Showing 99001 words to 102000 words out of 113985 words
ya fad'a yana ajiye tablet d'in daya rik'e, ta k'araso ta shige cikin hannun nasa ya rungumeta sosai, k'amshin turare sabulun wanka da kuma shampoo d'inta suka had'e cikin hancinsa, ya lumshe idonsa a hankali.
"I miss you!" he breathed.
Da dariyarta tace. "Ina naje? tunda ka dawo fa muna tare."
"Mhm-mhm, kina tare dai da yarinyar nan, hankalinki baya wajena."
Ta d'ago da kanta ta kalle shi.
"Amma na ta maka magana baka amsa ba."
Ya d'an had'e girarsa waje d'aya.
"Noory i hate to tell you this, but hankalina bai kwanta da mutanen nan ba, akwai wani abu a tare dasu."
Itama ta had'e tata girar.
"Kamar yaya?"
A cikin kansa yayi tunanin gaya mata gaskiyar abinda ruhinsa da kwakwalwarsa suka ji game da matar nan, amma sai yayi saurin dakatar da kansa, damuwa hakan zai sa a cikin kanta, damuwar da zata iya sake illata wani abun na jikinta, saboda haka ya canja zancensa da cewar.
"A halin da muke ciki Sa'adha da kuma yanayinki, kamata yayi muyi taka tsan-tsan da kowa, kinga dukkan abinda ya faru da idanunki, bana so mu sake experiencing makamancinsa."
Maimakon ta bashi amsa sai ta sunkuyar da kanta k'asa kawai, da alama kwakwalwarta ta tafi irin tunanin da take yi duk lokacin da zancen abinda ya faru tsakaninsa da Naani ya gifta... don abinda ya faru wani abu ne daya tabbata banda b'arin ruhinsa dake jikinta a lokacin ba abinda zai hana zuciyarta bugawa. Shi yasa tun daga wannan ranar in har ba dole ba, basa tab'a yin zancen abinda ya faru.
Shirunta yayi yawa, sai yasa hannunsa ya janyo littafin da take rik'e dashi sannan yace.
"A module nawa muke?"
Jin haka yasa ta d'ago da kanta ta kalli littafin daya bud'a akan cinyarsa, da sauri ta fara flipping cikin pages d'in sannan tace.
"Inajin 20 ne."
Imran ya k'ifta idonsa yana kallonta, Allah ya sani bai san wani irin so Sa'adha ke yiwa d'an cikinta ba, d'aki guda ne a yanzu ta ware da ba abinda take tarawa sai kayan 'yan babies, don duk inda suka fita ko 'yar feeder ta gani sai ta siya, da suka je siyan kayan abinci kuwa rabin siyayyar ta koma ne ta kayan yara da kuma tarin littattafan da suke guiding iyaye akan rayuwar yara, tun daga girmansu kuwa har teenage years.
Wani abin dariya har gaya masa take cewa in babynsu ya kai shekara sha biyar za'a d'inka masa kaya da yawa, saboda wai teenagers na buqatar kaya sosai a wannan lokacin.
****
A cikin kwanakin da suka biyo baya alaqar Nanne da maman yarinyar nan mai suna Safiyya ta k'ara habb'aka duk kuwa da rashin son hakan da Imran ke nuna mata a kullum, amma koyaushe sai ta kawo uzirin cewa su suke zuwa wajenta kuma ba zata iya korarsu ba.
A cikin haka ne wata rana ya dawo daga aiki ya tarar bata nan, kuma bai fita da motar dake da key d'in gidan a jikin nata ba, mamaki ya kamashi sosai lokacin daya kira ta tace masa wai tana gidansu Safiyyan.
Ransa yayi mutuqar b'aci ta yadda bai ko shiga gidan ba ya tsaya a waje yana jiranta har ta k'araso, yanayin yadda take tafiya kad'ai a hankali ne saboda girman da cikinta ya k'aru sosai, amma a haka har ta iya d'aukar k'afa ta fita ba tare da ta fad'a masa ba.
"I'm so sorry Ulfat!... Safiyya ce ta kira ni urgently wai..."
Ta fad'a sanda ta k'araso tana k'ok'arin lalubo key d'in a cikin bunch d'in dake hannunta, bai ko tsaya saurarata ba ya janyo hannun nata sannan ya b'alle handle din k'ofar ya cire shi gabad'aya ya jata ciki, bai tsaya ba sai da suka isa can cikin falo na biyu sannan ya zaunar da ita akan d'aya daga cikin kujerun. Idanunsa cike da tsantsar damuwa yace.
