Showing 9001 words to 12000 words out of 113985 words

Chapter 4 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28455

matar da ranar girkinta ce, ita zata bada odar abincin da za'ayi ta kuma tsaya a kicin d'in har sai an gama an rarrabawa kowanne d'aki, har da 'yan mazan kowa tray d'insa daban mai d'auke da flask, plate da cokula harda jug saboda ba'a taba yin abinci a gidan ba babu abin sha, musamman zob'o kusan kullum akwai shi a gidan nan.

Sannan ba wanda zaici abincin yace na gidan yawa ne don ma'aikatan gidan gabad'aya an bi musu da tsari akan tsafta, sannan ma girkin kamar gasa ya zama tsakanin matan, kowacce na son ace ranar girkinta abinci na dad'i saboda hatta baffa shi yake ci, bai taba son a banbanta nasa ba.

"Kije ki karbo mana."

"A wannan yunwar da nake ji yaushe zan iya sauka k'asa."

"Toh ai sai kisa hannunki tunda daga wanka kika fito."

Ta zuba abincin, ta koma kan kujera ta fara ci, idonta na kan agogo tana lura da lokaci. Bata san me yasa jikinta yayi sanyi ba duk da sun gama tsara komai ita da Amina, kuma ta dake ranta cewa zata yin, amma jikinta kwata-kwata ba kwari.

Ta rufe idonta tana tauna abincin, haka kawai taji ko dadi ma baya mata, saboda haka ta rufe shi ta zura dogon hijabinta.

"Ina zaki da tsakar ranar nan."

"Islamiyya mana, kin manta tun wancan satin na koma."

"Yaushe naji kina cewa canja ta zaki yi?"

"Na fasa ai."

"Ai miki wannan dukan kuma ki cigaba da zuwa?"

Ta hadiye yawu cikin makogwaronta.

"Inna ba lallai bane ma malamin ya kara shigo mana, bari inyi sauri kar su safiyya su tafi."

Tunda ta isa cikin ajin nasu ba wanda ta yiwa magana, da yake ma kusan rabin ajin na jin haushinta akan dukan data jawo aka musu sai ba wanda ya kulata, iyaka kad'an dake binta da sannu kawai. Ko da rahama ta iso ma da ka kawai ta amsa tambayar data mata.

Malamin fiqhu ya shigo ya biya karatunsa yayi bayani sannan aka fita sallah, ana dawowa malam murtala ya shigo aka fara bita, tunda aka fara kuwa nanne bata ko d'ago da kanta ba balle tayi karatun, har akayi izu biyar, sannan ya biya k'ari yace suma su biya. A nan ma ta k'ara dankwafar da kanta ta, tun yana kyalewa har zuciya ta kawo shi yace kowa yayi shiru.

"Sa'adha tashi ki biya karin da aka yi!"

Bata ko motsa ba balle ta nuna taji me yace. Ya sake maimatawa ba wani canji, Rahma dake gefenta ta tabo cinyarta bata d'ago ba, gabadaya 'yan ajin sun juyo kowa na kallonta, ai kuwa bai k'ara magana ba ya janyo bulala yayo kanta, Rahma tayi saurin matsawa sanda ya k'araso ya sauke mata guda d'aya a tsakiyar bayanta.

Ai kuwa tana jin vibration d'in bulalar a jikinta taji wani irin karfi da bata san tana dashi ba ya shige ta, kafin kwakwalwarta ta iya wani tunanin taji wata bulalar a jikinta ba shiri kuwa ta mike tsaye, ta fito bakin bencin ta tsaya daf dashi idanunta a tsaye kyam!

"Keh baki da hankali? ni kika tsayawa a kai haka, koma ki zauna...nace koma ki zauna!"

Tak'i zaman, ta tsare shi da dara-daran idanunta da bata san sunyi jawur ba, ya d'aga hannunsa ya k'ara mata wata bulalar, ba tare da tunanin komai ba kuwa nanne ta waska masa mari, mai kauri sannan ta cakumi wuyan rigarsa, ta d'aga shi sama har sai da kafarsa ta rabu da k'asa.

Ajin gaba d'aya ya rude da ihu wasu kuma suka yi waje, malam murtala yayi-yayi ya raba hannun nanne da rigarsa amma ya kasa gashi bata ko ihu balle magana, sai zazzare jajayen idonta take yi ga kuma radadin marin na shigarsa.

