Showing 48001 words to 51000 words out of 113985 words
ta sallameta, wai don ma za'ayi k'unshi yau ne, da ta tabbata sai yau d'in ma taje.
"Wata yamutsa fuskar ki fa baza ta sa in fasa ba wallahi..."
Aunty maryaman ta fad'a bayan ta tsaya a jikin gadon, ta mik'a mata.
"...ban kofin yanzun nan."
Nanne ta had'e rai sannan ta k'arb'a ta rufe idonta, ta had'iye shi a lokaci guda.
"Kya gama had'e ranki ne, Allah ya kaimu ranar da zaki zo da kanki ki tambayeni, anan zaki ga nawa had'e ran nima."
Bayan fitar ta, ta jawo ragowar katinan bikin dake kan bedside drawer.
Sau ba adadi kenan take karantawa, amma har yanzu gani take kamar ba nata bane, kamar ba sunanta ne a jiki ba. Idonta ya kai kan sunasa, wanda aka rubuta da italian font mai lankwasar nan.
Imran Siddiq!
Me yasa ne shi komai nasa ya had'u?
Wayar inna ta sake k'ara a kusa da ita, ba sai ta duba ba, tariga ta san ko waye, don a lokacin k'arfe goma ne daidai kuma ringtone d'in ma daban yake.
"Assalamu Alaikum."
Tayi murmishi sosai, a k'aidar waya wanda ya d'auka shi zaiyi sallama amma shi kullum ita ke amsa masa sallama, tana d'auka ya sani.
"Wa'alaikum Salam."
Muryarsa can k'asa-k'asa kamar mai jin bacci yace.
"Sweetheart anyi k'unshin?"
Murmushinta ya k'aru sanda ta d'go da hannayenta tana kallo, daga nan ta san abinda zai zama topic d'in wayar!
¡ñ©n¡ñ
I'm sorry for all d turanci in dix shapta, na san labarin nan na hausa ne but nayi editing d'in wani labarina ne na turanci, toh sai hausar take ta had'e min...
I'm so sorry...
kunjiii......
Hhhha! forget dat ni ba Imran bace.????
****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
32
Da fatan duk kun shirya don yau biki zamu yi, zan gaya muku komai kamar kuna wajen akayi.??
(¡î_¡î)
Iye di dide
Ayye yaraye nanaye 'yanmata...
'Yan matan yanzu sun saka kallabi ga coge
Hannayensu d'auke da zobe, 'yan gayu!
Iye di dide
Ayye yaraye nanaye 'yanmata...
Amarsu ta ango, ki kika ce kina so ungo
Jeki ki bashi tutar k'auna, 'yar gata!
"...Dan Allah jama'a a marmatsa daga hanya don Allah, amarya da k'awayenta sun shirya...hanyar da zasu shigo suke nema...masu d'aukar hoto da video dan Allah ku matsa gefe, amarya zata shigo."
Muryar Mc ta karad'e wajen yana yi yana kallon hanyar gate d'in gidan wadda ta cunkushe da tarin mutane jin ance Amarya ta k'araso. Daga gabansu train d'in k'awayen amarya ne wanda suka yi ankon wani dark yellow material sun jeru sai faman selfie suke yi wasu kuma na bin kid'an suna rawar, wajen ya cakud'e da hayaniya sai ka d'aga murya zaka ji na kusa da kai tukunna.
Nanne na zaune a cikin wata hadadd'iyar Hyundai da Imran ya aiko aka d'aukota daga wajen kwalliya, tana ciki sai kallon mutane take tana murmushi.
Wani material ne mai kyau pitch da red na fitted gown a jikinta, daurin head d'in kanta mai kyau dark red yasha duwatsu, sannan kwalliyarta light ce sosai, ba blush, ba fake lashes sannan ba heavy janbaki, lips d'inta light pink ne sosai sai kyallin gloss kawai da suke, sannan eyakeup dinta ma light ne, kohl d'in kawai aka sa suka fito.
Muryar Mc ta cigaba da karad'e wajen.
"Dan Allah jama'a a bawa amarya da k'awayenta hanya, ance mutanen Niger ne a wajen, dan Allah a matsa ba cukwi ake rabawa ba...amarya ce zata shigo ciki ku ganta.."
Abin ya bawa Nanne dariya, Bata ga Rahma ba amma ta hango Aminah nata k'ok'arin sake jera layin 'yan ankon wanda yawanci 'yan makarantar bokonsu ne, itama cikin shigar material d'in amma harda head, wani dark colour mai kama da golden, tayi kyau sosai musamman beads d'in data sha wahala kafin a had'a musu shi ya k'ara haskata, Ta kalli na wuyanta, yayi kyau shima dark red don tun a wajen kwalliyar ake tambayarsu inda aka had'a musu.
