Showing 69001 words to 72000 words out of 113985 words
rungume zuciyarta, ya mamaye kowanne lungu da saqo na cikin kanta, tayi murmushi mai fad'i tana kallon cikin idonsa.
"Sai kace dan Allah tukunna."
Sai ya d'an karkata kansa dab da kunnenta na dama, ya sauke muryasa can k'asa sosai yace.
"Dan Allah... iya d'an malam!"
Ta kyalkyale da dariya jin dad'i kafin ta zare hannunta daga nasa, sannan ta mik'e ta nufi kitchen. k'asa-k'asa yabi takun k'afafunta da kallo, rangad'ed'an jan k'unshin bikinta har yanzu bai gama fita ba.
Zuciyarsa ta matse da tunanin yadda nan da d'an k'ank'anin lokaci zai karya tata zuciyar da mummunan labarinsa a cikin kwanakin da ya kamata su zama na farin cikin rayuwarta, kwanakin da ko lallen bikinta bai gama fita ba.
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
44
(¡î_¡î)
Tun shigowarsa gidan, tunaninsa cike yake da abubuwa biyu da yake ta k'ok'arin daurewa, Rud'ani da kuma tashin hankali, yana cikin ryud'anin kalaman da jaamil ya gaya masa tun a Muzzaffar, lokacin da ya shak'e shi a jikin bangon fadar Naani bayan fitowarsa.
"Me ya same ka ne yarima? me ya shiga kwakwalwarka? wannan dalilin shi yasa Naani tak'i gaya maka ainihin abinda zai faru, yanzu kuma da ka jiyewa kunnenka me ya kamata kayi? kamata yayi ka shak'e ni kana zargin harda ni za'a kasheta? ita wace ce a wajena ko wajenka? kar ka manta fa ta shigo cikin rayuwarka ne saboda kuskuren da kayi tun farko, kuma nine sanadin da yasa ka same ta.
Sanadin da muka yi na k'arya wanda zai k'are nan da wani k'ank'anin lokaci, nan wajen shine rayuwarka yarima, anan danginka da duk wani tallafinka yake, can d'in da kake hangowa wani abu ne da ba zai tab'a d'orewa ba. Ya kamata ka janyo hankalinka daga duk inda ya tafi, nida Naani da kake tunanin zamu yi maka ba daidai ba mune sanadin duk wani abu daka samu a can, don ba don Naani ba babu ta yadda zaka iya samun jikin bil'adaman da zaka iya rayuwa a cikinsu, ba don ni ba kuma babu ta yadda zaka yi ka samu yarinyar a matsayin matarka.
Kaje cikinsu ne don aikin da Naani ta saka, ba don ka gina wata rayuwar da a yanzu kake mana kallon wad'anda zasu kwace ta ba, karka manta ko an cire ruhinka daga jikinta kuma ta rayu ba zai tab'a yiwuwa ka cigaba da zama da ita ba. Mun tsara hakan tun lokacin dana same ka da zancen ka aure ta kuma ka tabbatar min da zaka bada had'in kanka mu gyara kuskuren daka jawo tun farko.
Ko sau d'aya zuciyata bata tab'a yarda da zancenka na cewar baka son yarinyar ba amma nak'i nuna maka ne saboda na san bani da wata mafitar data wuce wannan a lokacin, sannan nayi zaton idan komai yazo k'arshe zaka iya daure zuciyarka mu k'arasa abinda ya kaimu tun farko wato aikin Naani, nayi zaton zaka daure zuciyarka ka farantawa halittar data tallafe ka har ka kai wannan matsayin da kake a yau, na zata zaka iya daurewa zuciyarka kamar sauran abubuwa da yawa a baya da muka sadaukar don samun farin cikinta...amma ban san cewa ka raba zuciyar taka gida biyu ba, ban san cewa ka bawa yarinyar irin matsayin da kake bawa Naani ba, ban san kuma cewa zaka iya had'a Naani da wata k'ask'antacciyar halittar..."
Imran ya tuna marin daya d'auke fuskarsa dashi a lokacin har saida jini ya fito ta idonsa, sannan a hankali muryarsa tace.
"Sunanta Sa'adha, ka sake kiranta da k'ask'antaciyar halitta ko sau d'aya ne kaga yadda zanyi kaca-kaca da fuskarka." ya fad'a kamar iya abinda yaji yace kenan.
