Showing 177001 words to 180000 words out of 209154 words

Chapter 60 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3045

abinda ya faru tin daga kan plan d’insu da mijinta na amfani da Safeenah da sukaso suyi har kawo yanda teburin ya juye zuwa kan Shemaun. Dik Ta sanar da Baddo saidai bata sanar da ita duk abubuwan da sukai da Mommy ba.

Baddo Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Toh meye laifin Safeenah a nan..? Ai idan akwai mai laifi kece number one sai ko mijinki.. Shi da kikai abin sabida shi gashi bai gani ba ya cazga maki rashin mutunci ya kwance miki zani a kasuwa.. Ki gode ma Allah ma da ba kan idanun yaranki abin ya faru ba.. Dama shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ginata gajeriya mai yuwa kaine zaka rufta ciki.. Yanzu ina ribar abinda kika so aikatawa ma wacce bataji ba bata gani ba.. Gashi ke kin kwan ciki kin rufta ciki wanda kikayi domin shi bai gani ba saima tozartaki da yayi a bainar duniya..”

Shemau ta katseta da fad’in “Salman baida laifi shawarin shashashar nan ne Safeenah da na d’auka ya kaini ya baro ni.. Banda ma b’atan baseera irin nawa mai zai kaini d’aukan shawarin da ya fito daga bakin Safeenah wacce batada ta cewa sai abinda aka tsara mata.. Zafin kishi ne kawai ya d’ibi Salman kuma nasan idan ya sauk’o zai fahimci cewa bani kawo masa maza cikin gida.. Tsaf zan wanke kaina a idon mijina dan har abada bazamu rabu ba..”

Baki sake Baddo ke dubanta kafin tace “Aw bayan wann mummunan wulak’anci da ya miki kina tunanin komawa gidansa.”

Da tsananin Mamaki Shemau ke duban Baddo “Toh ina zan koma..? Inada wajen komawa ne..? Ruga kike so na koma a titi kike so na k’arashi gantali na.. Nan gidan duniya bayan Salman da ‘ya’yana su waye nake dashi..?”

Baddo ta jinjina kai tace “Haka ne.. Dan ko kin koma ruga bana jin Inna Fini zata amsheki.. Kin wahala hannun matar K’anin mahaifinki.. Kin taso marainiya babu mahaifa.. Allah ya rufa miki asiri ya yaye miki wahalarki da k’uncinki kikai aure gidan masu arziki..”

Shemau ta jinjina kai tace “K’warai kaw Salman shine Gata na dan haka ko meye ya umarcen na masa zan masa matuk’a zan iya aiwatar da wann abin. Ina tsaka da shan wuya hannun Inna Fini ina kawo mata tallan Fura da nono cikin gari Salman ya hangoni daga cikin motarsa ya saye abinda nake saidawa ya kuma bini har rugarmu ya auroni dukda mahaifiyarsa bata so auren ba. Da shike yana k’aunata ya auroni ya tsame ni daga k’angin bautan gidan Inna Fini da Baffa. Akasi yanzun ma aka samu da rashin fahimta na tabbata zai fahimceni dan wllhi bazan koma hannun Inna Fini ba.. Ina nan cikin gari har ya hak’ura ya maidani kan ‘ya’yana.. Babu kalan bak’antani da Inna Fini da Baffah basuyi ba a idanunsa amma ya toshe kunne yace yaji ya gani zai aureni.. Har cewa sukai ni mayyace ni na cinye uwata zan lashe masa dangi amma dukda haka bai fasa k’udirinsa na aurena ba.. Toh ina kike tunanin zan koma Baddo bayan ma na riga na saba da rayuwar jin dad’i.”

Baddo ta girgiza kai tana murmusawa kad’an kafin tace “Tabbas Duniya karatu ta biya miki Shemau, bayan duk wann uk’uba da kika sha a rayuwa har zakiyi tunanin ki cutar da wani D’anadam bayan ke Allah ya cireki daga cikin wahalan..? Haba Shemau.. Ai idan wani zai mugunta wllhi ke bazakiyi ba sabida Kinsan abin Kinsan ya akeji idan aka cutar dakai.. Nayi matuk’ar mamaki da kikaso cutar da wata..”

Shemau tace “Baddo ya kike so nayi bayan wa mijina nake hakan.. Mutumin da ya zamto Gata da sutura a gareni.. So kike na juya masa baya ko me.?”

