Showing 75001 words to 78000 words out of 113985 words
ta tsorata amma tambayar da take son yi ta ture hakan.
"Nayi zaton kace kuna da jiki, nayi zaton kace an canja maka jikin ne zuwa na mutane, ta yaya toh ka iya shiga jikina?"
¡ñ©n¡ñ
@Shamsiyer ranar da kika fara karanta labarin nan, kika ce min in taimaka in turo next chapter kiji wane ne Imran d'in da Nanne take ciwon kai ta had'u dashi..??....I tynk muna chapter 4 ne lokacin, toh gashi yau na amsa tambayarki.
_@Zz kin tambaye ni jiya akan k'arin bayanin mene ne halittar ALBIE...I hope kema na amsa tambayarki._??
****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
47
Kuyi hak'uri da Ingausar da zaku tarar a wannan chapter, wani abun ne baya fitowa sosai a hausa.??
(¡î_¡î)
"Na fad'a miki muna possesing wasu qualities irin na aljanu kuma mun fisu k'arfi ma a wasu b'angaren, muna iya b'atar da jikinmu yabi iska a wasu lokutan amma ba frequently ba kamar yadda aljanu suke a kullum."
Ya k'arasa yana kallon yadda tayi shiru tana jinsa, yatsunta dake cikin nasa suna motsawa a hankali, kowacce kalma dake fita daga bakinsa ji yake kamar wani nauyi ake sauke masa, he felt free! Saboda tun daga lokacin da aka kawo ta gidansa yake son fad'a mata wannan gaskiyar daya lullub'e da k'arya, yana son ta ainihin shi waye kamar yadda itama ta bud'e masa zuciyarta ya san komai game da ita.
"Tun daga wannan ranar, na san cewa nayi wani babban kuskure saboda haka na kasa samun nutsuwa tare dani, jaamil bai san me ya faru ba, amma sai ya zab'i wannan lokacin ya kai k'arata wajen Naani, A karo na farko tun bayan zuwana na koma Muzaffar, na durk'usa a gabanta nayi mata rantsuwa ba cewa ba zan k'ara zuwa kusa dake ba.
Bayan sati biyu da kuma hakan, jaamil yayi tafiya nemowa mahaifiyarsa maganin ciwon kanta, a wannan lokacin ne na had'u dake kin fito daga wani gida da k'unshi a hannunki, banyi miki magana ba saboda alk'awarin dana d'auka na nesanta kaina dake, amma bayan na koma gida sai naji cewa ba zan iya sawa rabuwarmu aya daga nan ba, saboda haka na dawo na baki hak'urin wannan zafin dana gani a cikin idonki, if not...i knew they will hunt me forever!
Nanne tayi shiru tana jinsa, ya gaya mata b'arin wannan gaskiyar sanda take masa tambayoyin nan, abinda kawai ya b'oye shine dalilin da yasa baiyi mata magana ba, a wancan lokacin yace saboda ya san bata kula kowa a waje ne, sai yanzu take jin ainihin gaskiyar.
"Daga nan kuma na takura kaina na goge komai naki daga cikin zuciyata don a tunanina hanyata da taki sun rabu kenan har abada, ashe wata k'addarar bata ma soma ba saboda ba'afi sati d'aya ba na tashi da wata matsananciyar rashin lafiya da ban tab'a yin irinta ba, da kyar na iya k'arasa meeting d'in da nake dashi a ranar, wani meeting mai muhimmanci kan abinda ya kaini kamfanin.
Na kira jaamil yazo yayi jinyata, muka yi ta k'ok'arin gano abinda ya same ni muka kasa, sai daga baya wani tunanin yazo masa, amma bai gaya min ba sai da yaje ya tabbatar tukunna sannan yazo ya sanar dani cewa kema baki da lafiya."
Ya d'anyi shiru kafin ya cigaba.
"Kuma wai rashin lafiyata da taki ta faru ne saboda na shiga jikinki na bar b'arin ruhina tare dake."
Yaji wani abu ya fad'a zuciyarsa sanda ya fad'i hakan, sannan yaji hannun Sa'adha dake cikin nasa yayi rawa, amma bai tsaya ba ya cigaba.