Tana d'ago da kanta taga Anty maryama tazo gaban windon tana kwankwasa screen.
"Bana son rashin mutuncinki Nanne, ya ana ta jiranki zaki yi zamanki kina kallon mutane?"
Ta bud'e kofar da sauri tana dariya.
"Toh Aunty gani nayi duk an cakude hanyar...."
Kafin ta karasa muryarta ta b'ata a cikin d'imbin hayaniyar mutanen da suka matso da niyyar fara d'aukan hoto.
A lokacin Zainab ('yar autar mama halime) ta k'araso ta cikin mutane ta miko wata sabuwar atamfa mai kyau Ash da red. itama tayi kyau sosai kayanta light pink harda head, sai kallon Nanne take tana murmushi, itama tayi ta washe mata baki tunda ta san ba magana zata yi ba, ita haka Allah yayi ta kafin kaji muryarta da wuya.
"Yawwa Zainab, rik'e min d'aya kiga..."
Ta ware zani d'aya ta shiga d'aura mata a k'ugunta.
"Kayan meye kuma wannan?"
"Kayan kamu ne...sai anyi tukunna zaki cire su..."
Ta karb'i d'aya zanin ta yafa mata tun daga kan gwaggwaron har ya rufe fuskarta lokacin da Aunty Nafisa ke rabawa Aminah da wasu 'yan mata uku k'ananan kaskon turaren wuta dake hayak'i.
Nanne ta jawo hannun Aminah bayan ta k'arb'a tace.
"Gaskiya a canja wak'ar nan, ni ba zan shiga da ita ba."
"...Aikuwa ba ta yadda zan ga Mc anan? kin san dai ba zan kutsa in shiga..."
Kafin ta rufe baki, kid'an ya canja, nan take 'yanmatan suka fara bin takun wak'ar...
Ga turare
k'amshi..k'amshinsa yana gun amare.
Ga turare...
Cikin takun steps mai kyau aka shiga da Nanne filin harabar gidansu a matsayin amarya, mutane sai cincirindon d'aukan hoto suke duk da fuskarta da kayanta na rufe. aka kaita can gefe inda aka tanada wata 'yar karamar rumfa mai kujera d'aya.
Anan ta zauna har Inna da danginta tsofaffi suka k'araso, aka kuma nemi wasu daga cikin dangin ango da suka zama abin kallo kafin zuwan amarya suka zo wajen suma. Abin daya d'auki hankalin mutane dasu shine yadda dukkaninsu suke farare tas! kuma kyawawa, daga tsofaffinsu har yaransu kuwa.
Wata tsohuwa da Nanne ta gane a lokacin bikin su ya Aisha tayi ta rangad'a guda mai zak'i, sauran tsofaffin kuma na tsokanarta wai yau ranarsu ce, sai sun ga dama ma zasu bawa angon ita.
Inna ta bud'e sabon turaren a kwalinsa ta shiga fesawa Nanne tana ta zubo Addu'o'inta, wasu irin adduo'i masu kashe jiki wanda suka sata kuka wiwi sai dai kyar su Aunty Nafisa suka sa tayi shiru, suna fad'in zata b'ata kwalliyarta, ga 'yan biki na jiranta a waje.
Bayan an gama kamun ne, aka cire mata atamfar sannan 'yan matan suka sake jeruwa don raka ta main rumfar da zata zauna, tana fitowa wajen ya d'auka da wak'ar 'Duru' ta kowanne b'angare.
See the love i dey see for ur eyes..
I love you baby i no talk am twice
Your beauty making me do realize..
Say nepa don bring light..
So you must marry mee...
Eh eh...
You go love me
you go killing me baby..
you go follow me...eh
you are my remedy
you're my melody..
Eh baby na harmony
you go give me
Baby palanga...
i'll show you love dat you never seen....!
Tun Mc na magana akan d'aukar hoto har ya hak'ura yayi shiru. don kowa son d'aukan hoton yake saboda yadda 'yar k'aramar amaryar ta burge kowa cikin shigarta da kwalliyarta mai kyau.
Aka raba abinci mai dad'i cikin nutsuwa wanda hakan ya burge kowa, sannan kuma aka shiga rabon souveneirs a jaka ga duk wanda yazo zai tafi.
