Showing 30001 words to 33000 words out of 113985 words

Chapter 11 - WAYE-SHI COMPLETE HAUSA NOVEL

15 Jul 2024

28449

gudu mai nisa sannan ta tsaya a lokaci d'aya.

Cikin nutsuwa Baffa ya bud'e baki ya fara magana!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

21


(¡î_¡î)

Cikin nutsuwa baffa ya bud'e baki ya fara magana.

"Dalilin taruwarmu anan akan matsala ce data shafi Nanne, kowa ya san irin rashin lafiyar data fuskanta kwanakin baya, wanda bayan anyi duk wani k'ok'ari da kuma taimakon Allah ta samu sauki na 'yan kwanaki. Daga baya kuma ciwon ya sake tashi, bayan an kuma warkar dashi ya sake dawowa dai a cikin k'ank'anin lokaci.

Toh a zuwan da malaman suka yi na k'arshe ne suka same ni da zancen cewar har a lokacin basu iya gano ainihin abinda ya same ta ba, duk da rashin lafiyar tata tayi kama da shafar aljanu amma basu ga wani abu na alamar aljani a jikinta ba.

Saboda haka dasu da sauran k'arin malaman da suka zo a ranar, suka bada tabbacin cewa bak'ak'en aljanun ne ke son shiga jikinta, bana irin shafar aljanu da aka saba gani ba, saboda duk wani alamun hakan ya baiyana a jikinta. Sunce su irin wannan aljanun suna da wahalar fitarwa in dai har suka riga suka shiga jikin mutum, sannan suna mu'amala ne da mata da basu da aure kawai.

A lokacin sun bani shawarar cewa da za'a samu tayi aure nan bada jimawa ba, toh da tabbas aljanun baza su sami k'arfin cigaba da bibiyarta ba balle har su iya shiga jikinta. Toh tun daga wannan lokacin sai nayi ta bibiyar malamai wad'anda suke da ilimi akan irin wannan abin, amma kowa magana d'aya irin tasu dai yake maimaita min, in zan sami k'ari ma bai wuce wani yace anyi sa'a ma da har yanzu aljanin bai gama shiga jikinta ba.

Ana cikin haka ne kuma ta gamu da wannan tsautsayin, kuma wani abu ya sake faruwa na cewa taji ciwo a k'afa har an sami karaya amma bata jin zafi a wajen. Suma likitocin suka kira ni bayan sunyi duk bincikensu akan cewa jijiyoyin k'afarta ne keda matasala basa iya aikawa da wani abu zuwa kwakwalwarta, sannan ita kanta wai kwakwalwar tata akwai wani abu da suka gano a ciki kamar k'ari wanda basu tabbatar da menene ba.

Suka bani takardu gasu can a kujerar can akan inje insa hannu za'a sa ranar yi mata aiki. Sai dai ni tunda na karb'o su hankalina bai kwanta ba. Bayan kwana biyu sai d'aya daga cikin likitocin ya kira ni a waya. Yace yana so ne ya fad'a min gaskiya akan zancen aikin nan, duk wani abu da na gani a rubuce basu tabbatar dashi ba kawai hasashe ne, amma shi yana danganta rashin lafiyar Nanne da shafar aljanu don haka yake bada shawara a fara gwada magungunan hausa tukunna.

Da naji haka sai naga an sake dawowa kan dai zancen malaman nan ne, saboda haka sai na tafi wajensu da kaina sulaiman shi ya kaini, suka kuwa sake tabbatar min da abinda suka fad'a a baya, magunguna zasu bata sauki na d'an lokaci amma babu tabbacin cewa nan gaba aljanun baza suyi nasarar shiga jikinta ba sai dai in har tayi aure.

Don haka na yanke shawara cewa yi mata auren a yanzu shine kad'ai mafitar da muke da ita, wadda zata sa ayi fatan dacewa."

Ya juya a hankali ya kalli inna.

"Inna wannan shawara tace kawai, amma ina so inji ra'ayinki duk abinda kika fad'a a yanzu dashi za'ayi amfani."

Inna ta gyara zamanta sannan tace.

"Yo ni dama ai ka san me zance. Shekara biyu kenan harda watanni ba zan manta na tako k'afata har d'akin nan akan zancen auren uarinyar nan, nace maka ni a tsarin da iyayenmu suka raine mu, 'ya mace daga sha uku, hudu, biyar an kawar da ita. Amma ba irin zancen da baka kalailayeni dashi ba akan kai a cikin 'ya'yanka baka tab'a aurar da d'a bai gama sakandire ya fara ta gaba ba saboda haka inyi hakuri.