"Ransa ya b'aci sosai daya gano cewa har na shiga jikinki amma na b'oye masa, ya kasa karb'ar dukkan uzirina da hujjar cewa bana tab'a wasa da duk wani abu mai muhimmanci da Naani ta sani saboda haka ina sane nayi komai, bai san cewa tun lokacin da kika shigo rayuwata na rasa wannan confidence d'in ba, bai san cewa tun daga lokacin da nayi failing wajen controlling zuciyata akanki komai ya zame min sa'a ba."
Idanunsa suka lalubo fuskarta a sannan, ta sunkuya kad'an tana kallon hannunsa dake cikin nata, he wanted to tell her that itace abu mafi muhimmanci yanzu a rayuwarsa amma ya kasa samun k'arfin
yin hakan, yana fata ta fahimta a kowacce kalma da yake fad'a. A nutse muryarta ta fito.
"Nasha wahala lokacin, abubuwa suka yi ta tsoratani kala-kala, ya zama bana iya wani baccin kirki a kullum, sannan na tashi k'afafuna sun rik'e bana iya tashi, sai da Baffa ya kira wasu malamai suka yita addu'a sannan na samu sauk'i."
"Bayan taimakon addu'arsu Nima na taimaka wajen d'orar da sauk'inki Sa'adha."
Ta d'ago da idonta ta kalle shi.
"Lokacin da jaamil ya gane dalilin rashin lafiyar, ya gano cewa d'aya b'arin ruhin dake jikina zai iya kwantar dana jikinki zuwa wani lokaci, saboda in har suna tare ba abinda zai faru, sai sunyi nesa da juna ne sannan jikinki zai kasa rik'e wanda yake tare dake hakan yayi resulting a abubuwan dake tsorata ki. Saboda haka muka je gidanku a wannan daren kina bacci."
Nanne ta zare idonta lokacin da kwakwalwarta ta hasko mata wannan mafarkin da tayi na farko, wanda taga siffofi biyun nan tsaye akanta, da sanda d'aya daga cikinsu ya d'ora hannunsa akan goshinta taji gabad'ya ciwon jikinta yabi iska. Kafin ta iya samun damar tambaya Imran ya cigaba.
"Bayan wannan lokacin, ina zuwa in kwantar da ciwonki duk sanda ya fara k'ok'arin tashi yana tsorata ki yayin da jaamil ke can yana kokarin gano yadda zamu ciro b'arin ruhina daga jikinki, sai duk sanda naje na kwantar da ciwon naki ina rasa k'arfi sosai a jikina wanda har hakan yake shafar kuzarina a wajen aiki.
Jaamil ya k'are bincikensa, amma bai iya samo hanyar da zamu iya ba tare da taimakon Naani ba, kuma a lokacin ta shiga bautarta na tsawon watanni biyar saboda haka ya kawo shawarar cewa in aure ki, saboda in har b'arin ruhin yana tare da d'an uwansa zai zauna ne kamar sanda yana jikina ba tare da wani abu ya faru ba.
A lokacin da naji haka nak'i yarda Sa'adha saboda girman da zancen yayi min, dukkan intrest d'in da nake dashi akanki bai tab'a gangarawa kan maganar aure ba, saboda haka nak'i yarda da shawararsa shi kuma yayi ta bina da ita, daga k'arshe har ce masa nayi ni ba sonki nake yi ba don ya kyale ni amma sai ya k'ara kafa hujjar cewa dama ba zan aure ki bane don ina sonki, zan aureki ne don in gyara kuskuren dana jawo, a haka har yaci galaba akaina na amince cewa zan iya.
Daga nan muka fara tunanin yadda auren zai yiwu, na kawo shawarar cewa dole sai kin amince dani haka ma 'yan uwanki sannan komai zai tafi daidai, saboda haka jaamil ya bada shawarar na kad'e ki lokacin da kika je tsallaka titin nan siyo magani, ta haka na samu dukkanin wani contact dake da 'yan gidanku, kowa ya sanni kuma muka yi healing k'afarki ta yadda baki ji zafin ciwon jikinta ba ko kad'an.
A lokacin da hakan ke faruwa, jaamil yaje yayi controlling tunanin Malaman da suka yi miki addu'a, suka je suka gayawa Baffanki cewa bak'aken aljanu ke shirin shiga jikinki kuma aute ne kawai hanyar samun sauqinki."
Tunanin Nanne ya k'ulle a wannan lokacin, kallonsa kawai take yayin da magangamunsa ke shiga kanta kamar an tara bokiti a bakin famfo.
