Showing 45001 words to 48000 words out of 113985 words
fahimci cewa in har zasu tafi akan tsarin da suka yi da jaamil kawai to dole zasu fuskanci matsala nan gaba, don ba zata k'i aurensa ba amma zuciyarta baza ta yarda dashi ba wanda hakan dole zai jawo matsala nan gaba.
A daren ya lura kamar kuka take, daga baya kuma ya fahimci mafarki take yi kuma kamar wani abu ya same ta ne a cikin mafarkin, ya san zata iya farkawa a kowanne lokaci saboda haka yayi sauri ya d'ora hannunsa akan goshinta sannan ya shiga kwantar da d'aya b'arin ruhinsa dake tare da ita.
Sai dai kafin alamun cewa hakan yayi, ya fito, ta bud'e idonta da sauri tare da yin ajiyar zuciya, a sannan ya tabbatar da cewa mafarki tayi wanda ya tsorata, yana cikin d'akin har sanda tayi alwala ta fito sannan ta tsaya gaban mudubi, ya matso dab da bayanta ya tsaya don yaga abinda take gani a cikin wayar data d'auka.
Number daya kira yace mata zaizo ce, ita take ta kallo kamar tana so ta tantance ko shima kiran da yace mata zaizo a mafarkinta ya faru, ya lura ta haddace number saboda haka dole ya nemo layin duk inda ya shiga, don bayan ya kirata ba zai iya tuna inda yasa shi ba.
Ta d'ago ta kalli mudubin, a lokacin ne alamun cewa ciwon ya kwanta ya faru, wani hayak'i ya fito daga rabin fuskarta ya tarwatse a iska, kamar yadda yake yi kullum.
Tun daga yadda yaga ta tsorata a lokacin, ya san sai ya kwantar mata da hankali in ba haka ba abubuwa ne zasu k'ara cakud'ewa a cikin kanta.
Shi yasa bayan yazo ta hana shi ganinta, ya san sai yayi amfani da dabararsa don ya saita tunaninta, saboda haka ya kirata bayan sallar magriba.
Amma kamar yadda ya sani ne, bai yarda da kansa in yana tare da ita ba, bai yarda da zuciyarsa akanta ba. Saboda haka tun lokacin data amsa sallamarsa bai k'ara bi ta kan tsarinsu ba, yayi amfani ne da hanyar daya san zata kwantar da hankalinta kawai.
Bayan nan kuma ya tafawa kansa da shirmen da yayi, shirmen da ya fara tun ba'aje koina ba, shirmen da yayi k'ok'arin lullub'ewa jaamil d'azu cewar ba wani abu bane da zai b'ata tsarinsu, shirmen da yayi d'azu na aika mata da sweets d'in nan, sannan shirmen da yake shirin sake irinsa yanzu.
Ya bud'e cikin wayar ya shiga typing mata message.
Missing me already?...ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d'inki
Habibty...
Ya tsaya ya kalli abinda ya rubutu, sannan a hankali ya k'ara da..
...like crazy!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
31
(¡î_¡î)
"Kin min shiru Sa'adha don Allah kiyi magana, ko har yanzu fushin ne?"
Nanne ta sake tankwashe k'afarta akan gadon tana nannad'e bakin rigar filon dake kan cinyarta, a hankali tace.
"Kana lafiya?"
"Ina lafiya kuma yanzu da kika tambaya sai na k'ara jin lafiyar ta kama ni."
Tayi murmushi mai fad'i.
"Ina jinki ki fad'a min sau nawa kika tuna ni bayan lokacin da kika ce min sai da safe?"
Bata ce komai ba kamar yadda ya zata.
"Ko sau d'aya ne kawai sanda kika yi min flashing?"
Da sauri tace.
"Ni ba flashing nayi ba ban sani bane kawai kiran ya shiga na zauna a kusa da wayar."
"Irin wannan bayani haka kamar laifi kika yi?...yanzu toh ba wannan ba, baki tambayeni sauran bayanin jiya ba."
Ta d'an hade girarta kad'an.
"Wane bayanin?"
"Bayanin koni WAYE mana, ko ba kya sonp kiji abinda nace wa baffa ya bani aurenki? ko kuma ki san wane irin miji zaki aura?"
"Na san zaka fad'a min ai."
