Showing 87001 words to 90000 words out of 113985 words
fito da tsiron wata k'aunar sab'anin ta Imran, abu d'aya da take ji ba zata iya rayuwa babu shi ba a yanzu ya zama biyu.
K'aunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan k'aunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri ne na son tabbatar da abinda kake so, Allah ya sani a lokacin tana son Babyn cikinta kamar yadda take k'aunar ranta, watakila ma fiye. She wanted him so badly!
Hannun ta yana kan cikinta kuma zuciyarta nata sak'e-saken abinda zai faru nan gaba sanda taji hannun Imran ya dafa saman nata.
"Ciwon yake sake yi?" Muryarsa ta fito da alamun tsananin damuwar da yake son kwantarwa.
Ta girgiza kanta da sauri.
"Bana jin komai."
Ta amsa idanunta na kallonsa cike da mamaki, fuskarsa _was hard!_ babu wani emotion da zata iya tsinta a ciki, ita tayi zaton ganin farin ciki ko yaya ne a fuskarsa... for crying out loud ba'ayi ko awa d'aya ba fa da gaya musu sak'on da yafi kowanne muhimmanci a rayuwarsu, amma tun wannan d'an guntun murmushin da yayi wa likitan babu wata sigar farin ciki data gani tare dashi. Ta juyo da hannunta ta rik'o nasan tana cigaba da kallonsa, Kafin tayi magana ya rigata.
"Ki kwantar da hankaliki dan Allah Noory, ba abinda zai faru kinji?"
Ba abinda zai faru kamar yaya? itafa bata gane me yake nufi ba, anya kuwa ya fahimci ma me aka ce? ciki fa akace tana dashi, cikin dake shirin kawo d'a a tsakaninsu, ita ta zata daga fitar likitan zai k'ank'ameta ne saboda farin ciki ko ya d'auke ta ne yayi ta juyi da ita a cikin d'akin suna godewa Allah.
"Me kake nufi? Ba abinda zai faru a ina?" Ta yanke shawarar tambaya.
"Ba abinda zai same ki insha Allah ba abinda zan bari ya same ki, Nayi kuskure tun farko wanda ba zai gyaru ba, amma nayi miki rantsuwa ban taba tunanin cewa haka zai iya faruwa ba, da tuntuni na kare hakan...saboda waninmu bai taba shigowa cikin mutane ba, irin haka bata taba faruwa ba."
Kanta ya d'aure ta kasa fahimtar komai a cikin zancensa.
"Na kira jaamil yanzu munyi magana, akwai mahaifiyarsa bwama itama tana da jiki irin na mutane saboda yawan rashin lafiyarta da take zuwa kasashe daban-daban neman magani, zasu zo tare a cire wannan abun Noory insha Allah, tun kafin ya cutar dake."
Abu? d'an da zata haifa shine abu?
Imran baya son Babynsu kenan? Baya son abinda zata haifa? Me yake nufi? Ta yaya d'an mitsitsin halitta zai cutar da ita? A lokaci d'aya tunanin dake cikin kanta ya canja, hoton da take gani Imran d'auke da ita yana murna ya juye zuwa shi da jaamil suna k'ok'arin kashe d'anta, d'an kyakkyawan Babynta, kunnenta ya karad'e da k'arar kukansa.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! tunaninta ya hargitse a lokaci d'aya, ba zata taba yarda ba, ba wanda zai rabata da d'an dake cikinta, ba zata taba bari a cutar dashi ba, ko waye kuwa, ko shi Imran d'in ne kansa!
Taji sanda ya zame hannunsa daga cikin nata ya mik'e tsaye yana amsa wata wayar, cikin yare irin na d'azu, ta tabbata jaamil d'in ne suke sake tattauna abinda ba zai tab'a kasancewa ba.
Juyowar da Imran zaiyi cikin wayar ya kula da hawayen da take yi, Ya salam! ba dai wani ciwon take sake ji bada sauri ya kashe wayar ya dawo gabanta.
"Sa'adha me ya faru?"
"Ayunie so kake ka kashe Babyn mu?" muryarta ta fito cikin rawa.
Ya d'an tsuke ido yana kallonta, Baby? tunanin da take kenan? tunani take abinda ke cikinta Baby ne?
"Sa'adha we don't know what's in there...na gaya miki irin haka bai tab'a faruwa da irinmu ba, sanda nake wannan kuskuren ban taba sanin cewa ciki zai iya shiga jikinki ba, so for all we know a yanzu abinda ke jikinki zai iya cutar dake."
