Showing 39001 words to 42000 words out of 113985 words
take goge tv da tsumma a hannunta.
"Me yasa? wallahi ina son wak'ar duk da dadewarta."
Bata ce komai ba sai ta d'auki bokitin ruwan omon dake kusa da k'afarta ta matsa jikin window ta fara goge shi.
"Anya fa su inna yau zasu dawo, nifa banji kowa yace suna hanya ba?"
Rahma ta fad'a daga gefe inda take jera tarkacen inna cikin wata cupbaord. kwanan inna biyu kenan a niger, tun shekaranjiya suka tafi ita da baffa kuma a yau ake sa ran dawowarsu. A kwana biyun kuma Rahma tana tare da ita, tare suke kwana a dakin kuma tana iya kokarinta wajen ganin ta saki jiki suna harkokinsu tare kamar da amma bata iyawa, ko ta fara sai tunani da yawa yazo ya danne sukuninta.
Musamman a yanzu da tunanin dalilin tafiyar Inna da Baffa yafi damunta, wani abu ne da bai tab'a faruwa ba, in dai za'a je niger toh kusan rabin gidan ake tafiya a tare. amma yanzu daga su sai direban Baffa kawai suka tafi. kuma bata san me yasa ba, tana danganta tafiyarsu ne da lamarinta.
"Dazu kina wanka, Mama halime ta shigo tace sun taho."
Ta amsa mata a hankali.
"Toh Allah ya kawo su lafiya, in munyi sallah zamu je gidan Sumayyan?"
"Eh zamu je, na gayawa Mama Azumi ma zamu fita."
"Yawwa kinga sai mu tsaya in kai...."
No one else can do the things that
You do for me...
I wanna be there for you
Baby i really love you.
There is something about you that i cannot explain...
Wak'ar ta sake shigowa cikin kanta ta ture k'arshen maganar Rahman, sai kawai ta ajiye tsumman hannunta da sauri sannan ta nufi kan kujera ta lalubo wayar ta kashe.
"Na gaya miki bana son wak'ar nan."
Rahma ta juyo ta kalle ta, da gaske ne abubuwa da yawa sun canja game da Nanne, abubuwa da yawa da bata sansu ba bata kuma tab'a tunanin zasu faru kanta ba.
Bata k'ara cewa komai ba har suka gama aikin. ta zubo musu abinci suka ci sannan ta tattare kwanukan da niyyar sauka dasu k'asa. Sai dai bata kai bakin k'ofa ba wayar inna da bata tafi da ita ba ta shiga ringing a kusa da Nanne wadda ta baje magungunanta tana k'ok'arin sha.
Nanne ta kalli wayar a gefenta, bata san number ba, don haka ta barta ta gama rurinta sannan ta tsinke. bada dad'ewa ba aka sake kira, sai tayi tunanin ko inna ce tace a kira ta, tunda basu yi waya ba kuma ance sun taso.
"Assalamu Alaikum."
Imran ya rufe idonsa a hankali jin yadda muryarta mai sanyi ta ratsa jikinsa.
"Wa'alaikum salam." Shima ya amsa ba tare da ya bud'e idonsa ba.
A lokaci d'aya bugun zuciyarta ya tsaya, me yasa a kullum taji muryarsa take jin kamar wata murya ce data sani tun farkon rayuwarta, sab'anin sanin data yi masa na 'yan watannin baya ne kawai?
Mamaki ya kamata, ta cire wayar daga kunnenta ta kalli numbar, da gaske imran ne ya kirata? imran d'in data sani? bayan tarin kwanakin da suka wuce ba alamarsa?
Ta maida wayar a hankali kunnenta.
"Zan iya ganinki gobe?"
Muryarsa ta sake ratsa cikin kanta, ta juya ta kalli kofa inda Rahma take tsaye, babu kowa a wajen.
"Me za'a yi?"
Tana iya jiyo sautin murmushinsa daga daya b'angaren kafin yace.
"Hak'uri zan baki na tarin laifukan dana yi."
Nanne taji kanta ya fashe a lokaci d'aya. ita zai bawa hakuri.
"Laifin me kayi?"
"Suna da yawa, kuma in kika bani dama duk zan zayyano su duka da reasons d'ina."
Sai ta gyara zamanta, yatsunta na kanannad'e ledar dake gabanta.
"May be da yamma?"