Baddo ta katse ta da fad’in “K’warai kuwa babu biyayya ma wani abin halitta wajen sab’awa Ubangiji koda miji ne ko mahaifa.. Zalunci haramun ne Allah ya haramta ma kansa zalunci sann ya sanya shi ya zamto haramun a tsakanin Al’umma.. Idan mijinki yace sai Kun cutar da wani sai ki nusar dashi idan yak’i ganewa ke dai kar ki aikata duk hukuncin da ya d’auka akanki sai ki bar wa Allah lamuranki da sannu zai samar miki mafita amma ba wai ki bisa duk ku zama mugaye ba dan ya taimakeki a baya.”

Shemau ta d’anyi shiru sai kuma tace “Mijina fah ba mugu bane Baddo shi hakkinsa kawai yake nema wajen Yayansa Marwan wanda yayi kane kane akan hakkin nasa.. Yayansu yayi yarjejeniya a rubuce cewa ya mallaka ma Salman assets d’insa da dukiyarsa toh Marwan bai baiwa Mu’azzam ba sann bai baiwa Salman ba mai yake nufi idan ba handamewa yai ba.. Kinga kuwa mijina fad’a kawai yake akan abinda yake nasa ne.. Mahaukaciyar d’iyarsa ce da muka saka cikin plan d’in Ita Ta b’ata komai. Bansan wani b’atan baseera ne yakaini amfani da shawarin Safeenah ba..”

Baddo Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Koma dai menene sharrinku ne Allah ya maida maku kanku.. Ke kanki kince baki San wani b’atan baseera ne yakaiki d’aukan shawarin Safeenah ba.. Hakan kad’ai ya isheki ki gane ishara Allah ya nuna miki idan kinada rabon gyarawa amma idan kuma Bakida niyyan gyarawa wann ke ya ragema.”

Shemau ta dubeta had’ida tab’e baki kad’an kafin tace “Kinga ni bacci ma nake ji, kar ki damu ko a nan parlor zan kwana dan nasan gidan naki d’akuna biyu ne d’aya naku d’aya na yara.. Yo gidan ma babu AC bansan ya zanyi nayi bacci ba..”

Baddo ta tab’e baki tace “Ke kika San wann.. Ni mijina ma baya nan.. Bara na kawo miki abin shimfid’a.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa.

Shemau tace “Yama fi da baya nan.. Kafin ya dawo zan koma gidana.. Ina zan iya wann rayuwa..” Ta k’arashe tana mai gyara kwanciyarta.

Baddo dai girgiza kai kurum tai ta shige abinta ta bar Shemau nan kwance tana lissafi.
**
ABUJA

Musaddiq na shirin kwanciya Safeenah ta turo d’akin ta shigo sai sakin huci take.

Da mugun mamaki yake dubanta kafin ya jinjina kai kad’an yace “Kin dai San ni ba k’aramin yaro bane da zakike shigo min d’aki kai tsaye.”

“Bafa zan k’yaleka ba Musaddiq sai ka amsa min tambayata.. Ka fad’a min Idan tareda shegiyar matar Mu’azzam kuka dawo.?”

A tsananin kufule yake dubanta, yana tuna sharrin da suka tasamma d’aura ma Sadiya itada Shemau. Yai k’wafa kad’an kafin yace “Ki fice mun a d’aki Feenah..”

“Bazan fice d’in ba ank‘I a fice Ai dama gaskiyar Mommy ne tare kuke k’ulle k’ullenku kaida Mu’azzam.. Shiyasa kullum bayansa kake bi baka ganin laifinsa kaima.. A gaban idonka ya zab’i wancan Karuwar ya k’yaleni ina’yaruwarka harda wani binsu ka take masu baya kuyi tafiya.. Kai a dole ga mai rik’e masu jaka ko..”

A kufule wann karon yayo kanta yana nunata da d’an yatsa “Be thankful.. Ki gode ma Allah ban sanar da Mu’azzam abinda kuka tasamma yima matarsa ba Keda Aunty Shemau.. Kuma wllhi idan baki daina shiga hidiman gidan Mu’azzam ba zan miki abinda baki tab’a tsammani ba Safeenah.!”

Baki sake Safeenah ke dubansa “Eh lallai Musaddiq na yarda k’wayan Naka basa fad’a maka daidai.. Ni kake nuna ma yatsa kaman zaka daka.. Kawai ka dakeni sai nasan ka cika masoyin Mu’azzam.. Laifin Mommy ne da tuntuni bata jefa ka a Rehabilitation centre ba..”

