Showing 105001 words to 108000 words out of 113985 words
tsaya a lokaci d'aya, yayi sanyi k'alau cikin hannunsa amma numfashinta mai nauyi na cigaba da fita kuma zuciyarta na bugawa a hankali, hakan yasa ya fahimci cewa komai yazo k'arshe kenan... hargitsin dake azabtar da ita yazo k'arshe, abun da ke cikinta ya fito duniya... duniyar da a yanzu take a hargitse!
At long last, it was out of her!
Shiru na wani lokaci ya biyo baya kafin muryar Bwama ta karad'e cikin falon a hankali kamar mai rad'a.
"Masha Allah... Ourjaani yam!" ( He's so beautiful!)
Imran bai d'auke idonsa daga kan na Sa'adha ba, wad'annan chocolate idanun nata masu kyau da a yanzu suka hargitse suka koma jawur!
"Ayunie zan ganshi."
Muryarta ta fito tar! amma cikin rashin kuzari.
Bai ko k'ifta idonsa balle ya motsa don kwakwalwarsa bata aiki a lokacin, yaji me ta fad'a amma bai san ma'anar kalaman ba, hankalinsa yayi cilli can wajen tunanin yadda zai iya had'a jikinta ya koma daidai a yanzu da burinta ya gama cika. Yana iya jin sanda Bwama ta matso ta zuro abun ta tsakanin fuskarta da tasa, da sanda idanun Sa'adha suka k'ifta a hankali wajen saita ganinta akan abun, amma bai d'auke ganinsa daga kanta ba balle shima ya kalli abun da ya zama silar K'ADDARAR RAYUWARSU!
"Alhamdlilah." Muryarta ta sake fitowa amma wannan karon da wani irin amo da zaka iya sensing irin azabar da take daurewa.
For a second, babu wani motsi dake faruwa a cikin d'akin sai na hawayen Sa'adha dake gangarawa kan kuncinta da kuma sanda ta juyar da kanta gefe a hankali ta kalli wani wajen sannan ta dawo dashi kan halittar dake tsakaninsu, wanda kafin ya iya yunk'urin kallonsa Bwama tayi saurin janye shi daga jikinsu sannan yaji muryarta na umartar jaamil da ya karb'e shi, bai fahimci me ke shirin faruwa ba sai da tarin jini ya bullutso daga bakinta ya fallatsa akan fuskarsa.
****
Hoton da idanun Nanne ke d'auko mata a lokacin was blurry! a hargitse kuma yana rawa, ta kifta idonta a hankali don saita ganinta wajen kallon d'an k'aramin halittar dake gaban fuskarta yana d'igar jini.
Fatarsa mai d'umi ta manna akan tata yadda taji kamar tana rik'e dashi ne, jik'akkiyar fatarsa mai d'umi da tayi flooding wata irin nutsuwa zuwa ilahirin jikinta gabad'aya, idanunta suka yi focusing sosai akansa.
Baiyi kuka ba ko kadan sai numfashinsa dake fita da sauri kamar a tsorace yake, kansa sunkuf yake da yala-yalan gashin daya damule cikin jini... a k'asan jinin kuma wata irin fata ce mai tsananin kyau da haske, komai a cikin 'yar k'aramar fuskarsa was so perfect! da take jin kamar ba gaske bane, he was even more handsome than Imran tun a wannan stage din! duk da cewa kammaninsa sun fito a tare dashi amma idanunsa sak irin nata ne.
Wata irin nutsuwa ta sake kamata ganin cewa tunaninta, hasashenta, mafarkinta da kuma zuciyarta basu yi mata k'arya ba tsawon wannan lokacin, sannan wani b'angare na addu'arta ma ya karb'u, Her Baby was beautiful! yana da tsananin kyau kamar yadda kwakwalwarta ta ayyana mata tun daga lokacin d'in da ta fahimci cewa tana da CIKI.
"Alhamdlilah!" Taji ba abinda ya dace irin ta mik'a godiyarta ga ubangiji jalla wata Allah da ya karb'i roko da fatanta ya cika mata burinta.
A sannan ne kuma idanun Babyn suka d'auki hankalinta, kwayar idanunsa was familiar to her kamar ta tab'a ganinta a wani waje, ba tare da b'ata lokaci ba kuwa wannan mafarkin da take yi ya dawo cikin kanta.
Sanda fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye kamar lokacin baya akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sannan rik'e da wannan d'an karamin yaron fari tas! mai mutuk'ar kyau dake ta b'angala mata dariya.