Nace maka sam! Ni ina yiwa yarinyar nan kallon 'ya ne tunda nina ci kashinta da komai ba zan yarda tayi ta zama a gabana ina kallonta haka ba, toh Inace a yadda muka tsaya da kai cewa data k'are sakandiren zaka aurar da ita ne koh?"

Baffa ya d'aga kai. "Haka ne inna."

"Toh yanzu me ya rage a gamawar da har zakayi ta wannan dogon bayanin kamar mai shirin laifi? Koko kana tunanin bata isa auren bane?"

"Ba haka bane inna, shawara ce kawai na nema don kece da iko akanta."

"Toh in haka ne ko gobe ka tara jama'a ka d'aura mata aure, Allah ya hore min abinda zan had'a nan da sati d'aya a kaita gidanta."

Ya Ahmad yayi saurin gyara zama yace.

"Toh Baffa zancen karatunta fa? Tunda yanzu SS3 take, bai kamata ai ace ta tsaya kenan ba."

Inna ta gallaro masa harara.

"Ai zancen kenan, karatu...karatu ko uwar me yake muku oho."

"A'ah inna da gaskiyarsa shima, nima kuma nayi wannan tunanin. Zata cigaba da karatunta insha Allah, in lokacin yin WAEC da NECO yazo za'ayi mata registration tayi kuma ta cigaba har jami'a da yardar Allah."

"Toh amma Baffa..." Mama halime ta fad'a daga gefe.

"...Nace ana ta zancen aure, dama ita Nannen ta kawo wani tsayayye ne ko kuwa ya za'ayi?"

"Wannan dalilin shi yasa nasa aka kirawo ta nan itama, dan taji komai da kunnenta kuma in bata dama nan da wata guda ta gabatar min da wani, in har akayi bincike akansa babu matsala shikenan, idan kuma ba haka ba dama akwai tarin mutanen dake min magana akanta, don ak'alla abokaina uku suna min zancen nemawa 'ya'yansu kuma na tabbata kowanne a cikinsu ko nan da wata gudan nace baza a sami matsala ba."

Hajiya Babba tayi gyaran murya sannan tace.

"Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa, kowannenmu kuma sai ya taya da addu'ar nema mata sauki. Sannan kema Nanne sai kin kula sosai da kanki, tunda kinji duk abinda akace koh?"

A lokacin kowa ya juya ya kalli Nannen, wadda fuskarta ta jik'e sharkaf da hawaye da kuma gumi.

******

"Me suka tattauna?" Imran ya tambaya yana kallon jaamil.

"Komai ya tafi daidai, na gama nawa aikin saura naka."

Imran ya ajiye wayar hannunsa a gefe sannan ya kalle shi.

"Kana nufin dukkansu sun amince?"

"Na gaya maka komai ya tafi daidai, yanzu kai ya rage ka fara naka."

Ya ciji k'asan lebbensa yatsunsa a sark'e yana kallon 'yar vase flower dake can jikin tv-stand. Zuwa can kuma ya maida yatsun kan hab'arsa sannan ya huro iska daga bakinsa.

"Ta ina zan fara kenan?"

"Yarinyar ta riga ta fara sonka, kuma a yanzu bata da isashshen lokaci, saboda haka baka da matsala, inaga kai kad'ai ne zab'inta."

Imran ya juyo ya kalle shi, yana zaune daga kan two seater dake gefe yana kallon tvn dake kunne tana nuna tashar News, sun kashe fitila sai hasken tvn ne kad'ai a d'akin yana reflecting akan fuskarsa. Har wajen dining ba fitila sai hasken switches kawai da kuma na fitilar kitchen.

"Meye ne kake kallona?"

"Tunowa nayi da yadda kake damuna akan na rabu da yarinyar lokaci kadan daya wuce, yanzu kuma kaine me cewa inje wajenta."

Bai kula abinda ya fad'a ba yace.

"Ya kamata ka saba fad'ar sunanta tun yanzu. Don bana son abinda zata gane cewa kamar akwai wani dalilin da zaisa ka aureta."

Kafin ya bashi amsa wayarsa ta fara haske da vibration akan kujerar. Ya kalli screen d'in sannan yaja tsaki.

"Waye?"

