Showing 18001 words to 21000 words out of 113985 words
rage tsiwarta da surutu amma duk cikin tarin jama'ar nan ta rasa mutum d'aya da zata gayawa matsalarta, don in ba harkar taro ba bata fiye ganinsu ba, ba wanda sabonsu yayi karfi da ita a cikinsu. Inna ce kawai kuma bata jin zata fahimce ta a wannan lamarin.
Saboda haka Aminah bata yi niyyar zuwa ranar d'aurin auren ba amma ta takura mata sai da ta shigo, tayi ta mata k'orafi na yawan farkawar da take yi a kullum cikin dare ba tare da dalili ba. Aminan tayi-tayi da ita akan su fad'awa wani amma taki yarda don a tunaninta duk wanda yaji zaice aljanu ke damunta, ita kuma tayi rantsuwa cewa ba aljani a jikinta.
A haka sati biyu cike da taraddadi a wajenta suka wuce, 'yan k'ananan abubuwa kala-kala suka yi ta faruwa da ita.
Kamar yawan maganganun da take ji a cikin kanta wanda yanzu bata iya fahimtar abinda muryar ke fad'a, ko kuma kamar ana binta a baya in tana tafiya ko mutum ya tsaya a daidai bayanta, yawan kiran sunanta da take ji daga can nesa, da kuma alamun wani abu na tab'a fuskarta ko jan jelar gashinta.
Tun Inna bata lura da ita har tazo ta fara fahimtar wani abu, saboda yawan tsoratar da take yi da kuma azabar ciwon kai, sannan sau biyu tana tashinta cikin dare tace ana kwankwasa musu kofa alhalin ita bata jin komai.
Abu d'aya kawai dake sawa taji sauk'i a ranta da kuma rage mata tsoro shine yawan addu'o'in data rik'e bisa shawarar Aminah, Sannan bata tab'a zama ba d'ankwali a kanta.
Amma kallo d'aya mutum zai mata ya tsinto rashin kwanciyar hankali a idanunta, don gabad'aya sun d'ashe sannan sunyi fari fat! Ta rame kuma ta rage yawan magana. Ko sadiq yazo da tsokanarsa sai dai yayi ya gama bata iya biye masa, inna ma idan tana hirarta sai dai tayi ta binta da eh ko A'ah.
Mama Azumi da Rahma ba tambayar duniyar da basu yi mata ba amma tace musu ba abinda ke damunta. Daga k'arshe sai mama Azumin kawai ta b'ige da kawo mata jik'e jik'e tana tunanin ko shawara ce ke damunta.
A sati na uku baffa ya kirata akan rashin walwalarta da ya lura kwana biyu, shima ta kasa gaya masa abinda ke damunta sai shiru kawai. Ba yadda ya iya haka ya sallameta da umarnin ta koma islamiyarsu wani satin. Ta amsa sannan ta tashi ta tafi.
Sai dai kuma dukkaninsu ba wanda ya san me wani satin zai zo da dashi, satin daya rufta da wani b'angare na rayuwar gidan!
****
RANAR LARABA!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
12
(¡î_¡î)
RANAR LARABA!
Wajen karfe biyar da rabi na safe, inna ta fito daga cikin band'aki da alwalarta, ta tashi Nanne dake dunk'ule a cikin bargo sannan tayi falo inda daddumarta take.
Nanne ta bud'e idonta a hankali tana jin kamar baccin bai isheta ba, amma ba yadda ta iya ko bata tashi yanzu ba, ba zata kara minti talatin ba saboda tafiya makaranta. Tayi yunkurin tashi, a nan ne fa taji wani irin nauyi ya danne ta, gabanta ya fad'i ta sake yunk'urawa amma ta kasa, taji kamar wani gingimemen abu aka d'ora a jikinta,
Ta tattaro dukkan k'arfinta ta tara shi a hannayenta amma ta kasa mik'ewa, tsantsar mamaki ya rufe ta, me ya same ta kuma? Ta yaya zata kasa tashi? Meye akanta? Ta juya idanunta ta kalli jikinta babu komai sai wannan bargon da take lullube. Toh me ya faru da ita?
Sai kawai ta bud'e baki da niyyar kiran Inna ko har a lokacin bata tayar da sallar ba, anan ne zuciyarta tayi tsalle ta fice daga k'irjinta, don ta bud'e baki har ta furta sunan Innar amma babu sautin daya fito. Ba tare da ta tsaya wani tunani ba ta d'aga muryarta ta sake kiran, amma ta gagara tsinto sautinta.