Ta tuna da kwayar idanunsa sarai! iri d'aya ce data Babyn dake rik'e a gabanta yanzu, a hankali ta juyar da idonta kan hannun Imran dake rik'e cikin nata a lokacin, a b'ace yake gabad'aya da jinin dake fitowa daga jikinta, wanda har naso yake yana d'iga a k'asa. Ya salam! mafarkinta ne yake faruwa... mafarkin da ta dad'e tana turewa daga zuciyarta, mafarkin da bata tab'a d'aukarsa da wata daraja ba balle ya dame ta, mafarkin da bata san cewa shine hoton dake nuna k'addarar rayuwarta ba!
Da gabad'aya sauran k'arfin jikinta ta maida idonta kan Babyn but he was gone kafin ta iya sake ganinsa sosai! D'an kyakkyawan Babynta was snatched away, taji kamar tayi ihu a dawo mata dashi amma zafi da kuma jinin daya bullutso daga bakinta ya d'auke komai.
A cikin wannan azabar, a cikin wannan ciwon, a cikin wannan lokacin tunaninta ya gangara da ita can baya, lokacin data fara had'uwa da Imran, lokacin da ta fara ganinsa tsaye daga jikin wannan tsohuwar container ta dawo daga islamiyya, lokacin da ya fara shiga cikin tunaninta... wannan lokacin da bata san WAYE SHI ba, wannan lokacin da bata san komai game da rayuwarsa ba, wannan lokacin da zuciyarta ta fara sonsa ba tare da wani tunani ba, Sannan wannan lokacin da duk wani hargitsin rayuwarta bai faru ba!
Babu wani abu guda d'aya da taji zuciyarta tayi regretting yinsa tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu, saboda daga sanda da ta fahimci fara son sa, she knew she would follow him anywhere... and she have! kuma inda ubangiji zai sake dawo mata da komai baya, she beleived she would'nt change a thing! game da rayuwarta.
Imran k'addararta ne kuma tana sonsa, tana sonsa da dukkan ruhinta!
Ta san cewa a lokacin dukkaninsu a hargitse suke wajen ceton ranta daga yadda take jin ana tab'a kowacce gab'a ta jikinta da sauri da kuma k'ok'arin had'e yankan dake cikinta, da abubuwan da ake zura mata a baki da shigar tarin abubuwa cikin jikinta... amma kwakwalwarta bata d'auko mata dukkan hayaniya da maganganunsu, sai 'yan k'ananan abubuwan da bai kamata ace su take iya fahimta ba.
Tana iya k'irga kowanne sauti na fitar numfashin Imran dake kusa da ita, na Bwama da jaamil da yayi nesa dasu sannan 'yan k'ananan shallow numfashin da ta tabbata na Babynta ne, Tana iya iya jin faint k'arar A.C dake cikin d'akin, daga can kuma sautin k'arar wani abu, tana iya jin k'arar iskar dake kad'awa daga wajen gidan, tana iya jin fitar numfashi da kuma motsin abubuwa dake a can wajen...
Tana iya jin komai!
Tana iya jin komai d'in da bai kai muhimmancin bugun zuciyar Imran dake bugawa kamar zata fito daga cikin k'irjinsa a kusa da ita ba, Sannan tana iya jin komai d'in dake zamewa daga cikin kwakwalwarta kamar lokacin da mutum ke k'okarin rike ruwa a tafin hannayensa.
Bayan Second d'ari shida da tamanin da uku komai yazo k'arshe, komai yana nufin duk wani fata da burin rayuwarta!
Komai kuma yana nufin komai... sannan komai kuma yana nufin duk wata gwagwarmaya da k'addarar rayuwar SA'ADHA/NANNE!
***
Hannayen Imran rawa suke sosai sanda yake rik'e da wani abu da yayi kama da Allura wanda Bwama ta bashi da cewar ya cigaba da d'inke farkewar gefen cikinta yayin da ita ta koma k'ok'arin had'e fatar dake tsakiyar cikinta.
Idanunsa a jik'e suke sharkaf da baya iya gani sosai ta cikinsu sannan tunaninsa yana k'ara hargitsiwa ne da kowanne motsin dake faruwa a cikin d'akin, wannan sautin zuciyarta dake bugawa da k'arfi a k'asan hannayensa, luguden tasa zuciyar da ya d'auke concentration d'insa, sannan wata k'arar da bai san daga ina take fitowa ba.
