Showing 24001 words to 27000 words out of 113985 words
dashi ya dakata mu gama tukunna."
Minti biyu bayan hakan, malaman nan su biyu suka shigo falon baffa, suka yi musabaha d'aya bayan d'aya tare kuma da gaisuwa kafin su zauna a kujerun dake gefe.
"Ashe kuma jiya ma kunzo. Munje kaduna ne kuma mota lalace mana a hanya, shiya sa dare yayi mana."
Babban cikinsu ne ya amsa.
"Ya salam! Allah ya kiyaye gaba, haka shi sulaiman d'in yake fad'a mana wallahi, Da yake hajiya ce (yana nufin inna) tasa aka kira mu akan dai batun yarinyar nan."
A daidai wannan lokacin lami tayi sallama ta shigo, ta ajiye musu tray d'in hannunta dake d'uke da flask, sukari da kuma k'ananan cups d'in shan tea sannan ta fita.
"Alhaji a gaskiya munyi duk wani iya k'okarinmu harda taimakon wasu ma, don jiya mu bakwai muka zo gidan nan amma wallahi duk k'ok'arin namu ba muga wani aljani tattare da yarinyar nan ba.
Shi yasa muka sami matsaya d'aya wadda itace kowannenmu ya yarda da ita, cewar Aljanun ne ke k'ok'arin shafarta, kuma da alama daga cikin jinsi mai k'arfi ne duba da yadda take wahala tun yanzu."
Baffa ya gyad'a kansa alamun ya fahimta.
"Sannan kuma kamar yadda muka yi bayani ne a baya, hanya mafi k'arfi da yarinyar zata kiyaye kanta shine dole sai tayi rik'o da addu'o'i, da kuma yawan zama da alwala da karatun alqur'ani, idan har babu wad'annan magungunan da muka bayar ma ba lallai ne a samu tasirinsu ba."
"Toh su cikin gidan kun sake yi musu duk wannnan bayanin?"
"Eh duk mun fad'a musu, amma akwai wani dalilin daban wanda dole kai ya kamata mu samu, shine ma dalilin dawowarmu."
"Ina saurarenku.." ya amsa a hankali.
Malamin ya d'anyi shiru kamar yana jin nauyin abinda zai fad'a.
"Alhaji inda ace yarinyar tana da aure, ko kuma za'ayi mata aure nan da wani lokaci, hakan ba k'aramar kariya zai zame mata ba, don irin wad'annan Aljanun suna mu'amala ne kawai da matan da basu tab'a aure ba.
Amma in har mace bata da aure, da kyar ne su rabu da ita."
Baffa ya k'ank'ance ido ta cikin glass d'in dake fuskarsa yana kallonsa. Ba zaka yi iya banbace wane irin yanayi ne a fuskar tasa ba.
Haushi? Mamaki? Nazari ko kuma rashin yarda?
¡ñ©n¡ñ
Please share this story with your freinds and family.
Thank you for reading this document
*****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
18
(¡î_¡î)
A cikin mafarkinta na biyu, duhu ne sosai kamar wancan karon, sannan dogwayen mutanen nan biyu na tsaye a kanta. Jikinsu na daga karshen gadon amma kuma sunyi kusa sosai yadda bata ganin wata tazara tsakaninsu.
Bata iya ganin fuskokinsu, iya kafad'ansu ne kawai, kuma duk iya kokarinta, duk yadda ta kokarta ba abinda take gani a wajen da ya kamata ace kansu ne, bata ganin komai sai duhu.
Taji ta k'agu, kamar ta bud'e baki ta roki daya daga cikinsu ya d'ora hannunsa akan goshinta kamar wancan karon, wancan karon da tunda sanyin fatarsa ta ratsa jikinta, duk wani ciwo nata yabi iska.
Ta rufe idonta a hankali sanda ta hango hannun nasa na tahowa kan fuskarta, a hankali sanyin fatarsa ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta sannan duk wani ciwo nata yabi iska!
******
A satin da tayi wannan mafarkin, bata k'ara fuskantar wani ciwo ba, jikinta ya koma k'alau kamar yadda take a da, sai dai kuma ba wanda ya yarda da ita akan hakan. Kowa yana binta ne da kallon mara lafiya musamman inna, dake takura ta akan yin abubuwa, bata isa ta tsallake wani tsari na shan magungunanta ba koda kuwa sau daya ne a rana.
