Showing 3001 words to 6000 words out of 113985 words

Chapter 2 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28448

ka kuma sai ka soma bin ta da sharri, ina nanne ina wasu kayan surajo?"

"Rabu dashi inna, in ma na d'ebo ai dole nan zan kawo kuma zaki gani."

Sadiq yayi dariya kafin ya juya yana fad'in.

"Ni dai na fada miki, don wallahi kin san halinsa."

Ta sake jan tsaki sannan ta mike ta shiga bandaki don d'auraye hannunta. sai dai wani b'arin na zuciyarta tsoron kar da gaske sadiq yaje ya fadawa suraj cewa ita ta dauki kayansa ne, don ta tabbata ko muryar inna zata dushe wajen fad'a sai ya jibgeta kamar yadda ya saba, shi yasa ko kad'an basa shiri da inna.

Tana fitowa ta nufi can kasan kayan wankinsu inda ta cusa kayan nasa, kala biyu na shaddar gezna, wadda baffa ya bayar akayi musu aiki tun daga maiduguri, ta sake duk'unk'une su a ranta tana fad'in.

Ba dai ni zaka yiwa tsawa a gaban abokanka ba, wallahi haka zanyi ta kwashe duk wani abun da kake so.

Ta fada a zuciyarta.

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

03

(¡î_¡î)

Yana tsaye daga jikin wata tsohuwar container data raba gate din gidajen biyu yana lura da masu aikin feshi da suke yi a k'ofar gidan.

"Wai dama da gaske gidan nan tarewa za'ayi?"

Nanne ta tambayi rahama dake tafiya a gefenta lokacin sun dawo daga islammiyya.

"Tun jiya naji mama na fad'a, wai har sun fara kawo kaya ma...gwara ku sami makota ai gidan ya dad'e ba kowa."

Sun iso daidai bakin gate din kenan zasu wuce, d'aya daga cikin masu aikin feshin ya juyo da bokiti cike da ruwa zai watsar a kasa, cikin rashin sa'a sai abin yazo daidai da sanda suka k'araso wajen, ruwan gabadaya ya sauka a jikinsu, tun daga hijabi har kan takalmansu.

"Malama dan Allah kuyi hakuri, wallahi ban san kuna bayana."

Nanne ta d'ago da mamaki ta kalleshi.

"Kamar yaya muyi hakuri? Ta yaya zaka jika mu da k'azamin ruwan nan sannan kace muyi hakuri?"

"Toh in ban baku hakuri ba me zance?"

"Wallahi ba wani zancen hakuri sai ka biya kud'in kayan nan tunda uniform ne, ko kana tunanin zamu sake saka su ne a haka?"

Ya girgiza kansa rike da bokitin.

"Wannan ma zancen banza ne, ta yaya daga jik'a ku za'ace sai in biya kudin kaya?"

Jin muryar mutumin a sama yasa imran juyowa daga wayar da yake yi, idonsa ya gano masa ita tsaye daga jikakken uniform a kusa da kawarta, ta hade rai tana dallarawa mutumin nan harara sanda yake magana, abin yaso ya bashi dariya ganin yadda take fiffikewa wajen magana kamar zata cakume shi.

"Ka san Allah malam ba wani zance sai ka biya kudin kayan nan...."

"Na rantse da Allah in dai baku hakura sai dai ku san yadda zaku yi."

Wani daga cikin abokan aikinsa ya juyo yace.

"Haba 'yanmata ku baku san tsautsayi bane?"

"Bamu sanshi ba...abinda muka sani kawai a biya mu kudin da zamu sake kaya."

Rahama ta janyo hannunta.

"Dan Allah ki rabu dasu, yanzu in ya baki kudin ma karba zaki yi?"

"Wallahi karba zan, ni da hakkina...?"

Bata kai karshe ba, muryarsa ta katseta mai taushi daga gefe.

"Uhm kaga..." mai aikin ya juya.

"...Ka tambaye su nawa ne kudin kawai."

Ta juya ta kalle shi, jingine da container kofar gidansu, yasha farar shadda da hula mai kyau, ranar data fara ganinsa kenan, ranar da ya fara shiga cikin tunaninta....

"Baffanki ya fara fad'a kan bakya zuwa gaishe da su hajiya, don jiya yake ce min ya bawa halime shadda a dinka muku ke da zainab tace masa ai ita tafi sati biyu ma bata ganki ba, don haka da kin gama shiryawa yanzu kibi dakin kowacce ki gaishe ta."