Wannan karon sautin murmushinsa ya k'aru.
"Baki tabbatar ba?"
Ta lumshe idanunta sannan tace.
"Na tabbatar, Allah ya kaimu."
"Ameeen..."
Yaja Ameen d'in da d'an tsawo, sannan yace.
"...Nagode sosai."
Maimakon ta amsa sai kawai tace.
"Sai anjima."
Har ta cire wayar daga kunnenta, muryarsa ta katse ta.
"Sa'adha..."
Me yasa ne wai ya iya fad'ar sunanta fiye da kowa? bata ce komai ba amma sautin numfashinta ya tabbatar masa tana jinsa.
"Thank you!"
Dib! wayar ta katse.
Ta cire wayar ta kalli screen d'in, da sauri kuma ta shiga call log don ta sake tabbatar ba tunani take ba.
Sannan ta d'ago da ta kalli agogo.
K'arfe uku da rabi.
¡ñ©n¡ñ
Please ignore the songs in the chapter, i'm just kind of musical at that time.
But if you are intrested, the first one was.
I wanna grow old with you by westlife.
And the second.
Kedike by Chidinma.
******
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
27
(¡î_¡î)
Wajen cikin daji ne, dajin da bata tab'a zuwa cikinsa ba, amma somehow sai take jin kamar ta san wajen, kamar ruhinta ya tab'a zuwa...kamar wani waje ne da yake rik'e da wani tarihi na rayuwarta.
Inda k'afafunta suke tsaye fili ne kuma daga gabanta akwai tarin bishiyu, tarin bishiyun da take ganin kamar abinda tazo nema yana cikinsu ne.
Sai dai tana motsa k'afafunta, taji muryoyi da yawa na kiranta daga baya, muryoyin da ta kasa tantance su, kuma da yawa sunanta suke kira. ba tare da ikonta ba taji k'afafunta sun cigaba da tafiya wajen bishiyun nan, kamar tana zaune akan wani abu ne ana tura ta gaba.
"Nanne..!"
muryar inna ta fito daga cikin muryoyin nan, daga nan kuma sai ta fara tsintar sauran, akwai ta Rahma, Baffa, Sadiq, Amina, Mama halime, Mama Azumi, ya sulaiman da kusan rabin 'yan gidansu. kowannensu yana kiran sunanta da alamun gargad'i
Taji tana son juyawa taga kiran me suke mata, don a yadda take jin muryoyin kamar bata yi nisa dasu ba, sai dai kafin ta iya juyawa ta hango shi.
Imran ya fito daga cikin bishiyun nan yana kallonta da lumsassun idanunsa, kamar koyaushe yayi wani irin kyau sanye da light kaya, fuskarsa ta haska, sannan kyakkyawan murmushinsa ya kwanta sosai a gefen fuskarsa, sai da ta shagala da kallonsa sannan ya d'ago yatsansa guda d'aya yayi mata alamun ta biyo shi sannan ya juya ya koma cikin bishiyun. k'arar muyoyin suka k'aru a cikin kanta.
Amma sai taji duk basu dame ta ba, bata damu taje wajensu ba, bata damu ta san kiran me suke mata ba. Tafi son ta k'arasa wajen Imran, ta tambayeshi tarin abubuwa da yawa da suka shige mata duhu, abubuwan da take son sani game dashi.
Taku daya kawai ya shigar da ita cikin duhun bishiyun, amma sai wajen ya zama sab'anin tunaninta, a maimakon duhu wajen mai haske ne da kuma kyau, korayen ciyayi da fulawowi sun baje a koina, ga wani dutse daga can gefe yana zub da ruwa.
Taji wani ya rungumeta ta baya, hannayensa sun zagaye k'ugunta sannan ya d'ora hab'arsa a daidai lungun wuyanta, ko bata juya ba ta san Imran ne kuma zuciyarta ta riga ta nutsu dashi, saboda haka ta cigaba da tsaiwa ba tare da ta juya ba tana jin d'umin jikinsa akan fatarta da kuma yadda numfashinsa ke busawa a k'asan kunnenta.
A lokacin ne abin ya faru, taji an caka mata wani abu mai tsini a wuyanta, abin ya huda tun daga farkon wuyanta ya fito ta d'aya gefen.