Duk da cewar tasha yiwa inna bayani cewa ita bata ganin magungunan zasu kawo mata sauki, don wani abin ma kamar k'asa ce kawai, amma inna ta rantse ba abinda zai hana ta daina sha, a lokacin taji kamar ta bata labarin mafarkin da tayi har sau biyu amma ta fasa, don wani abu ne da cikakken mutum ma ba lallai ne ya yarda ba, Balle kuma Inna da rikicin tsufa ya fara kamata.
Saboda haka ta barshi a ranta kawai don babu na biyun inna a wanda zata fad'awa sirrinta.
Babban abin mamakin daya same ta ya faru ne bayan ta koma sabuwar islamiyyar data canja, anan ne ta gane cewa gidan da Imran yake a layin dake gaba kad'an da islamiyyar yake, Don ba sau d'aya ba sau biyu ba tasha jin wasu daga cikin 'yan makarantar na hirarsa, hirar had'uwarsa, da kuma abubuwa da yawa wanda muhimmi shine zancen shi kad'ai yake zaune a gidan da yake, don akwai wadda ta rantse ma ta san wadda taje har k'ofar gidan nasa ya tabbatar musu cewa ba mata a gidan. Kuma a kullum shi kad'ai ake gani yana shiga gidan.
Ranar data fara jin zancensa daga bak'in wasu 'yan ajin nasu, bata tab'a kawowa shi bane, sai da yazo wucewa a mota daidai lokacin tashinsu taji suna nuna shi tare da bayanin da aka gama a aji. A lokacin k'afafunta kusan mak'alewa sukayi a inda take tsaye, don tun ranar data fahimci ba'a gidansu walida yake ba, bata k'ara sake ganinsa ba kusan wata sati uku.
A lokacin har sadiq saida ta tambaya amma yace bai gane shi ba, duk da ya san kusan mazan dake layinsu. Tun daga wannan ranar kuwa sai ta fahimci kusan rabin hirar 'yanmatan makarantar in an had'u a masallaci kafin a tayar da sallar la'asar ta Imran ce. Kuma kowa da irin albarkacin bakinsa da yake fadi game dashi. 'yan k'alilan ne ke fad'an abubuwan alkhairinsa, kamar yawan sallah a jam'i da kuma kyakyawar mu'amalarsa da suke ji daga bakin yayyensu, amma da yawansu sunfi sukar zamansa shi kad'ai a gidan ne da cewar wani abu ne da ba'a saba ba, kuma ake masa kalon laifi, wasu kuma zancensu bai wuce yabawa komai na tsarin halittarsa da kuma yadda suke mafarkin samun miji ko saurayi irinsa ba.
A cikin satin, Nanne ta ganshi har sau uku amma ko kad'an bata bari ya ganta, duk da cewar daga cikin mota take hango shi kamar ya dawo daga aiki ko wani waje. Sai dai har cikin ranta tana so ko sau d'aya magana ta shiga tsakaninsu, watak'ila hakan yasa ta samu yi masa tambayoyin dake cin ranta game dashi. Tambayoyin da a kullum k'aruwa suke musamman yanzu da take jin hirarsa wajen mutane daban-daban.
****
Ranar Alhamis tana tsaye daga jikin mota a cikin asibiti tana jiran fitowarsu inna, wadda suka shiga ita da aunty amarya wajen gashin k'ashinta.
Da a cikin motar take kuma sai ta fito waje shan iska, don yau kwata-kwata bata son shiga ciki, Allah yaso sun taho da Aunty amarya ne itama zata ga likitanta, da ta san ba yadda za ta yi dole sai ta shiga.
Ta jingina bayanta tana kallon dogwayen bishiyun wajen, suna kad'awa a hankali kamar masu rangwada. Ta juya gefe ta kalli tsilli tsillin mutanen dake harkokinsu a harabar wajen, tana son irin yanayin nan, kamar ruwa zai sauka sannan kuma kowa na harkar gabansa.
Daga can ta hango wani container na kanti saboda haka ta tafi da niyyar siyan ruwa. Har ta siyo kuwa ta dawo da kusan mintuna goma sannan su inna suka fito. Tana hango su ta bud'e gaban motar ta shiga.
Idris direba ya taho shima daga jikin famfon da yake wankewata jarka ya shigo motar.
"Zamu biya ta Al-karama idris zan tsaya in sayi magani dan Allah."
Aunty Amarya ta fad'a daidai sanda idris d'in ya tada motar.
"Toh shikenan hajiya."
