Showing 36001 words to 39000 words out of 113985 words

Chapter 13 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28476

a zuciyarta ta yarda dashi tace zata kaishi wajen Baffa. Waye ma zai yarda a yanzu daga fara zuwa wajenta a fara zancen aure? In har dama ba ya shirya bane.

Sai kuma wata zuciyar ta tambayeta game da Imran, meya banbanta shi da sauran? Me yasa take tunanin in shi d'in ne zai yarda a d'an k'ank'anin lokaci ya aureta?

Tayi saurin ture wannan tunanin kar ya b'ata ranta.

Ta maida robar cikin fridge sannan ta dawo ta zauna akan kujera, a lokacin inna ta gama wayar, kuma iskar da akeyi ta k'aru, sannan gari ya dad'a duhu alamun a kowanne lokaci ruwan zai iya sauka, ta dunk'ule a cikin kujerar tana sauraron zancen inna da take mita akan dad'ewar su Aunty maryama.

Kowacce kalma tana shiga kunnenta, amma bata fahimtar komai.

Har aka d'auke ruwan, dab! Da maghriba akayi sallah, babu Imran ba alamun zuwansa. Zuciyarta tayi nauyi, sannan jikinta yayi ba dad'i. Amma kuma sai ta dinga bawa kanta uzurin cewa watak'ila ruwan ne ya hana shi zuwa.

Washegari rana ta fito har ta fadi, babu alamun zuwansa. Kwana d'aya, kwana biyu.

Sai ta fara tunanin ta karb'i shawarar da d'aya b'arin zuciyarta ke bata, na cewar ta cire imran daga ranta, yaci ace ta gane cewa shi bai dauketa a matsayin data dauke shi ba. Watakila ya riga ya manta da abinda ya gaya mata tun a daren nan. Koma ya manta da ita ya shiga harkokinsa.

Ya isa ta gane cewa duk sanda suka had'u chance d'in k'ara ganinsa yana sake mata nisa ne. Kuma bai kamata ta cigaba da damuwa dashi a ranta ba. Damuwa da mutumin da bata san waye shi ba.

Ya isa ta gane cewa ba daga Baffa yayi mata maganar aure bane imran zai zo yace zai aureta.

Akwai abubuwa da yawa yanzu a gabanta, su ya kamata ta fuskanta ba wani abu da ba zai taba yiwuwa ba. Sai dai a duk sanda ta tuna tarin taimakonsa gare ta sai wani b'arin na zuciyarta ya sake rik'e fatan cewa zai zo a ranar ko gobe.

Amma bayan sati d'aya sai ta hakura ta cire wannan fatan.

Komai na gidan ya sake dawo mata kamar da, shirye-shiryen inna ya k'aru, zancen aurenta kuma ya biye gabad'aya danginsu, sannan a kullum kwanakin da Baffa ya d'ibar mata k'ara matsowa suke, komai ya sake cakud'e mata. Fatan da zuciyarta ta samu game da Imran a dare d'aya kawai yayi mata nisa ya zama kamar bai tab'a faruwa ba.

BAYAN SATI DAYA.

BAYAN SATI BIYU.

BAYAN SATI UKU.

BAYAN SATI HUDU.

Baffa ya kirata!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

25

(¡î_¡î)

Lokaci yana tafiya a kullum kuma a kodayaushe. Walau cikin farin ciki ko bak'in ciki. A duk motsawar agogo guda daya, lokacin ne yake wucewa, lakacin da baza a sake maimaita irinsa ba.

Sau da yawa kuma, d'an adam baya fahimtar saurin zuwan lokaci sai ya tsara wani abu yasa masa rana. Anan ne zaka ga kamar ansa igiya ne ana jawo wannan lokacin. Hakan ce ta faru da Nanne, adadin kwanakin da baffa ya d'ibar mata ya k'are saboda haka a kowanne lokaci ta san tana iya samun kiransa.

Muryar Inna ta kutsa cikin kanta.

"Ni na gaji wallahi, had'a kayanki zaki yi ki tafi can wajen babar taki, watakila tunda ita ta kawo ki duniya ita kya iya hak'ura ki sake a wajenta, duk randa aka saka ranar auren kya dawo."

Nanne ta d'ago daga juya abincin hannunta da take yi maimakon ci ta kalle ta, kwata-kwata ta manta magana innan ke mata balle har ta iya rik'e abinda take cewa ko wanda ta fad'a a karshe.