“Nida ke waye yafi buk’atan tafiya Rehab.. Dalla Malama fice min a d’aki..” Ya k’arashe yana mai janyota ya turata waje.

Har zai maida k’ofar ya rufe ya dakata kad’an yace “Sai Ki kira Ally d’in naki ki mata jaje..!” Yana ida fad’in haka ya maida k’ofar ya rufe akan fuskar Safeenah.

Huci kurum take tana murza tafin hannunta.. Kardai plan d’insu backfired.. Taiyita kiran layin Aunty Shemau bai shiga.. Toh meye ne ya faru..? Wato kenan Sadiya ta dawo gidanta.. Ai kuwa sassafe zata tafi gidan ta gane ma idanunta hakan. Tai k’wafa kafin tasa kai ta wuce cikin tsananin b’acin rai.

**

Ni’imtaccen k’amshi ne mai gauraye da natsuwa ya tadashi daga baccin nasa.

Ya mik’e yana karanto addu’an tashi a bacci fuskarsa d’aukeda murmushi. Cikin zuciyarsa banda hamdala da gode ma Ubangijinsa baya komai. A haka ya mik’e ya nufi bathroom yayo wanka ya fito ya soma shirin fita Office.

Tin daga staircase yana sauk’owa yasan matar gidan gwana ce wajen tsafta, ko ina need Sai k’amshi dake tashi ga na room fresh gana turaren k’una dake tashi a natse cikin electric burner, ga na abinci na bada nasa kalan shima.. Gidan sai ya bada wani kalan k’amshi na musamman.

Can ya hangota cikin kitchen tana tsaye jikin working base tana chopping onions saman chopping board. Tana sanye ne cikin maroon top da ya kama jikinta d’amas Sai black three quarter wanda shima yai fitting d’inta. Sumar kanta ta tupkesa waje guda tayi ponytail style dashi. Tayi kyau sosai har kaman bazai iya janye idanunsa daga barin dubanta ba, just like a berbie.

Ya soma takowa a hankali ba tareda ya bari tai noticing d’insa ba, abinka da yankan albasa bama ta lura na zuwa ba hankalinta kacaukam naga abinda take. Chapp taji hannun mutum saman cikinta. Ta d’an saki k’ara a razane.

“Good morning Beautiful..!” Ya fad’i still tana nan rik’e cikin jikinsa.

“You scared me... I almost chopped my fingers.” Ta fad’i kaman zatai kuka.

Murmusawa yai yana kuma shigar da kansa cikin wuyarta “Every little thing scares you..” Ya k’arashe yana juyo da ita suna fuskantar juna. Hannayensa saman k’ugunta yayinda Sadiyar ta d’ingile k’afafunta ta zuba nata hannayen saman shoulders d’insa dan kar ta b’ata masa jiki da onions.

“You look fantastic.. I love you..” Ya fad’i yana bata light kiss.

Murmusawa tai kad’an kafin tace “Thank you... Handsome.”

Ya murmusa yana mai lakatan hancinta kad’an “K’amshi ya cika mun ciki tin daga upstairs.. Mai ake dafa mana ne..?”

Ta d’an marairaice fuska tace “Kai Handsome nothing special fah.. Kawai chicken Sandwitch ne served with black tea..”

“Sounds delicious.. But I think I’ll just have the tea.. Sauri nake suna jirana a office..”

Tai rau rau da idanu tace “Kai dan Allah Bazaka tsaya ka karya ba.. Kaga fah I’m almost done, onions d’in nan kawai zan zuba..Oh no no I’m sorry.. Bansan da wuri zaka fita ba.. I should have waken up earlier..” Tana maganar tana k’ok’arin rounding up.

Hannayenta ya kamo yana fad’in “Relax Beautiful.. It’s okay.. Na gode da kika tashi as early as you can bayan gajiyan hanya da kika kwaso.. You don’t need to stress yourself.. Badon Ina sauri ba zan tsaya naci, na riga na makara ne.. Ban saba makara ba suna can suna jirana..” Ya d’an kashe mata idanu guda kafin yace “But I guess ke kika sa na makara..”

Ta zaro idanu waje tace “Ni kuma..! How am I at fault.?”

Ya janyota jikinsa kad’an yana mata wasu salon kafin yace “Because last night I slept beside you shiyasa na makara..”

Ta rufe fuskarta kad’an cikeda kunya. Daidai nan wayarsa ta soma ruri.. Yusuf ne mai kira yai saurin cirota a aljihu yana fad’in “See, suna jirana.. I’ve to go now.. Take care I love you.” Ya fad’i yana manna mata peck a cheek d’inta.