Jaamil yasa hannu ya shafo jinin daya fito sannan ya d'ago ya kalle shi, baice komai ba sai ajiyar zuciya kawai da yake fitarwa kamar yana son danne wata zuciyar dake gaya masa cewa ya rama.
Imran ya sake shi sannan ya matsa baya yana cigaba da kallonsa. Ya riga ya sani, duk abubuwan daya fad'a gaskiya ne haka suka tsara tun farko, sai dai a yanzu baya jin zai cigaba da biyewa wannan gaskiyar, don zuciyarsa ta riga ta yadda da wata gaskiyar da yake ganin duk duniya babu wata halittar data isa ta kore hakan, gaskiyar cewa yana son Sa'adha kuma ba wani abu da zai bari ya shiga tsakaninsa da ita ko ya kawo k'arshen zamansu.
Aikin da Naani ta tura shi cikin bil'adama ba zai yiwu ba sai da b'arin ruhinsa wanda yake jikin Sa'adha, abinda suke kwad'ayin samu kenan da har suke ikirarin zasu fitar dashi unrespect of duk wani hali da Noorynsa zata shiga.
Amma yadda ya tsaya a wajen nan, ya d'aukarwa kansa alk'awarin cewa abinda su Naani ke shirin yi ba zai tab'a faruwa ba, zai kare Sa'adha da dukkan iyawarsa, zai d'auke ta zuwa wajen da d'ayansu ba zai tab'a ganota ba har sai ya sami hanyar da zai iya kawowa Naani abinda take buqata zuwa nan da wata biyun da komai zai faru, zai nemo yadda zaiyi ya iya rik'e DUTSEN NIL da b'arin ruhinsa guda d'ayan ba tare da na jikin Sa'adha ba, zai nemo dukkan k'arfin da zai iya kawo shi har gaban Naani, In ta samu abinda take so ya san zata barshi ya samu damar da zai iya k'arasa rayuwarsa ba tare da takurawar d'ayansu ba.
Don a yanzu ya riga ya yarda cewa dukkan wani farin cikinsa yana tare da Sa'adha ne, ba zai tab'a iya sake dawowa cikin su ya cigaba da rayuwa ba, zai zauna cigaba da zama a matsayin bil'adama koda Naani baza ta cigaba da tallafarsa ba, koda kuwa hakan zai zama sillar rasa ransa!
Ya taka k'afafunsa baya a hankali yana cigaba da kallon jaamil kafin ya juya da sauri da niyyar barin wajen. Daga can gabansa tarin cinkoson al'umma ne taf! dake jiran fitowarsa, amma bai damu ba, zai wuce ta cikinsu ya koma wajen Sa'adha tun kafin Naani ta samu labarin abinda ya faru yanzu tsakaninsa da jaamil.
"Do you think she wants you!?..."
Muryar Jaamil ta tsaida shi cak! a wajen.
"Bata san WAYE kai ba yarima, bata san ainihin waye kai ba, labarin wani Imran kawai ta sani, wanda babu shi a duniyar nan...akwai tarin dalilan da zasu k'alubalanci zamanku ko daga 'yan uwanta.
Idan kana son shirmen daka tsara a cikin kanka ya cigaba da faruwa dole sai ka sami had'in kanta tukunna wanda ba zai tab'a faruwa ba, daga lokacin da ka gaya mata gaskiya daga lokacin zata rabu da kai, saboda ba kai take so ba, Imran d'in da muka yi planting akanta ta sani kuma shi kad'ai take so!"
Wannan zancen shi ya kawo tashin hankalin tunaninsa na biyu, don gaskiyane Sa'adha bata san ainihin waye shi ba kuma bashi da tabbas cewa in har ta sani d'in zata cigaba da bashi trust d'in da yake samu a wajenta, saboda haka bashi da zab'i a yanzu illa ya fad'a mata gaskiyar da yake ta yiwa ado da k'arya, in ba haka ba dukkan wani abu daya tsara ba zai tab'a yiwuwa ba. Komai ya riga yazo k'arshe, kuma amsar da zai samu a wajenta ita zata yi determining k'addarar da zata faru nan gaba a rayuwarsa!
"Toh wanne zaka fara, wankan ko cin abincin?"
Ya d'ago idonsa ya kalleta tsaye daga jikin dining area, sannan tarin warmers d'in dake zube a gefenta.!
Yaya rayuwarsa zata kasance bayan yau?
Me zai faru dashi anjima?
Zai sake ganin irin wannan kulawar ta Sa'adha?
Zai sake ganin irin wannan kallon daga gareta?
