Showing 63001 words to 66000 words out of 113985 words
hasken dake nuna cewar gabad'aya duk wani hoto na gidan ya riga ya baiyana ga Naani, ta riga ta ga komai a can wajenta, sai dai abinda bai tabbatar ba shine in har ta shafi jikin sa'adha, zata iya yin komai ta gama cikin abinda baifi minti biyu bama amma in har hakan ne ba lallai yazo ya sami Sa'adha a yadda take yanzu ba.
"Na shirya, ina zamu je?"
Ya juya ya kalleta, ta saka wata doguwar riga ta atamfa mai kyau da mayafinta sky blue, gloss d'in da ta saka a bakinta mai kyalli ya taimaka wajen haska manyan kyan fuskarta, tana kallonsa da idanunta so innocent masu d'auke da tsantsar sonsa. Ya Allah! taya zai iya bari a cutar da wannan halittar ta dalilinsa.
Har ta bishi cikin mota suka hau titi suka bar gidan, baice mata komai ba itama ka bata k'ara tambaya ba, don ko maigadi baiyi tambaya akan yadda ya shigo gidan d'azu ba, watakila fuskarsa ta nuna musu alamun rashin son magana a lokacin.
"Da ka shigo falo d'azu kaga wani abu?"
Sa'adha ta katse shirun motar sanda suka hau kan main titi, a lokaci d'aya ya d'auke idonsa daga kan titin ya kalleta.
"Wani abu me?" zuciyarsa cike take da fatan amsarta ta zama sab'anin tunaninsa. ilai kuwa!
"Wani abu ne kamar k'adangare kamar tsaka ya mak'ale a jikin taga muka yita korarsa ni dasu Rahma yak'i tafiya."
Yaji zuciyarsa ta fad'a can k'arshen k'irjinsa, kamar ka cilla katon dutse cikin rijiya mai zurfi kana kallon tafiyarsa har lokacin da zai daki ruwan ya nutse, abinda suka gani ba k'adangare bane balle tsaka, d'aya daga cikin hakiman Naani ne, kuma in har sunzo gidan tun kafin tafiyar su Rahma kenan sun dad'e kenan. Dole ne akwai wani abu da ya sami Sa'adha wanda daga shi har ita basu sani ba.
"Ina zamu je?" Muryarta a hankali ta k'ara tambaya, ba tare da tunanin komai ba ya bata amsa.
"Asibiti."
Can d'in suka nufa, don in har bashi da tabass d'in abinda ya faru, dole neya sami mafita a yanzu, Sa'adha bil'adama ce, kuma jikinta irin na mutane ne, don haka in har wani abu ya canja a jikinta, asibiti zasu iya ganewa duk da ya san cewa baza su tab'a iya gano musabbabin abinda ya sameta d'in ba.
"Asibiti? waye bashi da lafiya? na fad'a maka ba abinda ya sameni..."
"Shshshsh...."
Yayi saurin katseta a k'asan numfashinsa ba tare da ya d'auke idonsa daga titi ba. Allah ya sani baya son magana a lokacin don abubuwa ne da yawa ke tarawa da d'ebewa a cikin zuciyarsa, sai akayi sa'a itama ta fahimci hakan bata k'ara magana ba.
Wani private hospital ya kaita, irin k'ananan asibitocin nan masu jiran suci kud'in patients. Yace a mata general check-up na komai da komai a jikinta, aka yanka masa kud'i ya biya, sannan suka shiga da ita.
Ya samu waje a waiting area d'in da ba kowa ya zauna jira, a lokacin ne jaamil ya turo glass door d'in ya shigo cikin siffar wannan matashin.
Imran bai ko d'ago da kansa ba har ya zauna a kusa da shi, jikinsa ya riga ya bashi cewa d'an uwansa ne wanda ba mutum ba. Ransa ya k'ara b'aci akan wanda yake a da, bai taba jin haushin jaamil kamar yanzu ba. Don me yasa zai tafi ya cigaba da abubuwa ba tare da saninsa ba, me yasa har Naani ta dawo bai sanar dashi ba? ta yaya ma ta dawo? a yadda lissafinsu yake ai har yanzu suna da kusan watanni biyu a gaba.
"Me ya same ta?" jaamil ya tambaya shima ba tare da ya kalle shi ba.
Bai ko nuna alamun yaji shi balle yayi niyyar bashi amsa, yana zaune perfectly still, ya dunk'ule yatsunsa na hannu d'aya akan bakinsa, kamar yadda dutse ke zama stiff a waje d'aya babu ko alamun fitar numfashi a tare dashi.