Inna ta katse tunaninta tana kurb'ar koko, Nanne ta kalleta sannan ta cigaba da shafa man da take bayan ta fito daga wanka.

Ko kad'an bata so haka ba, don duk cikinsu babu dakin wadda take son shiga, tafi son tayi harkarta kowa ma yayi tasa...in sun hadu a tsakar gida ko a baranda ta gaishe su da kai.

"Inna ni wallahi da wani waje zamu da rahma, in d'inkin ne ayi min iri d'aya da zainab kawai, waccar atamfar ma da baffan ya bayar ai ba'a tuntube ni ba suka yi min wata 'yar mitsitsiyar riga."

Zainab itace 'yar autar mama halime, kuma kusan sa'ar nanne don da watanni bakwai kawai ta girme ta.

"Ni ba ruwana da zancen dinki, in sun ga dama ma su dinke mata shaddar duka, nace dake kawai kije ki gaishe su, in sun ganki ai shikenan ba mai sake zuwa ya fadi wani abu akanki."

Ta hade rai kan ta nufi wajen kayanta don daga yanayin muryar innan, ta san da gaske take sai taje.

Dakin mama halimen ta fara shiga bayan ta shirya cikin wata doguwar riga ta jan material, sannan ta yafa dankwalin kawai akanta, hannunta rik'e da bak'ar leda mai cike da kanwa wadda inna tace ta kai can kicin wajen su mama azumi.

Maryam kadai ta tarar a falon, zaune akan kujera tana karyawa da alama bata dade da tashi ba, don kuwa akwai ta da son bacci musamman na safe.

"Maman tana ciki ne?" ta tambaya tsaye daga bakin kujera.

Kamar baza ta amsa ba, don sai da ta gama taune abinda ke bakinta sannan tace.

"eh."

"Gaisheta nazo yi."

Ta d'ago ta kalleta sarere.

"sai ki jirata ta fito."

Tana rufe baki kuwa Nafisa da zainab suka shigo, hannunsu rike da wasu manyan ledoji, kallo d'aya nafisa tayi mata ta shige, zainab d'ince kawai ta mata guntun murmushi kasancewarta mai saukin kai, don ba don rashin yawan maganarta ba da sun d'anyi shiri da nannen.

"Kar dai wai an samo?" cewar maryam da saurinta lokacin data sauko tana ajiye kofin hannuta a k'asan kujera. Nafisa ta mik'a mata ledar da take rike da ita tana fadin.

"Zauna nan, ina tashi daga bacci naga sak'onsa wai an samu kayan ba shiri na azalzali idris (direbansu), in gaya miki sha d'aya muna can, mun ma riga shi isa shagon."

Maryam ta hau zaro wasu tsantsara tsantsaran lesuna masu kalar milk da orange tana fadin.

"Sune kuwa, yanzu guda nawa ne anan?"

"sha tara ne, amma bamu bar shagon ba sai da nasa ya kulle guda talatin da daya a store kinga hamsin din kenan...don kar ma yace mana an siya wasu."

"Wooo...." ta d'an yi ihu sannan ta had'a da zagi.

"Wallahi kowa sai ya san anyi ankon da har a gama bikin gidan nan baza a sake yin irinsa ba."

Nanne ta kalli lace din da akewa ihu, don kyau yayi kyau don ba karya sun san harkar gayu, amma ya za'ace har a gama bikin kowa a gidan baza'ayi mai kyansa ba, ta tabbata ma wanda su hajiya babba zasu fitar sai yafi nasu tsada don ba had'i tsakaninsu.

Idonta ya kai kan kofin da maryam ta ajiye, ta juya taga duk hankalinsu ya tafi wajen kirga kayan, zainab kuma ta dauki wayar maryam din tana dubawa, a hankali ta matsa dab! da kujerar sannan ta damk'o k'ura-k'uran kanwa guda biyu, ta dubi tean da yasha madara kamar me, ta jefa ba tare da sun ankara ba.

"'yan kasuwar ne har suka dawo..." muryar mama halime ta ratso daga cikin d'akin kafin ta dage labulen ta fito, sai dai ganin nanne tsaye daga jikin kujera ya tsaida ta, cikin kissa tayi murmushi tace.

"Yau bak'uwa muka yi ne?"