Ta maida idonta ta rufe lokacin da k'arar bugun zuciyarta ya cika kunnenta, yana jijjiga ta kan cewa ta farka daga mafarkin da take, saboda haka ta tamke idonta ta sake bud'ewa sannan ta yi yunkurin tashi game da furta kalmar Bismillah amma ba abinda ya canja daga d'azu.
Zuciyarta ta k'ara tsalle cikin fargaba, kanta ya shiga juyi? Me kuma yake shirin faruwa da ita? Bayan duk abubuwan da take jurewa? Tana tunanin zasu wuce zuwa wani lokaci.
Ta sake yunk'urawar dai da dukkan wani k'arfi na jikinta amma wannan nauyin, wannan nauyin dake samanta ya hana jikinta d'agawa. Da gaske ne wani abu ya faru da ita ko kuma yana faruwa a yanzun, in ba haka ba ta yaya kawai zata kasa tashi, taji duniyar ta tsaya mata cak! Yanzu in bata mik'e ba me zai faru da ita kenan? Zata dauwama ne a haka? Koma mutuwa zatayi? Wannan tunanin ya k'ara rura mata wutar sabon k'arfi a cikin jikinta, tayi ta yunk'uri tana motsa yatsun hannu da k'afarta amma ba wani abu daya sauya.
Har k'arfe shida lokacin da inna ta idar da duk wasu nafilfilunta bata ji motsin Nanne ba, hakan yasa ta dawo cikin d'akin ta tsaya daga k'ofa ta kira sunanta.
"Har yanzu kina kwance? Yaushe kika koyi nauyin bacci ne...ga lokacin shiga wankan ki har yayi."
Shiru bata yi magana ba kuma bata motsa ba, ta sake kira ba amsa, sai ta k'arasa a hankali ta yaye bargon.
"Idonki biyu ashe? Ko ba zaki...."
Bata k'arasa maganar ba sanda ta lura bakin nanne na magana amma bata jin me take cewa.
"Baki da lafiya ne?"
Nanne ta girgiza kai tana kara gaya mata cewa ta kasa tashi ne da kuma magana amma ba alamun innar ta fahimce me take cewa.
"Yi magana mana inji, muryarki ce ta rike ko mura kike yi?"
Ta cigaba da girgiza mata kai tana fad'ar wani abu amma maimakon ta fahimta sai kawai hakan ya k'ara hargitsa ta, ta hau salati tana kokarin taso da ita, nan ma abu ya gagara sai kawai ta kara rud'ewa tayi waje da d'an saurinta tana neman wani.
Kafin k'arfe bakwai na safiyar, gabadaya kowa na gidan ya shiga tashin hankalin abinda ya sami Nanne, don wani abu ne da a tarihin rayuwar kowannensu bai tab'a gani ba, yayyunta maza haka suka yi ta k'ok'arin ciccib'arta daga kan gadon amma abu ya faskara, daga k'arshe suka yanke shawarar kawai a kira likita har gidan amma baffa ya hana, don tunda ya shigo cikin d'akin yaga yadda take dunk'ule a gado tana ta k'ok'arin yiwa kowa maganar da ba'a iya ji ga kuma hawaye ko'ina fuskarta, sai ya koma falo kawai ya kira waya yace da na ciki yazo.
Bai k'ara cewa komai ba daga nan, sai sanda hajiya Babba ta shigo yace ta taimaka ta taya su mama rabi bawa Inna baki ta rage kukan da take, don da mama Azumi ce ke bata hak'urin itama kuma daga baya ta fara nata. Mama halime ita ta tsugunna a gaban Nanne ta dinga karanto addu'o'i kala-kala tana tofa wa a koina na jikinta. Sadiq kuwa tunda ya shigo yaga yadda Nanne ke kuka sosai tana ta motsa bakinta alamun magana, ga kuma yayyansu duk sun taru sai kokarin d'ago da ita akeyi, ya koma d'aki yaci kukansa.
Hatta Aunty amarya da mama rabi sai da jikinsu yayi sanyi, don suna tsaye daga cikin d'akin kusan awa biyu kafin malaman da baffa ya kira su iso.
Anan suka umarci duk matan su fita, inda da kyar aka fita da Inna tana kuka tana a barta taga abinda zasu yi da idonta.
