Showing 15001 words to 18000 words out of 113985 words
wayar taci karo da hoton Suraj tar! akan screen d'in. Wani hoto da salim ya dauke shi a jikin motar ya Ahmad, a ranar sati biyu kenan da bikinsa sunje gidansa gabad'ayansu ganin Amarya.
Amina ta sunkuyo da kanta kad'an tace.
"Ba suraj bane wannan?" Nanne ta mika wa yarinyar wayarta.
"Eh na sanshi anan gidan yake."
Da jin haka ta juya ta kalli sauran k'awayen nata biyu.
"Kun ji koh? Na gaya muku wallahi shine...." ta dawo kan nanne.
"Dan Allah yaushe ya dawo daga cyprus d'in?"
"Wace cyprus?"
"Inda yake karatu.."
Nanne ta kalli Amina suka kyalkyale da dariya.
"Shi yace miki a cyprus yake?"
"Eh mana ba'a can yake karatu ba?" d'aya kawar ta tambaya.
Nanne tayi k'okarin danne dariyarta.
"Tsaya ma tukunna wane karatun?"
"Degree mana..." Aiko bata k'arasa ba suka sake fashewa da dariya.
"Dan Allah tambayarku fa muke..."
Basu ko kulasu ba saida suka kyakyata mai isarsu sannan da kyar Aminah tace.
"Yi hakuri, wallahi k'arya yake muku, kwanan nan suka gama waec da neco a makarantar mu."
"Ke toh anya kuwa shine, shi fa har facebook account dinsa gabad'aya komai na can ne."
"Ai shine..." d'ayar ta karba.
"...Ba kince mana harda outside number yake kiranki ba?"
Nanne ta kalle su tace.
"Wallahi duk karya ce, in gaya muku nan ne gidansu kuma ni k'anwarsa ce, in baku yarda bama kuzo in kaiku ku gaishe da Babarsa."
"Dan Allah da gaske kike?"
Ta sake kyalkyalewa da dariya kafin tace.
"Wallahi da gaske nake muku, d'azun nan ma ya gama fito da kayan wankinsa akan barandar can, ga d'akinsu can a kulle."
Ba shiri kuwa suka matso da kujerunsu kusa dasu. Yarinyar tace.
"Shifa ce min yayi a Abuja gidansu yake, toh d'azu da muka je sallah a cikin gidan sai naga wani family hoto a d'akin da muka shiga, harda wani a ciki kamar shi, muka yi ta doubting, shine fa na tambaye ku."
Tana maganar kamar zata yi kuka, Nanne na k'ok'arin matse dariyarta amma ta kasa saboda Amina data sunkuyar da kai tana ta kyalkyalawa tana mintsininta.
"Dan Allah ku bar dariyar nan, kuyi magana mana..."
"Yo me zamu ce? Karya ce dai ya riga ya tafka muku, don wallahi makarantar daya gama ma a tsakiyar garin nan take ba wani waje ba, kuma ko result d'in waec d'insu bai fito ba balle ya tafi wata jami'a, kullum suna gidan nan shi da twin brother dinsa, in banda bacci ba abinda suke sai yawo..."
Tun suna dariyar su biyu, har k'awayen yarinyar ma mai suna Ameerah suka bi sahun su, aikuwa basu rabu dasu ba sai da nanne ta sauke musu duk wani in and out na Suraj data sani, harda kuwa abinda yayi tun yana k'arami data ji labari.
Bayan sun rabu dasu, suka matsa wajen rumfar amaren Aminah tace zata dauke su a hoto, suka yi hotuna kuwa masu kyu abin mamaki jamila sai washe musu baki take, lalle buri ya cika an samu abinda ake so, Nanne ta ayyana a ranta.
Suna fitowa daga wajen, wayar Aminah tayi kara.
"Anzo d'auko ta, sa'adha ba zanzo kamu gobe ba sai jibi ranar mother's eve."
"Toh shikenan, bari in d'auko miki dankwalina ki taho min da mayafi kalarsa a wajen Aunty maimunah (yayar Aminan)."
"D'an 3 thousand ko 5?"
"Three d'in dai, an gaya miki kudi ne dani."
"Toh yi sauri don Allah hashim azalzala ce dashi wallahi."
"Kije wajen motar, zan same ki acan."
Ta cikin tarin jama'a da kuma kujeru nanne tayi ta kutsawa har taje can k'arshe wajen fulawoyi inda inna ke zube akan carpet da jama'arta 'yan tsofaffi wanda basa iya hawan kujera.
