Showing 27001 words to 30000 words out of 113985 words
tunani inna ta amsa.
"Wa'alaika salam, har ka dawo? Sannu da zuwa."
"Eh na shigo wallahi, munyi waya da sulaiman ne yake gaya min ta farka shine nace bari inzo inga jikin nata."
Muryar ta sake ratsa kowacce kusurwa ta d'akin, cikin amonta a hankali, Nanne ta bud'e idonta da sauri ta kalli bangon dake fuskantarta, A lokaci d'aya tunaninta ya dawo mata da sanda taji muryar ta kira sunanta kafin idanunta su rufe, da kuma muryar imran sanda suka yi magana har sau biyu.
Da gaske Rahma take kenan, da gaske ne shine ya kad'e ta ba wani, ta yaya k'addara zata sake had'a ta dashi a haka?
"Ai wallahi da kayi zamanka ma sai gobe ka shigo, don tunda ta farka ba kukan ciwon da take, da alama abun da sauki ba kamar yadda muka zata ba."
Taji numfashi ya zarce cikin kirjinta sanda ya sake magana.
"Toh Alhmdlilah, Allah ya k'ara afuwa."
"Ameen Ameen, k'arasa wajen gadon ku gaisa ai inajin idonta biyu."
A daidai lokacin Aunty maryama ta gama wayar da take, ta mike daga kujerar da take kai sanda ya karaso suna gaisawa. Sai kuma ta sunkuyo daidai kunnenta tace.
"Sa'adha juyo ku gaisa, mutumin d'aya hadu da tsautsayin buge ki ne."
Nanne taji duk wani silin gashi na jikinta ya mike tsaye, ta gyara zaman d'ankwalinta a hankali sannan ta juyo, k'amshin turarensa ya cika mata hanci sannan zuciyarta ta k'ara girma a cikin kirjinta.
Yana nan dai yadda ta sanshi, yadda ta fara ganinsa, yadda take hango shi daga nesa da kuma yadda ta ganshi ranar da ya shigo har gidansu. Shi kad'ai amma kwarjininsa ya cika ko'ina na dakin. Taji ta zama wata 'yar mitsitsiya a gabansa.
"Sannu Ya jikin naki?" muryarsa kamar yana rera magana ne.
Ta had'iye wani abu a cikin makogwaronta kafin ta iya amsawa.
"Da sauki, bana jin kowanne ciwo." amsar da take fad'awa kowa kenan.
Ya kalli kumbuarriyar k'afar tata sannan yace.
"I'm sorry, tsautsayi ne ya riga ya faru amma banso muka k'ara had'uwa a haka ba."
Idonta ya kai inda Aunty maryama ke tsaye sai taga bata nan, gwara da Allah yasa hakan, don baza ta so daga baya ta tsare ta da tambayar yaya akayi ya santa ba.
Amma duk da haka sai ta kasa amsawa, saboda kamar yadda ya faru ne sau biyu a baya, sanda ya fara mata magana da kuma sanda ya shigo gidansu, ji take yi ta takura a gabansa, balle kuma yanzu da yana tsaye a jikin gadon da take ne, babu wata tazara tsakaninsu.
"Allah ya k'ara miki sauki, na tabbata kafarki zata warke nan da k'ank'anin lokaci."
Ya tabbata? Shi likita ne dama? Abinda inna ke nufi kenan da tace yana tsaye akayi mata komai? Ko shi yasa ma maganarsa take da sanyi da taushi? Tunda ance da baki ma likita kan warkar da mutum.
Kamar ya karanci zuciyarta sai taji yace.
"Ni ba likita bane, daga dai yadda kika ce bakya jin ciwo ne, kowa zai iya cewa da alamun sauki."
Ta gyad'a kanta alamun ta fahimta.
"Ina k'awarki? Da safe tana ta kuka anan."
"Rahma?" ta tambaya kai tsaye don ta san itace.
"Sun tafi gida sai gobe kuma."
Daidai sannan nurse d'in ta murd'o k'ofa ta shigo.
"A'ah sauki ya samu kenan, har ana hira haka?"
Ta fad'a da dariya sanda ta nufo gadon.
"Alhmdlilahi ai, taji sauki kam." Aunty maryama ta taso daga gefen inna tana fad'a.
Ganin haka yasa Imran ya d'an ja baya kad'an sannan yace.
"Toh ni zan tafi Aunty, sai gobe in Allah ya kaimu, Allah ya kara sauki."
"Toh mungode fa, mungode Allah ya kaimu."