Ta biyosa tana fad’in “Toh tea d’in fah bazaka sha ba..”

“Kiyi hak’uri na makara I’ll make it up to you next time..” Ya k’arashe yana mai shigewa Mota.

Ta d’ago masa hannu tana masa waving. Ya sakar mata murmushi yana d’an kashe mata ido guda lokaci guda ya juya kan motar ya fice.

Ta juyo ta komo cikin gidan tana fad’in “May Allah always be with you my Inspector..” Haka ta k’arasa cikin gidan taci gaba da abinda take. Dik Sai ta kasa cin breakfast d’in itama. Kusan duka ta juye ma Patrick. Ruwan tea d’in da Aunty Larai ta bata kawai taita sha.

**


_Police Headquarters_


Motar prison ne ta k’araso aka fito da Assad hannayensa rufe cikin handcuffs. Hajiyarsa ta fashe da wani irin kuka Shaheed k’aninsa na rik’e da ita kaman zata duk’a k’asa sabida kuka. Shaheed sai tausan ta yake cikin k’arfin hali. Ya rik’ota Ta zauna saman wasu kujeru dake a k’ofar wajen.

Mu’azzam ya hangosu daga nesa tausayin mahaifiyar Assad fal zuciyarsa, da k’yar ya k’araso wajensu yana jin zuciyarsa na masa wani irin rauni.
Baima san mai zai soma fad’i ba, baisan da wasu irin kalamai zai lallashi mahaifiyar Assad ba.

Cikin kuka take duban Mu’azzam tana fad’in “Ya fad’a da bakinsa.. Ya amsa cewa yaci amanar aikinsa.. Maiyasa zai aikata haka.. Maiyasa Mu’azzam..Mai yake nema da tsanani a duniyar nan.. Bai duba maraicinsa ba bai duba d’iyarsa da yake fafutukan amsowa daga hannun matar can a Kotu ba..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.

“Hajiya Assad baida laifi.. K’age aka masa.. Baici amanar k’asa ba.. Baici amanar aikinsa ba.. Inada tabbacin abokina ba D’antadda bane.. Kuma zan tabbatar ma kowa hakan da izinin Allah. Ki kwantar da hankalinki kinji.. In sha Allah komai zai wuce.. Allah zai fidda Assad daga wann bak’in k’ulli da aka masa..”

Hajiya bata iya amsa sa ba sai kuka da take.

Ya dubi Shaheed yace “Take her home.. And make sure ta sami hutu.. Zan kula da case d’in Assad..”

Shaheed ya jinjina kansa yana mai amsa ma Mu’azzam d’in. A tare shida Shaheed suka kai Hajiya Mota Shaheed na rik’eda Ita tana cazgan kuka tana kama k’irjinta. Kai da gani kasan ba lafiya take ba.

Shaheed ya dubi Mu’azzam yace “Mun gode K’warai Inspector da d’awaniyarka.. Allah ya saka maka da alkahiri.”

Mu’azzam ya dafa hannun Shaheed yace “Kar ka mun godiya.. Banyi rabin abubuwan da Assad ya mun a rayuwa ba.. Nida Assad are practically brothers so dan na masa wani abu ba favor bane dole akaina nayi.. Ka kula da mahaifiyarku na maka alk’awari in sha Allah D’anuwanka zai fito.”

Shaheed ya jinjina kai a hankali yana kuma godiya wa Mu’azzam d’in kafin ya shige ya tada Mota.

Maleeka dake tsaye daga can gefe akan idanunta komai ya faru. Babu abinda ya d’aga mata hankali kaman ganin mahaifiyar Assad da tai cikin yanayi na tashin hankali.. Sai ta tuna nata mahaifiyar dake kwance gida tana jinya wanda duk kud’ad’en da take samu daga wajen su Chief ma ita take turawa. Hawaye guda d’aya ya gangaro mata.. Meye laifinta dan ta amshi kud’ad’e ta tura ayima mahaifiyarta dake tsananin jinya aiki.. Shin kowa bazai komai domin ya ceci mahaifiyarsa ba.. Tai saurin juyawa ta shige building d’in. Restroom ta shige tana cazgan kuka. A fili take furta “Meye laifina.. Meye laifina dan naso taimakon mahaifiyata..?”