Nanne taji dad'i ak'alla tana so su dad'e a waje saboda yanayin garin, kuma Al-karama yana da nisa daga gidansu.
Ta juya ta karbo wayar inna wadda kusan tasu ce su biyu, ta d'auki earpiece akan dashboard d'in motar ta cusa a kunnenta, sannan ta jingina kanta da glass d'in motar. Iskar dake shigowa na kad'a ta kota'ina.
A cikin wak'ar da take ji ta jiyo inna na fad'an wai bata sa dankwali ba, don abaya ce a jikinta sai kawai ta dauko d'an bakin mayafi mai adon jajayen dutsuna ta yafa, tunda suka fito innan bata lura da ita ba kenan sai yanzu da taji dad'in k'afafunta.
Ta k'ara lumshe idonta tana jin Aunty Amarya na gaya mata cewar ai haka yaran yanzu suke wai safiyya ma na yawan yin hakan, ta rasa wak'ar take ji ko hirarsu saboda haka ta ware volume d'in ta juya tana kallon titi.
Sun iso daidai Al-karama dake d'aya tsallakensu, idris yace ba sai ya juya ba bari ya tsallaka kawai ya karb'o, saboda haka Aunty amarya ta shiga binciko takardar maganin da kud'in daga jakarta sai dai bata kai ga d'aukowa ba wayarsa tayi kara, ya d'auka ya shiga magana k'asa-k'asa, daga baya kuma sai ya fita waje ya koma bayan motar.
Inna tace.
"Yo kinji shakiyanci, maimakon ya karb'a kuma ya tafi yana wayar sai mun jira shi ya gama abinda yake kenan?"
Aunty Amarya ta juya bayan motar ta ganshi yana ta sunkuyar da kai saboda haka tace.
"Toh watakila wayar mai muhimmanci ce, tunda naji ance ya fara neman aiki."
"Au ya gama karatun ne?"
"Inna tun yaushe kuwa, har ya kawo takardar gamawar tasa gida ana tayi masa murna, shekara biyu ne ai da yake diploma suka yi."
"Wallahi na manta, bawa Nanne toh ta tsallaka ta k'arbo miki, kan nan ya gama."
Da kyar Nanne kuwa ta karb'a ta fito, don ta riga taji dad'in zaman da tayi. Ta kashe wakar, ta ajiye wayar akan seat d'in sannan ta rufe k'ofar motar ta matsa gefe.
Ta tsallaka titi na farko kafin almarar da ta zama sanadin k'addararta ta faru.
ALMARA.
Don banda ita da ta tabbatar babu mota a kusa kafin ta tsallaka titi na biyu, babu wani d'an adam a wajen da zai iya bada shedar ga ta inda motar ta fito. Kawai sunji k'arar takewar birki ne da kuma wani irin ihu wanda karad'e wajen baki d'aya.
Nanne taji tayi sama, numfashinta ma yana tafiya tare da ita, sannan a lokaci d'aya kuma taji ta fad'o da k'arfi ta daki k'asa. Wata irin k'ara mai amo ta fito daga makogwaronta ta ratsa cikin kowacce gab'a ta jikinta. Taji kamar bayanta ya b'alle ne sannan dukka jikinta ya mata nauyi.
Numfashinta ya tsaya cak! a iya kirjinta, ta dunkule hannunta wajen k'ok'arin jawo iska ta shiga jikinta, a lokacin ne taji wajen ya rud'e da salatin mutane, muryoyi da yawa suka cika kunnenta, taji bata gane komai.
Idanunta suka shiga k'ok'arin rufewa, amma tana iya ganin dishi-dishi na tarin mutanen dake ta shigowa cikin ganinta. A lakacin ne, taji wani ya d'aga hannunta dake da nauyi, sannan wannan muryar, wannan muryar mai taushi tayi magana.
Kunnenta ya ture duk surutan mutanen dake wajen ya d'auko mata abinda muryar ke fad'a. Abinda muryar ta saba fad'a.
"SA'ADHA!"
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
19
(¡î_¡î)
Nanne ta bud'e idanunta a hankali tana jin kamar ta tashi daga bacci. K'amshin turare da warin izal ne suka fara shiga hancinta kafin hayaniyar mutanen d'akin ta ziyarceta. Idanunta suka ci karo da silin fari, a jikinsa kuma akwai fanka wadda ke juyawa da k'arfi.