Nanne ta juyo ta kalle shi sanda ya tsugunna yana wa inna sallama.
"Da fatan bakya kukan Allura don ita zamu yi yanzunnan."
Nurse d'in ta fada sanda ya d'ago shima ya kalleta, kawai sai tayi murmushi ta juya d'aya gefen.
*****
A cikin sati d'aya da kwanaki, Nanne ta maida 'yar k'ibar jikinta data rasa a baya na rashin lafiya, mutane suna ramewa a asibiti amma banda ita, don ciwo kanta baya mata balle kuma k'afar da aka daure, sannnan ga kulawa da take samu kota wane b'angare.
Sai dai ranar da aka fara mata dressing da taga wani dogon yanka a kafar tata, ga kuma k'ashinta yana lilo, ita kanta ta tsorata ace bata ji ko d'igon zafi a wajen. Su kansu likitocin suka rikice da tunanin ko wajen ya zama paralysed ne amma duk yadda aka taba tana ji, saboda haka a next dressing suka gaiyato wasu likitocin akayi ta bincike akanta, sai daga baya suka tsaya kawai akan cewar jijiyoyin wajen ne suka daina aikin d'aukar zafi zuwa kwakwalwarta.
Suka kira Baffa da zancen za'ayi mata aiki a wajen amma ba wanda ya san ya amince ne ko A'ah, don sadiq da yazo ya gayawa Nanne cewa yaji su ya ibrahim na fad'in wai ba zancen aikin kad'ai suka yi masa ba.
Ita kam! tun lokacin da taji ance jijiyoyinta ne suka daina aiki ta hutar da kanta da tunani. Fatanta ma kar su dawo da aikin don ba wanda ke son ciwo. Shi yasa ma da taji baffan baice komai ba ta mike k'afafunta ta cigaba hutawarta.
A cikin kwana biyar imran yazo sau hud'u. Kuma a duk sanda yazo gaisuwa zata shiga tsakaninsu har da 'yar hira. Shi yasa a kullum take tashi da kwarin gwiwar ganinsa. Wanda itama a lokacin bata san me yake faruwa game da ita ba, bata iya wani tunani mai kyau ba tare da fuskarsa ta shigo ba. Da gaske ne abinda Rahma ta fad'a ya kamata ta tambayi zuciyarta me take nufi? Me take nufi da yawan damuwarta akansa?
Amma ya zata yi? Fad'ar manzon Allah ce cewa zuciya na son wanda yake kyautata mata, tun da aka kawo ta asibitin nan, daida da kud'in magani Imran bai bari sun biya ba, yace shi yayi laifi kuma alhakin komai na wuyansa, saboda haka kullum 'yan uwanta da ita kanta cikin ganin k'ok'arinsa suke, a gefe d'aya kuma zuciyarta na k'ara rugurgujewa da tunaninsa.
Kullum tana tashi da fatan cewa zai baiyana a d'akin da zarar ya dawo daga aiki, da wannan annurin fuskar tasa mai k'ara masa kyau da kwarjini, hakan yasa ba'a tab'a karanto gajiyarsa, a kullum ka ganshi, zaka iya rantsewa a lokacin ya fito daga wanka bayan ya tashi daga baccin hutu.
A cikin sati biyu kawai, Nanne ta yardarwa kanta ta fad'a cikin yanayin da bata taba kawowa kanta ba. Yanayin damuwa da wani bayan harkokin gabanta, ta ayyana a ranta abubuwa baza su taba dawo mata daidai ba. Rayuwarta baza ta taba komawa kamar da ba, don ta d'auko wani abu ne da ba zai tab'a faruwa ba.
Ta fahimci cewa ta fad'a son IMRAN, ta shiga k'aunarsa ba tare da sanin me take yi ba!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
20
(¡î_¡î)
Iyaye....
Wasu mutane ne da Allah ya hallice mu daga b'angare na jikinsu, soyayayarsu wani abu ne da tun farkon halitta aka manne jikinmu tare da ita, shi yasa komai irin halinsu, komai tarin laifinsu, akwai wannan d'igon k'aunar da zai sa kaji cewa kaga wani naka. Nakan da har abada baza ka tab'a samun irinsa ba.
Nanne ta tsirawa matar dake gabanta ido, matar da ta ajiyeta tun bata kai shekara guda a duniya ba ta kama gabanta da sunan aure. A kullum ta ganta sai ta nanatawa zuciyarta wannan laifin, don ta samu ta iya jin haushinta ko sau d'aya ne amma ta gagara hakan, duk sanda ta ganta sai zuciyarta ta tsinke, gwiwoyinta suyi sanyi, taji kamar taje ta rungumeta ta lalabo duk wannan k'auna da d'umin uwar data rasa a baya.