"Sa'adha yauce rana ta k'arshe da magana ma zata had'a ki da mutanen nan ko a hanya ne kuwa, ban yarda ki sake barinsu su shigo cikin gidan nan ko ke kije wajensu ba."
Da mamaki a fuskarta tace.
"Kamar yaya Ayunie? me suka maka? na gaya maka wallahi matar tana da kirki, basu da wani aibu... ta kira ni ne kawai don in taimake ta hidaya ta makale kafarta a cikin kujera, and i call your phone busy kana ta waya..."
"Ban yarda ba Sa'adha, and that's it! kawai na gaya miki ban yarda ba!" ya katseta da sauri.
A yanzu girarta biyu ta had'e cikin b'acin rai.
"Kana nufin kenan haka zan zauna ba zan kula kowa ba, Ayunie na baro dukkan dangina fa a can, nan d'in wani waje ne da bani da kowa and for goodness sake i need some company, ta yaya zan zauna a gida ni kad'ai ba zan yi mu'amala da kowa ba kuma kullum ka fita ka barni?"
Ya k'ank'ance idanunsa yana kallonta.
"Kina nufin ba zaki rabu dasu ba?"
Duk da nauyin da idanunta suka yi mata a lokacin, amma Sa'adha ta daure zuciyarta ta fito da irin rashin kunyarta ta baya tace.
"Haka nake shirin fad'a."
Bai ce komai ba sai ya saki hannun nata kawai ya mik'e sannan yayi hanyar d'akinsa.
Wasa-wasa har dare Imran bai k'ara mata magana akan hakan ba, sannan bai fasa al'amuransa a cikin gidan ba, yaci abincinta, sunyi sallah tare har ya bata wayarsa sun gaisa da Inna, sai dai duk cikin hakan fuskarsa ba fara'a ko kad'an, hakan yasa ta takura don basu saba irin wannan zaman ba, zuciyarta ta dinga gaya mata cewa maganar da ta gaya masa bata kyauta ba kuma bai dace ba, saboda haka bayan sallar isha ta nufi cikin study room d'insa da niyyar bashi hakuri.
A jikin wata shelf ta same shi yana kokarin zaro wani littafi, ta tsaya dab da bayansa sannan ta kira sunansa cikin wata murya a hankali, hakan yasa shi juyowa rik'e da littafin ya kalleta ba tare da yace komai ba. kanta na sunkuye tana wasa da yatsunta tace.
"I'm sorry dan Allah, kayi hakuri, bai dace in fad'i abinda na fad'a maka d'azu ba kayi hakuri."
Imran yaji k'afafaunsa sun manne a inda yake tsaye? Sau nawa ne wai zuciyarsa take son Sa'adha, a yanzu yake shirin zuwa ya bata hakuri don zuciyarsa ta gaya masa cewa abinda yayi mata bai kyauta ba, tayi sacrificing abubuwa da yawa a rayuwarta saboda shi amma shi ya kasa hak'ura da wani abu guda d'aya kawai da take so? kamata yayi ya kyaleta ta cigaba da mu'amalarta dasu, tunda har yana bincike ta baya akansu ba tare da ta sani ba.
Jin yayi shiru yasa ta d'ago ta kalle shi idanunta alamun hawaye.
"Ayunie kayi hakuri mana, na gaya maka na daina, kuma Allah na kira wayarka har..."
Lips d'insa masu d'umi suka sauka akan nata, bakinsa na k'amshin permanent chewing gum d'insa na mint, hannayensa suka jata cikin jikinsa tare da rungumeta baki d'aya!
Ta rufe idanunta a hankali sanda kwakwalwarta ta shafe komai da ya faru a wannan ranar, ta manta zancen wata Safiyya da 'yarta, ta manta zancen da suka yi d'azu, ta tuno kawai cewa Imran yana sonta, he wanted her and she was all his! saboda haka ta nannad'e hannayen ta a wuyansa sannan ta bud'e kowanne waje a zuciyarta don ta karb'i sak'onsa.
A lokacin ne kuma abin ya faru, wani abu da bai tab'a kasancewa ba, wani abu da ya tabbatar mata cewa da gaske ne ita d'in a lokacin ta zama UWA, halittar dake cikinta yayi motsi da wani irin k'arfi!