Su uku ne malaman, wanda yake Babbansu shi ya tsaya daga daidai kan Nanne ya d'ora hannunsa akan goshinta. yayi ta wasu addu'o'i tana kuka tana raba ido tsakanin yayyenta da kuma baffa dake zaune akan stool d'in mudubi.
Kusan mituna goma sha biyar kafin ya kammala, sannan sauran guda biyun suka fito da wasu papers da aka rubuta wasu keb'antattun ayoyin alqur'ani suka fara karantawa cikin had'in baki a tare kuma da karfi.
Me zai faru?
Basu yi nisa ba sanda idon kowa dake d'akin ya gane masa komai. K'afafun Nanne dake dunk'ule suka mik'e a lokaci guda, haka ma hannayenta, sannan jikinta ya shiga wata irin jijjiga yana d'agawa sama kamar dukka gab'ob'inta zasu b'alle!
¡ñ©n¡ñ
*****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
14
(¡î_¡î)
RANAR LARABA!
Wajen karfe Takwas saura kwata, Imaran yayi parking motarsa a cikin kanfaninsu, ya fito ya d'an kalli yawan motocin gurin sannan ya gyara tie d'insa ya nufi cikin building d'in.
"Barka da zuwa ranka ya dad'e." malam iliya dake zaune a kusa da k'ofar elavator ya gaishe shi.
"Barkan mu dai Baba, fatan ka tashi lafiya."
Ya amsa da murmushi, ya san yanayin kallonsa da yake masa na cewar yau ya makara ne, wanda shima bai san ya akayi hakan ta faru ba, da kyar ya iya tashi yau saboda nauyi da jikinsa ya masa da kuma wani irin jiri da ya dinga ji. Sai da yasha duk wasu magungunan kariyarsa harda wanda ya shanye gaba daya ma sannan ya iya shiryawa da kyar ya fito.
Ya shiga cikin elevator d'in ya danna floor na shida, ya d'an jingina kansa da gefe yana kallon yadda numbobin ke canjawa suna yin sama.
Tunaninsa ya koma kan jaamil da ya dawo shekaranjiya, dole ne a yau ya neme shi su san yadda zasu shawo kan matsalar nan, tunda ba jikinsa ne ke ciwo ba balle yace irin rashin lafiyar bil'adama ce, tun daga cikin ruhinsa yake jin juyawar komai, kuma hakan ba karamin abu bane.
K'ofar ta bud'e, ya fita da sauri ya nufi office d'insa, kafin ya shiga ya hango Sales Personnel dinsu yana fitowa daga office d'insa, bai ko tsaya ba ya bud'e nasa office din ya shige, don a nasa matsayin na Marketing Manager ba yadda za'ayi ace sun hadu dashi su rasa abin tattaunawa, kuma a halin da yake baya bukatar magana a yanzu, yafi son ya samu waje ya d'an kwanta kad'an ko zaiji daidai.
Sai dai me? Yana isa teburinsa yaci karo da file d'in da aka ajiye masa jiya da yamma, na cewa k'arfe tara zasu shiga meeting da stakeholders d'in kamfanin G&M akan matsalar da suke fuskanta, kuma a matsayinsa na marketing manager kusan shine mai magana a wajen.
Yaja k'aramin tsaki sanda ya ajiye briefcase d'insa akan table din, speech din ba abu ne mai wuya ba, ko a wajen he can come with something kawai k'arfin zama a meeting d'in ne matsalarsa. Ya koma ya sawa kofar key sannan ya nufi kan couch d'in dake gefen window, ya zuge curtains d'in yayi kwanciyarsa anan yana jin kowacce jijiya ta jikinsa na fitar da rad'ad'i.
Har karfe tara aka fara taruwa a hall na meeting d'in babu alamun Imran saboda haka shugaban company DR. SULAIMAN TURAKI, ya bada umarnin aje office d'insa duba shi.
Imran ya bude idonsa da kyar sanda aka fara knocking d'in kofar, ba zai iya tashi ba saboda haka ya mik'a hannunsa kawai ya bud'e daga nan. Shamsu ya turo k'ofar ya shigo, ba hasken fitila sannan an rufe labulayen.
Yana ganinsa ya fara k'ok'arin mik'ewa.
"Ya salam, Imran baka da lafiya ne?"
"Wallahi, kaina ke d'an ciwo."
"To ai da kayi reporting kawai ka zauna gida, iI'm sorry, bari in fad'a musu."