A haka wasu malaman biyu suka shigo suka ratsa ta cikin cincirindon daliban suka raba su da kyar. Tana sakinsa kuwa ta sulale ta fadi kasa kamar an zare wani abu daga jikinta.

Aka fita da malam murtala, d'aya malamin kuma ya shiga bada umarnin a daga ta, rahama ce ta fara zuwa kanta tare da wasu mutum biyu, suka maida ita kan bencin. Nan fa makaranta ta rude daliban wasu ajujuwan suka dinga shigowa, malaman sukayi-sukayi kowa ya koma aji amma suka kasa, sai tururwar ganin nanne suke da kuma malam murtala da aka kai staffroom.

Har aka tashi, Rahma da sadiya suka raka nanne gida bata san inda kanta yake ba, don wani irin ciwo yake mata da kuma juyawa. Saboda haka koda rahama ta cewa inna bata da lafiya ne, bata d'aga hankalinta ba ta barta ta kwanta.

Tana yin sallar isha kuwa ta nemi kan gado, a lokacin tasha panadol ya kai hudu amma ba abinda ya ragu, da kyar ta samu bacci ya dauketa.

A cikin baccin, tayi mafarki da fuskarsa, fuskar IMRAN, muryarsa mai taushi ta cika kunnuwanta, a hankali kamar sanda yake mata magiyar sunanta. Sai dai wannan karon sunan ya fad'a, sunanta kad'ai.

"Sa'adha!."

**** ****

"Wai don Allah meya same ki?"

"Rahama nace miki ki daina zancen nan koh? Wai sai inna taji ne?"

"Nanne abin ne ya bani mamaki, na san baki da aljanu, amma d'aga malam murtala fa kika yi har sama, ta yaya kika iya?"

Nanne ta had'iye yawu, itama tun tashinta take wannan tunanin, ta rasa ya akayi taji wani irin karfi a daidai wannan lokacin, karfin da har ta iya daga mutum.

"Nifa ban sani ba, watakila kawai don na sa kaina zanyi ne, saboda haka ni kawai kiyi shiru kar wani ma ya jiki."

Tana fad'in hakan ta cigaba da cillo kayan wankinta daga cikin wardrobe.

"Bari in gama hadawa ki tayani sauka k'asa dasu bello zan bawa wankin, na nasiru baya fita wallahi."

"Nanne..." Rahma ta kira sunanta a hankali.

"Su malam murtala fa sunce zasu zo gidan nan yau, d'azu na hadu da malam mukhtar yake ce min anjima zasu zo."

Ta juyo a hankali rike da wata riga.

"Zasu zo? Me zasu zo suyi?"

"Wai hankalinsu ya tashi aljanin da ya shige ki mai karfi ne, malam murtala yace yaga alamunsa a cikin idonki."

Sakan daya-biyu tana kallonta kamar abinda ta fada ya tsorata ta, kafin kuma ta kyalkyale da dariya harda rik'e murfin wardrobe din.

"Kice malam yaji shak'a, wato a aljanun ma nawa mai karfi ne, aiko zan nuna masa wasu k'arin moves din da aljanin ya iya ne ma duk sanda ya sake dukana wallahi."

Rahma ta girgiza kanta.

"Yanzu toh ya zaki yi in sun zo?"

"Yafi ince karya suke min, ba dai baffa zasu gayawa ba...kar su fasa Allah ya kawo su."

****

Ya lumshe ido yana lokacin da muryar gefensa ke fita cike da bacin rai.

"...me yasa kake tunanin yin abinda ba zai tab'a yiwuwa ba? Me yasa zaka fara abinda ba zai d'ore ba?"

Ya ciza gefen lebb'ensa yana sauraren yadda iskar saharar ke kad'awa da karfi.

"Tana da kyau jamil, idan tana fad'a zaka ga kamar lebbenta zai koma ciki ne."

Jaamil yaja tsaki kafin ya sulale yabi cikin iskar saharar.

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

06


(¡î_¡î)

A daidai kofar shiga falon baffa nanne ta tsinci muryar ya sulaiman cike da bacin rai yana fadin.

"A tunani na baffa gwara a takawa yarinyar nan birki wallahi tun yanzu, abubuwan nata sun fara yawa."

Bata bari baffa ya bashi amsa ba ta murda handle din kofar ta shiga, sulaiman din ne kuwa zaune a katon falon yayin da baffa ke daga can karshe kasan kujerarsa, jaridu kusan uku a gefensa da kofin coffee dinsa.