Ta girgiza kanta da sauri.
"Ta yaya zai cutar dani wai? ta yaya zai cuce..."
"Kin manta ni ba mutum bane?" Yayi saurin katseta, ganin alamun bata fahimce shi ba ko kad'an.
A lokacin d'aya fuskarta ta koma blank! idanunta suka zare kamar yaune rana ta farko data ji hakan, don har ga Allah ita mantawa take Imran ba mutum bane tunda bata tab'a ganin wata alamar hakan a tare dashi komai nasa irin na mutane ne sak! ba wata tangard'a.
"Kin manta waye ni? ni ba mutum bane Sa'adha, saboda haka bana tunanin abinda ke cikinki zai iya zama mutum, zaki iya haifarsa da wata jirkitattiyar halittar or worse yazo a irin siffar mu...
Look bama wannan ba, ba zaki iya ba, jikin mutane da namu ba iri d'aya bane, halittarmu tana da k'arfin possesing abubuwa da yawa while mutane are weak, you're not strong for this Noory!"
Duk wannan bayanin da Imran yake yi, kwakwalwar Nanne ba fahimta take yi ba, abu d'aya kawai take gane shine Imran baya son Babynsu saboda baya so ko kad'an a samu wata alama da zata tab'a nuna cewa shi ba mutum bane, amma ita bata damu da wannan ba, in har Imran ya kasance k'addararta toh zata rik'i wannan ma a matsayin wata k'addarar tata, zata yi k'ok'ari da dukkan iyawarta ta raini Babynta, tana ji a jikinta cewa hakan wani alkhairi ne nata... So atleast she would try!
"Dan Allah ki fahimce ni." Ya fad'a yana sake rik'o hannunta.
Ta tsaida idonta sosai akansa sannan tace.
"Na fahimceka Ulfat, kuma nima ina son ka fahimce ni, ina son ka fahimci cewa ba zan tab'a iya kashe shi ba."
A lokaci d'aya kalar idanunsa suka yi duhu sosai alamun b'acin rai.
"Sa'adha, ba lallai irin Babyn da kike tunani bane a cikinki, for one second ki bud'e kwakwalwarki ki gane me nake nufi, abin nan zai cutar dake ta irin hanyar da baki sani ba, it's not some pretty Babyn da kike tunani."
Itama nata ran ya b'aci, ta d'age girarta d'aya.
"Zamu gani toh."
Tana fad'in haka ta mik'e tayi hanyar d'aki, ba tare da wani tunani ba Imran ya b'ace cikin iska ya baiyana a gabanta, a lokacin da bugun zuciyarta yayi wani irin bugawa cikin kunnensa, a lokacin yayi dana sanin abinda yayi, don ba sai ta fad'a masa ba ta tsorata sosai da hakan, amma tunanin zancen da suke yi ya danne wanda ke cewa ya bata hak'uri.
"Me yasa ba zaki gane abinda nake nufi bane? i can't stand to see you in pain,_Sa'adha abin nan zai iya kashe ki!"
Nanne ta had'iye tsoron dake kanta, yanzu ta k'ara fahimtar wani abin, yana tunanin zata iya mutuwa shi yasa ya damu kansa haka, baya son ya rasa ta, watakila sunyi daidai kenan a haka, itama tana tsananin son abinda ke cikinta baza taba iya bari ta rasa shi ba, saboda haka tace.
"Ba zai kashe ni ba Imran, I can do this."
Tana fadin haka ta k'arasa cikin d'aki ta rufo k'ofar, yaji sanda ta murd'a lock d'in ta k'ulle alamun bata buk'atar company d'insa, amma ba wannan ne ya dame shi ba, the fact that ta kira shi da Imran, wani abu ne da ya kwana da sanin cewa duk sanda ta kira sunansa toh ko tana cikin rud'ani ko kuma fushi, wanda a yanzu ya tabbata fushin take ji, A hankali ya zame k'asa ya zauna akan dandaryar tiles d'in, bayansa ya jingina da bangon corridor d'in.
Ya kai hannunsa don ya share gumin daya fito masa, amma sai yatsunsa suka nutse kamar zasu d'ago da fatarsa, duhun kwayar idonsa ya sake haskawa cikin sockets d'insu sannan bakinsa ya bud'e kamar zai yi ihu amma ba abinda ya fito.