Gabadaya kwakwalwarsa bata aiki a lokacin, kallon komai yake cike da rud'ani kamar dukkan tunaninsa ya gushe... don a yadda ya d'auka a baya ya fuskanci dubunnan tashin hankalin da bai san adadinsu ba, amma a yanzu ya tabbatarwa kansa wannan shine tashin hankali na farko da ya fara gani a rayuwarsa, koma a kira shi da wani abu da yafi hakan.
Ya damk'e hannayensa da k'arfi rik'e da allurar, wani irin karfi da yasa har k'ashin d'an karamin yatasansa na hagu ya b'alle.
A wannan lokacin Bwama ta fahimci cewa ba abinda ya iya k'arawa kan wanda ta bashi, saboda haka ta juyo da sauri ta karbi abin hannun nasa sannan ta bashi wani umarnin cikin k'arajin muryata.
"Waffa goure yelim! (pump her heart!Ka danna k'irjinta!)
Bai san ya akayi ya iya fahimtar hakan ba, watak'ila don hakan yana nufin wata direct hanya ne ta dawo mata da numfashinta, da sauri ya d'ora hannayensa akan k'irjinta ya shiga danna shi da dukkan sauran nutsuwarsa... it was harder! kamar jinin dake kwance a wajen ya daskare ne, wajen yayi tauri sosai.
Bai damu da zafin da karyayyen yatsansa keyi ba, hankalinsa ya tafi gabadaya wajen danna kirjin nata a hankali yadda ba zaiyi kuskuren b'alla shi ba, Bwama ta gama d'inke wajen sannan ta d'auko wani abu mai tsini da ruwa a ciki ta tsira shi a gefen hannun nata, Imran yana iya jin yadda jijiyoyin jikinta suka girgiza kamar shocking ya kamata.
Ki k'okarta Sa'adha, keep your heart beating!
Muryarsa ta fito da kaushi, da sanyi da kuma hasala, a mace take wannan karon babu wannan taushi da dad'in nata dake murk'ushe zuciyar Nanne, ya cigaba da danna hannayensa yayin da Bwama ta cigaba da sokawa da kuma had'e duk wani waje mai rauni a jikin nata.
Tun Imran na iya jin nauyin k'irjin nata har ya koma ya k'ame k'am! ya zama matacciyar d'agawa ce kawai ke biyo bayan hannunsa... amma bai daina ba, ya cigaba da pumping zuciyar tata while Bwama was working to put her back together.
Tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a falon sai fafutukar da Bwama da Imran keyi akan GAWAR dake gabansu!
Saboda abinda ya rage kenan, abinda ya rage daga karyayyen jikin Nanne dake kwance so still a gabansu, siffarta dake b'ace baja-baja da jinin jikinta.
Wa'adi ya cika, alk'alami ya riga ya bushe, Allah yayi hukuncinsa, Lalle ne kowacce rai lokacinta k'ayyadadde ne... Babu wani k'ok'arinsu kuma da zaiyi tasiri!
Amma duk da haka Imran bai daina danna kirjinta ba, ya cigaba da kokarin pumping iskar da bata da wani tasiri a jikin da ya zama gawa.
Ta mutu...
... ya sani.
Amma, ta mutu...
... bai yarda ba!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
59
(¡î_¡î)
K'arfe bakwai da 'yan mintuna na safiyar juma'a a cikin garin katsina, wayar Sulaiman ta shiga vibrating a kusa dashi, yaja tsaki a hankali cikin baccin nasa... don ya san kiran ba zai wuce na yazo ya kai 'yan makaranta ba in har an samu wani uzirin daga Idris direba.
Allah ya sani dole ne ma ya k'ok'arta a had'a aurensa dana 'ya'yan hajiya Babba Nasir da Muhammad da za'ayi cikin shekarar nan, don kusan duk wani responsibilty na gidan yanzu akansa aka d'ora, tunda ya d'auki annual leave d'insa bai samu ko kad'an ya huta ba, sunansa ne ke fara zuwa kwakwalwar kowa a duk sanda wani abun ya taso.
Yasa hannun ya jawo wayar zuwa kunnensa.
"Hello."
Daga d'aya bangaren muryar cikin wayar tace.
"Sulaiman kana gida koh?"
"Eh." ya amsa ransa a b'ace.
"Sunana jaamil, ni dan'uwan Imran ne mijin k'anwarka Sa'adha."
Jin haka yasa ya d'ago da kansa yana kallon silin kafin yace.
"Okay na gane.."