"Baffanki bai so yi miki aure a yanzu ba ko kad'an, don duk da k'ok'arin da jaamil yayi wajen sa zuciyarsa ta yarda da hakan, sai da yayi ta bin malamai kala-kala kuma kowannensu jaamil yana sawa su k'ara tabbatar masa da maganar dana farko suka fad'a."
"Baffan....." Muryarta ta fito involuntarily cikin rawa.
"We didn't hurt him Sa'adha...wallahi ba abinda muka yi masa, jaamil yayi controlling kwakwalwarsa ne ba tare ma daya sani ba, kamar yadda kike jin tunaninki yana canjawa a cikin kanki haka komai ya faru."
Ta kifta idanunta a hankali, tunaninta ya hasko mata sanda aka kaita wajensa sallama, sanda yake ta nasiha yana kuma bata hak'uri, Allah kadai ya san yadda yake ji a lokacin.
Imran yayi shiru don ya bata damar da zata wanke tunanin cikin kanta, yana murza hannunta a hankali cikin wani salo na rarrashi.
Nanne taji jinin dake cikin jijiyoyinta na gudu da wani irin sauri, wani irin saurin da taji dama tana da ikon da zata iya tsayar dashi, saboda hakan dad'a sawa yake taji komai ya had'e mata, sai dai yadda hannunsa ke motsawa akan nata a hankali ya shiga taimakawa wajen calming condition d'inta.
Bata san iya dad'ewar da suka yi a haka ba, zai iya yiwuwa kusan awa d'aya kafin ta iya samu dukkan maganganunsa su shiga kwakwalwarta. Bai motsa ba shima balle yayi magana yana rike da hannunta kawai, ta san a wannan lokacin bayan k'ok'arin yarda da maganganusa da tayi kamata yayi kuma taji tsoro, tsoron yadda rayuwarta ta gaba zata kasance ko abinda zai faru da ita, amma kwakwalwarta ta kasa hasko hakan, she couldn't think of anything except that he's touching her! hannunsa yana tab'a nata.
"Ka cigaba..." muryarta ta fito a hankali.
Taji sanda yayi ajiyar zuciya kafin shima muryarsa ta fito.
"Bayan Baffa ya tara ku ya fad'a muku cewa ya yanke shawarar aurar dake kuma ya baki wata d'aya ki gabatar masa da wani - sai naje wajensa bayan sati d'aya, Na fad'a masa labarin da kika sani kamar yadda muka tsara tun farko ni da jaamil, cewa ni d'an bauchi ne aiki ya kawo ni nan kuma iyayena sun rasu a hannun k'anin mahaifina na tashi.
Yayi maraba dani sosai sannan ya buk'aci in bashi lokaci cewa zaiyi bincike akan lamarina, bayan sati d'aya sai ya sake kirana ta hanyar yayanki Sulaiman wanda muka saba tun sanda kina asibiti, dana je ya buqaci in turo da iyayena suyi magana saboda haka jaamil ya sake yin aikinsa, ya turo dattijan mutane irin wanda ya san Baffa zai ga girmansu ta hanyar rufe masa ido amma a zahiri babu kowa, babu wasu mutanen da suka je.
A wannan lokacin na d'auki hutu naje Maldives. Wajen da tunda naje ba abinda nake iya tab'ukawa sai tunaninki Sa'adha, duk da cewa inata ture hakan daga zuciyata amma na kasa, tunanin yadda zaman mu zai kasance kawai nake, yadda zan iya rayuwa dake a matsayin matata alhali ba jinsinmu d'aya ba, tsoron cewa zan iya cutar dake ne yafi yawa da kuma tunanin yadda zanyi controlling zuciyata akanki.
Saboda a lokacin ina kokarin sawa zuciyata ta yarda da kalaman jaamil ne, na cewa sai na ture dukkan intrest d'ina akanki don zamana dake ba mai d'orewa bane, zai k'are a duk ranar da Naani ta dawo ta raba ruhina dake."
A daidai nan, yayi shiru yana shak'ar kamshin jikinta da kuma na gashinta wanda ya fito ta k'arshen d'ankwalinta, a lokaci d'aya kuma yana sauraren bugun zuciyarta, wani lokacin sai ya buga da k'arfi wani lokacin kuma ya tsaya gabad'aya, bayan wani lokaci sai ya koma daidai ya cigaba da bugawa a normal rate d'in da ya saba, a wannan lokacin ya fahimci cewa bugun zuciyarta shine sauti mafi muhimmanci a rayuwarsa.