Da kyar ta samu innar ta saurareta saboda jama'ar da suka yanyanmeta anata gaisuwa da Allah sanya alkhairi.
"Inna muk'ullin wardrobe zaki bani."
"Me kika ce?"
"Mukullin wardrobe wanda nasa a jakarki d'azu."
"Yana ina?"
"A cikin jakarki, na saka d'azu."
Ta miko mata 'yar purse d'in hannunta gabadaya, ta d'auka sannan ta mika mata. Da kyar ta iya tsallake su ta wuce, saboda kowa duk'awa kawai yake ana gaida 'yan tsofaffin.
Daga cikin gidan, sautin kid'an kad'an ake ji sannan ba mutane sosai, daga wajen kicin ne kawai da mutane suma kad'an. Har zata hau benen ta gano rahama da wata sun jawo buhun takeaway d'in sabulun salo,magarya da kuma turaren wuta wanda za'a rabawa mutane. Tausayinta ya kamata don wallahi tun yanzu ta san rahma ta gaji, sun aikatu sosai, ga kuma biki yanzu aka fara. Ta hango ta itama.
"Nanne akwai na k'awayenki dana ajiye a kicin, bari mu kai wannan in d'auko miki."
"Kinga ni mutum daya fa na gaiyata, kuma yanzu zata tafi ma, miko min d'aya kawai."
Ta jikin hannun benen ta miko mata sannan suka yi gaba.
Tun daga k'ofar d'akin nasu ta jiyo karar tv na tashi, mamaki ya kamata don ta san tunda satin bikin nan ya kama ba wanda yake kunna tvn. Ta d'an ja tsaki.
Watakila ma yara ne, tunda kowacce ta jajibo 'ya'ya anzo an cika musu gida.
Ta k'arasa ta kashe ta sannan tayi cikin d'aki. Ta bud'eshi da mukulli don shi a k'ulle yake saboda sha'anin biki, ta kunna fitila sanna ta bud'e wardrobe d'in ta shiga laluben d'ankwalin a wajen sababbin kayanta.
Kawai sai jikinta ya bata alamun wani ya shigo cikin d'akin yana tahowa wajen wardrobe din. Ta rufe murfin ta juyo, sai dai me? Babu kowa.
Ta d'an tsaya da mamaki sannan ta sake bud'e wardrobe din. Sai dai hannuta na kaiwa kan d'ankwalin ta sake jin alamun mutum na tahowa, ta tsaya tayi shiru tana saurare, sai da taji motsin ya karaso dab! da ita sannan ta sake rufe wardrobe d'in da wani irin sauri ta kalla.....
Irin dai d'azu babu kowa ba alamun mutum, sai dai kuma idonta ya kula da kofar d'akin tana lilo a hankali. Ta janyo mayafin da sauri kawai ta fito, ta kulle d'akin sannan ta juyo, abinda ta gani ya razana 'yan hanjin cikinta. Tvn data kashe yanzu an sake kunnata, amma yanzu ba sound ko kad'an sabanin d'azu da yake kusan a k'ure.
"Waye a d'akin nan?" Ta fad'a a fili tana kallon kowacce kusurwa.
Shiru ya biyo bayan maganarta, babu motsi a ko'ina sai tvn dai dake ta aikinta tana nuna tashar cartoon. Tayi ajiyar zuciya sannan ta k'arasa ta sake kashe ta.
Sai dai kuma me? Tana juyowa taci karo da kofar falon a rufe. Wani abu da rabon data ga anyi baza ta iya tunawa ba, don ko da daddare cikin d'aki kawai suke rufewa ita da inna. Sannan labulen ma da ya rufe k'ofar an d'age shi an mak'ale a gefe.
Ta k'arasa da sauri ta murd'a handle d'in.
A rufe take gam! Alamun da muk'ulli aka k'ulle!
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
10
(¡î_¡î)
Ta murda ta jijjiga, ba alamun kofar zata bude. Zuciyarta ta shiga dukan tara-tara don a cikin tunaninta ba zata iya tuna inda mukullan k'ofar nan suke ba, in ma suna nan din kenan.
"Akwai mutum anan?" Ta daga muryarta da karfi ta kira.
"Idan wani na jina dan Allah a bud'e kofar ta rufe dani."
Shiru ba motsi, sai tashin kid'an waje da take jiyowa kawai daga nesa. Hannayenta dake rike da k'ofar suka shiga rawa, ta cigaba da tsayawa a wajen tana rarraba zuciyarta waje-wajen neman mafita, aikuwa take ta tuna da tagar dake cikin d'aki wadda zata fitar da ita jikin barandar saman, ta koma da sauri wajen ta shiga kokarin zura mukullin, sai dai bata kai ga sawa ba lokacin da hasken tvn bayanta ya sake kamawa, sannan muryoyin cartoon d'in dake magana da larabci ya karad'e ko'ina a d'akin.