Nanne ta kalle ta daga inda take tsaye, sanye cikin wata hadaddiyar shadda data sha aikin dutse, abin yaso ya bata mamaki, don ta san ba wani shiri suke da mama rabi ba da har zata yi wannan kwalliyar don karb'ar lefen 'yarta, sai dai fa ko don ta cusawa mutan gidan haushi.

"Ya kika tsaya daga nan, zainab baku ce ta zauna ba, shigo ciki mana."

Kamar gaske. Ta ayyana a ranta kafin tace.

"Nan ma ya isa mama, dama zuwa nayi in gaishe ki, ina kwana."

"Lafiya kalau, ya innan da k'afa jiya na fita tun safe ai bamu gaisa ba."

"k'afarta da sauki, tace a gaidaku kuma."

"Muna amsawa, zauna mana."

"Ba komai mama, tafiya zanyi ma sai anjima."

Har ta juya maman tace.

"A'ah dawo kici abinci mana, maryam kina kallon kanwartaki ba kiyi mata tayi ba?"

Abin ma yaso bawa nanne dariya, wai a cikin gidansu ake mata tayin abinci kamar taje wani bak'on waje, abincin da a yanzu in ta tuburewa inna bashi take so ba, dole ta fad'awa mama azumi a canja in yaso wanda ba zai ci ba, ya nemi wani abin.

Ta girgiza kanta.

"A'ah mama taci abinta wallahi, a k'oshe nake."

Tana fadin haka ta juya ta bar dakin, sai dai kafin ta gama zura takalmanta taji sanda maryam ta furzar da wani abu sannan cikin muryar fushi tace.

"Meye wannan?"

Da murmushinta ta nufi falon aunty amarya, inda ta tarar gabad'aya yaranta na nan banda 'yan biyu da suka tafi wajen fitar da auduga, safiya da surrayya sun baje suna kallon wani film d'in larabawa, ta tab'e baki ganin yadda hankalinsu ya tafi gabadaya akai, ita abinda baya gabanta kenan kallo, don tvnsu ta dakin inna sai tayi kusan sati biyu bata kunna ba, tunda itama inna ba kallon take ba, sadiq dake can kan dining ya d'ago daga cin abincin da yake yi bayan su safiya sun amsa sallamarta.

"Kayan kika kawo a ledar? don wallahi na tabbata suna hanya yanzu."

"Sadiq na gaya maka ka fita harkata, don wallahi daga kai har kayan gabadaya sai in had'a in zage ku."

Ya kyalkyale da dariya harda buga table din gabansa.

"Na zata ai zaki ce harda mai kayan, tunda baki ji waccan shawarar dana baki ba bari in sake miki wata, kije ki canja kaya kisa masu nauyi-nauyi da zasu kare miki duka ba wannan fale-falen ba, don jawur zaki koma yanzun nan."

Taja tsaki kafin ta juya wajen surayya 'yar autarsu da bata fi shekara tara ba tace.

"Ina Aunty?"

"wanka take yi."

Kamar ta jira ta fito kuma ta tuna sadiq yace yanzun nan su suraj zasu dawo, kuma ba lallai ma ta samu wata tarbar arziki daga wajen Auntyn ba don haka tace.

"In ta fito kice nazo gaishe ta."

Har ta juya safiya mai bin sadiq ta tsaida ita.

"Yaya Aisha tace zata samu a gad'ar da cousins dinta zasu yi ranar kamu, in kina so ki fada mata kema ta saki."

Kamar tace mata eh kuma ta tuna rawa ce, daya daga cikin abubuwan da bata iya ba, saboda haka tace.

"Gaskiya bana jin inna zata barni."

Safiya ta gyada kanta sannan ta maida hankalinta kan tv. Dad'in nanne dasu kenan ita da surrayya basa taba mata rashin kunya ko wani abu, duk ko da cewar mahaifiyarsu bata sonta. Shi yasa itama take jin dadinsu musammam ganin sune kadai wad'anda ta girma a gidan.

Tana isa falon hajiya Babba ta tarar kanwarta mai suna Aunty hadiza da wata mata da bata sani ba sunzo ana lissafin adadin labulayen da za'a siya na gidan Aisha kasancewar sunje sun gano gidan.

Ta gaishe su suka amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ta tambayi inda Aishan take, hajiya babba ta shaida mata tana dakinta, tayi zaton zata kirata ne don haka ta cigaba da zama a wajen, sai dai ga mamakinta kai tsaye hajiyan tace ta tashi ta shiga dakin.