Ya Allah!
*****
"Me kika dafa mana?"
Ya fad'a sanda yaja kujera d'aya ya zauna, Nanne ta fito daga kitchen rike da cups a hannunta ta kalle shi, ya canja kayansa zuwa wata jallabiya mai kyau light brown. K'amshin turaren jikinsa ya had'e dana sabulun da yayi wanka.
"Me kika dafa Noory?"
Muryarsa can k'asa ta sake fitowa yadda duk sanda yayi hakan yake sata jin wani iri. Me yasa ne muryarsa take da tasiri akanta?
Ta matso kusa dashi ta bud'e warmers d'in, k'amshin wani abu curry, albasa da kayan k'amshi ya cika hancinsa, bai san cewa da gaske yana jin yunwa ba sai a lokacin don hargitsin dake cikin kansa yasa ya manta da sunan wani abu abinci, kuma a d'azu ya fad'a ne kawai don d'auke lokacinta daga amsarsa sa da take jira, don yana fatan kowanne k'arin lokaci ya taho masa da k'arin karfin gwiwa.
Ta zuba abincin a plate d'aya kamar yadda suke ci a koyaushe, yadda ya koya mata sannan ta zauna, a lokacin ya lura cewa akwai abinda yake damunta, idanunta sun nuna masa hakan duk da irin k'okarin da take na kar ya gane.
Shigarta ta dark purple kaya ya mata kyau sosai, duhun kayan ya k'ara fito da hasken fatarta da a yanzu ta zama So fresh mai laushi, d'ankwalin kanta ya zame kad'an yadda yana iya hango lallausar sumar kanta, bak'a wuluk sai shek'i take yi, yaji yana son zura hannayensa ciki yadda zasu lume cikin laushin gashin, ya salam! ya janye idonsa daha kanta da sauri don idan ya cigaba da kallonta zai iya mance duk wani abu dake gabansa a yanzu ya jawo ta zuwa jikinsa.
"Duk sanda nake cin abincinki Noory sai inyi ta mamakin me nake ci ne a baya."
Ta d'age gira d'aya tana kallonsa.
"For example kinga irin wannan abincin, a kwakwalwata gabad'aya babu irin tunaninsa, ban san ana yi irin su ma ba balle inje in siya."
"Irin wanne kake ci toh?"
"Sau da yawa nafi shan tea ko duk wani abu cereal, amma duk ranar da zanyi girki, to ba wuce taliya ko farar shinkafa...shi yasa a yanzu nake mamakin yadda akayi na rayu a baya."
Ta d'anyi murmushi kad'an.
"Kuma kin san duk sanda zanyi girki ban fiye amfani da plate ba?"
"A tukunya kake ci kenan?"
Ya d'aga kansa ya na kallonta.
"Kuma akan wuta, saboda in nazo d'and'anawa inji ko ya dafu, full cokali nake d'iba kuma sai in d'and'ana fiye da sau ashirin..."
Dariya ta kamata a lokaci d'aya.
"Ashirin fa? ai ka cinye abincin."
"Kamar kin sani, in na gama sai in ganshi d'an kad'an a tukunya, gashi kuma ni na kusa k'oshi...kinga ba amfanin plate kenan, sai kawai in k'arashe abuna da serving spoon d'in dana fara ci."
Nanne ta kyalkyale da dariya tana rufe bakinta, ya lumshe idanunsa a hankali yana kallon yadda take dariyar sosai.
She's so innocent! mintuna kad'an tana cikin damuwar da har fuskarta ta nuna yanzu kuma ta koma farin ciki, yaji kamar ya jawo ta ya rungume ta sannan ya b'oye ta daga dukkan wani hargitsin dake gabansu.
Idanunsa na kanta gabad'aya ranar, yana kallon dukkan activities d'inta kamar yana yi musu kallon karshe, bai san me zai faru ba, so he wanted to capture every single memory of her, yadda daga baya zai samu abinda zai rarrashi zuciyarsa kafin sanda da zata yi rauni ta karye gabad'aya.
A lokacin da ya dawo daga sallar maghriba, a sannan ya zab'i lokacin ya zama sanadin k'addarar rayuwarsa, ya zaunar da ita a falo lokacin da ta kawo masa yankakkun fruits masu sanyi a cikin bowl, ya zaunar da ita a gaban zuciyarsa dake bugawa kamar zata fito waje.
Ya zaunar da ita don gaya mata gaskiyar WAYE SHI!