"Na san laifina kake gani a yanzu yarima, amma dan Allah ka saurare ni, ka san ba zanyi komai don na b'ata maka rai ba."
Imran bashi da niyyar magana saboda ya cigaba da cewa.
"Ranar da na koma muzaffar, ranar bwama ta same ni da zancen cewa sun sami labari Naani zata fito a daren, ban yarda da zancenta saboda a yadda Ma'amun ya shaida min lokacin dawowarta bai yi ba. Sai dai abinda nima ya bani mamaki shine a wannan daren Naani ta dawo d'in kuma ban sami ganinta ba har kwanaki biyu, saboda a washegari ta zauna da mukkarrabanta kan matsalolin da suka faru bayan bata nan, saboda haka sai a rana ta biyu na same ta.
Tun kafin in fad'a mata komai yarima ta riga ta san zancen da zan gaya mata, ta riga taga komai ta san dukkan abinda muka aikata, sannan ta shaida min cewa abinda muka yi ba laifi bane, sai dai nayi garajen yanke hukuncin cewa ka aure ta, tace da ka cigaba da zuwa duk sanda ciwon ya tashi kana kwantar dashi da hakan yafi, amma na fada mata cewa kana loosing k'arfi ne da yawa duk sanda kayi hakan kuma baka iya maida hankali akan abinda ke gabanmu.
Saboda haka tace min zata cire ruhin daga jikinta sannan mu san hanyar da zaka rabu da ita ba tare da bil'adama sunyi wani tunanin ba a cikin abinda bai kai wata daya ba. Don tace lokacin da take jira yana k'aratowa kuma har yanzu bamu cimma manufar ba.
Naso sanar da kai hakan a washegari amma sai ciwon bwama ya sake tashi saboda haka ban sami kaina ba sai a yau da Naani ta sake kirana, nayi directing haskenta zuwa gidan da kuke.
Amma banyi tunanin cewa raba jikinta da ruhin zai iya tab'a matsalarta ba yarima, saboda ni shaida ne akan wahalar da nasha kafin na iya juya zuciyar mahaifinta zuwa son yi mata aure yanzu, naga irin tarin k'aunar da iyayenta da 'yan uwanta ke mata, ba zanso ace cikin sati d'aya kawai mun yi mata lahani ba.
Sai dai tunda har an cire...."
"Ba abinda aka cire."
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
41
(¡î_¡î)
"....Amma banyi tunanin cewa raba jikinta da ruhin zai iya tab'a matsalarta ba yarima, saboda ni shaida ne akan wahalar da nasha kafin na iya juya zuciyar mahaifinta zuwa son yi mata aure yanzu, naga irin tarin k'aunar da iyayenta da 'yan uwanta ke mata, ba zanso ace cikin sati d'aya kawai mun yi mata lahani ba.
Sai dai tunda har an cire...."
"Ba abinda aka cire."
Muryar Imran ta katse shi cikin kaushi. Ya juyo ya kalle shi har yanzu yana zaune so stiff ha tare alamar motsi ba, fuskarsa fayau take babu wani yanayin da zaka iya tsinta a ciki.
"Kamar yaya? Na tabbatar...
"Na sani..." Imran d'in ya sake katse shi.
"...hasken yaje har gidan, amma ba abinda ya faru." jaamil ya cigaba kallonsa mamaki na nunawa akan fuskarsa ko kuma rashin yarda ne?
"Amma ta yaya toh..."
"Nima ban sani ba."
Dukkaninsu suka yi shiru na wani lokaci kafin jaamil ya sake juyowa ya tambaye shi.
"Toh me kake yi anan?"
"Bugun zuciyarta ne baya bugawa daidai, I wanted to be sure saboda in nemo me ya same ta."
"Look yarima, na san cewa a idon mutane yanzu yarinyar nan matarka ce, amma ya kamata ka dinga tunawa kanka matsayinta a gurinka, matsayin da nan da wani lokaci zai shafe, saboda haka bai kamata ka d'auki lamarinta da girma haka ba, ni na zata wani abu ya sameta ne da na ganka anan, amma canjawar bugun zuciyarta kawai shi zai sa ka rud'e da tunanin zaka tafi neman me ya sameta?