Suna zaune ne daga cikin bedroom d'insu, a lokacin anyi wani ruwa mai yawa an d'auke. Saukarsu kenan daga adamawa ana dab! da fara ruwan.
"Inata magana kamar kina tunani, duk sunce a gaishe ki."
Ta sunkuyar da kanta a hankali sannan tace.
"Ai ban sansu bane Addano."
Ta kira ta da yadda taji 'yanuwanta na kiranta duk lokacin da taje.
Ta d'anyi tsaki kad'an.
"Shi yasa nake ta nacin a kawo ki ai, kwanaki nayi aike ya kai sau uku daga ace min baku yi hutun makaranta ba, sai a bada uzurin wai za'ayi biki a gidan ne."
"Da gaske ne ai, anyi bikin su yaya Aisha kwanakin baya."
Bata ce komai ba sai ta juya ta kalli k'afarta da a yanzu aka kwance sannan tace.
"Ance bayan karayar wai akwai wani ciwon ma koh?"
"Eh bayan anyi aikin ne bana jin zafi a wajen, shine likitocin suka yi bincike suka ce jijiyoyin k'afar ne keda matsala, suka yi magana da baffa akan za'ayi aiki a wajen."
"Ya yarda kuma?"
Ta girgiza kanta. "Bai yi magana ba dai tun bayan nan."
"Ai gwara a kyale ki, in waje ya warke me yasa kuma za'a tafi neman wani ciwon."
A sannan wata mata da suka zo tare ta shigo rik'e da 'yar karamar 'yarta da take goyo. (k'anwar nannen kenan.)
"Addano gata ta tashi yanzun nan."
Ta mik'o mata yarinyar wadda ke ta mutstsuka ido, nanne ta kalleta, k'anwarta a suna amma bata ma san sanda aka haife ta ba, 'yar kyakkyawar bafulatana da ita, mai dogon gashi kamar nata. Sai dai kuma an b'ata fuskarta da bille. Ta kai hannu ta tab'a 'yan kafafuwanta.
"Yaya sunanta?"
"Miryam. Koda haihuwarta ai na aiko kizo baffanki yace jarabawa kuke."
Bata ce komai ba ta cigaba da murza k'afar yarinyar.
"Gobe in Allah ya kaimu da safe zamu koma."
Sai ta d'ago ta kalle ta. "Baza ku biyo ta nan ba kenan?"
Nuratu ta girgiza kanta.
"Toh ai basu fad'a min da wuri ba, sai shekaranjiya fa aka aika, kuma gobe Babansu miryam zai dawo daga china. Kinga dole in koma da wuri."
Sai ta gyada kanta kawai tayi shiru. Don mijin nata d'an kasuwa ne dake yawan tafiye-tafiye, bai cika zama a gida.
"Nanne wai ajinki nawa ne?"
'SS3...wannan shekarar zamu gama insha Allah."
"Toh meye a ranki game da nan gaba, kema karatun zaki biye musu kiyi, koko zaki rufawa kanki asiri kiyi aure?"
Kalmarta ta k'arshe taso bata dariya, tayi aure a yanzu? Toh ta auri wa?
"A'ah zan fara karatun dai, idan auren yazo ina cikin yi, sai ayi."
Nuratu tayi ajiyar zuciya kafin tace.
"Na san dama sun cusa miki irin ra'ayinsu, idan zan baki shawara a matsayina na mahaifiyarki kuma ki d'auka, gwara kiyi aure tun yanzu ki samarwa kanki 'yanci. Karatu zaki iya yinsa koda aure goma akanki, kuma shine ma zaki fi yinsa cikin 'yanci."
Tayi shiru tana juya maganganun. Ba wai tana shirin yarda dasu bane, don ta san abu ne mai kamar wuya saboda haka sai kawai tace.
"Toh Addano ni a yanzu ma ba wanda nake kulawa ai."
Ga mamakinta, sai taga ta fuskanceta sosai, sannan ta gyara zaman miryam dake kan cinya tana shayar da ita.
"Wannan ba matsala bane Nanne, dama akwai zancen dana taho dashi tun daga gida, idan kin amince zan turo d'an wata yayata Nura, yaro ne mai hankali kuma shima d'an boko, don har ya gama karatunsa ma yana aiki a cikin adamawa, na tabbatar miki in kika amince dashi zaki ji dad'i nan gaba, kuma ta hanyarsa zaki dawo cikin 'yan uwanki."