Ba shiri ta cusa mukullin ta murda sanna ta fad'a ciki, ta ture net d'in daya rufe tagar sannan ta dira waje, bata san cewa sauri take ba sai da ta kusa yin karo da wata mata dake kokarin shigowa gidan bayan ta sauka k'asa.
"Ke hankali mana, bakya gani ne?"
Bata ko bi ta kanta ba tayi cikin tururuwar mutanen ta nemi hanyar gate, kafin ta karasa kuwa ta hango Aminan na sake shigowa.
"Ke na taho dubawa fa, kin dad'e wallahi."
"Yi hakuri." Ta mika mata dankwalin da sauri.
"Toh shikenan sai jibin, Allah huta gajiya."
"Ameen." Ta amsa a hankali. Saboda saurin da Aminan keyi, bata ko lura da yadda jikinta yayi sanyi ba, ta d'an rungumeta kawai sannan ta juya.
Daga nan mik'ewa tayi wajensu Inna, ta samu waje a gefenta ta zauna ta dunk'ule jikinta waje daya tana jinta wani iri, zuciyarta sai k'ara hasko mata da duk abinda ya faru take, tana ganin komai kamar Almara ko wani labari.
Bata kara tashi ba sai tare su innan, lokacin mutane sun fara tafiya, sannan cikin gidan ma an daddawo anata kacaniyar sallar isha, don cikin d'akinsu ma sanda suka shiga wasu ne ke ta sallar a falo. Sannan tvn a kashe.
"Nanne bud'e cikin d'akin muma mu dauro tamu alwalar."
Muryar inna tasa ta kalli kofar d'akin dake k'ulle, wani yawo ya zarce cikin makogwaronta don ta san sanda ta bud'e bata ko tsaya rufewa ba ta fita, ya akayi yanzu take a rufe? Kawai sai ta matsa kusa da innan sosai tace.
"Inna akwai wanda keda muk'ullan d'akin nan ne bayan na wajenki?"
"Kamar k'ak'a? Da kika shigo kinga an d'auki wani abu ne? Shi yasa fa nace dake tun shekaranjiya ki maida duk wani abu mai amfani cikin d'aki saboda mutane ba kowa ne...."
"Inna ba wani abu aka dauka ba.." tayi saurin katseta kar mutanen gefensu suji.
"Toh menene?"
Har ta bude baki zata ce wani abu kuma ta maida shi ta rufe, don bata san ta ina zata fara bayanin ba, irin wannan bayanin da ba kowa ne zai yarda ba, koda innan ce kuwa, don ita kanta a yanzu gani take kamar a tunaninta ne komai ya faru.
"Ba komai." Ta juya ta bud'e kofar aka fara layin alwala.
Har tayi sallar ta saka kayan bacci tunanin abin nan bai fita daga ranta ba koda minti d'aya. Wata dattijuwa mai suna falmata ta taimaka ta d'auko mata bargo daga can saman wardrobe d'insu, ledarsa duk tayi kura ta kakkabe shi ta d'auko, sannan ta d'auki filonta ta fito falo.
"Inna zanje wajen mama azumi acan zan kwana yau."
"Saboda me? Ku uku ne ma fa yau kawai a d'akin, mu da kiga ganmu duk nan zamu yada kai mu kwanta."
Kan ta amsa wata tsohuwa tace.
"keh rufa mana asiri kar daga zuwanmu ace mun kori 'yar masu gida."
Tayi guntun murmushi tace.
"Wallahi Gwaggo ba haka bane, can din kawai nake son kwanciya."
"'Yo ku kyaleta mana..." wata daga gefen inna ta karba.
"...Ran da muka zo nata bikin ai ba inda ta isa taje, sai mun ga dama ma zamu bawa angon."
Suka kyalkyale da dariya gabadaya. A haka ta juya ta bar d'akin, don ta sa a ranta cewa ba zata kwana anan ba.
****
Washegari da akayi kamu, Nanne bata kara bari ta zama ita kad'ai a waje ba, saboda haka babu wani abu daya k'ara faruwa irin jiya. Sai dai kawai jikinta ba dadi, yayi wani irin shafal! tana jin kamar bacci take ji amma ko ta kwanta baya tab'a zuwa.