"A'ah karka damu, yanzu nake shirin tashi dama...Its nothing."
Ba zai taba iya missing meeting d'in ba, don abinda zaije yayi sune 'yan kananan abubuwan da zasu hadu su gina masa YARDA a wajen Dr. Turaki, kuma YARDA, itace zata sa ya cimma manufar zuwansa cikin wannan rayuwar, itace zata sa ya cimma burin daya dad'e a zuciyarsa. Saboda haka da kyar ya tattaro duk wani karfinsa suka nufi meeting hall din.
Suna shiga Dr, Turaki ya yafito shi, ya zagayo ya biyo ta seat d'insa.
"Where have you been? Ka san we can't keep this people waiting..." sai kuma ya lura da idonsa. "...baka da lafiya ne?"
"I'm fine, just a minor headache. Bari mu fara."
Ya samu waje ya zauna, aka fara meeting d'in. Da kyar ya iya jurewa har d'aya kamfanin suka gama presenting reasons d'insu na kin amincewa da janye contract din da zasu yi sannnan ya tashi ya fara opposing komai da suka fad'a, tun suna iya protesting har ya d'aure su da jijiyoyin jikinsu, ba yadda suka iya haka suka yadda aka janye contract din. Wani abu da shi kansa Imran d'in bai san zai yiwu ba, kowa yayi ta zuwa yana taya shi murnar k'ok'arin da yayi sannan Dr. Turaki ma yayi ta shaking hannunsa yana murna, wanda hakan ya k'ara sawa kansa cigaba juyawa.
Saboda haka nan da nan ya nemi izinin tafiya gida, aka bashi kuwa da full assurance. Har ya kai k'ofar fita ya tuna ba zai ia driving ba, saboda haka ya dawo ya samu malam iliya ya bashi key d'in motarsa.
Sannan ya juya ya nufi bayan building d'in, sai da ya tabbatar babu wani ido dake ganinsa sannan yayi wani abu daya kusan manta shi a rayuwarsa, ya rufe idonsa a hankali ya sulale yabi iskar wajen.
****
Zuwa dare jikin Imran yayi tsanani sosai ta yadda baya iya ko mik'ewa, a lokacin sunyi duk wani k'ok'arin da zasu yi shida jaamil amma sun kasa gano komai. Ko sallah ma sai a zaune yayi.
Wajen sha biyu na dare, jaamil ya shigo d'akin ya zauna daga gefen gadon da yake lullube ya dafa goshinsa, har a sannan jikinsa da zafi sosai.
Ya d'an ja tsaki sanda Imran d'in ya bud'e idonsa.
"Na gaya maka ka fita daga jikin nan watakila zaka ji sauki."
"Nima na gaya maka ba ruwan jikin da abinda nake ji, tun daga cikin ruhina ciwon yake."
"Dole ne fa akwai dalilin ciwon nan, irin wannan abin baya faruwa haka kawai."
"Nima tunanin da nake kenan, amma na kasa gano komai."
Jaamil ya d'an yi shiru kafin yace.
"A tunani na kamar wani yana hukunta ka ne akan wani laifi da kayi, kuma a yanzu baka mu'amala da kowannenmu balle muyi tunanin wani, ko kuma ana son wani abu daga jikinka na asali, ko....."
Bai karasa ba ya tsaya, Imran ya juyo a hankali ya kalle shi, idanunsa sun tafi alamun tunani, kamar zai nemo wani abu daya sani ne amma ya manta.
"Me kake tunani?" ya tambaya da muryarsa mai zurfi da taushi.
"Ina tunanin na gano dalilin rashin lafiyarka...."
"Mene shi?"
Maimakon ya bashi amsa, kawai sai ya mike ya fita daga d'akin.
Tun Imran na jiran dawowarsa, har ya samu wani bacci mai nauyi ya tafi dashi wanda bai farka ba sai washegari da safe. A lokacin jaamil ya dawo yana zaune daga gefe yana juya wayarsa a hannunsa.
"Yaushe ka dawo?" ya tambaya yana murza idonsa.
Jaamil ya d'ago ya kalle shi sannan ya jefo masa wayar.
"An kira daga wajen aikinka na gaya musu cewa baza ka iya zuwa ba."
"Da baka fada ba, don jikina yayi kwari zanje yau."
"Ba zaka samu damar zuwa ba, akwai abinda zamu yi yau din."
Jin haka yasa ya juyo sosai ya kalle shi.
