Showing 51001 words to 54000 words out of 113985 words

Chapter 18 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28482

da niyyar fitowa ne. Da kyar ta iya sakewa dasu don Nuratun ta dage sai bayaninsu take mata wanda ita ba ganewa take ba.

"Nanne mun kawo kaya suna d'akin Inna, akwai standing fan da kayan kitchen set wajen goma sannan..."

Da sauri ta katse ta.

"Toh Addano madallah."

Bata san me yasa in suka kawo abu sai tayi mata bayanin komai dalla-dalla ba, ko gani take su innan zasu rik'e ne ko me?

Karfe sha d'aya da rabi, Aunty Maryama ta janyeta daga d'akin, zuwa can d'akin su Mama Azumi dake k'asa inda ba muyane sosai. Ta d'auko mata wata doguwar farar riga ta material daga cikin kayanta, rigar tayi kyau sosai saboda tana da bud'ewar umbrella.

"Ga mai kwalliya nan zata gyara miki fuska kisa wannan kayan, Sulaiman yace zasu taho da angon da abokanansa daga wajen reception su zo nan ayi hotuna."

Nanne ta juya ta kalli budurwar dake zaune akan kujera, ta baje kit d'in kwalliyarta, ita sai yanzu ta lura ma da ita tun da suka shigo d'akin.

"Bari inje kar su lami su tafi."

"Aunty dan Allah ki turo min Aminah."

Tana fita ta juyo ta kalli mai kwalliyar tace.

"Hoda kawai zaki sa min sai kwalli."

*******

Karfe Sha biyu da 'yan mintuna tawagar 'yan d'aurin Aure suka karaso gidan.

A lokacin Nanne ta gama shiryawa cikin kayan da suka mutukar karbeta, anyi mata rolling da wani farin mayafi mai taushi a saman rigar, tayi kyau kamar zanata akayi, sai dai duk da adadin kwallin dake idonta, sunyi fulufulu almun kowa ya ganta ya san tasha kuka.

A falon baffa kusan kowa ya taru aka yi ta d'aukar hoton, akayi da ita da Imran da inna, sannan akayi su hud'u harda baffa, sannan akayi da inna da su hajiya babba, sannan akayi da 'yan mazan gidan, da 'yanmatan gidan sannan akayi tayi da mutane da yawa.

Anan ne ma taga jamila, don taji ance duk amaren sun zo amma ita ko a bikin jiya bata ganta ba, su nafisa da maryam 'ya'yan mama halime kawai ta gani sai Aisha da har kyautar sababbin English wears ta mata kusan akwati guda.

Gabad'ayansu su hud'un sun canja daga yadda ta sansu, sunyi wani fresh dasu sun murmure, wani gefen zuciyarta ya hasko mata cewa itama haka zata zama nan da wani lokaci.

A sannan ne ta kalli Imran sosai sanda ya tsugunna shi da abokansa suna yiwa Baffa sallama, tun daya kirata a wajen kwalliyar nan, basu sake waya ba, koda yake ko ya kiratan a jiya ba d'auka zata yi ba, amma yau ma bai nemeta ba, tun safe har kuma aka d'aura auren.

Ta kalli kayan jikinsa yayi mutuk'ar kyau fiye ka da jiya, farar colour da Ash, ta dade a rayuwarta bata ga mutumin da komai ke yi masa kyau irinsa ba.

Idonta na kansa har sanda shida abokansa suka bar d'akin, abinda kuma ya dad'a bata mamaki shine, ko kad'an bai kalle ta ba, balle taga wannan murmushin nasa. hankalinsa ma gabad'aya baya kanta har suka tafi, kamar ita d'in bata da banbanci a yanzu da sauran mutanen d'akin.

Ta ture wani abu mai kama da damuwa dake shirin samun waje a zuciyarta, A lokacin Sadiq ya shigo ya biyo ta cikin mutanen ya kirata, tabi bayansa suka fita.

A daidai barandar wajen d'akinsu Sulaiman, Imran na tsaye yana kallonta, shi kad'ai ba tare da abokansa ba, akwai mutane dake ta hadaniyarsu a compound d'in, kwarjininsa ya cika idonta saboda haka ba musu k'afarta ta k'arasa wajensa.

"Kinyi kyau sosai Sa'adha, I just want a picture."

Kafin ta gama fahimtar maganarsa, ya rik'o tafin hannunta na hagu sannan ya juyar da ita gefe, masu hoton nan na tsaye suka shiga dallara musu.