Muryar ta d'anyi shiru bata amsa ba, hakan yasa shi k'ara bud'e idanunsa sosai sannan yace.
"Ina sauraronka."
Kusan sakan talatin kafin muryar ta sake magana da wani irin tattausan amo da ya ratsa har cikin jijiyoyinsa.
"Sulaiman, Sa'adha ta rasu jiya da daddare wajen haihuwa, a yanzu haka muna hanya tare da gawar tata zamu iso nan gida, ina maka ta'aziyya kafin k'arasowarmu."
A cikin abinda baifi kiftawar ido ba Sulaiman yaji tunaninsa ya zille daga cikin kwakwalwarsa ya rataye a iska, Mutuwa? Nanne ta mutu? Wace irin Mutuwa? Nannen da jiya ya shiga wajen Inna yaji suna waya da ita?
"Dan Allah malam ka gaya min gaskiya, wace Sa'adhan kake nufi?"
"Babu wanda yake wasa da mutuwa sulaiman, ba zan taba kiranka in maka karya ba Sa'adha k'anwarka nake nufi, Allah ya amshi ranta jiya wajen haihuwa, muna...
Bai ji k'arashen zancen ba saboda ya kasa gasgata kunnunwansa, ya kasa gasgata al'amarin, ya kasa gasgatawa wai da gaske Sa'adhan/ Nannen da yasani ce ake gaya masa ta rasu, rasuwa ta mutuwa irin wadda in ta kasance mutum ya tafi kenan har abada!
Hannunsa dake rik'e da wayar ya shiga rawa lokacin da muryar wanda ya kira kansa da jaamil ke cigaba da bayani wajen gaya masa cewa ya taimaka yayi wa su Baffa bayani cikin nutsuwa kafin k'arasowarsu, Nutsuwa? wace irin nutsuwa ke tattare da labarin mutuwa?
Sai ya ajiye wayar ya d'ora hannayensa aka kawai ya shiga rero Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un!
Yanzu wa zai tunkara da wannan labarin? Baffa zai samu yace masa 'yarsa ta rasu ko kuwa wajen inna zai je ya gaya mata Nannenta ta mutu? wannan wane irin sak'o ne ya rataya a wuyansa haka? yaji kwalla ta cika idanunsa lokacin da tunaninsa ya cakud'e ya rasa madafa, sai kawai ya janyo wata T-shirt dake gefensa ya d'ora akan wandon shaddar jikinsa sannan k'afafunsa suka nufi d'akin hajiya Babba, bai ko tunkari na mahaifiyarsa ba don ya yardarwa kansa cewa wannan aikin na manya ne, a yanzu Hajiya Babban ce kad'ai zata iya samun Baffa da wannan hargitsatstsen bayanin.!
****
Kafin k'arfe takwas na safiyar ranar, labarin rasuwar Sa'adha yayi tambari a cikin unguwarsu, haka nan kuma ya cigaba da watsuwa kusufa-kusafa na garin Katsina, sannan gidan ya fara cika da 'yan uwa da kuma mak'ota na kusa wanda hakan ya dad'a sanya hargitsi a zukatan al'ummar gidan.
Lokacin da motoci uku nasu Imran da kuma su ya Ahmad da suka je taro su suka k'araso cikin gidan, hawaye ko d'igo bai fito daga idanun Baffa sai sannan, sai a lokacin da ya d'aga ido yaga manyan 'ya'yansa na kiciniyar fito da gawar daga cikin mota, ya kalla yaga wai yau Nanne dake dake zagaye gidan da kafarta ce ake d'aukowa babu numfashi kuma babu wani abu dake motsi a jikinta, jikinta sanye da doguwar riga kamar zasu sauke ta ne ta taka da k'afarta duk da cewar an rufe fuskarta da hijabin kanta. Yaji wani sabon Imani ya shige shi sai ya shiga salati yana k'ok'arin maida kwallar dake shirin tunkud'uwa daga idonsa.
Wai Sa'adha ta tafi a yau, Sa'adha mai tsananin biyayya a gare shi, ta tafi a k'ananan shekaru masu cike da k'uruciya, ta tafi bayan tayi masa biyayyar da yake ganin ya tauye wani b'angare na rayuwarta...
"Allah ya jikanki Nanne, Allah ya yafe miki kurakuranki, Allah ya baki Aljannatul firdausi mad'aukakiya, Allah ya ingata shahadarki, Allah ya shafe zunubanki, Allah ya kyautata aiyukanki na alkhairi, Allah ya karbi ruhinki cikin daraja, Allah ya kyautata zuwanki, Manzon tsira ya karbi bakuncinki, Allah yasa mutuwar ta zamo hutu a gareki, na yafe miki duniya da lahira, Allah yayi miki rahma da gafararsa...."
