Showing 60001 words to 63000 words out of 113985 words

Chapter 21 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28480

al'amuransa d'ari bisa d'ari.

Shi yasa a kullum ya d'aga ido ya kalleta, ya kalli irin tarin yardar dake cikin idanunta, sai yaji rauni ya kama shi, yaji kamar ya zaunar da ita ya gaya mata gaskiyar dake b'oye a zuciyarsa, ya amsa tambayoyinta da dukkan gaskiyarsa, ba wai don abin ya daina damunsa ba ko don ya samu yardarta, A'ah sai don kawai yana son ta sanshi, ta san shi d'in na gaskiya. his real personality! kuma yana fatan in ta san hakan, wad'annan chocolate eyes d'in nata su cigaba da kallonsa da trust d'in da take bashi a yanzu.

Sai dai wani abu ne daya kwana ya tashi da sanin cewa duk yadda ta kai ga sonsa, kwakwalwarta ba zata tab'a iya karb'ar irin sirrikansa ba. Wani abu ne beyond expectation d'in tunanin d'an adam!

Don shi d'in wata halitta ce daban, d'aya daga cikin d'imbin halittun ubangiji da babu saninsu a wajen mutane, shi yasa ranar da yaga wadannan marks d'in a jikinta, ya la'anci kansa fiye da sau d'ari akan kasa fighting emotion d'insa da yayi har ya bari yayi kissing d'inta so deep haka, ya k'ara tabbatarwa kansa cewa da gaske confidence d'in da yake dashi a da ya juye zuwa luck yanzu, baya tab'a iya controlling zuciyarsa indai akan Sa'adha ne, abinda ya jawo masa komai tun farko.

Shi yasa tun daga ranar yasa a ransa cewa zai dage da dukkan iya k'ok'arinsa kar ya sake maimata irin mistake d'in ya nemi wata hanyar da zata d'auke hankalinsa daga kan jikinta ba tare da ita d'in ta fahimci komai ba, saboda haka a duk sanda yake tare da ita, sai yayi k'ok'arin maida full attention d'insa kan gashinta...sassalkan gashinta mai santsi da tsawo dake sashi manta duk wani shirmen cikin kansa. And it worked!

Ya tuno 'yan kad'an d'in tambayoyinta da sauka sashi tunani kafin ya iya bata amsarsu...

"Sanda ban sanka ba, sanda kawai nake ganinka a layinmu, daga baya nazo na daina ganinka, wani wajen ka tafi a lokacin?"

Babu inda naje. ya fad'a a cikin zuciyarsa don ya tuna lokacin sarai! wannan lokacin ne da ya takura kansa ya daina bibiyarta kusan watanni biyu, lokacin daya lura idanunta na iya ganinsa duk da cewa yana zuwa ne a yanayin da mutane basa iya ganinsa...wani abu da har yau bai san dalilinsa ba.

"Na manta lokacin Sa'adha, amma ina tunanin ko na tafi gida ne lokacin hutuna."

Kamar sauran amsoshin da yake bata, ta yarda dashi ba tare da tayi tunanin komai ba.

"Toh wajen wa kake zuwa? har sadiq na tambaya a lokacin yace min bai sanka ba."

"Da gaske? tun a lokacin kin damu dani haka? har kina tambaya a kaina?"

Kumatunta suka yi flushing zuwa red, abinda ke faruwa duk sanda ya fahimci tana jin kunya.

"Kawai na tambayeshi ne..."

"Don't budge please...zuciyata har ta fara tsallen murna, kar kisa ta tsaya dan Allah."

Tayi k'ok'arin fighting murmushin bakinta, his words pleased her! a hankali tace.

"Ina jinka toh, wajen wa kake zuwa?"

"Watakila Sadiq bai gane kwatancen da kika yi masa ba, amma wajen mutanen da kike gani na nake zuwa, akwai wani d'an office d'inmu da muke zuwa tare."

Karya ne, amma sai ta gyad'a kanta alamun ta fahimta.

"Ka tuna ranar da ka shigo gidanmu da daddare?"

"Na tuna Noory, bana tab'a manta duk wata rana da idona ya ganki."

"Me yasa a sanda muka had'u baka min magana ba, sannan da gaske dama kana zuwa wajen ya umar? saboda ni ban taba ganinka ba."

"That's more than one..."

Ya fad'a a k'asan numfashinsa, amma yayi deciding ya bata amsa kai tsaye, don tambayar bata da matsala, dole ne ta san akwai dalili, kuma shima yana da dalilai da yawa da zasu dace da amsarta.

