Showing 78001 words to 81000 words out of 113985 words

Chapter 27 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28461

gwaggo kika ce in fad'a miki fad'a zanyi, don kwanan nan zaki tsufa bari ki fara haihuwa ki gani, sai anzo ana musu dani ina wallahi k'anwata ce ana Sadiq wannan ai babarka ce."

Suka kyalkyale da dariya har Inna kafin ta d'auki filo ta maka masa.

"Toh ina d'an handsome mijin naki? Kin san kwanaki su Abubakar d'in bayan layin nan suka tare ni wai dan Allah in gaya musu a ina kuka had'u, wai sun san gayen tun zuwansa unguwar na ba wadda yake kulawa, maza ma sallama ce kawai ke had'a su."

Tace. "Toh me kace musu?"

"Kin san ni bana son irin wannan munafuncin, ce musu nayi wani mai dalilin aure ne a can baya ya had'aku."

Nanne ta sake kyalkyalewa da dariya.

"Kuma sun yarda?"

"Wallahi sun yarda, harda cewa wai zasu sa rana in raka su suma, na bisu da toh kawai."

A cikin hirarsu Inna ta tambayeta sanda zasu dawo daga tafiyar da tace mata zasu yi.

"Inna wallahi ban sani ba don bai fad'a min ba, kawai yace in gaya muku zamu yi tafiya."

"Ina zaku je?" Sadiq ya tambaya.

"Nifa ban sani ba, amma tunda da waya duk inda muka je zan kira ai."

"Kaga hajiya Amarya, wato honeymoon d'in ma baza'a fad'i ina ne ba don kar a dame ku."

Ta sake d'aukan filo ta maka masa.

"Ni nace maka honeymoon zamu je."

Inna tace.

"Duk inda dai zaku ya kamata a sani, tafiya irin wannan da zata iya yin nisa."

Sai bayan sallar isha sannan Imran yazo, ya d'an dade tare da Inna suna hira sannan yaje ya gaishe da baffa, kamar yadda yayi ta addu'a da sawa Nanne albarka haka shima yayi tayi masa, tare kuma da kallon da Imran ya fassara da cewar Ka kula da ita.

I will, da dukkan iyawata Baffa! Shima ya amsa da idanunsa.

Aka lodawa Nanne kayanta a mota sannan suka tafi bayan Inna tasa tabi su hajiya Babba duk tayi musu sallamar tafiyar da zasu yi.

"Kayan meye wannan?"

Imran ya tambaya sanda suka hau titi.

"Kayan ka ne."

Ya juyo sosai ya kalleta.

"Ni kuma? a ina na sami wannan kayan?"

Tayi dariya kafin tace.

"Wasa nake yi fa, wai ragowar kayan da ba'a kai min bane, yawanci ma na amfanin kitchen ne."

Yana jin haka ya maida idonsa titi, fuskarsa ba alamun murmushi balle dariya, Nanne tayi sensing wani abu na damunsa saboda haka tace.

"Ka san cewa kafi kyau in idanunka suka zama so light."

Kafin yayi magana tunaninta ya dawo mata da amsar daya bata kwanaki biyu da suka wuce, sanda ta tambayeshi game da idonsa dake kyallin silver.

"Shine na farko da kika fara gani Sa'adha, a yanayin halittar mu, mood d'in mu yana reflecting ne a idonmu, I'm being myself aroud you now, zan dinga sakewa duk sanda ina tare dake akan k'ok'arin b'oyewar da nake a baya, Saboda haka zaki ga yanayin idona na canjawa a lokuta da yawa."

A yanzu kuma taga sanda ya ciji lebb'ensa kafin yace.

"Wane color yayi yanzu?"

"Dark. So dark!"

Ya sake datsa lebb'ensa.

"Ban san me nake ji bane Sa'adha, I don't know what I'm feeling, 'yan gidanku sun yarda dani da yawa alhalin ina yaudararsu ne...kowannensu yana min kallon wani mutumin arziki, Wallahi bana son abinda nake Noory."

Nanne ta maida kanta gefe tana kallon titi, ita kanta a lokacin da Inna ta tambayeta game da zancen 'yan uwansa, da kyar ta iya lalubo karyar da tace mata sun zo basu dad'e bane suka koma garinsu.

Zuciyarta tayi nauyi da tunanin, in har su Inna suka ji gaskiyar WAYE Imran ya zasu yi? ya zasu ji in suka san wa suka aura mata? in har akwai matsalar da take hangowa a zamanta da Imran, bai wuce yadda zasu yi ta lullub'e komai ga iyayenta da 'yanuwanta ba, amma ita ta riga tayi deciding zuciyarta, ta tsaida ita a waje d'aya...zata zauna da Imran a kowanne hali in har ba zai cutar da ita ba.