***
Karfe d'aya na daren wannan ranar Nanne ta fito daga d'akin rik'e da waya a hannunta, sleeping dress d'in jikinta iya gwiwa, ta d'ora 'yar top akai.
"Ayunie ka gaya min inda kake mana."
Ta cikin wayar yayi murmushi sannan yace.
"Kina ina yanzu?"
"Ina falo."
"Good, now ki nemo letter N a falon."
Girarta biyu ta had'e waje d'aya.
"Letter N kamar yaya?"
"Just find it."
Mamaki ya kamata, me kuma Imran zaiyi da tsakar daren nan? ita dai ya san tayi bacci tun wajen sha d'aya saura lokacin da suke kallo, shi yasa lokacin da k'arar wayarta ya tashe tayi tunanin alarm din asuba ne, amma sai taga kiransa ne kuma k'arfe d'aya na dare, ya kira kusan sau uku kafin ta wartsake daga baccin ta d'auka... mamaki ya sake kamata da yace wai ta fito falo zai fada mata wani abu kuma kar ta kashe wayar, ta lalubo 'yar top din rigar baccinta ta dora sannan ta fito, yanzu kuma yace wai ta nemo letter N wano mamakin ya sake cinye ta, amma sai ta biye masa ta shiga bincikawa cikin falon.
"Atleast give me hint mana, ya letter N d'in take?"
Yayi murmushi sosai kafin yace kawai ta cigaba da dubawa, sai tayi kusan minti d'aya tana d'aga abubuwa sannan ta gano ta wani sabon pillow mai shape d'in N a tsakanin kujerun.
"A ina muka sami wannan pillown?"
Ta tambaya a cikin wayar da har yanzu ke kunnenta.
"Bravo habibty! yanzu ki taho dining, ki nemo double O.
Ta d'age girata d'aya kamar yana kallonta.
"Is This a game?"
"I think so, just find the O's."
Tana iya picturing yadda bakinsa ya zagaye a fad'ar O's d'in, tayi murmushi sannan ta nufi dining d'in rik'e pillown N.
A can ma tasha duba kafin ta samo O's d'in guda biyu a tsakanin serviette tissue.
"Now find the last letter Y a kitchen, sai in gaya miki inda nake."
Tana shiga kitchen d'in letter Y da aka hura ta ballon was waiting a saman island. Ta zube sauran gabad'aya suka had'u suka bada sunanta, sunanta a wajen Imran.
NOORY!
"Awwn... this is too awesome! Thank you Ayunie."
"Thank you too Babe. Ki bud'e back door d'in ina jiranki."
Jin haka yasa ta juya da sauri ta bud'e k'ofar kitchen d'in wadda take leading zuwa bayan gidan, wajen kamar gidansu na can ne, d'an karamin garden ne da wajen shanya.
At first ba abinda idonta ya gane mata sai duhun shuke-shuken, Sai da Imran ya kunna fitila ne sannan ta hango shi tsaye a tsakiyar wajen, samanshi katuwar Banner ce an rubuta.
I'M SORRY NOORY..!
AND CONGRATULATION FOR THE FIRST KICK...!
Ta rufe bakinta da dukka hannayenta biyun saboda tsananin mamaki, This is just out of the world.
Oh my heart, oh my heart!
Ta fad'a a hankali lokacin da ya ware mata hannayensa alamun ta taho, sai a lokacin ta janye wayar daga kunnenta sannan ta ruga da saurinta ta shige cikin hannayen nasa shi kuma ya binne ta a jikinsa.
"I'm sorry akan abinda ya faru d'azu habibty... I shouldn't have told you ki daina kula su, kawai zuciyata ce ke bani...."
"Shshshsh...." Tayi saurin katse shi tana d'ago da kanta.
"Abinda ya faru d'azu ya riga ya wuce Ulfat.... and this is just.... WOW!"
"I'm glad you like it." Ya fad'a da murmushi.
"A ina ka samu duk wannan abubuwan?"
Ta tambaya tana kallon flowers d'in da aka jera a jikin Banner.
"Interior Company da suka yi mana tsarin gidan nan na kira."
Ta jinjina kanta tana sake kallon abun, wato komai inda kud'inka da shagalinka, a yaushe har ya kira su suka had'a wannan abun. Hasken flash d'in wayarsa ya dallare idanunta.
"You look beautiful in kina tunani."