"Ta yaya kika sani? saboda kin san ina sonki?"
Kamar baza ta amsa ba sai kuma tace.
"Mhmmm.."
"Toh mhmm kema kina sona?"
Ta sake yin shiru.
"Ya Allah! Sa'adha kin mayar dani d'an jarida sai tambaya nake tayi akai-akai."
"Toh ina jinka, ka fad'a min."
"Shikenan mu ajiye wannan a gefe zamu dawo kansa daga baya, bari in fara baki tarihin mijinki tukunna.
Sunana Imran kamar yadda kika sani, amma full name d'in Imran Siddiq, ni d'an garin bauchi ne iyayena sun mutu tun ina yaro saboda haka a hannun k'annin mahaifina na tashi, A bauchi nayi duk karatuna da komai, sai daga baya na samu aiki anan garinku.
Aiki a company ORZ dake kula da harkokin talla na media platforms, shi yasa nake zaune ni kad'ai ba tare da kowa ba, don dukkan 'yan uwana suna can."
This is it! just simple kamar yadda suka tsara a farko zuwansa, haka normal rayuwar matashi irinsa ya kamata ta kasance.
Jin tayi shiru yasa ya cigaba da cewa.
"Tun daga bauchi 'yan uwana suka zo nema min aurenki kwanansu biyu a garin nan, kuma a duk kwanakin suna ta yabawa da irin tarbiyyar gidanku, sunce baffa mutumin kirki ne zanyi sa'ar auren 'yarsa."
Ta cigaba da nannad'e rigar filon a hannunta.
"Tun da suka koma kuma ake ta min waya daga gida, masu son ganinki na da yawa Sa'adha, basu san cewa ni kaina an hana ni zuwa ba."
Ya k'arashe zancen a hankali yana jin nauyin kalamansa na baya, tun farkon sanda ya fara wannan rayuwar, yana tafiya ne akan wannan tsarin, wannan k'aryar...amma tunda yake bai tab'a jin komai ba sai a yanzu da yake gayawa Sa'adha.
Saboda daga yanayin bugun zuciyarta da yake ji ta cikin wayar, ya san ta yarda dashi ne, ta yarda da duk abinda ya fito daga bakinsa.
Amma duk da haka yaji yana son sanin me take tunani a yanzu, meke faruwa a cikin kanta, ya rufe idonsa da k'arfi amma ya kasa jin komai, zuciyarta tayi masa nisan da ba zai iya reaching ba.
Saboda haka yayi shiru shima yana sauraren fitar numfashinta a hankali da kuma bugun zuciyarta. kusan minti biyu kafin ya kira sunanta, ga mamakinsa sai yaji ta amsa nan take.
"Zan iya ganinki gobe?"
"Me za'a yi?"
Kamar a lokutan baya, tana iya jiyo sautin murmushinsa daga d'aya b'angaren kafin yace.
"So nake inzo inyi hira da iyalina."
Kalmar tayi mata nauyi da kuma dad'i a lokaci daya, taji son da take yi masa ya k'aru a cikin zuciyarta, kamar a d'ebo yayi ne a k'ara akan wutar dake ci.
A hankali ta fad'i abinda take fad'a a kodayaushe.
"May be da yamma?"
"Baki tabbatar ba?"
Ta rufe idonta sannan tace.
"Na tabbatar Allah ya kaimu."
"Ameen Noory!"
Jin wani sabon sunan yasa ta bud'e idanunta kad'an sannan ta lumshe su.
Noory yau kuma?
Sunan ya mata dad'i sosai.
******
Har k'arfe hud'u na yamma Imran na jin kuzari a jikinsa da wani irin annashuwa daya manta lokaci na k'arshe da yaji haka.
Wayar da yayi da sa'adha d'azu k'arya ce, haka ma duk maganganun daya gaya mata, amma the fact that ta yarda dashi kuma a cikin duniyarta babu tunanin cewa k'aryar ne shi yake masa dad'i, yana son ya ture gaskiyar shima ya tafi da tunaninsa a hakan, ba don komai sai saboda yana jin dad'in abinda yake yi, yana jin dad'in duk wani moment d'in da yake tare da ita.
Duk cewa da yana tsoron kar biyewa son zuciyarsa ya jawo musu wata matsalar kamar yadda a baya ya jawo wadda suke cikinta a yanzu. Amma wannan tunanin baya tab'a zuwa duk sanda yake tare da ita.