Sa'adha fushi take dashi? ta yaya zaiyi mata bayanin cewa ba zata iya d'aukar abinda ke cikinta ba, ta yaya zai zai fad'a mata ta fahimce shi su gyara kuskuren da yayi. Me yasa ne abubuwa basa tab'a zama masa daidai game da ita? me yasa baya iya controlling zuciyarsa akanta? Baya tab'a behaving rules d'in da suka dace... he's just being himself around her! Saboda tana sawa yaji shi complete yaji shima wani ne mai iko, don tunda yake bai tab'a jin yana son abu kamar yadda yake son Sa'adha ba.
Yana zaune a wajen bai motsa ba har lokacin da alarm d'in wayarsa ya buga k'arfe d'aya lokacin sallar Azahar, bai san ya akayi taji alarm d'in ba don bayan wani lokaci yaji karar zubar ruwa daga can toilet d'in d'akin hakan ya tabbatar masa yau jam'in da suke yi ba zai samu ba kenan, saboda haka ya fita can balcony yayi tasa alwalar sannan ya shigo yayi sallah, sai dai har wajen k'arfe uku Sa'adha bata fito daga cikin d'akin nan ba shi kuma yayi alqawarin ba zai takura mata ba, zai barta tayi dukkan irin tunanin cikin kanta wataqila hakan zaiyi knocking sense cikin kanta ta fahimci abinda yake nufi.
Yaji gabad'aya ya takura gidan ya masa wani iri, duniyar ta tsaya masa cak! sannan zuciyarsa ta matse na rashin sanin ainihin tunanin da take game dashi. Ya kasa yin komai, Jaamil ya sake kiransa fiye da sau goma amma yana kallo ya kasa d'auka.
There had never been something like you and sa'adha before, dole sai kayi hankali da kasancewarku tare... Banbancin halittarku shi zai iya jawo wata matsalar a zamanku, akwai abubuwa da yawa da sai kayi taka tsan-tsan game dasu, strong emotion d'inka zai iya kawo wani abun yarima.
Ya tuno maganganun da jaamil ya fad'a masa ana gobe d'aurin aurensa da Sa'adha, gashi bai kiyaye komai a ciki ba.
Sai bayan La'asar sannan Nanne ta fito daga cikin d'akin, ta same shi daga jikin counter saboda haka ta tsaya daga nan, Zuciyarta tayi wani irin nauyi sanda ya d'ago ya kalleta, da lumsasun idanunsa dake cike taf da damuwa.
Imran ya gyara zamansa sosai yana kallonta, tayi wanka ta canja kayanta zuwa wata 'yar pink riga mai kyau iya gwiwa, ya tuna sanda ya hango rigar daga can sama bayan ya gama d'ebo sauran yazo biyan kudi, haka kurum tayi masa kyau yace a d'auko ta a had'a da ita. k'afarta ta dama a tsaye take, ta hagu kuma akan babban d'an yatsanta tana juyawa, kamar abinda yaro yake yi in zai tambayi abu yana kuma shakka.
"Ina so in tambayeka wani abu."
Ta yanke shawarar magana lokacin da taga bashi da niyyar barin kallonta.
"Ina jinki habibty." Ya fada shima daga inda yake zaune.
"I want to go home, ina son inje gida."
Ya gyad'a kansa a take.
"Zan duba inda flight gobe zan mana booking."
Ta gyad'a kanta a hankali, sannan ta juya ta koma ciki, Imran yabi bayanta da kallo yana jin kamar ya mik'a hannunsa ya jawo ta, _this is toture!_ bata san yadda rashinta a d'an lokacin nan ke azabatar dashi ba. Ya kifa kansa akan counter lokacin da itama ta buga k'ofar d'akin ta rufo.
Wasa-wasa har sallar isha Nanne bata da alamun fitowa daga d'akin, saboda haka bayan ya idar da salkar isha ya hada mata tea mai kauri sannan ya d'ebi wani abincin da wasu snacks d'in ya nufi d'akin, yayi niyyar b'alla k'ofar amma ga mamakinsa ya turawa ya ganta a bud'e. Ya shiga ya kunna fitilar dake kashe, a lokaci d'aya ya hango ta lullub'e daga tsakiyar gadon ta takure kanta.
Ya ajiye kayan da sauri ya isa gareta.