A ina take ne? Don tabass nan ba d'akinsu bane. Sai kuma kwakwalwarta ta tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta, tun daga tahowarsu titin Al-karsma gar zuwa sanda tazo tsallaka titin nan da sanda wata mota da bata san daga ina take ba tayi sama da ita.
"Ta farka ne?" wata murya da bata san kota waye ba ta kutsa cikin kunnenta.
"Ai kuwa kamar idonta a bud'e yake."
Wata ta matso jikin gadon sannan ta kira sunanta, a lokacin maganganun mutane daki suka fara raguwa, saboda haka ta yunk'ura sosai sannan ta ware idanunta, ai kuwa fuskar Aunty nafisa ta fara cin karo da ita, sai ta Rahma sannan kuma Inna.
Tayi k'okarin mik'ewa amma gabadayansu suka dakatar da ita. A sannan ne inna ta fara kuka tana fad'in.
"Sannu Nanne, ke dai kina ganin jarabawa daga Allah, ba don da sauran numfashinki a duniya ba, da yanzu wani zancen ake..."
"Inna dan Allah karki fara kukan nan, tun da ta farka ai godiya zamu yiwa Allah kawai." mama Azumi dake gefe ta katse ta.
"A kuma yi fatan samun sauki ba." mama rabi ta k'arasa.
Daga nan dukkan 'yan d'akin suka shiga matsowa ana yi mata sannu, wanda yawanci 'yan gidansu ne sai kuma k'alilan daga cikin matan layinsu. Ita dai bin kowa take da kallo don ba wani ciwo da take ji a jikinta...Bata kuma yi magana ba don ta tsinci muryar Aunty maryama na fad'in ba lallai ne ta gama wartsakewa ba.
Yaya Ahmad da ya umar suka shigo sai kuma suka juya don kiran likita ko nurse. A lokacin nanne taji wani irin fitsari ya cika mararta saboda haka ta kalli Rahma dake gefenta tace.
"Ke fitsari nake ji, raka ni toilet."
Rahma ta kalle ta sosai.
"Ai baza ki iya tashi ba, ban san ya za'ayi ba."
Sai kuma ta juya gayawa aunty nafisa. Nanne ta yunk'ura da karfi ganin abinda zai hanata, anan ne idanunta suka ci karo da suntumemiyar k'afarta d'aure cikin plasta an rataye ta a jikin wani abu. Mamaki ya kamata, ta motsa 'yan yatsun daga ciki taji suna motsi kuma ba wani ciwo, toh me zaisa a d'aure ta haka?"
"Nanne..." muryar aunty nafisa tasa ta juya. Tana magana k'asa-k'asa daidai saitin kunnenta.
"Baza ki iya tashi ba, akwai robar fitsari a jikinki saboda haka in kina ji kiyi kawai."
"Kamar yaya?" ta tambaya don a baiyane yake bata gane ba.
"Kin tuna me ya faru dake koh?"
Ta gyada kanta.
"Toh kin samu karaya ne a k'afarki, don haka baza ki iya tashi ba, amma an sa miki robar yin fitsari a jikinki."
Kanta ya kasa d'aukar zancen a lokacin d'aya, ta sake kallon k'afar tata, dama haka karaya take babu zafi ko kad'an. Sai kuma ta tuna da wanda ya kade tan, indan har ya karyata ai bai kamata ace baya nan ba. Kamata yayi yazo ya biya duk wani abu daza'a biya na asibitin nan, tunda ba akuya ya buge ba.
Ta juya da niyyar tambayar Aunty nafisan, sai kuma likita ya shigo tare dasu ya Ahmad, don haka kowa ya matsa ya basu guri, ya d'anyi mata tambayoyi akan yadda take ji ita kuma ta tabbatar masa ba wani abu da take ji a jikinta, amma da alama bai gamsu ba, don har allura ya sake mata a k'afar sannan yayi ta zuzzura mata wani abu a baki yana reading daga jikinsa.
Daga k'arshe yace a bata wani abin taci sannan tasha tulin magungunan dake zube a side drawer. Kafin ya fita ya sake tab'a kafar tata, sannan yace gobe zasu sake dressing.
Bayan sun fita aka mikar da ita zaune, ta jingina da filon bayanta sannan mama Azumi ta shiga bata abinci a baki. A lokacin ne ta tambayi inna dake zaune a gefensu ina mutumin da ya kad'e ta yake. Ga mamakinta sai ji tayi innan tace.