"Inna me nayi?"

Ta tambaya a lokaci d'aya kuma taji kunyar tambayar. Ita kanta ta san ko makaho ne yake tare dasu ya san cewa ta canja daga Nannen da kowa ya santa zuwa wani abin daban. Wani abu da ita kanta bata sanshi ba. Ta zama kamar wani gunki dake tafiya a doron k'asa, tayi losing duk wasu emotions d'inta.

"Ba abinda kika yi, kuma matsalar kenan, ba abinda kike yi Nanne!"

Ta rufe idonta a hankali, a cikin wata d'aya da 'yan kwanakin da suka wuce me nene bata yi? bata tab'a fashin makaranta ko sau d'aya ba, karatun da a da bata yi yanzu a kullum cikinsa take, anyi jarabawar first term tazo ta shida a maimakon na goma sha da take d'auka a baya, sannan a iya wannan lokacin ta had'a haddar izu bakwai a islamiyya.

Sai dai bata hira, bata dariya, bata kuka sannan bata tsokanar da kowa ya santa da ita, ta koma kamar wancan lokacin da baffa yayi meeting akanta, lokacin da imran baizo yasa mata wani fata a dare d'aya kawai ba.

"Inna me kike so nayi?"

"Au tambayata ma kike yi? Da lokacin da kike harkokin ki ni kike tambaya me zaki yi?"

Tayi shiru tana cigaba da juya abincin, kafin a hankali kuma tace.

"Kiyi hakuri."

"Ni ba hakuri nake so ki bani ba."

"Toh me kike son inyi?"

Har ta bud'e baki kamar zata yi magana kuma sai tayi ajiyar zuciya sannan tace.

"Nanne, kin san dai ba'a kanki aka fara zancen irin wannan auren ba koh? Ba akanki aka fara aure a irin wannan shekarun ba sannan kin san ba'a kanki aka fara aure kafin a kammala makaranta ba koh?"

"Na sani."

"Toh me yasa zaki sa kanki a cikin damuwa irin haka? Koh auren ne kwata-kwata bakya so?"

Tambayar tasa ta d'ago da kanta da sauri ta kalleta. Tunda aka fara zancen nan ba wanda ya tab'a bata zabi, ba wanda ya tab'a tambayar ra'ayinta. Kowa yaji zancen ko aka gaya masa, fatan alkhairi kawai zaiyi wasu ma su fara binta da shawarwarin da suka danganci auren.

Amma yanzu ga inna na tambayar ra'ayinta, innar da'a yanzu in ta bude baki tace bata amince ba shikenan an rufe babin zancen sai wani kuma. Zuciyarta tayi zurfi cike da rokon Allah yasa ta fahimce ta. Ta gyara zama a hankali sannan ta d'aga kai.

A lokacin taji inna ta rafka salati sannan ta ka'rashe da...

"Na shiga uku ni saudatu, wallahi yau na dad'a tabbatar da zancen malaman nan, dole akwai abinda ke faruwa tare dake Nanne amma banda haka ni ina na tab'a jin macen data bud'i baki tace bata son aure? Sannan don har ance za'a yi mata ta fita haiyacinta ta shiga kunci tana wannan ramar?

Toh wallahi tun wuri ki fita idona in rufe kafin in sassab'a miki..."

Bata bari ta k'arasa ba ta d'auki plate d'in tayi cikin d'aki. Wani k'ololon abu ya makale mata a wuya, taji ina ma kuka zaizo mata a lokacin, watak'ila in ta samu tayi zata samu sauk'i a ranta.

Sai kawai ta zube a k'asan gado sannan ta kwantar da kanta a gefe, ta jawo wayar inna dake kusa da filo, one missed call ya nuna akan screen d'in, ta bud'e ta a hankali sannan ta shiga cikin call log d'in. Sunan Addano ya nuna tar akai, yadda tayi saving number Nuratu dashi.

A cikin sakan d'aya kawai, tunaninka da yawa suka faru a cikin kanta. Ta tuno da zancen da suka yi da ita a wannan zuwan nata na k'arshe, zancen da a lokacin ta d'auke shi ta ajiye a gefe tana tunanin ba na lokacinta bane.