A haka har akayi kamun aka gama, da daddare ma ta sake d'ebo kayan kwanciyarta tayi d'akin su mama Azumi, sai dai a yau ta lura da kallon da inna ke mata, kallo irin na rashin yarda cewa k'in kwananta a d'akin ba don wani dalili bane.
Washegari da rana wajen uku tana kwance a tsakiyarsu innan da wata Gwaggo ladi, a lokacin an fara shirye-shiryen tafiya wajen mother's eve d'in, masu wanka da shiryawa nata yi. Aunty maryama ta shigo (D'aya daga cikin 'ya'yan kanwar inna) tana kara rok'on su akan su shirya aje wajen event d'in dasu suma, inna ko ta dora daga inda ta tsaya a daren jiya, wai biki in ya wuce cikin gida ya koma party, su ko tsoffai-tsoffai dasu ba zasu party ba.
"...in banda abin su hajiya Babba suma ai ba inda ya kamata suje, wajen da akace surikanka maza zasu zo, me zai kai k'afarka?"
Nanne ta tab'e bakinta.
"Inna duk wannan abin fa kauyancin da ne, don kawai surikansu zasu zo sai suk'i zuwa bikin 'ya'yansu? Kenan duk randa suka zo gaishe su har gida ma sai suk'i fitowa."
Kan inna ta amsa gwaggo Ladi ta karb'e.
"Rabu da 'ya'yan yanzu Ramatu, ba abinda zasu gane ai, abinda yanzu za'ayi auren yarinya washegari ta fito tsabar rashin ta ido? Ni sanda aka kaini d'akin miji sai da na shekara biyu cur! Sannan da yarsa ta haihu yace in shirya inbi 'yanuwansa ranar suna, ke zo kiga farin ciki wankana uku a ranar nan."
"Yo komai ai ya canja, bikin ma dai ana yinsa ne kawai, amma ace abu baza a fara ba sai bayan la'asar a dawo tsakar dare. A da biki ai tunda duku-duku maza na dawowa daga asuba zaku tafi aje a yini, da anyi sallar magriba kuma kowa ya dawo gida, kuyi abinku a mutunce."
Nanne tayi shiru tana sauraren hirarrakinsu, idonta na hasko mata komai da suke fad'a cikin nutsuwa. Doguwar riga ce a jikinta sai bata d'aura dankwalin ba kawai ta yafa shi, fuskarta tayi fayau! filon da take kwance na daga tsakiyarsu, sannan ta jawo jelar kitsonta d'aya tana kanannad'ewa da yatsunta. Zuwa can taji inna tace.
"ke baza ki soma shirin bane, an kusa la'asar fa."
"Inna nayi wanka ai, kaya kawai zansa kuma sai Aminah tazo."
Suka juya suka cigaba da hirarsu.
Tun tana jinsu har bacci ya fara shirin d'ibanta a cikin hayaniyar d'akin, sai dai me? Ba zato ba tsammani kawai taji alamun wani abu kamar hannu mai taushi ya shafa fuskarta, tun daga farkon sumarta har zuwa gefen hab'arta.
Ta bud'e ido da sauri ta dafe wajen, zuciyarta na bugawa ta d'ago ta kalli su inna ko sun lura da ita amma hankalinsu na kan kulolin abincin da ake shigowa dashi d'akin.
Ta shafa wajen taji yayi sanyi k'alau kamar an d'ora k'ank'ara. Kowacce jijiya ta jikinta ta shiga aiki, Ta kasa d'auke hannunta gabanta na cigaba da fad'uwa.
A lokacin ne abin ya faru.
Wannan muryar...wannan muryar mai taushi ta cika kunnuwanta.
"Kinyi kyau!"
¡ñ©n¡ñ
WAYE SHI?
AYSHA SHAFI'EE
11
(¡î_¡î)
"Wallahi Aminah da gaske nake miki a dakin nan k'ofa ta rufe dani tv tayi ta kunnuwa ita kad'ai, jiya kuma gaba d'aya jikina ba dadi, yadda kika san wata bugaggiya haka na koma, duk inda na samu waje in kwanta amma ba baccin. Sannan yanzu na gaya miki murya naji sosai ta min magana a cikin kaina."
Aminah tayi shiru zaune daga bakin gadon.
"Kuma kin tabbata ba wanda yaji maganar."
"Ba wanda yaji, a cikin kunnena kawai naji ta fa, kamar irin nasa earpiece."
Suka sake yin shiru gabad'ayansu.
"Me kike tunani?"
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tayi ajiyar zuciya tace.
"Anya sa'adha kina tunanin ba aljanun ne suke tsorata ki ba?"