Ta zube daga tsakiya tana gaishe shi, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya nuna mata gefen hagunsa, ta mike ta koma can. Ba yadda sulaiman ya iya dole ya fita don ya san baffan baya bukatarsa a lokacin.

"Sa'adha me ya faru a makarantarku jiya?"

Muryarsa taso ta yanke karfin gwiwar da ta shigo dashi, ta hadiye yawu a hankali kanta na kasa tace.

"Wace makarantar? Islamiyya ko boko?"

"Islamiyyarku ta bayan layin nan."

"Babu komai, jiya ma da wuri aka tashi."

"Ya akayi akace kin mari malami jiya?"

Da saurinta tace.

"Duk wanda ya gaya maka karyane baffa, ni ba abinda nayi."

Ya gyara zamansa yana kallonta sosai.

"Baki san kin mare shi ba?" Ta d'aga kai.

"Kenan in yarda da abinda malamanki suka fada?" Tayi shiru.

"Nan wajen yayanki ya rako su suka zauna suna fada min wai ba'a hankalinki kika yi komai ba, aljanu ne suka shige ki kuma suna tunanin masu k'arfi ne."

Ta bata rai, ta kirkiro hawaye. "Wallahi baffa karya ake min ni babu aljanin daya shiga jikina, kullum sai nayi addu'a kafin na kwanta."

"idan haka ne sa'adha, toh me zaisa ki daga hannu akan malaminki, ni dai na san har ga Allah ba'ayi miki wannan tarbiyar a gidan nan ba. Wadda ta raineki ita ta raine ni, kuma na tabbata inna baza ta taba cewa kije ki mari malamin ki ba."

Ta shiga rera kuka tsakaninta da Allah tana bashi hakuri, yayi ta nasiharsa akan girman malami da kuma girman laifinta kafin ya sallameta, sai dai har ta gama bashi hakurin ta fita, ransa bai dawo daidai ba.

Tana zuwa daki ta tarar inna ta fara gyangyadinta na maghriba, ta shiga toilet ta wanke fuskarta tana fadin.

Ta Allah ba taku ba, wato a tunaninku baffa yace ku tafi dani ayi min ruk'iya, a sami abin jibga...ba sai kun sake ganina ma a islamiyyar ba.

Ta fito falo ta zuba abincinta sannan ta kunna tv. Abinda ya tashi inna kenan ta mike da salati.

"Me ya sami idanunki suka kumbura?" ta tambaya tana kare mata kallo.

Nanne ta dan ja tsaki, matsalar fuskarta kenan, ko hawaye tayi sai idanunta sun kada.

"Ba komai, kaina ne kawai ke ciwo."

"Ke anya lafiyar ki kalau kuwa? A satin nan sau nawa kika yi wannan ciwon kan?"

Ta d'anyi shiru, duk da ba ciwon kan take ba amma abinda inna ta fada haka ne. Bata fiye ciwon kai ba amma kusan a satin nan sau uku tana yinsa. Anya lafiyar tata kalau kuwa? Sai kuma tayi saurin kawar da zancen kar inna ta shiga damuwa.

"Watakila wahalar komawa makarantar nan ce, in zubo miki abincin ko sai kinyi isha?"

Lokacin da taje jera kayan da aka kawo mata daga wanki, handkerchief din daya bata ya fado, ta sunkuya a hankali ta dauka, tun a wancan daren data ninke shi ta ajiye bata kara bi ta kansa ba, babu ko kanshin turare a jikinsa amma sai taji gabanta ya fadi sanda ta kaishi kan hancinta, wani irin faduwar gaba mai nauyi, kamar an cilla katon dutse cikin ruwa.

Ta ware shi gabadayansa, anan wani mamakin ya tsaida numfashinta, d'an karami ne da baifi a dunkule shi ba. Toh amma yaya akayi a wancan lokacin ya d'auki tarin adduwar data yi kusan rabin leda?

Adduwar da kusan sati d'aya kenan har yanzu bata kare ba?

*****

Gari ya waye, rana ta bude a sararin sama. Yana bud'e idonsa yaci karo dana jaamil zaune akan stool d'in mudubin dake dakin.

"Barka da tashi, ashe ka canja gida?"

Ya mutsika idonsa.

"Wallahi, kwana waje tara kenan da dawowa ta."

"Allah ya sanya alkairi, bamu sani ba ai da munzo mun taya ka d'iban kaya."

"Ai da yake abin ne yazo ba shiri, amma kar ka damu kanka ma ban debo komai na can ba, komai sabo na..."

