40!
Anyi setting din wajen kamar yadda turawa suke irin parties dinsu, babu kujera ko daya da aka jera in ka d'auke ainihin resting chairs na cikin park d'in, tebura ne kawai a ajiye tsill-tsilli cikin adon yadi da flowers pink, akansubakwai tarin lemuka da snacks da aka jera, kowanne gaban table kuma akwai mutanen dake tsaye rike da lemukan ko snacks anata gaisawa da murmushi ta cikin cool music d'in dake tashi a wajen.
Wani abin sha'wa kuma, akwai wasu fitulun ado dake rataye a jikin bishiyun cikin different colours pink, blue, yellow, red...round dasu irin fitulun 'yan china. Daga can inda yake facing tables d'in high floor ne cikin ado na pink flowers akwai mike da kuma tarin Awards d'in da aka kange cikin wani box na glass.
K'arfe hudu da rabi daidai Imran yayi parking hadaddiyar Hyundai d'insa cikin jerin gwanon motocin dake jere a wajen.
"Welcome to my success habibty!" Ya fad'a yana kallon Sa'adha dake zaune a gefensa.
"I'm so so proud of you Ayunie!" Ta fad'a da murmushi.
A lokacin cikinta baiyi girma sosai ba, saboda haka ya b'oye tsaf! cikin doguwar maroon rigar da tasa mai small prints d'in pitch flowers a jiki, tayi rolling da wani tattausan mayafi shima pitch colour, fuskarta ba kwalliya sai rambad'eden kwallin da ta saka a sama da k'asan idanunta wanda ya k'ara fito da girmansu ya kuma b'oye d'ashewar da suka yi.
Rigar was so flowy da bayan sun fita ta dinga ja akan grass carpet d'in, Imran ya rike hannunta cikin nasa suka nufi wajen wasu kofofin glass masu duhu da suke hanyar shiga wajen, Nanne ta d'aga kai ta kalli hadaddun flowers d'in nan da suka rubuta.
ORZ AT 40!
Ta shak'i fresh k'amshinsu ya arce har k'irjinta, tun kafin su shiga ta san cewa wajen ya had'u saboda haka taji ta matsu d'imbin mutanen da Imran ke introducing d'inta a wajensu su k'are don su shiga ciki, sai dai ta kula kowannensu d'okin ganinta a matsayin matar Imran yake.
"Ah, Imran tun d'azu nake jira...you're a bit late."
Wata sassanyar murya tasa Nanne juyowa daga kallon hanyar da mutane ke shiga, idanunta suka ci karo da wadda ke k'arasowa gabansu, wata kyakkyawar mace cikin shiga da kwalliya ta alfarma, kalar fatarta so cream mai kyau, sannan manyan idanunta cike da kyallin farin ciki sanda ta tsaya a gaban Imran, matsatstsiyar doguwar rigar jikinta kalar fara nata haskawa cikin lumshin yammar, yankan rigar was so skillfully ta yadda hakan ya fito da duk wani rise and dent (d'agawa da tashi) na jikinta.
Imran ya d'an taka baya kad'an ganin yadda ta tsaya dab! dashi, sannan ya juya da fuskarsa yana murmushi ya kalli Nanne.
"Noory ce ta tsaida mu, she kept redoing her veil wai baiyi kyau ba kafin a samu wannan ya tsaya."
Shi bai gani ba, amma Nanne da idanunta ke kanta tsaf taga giftawar b'acin rai k'arara a fuskarta kafin wani munafukin murmushi ya maye gurbinsa.
"Let me introduce you to my wife."
Taji ya sake rik'o hannunta, tun da suka tsaya a wajen abinda yake fad'a kenan, amma Nanne bata ji dad'in kalaman ba irin yanzu da yake fad'a a gaban wannan mai kama da shahararrun 'yan duniyan da bata san ko wacece ba, shi kansa a cikin muryarsa ta fahimci wani abu kamar tink'aho da kuma alfahari.