"Maryam." ya amsa a tak'aice.

Jaamil ya juyo ya kalli wayar sannan yace.

"Kar ka damu, idan ka zama ANGO zata kyale ka ne."

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

22


(¡î_¡î)

Nanne ta tsirawa fuskarta ido a mudubin toilet tana nazari. A cikin sati d'aya kawai ta wani irin zabge kuma idanunta sunyi fari fat! sun d'ashe, kamar masu shirin fad'awa duk wanda ya kallesu irin adadin hawayen da suka zubar, ta kai hannu ta tab'a wuyanta a hankali inda wani rami ya fito tsakanin k'asusuwanta biyu.

Watakila na rashin cin abincin da bata yi ne, ko kuma na yawan tunanin dake faruwa a cikin kanta. A sati d'aya kawai, kwakwalwarta tayi sak'a da warwara akan dubunnan abubuwan da a gabad'aya shekarunta na baya bata yi ba. A kullum zata tashi da fatan cewa wannan zaman da akayi na falon baffa bai faru ba, amma cikin awa daya kawai fatanta zai ruguje saboda irin hada-hadar da inna keyi kamar a satin ne za'a d'aura mata auren.

Aure. A kullum ta fadi kalmar ta sake maimaita ta tasan cewa bata shirya masa ba, don wani abu ne da kwakwalwarta bata taba hasko mata shi nan kusa, bama haka ba, ba zata iya tuna ranar da wai ta hango kanta a gidan aure ba. Balle kuma yanzu da akace za'a tura ta cikinsa nan kusa.

Kwallar da ta taru a idonta d'aya ta ziraro kan kumatunta, tasa bayan hannunta da sauri ta share. Ta riga ta yiwa inna alkawarin daina kuka, tayi mata alkawarin karbar al'amarin nan hannu biyu tun ranar data tasa ta a gaba da rok'on ta taimaka ta dawo da rayuwarta kamar da.

Don tun bayan fitowarta daga falon baffa a waccan ranar komai nata ya canja, ta daina magana, ta daina dariya, ta daina shiga mutane, bata da aiki sai ta dukunkune kanta a gado tayi ta turkar kuka. Ba irin magana da bin bakin da kowa a gidan bai mata ba amma bata ko fahimtar abinda suke fad'a.

Sai da inna taga abin nata na neman d'orewa ne yasa ta sameta ita kadai ta ajiye duk wani fad'anta a gefe ta rok'e ta akan ta taimaka ta yiwa mahaifinta da ita biyayya, tace su iyayenta ne, bai kamata su nemi abu a wajenta ba amna da sunan baffa da kuma ita yau tana neman alfarmata da ta basu had'in kai wajen gyara rayuwarta, don abinda suke k'ok'arin yi d'in taimako ne ga ita kanta.

Abin ya bata tsoro ganin innan na shirin durk'usa mata, a lokacin sai ta manta da komai tayi mata alkawarin cewa ta amince baza ta sake nuna damuwarta ba, tana hawaye itama innan nayi. Kuma tun daga wannan ranar, take kokarin ture duk wata damuwarta ganin ta farantawa innan. Bata k'ara kuka ko nuna b'acin ranta ba, sai dai kuma ta koma wata sabuwar halittar daban.

Bata magana, sai bada amsar abinda aka tambayeta kawai, bata dariya bata kuka, abinci ma tana cin iya wanda ta san zai hana ta galabaita ne kawai. A kullum zuciyarta cikin tarawa da d'ebe tunani kala kala take kawai.

Tunanin yadda zata yi ta fad'akar da kowa cewa ita ba wasu bak'ak'en aljanu dake shirin shafarta, rashin lafiyarta cuta ce kawai ba komai ba. Musamman baffa, tasha had'a irin kalaman da zata je ta tsugunna a gabansa ta fada masa ya gane cewa ita lafiyarta kalau, ya taimaka ya janye maganganunsa rayuwarta ta koma daidai, amma a kullum ta tashi taga wannan farin cikin na fuskar inna, sai tunani ta ya karye ta shiga lalubar wata hanyar da zata fitar da ita.

"Yanzu Nanne har yanzu kina cikin band'akin nan?"

Muryar inna ta dawo da ita cikin zahirin da take.

Da sauri ta bude fanfaon sink d'in sannan ta taba butar dake gefe da kafarta, jin k'arar yasa innan tace.