Ka manta da abinda yake gabanmu ne? ko ka manta rantsuwar da ka min na cewa ba son yarinyar nan kake ba kuma intrest d'in da kake dashi akanta ya riga ya tafi, ita kanta Naani da wannan kalaman naka ta dogara bata yi fushi damu akan abinda muka yi ba, ta yarda cewa tunda har baka son yarinyar, rabuwarku ba zata sa ka kasa cigaba da abinda muka fara ba...amma yanzu canjawar bugun zuciyarta kad'ai yasa ka a wannan halin me zai faru kuma ranar da ka rabu da ita?"
"So, wannan shine jaamil d'in?"
Muryar Nanne tasa kowannensu ya d'ago da kansa cikin wani irin sauri suka kalleta, tana tsaye d'an taku kad'an daga gabansu tayi folding hannayenta a k'irji. A lokaci d'aya Imran ya mik'e yaje kusa da ita.
"Me suka ce?"
Ta d'an kalle shi ta gefen ido amma hankalinta na kan jaamil wanda ya sandare a wajen da tsananin mamakin yadda akayi ta sanshi, ta san sunansa...for real? kenan Allah kad'ai ya san adadin sauran abubuwan da Imran ya fad'a mata, dole ne ya damu da lafiyarta ashe. His sharing a part of him with her!
"Allaura biyar fa aka min, kuma a hannu d'aya wai duk test ne."
Muryarta mai dad'i ta fad'a tana nunawa Imran hannunta. Jaamil yaji wani abu mai kama da tausayinta a cikin zuciyarsa, tana cikin wani sirad'i mai had'ari amma bata sani ba. Her voice was innocent!
Imran ya murza 'yan yatsun nata yana fad'a mata wani abu da bai maida hankali yaji ba, sannan yayi kissing saman goshinta, ta ture shi a hankali tana murmushi.
"Naji dadin ganinka Jaamil, ka taimake shi don har na fara tunanin ko bashi da freinds ko d'aya."
Jaamil ya juya ya kalli Imran, da ido yayi masa alamun zaiyi masa bayani daga baya, saboda haka ya kalleta yace.
"Nine da laifi amarya, kamata yayi inzo har gida in gaishe ki amma na d'anyi tafiya ne."
"Tafiya?" Ta juya ta kalli Imran.
"Bai fad'a ba kuma."
Kafin Imran d'in yayi magana wata Nurse ta k'araso tace da Sa'adha likitan da zai fad'a musu result d'in tests d'in na jiranta, tare da Imran suka tafi bayan ta rok'i jaamil akan kar ya tafi. Ba yadda ya iya haka ya zauna har suka fito, daga nan suka koma gida.
Inda sa'adha ta rik'e shi da hira da d'awainiyarta har sai bayan sallar maghriba sannan ya samu ya tafi, Imran na tayi masa dariyar yadda a dole yau yaci abincin da Sa'adha ta tarkata masa kala-kala, tun yana iya ci har sai da ya fito k'iri-k'iri ya gaya mata ya k'oshi sannan ta daina kawo layin cimar da bai tab'a ci ba kala-kala.
Imran ya gaya masa cewa ta tambaye shi su waye freinds d'insa ne shi kuma ya rasa sanda bakinsa ya furta mata sunansa, amma ya tabbatar masa bayan hakan babu wani abu nasa data sani.
Bayan jaamil ya tafi, ya taya ta suka yi tarin wanke-wanken data tara, zuciyarsa cike da farin cikin irin karb'ar da ta yiwa jaamil, yaji dama yana da wasu 'yan uwan da zasu taya shi ganin kyautatawar matarsa, saboda itama tana masa tambayoyin da suka shafi 'yan uwansa amma bata cika matsawa sosai ba.
Zuciyarta a kullum tana danganta shine da abubuwa masu kyau kawai, alhalin shi d'in akasin hakan ne a wajenta.
Ya tuno bayanin likitan nan da yake gaya musu cewar komai a jikinta lafiya k'alau yake, kawai bugun zuciyarta ne ya ragu kuma shima 'yan dalilan dake sashi ba masu k'arfi bane. Hankalinsa ya kwanta a lokacin amma tunanin abinda zai faru nan gaba kuma yazo ya rugurza komai.
Don kamar yadda jaamil ya fad'a masa ne kafin ya tafi, rashin jin komai da suka yi daga wajen Naani ba lafiya bane, dole akwai wani dalilin da har haskenta ya shigo gidan amma bai iya tab'a Sa'adha ba, don haka dole suyi tsammanin jiran koma meye a yanzu.