Zuciyarta ya soma tuhumarta “Idan wanda kika d’aura ma sharri ya rasa nasa mahaifiyar fah ke taki ta rayu shin wane riba kika samu a cikin hakan.. Shin kin mance duk kalan abubuwan alkahiri da Assad ya miki..? Shin kin mance gwagwarmayar da kuka sha tare.? Shin kin mance barkwancinsa musamman a lokutan da kike tsananin son ganin Inspector Gamji ya kula ki.. Assad was there for you.. Yana k’ok’arin kwantar miki da hankali dukda yasan Abokinsa baki ishesa kallo ba balle ki shiga cikin jerin matan da yake so.. Shin duk kin mance abubuwan da Assad ya miki Maleeka.? Why Assad..? Why him.. He’s a good guy.. A kindhearted wanda a koda yaushe baida burin da ya wuce ya kyautata ma mutane.. Assad bai cancanci haka ba. Ta rintse idanunta hawaye na gangaro mata. Daidai lokacin wayarta ya soma ruri.. Ta saka hannu ta d’auka k’aninta ne yake kira daga gida..

Daga yanda taji muryarsa tasan babu lafia. Cikin kuka take tambayarsa meke faruwa.. Nan take ya sanar da ita Mahaifiyarsu ta mutu ana k’ok’arin shiga da ita tiyata...

Wani irin kuka Maleeka ta fashe dashi tana mai silalewa k’asa.

Taci kukanta ma’ishi tana kiran Mamanta. Saida tai ma isanta kafin kukan nata ya lafa.. Jiki babu k’wari Ta mik’e Ta fito.

Chief ta hanga k’ofar Office d’insa, alama kawai yai mata da ido ta gane mai yake nufi. Jiki babu k’wari ta nufi Office d’insa.

**

Mu’azzam kaw yana isa asibitin ya shiga har office d’in securities d’in, mutum guda ya samu a cikin Office d’in wanda yake kula da na’urar cameras d’in.

Suka gaisa kafin ya nuna masa ID d’insa yace “FCID, inaso ka min playing cctv footage na cikin asibitin nan for the last 2weeks..”

Mutumin ya d’an sosa kai sai kuma yace “Sir.. Baka tunanin yayi tsayi zai d’auke mi some hours..”

Murmusawa Mu’azzam yai kafin yace “Barin fad’a maka exact date d’in da nake so kamun playing..” Ya k’arashe yana mai fad’a masa exact date d’in.

Security d’in ya d’an fara ‘yan kame kame.

Gefen suit d’insa Mu’azzam ya d’aga bindiga ya bayyana. Lokaci guda ya dafa security d’in dake zaune saman kujera gaban Computer ya d’an rank’wafo kad’an, cikin kwantar da murya yace “Zaifi maka kyau idan kayi abinda nace.. I can kill you right here and burry your body ba tareda wani ya gane hakan ba.. Just do what I ask you to do.” Ya k’arashe yana mai manna bakin bindiga a k’eyar mutumin.



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*



*56*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





Chief ya girgiza kai kad’an yana dubanta “Meke faruwa..? Ya na ganki haka..?”

Kuka Maleeka ta kuma fashewa dashi, cikin muryar kuka take fad’in “I just... I... I just lost my Mom..!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai zama saman kujera.


Chief ya dubeta da fuskar tausayi yana girgiza kai “Kiyi hak’uri Maleeka.. Sorry for your loss.. My condolences..”

Maleeka dai bata iya cewa komai ba Sai cazagan kukanta take tana kiran mahaifiyarta.

Chief ya k’araso ya mik’a mata ruwa yace tasha. Babu musu ta amsa tana sha tana kuka. Saida tai mai isarta kafin kukan nata ya tsagaita.

Chief ya jingina jikin tabel yana dubanta “Maleeka..”

Ta d’ago watery eyes d’inta tana dubansa. Yayinda Chief yaci gaba da fad’in “Naga irin kallon da kike wa mahaifiyar Assad lokacin da za’a fita dashi.. Na hango nadama da tarin danasani cikin k’wayar idanunki.. Na hango tausayi da son jada baya a tattare dake... Maleeka if you dare think of double crossing me, wllhi wllhi I won’t hesitate to execute you.. Shawari nake baki.. Don’t you ever think of ratting us out.!”

Da tsananin mamaki take dubansa, Ta girgiza kai kad’an tace “Yanzu nace maka Mahaifiyata Ta mutu.. Ko ganinta banyi ba.. Mahaifiyata ta rasu ko cikakken 1hr batayi ba amma har kanada guts d’in da zaka dubi cikin idona kace zakai threatening d’ina Chief..? Shin kai wane irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login