"Toh Allah kuwa ya sawwake miki. Kiyi ki fito Rahman tun dazu take zaman jiranki, ga dare nayi."

Jin sunan Rahma yasa ta tuna da cewar yau zasu je can gidan malaman ta karbo magunguna, abinda yasa dole saida ita saboda akwai wani turare da malamin yace za'a dinga mata duk sati, kuma matarsa ce take yi. Sunje wancan satin anyi mata saura na yau kenan. Ta ja tsaki a k'asan numfashinta. Allah ya sani bata ko son ganin mutanen nan. Don a tunaninta, sune silar duk wani hali da take ciki a yanzu.

Ta d'auko sabulu ta wanke fuskarta sannan ta fito. Ta d'auki hijabi milk dogo mai hannu ta zura akan kayanta kafin tayi falo. Tana fita inna ta kalleta tace.

"Koma ki d'auro dankwali."

Bayan abinda da bai kai minti d'aya ba ta sake fitowa ta d'aura dankwalin, bak'i irin na abaya.

"Toh ungo nan...ance idris ya fita da motar kuma yayyenki ba wanda ya dawo, ku hau adaidaita sahu kuje ku dawo kuma dan Allah kar ku dade, ana gamawa ku taho, ko sadiq za'a kira ya raka ku ne ma?"

Rahma tace.

"Inna kin manta sun tafi kaduna. Ba komai zamu iya zuwa mu dawo, ai ba nisa sosai."

Har suka fita bakin titi, Nanne bata yi magana ba, sai da suka hau adaidaita sahun sannan Rahma ta kalle ta tace.

"An kawo irin takalmin nan da kika ce kina so, wanda ake siyarwa a mak'otanmu."

Ta kalleta kawai sannan tace.

"Mhmmm."

Kamar Rahman zata sake magana kuma saita yi shiru. Haka kawai sai Nanne taji ba dadi, babu laifin rahma ko d'aya a cikin halin da take, bai kamata ta canja mata haka ba. Ta tuno yadda ta damu sosai lokacin da take ta kukan nan, a kullum zata shigo d'akin ta dubata sau ba adadi kuma bata tab'a gajiyawa ba akan bata hakuri. Sai ta juya ta kalleta tace.

"Kuma akwai kalar wanda na gani a wajenki d'in?"

Jin haka yasa ta amsa da sauri.

"Akwai mana, ba dai kamar baby pink ba? Har na d'aukar miki ma."

"Kiji zumudi, to da na fasa siya fa."

"Sai in karbo kud'in a wajen inna in sai miki."

Taji wani abu kamar murmushi zai fito ta gefen bakinta. Wanda a 'yan kwanakin nan ta manta cewar fatar baki na da wani aikin sab'anin magana da kuma karbar abinci. (Gimbiya ruwaila- daga d'aya labarina na komai Nisan Dare!)

Basu wani dad'e a gidan ba suka gama abinda zasu yi suka fito. Sai dai har sun kai bakin titi, Nanne ta tuna ta manta purse d'inta da kud'in motar ke ciki a gidan. saboda haka tayi sauri ta koma Rahma kuma ta tsaya jiranta a kofar wani shago.

A inda gidan malamin yake, cikin wani k'aton gida ne irin na mutanen da, irin Family house d'in nan dake d'auke da waje-waje, kuma gidan nasa na daga tsakiya ne, saboda haka da kyar ta iya ganewa, sai dai kafin ta shiga ciki ma wani yaro ya fito rik'e da purse d'in nata da gudu, da alama cewa akayi ya biyo bayansu.

Ta karb'a sannan ta juya, sai dai kuma ta kasa gane hanyar data biyo, kawai sai tayi ta bin lungu-lungu har ya fitar da ita ta wata k'ofa daban da bata nan suka saba shiga ba. Amma sai tayi tunanin ai duk titi ta zata kaita saboda haka kawai ta fita ta nan.

Sai dai me? Layin ya zama daban da wancan, kamar ta koma cikin gidan kuma taga k'ila ta sake b'ata gwara kawai tabi hanyar ta fitar da ita titi inda rahma take.

Layin babu wani haske dake fitowa daga dukkan gidajen wajen kuma babu mutane sosai, saboda haka ta k'ara sauri ta nufi inda take tunanin zai fitar da ita titi, a lokacin ne ta hango wasu mutane biyu su kad'ai sun karyo kwanar dake gabanta. Suna tafe suna magana da karfi tare da kyalkyala dariya.