"Uhmm....Siddiq are you with us?"
Muryar Ibrahim ta shigo cikin tunaninsa, ya d'ago da sauri ya kalle su, sai yanzu ya tuna suna zaune a cikin office d'insa su biyar suna tattaunawa akan advert d'in sabon company da suka yi meeting dasu d'azu, wanda har sunyi signing contract da komai yanzu zasu fara shirya yadda za'a baiyana wa al'umma kayaiyakinsu ne, wato irin tallan da za'a yiwa jama'a.
"I'm sorry dan Allah, wani abu ne ya d'an shiga kaina."
Ya karb'i file d'in da yake mik'o masa ya shiga karantawa, sai da ya gama tsaf! sannan ya d'ago ya kalle su yace.
"I don't think i like this idea, can't you come up with anything that will leave an immediate and strong impression?"
Wani usman ya d'an duba paper gabansa sannan yace.
"We just thought since the products are fibres, a simple advert will do."
Imran ya girgiza kansa.
"You should'nt have thought that, advert komai k'ank'artarsa komai rashin amfanin kayan ga al'umma, hakk'in mune mu tallata shi in a way da zamu iya karkata tunanin mutane daga kan neccesssities d'insu zuwa shi.
Saboda haka zuwa gobe, just keep thinking about something any idea that wiil catch the mind of viewers, prepare something more spectacular please.
Usman after that, I think you can work with Director Phillps to come up with a way to convey it. Ibrahim you will be in charge of the copy writing, and Maryam...
Ya juya ya kalleta, tana zaune a gefensa cikin shigarta ta matsatstsun kaya kamar kullum d'an karamin mayafinta na reto a kafad'a. Ba abinda ya sashi tsayawa da maganar kenan ba, hannayenta, hannayenta da suka sha wani had'add'en kunshi daya zauna d'as akan farar fatarta. Bai san ya akayi tun farko ya bari ta fahimci cewa yana son k'unshi ba, shi yasa duk sanda ta san zasu had'u take zuwa tayi don ta san ko ba komai zata samu alfarmar ya saurareta. Ya had'iye wani abu a mak'ogwaronsa kafin ya cigaba.
"...make a list of all the client that we will work with for the next quarter by tomorrow."
Ya juya ya kalli wata dattijuwar mata da kowa a companyn ke kira da Aunty Fati, mace ce mai tsananin kirki da sanin hakk'in al'umma, shi kansa yana ganin girmanta sosai saboda yadda ta maidashi kamar d'anta, don babban d'anta ma Abdullahi ya girme shi kuma ya sanshi duk sanda suka had'u suna gaisawa sosai.
"Aunty can you make me an appointment with Dr Turaki? I need to see him tomorrow."
Tayi murmushi kafin tace.
"Insha Allah Imran."
"Okay, we can call it a day."
Da haka kowa ya d'auki takardunsa suka mik'e, sai dai kafin Aunty fati ta kai ga fita, Imran ya tuna da abinda jaamil ya gaya masa jiya.
"Abu biyu ne da suka rage mana yanzu, wai akwai kaya da ake kaiwa gidansu yarinyar sunansa lefe, ni ban san ta yaya zamu had'a su ba.
Da kuma zancen gida, dole ne sai ka tashi daga gidan nan, saboda yayi kusa daga gidansu kuma ance min suna kawo kayan gida daga wajensu suma. Saboda haka inda zaka nema bana tunanin sai ka sayi komai.
Tuno hakan yasa yayi saurin tsaida ita, ta dawo ta zauna a kujerar dake gefensa.
"Aunty Faty wani abu ne ya taso min wallahi, kin san families d'ina ba'a nan kusa suke ba kamar yadda na fada muku..."
Ya d'an yi shiru yana juya abinda zai fad'a, amma murmushin fuskarta ya sashi cigaba da magana.
"...Toh aure na ne ya tashi, kuma bana son har sai na tafi can kafin a had'a lefe, shine nake so in tambaye ki ko zaki taimaka..."
"Kar ka kuskura ka k'arasa Imran, in har kace taimako kenan baka yin uwar dani kamar yadda ni na d'auke ka, Alhmdlilahi, wallahi naji dad'in wannan zancen sosai, dama na dad'e ina maka sha'awar aure a wannan lokacin, don shine cikar mutuncin kowanne mutumin arziki.