"Habibty wannan itace maryam 'yar office d'inmu, and maryam this is my Sa'adha!"
Ta had'iye k'ullutun wani abu a mak'ogwaronta sannan ta matso ta kamo hannun Nanne.
"Barkanki da zuwa duniyarmu ta ORZ Sa'adha, it's nice to finally meet you."
"Ofcourse." Nanne ta amsa cikin sanyin muryarta. "Its nice to meet you too!"
Maryam ta gyad'a kanta sannan ta juya tace da Imran.
"Ina jin su Ibrahim sun k'araso bari in duba."
Da wannan excuse d'in ta saki hannun Nanne da yasha wani jan k'unshi tar! dashi sannan ta juya cike da d'acin rai, Imran ba zai tab'a zama nata ba, ta biyawa zuciyarta abinda ta shafe wata da watanni tana haddacewa, amma maimakon zuciyar ta karb'a sai ta dawo mata amsar cewa.
Dama kema kinyi jan k'unshin!
Kafin Nanne ta k'are kallon rigar jikin maryam, Imran ya jata zuwa gaba inda mutane ke ta layin shiga, sasassanyar yammar watan August ta sake haska kyan da kowannensu yayi!
Sai dai suna taka k'afarsu cikin wajen, duk wata jijiya ta jikin Imran tayi sensing k'arfin radiation d'in dake jikin dutsen Nil, a lokaci daya kuma idanunsa suka masa zooming can cikin wannan box d'in dake d'auke da tarin Awards, kuma ba tare da b'ata lokaci ba kyallinsa ya haska a idanunsa fiye da duk sauran stones d'in dake jikin kowanne Award...
"This is beautiful! Zamu dad'e a wajen nan dan Allah?" Muryar Sa'adha a gefe ta katse tunaninsa tana kallon adon wajen.
Bayan kusan minti talatin, gaisuwa da gabatarwa suka cigaba da gudana wajen, kusan saida Imran da Nanne suka gaisa da kowa a wajen har kuwa da 'yan other companies d'in da aka gaiyata, daga nan kuma bayanai suka fara...Shamsudden da yake a matsayin MC shi yayi leading taron wajen kiran mutane d'aya bayan d'aya dake zuwa suna bada speech d'insu kan abinda ya shafi kamfanin... success, challenges, failure, competition, achievements da duk dai wani abu da ya kasance da kamfanin tun farkon had'a shi, don an gaiyato manyan mutane ma da tun farko aka kafa kamfanin dasu.
Imran shi yayi bayanin achievements d'in da kamfanin ya samu cikin shekara d'ayan da yake nan, wajen ya d'auka da lallausan turancin dake fita daga bakinsa yayin da idanunsa ke kan Sa'adha, wadda tayi masa tsananin kyau fiye da kowa a wajen, kalar mayafinta ya k'ara haskawa da fito da kyan fuskarta.
Sannan ga d'an bump d'in cikinta da yake iya ganowa, bump d'in dake bearing babynsu ita dashi... his child! wani abu da bai tab'a tunanin zai samu da ita ba, abun dake dad'a tabbatar masa cewa itace duniyarsa... gabad'aya duniyarsa tsaye tana kallonsa da alfahari cike a idanunta.
Sai wajen Shida da rabi sannan lokacin da Imran ke jira ya k'araso, lokacin da yayi tanadi ta tsumayinsa tsawon shekara guda, lokacin da duk wani canjinsa ya faru saboda shi, lokacin da ya zamo silar gata da tallafin rayuwarsa tun a farko, lokacin da ya shigo da Sa'adha cikin k'addararsa kuma ya mayar da ita duk wani hope d'insa a yanzu, sannan kuma lokacin da zaiyi determing fansar da zai d'auka akan Naani, fansar da zai hana ta abinda ta dad'e tana muradi, abinda ta sadaukar da abubuwa da yawa nata don kawai ta same shi.