Duk cikin wannan lokacin bata motsa ba, saboda haka bayan ya tabbatar kwakwalwarta ta gama absorbing kalamansa na baya, ya cigaba.
"A sannan jaamil ya kira ni da cewar lokaci yayi, saboda haka hutuna bai k'are ba na tattaro na dawo. Bayan dawowata na sake zuwa na sami Baffa, shi ya bani ranar da zanzo in same ki, saboda haka na kira ki na tambaya, amma dana zo kika hana ni ganinki.
A wannan lokacin na fahimci cewa bayan had'in kan Baffa da muka samu, dole ne kuma sai na nemi naki in har ina so abubuwa su tafi mana daidai, ba tare da son ran jaamil ba na dinga kiranki a waya da duk wata hanyar dana san zan shawo kanki, har na fara koya miki yadda zaki so ni kamar yadda na fad'a miki."
"Saboda me?" Ta tambaya.
Imran ya kasa gane dalilin da yasa ta tambaya, bata san cewa b'acin ranta koya yake can cause him physical pain ba? Bata fahimci cewa yana k'aunarta fiye da tasa rayuwar ba?
"Sa'adatu." Ya kira full name d'inta yadda zata fahimci cewa he's so serious, ya d'ago da d'aya hannunsa da baya rik'e da nata ya kamo gefen fuskarta.
"Ba zan tab'a iya rayuwa mai kyau ba in har na zama sanadin abinda zai dame ki, you don't know how it tortured me to see you hurt."
Nanne ta sake damk'e hannunta dake cikin nasa tana kallonsa, ya lumshe idanunsa a hankali by the pleasure, zai sake magana tayi saurin tsayar dashi ta hanyar d'ora yatsunta akan lebb'ensa, Bayaninsa bai kai k'arshe ba, akwai sauran abubuwan da suka rage itama kuma akwai sauran tambayoyin dake cikin kanta, amma wannan kalaman nasa ya ture komai, taji iya su kad'ai sunyi convincing zuciyarta sun ture duk wani sauran duhu dake cikin kanta game dashi.
A hankali tana kallon idanunsa da suke kyallin silver har yanzu tace.
"You are the most important thing to me too! the most important thing to me ever Ulfat!"
¡ñ©n¡ñ
Did we just heard the first nickname d'in da Nanne ta kira Imran?
Me ne tunaninku akan duk wannan gaskiyar da Imran ya bud'ewa Sa'adha a yau?
Kuna tunanin zai fad'a mata ma had'arin dake gabanta game da Naani?
Me zai faru a next chapter?
****
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
48
(¡î_¡î)
"Kin gansu koh?" Inna ta tambaya daga falo zaune akan dardumarta.
"Eh na gansu, ashe suna da d'an yawa ma."
Nanne ta amsa sanda ta dawo cikin falon ta zauna a kusa da ita.
"Toh na nan ne masu yawan kenan, ai na zata na wajen Azumin sune suka fi yawa."
"Au wai da akwai wasu ma a wajen mama Azumi?"
"Akwai mana, wad'annan ai ina jin na wajen Nuratu ne da suka kawo ran d'aurin aure da kuma na sauran mutanen da suka dinga kawowa daga baya, toh na wajenta kuma ina jin sune ragowar wanda su Nafisa suka je kasuwa aka manta ba'a kai ba."
Nanne ta mik'a hannu ta d'auki sala d'aya na lemon dake gaban Innan kafin tace.
"Wallahi dama an barsu anan kawai, ki dinga yin gudunmawa dasu tunda a can d'in ma fa sai kiga wani abin har guda biyu iri d'aya."
"A'ah, d'iban kayanki zaki yi ki tafi dasu ni yaushe zan d'ebi kayan kitchen in tafi kai gudunmawa, ai duk wanda zan bawa gudunmawa yanzu kud'i yake zato daga gurina.
Kuma kayan har fa da wanda su Nuratu suka kawo, me zai kaini tab'a su? a ranar ma da zasu tafi har tambayar su maryamah suka yi wai ko su tafi dasu ne tunda zasu je gidan naki kafin su wuce tace musu su barshi za'a kai, nayi ta fad'a da tazo ta gaya min anan, nace don me zata hana su, su kwashi tarkacensu mana suyi gaba idan gani suke zamu rik'e wani abin zamu yi, in banda ma....."