Ta rufe fuskarta da hannayenta tana fad'in ta yaya zai d'auketa fuskarta muzu-muzu daga bacci amma ya janye su ya k'ara d'aukarta wani hoton, tun yana d'aukarta ita kad'ai har daga k'arshe ya shiga had'awa dashi, sai da suka kusan cika camera d'insa da selfie sannan yace.
"Noory do you care for a dance?"
Ta zare idonta a lokaci d'aya.
"Rawa yanzu?"
"Yes, I just thought we should celebrate the first kick."
"Kusan fa k'arfe d'aya da rabi yanzu na dare Ayunie."
"Me kike tsoro?"
"Aljaanu mana." Ta fad'a kai tsaye.
Ya kifa kansa cikin kafad'unta yayi dariya sosai kafin ya d'ago da kansa.
"You can't be serious dear, wane aljaani zaki tsoro in kina tare dani, beleive me ko cikin gidan nan ba zasu iya shigowa ba balle kusa dake."
Murmushin da tayi ya bashi damar sake tambaya.
"May I have this dance habibty?"
"Dance ba wak'a?" Ta tambaya girarta d'aya a d'age.
Da sauri ya matsa baya ya d'auko bluethoot d'insa. Yana dannawa wakar ta karad'e wajen cikin mid volume.
Ya k'araso ya miko mata hannunsa, ta d'ora nata akai sannan yasa d'aya hannunsa ya nannad'e kugunta...
"So slow..."
Ya rad'a a kunnenta sanda suka fara bin takun wak'ar.
Darling, just kiss me slow,
Your heart is all I own
And in your eyes you're holding mine
Baby, I'm dancing in the dark
With you between my arms
Barefoot on the grass, listening to our favorite song
When you said you looked a mess,
I whispered underneath my breath
But you heard it,
Darling, you look perfect tonight...
Ya sake rik'e ta a cikin jikinsa, sannan ya sunkuyo da fuskarsa ya d'ora goshinsa akan nata, tsinin hancinsa na tab'a nata, a hankali muryarsa mai taushi da zurfi ta shiga bin wak'ar...
Well I found a woman
Stronger than anyone I know
She shares my dreams, I hope that someday I'll share her home..
I found a love, to carry more than just my secrets
To carry love, to carry children of our own...
Nanne ta rufe idanunta a hankali tana jin zuciyarta kamar zata kumbura ta fashe saboda dad'i, that moment was the PERFECT and most wonderful moment a wajenta, tun lokacin data samu cikin nan suke fuskantar abubuwa kala-kala, ba irin tashin hankali da tudun da basu fad'a ba, amma yanzu da take cikin hannunsa a wannan lokacin ta manta da duk abun da ya faru a baya, ta manta da komai...
She wanted to start everything afresh!
*****
"Yanzu toh shi ya fita?" Inna ta tambaya daga cikin wayar.
"Eh ai kusan kullum sai yamma can yake dawowa, asabar da lahadi ne kawai yake gida."
"Toh gaskiya kuwa zamanki bai kyautu a haka ba, kinga tun wancan watan nake faman lalubawa in samo wadda zata zauna dake amma abun na neman gagara, don can niger duk yawanci zawarawan sunyi aure wasu kuma sun koma d'akin mazajensu.
Anan kuma su lami ne kad'ai da ba shiri kuke yi ba, in ba suba kin san duk sauran ma'aikatan da aurensu... wancan satin ma muku yi zancen da Azumi take cewa ko ita zata zo, nace ai tafiyarta ba zai yiwu ba, don kusan komai na harkar kitchen din nan yanzu a hannunta take, don haka ki tambaye shi shi a nasa 'yan uwan a samo wata dattijuwar tazo ta zauna daku, amma ba zai yiwu ace a wannan halin kina zama ke kad'ai a gida ba."
Nanne ta damk'e wayar a kunnenta lokacin da ta lalubi kujera ta zauna, bata dad'e da gyara gidan tsaf ba, saboda haka sai k'amshin turare yake, a gabanta flat screen d'in Tv ne ke nuna tashar "Star life" a lokacin k'arfe uku saura ne na rana.
"Ko ba kya jina ne?" Inna ta sake fad'a daga cikin wayar.
"Eh naji inna, in ya dawo zan fad'a masa insha Allah."
"Yawwa kinga inda wata ai ko haihuwar ce ta kama ba sai kin taho ba, daga nan ma a samo wata kafin sannan, tunda dama banda su maryama da suka rako ki ai ba wanda yaga inda kuke."
Jin haka yasa Nanne ta turo baki kamar tana ganinta.