Gabanta ya fad'i, sannan zuciyarta ta buga da k'arfi.

Tayi saurin matsawa gefe don ta basu hanya. A lokacin suma suka ankara da ita sabada haka tayi saurin sunkuyar da kanta.

"'Yanmata..!" d'aya daga cikinsu ya kira sanda suka zo dab da ita, ta san da ita suke tunda babu kowa a wajen amma sai tak'i d'agowa ta cigaba da tafiya.

"Yanmata tsaya mana." mutumin ya sake fad'a sanda ta wuce su, suka juyo suka biyo bayanta. Ta k'ara damk'e purse d'inta sannan ta k'ara sauri.

"Tambayarki kawai zamu yi." muryan d'ayan ta fada da alamun dariya yake yi. Ta juya baya ta hango suna binta, ga gidan data baro daga can bayansu ba yadda za'ayi ta koma, sai tayi kwanar gefenta kawai da sauri tana jin takunsu a bayanta.

Ta hango wani haske kamar na mota ya tahowa, wani dad'i ya ratsa zuciyarta sai dai a lokaci d'aya tafi kasancewar motar bata ko tsaya ba ta karya wani layi ta b'ace.

"Idan kika tsaya ba abinda zai same ki, zaki koma gidanku lafiya."

Ta sake jiyo muryarsu daga bayanta, sai kawai ta nufi kwanar da motar ta shiga da sauri idanunta kuma na lalube a hanyar, ko zata ga wani abin da zai iya taimaka mata wajen kare kanta, katako, dutse, k'arfe ko duk wani abu da zai zame mata a matsayin makami.

Ba tsammani kawai taji hannu ya fizgo kafad'unta ta baya, ta dawo tangal-tangal sannan tayi yunk'urin fizge hannunta, bata san cewa ba da karfi aka rik'e ba saida taji tayi baya ta daki ginin wani kango.

"Haba 'yanmata, tambayarki fa kawai zamuyi."

Katuwar muryar mutumin ta fada. Ta damk'e purse dintama hannayenta na rawa sannan idonta na kallonsu d'aya bayan d'aya.

A daidai sannan ne fitilun mota suka haske wajen gaba d'aya, motar ta taho da sauri kamar zata bige su gabadaya kafin a taka wani irin birki da k'ararsa ta karad'e wajen!

¡ñ©n¡ñ

WAYE SHI?

AYSHA SHAFI'EE

23


(¡î_¡î)

Nanne ta k'ara ware idonta ganin wanda ya fito, mamaki ya kusa cinyeta amma kuma sai taji duk wani tsoronta da fargaba sunbi iska, taji kamar ta riga ta kub'uta ne daga hannun mutanen, sannan taji bugun zuciyarta ya dawo daidai.

"Lafiyarki kalau? Ba abinda ya same ki? Ba abinda suka yi miki?"

Wannan muryar mai taushi ta jefo tambayoyin a lokaci guda. Maimakon ta bashi amsa sai ta juya inda mutanen ke tsaye, ga mamakinta sai kawai ta hango su daga can gaba suna gudu.

"Ba abinda ya sameki?" Imran ya k'ara fada tsaye kusa da ita."

Ta juyo ta kalle shi, sannan motarsa dake gefe k'ofa a bud'e.

"Ta yaya kazo nan? Ta yaya ka san ina nan?"

"Kin tabbata ba abinda ya same ki?"

Ya tambaya kamar baiji me tace ba, sai kawai ta d'aga kai har a lokacin tana damk'e da purse d'inta.

"Mu bar wajen nan."

Ba musu tabi bayansa ta bud'e k'ofar gaba ta shiga, wani sanyi da kamshi ya ziyarci koina a jikinta. Ya tada motar sannan yayi kwana ya bi hanyar data baro a baya. Har a lokacin hannayenta rawa suke saboda haka bata ce komai ba, Bayan sun fita titi ya juyo ya kalleta.

"Kin tabbatar ba abinda ya same ki?"

Ta daga kanta da sauri.

"Baki buge ba? baki fadi ba? bakya jin jiri ko..."

"Bana jin komai." ta katse shi a hankali idonta na kallon titi.

Kawai sai ya rage saurin motar sannan yayi parking a gefen titin, kusa da wani shagon saida robobi. Ta juyo ta kalle shi, shima ita yake kallo.

"Sa'adha kin tabbata mutanen can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login