Showing 72001 words to 75000 words out of 113985 words

Chapter 25 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28472

a da nake musu hangen nesa. Ta maida ni tamkar d'anta ta lak'aba min sunan YARIMA.

Nima a lokacin na d'auki dukkan soyayyata na dank'a mata, na yarda cewa bani da wani farin ciki a duniyar nan daya wuce nata, saboda haka duk wani abu daya zama na taimako gareta bana tab'a kasawa wajen aikata shi.

Jaamil d'a ne a wajen 'yaruwarta kuma suna zaune su duka biyun a wajenta, tare dashi na taso a masarautar Naani, ya zama tamkar d'an uwa na kuma abokin da nake dashi duk duniyar nan.

A cikin haka ne ta kirani da buqatarta na son samun wani dutse da take wanda za'ayi amfani dashi don samun k'arin kariya a nahiyarmu, ta shaida min a lokacin cewa dutsen yana hannun bil'adama ne a cikin wani kamfani da suka nannad'e shi a matsayin Award d'insu banda haka su basu san wani amfaninsa ba.

Naani zata iya bani damar da zan shigo cikin mutane a dare d'aya in d'auko mata shi in koma, sai dai in muka yi hakan ba zai taba yi mana amfanin da muke so ba, dutsen yana aiki ne kawai ga duk wanda ya same shi ta tsaftatacciyar hanya, wato ko dai mai shi ya d'auka ya baka da yardarsa, ko ka same shi ta hanyar guminka ko kuma duk wata hanya da zata kawo shi hannunka da take mai tsafta.

Saboda haka ta kira ni a lokacin ta gaya min cewa zata tura ni cikin mutane, inje wannan kamfanin a matsayin ma'aikaci, inyi aikin da zaisa har su yarda dani, wannan dutsen a matsayin Award ya shigo hannuna.

Sa'adha tunda nake a da, ban tab'a bada hankalina akan sha'anin bil'adama ba, a kullum ina musu kallon wasu halittu dake can nesa damu wanda bamu da alaqa ko kad'an tare, a iya inda nake samun labarinsu shine in na shiga cikin Aljanu wanda su suka sansu sosai.

Saboda haka a sanda ta fad'a min hakan, ban kawo komai a raina ba, naji a jikina ne cewa zanje inyi mata aiki kamar sauran dukkan ayyukan da take sani.

A cikin abinda baifi wata biyu ba, Naani ta samar mana da jiki mai irin siffar mutanen da zamu shiga cikinsu nida jaamil tunda na gaya miki bama iya possesing siffar mutane, jaamil zai zama mai taimakamin a komai saboda haka Naani ta bashi damar da zai iya komawa ainihin halittarsa a kowanne lokaci kuma ya iya komawa Muzaffar, ni kuma bani da ikon yin hakan saboda kar hankalina ya rabu gida biyu.

Naani ta had'a ni da wani aljanin daya karanci halayen mutane ya koya min abubuwa da yawa na mu'amalarsu da kuma yadda suke rayuwa. A lokacin na dinga jin kamar ba zan iya komai ba, don ganin rayuwarku nayi kamar irin tamu ta kurkuku, lokacin da za'a kulle ka a hana ka duk wani freedom na pissibilities d'inka.

Amma tun daga ranar dana sauko cikin mutane Sa'adha, tun daga wannan ranar rayuwata ta canja, ta canja in a way da ban san ta yaya zan miki bayani ba, naji ne kawai kamar a dawo min da rayuwar dana rasa a baya, rayuwar da zanga iyayena da dukkan 'yan uwana.

Naje kamfanin ni da jaamil nayi dukkan wasu cike-cike irin na mutane da Naani ta shaida min cewa an gama samo min aikin da komai kawai abinda zanyi kenan, daga nan muka tafi neman gida.

Aka kaimu wani gida da ake masa gyara har na biya deposit, wannan gidan da yake layinku, inda na fara ganinki kin dawo daga islamiyya..."

Ya d'anyi shiru kafin a hankali yace.

"Kin tuna....?"

Bata ce komai ba sai kallonsa da take kawai tana k'ifta ido, ya sa hannayensa biyu harda wanda yake had'e da nata yayi cupping fuskarta a tsakanin tafin hannun nasu.