Zancen lefe kuma kar ka sami damuwa, insha Allahu za'a had'a ba da wata matsala ba, dana koma gida zan samu 'yan uwana, mu zauna muyi lissafin yadda muka had'a na Abdullahi, zaka ji duk wani bayani daga baya. Nayi murna sosai wallahi, Allah ya tabbatar mana ya sanya alkhairinsa a cikin lamarin.
Allah yasa kuma ta zama alkhairi a gare ka da kuma 'ya'yan da zaku samu a gaba."
*******
A cikin sati uku, kusan komai ya koma daidai a rayuwar Nanne, sunyi jarabawar first term sun k'are har an bada hutu na wata d'aya.
Hutun data san ita ta gama zuwa makaranta kenan, don baza ta koma second term ba sai lokacin Waec da Neco kawai kamar yadda baffa yace. Shirye-shirye ya kankama sosai daga kowanne b'angare, don hatta iyayen Imran maza sun kawo lefe akwati goma sha uku, Sannan ya had'a ta da'yan uwansa a waya sun gaisa.
Daga b'angaren inna kusan ba abinda bata tanada ba na harkar kayan d'akinta, ko baffa abinda ya bayar kad'an ne inna tace ta yafe masa tunda bai dad'e da bikin mata hud'u ba.
A cikin wannan lokacin ma Nuratu tazo da nata gudunmawar ita da 'yan uwanta, a sannan ne kuma Nanne take jin cewa shima Nuran da tayi mata zancensa an kusa bikinsa a lokacin itace bata sani ba a lokacin.
Ranta yayi fari kal! da tunanin shawararta Nanne ta karb'a ta yarda da aure a yanzu, musamman kafin su tafi da Imran yazo suka gaisa, sai farin cikinta ya k'aru, tana ganin ba k'aramar sa'a Nanne tayi na samun miji irinsa ba.
A kullum kuma alak'ar dake tsakanin Nanne da Imran k'aruwa take, a yanzu ta saba dashi sosai don har tana sakewa tayi masa hira a waya ko kuma in yazo. Duk da cewar wayar tasu tafi yawa, don a k'aida ne kullum zai kirata sau uku, da safe in ta tashi, da rana in yana office, da kuma da daddare in zasu kwanta.
Da gaske ne ya dad'a koya mata yadda zata so shi, don ko kad'an yanzu ba alamun wannan damuwar data shiga kwanaki sanda baffa yace aure zai mata, ta daina tunanin duk wasu abubuwa da zasu faru nan gaba, burinta kawai a kullum Imran ya kirata ya kara tuna mata cewa ta kusa zama tasa, duniyar gaba da take hangowa mai tsananin kyau ce tunda tana tare dashi.
Don hatta karatun da take tunanin zata cigaba a yanzu ji take yi meye ma amfaninsa in dai Imran yana cikin duniyarta.
Kusan komai ya gama kammala a satin da aka tsayar na auren. Imran ya bada muk'ullin gida a can wata unguwa dake nesa dasu.
Gini ne na zamani mai kyau sosai, d'an moderate house mai d'auke da falo biyu da three bedroms, dining da kitchen da kuma toilets uku. Ba wai tamfatsetsen gida bane amma yadda ya zama well furnished ya k'ayatar da kowa akayi ta santinsa.
A yadda inna ta tsara, babu wata hayaniyar biki da za'ayi. Kamu da walima ne za'a fara ranar juma'a anan cikin gidan nasu, sai washegari asabar ayi d'aurin aure da yini. Da yamma kuma akai amarya.
Nanne ta gaiyaci kusan duk 'yan ajinsu na islamiyya da kuma boko, don har islamiyar data bari sai da taje ta kai musu cards d'in, kowa yayi ta mamakin yadda basu tab'a jin zancen ba sai kati kawai suka gani, don lokacin da ta gayawa Aminah komai, sai da ta gargad'e ta kar ta fad'awa mutane saboda gudun surutu.
'Yan islamiyya kuma ba wajen wanda zasu ji tunda Rahma ba fad'a zata yi ba, kuma ko wasu daga 'yan layinsu ma basu ji ba sai da komai ya matso kusa.