Duk cikin wannan hargitsin idon Nanne na kan mutanen da akace 'yan uwan mijinta ne, tun bayan da akayi kamu, basu kara tasowa ba sai da aka kira su d'aukan hoto, sannan basu sake ba balle har su d'an shiga cikin 'yan uwanta, iyaka wanda yayi musu magana kawai su bishi da murmushi. Gasu farare tas! dasu kamar wani jinsi na shuwa Arab, sannan ta lura yawanci attention d'in mutane yana kansu.
"'Yan uwan mijinki miskilaine, amma fa akwai kyau kamar shi, zaki haifo beauties in gaya miki."
Aminah ta rad'a mata a kunne, ta kai mata duka sanda tawagarsu Inna ke shigowa rumfar don d'aukan hoto suma.
K'arfe bakwai daidai Mc ya fara shelar cewa Ango da tawagar abokansa sun k'araso. Nanne taji wani irin farin ciki ya kamata ashe rok'on da tayi ta masa yana cewa ba lallai yazo ba dama duk jinta kawai yake kenan, ko d'azu a wajen kwalliya daya kirata yawo yai ta mata da hankali da zancen zai zo ko ba zai zo ba.
A lokacin mutane sun fara raguwa, amma daga jin ance Ango yazo, sai taga kamar dawo dasu akayi, saboda yadda kowa yake mik'a wuya yana jiran yaga wane ne Angon, hatta k'awayenta na makaranta da 'yan islamiyya ta lura duk hankalinsu ya tafi wajen ganin adadin girman Alhajin da suke zaton ta aura.
Mc yace k'awaye biyu su raka amarya ta taho da Angonta, sai a lokacin taga Rahma da kuma wata Sadiya Awwal, don Aminah ta tafi can fafutukar karb'owa 'yan ajinsu jakar souveneirs.
A lokacin da suka k'arasa bakin gate d'in ta hango Imran a tsakiyar abokansa, ji tayi kamar zata narke a inda take tsaye saboda tsabar kyan da yayi, yasa kaya shade d'in brown da babbar riga wadda akayi mata aikin da darkbrown zare, sannan hular kansa ma darkbrown ce, yayi wani irin fresh yayi kyau kamar a cikin zane yake, murmushin fuskarsa ya k'ara dulmiyar da ita, taji kamar ta juya baya ne ta hango wata amaryar na tahowa wajensa, don ji take yi kamar ba itace dashi ba. he's too good for her!
"Ya salam!... kinyi kyau sosai Sa'adha i can't breath."
Ya rad'a a daidai kunnenta sanda ya k'araso gabanta, tayi saurin juyar da fuskarta kan hasken flashers d'in dake ta dallare su. Ta gefen idonta tana iya hango bakin Sadiya Awwal a bud'e, idanunta na nuna tsananin mamaki, kamar taga wani abu ne da a zahiri ba zai tab'a zama gaskiya, to ba ita kad'ai ba kusan dukkanin mutanen ciki da kuma sauran k'awayenta haka suka cika da tsantsar mamakin ganin had'uwar Imran.
A lokacin kowa ya san hotonan da aka d'auka a baya ba komai bane, don har Mc ya fara shirin yace Amarya da Ango su shigo tsakiyar fili, yaga abin ba zai yiwu ba ya samu kujera kawai ya zauna, wajen ya zama ba abinda akeyi sai d'aukan hoto da kuma wasu 'yan mata dake rawa.
A sannan ne ma yayyenta maza gabad'aya suka zo, bata san wa ya tsara hakan ba amma abin ya burgeta, suma su san ana biki a gidansu ba ace iya d'aurin Aure kawai zasu ba, Sadiq yayi ta tsokanarta dashi da tarin nasa gaiyar na 'yan ajinsu maza wato 'yan B class, daga baya kuma suka koma kan 'yan matan ajin nasu wajen ya koma musu kamar School party.
Akayi ta hotuna sannan aka kawo musu abinci tare da sauran abokan Imran, filin ya koma na 'yan samari da k'awayenta 'yanmata kawai.
Kusan duk mutanen da suka d'auki hoton Amarya da Ango sun d'auka ne Imran baya kallon camera, idonsa da hankalinsa gaba daya na kan 'yar Amaryasa dake ta murmushi kamar ba ita ce tasha kuka d'azu ba.