Numfashinta ya tsaya cak, sannan jini ya shiga gangarowa kan fatarta, tayi k'asa ta fad'i da baya sannan zafi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta, taji ruhinta na barin jikinta a hankali sannan idonta na shirin rufewa.
Amma kafin komai ya d'auke mata, fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sannan hannayensa na d'igar da jini!
Nanne ta farka da wata irin ajiyar zuciya mai k'arfi idanunta a zare, wayar inna dake gefenta ta fad'i k'asa ta gangara wajen dressing mirror.
Ta juya kowanne b'angare ta kalli wajen da take, cikin d'akinsu ne ba wani waje ba, Rahma na kwance a kusa da ita tana baccinta hankali kwance, ta kalli agogon dake saman dressing mirror.
K'arfe uku da rabi na dare.
Ta koma da baya ta kwanta akan filon, sannan ta shiga tofa adu'o'i a jikinta, amma har kusan mintuna ashirin baccin yaki dawowa, Sannan hankalinta ya kasa kwanciya, tunanin mafarkin ya cika kanta, saboda haka ta mik'e ta shiga toilet ta d'auro alwala da niyyar sallah.
Tana fitowa idonta ya kai kan wayar inna dake k'asan mudubi, ta sunkuya a hankali ta d'auka, hannunta ya shiga call log ta lalubo number da Imran ya kirata jiya, tana nan rad'au a rubuce ba'a tunaninta ne komai ya faru ba, idonta ya kai kan time d'in da kiran ya shigo.
K'arfe uku da rabi na rana.
A lokacin fuskarsa ta cikin mafarkin nan ta sake haskawa a idonta, da sauri ta ajiye wayar gabanta na fad'uwa, me mafarkin ke nufi? wannan kiran dasu inna ke mata, wannan murmushin imran din sannan yadda ya rungumeta, yadda take jin numfashinsa a wuyanta kamar gaske da kuma sanda ta fad'i k'asa, ta hango hannayensa da jini?
Jini? jinin waye? ita dai ta san taji zafi a wuyanta amma bata ga fitowar jini ba.
Ta rufe idonta a hankali sannan ta bude su akan mudubin dake gabanta, idanunta sunyi zuru-zuru kamar tayi kuka.
Ta k'iftasu a hankali tana k'arewa yanayinta kallo, a sannan ne abin ya faru, a sannan ne gabanta ya fad'i sannan dukkan tsoro ya shigeta.
Ganinta ya koma dishi-dishi, sannan wani hayak'i ya fito daga rabin fuskarta ya tarwatse a iska!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
28
(¡î_¡î)
"Wai Rahman ta tafi ne?"
Inna ta tambaya tana kallon Nanne dake kokarin sa hijabinta, a lokacin karfe bakwai da kwata na safe.
"Ta tafi tun d'azu kina sallah, zata je makaranta ai."
Ta fad'a a hankali, saboda kanta dake tsabar ciwo. Tun bayan lokacin data farka daga mafarkin nan da kuma abinda ta gani a cikin mudubi.
Bata san iya adadin sallar da tayi a lokacin kafin gari ya waye ba sannan ta iya samun nutsuwa.
"Amma kuwa Rahma bata kyauta ba, ga tsarabarsu tun jiya na ware tana kallo shine zata tafi bata fad'a ba."
"Inna zata dawo ai, ga kayanta ma fa bata d'auka ba."
Nanne na rufe bakinta ta jiyo horn d'in idris daga compound saboda haka ta d'auki jakarta tayi waje tana fad'in na tafi.
"Yau kar ki tsaya wannan lesson d'in naku, ana tashi ki biyo su safiyya ki taho."
Daga k'afar bene ta amsa da toh ba tare da tayi la'akari sosai da abinda innan tace ba.
A makaranta gabad'aya bata da walwala, duk da cewa kusan kwana biyu haka take amma yau ko hirar da take dagewa suyi da Amina ta kasa, tunaninta ya rabu kashi kashi, ga azabar da ciwonta yake sannan ga tsoron mafarkin da tayi a jiya da kuma fuskar da ta gani a mudubi, don ta tabbata taga wani abu kamar hayaki ya fito daga fuskarta, ta shafa wajen a hankali tana so ta cusawa zuciyarta cewa ba da gaske bane.