Shamsudden ya sake gaiyato Dr. Turaki kan high floor d'in a karo na uku bayan bayanin da yayi a baya don zuwa ya mik'a tarin Awards d'in nan ga duk wad'anda aka zab'a!
"I would first like to say my hearty congrats to each and every member that will come up here...
Muryarsa ta disashe a cikin kan Imran lokacin da ya lura wani a gefe na kallonsa sabanin yadda hankalin kowa ya ta'allak'a wajen sauraren Dr. Turakin, ya juya da sauri amma mutumin was so fast fiye dashi, ya d'auke idonsa da wani irin sauri kafin Imran d'in ya kai ga kamashi.
Bayan kamar minti biyar lokacin da aka fara kiran mutane suna karb'ar Awards d'in, Imran ya sake juyawa yaga ba alamar wannan mutumin.
"They are here! Ban san ya akayi ba yarima, amma Naani ta san cewa muna nan!"
Da sauri Imran ya juya ya kalli jaamil wanda a lokaci d'aya ya k'araso ta cikin mutanen nan ya tsaya a kusa dashi.
Kafin ya bud'e baki yayi magana, muryar Dr.Turaki a cikin speaker ta karad'e wajen da kiran sunansa.
Ya juya kansa a hankali ya kalli can kan high floor d'in, a hannun Dr. Turaki wannan Award d'in ne, Award d'in dake d'auke da dutsen Nil... haskensa ya haska cikin idanunsa Sannan a gefen damansa Sa'adha ta sake damk'e hannunsa dake cikin nata!
****
Zuciyarsa ta gaya masa cewa dole ne ya k'ara tsananta duk wasu matakai daya d'auka a baya, don canjin wajensu bashi ke nufin cewa Naani ta hak'ura da tunkararsa ba... abinda yayi mata wani abu ne da ba zai tab'a goguwa a ranta ba kuma ba zata tab'a hak'ura dashi ba, hak'ura da abinda ta riga ta d'ora zuciyarta akai tun wani zamani da bai sanshi ba, hak'ura da abinda take masa kallon duk wani fatan da burin da da take dashi har ma da wanda zata samu a gaba.
Hak'ura da abinda ta riga ta ta'allaka zuciyarta akai tayi sacrificing abubuwa da yawa akansa... sannan hak'ura da abinda shine dalilin 'yanta shi ta bashi duk wani gata na duniya, abinda ta yarda cewa har cikin zuciyarta zai yi mata shi, ta yaya don ya tarwatsa duk wannan burin nata a rana d'aya kuma yayi tunanin cewa zata rabu dashi cikin sauk'i...? har yayi saken da zai bar Sa'adha under protection din da a yanzu yake ganin baya amfanin komai.
Tunda har zasu iya turo wani abu nasu har cikin gidan da yake tak'ama baza su iya shigowa ba, don wani b'ari na zuciyarsa bai yarda ko kad'an da yarinyar dake zaune a gaban Sa'adha yanzu ba, yarinyar da tunda ya shigo gidan yaji tana nemanta zuciyarsa ta d'arsa masa wani abu game da ita.
Bayan ta gano ta kuma a can sama da cewar fitsari tayi a toilet ba abinda ya canja game da zarginta a zuciyarsa, don daga yadda take mu'amala da Sa'adha kamar ta riga ta saba da ita ne tun wani lokaci na baya, ba wai yau kawai daga fitarsa suka shigo ita da mamsnta a matsayin mak'otansu ba kamar yadda ta gaya masa, k'arin wani abu kuma yarinyar was too beautiful fiye da irin mutanen da ya saba gani.
Yaso koda sau d'aya ya bawa Sa'adha hint d'in da zai sa ta gane bai yarda da ita ba amma hankalinta gabad'aya baya kansa, ya tafi wajen tarairayarta da bata duk wata kulawa data buk'ata.
"Daddynki baya dariya ne?"