Har abokansa data fahimci 'yan wajen aikinsu na tayi masa tsiya wai 'Gobe ne fa'
Sai wajen goma sannan tawagar Ango suka bar wajen kasancewar a lokacin kusan kowa ya tafi. Aka bar Nanne da sauran 'yan gidan nata cigaba da d'aukan hoto, musamman 'yan niger wanda ak'alla kowaccensu tayi fiye da kala goma, sai da mai hoton yaga abin nasu ba zai k'are ba ma sannan ya tattara ya tafi shima.
"Na shiga uku, sallah Rahma ko maghriba fa banyi ba."
Nanne ta fad'a lokacin da rumfar ta zama daga ita sai su Rahman kawai.
"Wallahi muma bamu yi ba yanzu zamu je mu had'a da isha, sai dai Allah ya yafe mana."
Aminah ta kalleta tace.
"Ki zauna in samo ruwa da hijabi kawai muyi anan, don wallahi kina shiga ciki ba samu zaki yi su barki ba, mutane ne kamar ba wanda ya tafi ciki aka koma."
Bayan an k'are duk wata hayaniya ta daren, Nanne ta samu tayi wanka sannan ta lalubi gadonta, wanda inna ta hana kowa kwanciya a d'akin sai ita da Amina da Rahma kawai. A lokacin k'arfe biyu saura na dare, amma ko'ina a gidan da hayaniya don da yawa basu da alamar yin bacci.
Tana kwanciya akan gadon taji kamar an dake ta da guduma a tsakiyar kanta, shikenan fa yanzu wannan ne daren ta na k'arshe a gidan nan, darenta na k'arshe a d'akinsu sannan darenta na k'arshe akan gadonta.
Daga gobe rayuwarta zata canja, komai zai canja game da ita, za'a d'aura mata aure da wani ta tafi ta bar kowa data sani, ta bar Innarta ta tafi wani gidan daban ta fara rayuwa tare dashi, shi kad'ai kawai a gida d'aya...ta yaya zata fara hakan? anya zata iya kuwa?
Ita fa duk bata hango wannan ba sai yanzu, yanzun da taga cewa da gaske ne fa, da gaske gobe za'a sallamata. wani irin tsoro ya kamata, ta tashi zaune ta rungume filon da k'arfi sanda hawaye ya cika idonta.
"Me ya faru?"
Rahma da ta fito daga band'aki da brush a hannu ta tambaya tana kallonta, hawayen daya taru ya gangaro kan kumatunta masu d'umi dasu. Aminah ta juyo daga lalubo kayan baccinta a cikin akwati tace.
"Me kuwa ya faru? taraddadin barin gida ne ya fara kamata...sai hak'uri Sa'adha, wani kukan ma ai sai gobe..!"
Ta fad'a da murmushinta, wanda hakan yasa hawayenta k'aruwa. Rahma ta zauna a gefenta.
"Toh meye abin kuka Nanne, aure ai abin farinciki ne da godiyar Allah, don Allah kar kiyi kuka, keda ba nisa zaki yi ba a garin nan fa zaki zauna, duk sanda kike so zamu zo kuma shima na san zai dinga kawo ki kiga inna....
Maimakon kalaman su kwantar da hankalinta sai taji kukan ma ya sake k'aruwa, ta kifa kanta akan gadon ta shiga rera shi kuwa, tana jin wani k'ullutun abu a k'irjinta.
Tun Aminah na tsokanarta har taga dai abin da gaske ne ta sauko ta fara bata hak'uri itama.
******
A cikin wannan daren mai d'aukar hoton nan ya shiga aikin editing pictures d'in daya d'auka shi da yaransa, saboda kar aiki ya musu yawa don gobe ma zai je yayi na d'aurin aure da yini kuma a satin suna da biki uku da zasu je.
Suna ta editing d'in suna kuma printing wasu har wajen k'arfe uku na dare, a sannan ne suka ci karo da wani abu mai tsananin mamaki daya d'aure musu kai.
Wani abu da kowannensu ya kasa yarda cewa daidai idonsa ke gane masa, wani abu da yasa kusan dukkaninsu suka cika da tsantsar tsoro.
Gabad'aya hotonan da suka d'auka na mutanen da akace dangin ango ne, babu abinda ya fito a cikinsu sai Amaryar kawai, amma dukkaninsu...dukkaninsu yadda suka tsaya a kowanne gefen babu siffarsu, sai siffar Amaryar kawai da kuma mutanen can baya.
Kuma ga alamun cewa da mutane a kusa da ita daga yanayin tsaiwarta amma kuma babu kowa.
Suka binciko gabad'aya hotonan da suka d'auka, kowanne daidai yake sai iya na dangin angon da akace ne kawai.