Nanne kawai murmushi take tana kallonta, tayi missing hirar nan tata kamar me? yadda zasu zauna irin yanzu wajen k'arfe d'aya kafin tafiyarta islamiyya suna ta hirarrakinsu, na 'yan uwa da kuma yanayin zamantakewar yau.
Tun wajen k'arfe tara na safiyar yau da Imran ya ajiyeta a k'ofar gidansu take jin wani canji a zuciyarta, gani take kamar ta dawo duniya ne daga can wani baqon wuri da aka kaita, sanda ta shigo taga inna kuma sai kewar komai ta dad'a kamata, ta rungumeta da k'arfi su mama Azumi da suka rako ta tun daga tsakar gida suna ta fad'in wai zata b'allata, amma itama innan bata damu ba, ta rik'e ta sosai tana ta lale maraba da Amarya.
Da kyar ta iya barin d'akin maq taje ta gaishe dasu hajiya Babba, kowa sai fara'a yake mata ana kuma bata wani girman da a da bata san dashi ba, don mama rabi wai harda rako ta bakin kofa, matar da a da kanta a d'age take amsa gaisuwarta.
Babban abin mamakin data gani shine daga wurin yayyenta maza, duk wanda ya lek'o yiwa Inna sallama zai fita, in ya ganta sai ya tsaya su gaisa, a baya kuwa wani ma hamb'are kafarta zaiyi ya shige wajen innan.
'Yan biyu ma da suka shigo bayan sun tashi daga baccin asarar su Saleem da murmushinsa yayi ta tambayarta ya sabon waje da kuma mijinta, Suraj ne kawai ya d'an mata wani guntun murmushi daya d'auke in second sannan yace 'kin zo dama.'
"Yanzu Inna to ke kad'ai kike kwana a d'akin nan?"
Ta tambaya sanda take taya innan rarraba goron da take bayarwa a kai masallaci sadaka duk ranar juma'a.
"A'ah bayan tafiyar su maryamah ai Azumi nan ta dawo, tare muke kwana kiga mu sha hirar mu ma har fare ya raba."
"Kai Inna, wai harda kusha hira...irin kin samu wadda ta fini d'in nan."
Ta fad'a kamar zata yi kuka.
"Yo kiji min 'ya, ke ba wanda ya fini d'in kika samu ba? yanzu da za'a ce kizo ki kwana biyu ai ba yarda zaki yi ba."
"Haba dai Inna, wallahi ba'a fad'a d'in bane."
Ta fad'a tana d'aukar wani lemon, sai dai me? duk yadda ta kai ga d'okin gidan ana yin sallar la'asar taji ta fara tunanin sanda Imran zai zo su tafi, sau da yawa tana irin wannan dad'ewar bata ganshi ba in yana wajen aiki, amma yau da banbanci, a wani waje take da ba inda zai dinga tuna mata da abubuwansa, inda ya zauna yayi wani abin, inda yayi magana, abinda ya d'auka ko kuma inda ya tsaya yace mata wani abun.
Rahma ma tazo sun sha hira amma duk inda ta kai ga jin dad'in hirarsu ita da Inna, tunaninta yana zamewa wajen hasko mata wad'annan kyawawan idanun nasa da yake yawan lumshe mata su, ko muryarsa, ko yadda yake rik'eta, dama sauran tarin 'yan k'anan abubuwan da bata san tana lura dasu ba.
Da gaske ne ta yarda cewa rayuwarta ta canja, tun daga lokacin da aka d'auketa aka kaita gidansa, rayuwarta ta canja ta hanyar da baza ta iya fassarawa ba sai dai kawai wanda ya san irin hakan ya gane.
Wajen k'arfe biyar, Sadiq ya shigo d'akin da tsokanarsa yana fad'in.
"Yan mata ta zama matar aure...!"
Nanne ta juya idonta tace.
"To ya ranka? girma ne dai dole yanzu Allah ya riga ya bani kuma inda mutunci ma kamata yayi ka dinga kirana da Aunty, tunda yanzu ka san na wuce ajinka."
"Wallahi ba matsala..." ya fad'a yana zama a kujerar da take kai.
"Ni yanzu ko