Ta tabbata yanzu idan taji abinda ke faruwa zata fi kowa cikin farin ciki, watakila ma har tafi inna. Sai kuma ta tuno da zancen d'an yayarta da tayi mata, wanda tace har yana aiki a cikin adamawa, kwakwalwarta tayi k'ok'arin tuna sunansa amma ta kasa.

Idan har abubuwa sun cakud'e mata a yanzu ana shirin aurar da ita ga wanda bata sani ba, me yasa ba zata bi shawarar Nuratu ba ta yarda da wanda take tunanin had'asu? Tunda kamar yadda tace ne ko ba komai zata shiga cikin dangin mahaifiyarta.

Amma kuma ta san wane irin mutum ne shi? Ta san halayensa? Sannan zai yarda ya aureta a iya lokacin da Baffa ya fad'a? Idan ta aure shi adamawa zata koma kenan? Zai barta ta cigaba da karatunta? Wace irin rayuwa zata yi a can?

Tambayoyi da yawa suka dinga yawo a cikin kanta har ta kwanta a ranar, komai ya cakud'e mata, tana ganin kamar an d'ora rayuwarta ne akan faranti dake hannun k'aramin yaro yana gudu. kuma a kodayaushe zata iya fad'owa.

Ta san in har tayi kuskure guda d'aya a yanzu zai shafi rayuwarta ne har abada. Don zai iya yiwuwa tayi kuskuren barin baffa ya zab'ar mata mijin da ba lallai taji dadin aurensa ba, sannan zai iya yiwuwa ita da kanta tayi wannan kuskuren.

Ta rufe idonta a hankali sanda ta sake k'udundunewa cikin bargonta. Kanta cike da tunani fal! Wanda bayan ta farka washegari ta takura kanta ta samu matsaya d'aya.

Ta d'auko wayar inna ta turawa da Nuratu sak'on text. Abu mai muhimmanci a ciki shine.

"Addano na amince da zancen, ki turo SHI!"

BAYAN SATI DAYA!

Baffa ya kirata!

*******

"Naji dad'i kwarai da bin maganata da kika yi Sa'adha. Haka ya tabbatar min da cewa baki d'auki fushin da wasu 'ya'ya ke d'auka da iyayensu ba a irin wannan lokacin.

Kin kab'i kaddararki da hannu biyu ba tare da kin bari ta tauye ki ba, sanda naga result d'inki nayi farin ciki sosai fiye da yadda zan misalta miki.

Amma a lokacin da mutanen da kika turo suka zo min da zancen neman aurenki, a ranar nayi sallah ta musamman ga Allah Sa'adha, na godewa wa Allah sannan nayi alfari dake fiye da koyaushe.

Kin d'auki hanya mai b'ullewa wadda zaki ga amfaninta, kinyi min biyayya duk da cewa hakan zai tauye abubuwa da yawa na tsarin rayuwarki, amma ina tabbatar miki zaki yi tutiya da abinda kika yi nan gaba, biyaiyarki baza ta tab'a cutar dake ba.

Nayi bincike akan yaron da kika turo, kuma daga kowanne b'angare ban samu aibinsa ba, saboda haka zamu zauna da iyayensa, mu yanke duk abinda ya dace. Tashi kije Allah yayi miki Albarka."

Nanne taji kwalla na taruwa a idonta bayan ta fito daga falon baffa a lokacin, kwalla ce wadda ta manta yaushe rabon da taga irinta a idonta, kwallar dake tabbatar mata komai yazo k'arshe kenan, ta rufe idonta a hankali sanda d'uminta ya gangaro ya taho kan kumatunta.

Shikenan abinda take wa hangen nesa ya kusa faruwa, Baffa ya yarda da mutumin da a yanzu ta san sunansa Nura. Mutumin dake shirin zama wani b'ari na rayuwarta!

******

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

26


(¡î_¡î)

Another day...
without your smile.
Another day...
just passes by.

But now i know, how much it means.
For you to stay right here with me.

The time we spent apart will make our love grow stronger.
But it hurts so bad I can't take it any longer...
I wanna grow old with you.....

Wakar ta katse a daidai nan sakamakon kiran daya shigo cikin wayar. yadda ya tallafe bayan kansa da duka hannayensa biyu ya masa dadi, saboda haka bai ko motsa ba har kiran ya katse.

Yana kwance ne akan irin dogwayen kujerun nan na bakin beach, yana jin iskar wajen mai sanyi da dad'i na kad'a kowanne particles na gashin jikinsa, ya mak'ala earpiece a kunne sannan idanunsa a bud'e yana kallon adon taurarin dake haskawa a samansa.