"Yaro d'an Albarka, Nanne ki gode Allah, tun jiya d'an nan dashi ake ta fafutukar komai...yana tsaye anan wallahi har safe, sai d'azu sulaiman ya takura masa ya koma gida ya huta, amma anjiman nan na san zaki ganshi ya dawo."
Kafin ta amsa mama Azumi ta k'arba.
"Wallahi dai kuwa an samu d'an kirki, a wannan zamanin wani ai guduwa zai yi."
Zata yi magana inna ta sake katseta.
"Ai kowa yaga k'ok'arinsa wallahi, har su hajiya babba zuwansu d'azu saida suka yita yaba masa, banda tsautsayi ya gifta ai yaron da alamun hankali, bai kamata ace yana wannan gudun ba."
Ganin abinda zata fad'a ba zaiyi tasiri akansu ba yasa ta maida bakinta tayi shiru. Ita taso taji inna ta fara fad'a ta kara tunzura ta akan a damk'e mutumin sai ya biya komai da za'a tambaya na asibitin.
Wajen k'arfe uku, rahma ta matso kusa da ita.
"Kin san me?"
Ta gyara kwanciyarta sannan tace.
"A'ah me ya faru?"
"Kin san waye ya kad'e ki?"
"Ta ya zan san d'an rainin..."
"Kar ki karasa...Wannan mutumin ne fa."
"Wanne?"
"General topic d'in islamiyya."
Ba tare da wani tunani ba bakinta yace.
"Imran...?"
"Au sunansa kenan? Wanda dai muka tab'a gani a jikin gidansu walida kafin su tare."
A lokaci d'aya Nanne taji komai ya tsaya mata, imran ne ya kad'e ta? Ta yaya hakan zata faru? Me zai kaishi Al-karama a wannan lokacin? Taji zuciyarta ta shiga bugawa kamar lokacin da yaje gidansu, anya kuwa shi din ne, ko dai gizo idon rahma ya mata. Taya in shine zai tsaya kamar yadda inna ta fad'a...Amma me zai hana shi? Wata zuciyar ta tambaya, laifinsa ne ya kad'eta dole ya tsaya yaga samun lafiyarta, sannan ma ai ya santa.
Sai kuma tayi saurin goge hakan, ta nemo zahiri tasa a zuciyarta, ya taimake ta ne kawai sau d'aya ya kuma tambayi sunanta amma ba lalkai bane ya iya rike saninta har yanzu.
"...Na san abubuwa game dake fiye da cikin yatsu..."
Ta tuno abinda ya fad'a wancan karon. Idan har yana nazarinta ne a da, yanzu ya daina don rabon data ganshi a layinsu kusan wata uku kenan.
"Shi yasa nace miki kar ki k'arasa don duk sanda akayi zancensa, sai kin fad'a irin wannan tunanin."
"Ta gallara mata harara da gefen ido.
"Me kike nufi?"
"Ke zan tambaya me kike nufi tunda har sunansa kin sani."
Har ya yamma duk wanda ya shigo sannu yake mata, ita kuma ta tabbatar musu da ba wani ciwo a jikinta. Amma ko sau nawa ta fad'a babu alamun cewa suna yarda da ita saboda haka ta kwanta kawai ta rufe fuskarta.
Bayan sallar la'asar, wajajen karfe biyar mutane da yawa suka tafi, sannan masu zuwa ma aka dakatar dasu, sai da kyar ma aka bar Aunty maryama tare da inna don su kwana a wajenta, don a yadda aka tsara Aunty maryaman ce kad'ai zata kwana amma inna ta kafe cewa baza ta bar asibitin nan ba tare da Nanne ba.
Wajen karfe takwas saura, Nanne taji wani irin bacci ya fara fizgarta saboda haka ta rufe idonta, ta daina saurarar hirar da Aunty maryama keyi ita da mijinta wanda ya tafi aiki can abuja, tana bashi labarin dukkanin abinda ya faru. Inna kuma na daga k'asan d'aya gadon da ba kowa, tana nafilarta.
A lokacin ne suka ji an kwankwasa k'ofar dakin a hankali, inna da tayi sallama ta bada izinin a shigo, don dukkansu sun zata nurse din da tace zata dawo da daddare akan x-ray d'in da akayi a kai ne, wanda nanne ta kasa gane alak'arsa da karyewar k'afa.
"Assalamu Alaikum."
Wannan muryar, wannan muryar mai taushi ta ratsa kunnen Nanne. Kafin tayi wani