Tun daga kofa take k'arewa dukiyar da aka narka a dakin kallo, tana iya tunawa shigarta ta karshe komai na dakin lemon green ne amma yanzu an canja zuwa milk and ash, gaskiyane da inna ke cewa ita kanta hajiya babba mai kudin kanta ce, su mama rabi kawai haukansu suke a gefe.

"A'ah daga nan, karaso mana."

Aisha dake kwance a gado tana waya tace da nanne.

"...zaka d'an ara min miti biyu?" ta tambaya cikin wayar, wanda suke wayar da ba tantama nanne ta fahimci wanda zata aura ne ya fadi abinda ya sata murmushi kafin ta katse kiran ta mike zaune.

"kina lafiya? Kwana da yawa?"

"Lafiya kalau." Nanne ta amsa da murmushi, a ranta tace 'ya'yan hajiya babba kenan, ko basa sonka baza su taba nunawa ba shi yasa a duk sanda ta gansu gaisuwar mutunci ke hada ta dasu, duk ko da kafin ta gansu din aiki ne, don ko ita Aisha da take mace sai tafi sati bata ganta ba don kusan kullum a makaranta take yini, balle kuma mazan dake aiki, kuma yawanci ma sunfi shiga dangin mamansu.

Daga nan bata ko kalli hanyar d'akin mama rabi ba wanda ke cike da mutane tayi kasa ta nufi kicin. Anan ta tarar gabadaya ma'aikatan gidan harda wanda ba b'angaren girki suke ba anata hada hadar abinci kala-kala da kuma snacks fal duk cikin umarnin mama rabi.

Ta wuce can karshe inda mama azumi dasu lami ke packaging wasu snacks d'in a foil paper.

"Farar mace alkyabbar mata, balle kuma in tasa jan kaya, haba wa!."

"Kai mama azumi, kema ai jan kayan ne a jikinki."

"Yo ke kya had'a fatar budurwa data tsohowa irina."

Tayi murmushi sannan ta mik'a mata ledar.

"Gashi inji inna."

"Me muka samu....kinga kanwa mai kyau wallahi, a ina ta same ta haka?"

"Wa ya sani...." ta fada tana d'anewa kan durowar data zagaye k'aton kicin d'in, bata ko kalli su lami ba dake ta faman d'auke kai suna maganganu don su nuna kamar basu ganta ba.

"...Naji kamar tana kawo mata akayi. Mama azumi a d'an zubo min kad'an yunwa nake ji."

"Kai uwata, na san fa tare kuka ci tuwon nan da inna, ina yunwa ta isa ta kamaki?"

"Toh dan Allah a d'an bani ladan k'anshin da naji."

"Haka dai zaki ce, kuma wannan ai ko baki fad'a ba."

Ta yago foil paper dake hannunta ta shiga zubo mata su samosa da meatpie wadanda ke cike taf! da nama bisa umarnin mama rabi. Tana ci suna hirarsu da tare, don dad'i sai shilla k'afafunta take yi tana zuba santi wanda kesa mama azumin dad'a tsokanarta.

"Toh ga fa 'yan gona nan sun dawo."

Mama azumi ta fada tana duban windon dake bayanta, nanne na juyawa ta ci karo da samarin gidansu kaf! Su tara, har kuwa da yaya Ahmad da yaya ibrahim masu aure, sun sako baffa a tsakiya kowanne cikin shadda mai kyalli da hula kalar kayansa, baffan sai murmushi yake yana yiwa ya Ahmad magana, idonta ya kai kan 'yan biyu da suka yi ankon shudiyar shadda daga gefen yaya umar, kamar kodayaushe suraj ya had'e girar sama data k'asa kamar me shirin lailayo zagi, ta inda ake gane su da salim kenan don shi ba laifi yana da d'an sakin fuska.

Cikinta ya bada k'ara lokacin da tayi saurin juyowa don kar su ganta, mama Azumi kuwa sai fadi take.

"Masha Allah, masha Allah...Allah ya bawa kowannen ku zuri'a irin haka kuma."

Ta had'iye abinda ke bakinta kafin tace.

"Haba dai in kowannensu ya sami 'ya'ya irin haka, ai ina jin sai mu shiga tarihi a matsayin zuri'ar da suka fi kowacce yawan haihuwa."

"Yo ai ba abin gudu bane uwata, 'ya'ya fa suna d'aya daga cikin rahamomin duniya."

Daga nan ta juya tana bawa su lami odar a shiryawa 'yan mazan abinci don ta san yanzu kowannensu zai fice ganin mata sun fara cika gidan.