A wannan lokacin Nanne taji d'umin hannunsa kamar yana zuk'e damuwar dake tare da ita ne, jikinta yayi wani irin sanyi sannan a hankali ya shiga rawa, amma abu d'aya ke yawo a ranta, Me ya sami Imran? tayi zaton zata ga murnarsa fiye da haka, a yanzu da ta riga ta zama tasa? amma ko murmurshi irin na jiya bata samu ba.

*******

Wajen karfe d'aya Addano da 'yan uwanta suka yi sallama suka tafi ganin gidan amarya daga nan kuma zasu wuce adamawa.

Yini bikin ya cigaba da wakana, a kowanne lokaci mutane k'ara zuwa suke yi, musamman wad'anda basu samu zuwa jiya ba, k'awayenta ma da d'an yawa sun zo, anata d'aukan hoto da rawar kid'an kwarya, Har saida aka d'ora wata tukunyar abincin a gidan sab'anin da farko da duk kawowa akayi daga wajen da akayi order.

Kafin La'asar muryar inna ta dashe saboda yawan magana da amsa gaisuwa. A sannan ne kuma aka fara shirye-shiryen kai amarya.

Motocin da Imran ya aiko dasu tun daga farkon layin aka jera su har bakin titi, saboda yawa mutane har canja mota suka dinga yi, sai a shiga wannan a fito.

Aka sa Nanne ta sake wani wankan sannan ta shirya cikin wata lallausar lafaya kalar lemon green, jikinta sai tashin sassanyan k'amshi na turarurruka daban-daban yake yi, a lokacin zuciyarta ta riga ta gama tsinkewa, gani take ko ku'da ne ya hau kanta zata iya fashewa da kuka.

********

"....Aljannarki tana wajensa Nanne, shi yasa nake ta maimaita miki biyayya da hak'uri, hak'urinki shi zai sa miki tausayinki a ransa sannan biyayyarki ita zata maye gurbin duk wani abu da zaki nema a wajensa..."

Kukanta ya k'aru sosai to the point that duk wata doguwar maganar data biyo bayan nan bata iya jinta, tunaninta ya cakud'e gabad'aya ya tafi can wani waje, ta damk'e hannayen Aunty Nafisa dake gefenta tana sheshshek'a jikinta har d'agawa yake saboda ajiyar zuciya. Inna da muk'arrabanta suka yi tanasiharsu suna zaiyano abubuwan da ita a lokacin ba fahimtar su take yi ba.

Daga k'arshe aka kaita wajen Baffa, a nan ma taci wani kukan ta k'oshi don bud'ar bakin sa da farko hak'uri ya fara bata, zuciyarta ta tsinke...ta yaya baffa zai bata hak'uri? akwai abinda zai tab'a yi mata a duniya da zai sa ya bata hak'uri?

Tayi niyyar ta gaya masa ita ba abinda yayi mata, ita ba a cikin damuwa take ba, auren Imran ba zai zame mata matsala ba, amma kukan dake cinta ya hana ta, tana ji tana gani aka fitar da ita daga gidansu aka sata a mota, gidan da ta taso tun yarintarta, gidan da mahaifiyarta ta tafi ta barta a cikin sa, gidan da Inna ta raine ta da dukkan kulawarta, gidan ta fara gina rayuwarta a cikinsa, da gaske ne da ake cewa aure yak'in mata, yau ta fahimci wannan yak'in da ake nufi, don a yanzu ji take kamar runduna guda zata tafi tunkara.

¡ñ©n¡ñ

Pheeewwwwww......mun gama harkar biki, duk wata hayaniya ta k'are...komai yazo k'arshe an dai tafi da Nanne gidan Imran, abinda muke jira tun farkon labarin nan ya faru.

Anyi auren, d next agenda shine yadda zaman zai kasance, zaman wata halitta da kuma mutum a matsayin zaman aure? yadda Nanne zata san waye Imran, tunda a yanzu da gaske ta zama b'arin rayuwarsa.

Amma me kuke tunani yasa Imran ya fara canja mata tun a rana d'aya kawai?

Ina zancen masu daukan hoton nan?

May be zamu ji a next chapter.??

***

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

34


(¡î_¡î)

Mutane sun ragu sosai a lokacin duk an tafi d'akin ya rage daga su Aminah sai Aunty maryamah da Aunty Zainab kad'ai, har a lokacin Nanne na k'udundune a cikin lafayarta tana sheshshek'ar kuka.

Aunty zainab dake kan stool ta kalli agogo tace.