"Sa'adha me ya sameki? Ciwo kike ji?"
Ta d'ago da jikakkun idanunta ta kalle shi.
"Sai yanzu kaga damar zuwa? Ayunie tun d'azu nake jiranka."
Bai san sanda ya janyo ta gabad'aya jikinsa ya rungume ta ba.
"I'm so sorry Noory, na zata kina buqatar lokaci ne ke kadai."
"Wane lokacin nake buqata ni kad'ai ulfat? wane lokacin nake buqata da babu kai?"
Ya sake rungumeta yana shafa bayanta.
"Kiyi hakuri, na zata fushi kike dani."
Ta dunk'ule hannunta ta shiga dukan kirjinsa.
"Fushi nake yi da kai mana, fushi nake yi da kai sosai, kuma tun d'azu nake jiran kazo ka bani hak'uri..."
"Toh ai kin k'ulle k'ofarki."
"Ba ka iya b'allawa ba, jiya ba ka b'alla k'ofar toilet ba, ba sai ka b'alla ka shigo ba."
Ya d'ago da fukarta daga jikinsa ya kalle ta.
"Toh Noory sai in ta b'alla musu k'ofofi?"
Ta sake kai masa wani dunk'ulallen naushi, shi kuma ya k'ara rungumeta a jikinsa!
A can cikin rigarsa ya jiyo muryarta.
"Ba zan mutu ba Ayunie, I will keep my heart beating, inada k'arfin da zan iya rik'e Babynmu insha Allah, ina son shi Ulfat...ina son shi sosai!"
n
So we just had our first fight!
Nanne da Ayuninta sunyi fad'a...!??
Me kuke tunani game da abinda Nanne ta fad'a a k'arshe? Kuna ganin Imran zai bar mata Babyn?...ko kuma ince littlle monster kamar yadda Imran yake tunani?_??
****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
53
So I tynk ban tab'a dedicating chapter to kowa ba, amma yau i would lyk to dedicate dix chapter to all my university fans... wad'anda makaranta ta b'oye min su bana jin comments kwana biyu...I feel you guys Allah ya taimaka muku!??
Sauran readers d'ina kuma na gaishe ku, hope kuna cikin farin ciki, if not Allah sa kuji alert!??
(_)
"Zamu iya shiga yanzu."
Jaamil ya fad'a yana kallon mahaifiyarsa, suna tsaye daga balcony main k'ofar da zata shigar dasu cikin gidan Imran. A lokacin zuwansu kenan daga can Muzzaffar cikin tafiyar da suka kusan kwana suna yi saboda rashin lafiyar jikinta sosai.
Daga lokacin da ya zauna ya shaida mata dukkan abinda ya faru da Yarima da kuma irin taimakonta da suke nema daga sannan hankalinta ya tashi ta rasa nutsuwarta sai da tasa suka taho a lokacin.
Ya riga ya sani a koyaushe mahaifiyarsa tana d'aukan al'amarin yarima da daraja, duk sanda wani abu nasa ya taso zata bada dukkan kulawar da zata iya, don har cikin zuciyarta ta amince shi d'a ne a wajen 'yar uwarta NAANI, ta yarda da hakan tun daga ranar da Naani ta d'auko shi ta kawo shi cikin masarautar, zai iya cewa mahaifiyarsa itace sanadin abokantakarsa da yarima, don a farkon zuwan yariman basa shiri ko kad'an, sai da taimakonta da kuma yadda take jawo shi a jiki sannan suka zo suka fahimci juna.
Baya manta ranar da Naani ta kira mahaifiyarsa tayi ta mata fad'a akan yadda take kokarin janye shi daga wajenta, a cewarta tana masa abubuwan da ita bata yi masa saboda haka ta mata gargadin shiga harkarsa, a wannan ranar ya tabbatar da cewa Naani zata iya b'atawa da kowa akan yarima, daga wannan ranar kuma alaqar mahaifiyarsa da yariman ta nesanta, amma bata tab'a gaza bashi taimakonta ba a duk lokacin da zata iya, saboda haka ya san ba abin mamaki bane don ta rikice jin irin matsalar da yake ciki a yanzu, matsalar da ko Naani bata san da ita ba.