Nanne taji kanta ya daure ta kasa fahimtar farko da k'arshen zancen, amma abun da yafi daukar hankalinta da tace zata dawo cikin 'yanuwanta.
"Addano wadannan su ba 'yanuwana bane?"
"Yan uwanki ne amma bana uwa ba, kuma ke mace ce, duk girmanki dangin uwa sune martabarki, yanzu ki duba fad'in gidan nan kaf! Duk randa akace babu ran inna wallahi ko kinyi aure kika zo sai dai kiyi ta kame-kamen wajen zama. Amma inda cikin 'yanuwana kike sai inda kike so zaki jefa k'afarki."
Tayi shiru kawai tana jinta, don ta san abinda take fad'a wani abu ne da ba zai tab'a yiwuwa ba, ita a yanzu kwata-kwata ma harkar aure bata cikin lisaafinta, abinda ke gabanta daban ne.
Kuma ko zata yi auren ma, ba zai yiwu da wani wai shi Nura ba, mutanen da basu santa ba, basu damu da saninta ba, sai a yanzu ne zata yi musu amfani?
Baza ta iya musa mata ba, sai kawai ta dinga binta da kalmar toh, a k'arshe kuma tace mata zata yi tunani, ita kuma tayi ta jaddada zancen akan ta kira ta duk lokacin da ta gama amincewa zata turo Nuran. Da haka aka zo d'aukansu daga can gidan da zasu kwana bayan garin ya d'an sha.
Bayan sallar magriba Nanne ta kwanta akan bargon inna dake shimfide a k'asan window na falo, yanayin garin na yadda iskar damina mai sanyi take kad'awa da kuma k'anshin jik'akk'iyar k'asa ya taimaka mata wajen ture duk wani tunani a kanta, ta janyo abinda ke cin ranta. Tunanin Imran!
Tun bayan sallamarta da akayi daga asibiti sau biyu kawai yazo, na farko ma bata ganshi ba tana bacci. Sai a na biyu shi kuma bai dad'e ba yana ta sauri. Gashi har yanzu bata fara fita ba balle ta ganshi a hanyar islamiyya.
Kuma a kullum, a kowacce rana tana jin zuciyarta ta k'agu da son sake ganinsa. Sai a yanzu take sake tabbatar wa kanta da gaske son Imran take, kuma ba tun yanzu ba, tun ranar data fara ganinsa ta kasa manta shi, har zuwa yanzu da komai ya cakud'e mata.
Ta san koda ta ganshi d'in ma, ba abinda zai faru ko ya canja, sai dai ta k'ara d'aukarwa kanta wahalar da zuciyarta ta jawo mata. Wahala mara yankewa, wahalar da a 'yan shekarunta bata san zata fad'a ba.
Wani b'angare na zuciyarta ya fad'a mata cewa ta taimakawa kanta tun yanzu ta cire imran daga ranta, donshi matsayin daya d'auke ta daban ne. Ya taimaka mata a farko kuma ya taimaka mata a yanzu da tsautsayi ya had'a su, kuma babu komai bayan hakan. Amma duk sanda tayi wannan tunanin sai maganar daya tab'a fada mata tazo ta ture komai.
"Abubuwan dana sani game dake, suna da yawa...."
Ko ba komai akwai lokacin da shima ya damu da ita.
Ta lumshe idonta a hankali tana kallon yadda iska ke turo labulen windon, su inna na daga gefenta suna firfito da kayan da Nuratu ta kawo ana gani. A lokacin ne rediyon inna dake kunne ta fara playing wata wak'a sakamakon gama wani shiri da akayi.
....Sitting wide eyes open behind this four walls hoping you'll call,
It's just a cruel existance i guess no point hoping at all.
Baby, Baby..
I feel crazy, up all night! All night!
Everyday, you give me something...but you said nothing.
Whats happening to me?!
(if u can relate dix moment, Allah muku albarka!)
*****
BAYAN SATI DAYA.
Tana zaune tana jiran isowar Rahma, yau a gidan zata kwana don haka ta tafi siyo musu wainar fulawa a can bayan layinsu, inna ta fito daga d'aki sanye da hijabinta a karkace.
"Baffanku ne ke kiranmu tare dasu hajiya, da sune ma zasu zo nan nace A'ah gwara mu zauna a can falon nasa."