"Gaskiya tafiya zamu zo muyi, babu alamun zuwan dangin ango a wannan daren."

Daidai sannan wayar aunty maryama tayi k'ara, bata nan tana kitchen ita da Rahma saboda haka Aunty zainab d'in ta d'aga.

Abu daya ta fad'a Nanne ta gane inna ce mai kiran.

"Gamu nan, yanzu zamu taho wallahi bari in gaya musu."

Ta kashe wayar sannan tace da Aminah.

"D'auki jakarki, bari in kira su tafiya zamu yi."

Tana fita Aminah ta cigaba maganar da take mata.

"....Sa'adha dan Allah ki rage kukan nan, kar ya shigo ya ganki kina tayi ba k'akkautawa."

Da kyar ta had'iye shi a mokogwaronta tace.

"Yau zaki tafi?"

"A'ah sai gobe dai, ai yanzu dare yayi su Rahman zan bi."

"Dan Allah toh kizo goben."

"In naga wasu zasu zo, zan biyo su amma gaskiya ba zan miki alkawari ba."

Tayi raurau da ido kamar k'aramar yarinya.

"Gaskiya ne ai sa'adah, aure fa kika yi, dole ne ki hakura da komai ki saba da canjin rayuwarki."

Canji rayuwa, canjin rayuwarta...tun jiya take maimaitawa kanta wannan kalmar amma har yanzu ta kasa nutsewa cikin kanta, tana kallo ba yadda ta iya haka suka tafi suka barta, bayan su Aunty maryama sun k'ara binta da nasihohin da ita ba fahimtarsu take ba. Tashin motarsu da kuma rufewar gate d'in data fahimci akwai maigadi a gidan ya dawo da hawayenta, ta sake dukunkune jikinta akan gadon tana jin gidan ya mata girma, kamar wata tsakuwa guda d'aya akan faranti.

Bata san iya adadin mintunan da suka wuce ko lokacin da ya tafi ba kafin ta jiyo wani k'arar bud'e gate d'in, ta san dai kawai a lokacin hawayenta sun k'afe, sai ajiyar zuciya da take yi a hankali.

Ta rufe idonta sanda ta jiyo k'arar taku daga inda take tunanin corridor ne, ba sai an gaya mata ba ta san waye ya shigo, Imran ne, mutumin da a yanzu kowa ke kira da mijinta.

"Assalamu Alaikum.."

Wannan muryar, wannan muryar mai taushi ta shiga cikin kunnenta, sai dai yau ba a waya ba, ko kan kan hanya ko gadon asibiti, a cikin gida ne, gidan dake mallakinsu su biyu a matsayin mata da miji.

Ba tare da ta d'ago kanta daga tsakanin cinyoyinta ba ta amsa a hankali, ba lallai ne ma in yaji ba.

"Hey...." muryar ta sake shiga kanta da wani irin amo sanda ya zauna a gefen gadon sannan bata zato taji ya lalubo hannuta daga cikin lafayar.

Numfashinta ya d'an d'auke a lokacin da d'umin hannunsa ya ziyarci fatarta, kamar dazu taji wani abu na shiga jikinta yana soothing damuwarta.

"Kuka kike yi?"

Kamar mai bashi amsa sai tayi ajiyar zuciya tare da jan hanci, shima ya d'auki hakan a matsayi amsa.

"Kukan rabuwa da Inna ne?"

Bata amsa ba yace.

"In dai haka ne dan Allah kiyi shiru, ko gobe in kina so zan kaiki wajenta..."

"Kinjiiii...?"

Taji kamar ta d'ago a lokacin ta tambaye shi da gaske yake? da gaske gobe zai iya kaita gida? amma hannunsa dake nannad'e da nata ya hanata magana, wani abu ne daga cikinsu yake shiga jikinta yana goge duk wata damuwarta.

"Sa'adha..." ya kira sunanta a hankali.

"Ko mu koma yanzu sai mu dawo anjima?"

Ta d'ago da kanta da sauri ta kalle shi.

Ya salam! yayi kyau cikin wani bak'in yadi d'inkin fitted mai kyau, sannan yasa bak'ar hula wadda ta fito da d'an hasken fatarsa.

Yana kalonta da idanunsa masu kama da maik'o a cikinsu, da kuma d'an k'aramin murmushi a lebb'ensa, murmushin da a d'azu taso ganinsa kamar me. Ta sauke kanta k'asa sannan muryarta ta fito.