Sannan ga Babban abun dake gabanta a yau, zuwan Imran wajenta, mafarkin da tayi ko kad'an bai girgiza zuciyarta akansa ba, ji tayi ma ta k'agu sosai yazo ya warware mata tarin k'ullin dake cikin kanta game dashi. Amma kuma bata san ya zasu had'u ba don ko Rahma bata gayawa zancen kiran da yayi mata ba, amma ta san in har zai zo d'in zai gaya mata lokaci.
Ta kwanta akan bencinsu sanda ajin nasu ya rud'e da surutu sakamakon rashin shigowar malami a last period d'in da suke da ita, wasu sun had'a group-group suna ta hira wasu kuma na daga can gaban ajin suna kid'a da benci suna rawa, a cikin masu rawar harda Amina, saboda haka ita kad'ai ce a row d'insu dake can k'arshe, kowa ya tafi harkarsa.
Ta rufe idonta a hankali tana sauraren wak'ar sa'adu bori da masu rawar suka had'a baki suna yi.
Haba yarinyar nan...dan Allah juya, idan baki juya ba...kinci amanata, mai abin dad'i kawo eh mara abin dadi ko....
Sai da aka kad'a k'ararrawar tashi sannan ta tuna da abinda inna tace mata, saboda haka ta yiwa Amina sallama ta fito tare da wad'anda basa yin lesson d'in. Zuciyarta cike da tunanin me za'ayi a gidan da inna tace ta dawo da wuri, amma har suka koma bata hango wani abu da ake shirin yi ba tun dawowarsu innan a jiya da rana.
Sanda ta shiga d'akinsu, Mama Azumi na zaune suna magana da inna wanda shigowarta yasa dukkaninsu sukayi shiru sannan Mama Azumin ta mik'e tana fad'in wa inna sai anjima zata shigo.
Bata nuna komai ba ta gaishe su sannan tayi d'aki, ta fad'a toilet tayi wanka da ruwan zafi sosai don ta samu k'arfin jikinta, har a kanta ta dinga kwarawa ruwan da fatan zai wanke tunanin wannan mafarkin da tayi.
Ranar Alhamis ne saboda haka ta zura doguwar rigar wani light material ta fito falo.
"Nanne k'araso nan magana zamu yi."
Inna ta fad'a ganin tana shirin zuba abinci, ba musu ta rufe flask d'in sannan ta dawo ta zauna a kusa da ita.
"Ina so ki nutsu sosai ki saurareni da kyau, abinda zan fad'a ba neman ra'ayinki nake ba ko son jin shawarki, abu ne da manyanki sun riga sun gama yanke komai kuma in ba wani ikon Allah ba, ba abinda zai sa a canja shi."
Nanne ta tsura mata ido kawai tana jiran kalamanta na gaba, don ta tabbatar ita a yanzu babu wani abu da zai sake girgiza zuciyarta.
"Tafiyar da muka yi nida baffanki akan maganar ki ne.
Ni ban san yaushe kuka shirya da yaron nan ba don baki gaya min ba amma bayan baffanki ya tara mu akan zancen rashin lafiyarki yaje wajensa da sati biyu, ya nemi izinin zuwa wajenki amma baffan yace masa ya dakata tukunna. sai da yayi bincike akansa ya tabbatar da halayensa sannan yace dashi ya turo iyayensa.
Toh wani abu na ikon Allah kuma bayan sun zo, sai suka nuna cewa shi yaron ya shirya kuma da wuri suke son ayi auren duk da haka baffa bai tsaida wata magana ba sai bayan sati guda da suka dawo, anan aka tsayar da lokacin aurenki nan da wata guda kamar yadda shi baffan yace ko kafin nan ko kun k'are jarabawar wane ne term oho...
Yana gaya min zancen nan na d'aga hannu na godewa Allah, don dama ni inda nake tunanin yin magana sai in har ya had'a ki ne da wanda bamu sanshi ba, toh shine zance a d'an dakata mu dake mu fahimci halinsa tukunna. Amma tunda har Allah yasa an sanshi kuma shima baffan ya yaba da hankalinsa shikenan nayi shiru da bakina.
Don haka zuwan da muka yi niger, mun tattauna ne da duk 'yan uwan mahaifinki kuma Alhmdlilahi kowa yaji dad'in zancen wallahi.
Abinda yasa nace ki dawo da wuri kenan yau, don yace zai zo ku gana kuma na san kema ya gaya miki."