"Gaskiya Inna ni nafi son in taho nan, kome za'a yi maka ai ba kamar a gida ba kinga."
"Toh wannan kuma sai kin shawarta dashi, tunda shi ba 'yan uwa a kusa ne dashi ba, yaushe za'a barshi ya zauna shi kad'ai?"
"Karki damu Inna, na san ma zai yarda."
"Ko kuma zaki rok'e shi ya yarda ba."
Tayi dariya sosai kafin tace.
"Jiya ma sunyi waya da yaya sulaiman yace ya gama yi min registration na WAEC da NECO din."
"Toh ke da ba lafiya ba, yaushe zaki yi wata jarabawa."
"Inna ai kafin lokacin ina jin ma munyi wata d'aya."
"Da d'anyan jego zaki kenan kamar dole?"
Sai da ta sake wata dariyar sannan tace.
"Inna koh a yanzu fa ba wani ciwo nake ji ba, balle a lokacin insha Allah, kawai dai ramar ce."
A sannan ne taji kamar ta gaya mata motsin da a yanzu kusan kullum cikin nata keyi, alamun cewa ko meye a ciki yana da rai da kuma k'oshin lafiya, amma haka kawai sai taji bakinta ya k'ulle.
"An kawo kud'in auren Rahma jiya."
Idanunta suka zare a lokaci d'aya.
"Amma shine bata gaya min ba? shekaranjiya fa muka yi waya da ita."
"Yo ai itama bata san za'ayi haka ba, tambaya kawai suka zo a jiyan kuma aka b'ige da karbar kudi, ai kin san ma yaron, d'an mak'otansu hajiya karima... yaro mai hankali wallahi."
"Ai shikenan na kira ta yanzu in mun gama wayar, Allah ya tabbatar da alkhairi."
"Ameen, ina Aminatu kuwa?"
"Tana nan ranar juma'a ma munyi waya harda ummanta tace a gaishe ki."
"Ita ba'a fara zancen nata auren ba?"
"A'ah gaskiya, sai dai nan gaba tukunna."
"Toh Allah ya had'a kowa da rabonsa."
"Ameen, mama Azumi bata kusa ne?"
"Eh, ta fita nan baya gaisuwa, k'anwar iyan shehu ce ta rasu wajen haihuwa."
Haka kurum Nanne taji gabanta ya bada wata irin k'ara data amsa har cikin kunnunwanta, jikinta yayi wani iri a lokaci d'aya, da kyar ta iya lalubo muryarta tace.
"Allah sarki, Allah ya jik'anta."
"Ameen dai, tayi shahada wallahi, ance 'yarta tana nan kyakkyawa da ita."
Kafin Nanne ta amsa, falon ya karad'e da sound din bell da aka danna daga waje, Saboda haka tace.
"Inna zan kira ki anjima, inaga nayi bak'i ne."
A hanyarta ta bud'e k'ofar text d'in Imran ya shigo yayi appearing akan screen d'in wayar.
I'll be home a bit late habibty, zan yi miki bayani insha Allah when I'm back, love you Babe.
...like crazy!
Da murmushinta tayi locking wayar sannan ta bud'e k'ofar. A lokaci d'aya k'arar b'allewar wani abu kamar k'ashi ta d'auka a bangwayen falon sanda wayar hannunta ta fad'i ta tarwatse a k'asa.
"Owwwh..."
Muryar Nanne ta fito a hankali yayin da ta zare idanunta, kwakwalwarta ta kasa fahimta, ta kasa d'aukar abinda ke faruwa, A cikin cikinta wani abu ya fizge zuwa opposite direction d'insa.
Ripping. Breaking. Ciwo.
Wasu k'ananan bakaken spots suka shiga rufe hasken dake cikin d'akin a idanunta lokacin da k'afarta ta kasa d'aukarta ta fad'i k'asa akan cikin nata, a lokacin tayi k'ok'arin lalubo zuciyarta, find it! amma she was so lost inside the pain, komai ya d'auke mata, makogwaronta ya cika da radad'i sannan duk wata iska ta d'auke mata.
Hannayenta dake rawa suka lalubo kan cikinta da niyyar kare abinda ke ciki, amma d'aya ya karasa d'ayan kuma ya kasa kaiwa, she couldnt feel it, she could'nt feel herself! Bak'aken spots d'in nan suka sake cika idonta gabad'aya.
A half second later, ta kwalla wata irin k'ara da wani abu kamar shak'ewa ya katse ta, and