"Yanzu dare yayi ai." ita har ga Allah a lokacin ta yarda cewa zai iya mayar da ita gidan ne a yau, saboda haka ta k'arashe da cewa.

"A bari kawai sai goben."

Taji k'arar murmushinsa kafin ya lalubo d'aya hannun nata.

"Zo muje kiga..."

Ya mik'e tsaye rik'e da hannayen nata, ba musu kuwa k'afafunta suka mik'e suma, ya jata har jikin wata k'ofa dake gefen wardrobe, wanda ta san toilet ne, aikuwa yana bud'ewa mamaki ya kamata ganin girmansa da bata yi zato ba, gashi komai na cikinsa light Ash ne, daga toiletries har tiles d'in, sannan ga wata fitila mai k'arfi da ko allura ce ta fad'i tana zaton za'a ganta.

Ya tsayar da ita a jikin sink sannan ya koma ta bayanta ya rik'o kafad'unta, daga cikin mudubin da suke facing tana iya ganin tazarar kafad'arsa da kanta, ta san yana da tsawo amma bata san cewa banbancin ta dashi ya kai haka ba.

"Sa'adha... I want to tell you something."

Ya fad'i kowacce kalma a hankali kuma da nutsuwa, idanunsa kuma basu bar kallonta ta cikin mudubin ba, rudani da wata irin kasala suka saukar mata sanda taji ya zamo hannayensa daga kafad'arta, ya rik'o tafin hannayenta, zuciyarta ta dinga bugawa har tana jin kamar zai iya jinta.

Sannan tunaninta ya tsaya cak! ta tsura masa ido ta cikin mudubin, kwarjininsa na k'ara dulmiyar da ita, musamman idanunsa da suke da kyalli kamar ya d'iga mai a cikinsu, They were clear and deep! taji zata iya nutsewa a cikinsu ta manta da duk damuwarta.

"I want to share a part of my life with you, kiyi hak'uri na san kin gaji...amma in ya wuce yanzu, ya wuce yau bana tunanin zan iya sake fad'a miki."

Ya sake shiru yana sauraren fitar numfashinta, kamar iya abinda zai fad'a kenan kafin ya fara.

"Sa'adha tun da na tashi a rayuwata ban tab'a sanin iyayena ba, sun rasu tun kafin in san kaina, haka kuma bani da wani dan'uwa na jini, sannan rayuwata tana had'e da k'alubale da yawa, na fuskanci wahalhalu da yawa a lokacin yarintata, sai daga baya na sami tallafin wata halitta da ta rik'e ni da dukkan kulawarta, ta jawo ni jikinta, ta bud'e min sabuwar duniyar dana sami komai dana rasa a baya, 'yan uwa, d'aukaka, matsayi da kuma tarin abubuwan da a da nake musu hangen nesa.

Shi yasa nima a lokacin na d'auki dukkan soyayyata na dank'a mata, na yarda cewa bani da wani farin ciki a duniyar nan daya wuce nata.

A cikin haka sai k'addara ta jefo ni wajenki, tun daga ranar dana fara ganinki kuma rayuwata ta canja. ban san taya zan fad'a miki ki fahimta ba amma zuciyata ta fara sonki tun ranar da kuka dawo daga islamiyyar nan ke da Rahma, tun ban san ko ke wacece ba, da farko nayi kok'arin takura kaina da cewar ni da ke bamu dace ba, amma duk lokacin da nake tare dake ko na ganki sai zuciyata ta kasa daurewa.

For the first time tun lokacin da na sake sabuwar rayuwa nayi failing a wani abu, nayi failing wajen controlling zuciyata akanki, shi yasa na fara bibiyarki tun baki sani ba, har kika fara lura dani. Daga nan kuma abubuwa da yawa suka dinga had'a mu, har zuwa yanzu da Allah ya k'addara aure zai shiga tsakanin mu.

So, kome zai faru Sa'adha, kome zai faru nan gaba, I want you to keep in mind that son da nake miki da gaske ne, and it will forever be real."

Yana rufe bakinsa, ta juyo da fuskarta ta kalleshi, yana tsaye dab! da bayanta ne, saboda haka numfashinsa ya shiga busawa akan goshinta.

"Me zai faru nan gaba?" mamaki ya fito sosai a 'yar karamar muryarta.

Ya lumshe idanunsa akanta.

"I don't know, abubuwa da yawa suna faruwa a rayuwar nan, i just felt like telling you saboda gudun mistunderstanding nan gaba."