Kamar yadda shima baiyi mamaki ba lokacin da yariman ya kira shi ya shaida masa halin da Sa'adha take ciki, don tun daga ranar daya same su a asibitin nan, kuma yaje har gidansu yaga irin rayuwar da suke shimfid'iwa, zuciyarsa ta gaya masa cewa Imran ya bar cikinsu har abada, banda b'arin ruhinsa zuciyarsa ma tana tare da ita kuma baya jin akwai wani dalili a duniyar nan da zai iya sawa ya rabu da ita.
"Ka tabbata da yardarta zan ganta? ka san fa ban tab'a had'uwa da bil'adaman daya san ainihin koni wacece ba."
Jaamil ya kamo hannayenta duka biyun.
"Bwama, ni ban san mutane ba kuma ban san halaiyarsu ba, amma na san cewa yarinyar nan tana d'aya daga cikin d'aid'aikun mutanen da ba a koina ake samunsu ba, tana da kyakkyawar zuciya, k'arfin hali da kuma rashin tsoro, ta amince da yarima ta bashi yardarta duk da sanin da tayi na waye shi, sannan a yanzu tana shirin saudakar da rayuwarta saboda wani abu nasa, me yasa kike tunanin ganinki zai girgiza zuciyarta?"
Bwama ta gyad'a kanta a hankali cike da fahimta sannan jaamil ya saki d'aya hannunta ya bud'e k'ofar dake gabansu.
"Na yarda da ita Noory, ba abinda zata miki."
Ya tsinkayi muryar Imran cikin whisper lokacin da suke taka corridor d'in da zai sada su da falon gidan.
"I trust you too Ulfat!"
Soft muryarta ta fito bayan tasa, a hankali kamar mai rad'a, ya runtse idonsa kad'an da tunanin yadda take bawa Imran wata irin makauniyar yarda da baiyi deserving ba.
A lokacin da suka yi kwanar cikin main falon, a lokacin idanun bwama suka hango mata Sa'adha tsaye daga jikin Imran d'in, hancinta ya shak'o mata k'amshinta a take.
The warm clean k'amshin bil'adama!
Kusan tana b'oye a jikinsa sanye da doguwar rigar abaya bak'a, ta yafa jan mayafi d'an k'arami a kanta. A cikin sakan d'aya bata ga komai ba sai ainihin kammanin bil'adama kawai, fatar ta mai kyau mai taushi, sannan idonta manya chocolate colour...lips d'inta a tsuke kamar tana tamke wani abin.
A sannan ne kuma bwama ta lura da kammaninta sosai, kammanin dake can k'asa suna fara rarake ta a hankali, so slowly yadda idanun mutane ba zai iya gani ba...k'asan idanunta sun fara rami suna zurmawa k'asa, fatarta ta wajen kuncinta ta tattare kamar zata tsinke, gashinta daya fito ta saman mayafin ya fara dunk'ulewa sannan akwai alamun yatsunta da k'ugunta sun fara ramewa.
Hakan ya tabbatar mata cewa duk abinda ke cikin Sa'adha a lokacin ya fara janye karfin jikinta ne yana gina nasa.
"Barka da zuwa bwama."
Imran ya fad'a cikin yaren hausa, ta fahimci yayi hakan ne don matarsa saboda haka itama ta amsa masa da murmushi.
"Barkanmu yarima, Barkanmu dai!"
Nanne ta kalli Imran da gefen idonta d'aya, da kai ya mata alamar cewa zata iya magana saboda haka ta kalli bwama tace.
"Barka da zuwa Mama."
Ta fad'i hakan ne saboda bata san ma'anar bwama ba, saboda ba zata iya fadar sunanta kai tsaye ba, sai dai kuma hakan yasa bwama jin wata irin kauna da tausayinta, ta ayyana a ranta cewa Nanne nada zuciya mai kyau duk da wannan shine farkon had'uwarsu, amma zuciyarta mai kyau ce tunda har bata iya hasaso mata irin had'arin data ke shirin sa kanta a ciki ba, had'arin dake shirin tauye rayuwarta, saboda haka maimakon ta amsa sai ta k'arasa da sauri ta fito da ita daga jikin Imran sannan ta rungume ta.
A lokacin Imran yaga cewar ya dace su basu guri, saboda haka ya murza yatsunta da basu gama fita daga cikin nasa ba a hankali sannan yayi wa jaamil alama da zasu iya fita.
Ta saman kafad'un bwama Nanne tabi bayansa da kallo tana jin zuciyarta wani iri, a yanzu ta riga ta saba da communication d'insa ta hannu saboda haka