Haka kawai Nanne taji gabanta ya fad'i ta juyo ta kalli inna.
"Ke dasu hajiya? Har dasu mama rabi kenan."
"Eh mana da duka matan nasa, na san dai wani abun ne ya taso, in ba haka ba yaushe rabon da ayi irin wannan zaman...tun lokacin da tsautsayin nan ya fad'a kan muhammad daya kad'e yaro a mota."
Nanne ta tuna lokacin, ya muhammad na wajen hajiya babba ne ya tab'a kad'e wani yaro a mota bisa kuskure, abinda yasa bata manta ba saboda azumin da yayi tayi har sittin, kullum su mama Azumi suyi ta hidimar kayan shan ruwansa. Tabass kafin baffa yayi irin wannan kiran sai abu mai muhimmanci ya taso tukunna. Ta had'iye yawu cikin makogwaronta sanda inna tayi hanyar k'ofa.
"Inna ki gyara hijabin naki."
Bayan kamar minti biyar Rahma ta shigo d'auke da leda da kuma faranti.
"Na dad'e ko? Wallahi layi ne da ita kamar me."
Ta sauko k'asa ta karbi plate din. "Baki ma wani dad'e sosai ba...juye mana ita a ciki."
Rahma ta zauna tana zubawa. "Kin san har na taho na tuna bata bani yaji ba, saida na koma."
"keh na tuna Amina ta bani wani flash da film d'in india a ciki, bari in d'auko in sa mana."
Ta tashi da sauri ta nufi d'aki, da fatan film d'in zai d'auke mata hankali daga tunanin dalilin meeting d'insu inna, don haka kawai take jin jikinta wani iri.
Ta dawo, tasa flash d'in a jikin TV sannan suka zauna cin wainar. Sai dai tana kai lomar farko bakinta, sadiq ya d'age labulen d'akin ya shigo.
"Ai tunda naji dama kina cewa anan Rahma zata kwana na san wani abin kuka shirya, wato ga waina fulawa mai zafi da zob'o ga kuma TV kunsa a gaba."
Nanne tana kallonsa tace.
"Kai kuma gulma na cinka sai kazo kaga me akeyi...Rahma dan Allah san masa ya bar nan wajen."
Ya tab'e baki.
"Allah ya kiyaye inci wannan abar, ni baffa ne ya aiko ni yana kiranki."
A lokaci d'aya taji k'arar wani abu ya tarwatse a k'irjinta, shikenan abinda take tsoro ya faru, akanta za'ayi meeting d'in nan shi yasa dama tun d'azu jikinta ya bata.
"Da gaske kake dan Allah?"
Ya langwab'e kai ganin ta tsorata a lokaci d'aya, ya sami abinda yake so.
"Da gaske nake 'yan mata, kije ki girbi abinda kika shuka."
Ta d'auki kofin robar dake gabanta ta jefe shi dashi, yayi saurin kaucewa sannan ya fita yana dariya.
Sanda ta tura k'ofar falon baffa ta shiga da sallama, jikinta gabad'aya yayi sanyi sannan zuciyarta ta sallama cewa duk abinda zai faru bai zai mata dad'i ba kuma dole ne ta karb'e shi hannu biyu, tunda wad'anda ke cikin d'akin sune da iko da ita da kuma duk wani abu nata.
Inna tana zaune daga k'asan labule hajiya Babba na gefenta, sai Aunty Amarya, mama halime da kuma mama rabi.
A d'aya gefen, ya Ahmad ne da ya ibrahim wanda bata san yaushe suka zo daga gidajensu ba, sai kuma sauran, ya sulaiman, muhammad, ishaq, Nasir da kuma ya umar. 'yan biyu ne kawai basa nan, inda ta fahimci daga kansu aka tsaya kenan. Toh me zai sa a tsallake su, a tsallake sadiq a taho kanta?
D'akin ya mata girma, ta rasa inda zata zauna sai da Baffa dake tsakiya ya yafito ta da hannu ya nuna gefensa. Ba yadda ta iya haka ta tsallake kowa ta nufi inda yake zaune a k'asan kujerarsa.
"To tunda kowa yazo, Babban yaya sai kayi mana addu'a koh." ya fad'a yana kallon yaya Ahmad wanda yayi d'an murmushi kafin ya fara.
"Salati goma ga Annabi(SAW)...."
Har aka shafa Nanne bata tabbatar duk abinda aka fad'a tayi dukka ba, don zuciyarta lugude kawai take kamar wadda tayi