Wanda a yanzu, babu su ba alamarsu!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
33
(¡î_¡î)
Sautin kid'an algaita, kid'an marok'a, hayaniya da turereniyar mutane a layin gidan Alhaji Mustapha Bashir shi zai tabbatar maka cewa ba'a dad'e da d'aura auren ba. Auren...
IMRAN SIDDIQ
DA
SA'DAH MUSTAPHA
Ko ina ka duba mutane ne cikin kaya masu kyau anata d'aukan hotona da kuma k'ok'arin kaiwa wajen ango don taya shi murna.
Imran yayi kyau cikin fararen kaya, hula kalar Ash wadda ta dace da aikin kayansa, sai faman murmushi yake yana gaisawa da kuma d'aukan hoto da mutanen da yawanci ba saninsu yayi ba.
Daga cikin gidan kuma mutane ne koina fal! anata hidima da hayaniya, masu rabon abinci nayi, masu rawar kid'an kwarya nayi, masu hira had'e da gud'a nayi, kowa nata farin ciki da annashushuwa sai dai duk wannan abin da ake, Nanne na can d'akin Aunty amrya inda su Aunty maryama suka tsaya akanta da abinci, don tun jiya ba wani abin kirki da taci sai kame-kame kawai.
Tana cin abincin tana share hawaye kamar k'aramar yarinya, jikinta wani lallausan lace ne colour maroon and pitch da akayi masa d'inki mai kyau, adon rigar yasha stones sannan skirt din 8 pieces ne mai bud'ewa sosai.
Aunty Nafisa ta shigo cikin d'akin da kwalliyarta itama.
"Akace kuna d'akin mama halime, can naje ban ganku ba."
"Ai can ta tafi ita da Aminah ta b'oye d'azu, yanzun nan muka kawo ta nan, gata nan tana ci kamar guba ake bata."
Nanne ta k'are hade rai jin haka, ita fa yunwar ce kwata-kwata bata jinta, saboda gabad'aya jikinta dama tunaninta wani iri take jinsu kamar ba'a jikinta suke, ga kuma fad'an Aunty maryama da tun safe take binta dashi, ita bata tab'a ma ganin amaryar da akewa fad'a ranar bikinta ba sai ita.
"Idan ta gama, tazo falon inna babarta da 'yan uwanta sun zo."
Nanne ta had'iye lomar bakinta jin haka, a d'an tsukin nan taga Nuratu kusan sau hud:u kenan, wanda a da sai ta shafe kusan shekara biyu bata ganta ba, hakan na nufin cewa da gaske rayuwarta ta canja kenan, ko kuma tana shirin canjawar don bata sani ba ko a yanzu an d'aura au....
Aaaayiryiryiryiri....!
Wata tsohowa ta bankad'o labulen d'akin ta shigo ita da wasu matan.
"Aure ya d'auru...an d'aura shi yanzu yanzun nan....Sadakinki dubu d'ari 'yan nan...kin zama matar aure, Rana bata k'arya, girma ya hau kanki sai fatan...
Nanne taji kamar a daidai lokacin nan matar ta d'auko wani k'aton dutse tad'ora mata a kai, shikenan yanzu ta zama matar AURE? kuma matar Imran? duk mutanen nan sun shaida kuma ba wanda ya isa ya kwance?
"....Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Allah yasa bad'i war haka muzo suna...."
Hayaniyar matan ya cika kanta, sai kawai ta ajiye plate d'in hannunta ta koma ta duk'unk'une akan gadon Aunty Amarya, ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta sannan a hankali hawaye masu d'umi suka shiga bin kumatunta.
"Kuka ba naki bane 'yar nan, ke da Allah ya kashe ya baki zankadeden saurayi kamar a manna a goshi...Tashi zaki yi kiyi sallah ki godewa Allah...."
Mutane suka cigaba k'aruwa a d'akin, kowa sai faman shigowa yake yana 'Nanne Allah ya sanya alkhairi' Tun tana jinsu har tunaninta ya zame daga d'akin ya tafi yadda zata iya zuk'e kowa na gidan ta mayar dashi inda ya fito, bata son ganin kowa a yanzu, so take kawai a barta daga ita sai Inna a d'akinsu ko ta samu ta rok'e ta cewa a bar zancen tafiya da ita yau, a bari sai zuwa nan da sati d'aya watak'ila kafin nan ta shirya tukunna.
Kusan minti talatin sannan Nuratu da tawagar 'yan uwanta su shigo d'akin, shima da kyar don sunga Nannen bata