Amma duk da haka sai da zance ya fara yawo a makarantar bokonsu cewa auren kud'i zata yi, wai irinsu dama basa gama makaranta suke samun Alhazan birni su aure su. Sai dai da yake shine bikin 'yar Ajin na farko da zasu fara, sai d'oki ya hana wannan gulmar tasiri, kowa ya shiga fafutukar siyan an anko wanda Amina ta fitar da kuma shirye-shirye.
Sanda Nanne taje ita da Rahma suka kaiwa su Malam Murtala katin d'aurin aure, ba karamin farin ciki da murna suka nuna ba, ta san tunaninsu iri d'aya ne da malaman da suka cewa Baffa aljanu na shirin shigarta kuma aure ne kawai abinda zai iya kore su.
A yanzu da sune silar farin cikinta bata sani ba gode musu zata yi sab'anin a farko da take ji sun juya duniyarta upside down?
Ranar laraba da daddare bayan ta wanke lallen da aka tsantsara mata, tayi wanka sannan ta saka kayan bacci, da kyar ma ta iya samun wanda zata saka don inna ta riga ta gama had'a dukkanin kayanta da zata tafi dasu sauran kuma duk ta rabar, harda wad'anda take tsananin so ba damar tace a bar mata.
Ta kwanta a kan gado cike da gajiya, daga nan tana iya jiyo hayaniyar 'yan falo wanda ke cike taf! ana musu nasu lallen.
Idan wani ya shigo cikin ba zaice dama bayan bikinsu ya Aisha 'yan niger sun koma ba, don wannan karon harda k'arin wasu aka samu tunda bikin na inna ne.
Banbancin kawai shine na 'yan uwansu mama halime, mama rabi da kuma hajiya Babba da basa nan wannan karon. Duk inda ta juya taga mutane sai ta kasa yarda cewa wai bikinta za'ayi, wai duk sunzo ne duk saboda ita kawai...
Wayar inna a kusa da ita tayi k'ara, Amina ce, ta d'aga ta kara a kunnenta.
"Toh Wallahi dole jibi sai mun fita da wuri, don su Aysha mahmoud naji duk sunce wajen suma Zarah zasu je kwalliya, kuma kin san ita first come first serve take yi, zata iya miki ni tawa tace sai ta musu tukunna ta b'ata mana tsari."
"Toh Allah ya kaimu sai mu tafi tun sha d'aya, me ake ciki da masu ashoken?"
"Gobe zanje in karb'o insha Allah, don sun kirani sunce sun gama, sai dai mai beads ne zai b'ata min rai da alama, don jiya sai masifa yake wai an bashi a k'urarren lokaci."
"Kiji sai kace ba biyansa za'ayi ba, shi kad'ai ne ya iya, in kinje bai gama ba ki bar masa kayansa aje wani wajen, na san ko ya aka k'ara musu kud'i akai da gudu zasu yi wallahi."
"Nima tunanin da nake yi kenan, yawwa ki cewa Rahma mu had'u goben wajen sha biyu, tace zata kai kayanta itama a mata beads d'in."
"Toh shikenan, in mun fito saloon sai ku had'u kawai, don wajen goma dama nake tunanin mu fita."
"Amma dai Sa'adha ba mai zaki sawa kanki ba koh?"
"Wallahi da nayi niyya amma Aunty nafisa ta hanani, steaming kawai zanyi."
"Ai gwara, in ba haka ba b'ata gashinki zaki yi, duk laushinsa me zaki k'ara akai."
"Toh kar dai ki manta gobe duk ki d'ebo kayanki, dazu na k'ara kiran umma (maman Aminar) tace da kwana biyu da uku ai duk d'aya ne."
"Eh nima dazu ta fad'a min, zan d'uro akwatuna na a motar Sani, da daddare ya kawo min in na gama zagayena a gari."
"Toh shikenan sai goben."
Tana kashe wayar Aunty maryama ta shigo da kofi a hannu, Nanne taji ranta ya b'aci a lokaci guda, d'azu har tana murna cewa sun manta ashe yana tafe, kusan sati biyu kenan ana d'ura mata jik'e-jik'en da ita ba amfaninsu take gani ba.
Ance na gyaran jiki ne, bayan na gidan matar da kusan satinta biyu tana zuwa sai jiya