Numfashinta a lokacin fita yake tare da nasa cikin nutsuwa kamar sunyi setting d'insa a tare. Imran ya kalli cikin wad'annan chocolate idanun nata, cike suke da d'imbin tambayoyi da kuma confusion, It was the same experession da yake hangowa a cikin kansa zata yi tun ranar da aka d'aura musu aure.

And as he stared into those deep brown eyes, ya gano banbancin tunaninsa da yanzu, a tunaninsa bayan duk wannan experessions d'in akwai tarin tsoro fal a cikinsu - amma a yanzu babu koda d'igon wannan tsoron, babu shi ko kad'an!

"I can't go on...ki fad'a min me kike tunani dan Allah."

Ta sake k'ifta idonta a hankali ba tare da tace komai ha, shima yayi shiru yana kallonta, he couldn't read her thoughts amma yana iya karantar abinda ke idonta clearly...tana cikin rud'ani kuma shima abinda yake ji kenan, sai dai yadda idanunta ke fluttering akansa yasa masa jin wata irin kasala a jikinsa, yaji d'umin fuskarta dake cikin hannunsa yana tura wani abu kamar electricty a kowacce jijiya ta jikinsa, a cikin tunaninsa ya hango yadda zai iya sunkuyawa a hankali yaji d'umin dake kan lips d'inta. Yayi saurin k'ifta idonsa kafin yace.

"I don't want you to be afraid... kar kiji tsorona Sa'adha dan Allah."

Muryarsa mai taushi ta fito a hankali kamar cikin rok'o, amma shi kansa a lokacin ya san abinda ya fad'a bashi da ma'ana, abinda ya kamata taji kenen, TSORO. Taji tsoron shi d'in dake zaune a gabanta yana gaya mata cewa shi ba mutum bane, shi wata halittar ne daban sab'anin tata ta mutane.

Nanne ta sake k'ifta idanunta a hankali tana kallonsa, his eyes were watching her, kyakkyawar fuskarsa kusa da tata sosai! kamata yayi ta fizge daga rik'onsa, tashi ta bar d'akin, ta bar gidan, ta bar unguwar ma gabad'aya, ta tafi duk wani waje da zai nesanta ta dashi.

Imran yayi shiru yana jiran abinda zata ce, gabad'aya duk wasu senses na jikinsa su d'aure tamau wajen sauarenta, ji yake kamar yaune rana ta farko da zai fara jin muryarta, Idonsa ya d'auko masa sanda ta rufe idonta a hankali sannan ta matso da fuskarta cikin wuyansa.

"I'm not afraid of you...!"

¡ñ©n¡ñ

Alhmdlilah ??????! yau kowannenmu zaiyi bacci da minshaaari...????Imran ya fad'a mana WAYE SHI da bakinsa bana wani ba.

I tynk abinda kowannenmu yake jira kenan daga tiltle d'in ma littafin...nd phewww! munji shi a yau.??

Do you tynk d story ends here???

I say Nahh, yanzu ne wasu abubuwan zasu fara unfolding.

Yanzu ne stanza littafin zata fara fitowa wato "Soyayya tsakanin mutum da wata halittar."

Yanzu ne zamu ji dukkan wani abu daya shige mana duhu a labarin.

Yanzu ne komai zai fito fili a fara battle d'in dake kwance a k'asa.

Yanzu ne Imran zai fahimci ainihin intention d'in Naani akanshi, da gaske tana son shi ko kuwa akwai wata manufarta ta taimakonshi?

Yanzu ne zamu ji in Imran zai gayawa Nanne irin had'arin dake gabanta.

Yanzu ne zamu ji yadda za'ayi burin sareefa ya tabbata.

Akwai abubuwa fa da yawa dake kudundune har yanzu.??

Masu rok'ona kan cewar Imran ya zama mutum na san na karya zuciyarku yanzu...don haka ina baku hakuri kwando-kwando.

Imran yace wai yaji a news cewa sugar yana kwantar da anger dake jikin mutum, zaku taimaka kusha wannan ko zamu samu fushin da kuke dani ya ragu...?????????????

Thank you for the support on this story so far. I feel like with each chapter I become a better writer and if it wasn't for those of you who have been reading it and reviewing I probably would have never gotten this far!..????

*****

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

46


(¡î_¡î)

Nanne ta k'ifta idanunta a hankali tana kallonsa, his eyes were watching her, kyakkyawar fuskarsa kusa da tata sosai! kamata yayi ta fizge daga rik'onsa, ta tashi ta bar d'akin, ta bar gidan, ta bar unguwar ma gabad'aya, ta tafi duk wani waje da zai nesanta ta dashi.