"What's with d'ankwalin kanki yau?"
Ya tambayeta da daddare lokacin da suke zaune a falo, ya d'auko system d'insa yana k'arasa wani kwantan aikinsa dake ciki, ita kuma tana gefensa tana b'are tulin maggin da take tarawa a cikin wata jar, idonta na kan tv tana kallon wani tsohon indian film da wata channel ke nunawa.
Ta kai hannu ta tab'a d'ankwalin kamar tana so ta tabbatar in yana nan d'in.
"Aunty maryamah tace in daina zama ba d'ankwali."
Ya juyo ya kalleta. "Saboda me."
Tayi shiru kamar ba zata fad'a ba sannan ta kalle shi tace.
"Wai saboda aljanu zasu iya shiga jikina."
Yadda tayi maganar ya bashi dariya kamar itama bata yarda da abinda ta fad'a ba, yayi murmushi a k'asan numfashinsa sannan ya jawota jikinsa.
"Aljanu kike tsoro?"
Ta girgiza kanta.
"Su suke fad'a dai, bana fad'a maka wasu malamai sunce har bak'ak'en aljanu ne wai suke son shiga jikina ba."
Har yanzu da murmushin a fuskarsa yace.
"Duk ki rabu da wannan zancen Noory, in dai har kina tare dani ba aljanin daya isa ya shiga jikinki... babu shi a duniyar nan!"
Ta d'ora idanunta sosai a kansa.
"Ta yaya ka san hakan?"
Ya kai hannunsa a hankali ya cire d'ankwalin sannan ya cusa yatsunsa ya warware bun d'in da tayi da gashinta.
"Saboda su kansu Aljanun suna tsoron irin jinsi na Sa'adha."
Kanta ya d'aure da mamaki.
"Wane irin jinsi ne kai d'in?"
Ya tura kansa gefen wuyanta yana shak'ar dadd'an k'amshin shampoo d'inta kafin ya amsa.
"Jinsina na masu yawan addu'a mana."
Tana jin hakan mamakin fuskarta ya kwance, sannan murmushi ya maye gurbinsa.
*******
K'ARFE BIYU DA RABI.
K'arfe biyu da rabi na daren wannan ranar abinda Imran ke tsammanin jira ya faru!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI"EE
42
Wannan chapter ta k'unshi zallar bayani na abubuwa da yawa da muke son kwancewa daga farkon labarin nan.
(¡î_¡î)
MUZAFFAR!
Ta tsirawa taswirar fuskarta ido ta cikin garai-garai d'in ruwan dake wucewa a gabanta. Watakila ta shafe awanni biyar zaune a wajen koma fiye da hakan, ba zata iya tantancewa ba, don dad'ewarta a wajen ba damuwarta bane, fatanta kawai abinda take zaman jira ya k'araso, ya k'araso gareta ta sashi a idonta ko ta samu nauyin dake zuciyarta ya kauce, wani nauyi daya taru tun tsawon shekara guda data wuce.
Tana zaune ne a bakin wani rafi, ta d'age rigarta kad'an ta zira k'afafunta ciki, sunkuyawar da tayi ta zura hannuta yasa dogon gashinta ya bita cikin ruwan, yana motsawa a hankali tare da gudunsa, sannan daga kowanne gefe na lambun tarin hadimanta ne ke tsaye suna gadinta.
Duwarta ta fara ne tun lokacin da YARIMA ya bar cikin duniyarta da niyyar yiwa Naani wani aiki da har yau bata san mene ne ba, bayani d'aya kawai ta sani wanda ya fad'a mata kafin tafiyarsa na cewar sai tayi hak'urin jure rashinsa don ba zata iya ko jin muryarsa ba daga can inda ya tafi d'in, a lokacin komai zai kasance ne cikin watanni hud'u kawai, amma a yanzu, shekara d'aya itace k'irgen da kowa keyi na tsawon tafiyarsa.
Tayi hak'urin har ya k'are ta sake lalubo wani ta d'ora ya cigaba cinyeta, cinye siffar da take mutuk'ar so a rayuwarta. Idonta ya sake kaiwa kan ruwan, watak'ila da ita bil'adama ce da in ta samu biyan buk'atunta nan gaba kad'an hankalinta ya kwanta da sai jikin ya koma yadda yake, amma abu ne da ta san ba zai tab'a faruwa ba wanda ya tafi ya riga ya tafi kenan!