"That reminds me, kace ka gano dalilin rashin lafiyata, so ina kaje jiya?"
Jaamil yayi ajiyar zuciya sannan a hankali yace.
"Ya sunan yarinyar nan?"
A lokaci d'aya kwakwalwar Imran ta soma aiki, don mace daya ce jaamil zai tambayeshi ita haka, yarinyar daya riga ya goge komai daya dangance ta daga cikin rayuwarsa ya ajiye a gefe. Me zai kawo zancenta kuma yanzu?
Ya had'iye abinda ke bakinsa kafin yace.
"Sa'adha...?" sunan da bai taba tunanin zai sake furtawa ba.
Jaamil ya gyada kansa sannan yace.
"Itama bata da lafiya!"
¡ñ©n¡ñ
NB.
Me kuke tunanin ya samu Nanne?
Meye had'in rashin lafiyar Nanne data Imran?
*****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
15
(¡î_¡î)
Bata taba tunanin yaya ake mutuwa ba, ko yadda ruhi ke fita daga cikin jiki. Duk da cewar koda ta yin ba zata taba yarda cewa haka mutuwar take ba.
Ta tsaida idanunta akan siffofi biyun dake tsaye akanta, bata iya ganin fuskokinsu don a cikin duhu ne, saboda haka bata san ko su waye ba, amma tana ji a jikinta cewa kamar ta sansu ne tun asali, kamar sune wani b'ari na jikinta da ta dade tana nema.
Saboda haka, hankalinta ya kwanta, zuciyarta ta sami nutsuwa, ta maida idanunta ta rufe a hankali sanda hannun d'aya daga cikinsu ya sauka a goshinta, wani sanyi ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta sannan duk wani ciwo nata yabi iska!
*****
Lokacin da ta farka da safe, wani abu ya canja, wani abu daban da yadda ta saba gani, ta shiga zagayawa da idonta cikin d'akin. Akwai dai hasken rana dake shigowa ta cikin labule, wanda yayi tar! Kamar an kara masa kala.
Sai kuma ta lura ba hasken bane kadai yayi wannan tar d'in. Komai na d'akin ne idonta ke dauko mata shi haka. Kamar taje wankin ido an cire duk wani datti dake cikinsa. Muryar inna ta fara shiga kunnenta, tana karb'ar gaisuwar mutane da yawa da d'akin ya d'auka da maganganunsu.
"Lafiya kalau mun gode Allah, ya wajen naku kuma."
Muryar wani namiji ta amsa.
"Lafiya kalau inna, ya kuma mai jikin? Mun shigo ne sai Hajiya take fad'a mana wallahi."
"Da sauki, da sauki wallahi an gode Allah."
Jin haka yasa ba shiri ta juyo da kanta b'arin da suke, anan idonta ya gane mata dakin cike taf da jama'a, bayan inna akwai su Aunty maryama da Aunty nafisa, da kuma wasu mata biyu da bata sansu ba. Sai hajiya Babba dake tsaye daga bakin k'ofa ta rako k'aramin k'aninta da yayi aure kwanaki da matarsa, yana rik'e da d'ansu a hannu, sai yanzu ta gane muryarsa ce taji.
Aunty maryama ta taso da sauri ta nufo kan gadon.
"Nanne kin farka, sannu ya jikin naki?"
Jikinta? Me ya sameta? ta kalli sauran jikin nata, sannan kwakwalwarta ta tuna da duk abinda ya faru. Aikuwa da sauri ta mike daga kwancen da take, a tunaninta zata sake jin wannan nauyin irin na jiya.
"Yi a hankali karki fad'i." Aunty Nafisa ta fad'a rike da 'yarta, ilham a hannu.
"Aunty naji sauki, ba wani ciwo a jikina."
"A'a Nanne jikinki ba kwari, maryama jinginar da ita da filon nan."
"Inna bana son sake kwanciyar dan Allah." Ta fada har cikin ranta, don da gaske gani take in ta sake kwanciya zata kasa tashi.
"Inna a barta ta sauko k'asan, ai da alamun sauki a jikinta." hajiya babba ta fad'a tana k'arasowa cikin d'akin.
Aunty maryama da d'aya daga cikin matan nan suka kama ta aka sauko da ita kan carpet, kowa sai faman yi mata sannu yake.
"Toh mu zamu koma inna, Allah ya kara sauki ya bata lafiya."
Wannan k'anin hajiya Babba ya fad'a, sannan suka yiwa sauran sallama