Tana son shi, kuma tana sonshi har cikin zuciyarta!

********

"At least ka d'an bani hint mana, ko don in san irin kayan da zan d'auka."

Nanne ta fad'a tana kallon Imran dake kwance akan gado yana cafe kayayyakin da take jefowa daga cikin wardrobe, ya d'ora kafarsa akan d'aya, sannan hannunsa d'aya cikin gashinsa.

"Hint kike so? toh dogwayen rigunan ki ma zasu yi, akwai musulmai a inda zamu je."

"Musulmai? wane yare suke yi?"

"Kala-kala, amma karki damu za'a samu wanda kika iya."

Ta matso kusa da gadon tace.

"Toh farare ne ko bak'ake mutanen wajen?"

Ya d'age girarsa d'aya yace.

"I think suna da haske."

Nanne ta tsuke baki tana kallonsa sanda durk'usa a gefen gadon rike da wani pink mayafi.

"Toh wajen zafi ne dashi ko sanyi?"

Ya d'an tsaya yana kallonta.

"Wai wayo kike son yi min?"

Ta karkata kanta kad'an.

"Ta ya zan maka wayo so nake kawai in sani..."

"Mhmm-Mhmm baby girl, wannan k'ifta idon ba zaiyi tasiri akaina ba..."

Ya karb'e mayafin hannunta sannan ya jawo ta kan gadon.

"...In kina son ki san inda zamu ki bari gobe insha Allah zaki fara gani."

"Fara gani ba waje d'aya bane kenan?"

Imran ya juya idonsa, sannan ya mik'a hannunsa sama ya kashe switch d'in d'akin.

"Enough talking for today, in ba haka ba zaki sa in fad'a miki komai da komai yanzu."

"Ban k'arasa had'a kayana ba fa." Ta fad'a a cikin duhun.

Ya lalubi gefen kunnenta ya rad'a mata a hankali.

"Wanda ya shiga cikin akwatin sun isa Sa'adha, beside bana jin ma duk wannan kayan zasu yi miki amfani sosai a can."

Ta lumshe idanunta tana shak'ar k'amshin jikinsa.

"I give up Ulfat! na hak'ura da sani Allah ya kaimu goben."

"Ameen Habibty."

Bayan kamar minti talatin, har Imran na tunanin tayi bacci, yaji muryarta ta kira shi a hankali.

Can k'asa-k'asa ya amsa shima kamar ya fara bacci. Ta b'alle buttun d'in gaban rigarsa a hankali sannan tace.

"Yaushe Naani zata dawo? Kuma me zai faru in ta dawo?"

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

49

(¡î_¡î)

"Naani ba yanzu zata dawo ba, kuma kafin ta dawo we will figure a way out, ba abinda zai faru insha Allah Sa'adha, kuma ba zan tab'a rabuwa dake ba."

Wannan sune kalaman Imran na jiya da suka kwantar da hankalin Nanne kuma suka bata kwarin gwiwar tashi a yau ta kammala komai na tafiyarsu, ta gyara gidan ta rurrufe komai da ta san zaiyi k'ura. Karfe goma sha biyun rana tayi musu ne a cikin airpot, har Imran ya gama duk wasu shige da ficensa tana tsaye bata san inda zasu ba, sai da suka shiga cikin jirgin ne sannan ta tambaye shi.

"Zamu dad'e bamu dawo ba?"

Maimakon ya bata amsa sai ya kamo hannunta cikin nasa ya murza a hankali.

"I love you!"

Hakan ya tabbatar mata cewa ba zata sami amsarta ba, saboda haka ta kwantar da kanta a gefen kafad'arsa kafin a hankali tace.

"That's why we're here."

*******

"Lagos..?"

Nanne ta tambaya sanda suka sauka daga jirgin bayan tafiyar kusan awanni biyu.

"Itace hanyar da zamu bi ta farko."

Ya fad'a da murmushi sanda yaja hannunta suka nufi hanyar building d'in terminal, anan bayan wasu cike-ciken da kuma b'ata wani lokacin suka k'arasa international counter inda suka yi boarding wani flight d'in.

"Australia?" Ta sake tambaya sanda ya karbi tickets d'in suka mik'e wata hanya.

"Itace hanyar da zamu bi ta biyu." ya fad'a da wani murmushin.