Nanne taji ta zama kamar gunki ne zaune a wajen, abu na farko daya d'aure mata kai shine, tana cikin gidan nan har ake jelan zuwa neman aurenta bata sani ba? don ita baffa kawai ya gaya mata cewa yana bincike akan wanda ta turo wajensa ne amma ko Addano bata kira ta tace mata har iyayensa sunzo ba.
Sannan ita ta zaci baffa ko inna zasu nuna rashin amincewarsa akan cewa Nuran daga dangin mahaifiyarta yake sai gashi har komai ya tafi daidai an tsaida ranar aure wata d'aya? wata d'aya kawai?
Sannan zai zo wajenta yau? ita bata shirya ba, tana bukatar lokaci amma ba yadda ta iya, tunda inna ta fad'a mata tun farko cewa bata da zab'i abinda zata fad'a mata umarni ne kawai, muryarta na rawa tace.
"Amma inna ba wanda ya fad'a min duk wannan abubuwan da suke faruwa ko ita kanta Addano bata kira ni ba."
"Nuratu kuma? yo ina ruwanta da wannan sha'anin? koko bamu da ikon mu yanke abu akanki sai da izininta? tunda ita kad'aice me iko dake? toh bari kiji kalma d'aya akan lamarin nan bata sanshi ba kuma habu abinda zai canja, ban k'i ba dai yanzu da aka yanke lokacin a gaya mata."
Cike da mamaki Nanne ta kalleta tace.
"Inna na san dole zata sani ai tunda wanda kuke zancen akansa d'an uwanta ne."
"Ban gane ba, Imranan ne d'an uwanta? toh ni a yadda baffa yace min game da asalinsa banji wata dangantaka data had'a shi da adamawa ba."
Wani irin bugawa zuciyarta tayi, gabanta ya fad'i, sannan kwakwalwarta ta yanke daga fahimtar komai, me inna ke cewa? wane Imran d'in take nufi? wane Imran d'in ne yazo neman aurenta? watak'ila dai mafarki take irin na jiya, kuma zata iya farkawa a kowanne lokaci, saboda haka ta tsura mata ido kawai ta cigaba da kallonta kamar wadda kammaninta suka canja gabadaya.
******
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
29
(¡î_¡î)
Sai dai kafin k'arfe biyar na yammacin ranar, inna ta tabbatar mata da cewa da gaske imran ne yaje wajen Baffa neman aurenta kuma har an amincewa iyayensa an bashi ita.
Ta zauna tayi mata bayani sosai akan cewa ba ita ta tura shi wajen baffa ba, ita irin wannan maganar ma bata tab'a had'a su ba amma inna ta kasa fahimtarta, zance d'aya kawai take maimaitawa cewar ai daman abinda ya dace kenan a shari'ar musulunci, a fara tuntub'ar iyayen yarinya kafin ayi mata magana, kuma gwara shi akan baffa ya bada ita ga d'aya daga cikin 'ya'yan abokansa da bata san ya suke ba, tunda dai ko babu imran aurenta ba zai d'auki lokaci ba.
Ta san cewa a zuciyarta tana son imran, amma yanzu da kawai maganar aure ta shigo tsakaninsu, bata san yaya zuciyarta zata dauki abun ba. bata san me ya kamata taji game dashi ba, tunda shi bai taba fad'a mata yana sonta ba, kuma a tsawon lokacin daya kai kansa wajen baffa bai nemeta ba, yayi amfani yawunta ya gabatar da kansa, sai a jiya daya san zai zo yau sannan ya kirata a waya, ita kuma ta kasa daure zuciyarta ta ja ajinta, kawai ta amince da zuwan nasa.
A sannan ne kuma ta san abinda inna da mama Azumi ke tattaunawa sanda ta dawo daga makaranta, kayan tarba sosai aka had'a masa na snacks da lemo har kala biyu, don ta hango su a hannun lami sanda ta shigo d'akin karb'ar muk'ullin falon waje da aka sa su halliru suka share.
"Nace miki ki maida wannan rigar ko? ina hankalinki yake tafiya ne wani lokacin?"
Inna ta katse tunaninta, ta juya ta kalli rigar da ta d'auko, ash doguwar riga ce mai kama da abaya sannan mayafinta yana had'e da d'an k'aramin hijabi a jikinsa. ita bata ga abinta tayi ba da inna zata ce ta mayar, kuma ma ai ita ta siyo mata a makka, in har bata da