"Na san bakya kula kowa a waje lokacin, na san duk namijin da yayi miki magana a hanya bakya amsawa shi yasa nima banyi wannan gangancin ba, sannan da gaske ne ina zuwa wajen umar amma a ranar kamar yadda na fada miki wajenki nazo ba wajensa ba."

"Toh me yasa kazo bani hak'uri?"

Ya d'an hadi'ye yawu, tayi tambayar ne ba tare da wani tunani ba, amma amsarsa zata iya sa mata wani tunanin, saboda haka yayi deciding sirka zancensa da gaskiya.

"Bayan na koma gida, zuciyata ce ta kasa nutsuwa da tunanin abinda nayi ban kyauta ba, tunda har na tab'a miki magana kuma kin amsa min, kin tuna ranar?"

Tayi murmushi a hankali sannan tace.

"Adduwa, kad'anya, taura, magarya, d'inya da kuma d'ayan mai kwallo da yawa a ciki...."

Yayi murmushi shima.

"Right, wannan ranar...shi yasa nazo na baki hakuri saboda a rayuwata bana tab'a son in zama sillar b'acin ran wani...musamman ma kuma ke."

"Ka kyauta sosai saboda da baka zo ba, bana jin zan iya wani baccin kirki a a ranar."

Zancen ya masa dad'i sosai, yayi dariya a hankali amma kuma mai zurfi har saida jikinsa ya jijjiga tare da nata, tunda tana kwance ne a jikinsa ne wajen karfe sha d'aya na dare, ya murza 'yan yatsunta dake sarke da nasa kafin yace.

"Nagode for ur cocern Noory!"

Daga nan dukkan wata tambayar data biyo baya ta shafi likes and dislikes d'insa ne da take son sani, kuma baya tunanin akwai kalma d'aya da ba ainihin gaskiyarsa ya fad'a ba anan.

*******

"Tunanin me kake yi Imran?"

Muryar ta janyo shi daga duniyar space d'in daya tafi a cikin office d'insa. ya d'ago da kansa a nutse ya kalli Shamsudden dake tsaye a gaban table d'insa.

"Na tabbata baka yi sallama ba shi yasa kake zaton tunani nake yi."

"Amma nayi knocking kuma har na shigo baka jini ba."

Yayi murmushi a gefen kumatunsa kafin yace.

"May be tunanin amaryata nake."

Shamsudden yayi murmushin shima tare d'aga hannayensa sama.

"Afuwan, ai na manta kai d'in sabon ango ne, watakila ko don bamu ga ka d'auki hutu bane."

"Karka damu, Kwanan nan zan d'auka insha Allah."

"Allah ya kaimu, dama kayi baqo ne nazo in gaya maka."

Girarsa ta had'e waje d'aya.

"Baqo? me yasa bai shigo ba toh?"

"Ban sani ba, shigowata kenan malam hamisu masinja yace in taimaka in gaya maka don Dr. Turaki ya aike shi."

Ya gyad'a kansa a hankali.

"Well nagode, bari inje in gani."

Shamsudeen na fita ya rufe file d'in dake gabansa, wanda bai ko yi halfway na signing sababbin arrangement d'in da zasu fara da wasu companies ba.

Ya bud'e drawer gefensa yasa shi a ciki, idanunsa suka gane masa kwalin hadaddiyar wayar da ya siyowa Sa'adha d'azu, murmushi ya sub'uce a kumatunsa hango irin farin cikin da zata yi yau, ya maida drawer sannan ya fita daga office d'in ya nufi hanyar elevator, yana sauka ground floor yaci karo da malam hamisun ya dawo daga aikensa.

"Yawwa yallab'ai wallahi aiken Alhaji ne ya tsaida ni, shi yasa nace da maigidana ya taimaka ya gaya maka."

"Ba komai Baba, a ina yake mai jiran nawa?"

"Yana daga wajen ajiyar motoci ranka ya dade."

Da jin haka Imran ya fahimci waye baqon nasa. Yana isa parking lot d'in ya hango wannan matashin tsaye a jikin wata mota kamar wancan lokacin daya wuce a baya.

"Na san dai sati d'aya ya isa ace ango ya huta, tunda gashi har ya fito aiki."

Muryar jaamil ta shiga kunnensa.

"Kwana bakwai fa jaamil, ka san dole zan neme ka amma kayi zamanka saboda ka san ba ta yadda zanyi na sameka."

Maimakon ya amsa sai yayi murmushi ya kalli wajen yace.