Tafiyar daga lagos zuwa Australia awa bakwai ne, but it was comfortable tunda suna zaune ne a fad'ed'en seat d'in first-class. Abinda ya sata tunanin irin kud'in da Imran ke dashi.

"Ayunie..."

Ta kira a hankali tana kallon hannunsa dake nannad'e a cikin nasa, Babbar hanyar communication d'insa, sau da yawa zasu zauna suyi shiru amma in har hannunsa na cikin nata, sai taji kamar magana suke yi.

Sai da Imran ya d'anyi shiru sannan ya fahimci sabon sunan da ta kira shi dashi, wani dad'i ya ratsa shi, yayi murmushi kad'an sannan ya amsa.

"A ina kake samun kud'i, na zata tunda baka dad'e da shigowa cikinmu ba, bai isa ka tara kud'i da yawa ba."

The question is so silly, Yayi k'ok'arin kar yayi dariya amma ya kasa hana kansa.

"Na gaya miki Naani ta tanadar min komai kafin zuwana, akwai account guda da dimbin kud'i wanda a lokacin ban san adadinsu ba, sannan tunda na fara aiki, ina samun kud'i a kowanne wata da har wani amfani nake dasu sosai ba."

Ta gyada kanta alamun ta fahimta. Ya matso da bakinsa dab! da kunnenta sannan a hankali yace.

"I like the name...AYUNIE...yana da dad'i sosai Noory."

Tayi murmushi tana b'oye fuskarta a jikinsa. Zuwa can ta d'ago ta kalle shi.

"Ka tuna ranar da ka maida ni gida da daddare?"

Ya d'anyi shiru kafin ya amsa.

"I dont want to talk about it, bana son tuna wannan ranar habibty."

"Saboda me?"

Saboda mutanen nan. Ya amsa a cikin kansa, mutanen daya kasa d'aukan wani mataki akansu saboda ita, saboda kar taji tsoron da zai sa mata wani zarginsa a lokacin.

Amma yaso ko da motarsa ne ya take su, ko kuma ya shak'e wuyansu ta yadda k'ashin wajen zai kakkarye, ko yayi ta marin su har sai jinin jikinsu ya gama fita ta baki. He wanted to kill them so bad, yadda duk sanda ya tuna hakan sai yaji kamar zai danne hak'oran bakinsa har sai sun marmashe. Bata damu da rashin bata amsa da yayi ba ta zarce da tambayarta.

"Ranar ma yana cikin tsarinku?"

Ya girgiza kansa da sauri.

"Baya ciki ko kad'an, i swear to you k'addara ce kawai ta had'a ni dake a ranar, naje gidan wani d'an office d'inmu ne a hanyar daya takura mana da gaiyata ni da sauran mutanen office d'in, tun yamma ma muka je muka kai har bayan maghrib, ni na riga su fitowa shine lokacin da na hango ki a hanya..."

Ya kasa k'arasawa saboda tunanin wad'annan mutanen.

"Lokacin da ka kaini wannan chemist d'in? k'arfe tara da minti goma sha biyu amma har na koma gida tara da minti ashirin, ta yaya hakan..."

"I was driving so fast..." Ya katseta.

"...Na kare idanunki ne kawai daga gani amma sauri nake yi sosai, saboda bana so hankalin Inna ya tashi duk da cewa Sulaiman ya fad'a mata."

Ya fad'i kalaman da gaskiya har cikin zuciyarsa, ya riga yayi wa kansa alk'awari ha zai sake b'oye mata komai ba a zamansu zai fad'a mata dukkanin amsar da take nema da dukkanin gaskiyarsa sai dai banda abu d'aya.

Abu d'aya daya san cewa yafi k'arfin tunaninta, abu d'aya da in ta sani zai zama sanadin rasa nutsuwarta, abu d'aya da zai sa ta daina sakewa dashi, ba zai tab'a iya fad'a mata cewar Naani ta dawo kuma baza'a iya raba ruhinsa da nata ba tare da a rasa ransa ko nata ba.

Tun tana masa tambayoyi kala-kala na wasu 'yan k'ananan abubuwan da bata fahimta game dashi ba har tafiyar ta mik'a bacci ya kamata, wani bacci mai nauyi da bata ko farka ba sai lokacin da suka isa k'asar Australia, da daddare ne lokacin saboda haka bayan sun sauka da kyar take iya bud'e idonta a cikin hasken fitulun dake dallare a ko'ina, kwata -kwata bata san abinda Imran keyi ba, kawai janta yake yi tana binsa a cikin hayaniyar Airport d'in mai cike da yare kala-kala a lokaci d'aya kuma tana k'ok'arin bud'e idanunta.