Adonsu mai kyau, yadda suke shining akan black universe d'in samansa. ya had'e dogwayen gashin idanunsa waje d'aya sannan ya sake bud'e su, taurarin na da kyau, idonsa ya gane masa kuma kwakwalwarsa ta fad'a masa, amma hakan ya kasa tafiya cikin zuciyarsa.

Zuciyarsa da ta kasa nutsuwa tun zuwansa k'asar nan. sati hudu kenan, sati hudu yazo da niyyar hutu amma abin ya zama kamar yazo ne don ya samu isashshen lokacin da zai dinga tunaninta. tunanin wadannan idanun nata.

Ya salam! me yasa ne ya dawo da wannan tunanin, a d'azu har a sallarsa yayi wa Allah alk'awarin ba zai sake kawo ta a ransa ba, amma awa biyu kad'ai ta karya hakan.

Fararen idanun nan nata masu kamar an zuba musu madara, su suka fara jan ra'ayinsa gareta. Bayan ya samu ya takura kansa ya rabu da ita kuma k'addara ta sake hada su, a yanzu kuma da k'addarar ke shirin sake had'a su, so yake ya ture wannan intrest d'in daya samu akanta tun baya, baya so ko kad'an ya sake dawowa cikin kansa.

Don abinda zai had'a su d'in na dan lokaci ne kawai, kuma da komai yazo k'arshe zai fita daga rayuwarta ne har abada, Abada wadda bata da k'arshe. Saboda haka yake k'ok'arin hana kansa jawo musu wata matsalar.

Don shi kansa zaman da zasu yi tare ma wani k'alubale ne da sai yayi mutuk'ar taka tsantsan da kansa. halittarta da tasa ba d'aya bace, in dai yana tare da ita dole ne sai koyaushe hankalinsa ya zamo hundred percent a tare dashi, in ba haka ba zai iya mantawa ko wajen rik'e hannunta ko tab'a kyawawan idanunta, ya rik'e ta da karfi irin nasa da zai sa k'ashinta ya rugurguje.

Ya salam! me ya same shi ne kuma? yanzu ya gama yiwa kansa fad'an tunanin idanunta yanzu kuma ya koma tunanin rik'e ta? me zaisa ya rik'e ta? auren da zasu yi ba na gaske bane, zai aureta ne don samun kariyarsu su duka biyun ba don wannan shirmen da zuciyarsa ke kawo masa ba.

Dole ne ma tun a yanzu ya nemi hanyar da zai nesanta zuciyarsa da ita, ko don ma jaamil. ya tuno maganganun da suka yi na karshe kafin tahowarsa nan.

Komai zai tafi mana daidai yarima, dama a lokacin da na kawo zancen nan, tsorona d'aya ne na yadda zamanku zai kasance.

Don yadda kake da intrest akan yarinyar nake tunanin zaka iya jawo mana wata matsalar, ko a lokacin zamanku ko kuma a lokacin da zaman zai k'are. amma tunda ka tabbatar min da baka sonta hankalina ya kwanta, na tabbatar baza ku sami matsala ba.

Ya rufe idonsa sanda ya tuno hakan, yasha gayawa jaamil abubuwan da yawa wanda yake nufi da gaske amma baya yarda dashi, sai a lokacin da ya gaya masa wani abu da shi kansa bai tabbatar ba sannan kuma ya yarda.

Don shi kansa a lokacin daya fad'awa jaamil cewa baya son Sa'dha, yayi amfani ne kawai da kalmar don a tunaninsa hakan zaisa jaamil yace ya fasa wannan shawarar. Saboda tun lokacin da ya fad'a masa ita, hankalinsa ya kasa nutsuwa don bai yarda da kansa in yana tare da ita ba, bai yarda da zuciyarsa ba.

lokacin daya sake bud'e idonsa akan taurarin, sai yaga kamar ansa hannu ne an jera su cikin wani tsari da yayi kama dana fuska. fuskar mutum d'aya a duniya wadda ya tab'a jin irin wannan abin game da ita. Gimbiyarsa
Sareefa, 'yar uwarsa kuma 'yar uwar halittarsa dake can wata nahiya tana jiransa.