Sai tayi shiru kawai kwakwalwarta na nazari, amma nazarin ma ya kasa yiwuwa saboda yadda yake tsaye dab? da ita, tunda take bata tab'a tsayawa kusa da wani namiji haka ba, sai a yau ranar farko da ta zama matar aure.

Tunaninta ya katse, sanda ya d'ago da hannunsa a hankali ya sake juyar da ita tayi facing sink d'in, sannan ya kunna fanfon ruwa ya fara zuba.

"Kiyi alwala muyi sallah Sa'adha, mu rok'i Allah ya kore duk wani abu da zai shiga tsakaninmu."

Har tayi alwalar ta bishi jam'in sallah raka'a biyu, kwakwalwarta nazari take yi sosai na maganganunsa, amma har a lokacin abubuwa da yawa ta kasa fahimtarsu.

Bayan sun idar da sallar, ya juyo ya sake rik'e tafin hannayenta sannan yayi addu'o'i wanda da yawansu na nema musu zaman lafiya ne sannan yace da ita taje tayi wanka ta rage kayan jikinta.

Yana fita daga d'akin ta murd'a muk'ulli sannan ta cire lafayar jikinta, akwai heater a band'akin ta had'a ruwa mai d'umi sannan tayi wankan, tana yi tana kallon band'akin tana tuno nasu itada inna, tana ganin kyansa kamar me amma wannan ya ninka shi a komai.

Ta zura wata doguwar rigar bacci har k'asa bayan ta fito sannan ta feshe jikinta da turare. Har ta kashe fitilar ta kwanta sai kuma wani tunani yazo mata, ta taso ta bud'e muk'ullin sannan ta koma tana sak'e-sak'en yadda daren yau zai kasance mata.

Maganganun Imran suka yi ta yawo akanta, ta san addu'ar neman zaman lafiya abu ne mai kyau da ya dace su fara dashi, amma yadda yayi ta maimatawa da kuma addu'o'insa da suka fi yawa akai, ya sata wani tunanin.

Ta dunk'ule hannayenta tana tuno yadda a dare d'aya kawai ta fara sabawa da yadda yake rik'e su.

Kusan minti biyar sannan ya turo k'ofar d'akin ya shigo, da alamun shima wanka yayi, don ya canja kayansa zuwa wata light jallabiya, gashinsa alamun a jik'e sannan k'amshinsa ya cika d'akin.

Ya shigo cikin bargon lokacin da ta sake duk'unkune jikinta daga can k'arshen gadon, bata ko d'ago da kanta ba don idanunta na kan yatsunta, amma taji alamun kamar ya kalleta kafin yaja bargon jikinsa sannan yace.

"Allah ya tashe mu lafiya wifey."

Wani dad'i ya ratsa ta, abinda take fatan taji kenan, sai kuma yazo har da k'arin wani sunan mai dad'i. Wifey!
tayi murmushi a hankali sannan ta amsa.

"Ameen."

Asuba ta gari!

¡ñ©n¡ñ

Me kuke tunani game da abinda Imran ya gayawa Sa'adha....?

Da gaske ne maganganun ko hakan ma na daga cikin tsarinsu?

****

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

35

Allah abin godiya, kwana na uku ina tunanin yadda zan k'arasa chapter nan, sai d'azu ina cikin wanke gashina komai ya fito POP!....so i was tynking duk ranar dana rasa idea kawai toilet zan tafi in tara kaina a famfo.....hehehehehe!????

Don't mind me please!

Enjoy!??

(¡î_¡î)

"Zaka jira nan da kamar minti goma ayi warming d'insu sir."

Matar dake zaune a kujerar cashier ta fad'a fuskarta d'auke da mirmushi.

Good. Imran ya amsa a cikin ransa a fili kuma sai ya d'aga mata kai sannan ya juya ya fita daga restaurant d'in ya nufi cikin motarsa ya zauna.

Yana bukatar lokaci dama, alone time d'in da zaiyi tunanin dake cikin kansa kala-kala. A driving seat yake zaune amma senses d'in hancinsa na iya jiyo masa wannan cool k'amshin da yaji a jikinta jiya, alamun har a yanzu motar bata rabu da k'amshin inda ta zauna sanda za'a kawo ta gidansa.

Komai ya riga ya kammala a yanzu, Sa'adha ta zama matarsa bisa k'okari da fasahar jaamil, saboda kusan komai daya faru shi ya tsara, shi ya tsara duk tarin abubuwan da suka faru a d'an tsukin nan, tun daga kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login