¡ñ©n¡ñ
I promise ba wani kewaye-kewaye, chapter k'asa tazo da direct bayanin WAYE IMRAN, and d intresting part...daga bakinsa zamu ji komai...!??
*****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
45
(¡î_¡î)
"Sa'adha kin san a yanzu ke matata ce koh?"
Nanne ta d'aga kai a hankali tana kallonsa, ya sake damk'e hannuta a cikin nasa kafin ya cigaba.
"Kin san kuma cewa babu wani secret tsakanin mata da miji koh? tun daga ranar da aka d'aura mana aure komai namu ya zama d'aya, walau farin ciki ko bak'in ciki bai kamata d'ayan mu ya b'oye wa d'aya ba..."
Yayi shiru tare da yin ajiyar zuciya yana kallon hannusa dake sarke nata, zuciyarsa na tattaro dukkan kalaman da yayi bitarsu fiye da kirgen mai kiga. Yayin da Nanne ta cigaba da kallonsa blankly tana jiran taji abinda yake shirin fad'a mata, taji dalilin da yasa yake cikin damuwa kwana biyu.
"Ina so ki fahimce ni sosai a yanzu, ki bud'e kwakwalwarki ki fahimce ni dan Allah...Sa'adha na miki wani babban laifi tun daga farkon had'uwata dake har zuwa yanzu, nayi miki laifi dake dasu Baffa dama duk wanda ya san labarin auren mu..nayi muku laifin da za'a iya kira da yaudara koma wani abu fiye da hakan."
Zuciyarta ta buga amma a hankali sakamakon mamaki daya zagaye tunaninta a lokaci d'aya. Laifi kuma? wane irin yaudara?
Ya sake wata dogowar ajiyar zuciyarsa yana kallon carpet d'in da suke kai unseeingly, sannan ya cije gefen lebb'ensa kamar zai datsa shi.
Lokacin daya d'ago da kansa, yanayin idanunsa sun canja daga haske zuwa wata kala da tayi kama da silver, wani abu da Nanne bata tab'a gani ba.
"Sa'adha ni ba irin jinsin halittarki bane, I'm not human.!"
Ya fad'i kalaman da dukkan wata dauriyarsa yana cije bakinsa kamar baya son su fito, don ba don tana kusa dashi sosai bama ba lallai bane taji me ya fad'a ba.
Ya cigaba da kallonta da idanunsa so stiff a kanta, yana karantar yadda fuskarta take absorbing kalaman, bata ce komai ba? me take tunani? anya kuwa taji abinda ya fad'a? ya tsirawa idanunta ido bada ko k'iftawa ba amma ya kasa tsinto wata ma'ana guda d'aya a cikinsu, they were blank! watakila can k'asansu lullube yake da tarin tsoro, watakila kuma tana tattara dukkan k'arfinta ne waje d'aya yadda zata kwalla ihu a kowanne lokaci.
Wani abu mai kama da lokaci ya tsaya cak! a cikin kan Nanne, ta maimata abinda ya fad'a a cikin kanta sau ba adadi, tana rarraba su filla-filla don ta nemo real ma'anarsu.
"Kai ba mutum bane?"
She tried the words out, ko zata ji ma'anar ta fito akan lebb'enta amma ta gagara fahimtarsu, sai mamakin yadda harafan suka had'u suka yi forming sentence d'in.
"Yes, I'm an illusionist, wata halittar daban da taku."
Ta tsira masa ido tunaninta baya aiki a lokacin, shima kallonta yake da idanunsa a tsaye kyam! zata iya rantsewa tunda take dashi bata tab'a ganinsa so serieos irin yanzu ba, taji tana nutsewa cikin a idanun nasa zuwa wani k'arshe mai nisa, miles and miles away! amma duk nisan da ta kai ta kasa gano ma'anar abinda ya fad'a.
"Okay." Ta fad'a a hankali cike da mamakin yadda muryarta ta fito so calm, watakila don tunaninta ya riga tsaya ne a lokacin.
"What?" Ya fad'a a fili yana kallonta, gaya mata yayi fa shi ba mutum bane and the best amsar data samo shine Okay?
"Sa'adha ki fahimce abinda nace kuwa?"
Ta girgiza kanta da sauri.
"Ban gane ba Imran, ban gane me kake nufi ba."