Ta girgiza kanta da sauri.
"Ni dake fa mun san ba haka bane tunda pretending nayi, kawai dai ina tunanin wani abu ne daban."
"Wani abu daban kamar me? Kin san dai mutane basa jin irin haka, kuma aljanu ne kawai zasu iya irin wannan abin." ta sake girgiza kanta.
"Duk da haka gaskiya ba aljanu bane, bana ji a jikina hakan ya dangace su, sai dai wani abin daban."
"A'ah, dama kuna nan?..." Aunty ni'imah ta shigo tana fad'a, biye da ita wasu matan ne guda biyu.
"Nanne baki shirya bama? An fara tafiya fa."
"Yanzu zansa kayan."
Suka juya suka fara kwalliya da d'aurin d'ankwali a gaban mudubi, suna yi suna hirar dangin mijin jamila da suka zo daga nijer a yau d'in. Aminah ta jawo wata leda a kusa da kafarta tace.
"Ga d'ankwalinki da mayafin."
"Material d'in ya min kyau, ankon su waye?"
"Nasu hajiya Babba ne." Ta amsa a tak'aice tana zaro rigar daga cikin wardrobe.
Kamar yadda yake a al'adarta, doguwar riga ce akayi da material d'in (lemon green&milk) mai bud'ewar umbrella da d'an karamin hannu. Ta saka sannan tayi d'auri mai kyau, ta yafa lemon green mayafin da Amina ta kawo mata a kafad'a, hoda kawai ta shafa da lip balm mai kyalli ta saka silver d'ankunne da abin hannu, amma tayi kyau sosai fuskarta tayi fresh da kuma kyau.
A wajen event d'in suka cigaba da tattauna matsalar, sai da Rahma tazo wajensu ne sannan suka yi shiru, don Nanne ta nuna bata so wani d'an gidansu yaji.
Wajen biyar da rabi Amaren suka shigo tare da Angwayensu, kowacce da irin kalar kayanta itada angonta. Jamila da take Babba ce ta fara shigowa itada zugar k'awaye da cousin d'inta masu anko, tayi shigar ash and black shima Angon nata yasa shadda ash da aikin black, sai wani d'add'age gira yake yana kallon mutane d'aid'ai. Abokansa mutum hud'u ne kawai a bayansu.
Nafisa da maryam su ankon Maroon colour suka yi duk su biyun kayansu iri d'aya, don dai su nuna cewa su 'yan d'aki dayane, 'yanmatansu masu ankon lace d'in da akace yafi na kowa suna farko da bayansu. Sunyi kyau sosai, don Angwayensu ma duk brown shadda suka sa amma kowa da aikinsa.
Kafin Aisha da Angonta su shigo sai da aka canja wak'a aka sa na step dance d'in 'yanmatanta, su safiya da surrayya na ciki suna bin rawar kamar kowa, abin ya burge mutane yadda suke takawa a hankali, daga bayansu kuma Aisha ta shigo da nata Angon cikin kwalliyar Royal blue da milk, shima yasa milk shadda sai washe baki yake yana dariya.
Ga tarin abokansa a baya suna shigowa kamar baza su k'are, kafin su k'arasa wajen zamansu ya sunkuya ya rad'awa Aishan wani abu, aiko ta tuntsire da dariya tana sunkuyar da kai.
Duk wannan abin, Nanne bata ga ko d'aya ba, don tana zaune bata tashi ba, tunaninta gaba daya ya tafi wajen neman abinda ke damunta. Sai da suka gama zama Mc ya kiran masu bud'e taro da addu'a sannan tace dasu Aminah tana zuwa, ta mike tayi wajen fita, a hanyar ta had'u dasu Aunty maryama sun d'ebo jakunkunan souvenirs, kowannensu ya kama fad'an wai me yasa bata shiga tawagar su Aisha ba, ga anko a jikinta amma ta zauna kamar 'yar gaiyata.
Ta juya idonta, ita ba abinda ke gabanta kenan a yanzu ba, so take kawai ta fita ta samu waje a tayi tunanin dake cikin kanta.
"Rike wadannan maza, mu fara rabawa daga can."
Ba yadda ta iya haka ta karb'a ta bisu. Har aka tashi daga bikin kuwa bata sami wannan hutun ba, don daga k'arshe ma sai sulalewa tayi tabi Aminah da aka zo d'aukanta suka sauke ta a gida.
Har aka gama bikin ranar lahadi aka kai amare Nanne bata k'ara samun walwala ba, mutane suka yita tambayar meya sameta ganin duk ta