Ya tsinkayi muryar yarinyar lokacin da take shan Coco pops d'in da aka kira shi ya taho dashi, Sa'adha ta juyo ta kalle shi.
"Yana dariya mana harda kyakyatawa." Da idonta da kuma baki tayi masa inkiya da "Smile mana."
Kawai sai ya mik'e daga kan kujerar da ya zauna yana kallonsu yace, bari in shiga in shirya.
Sai dai har ya gama wankansa ya fito yasa kaya ba alamar Sa'adha ta biyo shi d'akin, yaji zuciyarsa ta k'ara matsowa wuya akan yarinyar, ta yaya zata d'auke hankalinta gabad'aya har haka? Bai ko taje kansa ba ya juya ya koma k'asa. A kitchen d'in ya samesu sun baje bowls cike da fulawa tana koya mata yankan wani abu akan chopping board.
"Daddynki ya dawo!" yarinyar data d'ago tana kallonsa ta fad'a. In one swift move ta d'ago ta kalle shi sannan tayi wannan murmushin nata mai dulmiyar dashi cikin duniyarta.
"Awwn you look fine, come sit... ga abincinka na gama."
Ta fad'a tana nuna mishi kujerar dake facing d'insu, yarinyar ta zagayo da sauri ta janyo masa kujerar alamun ya zauna, yayin da Sa'adha ta d'auraye hannunta a sink din jikin island din sannan ta shiga jero masa warmers da plates d'in data had' tana fad'in.
"Samosa muke yi Ayunie, don haka a bar space d'inta."
Ba yadda ya iya haka ya k'araso ya zauna yana jin kamar ya shak'e yarinyar ta b'ace daga cikin rayuwarsu.
"Baza kici ko kad'an ba?" Ya tambaya sanda ta gama zuba masa ta saka spoon d'aya.
"I don't feel like eating, may be ko anjima."
Da haka bata k'ara cewa komai ba ta koma suka cigaba da aikinsu, suna yi suna hirar da take sako shi a ciki amma baya magana, daga gefen idonsa ya hango sanda yarinyar ta rad'a mata cewa.
"Daddynki bai combing gashinsa ba."
Ransa ya kai karshe a b'aci, kawai sai ya ajiye spoon d'in hannunsa ya mik'e ya fita daga kitchen d'in tun kafin Sa'adha tayi magana, maganar da yake zaton zata yi daga lokacin daya shigo cikin kitchen d'in, amma bata ma lura dashi ba balle wai gashinsa, sannan for the first time tun zuwansu gidan ta shirya masa abincin da yaji dad'insa amma bata ko bashi hankalinta ba balle taji complimemt d'insa.
Bai samu sauk'in b'acin ransa ba saida ta gaya masa zasu maida yarinyar gida, bayan ta cika ta da dukkanin wani abu da a san tana dashi, don leda guda ya d'auka sanda ita kuma ta rik'e hannunta suka nufi gidan nasu wanda ke d'an gangarensu kad'an, kasancewar unguwar yanayin gine-ginenta kamar irin tsarin turawa ne.
A lokacin da suka tsaya jikin front door d'in gidan, matar da Nanne ta kira da maman yarinyar ta bud'e k'ofar, a lokacin Imran ya san cewa ba yarinyar ce abinda ya kamata zuciyarsa ta zarga ba,
MAMANTA CE!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
57
Lenghty chapters for you! ??
(¡î_¡î)
"Are you free?"
Muryar Sa'adha ta fad'a daga k'ofar d'akin, Imran ya d'ago ya kalleta, tayi wanka tasa wata 'yar k'aramar rigar Bacci, ta tufke gashinta baya sannan jela biyu na kalbar da tayi a gaba na reto, girman cikinta ya k'ara fitowa ta fragile jikinta, a hannunta wani k'aton littafi ne mai hardcover da rubutun...
100 THINGS YOU SHOULD KNOW ABOUT BABIES.
"Come here."