Bayan kamar minti talatin suka yi connecting to wani jirgin da bata san ina ya nufa ba don suna shiga ta sake k'udundunewa a jikinsa ta koma baccinta.

Sai bayan kusan awa biyu sannan ta farka, har a lokacin basu sauka ba, ta tsakuri abinda zata iya ci a cikin abincin da a kawo, sannan ta shiga tambayarsa inda zasu je kuma, amma yak'i fad'a mata kuma ya hanata ganin takardun airport d'in dake hannunsa.

Haka ta hakura ta sake langab'ewa a jikinsa tana jin kowacce gab'ar jikinta na amsawa sakamakon kusan zaman awa goma a jirgi, ta tabbata yanzu a Nigeria tsakar dare ne su da suka taso tun wajen karfe biyuna rana.

Lokacin da jirgin ya sauka bayan tafiyar awa uku da 'yan mintuna, Nanne ta ware idonta ganin k'aton signboard mai d'auke da haken fitilu dake ta dallare ta yana walk'a kalmomin.

WELCOME TO MALE!

"Ina ne kuma Male?"

Ta tambaya sanda aka gama X-ray d'in kayansu wani bature mai uniform ya d'ora su akan gurney ya biyo bayansu.

Yayi murmushi yana kallonta kafin yace.

"Itace hanyar da zamu bi ta uku!"

Daga haka bai k'ara mata magana ba ya rik'e hannunta har suka fita daga cikin airpot d'in, wannan mutumin na ta binsu ture da gurney d'in.

Nanne in banda zare ido tana kallon mutane ba abinda take, jinsi ne kala-kala na dangain fararen mutane ke ta harkokinsu, tsilli-tsilli kawai take hango bak'ar fata shima ba irin wanda ta saba gani ba, don fararen ma gani take kamar ba'a gaske take ganinsu ba, das-das dasu, ga gashi yala-yala daga mazan har matan.

Da yawansu sanye suke da dogwayen riguna irin na jikinta, wasu matan ma harda Niqab so she didn't felt so different in banda fuskarta data kumbura sakamakon baccin data sha. Ta tuna maganar Imran a jiya ne ko shekaranjiya.

"...dogwayen rigunan ki ma zasu yi, akwai musulmai a inda zamu je."

Saura kad'an tayi tuntub'e ba don yana rik'e da ita ba sanda ta hango wata 'yar yarinya fara tas! mai bak'in gashi dogo, kayan jikinta masu kyau harda wata 'yar karamar jaka ta goya a bayanta, ita da mamanta ne maman nata waya ita kuma tana tsaye a kusa da ita sai 'yan juye-juyenta take, taji kamar ta koma ta d'auko ta ace ma an bar mata ita har abada.

Sanda suka fita can harabar airport d'in, Imran ya d'auko wayarsa data lura ya canja sim tun a cikin jirgin ya kira waya cikin wani yare da bata idea wanne ne. baifi minti biyu ba, wata shuttle bus ta k'araso inda suke, mai gurney d'in nan ya saka musu kayansu Sannan suka shiga, babu kowa sai driver da yake kamar bafaranse don ta tsinci wasu 'yan kalmomi a maganar da suka yi shida Imran, mamaki take yi na adadin yaren daya iya.

"Mun kusa insha Allah Noory" Ya fad'a yana kamo hannunta, bata ce komai ba sai murmushi kawai data masa.

Motar ta cigaba da tafiya ta cikin manya-manyan titunan masu d'auke da fitulu rutu-rutu da kuma mutane, mutanen da Nanne ke gani wasu iri a idanunta, a hankali kuma yawansu dana gine-ginen ya ragu har suka k'araso edge na titin, a gabansu duhun wani k'aton ruwa ne daya mamaye gabansu gabad'aya.

Motar ta tsaya a k'arshen wani titi daya tsaya a daidai hanyar da zata d'auke ka zuwa port d'in dake gabansu, 'tashar jiragen ruwa' gasu nan fal manya da k'anana, wadu daga can nesa a cikin ruwan wasu kuma a tsaitsaye.

Nanne taji ta had'iye yawu sanda ta d'aga ido ta hango wani tafkeken jirgin a tsaye cikin ruwan, taji wani imani ya ratsa ta ganin yadda duk girmansa yake tsaye a cikin ruwan ba tare da nutsewa ba. Imran ya rik'e hannunta zuwa wata doguwar hanya ta katako data kaisu can bakin ruwan, yana ta magana da mutane kala-kala cikin yaren da bata ganewa. Daga k'arshe suka ka'rasa wajen wani d'an madaidaicin jirgi fari tas dashi, sai kyalli yake alamun sabunta, aka saka kayansu da wani ya d'auko lokacin da matukin jirgin ke warming d'insa.