"Abin da mamaki, last time da muka tsaya anan nazo ne in k'ara jaddada maka cewa kar kaje wajen yarinyar nan...yanzu kuma gata a matsayin matarka."

"Sunanta Sa'adha."

"Ko kuma habeebty ko Noory."

Mamaki ya kama Imran a lokaci d'aya.

"You're spying on me?"

"Ba komai ba, kawai irin part d'in da kuke hira a falo, kuke cin abinci tare da kuma in kana wasa da gashinta ko..."

Kafin ya k'arasa Imran ya jefe shi da wayar hannusa, tana k'arasowa ya cafe ta da wani irin sauri irin wanda idanun mutum ba zai iya d'auka ba.

"Ka kwantar da hankalinka yarima, I assure you baka yi wani abu ba daidai ba, ya kamata dama kayi komai yadda zai dace da tunaninta, 'yan mistake d'in kad'an ne kuma I didn't blame you, yarinyar tana da d'auke hankali."

"Ba wannan nake son ji ba, me ya hana ka contacting d'ina har tsawon sati d'aya?"

"Wani dalilin ne yarima, wanda ya shafe naka."

"Wane dalili ne da kai a yanzu da yafi abinda yake gabanmu?"

Maimakon ya amsa sai yace.

"Ya ciwon nata?"

Imran yayi shiru kamar ba zai bashi amsa ba shima kafin yace.

"Kamar yadda ka sani ne ai ba abinda zai faru in har muna tare, yana nan kwance a jikinta."

Jaamil ya gyad'a kansa a hankali yace.

"Allah yayi wahalarmu ba zata yi tsawo ba yarima, don a yanzu komai yazo k'arshe.

Naani ta dawo kuma zata raba yarinyar da b'arin ruhinka a yau d'in nan!"

**********

Imran ya bud'e k'ofar motarsa da wani irin k'arfi da yasa handle d'in b'allewa ya fito gabadaya, Alarms d'in jikinta suka hau k'ara da k'arfi, amma bai damu ba tunda har kofar ta bud'e, ya tayar da ita sannan ya danna button d'in hood d'in jikinta alarms d'in suka yi shiru.

Ya juya ya sata a reverse sannan ya bar cikin parking lot d'in da dukkan saurin da zai iya, ya canja gear jiki zuwa ta farko sannan ya shiga canja k'afarsa daga wajen clutch zuwa danna accelerator da sauri, hakan yasa motar ta cilla kan hanyar da zata kaishi main gate d'in fita daga wajen cikin wata irin k'ara data dauki hankalin gabadaya mutanen dake wajen, amma bai damu ba, burinsa kawai a lokacin tayoyin su cigaba da cillawa dashi zuwa inda hankali da ruhinsa ya tafi.

Ya canja gear zuwa ta biyu sanda yasha kwanar data hau dashi kan titi, ya sake danne accelerator sannan ya maida gear zuwa uku, injin motar yayi wani irin kuka kamar shima yana fad'in amincewarsa game da yadda motar ke tashi akan titi.

Maganganun jaamil suka karad'e kunnensa kamar daga cikin speakers d'in motar suke fitowa.

"Bama buk'atar wani b'ata lokaci, ina tunanin komai zai gamu a yau..... sai mu nemi hanyar kuma da zaka rabu da ita cikin sauqi.

Naani tace abinda muka yi ba kuskure bane, sai dai garaje....munyi garajen yanke hukuncin cewa ka aureta....

Ya kalli agogon kan dashbord d'in motar, minti uku ta wuce tun sanda jaamil yake fad'a masa wad'annan maganganun, minti uku ya k'ara akan halin da Sa'adha ke ciki a yanzu, yaji kamar ya cillar da motar ya fita yabi iska amma ya kasa saboda ya riga ya d'auki hankalin mutane da yawa kuma kowa na kallonsa.

Yayi ta kurd'awa ta tsakanin motoci baya ko lura da ihun horn d'in da ake danna masa da kuma yadda hannuwa suke fitowa ta window alamun zagi, kwakwalwarsa kawai aunawa take da tunanin hanyar da ta rage a gabansa kafin ya isa ga Sa'adha, wani irin abu mai zafi ya yanke kwakwalwarsa da tunanin wane hali take ciki yanzu, meke faruwa da ita ko kuma me ya riga ya faru?

Yayi rantsuwa a zuciyarsa tafi cikin k'irga cewa in har wani abu ya sameta, sai ya dagargaza ruhin jaamil, sai ya dagargaza shi yadda ba zai sake amfanuwa ba tunda har zai iya yanke wani abin a cikin al'amarinsu ba tare da shawararsa ba.