Ya kamata yayi wa kansa fad'a, Sa'adha ba abokiyar rayuwarsa bace, zata shigo ciki ne kawai kuma ta wuce a lokaci daya. kamar mutum ne ya shiga d'aki mai kofa biyu, ya shiga ciki ya fita ta d'ayar kofar ba tare da tsayawa ba.

Saboda haka ya san zai daure, shi ba matsoraci bane kuma bai tab'a tsoron wata gwagwarmaya a rayuwarsa ba, yana fuskantar komai da kwarin gwiwarsa kuma ya tsallake shi. me yasa yanzu zai damu kansa da tunani akan Sa'adha?

K'arar tsinin takalman dake taka floor din da akayi na katako ya ziyarci kunnensa, kuma ya san waye ba tare da ya bud'e idonsa ba. a sati na hudu da yazo wajen nan don hutawa ba zai iya k'irga iya adadin matan da ya ture daga hanyarsa ba, wasu sun hakura wasu kuma har a yanzu suna cigaba da nacinsu.

Wadda take tahowa a yanzu sunanta, Kathy, kwananta hud'u kenan da fara aiki a hotel d'in da yake, kuma kamar sauran tunda tazo take fatan kawo kanta gare shi.

"Hello, my name is Kathy, and i'm the server tonight. What can i get you to drink?"

Muryarta ta fad'a daga gefe, wai bata fahimce cewa ta fad'a masa sunanta wajen sau biyar bane?

Ya bud'e idanunsa a hankali ya kalleta.

"Nothing." ya fad'a da muryarsa mai zurfi.

Sai da ta d'auki ta wasu sakanni kafin ya lura ta fahimci me ya fad'a, kamar ta tafi wani tunanin daban. Tayi murmushi da sauri sannan tace.

"Okay, but if you ever change your mind..."

Sai ta fito da wata 'yar paper daga dan k'aramin aljihunta na gaba ta dora akan jikinsa. sannan tayi murmushi ta juya.

Imran ya bita da kallon mamaki, kodayake ba abin mamaki bane inda ya bar kansa tun farko yaji me tunaninta ke cewa. A lokaci daya al'adar bahaushe musulmi ta burge shi, ya hango tarin matan dake damuwa dashi, ko kuma da siffarsa data fi kama da tasu, amma babu wadda ta tab'a fito masa kirikiri da bukatarta, sai dai 'yan kewaye-kewaye kawai.

Ya godewa Allah da dalilin zuwansa cikin mutane bai kasance a cikin turawa ba, wayarsa ta sake katse sabuwar wak'ar dake playing.

Ya mik'e zaune sosai, iskar dake kad'awa ta d'auki paper tayi wani waje da ita. yana sliding answer button muryar jaamil ta shiga cikin kunnensa.

"Me ya same ka yarima?"

Maimakon ya amsa masa sai yayi murmushi mai k'ara sannan yace.

"Wallahi kullum kara komawa more human kake, its a miracle, yau kaine ke kirana a waya?"

jaamil yaja tsaki sannan yace.

"Ba dole in kiraka ba, na duba duk inda nake tunani ban ganka ba."

"Kamar yaya? ba na gaya maka inda zani ba?"

"Ko dai ka fada min inda zaka je da farko, don gani a k'asar Bulgaria d'in kuma baka cikinta.

Imran ya cusa yatsunsa cikin gashin kansa da iska ke kad'awa.

"Oh my god, na manta ban fad'a maka bane, ina maldives sanyi ne ya koreni daga bulgaria kwana na d'aya."

"I don't care, yaushe zaka dawo?"

"Yaushe zan dawo? gaskiya ba rana. I have almost 2 weeks a cikin leave d'ina fa, meya faru?"

"Komai ma ya faru, lokacinmu ya k'are sannan ciwon yarinyar na shirin dawowa.

Sai da numfashinsa ya d'auke jin jaamil ya fara maganar sa'adha, sati hud'u kenan yana hirar ta a zuciyarsa amma bai furta ko sunanta a fili ba.

Daga d'aya bangaren jaamil ya rage sautinsa sannan yace.

"lokaci yayi yarima, ina fata ka shirya."

*******

From the first time i met you...

There was something about you
I can never forget the way you thief my heart.

I didn't try to pretend you
I ain't like gonna send you
But i know like we're friends too.

Cuz you gave me a spark
I just can't help myself,
I want be your all
And i see no one else....

"Rahma dan Allah kashe wak'ar nan..."

Nanne ta fad'a lokacin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login