Ya juyo ya kalleta a hankali tare da mik'o mata hannunsa d'aya.

"Bismillah..."

Nanne ta juya ta kalli k'aton tekun dake gabansu, bakikirin ba wani alamun haske, ga manya-mayan jirage a cikinsa ga kuma iska na kad'awa kota'ina, sanna ga tarin fararen mutanen da bata taba ganin irinsu ba. Ina zasu je a cikinsa? Sai kawai ta girgiza kanta da sauri.

"Ba zan iya ba, ba zan iya shiga cikin ruwan ba, ina zamu je a cikinsa?"

"You have already trust me Sa'adha, kin riga kin yarda ba zan cutar dake ba, So you don't need to be afraid"

Yayi maganar a hankali cikin husky voice d'insa, Nanne taji iskar dake kad'awa ta hura koina na jikinta, zuciyarta tayi nauyi a kirjinta cike da tsoro, amma ta kasa daurewa kyawawan idonsa da kuma hannunsa dake jiran nata saboda haka ta had'iye yawu sannan a hankali ta d'ora hannunta akan nasa.

"I'm here.." Ya fad'a a cikin kunnenta sanda ya rik'e waist d'inta ya shigo da ita cikin jirgin. Ta d'aga kanta kawai ba tare da ta d'ago daga kallon deck d'in ba.

Daga tsakiyar akwai wata rumfa mai d'auke da wata doguwar kujera mai taushi, daga gaba kuma rumfar mai tuk'a jirgin ce, ya rik'e ta a hankali cikin lilon da jirgin yake suka zauna kujerar nan, hannayenta a duk'unkune cikin rigarsa ta cukwikuyeta, bayan kamar minti biyu mutumin ya tada jirgin suka figa cikin igiyoyin teku, wata iska mai dad'i tayi spraying akan fatarta, tana jin sanyinta koina na jikinta, ta juya baya a hankali tana ganin yadda suke wa fitilolin garin Male nisa, a hankali taji tsoron nata yana tafiya tare da iskar wajen atleast hakan yafi da ace ta kalli bak'in tekun dake gabansu.

Bak'in tekun da bata san inda zai kaisu ba, bayan kamar minti goma ta tambayeshi in sun kusa, ya kalli agogon hannunsa sannan yace.

"About another ten minutes."

Tayi ajiyar zuciya sannan ta sake binne kanta a cikin wuyansa. Watakila Muzzafar d'in tasu zai kaita, inda zata ga ainihin 'yanuwan halittarsa.

Bayan kamar minti goman kuwa, ya kira sunanta a cikin rugugin k'arar injin jirgin.

"Sa'adha d'ago kiga."

Hannunsa ya mik'e straight zuwa gabansu.

Nanne ta juyo a hankali tabi hannunsa da kallo, a lokacin taji ragowar tsoron dake kwance a zuciyarta ya washe gabad'aya...ta kifta idonta ta sake k'iftawa, ba karya bane su d'in ne dai suke dosar wani waje mai cike da yawan fitilu kala-kala da kuma dogwayen bishiyun kwakwa kyawawa, wasu irin dogwaye da hata taba ganin irinsu ba, tun daga nan kuma tana hago wasu irin had'addun gine-gine masu sa zuciyar mutum tsayawa, gabad'aya wajen is a combination of beauty wanda bata tab'a gani ba.

"Ina ne nan?" Ta fad'a a hankali muryarta can k'asa, sanda jirgin yayi kwana ya nufi wata hanya inda ta hango wasu jiragen tsaye daga k'arshen gab'ar wajen.

Yaji me tace duk da rugugin injin da kuma k'arar iskar dake kad'awa.

A hankali ya rad'a a cikin kunnenta.

"Welcome to Maldives Island!"

¡ñ©n¡ñ

Dan dan dan dan dan....

Honeymoon starts here!??

You don't wanna miss d next chapter!??

Babi na hamsin ba wasa bane.??

*****

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

50

(¡î_¡î)

A hankali take taka marbles d'in cikin gidan mai wani irin santsi da barefoot kafafunta, Saboda ta ajiye takalminta tun a cikin jirgin nan, sanda ta fara fitowa ta nutsar da k'afarta a cikin yashin beach d'in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login