Amma ta kasa ko motsi, idanunta na kallon nasa wanda ke cike da matsanancin rok'o irin na yaro k'arami sanda ya maka laifi, bayan hakan kuma akwai hanqoro na jiran abinda zata fad'a, a hankali ta shak'i sassanyan k'amshin dake fitowa daga jikinsa, wani k'amshi mai sanyi da dad'i, Taji zuciyarta na ayyana mata cewa k'amshin zai iya kwantar da hargitsin dake cikin kanta, saboda haka ta matsa a hankali ta cusa kanta cikin wuyansa sannan ta fad'i abinda yake gaskiyar zuciyarta.

"I'm not afraid of you...!"

Da gaske ne ko kad'an babu d'igon tsoronsa da kalamansa suka sa mata, sai dai tarin mamaki fal da kuma rud'ani, gani take yi kamar a mafarki ko labari ne kad'ai abinda yake gaya mata zai faru, ta ture tunanin dake shirin kawo mata tsoro ta janyo b'arin zuciyarta dake cike da tausayinsa, tausayin irin rayuwar bautar da yayi a baya, wani abu da kwakwalwarta ta kasa hasko mata.

"I'm so sorry Noory, dan Allah kiyi hak'uri."

Muryarsa ta fad'a daga saman kanta amma bata ce komai ba, sai yayi shiru kamar me jira. Zuwa can ta d'ago da kanta ta kalle shi, idanunsa har a lokacin basu canja daga launin silver, Ta yaya ne suka koma haka? akwai tambayoyin da yawa a cikin kanta a lokacin, saboda haka ta saka wannan ma a cikin jerinsu.

"Wace irin halitta ce ALBIE? ni ban tab'a jin sunan ba ko a tarihi."

Ya kalleta sosai kafin ya amsa.

"Akwai tarin jinsin halittun Ubangiji a duniyar nan Sa'adha wanda tunanin d'an Adam bai sansu ba. abinda kowa ya sani kawai sune manya-manyan halittun; Mutane, Aljanu, Tsirrai da kuma Dabbobi.

Amma a k'arkashin kowannensu akwai jinsi kala-kala, idan kika d'auki dabba misali, akwai su da yawa, na k'asa da cikin ruwa, kuma ba kowanne irin jinsi kika sani a cikinsu ba ko aka ambata a alqur'ani ko hadisi, akwai wanda ma baza'a tab'a saninsa ba har duniyar ta ka're.

Ko a cikin ku mutane akwai jinsin k'abilu fal! wanda ba wanda ya san yawansu kuma ba kowanne aka ambata ba, toh haka a cikin jinsin Aljanu ma akwai irinmu da yawa da ba kowa ya sani ba. Mu ba Aljanu bane amma za'a iya danganta jinsinmu dasu tunda bama cikin mutane ko dabbobi."

"Kuma kuma musulmai ne?"

Ya d'anyi guntun murmushi yana kallonta.

"Yadda addini yake kala-kala a cikin mutane da aljanu, haka yake ma a wajenmu, bayan musulunci akwai wasu da yawa, sai dai a nahiyarmu, musuluncin shi yafi k'arfi."

Tayi shiru tana motsa yatsunta a hankali kafin tayi tambayar da take ganin itace jigon komai.

"Me yasa ka aure ni?"

Ta fad'a tana kallon labulen dake can bayansu, it was difficult for her ta fad'i kalmar aure tsakaninsu a fili.

"Saboda ina sonki Sa'adha." kalaman suka fito cikin muryarsa mai taushi, muryar da sai a yanzu Nanne ta lura cewa tayi dad'i da yawa ta kasance ta mutane. Mutane musamman maza basu da irin wannan taushi da zurfin muryar. It was so velvety-husky!

Ta dawo da kallonta kan fuskarsa, cikin d'an guntun tunani tace.

"Ban gane ba, nayi tunanin kazo yin aikin da aka turo ka ne ba wai kayi rayuwa a cikin mu ba."

Yayi shiru kafin ya k'ifta idanunsa a hankali.

"Ta yaya zan miki bayani ba tare da na tsorata ki ba..."