Bai karasa ba jaamil ya dauki wata kwalbar turare dake kan mudubin ya jefo masa, amma maimakon ta same shi sai ta wuce ta cikin jikinsa ta daki bango ta tarwatse.

"Kwana na uku kenan ina faman nemanka yarima, ina tunanin ba gidan da ban shiga ba a garin nan."

Imran ya mike zaune.

"Toh saboda me zaka shiga nemana? na san dai ba wani abu ne ya taso daga gida ba."

"Idan a wajenka babu wani abu, ni dole ne inyi taka tsantsan da kai don duk abinda ya faru Naani zata ce laifina ne."

"Me zai faru? Ba dai zancen zamana haka bane kuma ta sani?"

"Banda wannan, kaima ka san me nake nufi."

"Baka yarda da rantsuwar da na maka bane?"

"Ina tsoron sha'aninka ne yarima, don tunaninka daban ne."

Imran yayi gajeriyar hamma sannan ya lumshe kyawawan idonsa.

"Ka san me? Yunwa nake ji, bari in hada mana wani abun sai ka cigaba da gaya min maganganun daka saba, nima ina baka amsa da wadanda na saba...so, me zaka ci?"

Jaamil ya girgiza kansa yana masa kallon Ba inda zaka.

Mintuna goma bayan haka ya gaji da zaman d'akin ya bishi can kan dining d'in dake tsakiyar had'ad'd'en kicin d'insa (island).

"Ga ruwan zafi nan a kettle sannan akwai differents tea-bags a cikin cabinet din can ka zabi wanda kake so."

A wannan lokacin jaamil ya san hanyar kawai da zai iya samun had'in kansa shine ya biye masa, saboda haka ba musu ya nufi jikin durowoyin ya d'auko wanda hannunsa ya fara kaiwa kai sannan ya dawo ya zauna a kujerar dake fuskantarsa.

Ya had'a tean kamar yadda yasha ganin imran na yi sannan ya shiga juyawa, idonsa na kan yadda yake ta cin kwan daya soya da fork yana kuma duba cikin wayarsa.

"Me yasa ka tashi daga wancan gidan?" ya tambaya kai tsaye.

Ba tare daya d'ago ba ya amsa.

"Na fada maka kwanaki nayi mistake wani mak'ocina ya ganni na shiga ta jikin katanga, bana son suspense!"

Jaamil ya gyada kansa.

"Toh me yasa ka dawo nan wajen?"

"Saboda ina son unguwar and yayi kusa da wajen aikina."

"Kuma yayi kusa da gidansu."

Da jin haka imran ya tsaya da taunar da yake da kuma danna wayar. jaamil ya sake maimaitawa.

"Yayi kusa da gidansu yarima kuma ka sani."

"Ka san me? lets get this straight..." ya dire wayar hannunsa da fork din.

"...Ka kai karata wajen Naani, ka fada mata duk abubuwan da nake tunanin sirri ne tsakanina da kai, and yes! na yarda cewa nayi kuskure, nayi kuskure dana bari ta sanni har kuma nayi mata magana, sannan nayi rantsuwa ba zan k'ara zuwa kusa da ita ba, toh me ya kawo wannan zancen yanzu?"

"Saboda ban yarda da rantsuwarka ba."

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

07


(¡î_¡î)

"Wai ya na gansu ne kala-kala?"

Amina ta tambaya tana warwara katunan dake kan bencinsu. Nanne ta tsotse kwallon agwalumar bakinta tace.

"Wai fa bayan events ukun da za'ayi kowacce sun had'a nasu daban zasu yi da yan'uwansu, shine baffa yace shi 'yanuwansa kala d'aya ne kuma dole zasu je na kowa don haka suyi a rana daban-daban."

"Toh ai dates din sun hargitse min, kati wajen bakwai wanne za'a fara?"

"Kinga fa, event din farko shine wankan amare ranar litinin, shi inna ce ta hada da daddare za'ayi, sai kamu washegari talata shima a gida za'ayi, laraba mother's eve na kowa da kowa a wannan event center din, Alhamis shine bikinsu hajiya Babba suma ga inda zasu yi, juma'a na mama rabi itama da wajenta, Asabar kuma nasu mama halime, sai lahadi a d'aura aure kowacce ta kama gabanta."

"Tabdijam! Wannan ai gajiya zaku yi, bikin ba zai taba dadi ba."