Nanne ta dad'e a kicin d'in tana ta ganin hada-hadarsu kafin Rahma tazo ta tarad da ita.

Rahma ita kadai ce k'awar da take da ita bayan kawarta ta makarantar boko Amina, jikar d'aya daga cikin tsofaffin ma'aikata gidan ce wadda ake kira da hajiya, a yanzun haka ita hajiyan ta rasu sai babar rahman ce ta maye gurbinta kasancewarsu masu k'aramin hali, wanda a yanzu shekara biyar kenan tun rahman na 'yar karama take zuwa da ita har ta fara wayon da take d'an kama mata wasu abubuwan, dalilin da yasa ma kenan ya zama kullum tare suke zuwa, don gidansu ba nisa daga nan.

K'awancen nasu ya fara ne tun suna k'anana lokacin da kowannensu bai san ciwon kansa ba, in sunzo za'a had'u dasu zainab da nannen ayi ta wasa wani lokacin ma har da sadiq da yazama sune sa'anninsa. Sai dai tsakanin nannen da rahma ne kawai abotar ta d'ore saboda ita rahman tana da tsananin hakuri, tana jure duk wani rashin mutunci da abubuwan da nannen ke saka ta har zuwa yanzu da don kanta take ragwanta mata ganin irin hak'urin da take yi da ita.

"Wai tun d'azu dama kinzo ina nan inata jiranki?"

"Kiyi hakuri yau aikin gidan ne da yawa, kin ganni ko hijabi ban cire ba wallahi tun zuwanmu."

"Toh ya zancen zuwan? Zamu je fa."

"Ki bari dai zuwa d'an anjima in anci karfin aikin, yanzu in na tafi mama zata iya yin magana."

"Saboda ke sai a kasa yin wani abin, kin san fa anjima 'yan kawo lefe ne zasu zo, gidan k'ara cika zaiyi."

"Toh bari in gaya mata inji."

"Ki dai wanke hannunki bari inje in d'auko mayafina."

Ta mik'a mata ragowar meatpie da samosan hannunta kafin ta diro k'asa.

"Nagode." Ta k'arb'a da murmushi.

Nanne na d'age labulan kofar d'akinsu tayi turus! Ganin 'yan mazan gabadaya sun baje a cikin falon, inna na daga tsakiyarsu tana ta washe baki, kowannensu kuwa ya d'ago ya kalli kofar d'akin harda yaya sulaiman dake maitar danna waya.

Ta had'iye yawu lokacin da yaya Ahmad ke fad'in.

"Ke dama kina nan?"

Duk da da gabanta dake fad'uwa a ranta saida tace.

"Ina zani nida gidan ubana."

Tayi kamar ta juya ta koma amma muryar hadiza ta katse ta daga baya.

"Zamu wuce."

Ta juya ta gansu kusan su biyar d'auke da manyan-manyan tire shak'e da kayan abinci.

Ba musu tayi cikin d'akin, sannan ta dan durkusa ta gaishe su lokacin da ake ta faman dire musu abincin.

"ke zo nan!"

Tar! muryar suraj ta kirata a cikin hayaniyar da aka fara ta zuba abincin, ba damar tace bata ji ba don saboda wani tsautsayi yana magana ta kalle shi.

"An shanya min kaya a baranda jiya kuma daga nan ba'a gansu ba."

Ya fada kamar mai bata labari bayan ta isa gabansa, zuciyarta cike da tsoro ta daure tace.

"Toh ni meye had'ina da kayanka?"

A cikin hayaniyar nan suka tsinci muryar innan na fad'in.

"Surajo me tayi maka ne?"

Bai ko bi ta kanta ba yace.

"Kije ki d'ebo min su yanzu kafin in mik'e in fasa kanki." ya fad'i kalmar fasawar kamar zata fashe da bakinsa.

"Ban gane ba, kana nufin ni na d'auka? Toh ni ba barauniya bace, kuma ko zanyi sata ma sai in k'are a kayanka..."

Kafin ta rufe bakinta kuwa taji saukar wani azababben mari a fuskarta wanda ya taho tare da salatin inna.

"Kai meye haka?"

Yaya Nasir da yaya umar suka had'a baki wajen fad'a, nanne ta rusa wani irin kuka da rabinsa na k'arya ne.

"Me tayi maka?" ya muhammad ya tambaya, kafin ya amsa kuwa inna ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login