Da gaske ya yarda bata gane d'in ba, don tunda yake da ita bai tab'a jin ta fad'i sunansa ba sai yanzu. Zuciyarsa ta cika da wani sabon hope d'in daya manta yaushe rabon da yaji irinsa, ya sake damk'e hannunta kamar yana tsoron zata iya kwacewa a kowanne lokaci ta gudu.
"Ki kwantar da hankalinki kinji? zanyi miki bayanin komai tun daga farko...you don't have to talk."
Ta had'iye wani katon abu a mak'ogwaronta tana kallonsa da idanunta so wide kamar zasu fito.
"Ni ba mutum bane Sa'adha..." Ya sake maimata abinda bata ganewa.
"...na fito daga jinsin wata halitta da ake kira ALBIE, na san baki tab'a jin koda irin sunan ba, saboda bama shigowa cikin bil'adama mu'amalarmu tafi yawa ne tare da Aljanu wanda sune 'yan uwan halittarmu, duk da cewa akwai tarin banbanci tsakanin halittarmu da tasu."
Nanne bata san ko akwai iskar dake fita da a kirjinta ba koma tana iya numfashi ba a lokacin, kwakwalwarta ta riga ta gama cakud'ewa, da kyar ta iya maida tunaninta kan muryarsa dake cigaba da magana.
"Aljanu basu da jiki amma mu muna dashi, suna iya shiga jikin bil'adama mu kuma bama iyawa ba tare da bin wata hanyar ba, sannan jinsin Aljanu yana da yawa a doron k'asa yayin da mu kuma 'yan kad'an ne a duniya, bamu da yawa sosai. Sannan akwai abubuwa da yawa wanda muka fip aljanu k'arfin yi, sai dai kamar yadda mutane suka fisu daraja haka suma suka fimu daraja saboda suna iya mu'amala dasu, mu kuma bama iyawa
Wasu daga cikin mutane da suke da sani akan aljanu da rabe-rabensu su sun san wani abu game damu amma ba komai ba, kuma suna danganta mune da jinsin bak'ak'en aljanu tunda sun san muna posessing wasu abubuwan da aljanun basa iyawa sai dai manyansu.
Akwai wajaje da yawa a duniya inda irin jinsinmu suke rayuwa, amma sunan nahiyar dana fito 'Muzzaffar"
"Ta yaya...."
Muryarta fito daga can k'asan makogwaronta amma yayi saurin katseta.
"Shshshsh... you don't have to talk remember?"
Ta d'aga kanta a hankali, har yanzu hannayenta na cikin nasa.
"Kin tuna abinda na fad'a miki ranar da aka kawo ki gidan nan? every single word a lokacin gaskiya ne Sa'adha, tun da na tashi a rayuwata ban tab'a sanin iyayena ba, sun rasu tun kafin in san kaina, haka kuma bani da wani dan'uwa na jini dana sani, duk sun mutu a wani yak'i daya had'amu da wasu irin jinsinmu dake wata nahiyar.
Na tashi babu gata a cikin wata irin rayuwar da babu komai a cikinta sai fafutukar neman yadda zan rayu, nayi bauta a wajen irin jinsinmu da yawa kafin daga bisani na koma bawan wani mai suna 'Darshan' na shekara uku a wajensa kafin daga baya ya tattara dukkan dukiyarsa da nufin komawa Muzaffar, don a lokacin muna wata nahiya ne da ake kira 'Sabeel'.
Dukiyarsa ta had'a harda tarin bayinsa wanda yayi niyyar zuwa Muzaffar d'in ya sayar dasu da tsada, kuma a cikin bayin nasa har dani Sa'adha. Sai dai a ranar da muka shigo Muzaffar a daren ya rasu, lokacin yana kwance a d'akin hutawar daya kama na cikin kasuwar garin, mutuwarsa tasa kowa ya rud'e a wajen kasancewarsa baqo a gurin, a cikin wannan hayaniyar na samu na kwance sark'ar da aka d'aure ni na gudu.
Na fad'a can cikin Nahiyar muzaffar na samu wani wajen da ba wanda ya san ni na cigaba da rayuwata.
Kin tuna na fad'a miki na samu tallafin wata halitta bayan duk wahalhalun dana sha a baya? wannan halittar itace Naani, Shugabar Nahiyar Muzaffar, na had'u da ita ne lokacin dana rasa duk wani tallafi a rayuwa, ita ta rik'e ni da dukkan kulawarta, ta jawo ni jikinta, ta bud'e min sabuwar duniyar dana sami komai dana rasa a baya, 'yan uwa, d'aukaka, matsayi da kuma tarin abubuwan da