Ya sake danna pedal d'in k'asan k'arfasa da k'arfi sannan ya tura gear zuwa ta hud'u, RPM d'in motar ya tafi zuwa wajen Eight thousand, motar ta sake cillawa saman titi.

Zai isa wajen Sa'adha ba tare da komai ya faru ba, ya cigaba da gayawa zuciyarsa da fatan zata fahimta ta rage k'arfin bugawar da take yi, ba abin da zai same ta, ba'a yanzu zamansu zai zo k'arshe ba...komai zai cigaba zuwa tsawon watanni kamar yadda tunaninsa ya tsara tun farko. Ya danne clutch d'in motar da k'arfi sannan ya maida gear zuwa biyar, motar ta k'ara gudu akan mahaukacin wanda take yi da farko, ya dinga wuce motoci da ginunnukan da suka zama blur a idonsa.

Daga can gaba idonsa ya hango masa wani had'dd'en traffic na jerin motocin da basa ko motsawa, taraffic a wannan lokacin? taya zai zauna yana jira alhalin bai san halin da Sa'adha ke ciki ba? kowanne wucewar second d'aya ji yake kamar lattin awanni yake yi.

Kawai sai ya maida gear zuwa uku sannan ya juya kan motar cikin wani irin sauri ya shiga wata kwana daga gefensa, bai tab'a bin hanyar ba kuma bashi da tabbas d'in inda zata kaishi, yayi ta binta kawai yana yin kwanoni lokacin da mutane da yara ke ta gudu suna matsawa gefe don kar ya buge su.

A haka ya samu ya lalubo wata hanyar data maida shi kan titi, yana fahimtar inda yake ya sake danna accelerator k'asa, ya d'ane kan titin tare da tura clutch sannan ya maida gear zuwa hud'u. Ya dinga wuce shaguna da mutane a hanya suna ta harkokinsu ba tare da sanin had'arin dake faruwa gaba dasu kad'an ba.

Idonsa ya kai kan wani sign dake jikin street d'in da yake kai, few more minutes! ya sake fad'awa zuciyarsa, few more minutes suka rage ya k'arasa wajen Sa'adha, a da in yazo wajen gani yake kamar ya zo gida ne, amma a yanzu titin ya k'ara yi masa tsawo, yaga kamar ba hanyar da ya sani bace, sai da kwakwalwarsa ta jiyo masa bugun zuciyar Sa'adha sannan ya tabbatar hanya daidai yake bi, wani irin releif ya sauka a jikinsa, releif sosai da yasa zuciyarsa matsewa cikin zafi...sai dai bugun zuciyar tata was weak, bata bugawa a normal rate d'in data saba. Me ya same ta?

Har ya k'araso kwanar gidansa bai rage gudun motar ba, sai da yazo dab! da kwanar sannan ya taka birki da k'arfi motar tayi sliding sideways ta shiga kwanar.

Tun daga nesa idonsa ya hango masa malam Aminu ya bud'e kofar gate d'aya kamar yana gyara wani abu, ya danna masa horn wanda ya karad'e layin gabadaya, yana d'agowa yaga shine yayi sauri ya rarumi d'aya kofar ya bud'e, da kyar Imran ya iya tsaida motar sanda ya shiga cikin gidan, 'yan inches ne kawai suka rabata daga hawa balcony da zai kaika k'ofar falo.

In one swift move ya tura k'ofar motar da kad'an ya rage ta b'alle daga hinges dinta, ya nufi kofar falon ya b'alle handle d'inta don ba zai iya tsayawa bud'ewa ba.

K'ofar na wangalewa idonsa ya gane masa abinda yake tsoro, abinda zuciyarsa ke taraddadin faruwa, yaji yaji dukkan jijiyoyin jikinsa sun tsaya cak da aiki, bugun zuciyarsa ma ya d'auke na wani lokaci...idanunsa suka tsaya akan abinda ke gabansa.

Wani dunkulallen haske dake lilo a iska, haskensa ya tarwatse ya baje ko'ina a cikin falon, daga k'asa kuma jikin inuwarsa, wani tambari ne ya fito, tambari irin na adon sarautarta!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

40

(¡î_¡î)

Imran ya tattaro dukkan wani ragowar k'arfi na jikinsa ya k'ifta idanunsa a hankali sanda wannan hasken ya d'auke cikin abinda baifi second d'aya ba, daga shi har inuwarsa suka dunk'ule suka bi cikin iska.