K'okari yake kar hawayensa ya fito a gaban 'ya'yansa, kar ya fiddo da raunin da zai haddasa karyewar zuciyarsu alhalin yana iya ganin tsananin dauriyar kowannesu a cikin idonsu.
A lokacin kuma gidan ya k'ara rud'ewa, mata suka shiga kuka mai d'agawa kamar a da suna tunanin jiran da suke zai zo musu da wani abun ne sab'anin hakan.
Aka shiga da gawar Nanne har cikin d'akinsu ita da inna, Innar da a lokacin bata cikin haiyacinta, tun bayan shaida mata labarin da akayi take ta hailala mai cike da maganganu, maganganun da suke nunawa tar! cewa bata cikin haiyacinta, don har fad'i take cewa Nanne bata mutu ba watakila tayi bacci ne kawai a mota kuma zata tashi da zarar sun kawo gida, sai dai duk da wannan sambatun harshenta na kiran Lailaha ilallahu muhammadur rasululahi duk sanda ta juya taga irin kukan da mutanen dake gewaye da ita keyi, tana yi tana fad'in.
"Na gaya muku ku bar fidda hawayenku, ba dai ance suna hanya ba? da sun iso zaku ganta garau... Azumi ki gaya musu mana ba jiyan nan nake ce miki munyi waya da ita ba? har nake gaya miki tace zata sake kirana bamu gama magana ba tace tayi bak'i? Ke Halime dauki wayar mana ai zaku ga lambarta a ciki..."
Lokacin da aka shigo da ita cikin d'akin, da saurinta ta kwace hannayenta dasu Mama Azumi ke rik'e dasu ta rarrafa ta bud'e fuskarta dake lullube da hijabin, kyakkyawar fuskar Nannenta da ke fes! cike da annuri da kuma alamun nutsuwa irin ta mai bacci, kamar za'a kira sunanta ta bud'e wad'annan fararen idanun nata ta amsa.
A lokaci guda ta d'anyi sororo tana kallonta, kamar mai son lalubo wani abu nata daya fad'i akan fuskar, amma ba wani abun take son lalubowa ba face fahimta da tayi cewa babu alamun rai a tattare da ita, babu rai a jikin Nannen da take mutuqar so a rayuwarta, Babu rai a jikin Nannen da taci burikka da yawa akanta, Babu rai a jikin Nannen da taci burin ganin 'ya'yanta na yawo a tsakar d'akinta, Babu Nannen da taci burin ganin ta samar mata rayuwa mai kyau da inganci, Babu Nannen da take tsananin so fiye da 'ya'yan da ta haifa a cikinta! Sai kawai ta hau girgiza kafad'unta tana fad'in.
"Da gaske suke kenan? Da gaske ne abun da suke fad'a kin mutu? Ta yaya zaki mutu a yanzu? Don kawai jiya mun yi waya na gaya miki k'anwar iyan shehu ta rasu wajen haihuwa sai kema ki mutu? Ki dubi girman Allah kiyi hakuri ki tashi wallahi ba zan kara gaya miki zancen mutuwar kowa ba, wayar ma zan yar da ita, ke da kika ce min watan gobe zaki taho gida haihuwar? ina nan ina tanada miki kayan wanka, me yasa zaki haihu yanzu? me yasa zaki haihu ki mutu Nanne? me yasa zaki mutu da k'uruciyarki bayan nice tsohuwa? me yasa zaki tafi ki barni? me zanyi da rayuwar....."
Bata kai k'arshe ba idanunta suka juya luu sai kuma ta tafi ta fad'a kan jikin nata... nan d'akin ya kara rud'ewa aka d'auke Inna zuwa cikin d'aki, yayin da Ya Ahmad ta koma motarsa da sauri don d'auko first aid box d'insa, Kafin ya kai ga dawowa Rahma wadda tana shigowa tayi ido hudu da gawar ta fad'i itama.
Haka waje ya k'ara rudewa cike da alhini da kuma tashin hankali, Ya Ahmad ya dinga zarya tsakanin Inna da Rahma don ceto nasu ran, yayin da mutane suka cigaba da cika a gidan, musamnan maza kowa na son samun sallar jana'izar da ake shirin yi.
Duk wannan abin da akeyi,