Sanda ya fad'i hakan yaji hannunsa d'aya da baya rik'e da nata yayi sanyi, saboda haka ba tare da ya nemi izini ba ya lalubo d'aya hannun nata yayi sliding nasa a ciki, nan da nan kuwa tunaninsa ya zama distracted.

"Hannayenki suna da laushi, ina son d'uminsu." muryarsa can k'asa tare da yin ajiyar zuciya. Bata ce komai ba shima yayi shiru kamar mai jera tunaninsa.

"Kin tuna ranar dana fara ganinki kin dawo daga islamiyya?" Ta d'aga kanta.

"Zuciyata ta fara sonki tun a wannan ranar Sa'adha, tun a ranar dana fara shigowa cikin bil'adama, a lokacin da ban san komai ba kuma ban san ya rayuwar zata tafi dani ba, sannan ban san ko ke wacece ba amma zuciyata ta karb'e ki wholheartedy, duk da cewa ban fahimci hakan ba a lokacin nayi zaton kawai abinda kika yi ne ya burge ni don ban tab'a ganin hakan ba.

A ranar jaamil ya gaya min cewa wannan gidan na layinku ba zaiyi min dad'in zama ba saboda yawan mutane a wajen, saboda haka na canja wani a can wata unguwa, bayan nayi settling komai kuma na fara bibiyarki ta hanyar zuwa layinku, a haka na gano lokacin da kuke fita makaranta da safe, sai inzo in wuce ku kamar na dawo daga morning training don in ganki, da kuma sanda kuke tashi daga makaranta, sau da yawa zanje a siffar da bazaki ganni ba, in tsaya a parking lot d'in da ake zuwa d'aukarku, don in saurari dukkanin hirarki..."

Nanne taji k'arar wani abu kamar murmushinsa can k'asa, ta d'ago daga kallon hannayensu da take ta kalle shi, murmushin kuwa yake kyallin siver idonsa ya haska a cikin nasa.

"...Na san duk wata fitinarki a lokacin Sa'adha, kin tuna ranar da kuka tsayar da wani tsoho mai turmi?"

Ta maida kallonta k'asa a hankali, ta tuna lokacin sarai, ita da Amina ne da kuma wata Aisha, suka tsaida tsohon nan suka yi ta cinikin wani k'aton turmi daya d'auko, kusan minti ashirin yana ja suna ja har dai ya sallama musu akan wani farashi mai sauk'i, sannan suka ce wai ya dawo gobe zasu taho da kud'in, ai kuwa ya d'auki turminsa ya tafi yana zaginsu tare da Allah ya isa.

She smiled, and he smiled ruefully back.

"Bayan haka Noory kullum da yamma lokacin dawowarki daga islamiyya zanzo in tsaya daga wajen wasu samari da mafi yawa suke taruwa daga jikin mota a sigar da ba mai ganinna.

Sai dai a kullum ina gayawa zuciyata cewa abinda nake ba daidai bane, zai iya zama min matsala musamman idan Naani taji, amma kuma duk sanda na kwana biyu bai ganki ba, bana iya focusing akan aikina, Saboda haka a kullum zan cewa kaina daga ranar ba zan k'ara zuwa wajenki ba, amma gobe zan dawo.

Ban ankara da cewar abinda nake yi da gaske zai zame min matsala ba sai ranar dana ga cewa kina iya ganinna bayan kuma ina zuwa ne a sigar da idon mutane ba zai iya d'auka ba. Sau da yawa zaki juyo kamar kin kalle ni sai kuma kiyi saurin juyawa ki kalli Rahma da kuke tafiya tare. Tun daga wannan lokacin ne na takura kaina na daina bibiyarki kusan watanni biyu, shine wannan lokacin da kika ce kin daina ganina."

"Me yasa a lokacin dana tambayeka wajen wa kake zuwa ka min k'arya?"

Ya d'ago hannayensu yana kallo sannan yace.

"Ta yaya zan gaya miki a lokacin cewa ba wanda ya san ni saboda ina zuwa ne a siffar da ba wanda ke ganina?"

"Toh me yasa ni kad'ai nake iya ganinka? kana tunanin inada wata matsalar ne?"

"Nine nake zuwa a siffar da mutane basa ganina, and you're worried that kice mai matsala?"

Imran ya fad'a da d'an guntun murmushi a fuskarsa, ta fahimce dukkan manyan abubuwan da ya fad'a amma wannan kawai ya sata tunani? ya kalli fuskarta, wani abu kamar damuwa etched deep between her eyes, sannan tana ta tauna lebb'enta.