Yana taka k'afarsa cikin falon, k'amshin wani daddad'an turaren wuta ya shiga hancinsa ba tare da shawara ba, gidan yana nan kamar yadda yake a kullum, komai zaune a muhallinsa cikin gyara tsaf! sannan shiru babu alamun wani abu mai rai a cikinsa, tunani kala-kala suka karad'e kwakwalwarsa a lokaci d'aya, yaji kamar ya ture bagwayen gidan, koina ya fito a lokaci d'aya.

Zai iya yiwuwa Sa'adha na d'aya daga cikin d'akunan a wani irin hali, watakila tayi ihu da kuka har ta gaji maigadi ba jiyota ba tunda yana can bakin gate, watakila tana dunk'ule a waje daya cikin muryarta ta dashe cikin mawuyacin hali... watakila kuma abinda ya faru da ita ya shafe duk wani hasashensa.

Ba abinda bai kawo ba cikin zuciyarsa kafin ya isa k'ofar d'akin da yake iya jiyo bugun zuciyarta a hankali kamar irin bugawar zuciyar jariri, ba tare da wani tunani ba ya buga k'ofar d'akin da karfi ta bud'e.

Kunnensa ya jiyo masa k'arar shak'ar numfashi cikin tsoro kafin idanunsa su gane masa Sa'adhan, tsaye cikin wata had'dd'iyar riga royal blue data wuce gwiwarta kad'an, gashin kanta a tufke cikin bun sannan hannunta rike da kunnenta na hagu tana mak'ala wasu 'yan kananan silver d'ankunne.

Cikin giftawar abinda bai kai second d'aya ba, Imran ya manta duk wasu rules na mu'amalar d'an adam yayi appearing a kusa da ita, Idanunta suka zare cike da tsoro tana kallonsa.

"Yanzu ka dawo? me ya faru...?"

"Sa'adha me ya same ki? me ya faru.?"

Tambayoyinsu suka had'e a lokaci guda hakan yasa kowannensu yayi shiru, ta had'iye yawu tana kallonsa kafin ita ta fara magana.

"Ba abinda ya same ni, me ya faru?"

Maimakon ya bata amsa sai kawai ya shiga lalubar gabad'aya jikinta kamar me neman wani abu daya rasa.

"Me ya faru ne? me ya same ni?"

Ta sake tambaya muryarta na shaida alamun tsoro. Ya cigaba da duba koina a jikinta yana yayyage rigar wajen da duk hannunsa ba zai iya kaiwa ba. Nanne taji zuciyarta ta cika da wani irin tsoro, hannayenta suka shiga rawa, meke faruwa? meya same shi? ko kuma ita me ya sameta yake nema a jikinta.

Tasa hannayenta duk biyu ta rike nasa sanda yake kok'arin yage d'aya kafad'ar rigar, wanda ya zama shi kad'aine abinda ya rik'e ta a jikinta, ta kalli idanunsa sosai sannan tace.

"Me ya faru dan Allah? meya same ni? in bruises d'in nan kake nema gabad'aya sun tafi, dama na gaya maka baza su dad'e ba, guda d'aya ne kawai ya rage a nan..."

Ta k'arasa tana nuna masa k'asan hab'arta, ya d'ora hannunsa a wajen sannan ya zamo dashi kan k'irjinta daidai saitin zuciyarta, yayi shiru kamar yana sauraren wani abu sannan a hankali da muryarsa mai zurfi yace.

"Me ya sami zuciyarki?"

"Huh? zuciyata kuma?" ta tambaya blankly tana kallonsa.

"Bayan na fita wani yazo?"

Ga mamakinsa sai yaga tayi murmushi mai fad'i sannan tace.

"Su Aunty ne suka zo, su wajen biyar baka ji dad'in dana ji ba wallahi, harfa dasu Amina da Rahma, su basu dad'e ma da tafiya ba..."

Jin haka yasa yayi saurin katseta.

"Yanzu suka tafi?"

"Eh, baza sufi minti talatin ba dai..."

Minti talatin, a cikin minti talatin komai zai iya faruwa ba tare da ta sani ba...sai ya juya da sauri ya bud'e wardrobe dinta, ya d'auko first kayan da hannunsa ya fara kaiwa yazo ya sasu a cikin hannunta.

"Ki saka yanzu ki fito ina jiranki."

Bai jira me zata ce ba ya juya ya koma main falon, ya tsaya daidai tsakiyar carpet d'in inda wannan hasken ya fito,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login