"Ko dai su gaji, an gaya miki kowanne zanje, ni kawai bak'in cikina za'a hana ni baccin safe weekend."

"Toh ba kowanne zaki ba ni kika tattaro ki kawo min gabadaya?"

"Ai wai ki zab'a ki darje, wad'ancan guda biyun fa na mama rabi da mama halime duk card admits ne, inda zaki san abin k'aranta ne, ita hajiya babba data isa babu wani sai da kati, kowa shiga zaiyi kuma yaci ya koshi."

"Toh wanne zaki a ciki?"

"Duk wad'anda za'ayi a gida ina nan, sai mother's eve da kuma na hajiya babba."

"Biyun nan ne baza ki ba kenan?"

"Gaskiya dai, kuma fa mama halime harda wani aiko min da anko."

"Ke dai kawai ba kya son matar nan ne amma wallahi tafi mama rabi kirki. Bar ma zancen bikin nan, baki ban labarin ba."

Nanne ta tsotse wani kwallon, tana tand'e baki.

"In gaya miki sai ga sallama wai malam mukhtar ne yazo, inna har tana washe baki da taga zan fita ta zata na fara sauraren irin mayun nan ne masu nacin aike, na fita na gaishe da bawan Allah nan...ya kuwa hau bayani tiryan-tiryan wai wallahi akwai abinda ya same ni da ban sani ba, malam murtala har wace k'asa ce yaje akan sannin sirrin aljanu kuma wai wallahi ya ga aljani a jikina sanda na shake shi."

Amina ta kyalkyale da dariya harda buga benci.

"Na yarda dake wallahi sa'adha, nina san zaki iya shi yasa nace miki kawai ki zare idonki ki mari mutum!"

"...mhmmm ina kaiki ke dai, ya gama bayanansa ya kawo wani k'ullin leda, wai ingattattun magunguna ne da aka kawo daga madina, dana wanka, na sha da madara ko nono, na shafawa a kai, na wace tsiya-wace tsiya, ni dai na karba nayi godiya, ina shigowa gida kuwa na jefa a sharar compound kar ma wani ya ganni dashi."

"Ke amma fa sunyi kokari, magungunan aljanu fa ance da tsada."

Nanne ta galla mata harara. "Toh in gaya miki a satin dana koma na bada kudin makaranta, na tabbata dashi suka siyo tunda sun san ba dawowa zanyi ba."

Amina ta sake kyalkyalewa da wata dariyar.

"wallahi ko hakane sunyi kokari, tunda zasu iya cinyewa."

"Can musu da iyayi, ni yanzu abinda ke gabana daban."

"Allah koh? meye a gaban naki?"

A lokaci d'aya bugun zuciyarta ya k'aru, don duk duniya abinda ke d'an damunta guda d'aya ne, ji take yi kawai tana son sake ganin IMRAN, a kwanakin baya da bata ganinsa bata damu kanta haka ba, amma tun daga wannan 'yar maganar da suka yi shikenan kuma take jin wani abu kamar damuwa a ranta na rashin ganinsa kusan sati biyu.

Gashi ba wanda ta sani da zata tambaya, k'anwarsa ma da take gani tare da safiya yanzu basa haduwa tunda ta bar islamiyyar, ba sau daya ba, ba sau biyu ba tasha leka bakin gate da zummar ko zata ganshi, har ta gaji ta yardarwa kanta cewa da gaske baya nan, ya sake irin tafiyar da yayi kwanaki.

Wai meye had'ina dashi ne ma da zan damu kaina da son ganinsa.

Ta ayyana hakan a wani gefen zuciyarta lokacin da yatsunta suka matse agwalumar har saida wani kwallon ya bullutso.

*****

Ya jingina da kujerar bayansa yana juyawa a hankali, idanunsa a rufe yana sauraren assistant dinsa dake gefe yana karanto report din karshen wata shida na ma'aikatarsu. Kwakwalwarsa na jin komai daki-daki yana saving d'insa, daga yanayinsa kad'ai wani zai zata shine shugaban kamfanin gabadaya. Kamfanin nasu na 'ORZ' dake kula da duk wasu harkokin talla da ake gudanarwa a media platforms da kuma billboards na kan titi.

Ya bude idonsa da sauri sanda yaji wani abu daya dau hankalinsa.

"Kaji koh? Kaji abinda nake fad'a masa exactly last six months?"

Mr. Marvin ya rufe file din.

"Shima ana kai masa result din abinda ya fara cewa kenan, yace abinda imran yake fad'a ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login