A tsawon rayuwarta ba abinda take mutuk'ar k'auna irin siffar bil'adama da kuma son shiga cikinsu, amma sai ya zama kamar abubuwa da yawa a rayuwar tata, Naani tayi mata katanga dashi akan dalilin da ta san ba zai rasa nasaba da d'aya tilo da idonta kad'ai ke gani ba. Gata d'aya da tayi mata shine mayar da jikinta da tayi ya koma irin na bil'adaman, wani abu da ita kad'ai ke dashi a duk fad'in nahiyarsu.
Amma duk da haka ta k'udirce a zuciyarta cewa sai ta fanshe duk wata wahala data sha a wajen dukkaninsu, duk wanda keda hannu a cikin bak'in cikin data tashi dashi.
Mussaman shi yariman, wani halitta data tsana fiye da kowa a rayuwarta, ta tsane shi tun lokacin da hankalinta ya iya banbance tarin k'aunar da Naani ke masa akanta, Bata tab'a ganin Uwar dake fifita d'an wani sama da nata ba irin tata uwar, ita kad'aice 'yarta a duniyar nan, amma hankalinta da tunaninta baya tab'a zama akanta, ita d'in koyaushe tana zuwa ta uku ne a jerin al'amuranta.
YARIMA DA JAAMIL sune sunayen data tsana fiye da komai a rayuwarta, kuma sunayen data yi alkawarin sai ta kawar dasu a duniyar nan, sai ta zama ajalinsu, ta yadda dukkan wani abu da Naani ke shirin mallaka musu zai dawo gareta, ya zama dukkan tanadin da take shirya musu ya k'are akanta, yadda bayan taga hakan itama daga baya ta kashe ta.
Ta dad'e da tsara wannan shirin a cikin kanta, abu d'aya ne ta tsaida faruwarsa har yanzu, shine tafiyar yarima, domin komai zai fara ne bayan ya aureta. Shi yasa a yanzu take zaman jiran wannan nauyin zuciyar tata ya kauce!
"Ranki ya dad'e sak'on ya iso...yarima ya shigo cikin masarauta yanzu."
Wata hadima daya shigo lambun a daidai wannan lokacin ta fad'a kanta a k'asa.
A hankali wani murmushi ya sauka a gefen kumatun SAREEFA, wani murmushin da tayi tanadinsa tsawon shekara guda!
Lokacin data k'arasa cikin masarauta, komai ya canja...a jiya ne kad'ai Naani ta sanar da zuwansa amma a jiya kad'ai aka canja fasalin komai gabad'aya.
K'erarren ginin masarautar yana tsaye kyam! cikin wata irin k'awa da ado na alfarma, an canja launin kalarsa zuwa kalar rawaya da fari, yanayin lokacin yamma ne mai cike da lumshi da kuma iska mai dad'i, amma duk da haka tsuntsaye ne birjik! tun daga hanya sunyi rumfa da fuka-fukansu cikin wani tsari mai ban sha'awa, sannan ga tarin halittu nan taf! jinsi kala-kala suna durfafin isowarsa, ko'ina ka juya fuskoki ne cikin farin ciki, ga kuma tashin wani kid'a mai dad'i dake tashi a ko'ina.
Zuciyar Sareefa ta matse ganin irin tarin k'aunar dake fuskokinsu, a dawowarta na k'arshe masarautar, bata samu koda rabin wannan tarbar daga wajen kowa ba, hatta daga Naani kuwa saboda ta tabbata k'awata masarautar ma anyi ne bisa umarninta.
A ranta ta ayyana cewa saura lokacin kad'an duk wannan ikon ya dawo mallakinta, ta tsaida hadimanta daga bin bayanta sannan tabi iskar wajen ta baiyana a cikin masarautar!
*******
Imran na tafe cikin siffar da al'ummar nahiyarsa suka sanshi a matsayin YARIMA, a gefensa jaamil ne shima cikin ainihin tasa siffar suna ratsawa ta cikin tarin halittun da suka yi durfafin ganinsa, kowannensu cike da farin cikin ganinsa bayan wani tsawon lokaci.
Nan d'in shine k'asarsa, mahaifarsa inda jinsinsa da duk wani gatansa yake, kuma ya saba da rayuwa a cikinsa tun zamanin k'uruciyarsa, ya saba da wannan matsayin da ake bashi sannan ya saba da wannan yanayin da jikinsa ke ciki, amma a yanzu ji yake komai ya dawo masa sabo, kamar ansa wani