"Karki damu, ba wani matsala bane, ina tunanin alama ce na cewa ni dake are meant to be together."

Ta sake tauna lebb'enta sannan tace.

"Shi yasa na tambayi Sadiq a lokacin yace min bai sanka ba."

Maimakon ya bata amsa sai ya zare hannunsa daga cikin nata ya kaishi kan bakinta, ya janyo lebb'en daga cikin bakinta.

"Zaki ji wa kanki ciwo..." Kalaman suka rataye a iska kamar ba iyakar abinda yayi niyyar fad'a ba kenan.

Nanne ta kalli cikin idanunsa har yanzu suna kyallinsu na silver ga wannan sassanyan numfashin nasa yana kad'a fuskarta a hankali, zata iya zama tare dashi haka zuwa tsawon lokacin da baza ta iya tantancewa ba, amma a halin yanzu akwai tarin abubuwa da take son sani, labarin bai kai k'arshe ba saboda haka ta d'an matsa baya kad'an sannan tace.

"Bayan nan ban k'ara ganinka ba sai ranar daka fara min magana."

"Right... lokacin da nake zuwa ganinki, jaamil ya lura da abinda nake yi, saboda haka ya dawo daga Muzzaffar lokacin dana riga na daina zuwa wajenki yayi min gargad'in cewa in daina abinda nake tun kafin Naani ta sani, ganin yadda ya d'auki abin da zafi yana ta b'ata rai, sai nayi tunanin in k'ara tsokanarsa saboda haka a ranar muna tare dashi na hango ki nazo nayi miki magana don ya gani, sai dai wannan maganar ta rushe duk wani tarin k'ok'arin da nake na avoiding d'inki, naji cewa ba zan iya sake nesanta kaina dake ba, saboda haka na dawo da zuwa ganinki."

"A wannan ranar na kwana da wani irin ciwon kai, hakan yana da alak'a da kai?"

"I'm afraid yes, saboda na tab'a jikinki a karo na farko."

Ta kalle shi da mamaki, idonta na nuna tambayar da bata furta ba.

"Sanda nazo baki handkerchief d'in nan, yatsana ya tab'a naki kad'an yadda ke baki ji bama."

Ta had'iye wani abu a mak'ogwaronta kafin tace.

"A lokacin nayi tunanin handkerchief d'in Babba ne, amma daga baya dana d'auko sai na ganshi d'an karami."

"Mhmm Mhmm..." Ya girgiza kansa yana kallonta.

"That's not something important...Ki gaya min ciwon kan naki ya dad'e a ranar?"

Ta girgiza kanta a hankali.

"Dana tashi da safe babu shi."

A cikin kanta, ta tuna mafarkin da tayi da muryarsa a lokacin, muryarsa mai taushi data ambaci sunanta.

"Bayan wannan ranar na kasa daurewa da daina ganinki, na cigaba da zuwa duk da irin magiyar da jaamil yake min, a sannan ne kuma nayi wani abu da ban tab'a yi ba tunda nake a rayuwata..."

Ya tsaya a lokaci d'aya sannan ya kawar da kansa daga kallonta. Itama bata ce komai ba ta cigaba da kallonsa har zuwa sanda yayi deciding cigaba da magana.

"Naje makarantarku lokacin da kike gayawa k'awarki kina son aljanu su shiga jikinki don ki mari wani malaminku...i was instantly jeleous! da naji kina nenan aljani a tare dake, kuma na san a wannan lokacin da an sami aljanin da ya jiki zai shiga jikinki ne da hujja and i don't think i can stand that... ba zan iya jure ganin wani tare dake ba, alhalin nima zan iya taimaka miki ta wannan hanyar, saboda haka ba tare da nayi shawara da kaina ba na shiga jikinki a islamiyyarku."

He sounded ashamed, kamar yana admitting wani rauninsa. Nanne taji kanta ya d'aure, tunaninta ya hasko mata Malam Mukhtar, sanda yazo k'ofar gidansu yana gaya mata cewa Malam Murtala ya rantse cewa yaga aljani a jikinta, ashe Imran ne? Ta yaya ya ganshi a matsayin aljani? Ta yaya ma ya iya shiga jikinta? Common sense d'in kwakwalwarta na gaya mata cewa kamata yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login