Showing 96001 words to 99000 words out of 209154 words
kai yana dubansa “Just what do you think you are doing..? What has gotten into you.?” Assad cikin fad’a fad’a yake maganar. Ya shafi kansa kad’an yana duban Mu’azzam da ya dafe benci ya kifa kansa kurum ba tareda yace komai ba Sai zuciyarsa dake tafarfasa.
Assad yaci gaba da fad’in “You attacked her lawyer Mu’azzam.. What if wani yaga hakan.? Ka godewa Allah babu kowa wajen...”
Katsesa yai da fad’in “I do not give a damn Assad.! Didn’t you hear what that imbecile was saying.? Ko bakaji abubuwan da yake fad’i bane..?” Ya fuzar da fuci yana duban Assad d’in “Kar ka sake dakatar dani Assad.. Idan kuma ba haka ba..?” Yaci gaba da girgiza kai kafin yace “I don’t know what I might do to you..!” Yana ida fad’in haka ya fice daga wajen gaba d’aya.. Yana ficewa ya hango Musaddiq ya fito daga motarsa. Sukai tsaye suna duban juna, kana ganin fuskar Musaddiq zaka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali ne wanda baki bazai iya fad’i ba. Mutuwar Ikram ya dawo wa Musaddiq sabo.
Mu’azzam ya k’ok’arin danne nasa tashin hankalin kad’an yana mai k’arasowa kusan Musaddiq d’in.
Cikin wane irin yanayi Musaddiq ke dubansa “Is it true.?” Ya tambaya yana duban Mu’azzam d’in.
Mu’azzam ya d’an kauda Kai gefe kad’an yana fuzar da fuci a hankali.
Musaddiq ya sake fad’in “Da gaske ne.. Safeenah itace prime suspect.. Did she kill Ikram..? C’mon Mu’azzam answer me talk to me now.?!”
Jinjin kai Mu’azzam yai a hankali yana duban Musaddiq d’in “I’m afraid yes.!” Ya k’arashe yana jinjina kai alamun tabbatarwa.
Kauda Kai gefe Musaddiq yai yana mai rik’e bakinsa da duka hannayensa biyu.. Safeenah ta kashe masa Ikram. Ta rabasa da Ikram.. His very own sister.. Ji yai kaman bashi a duniyar, k’afafunsa na barazanar gaza d’aukansa.
Cikin sauri Mu’azzam ya tallafosa ya rik’esa sosai “She.. Killed her.. Ta kashe mun ita.. Ta rabani da ita.. Maiyasa zatayi haka.?!”
Saurin rungume Musaddiq Mu’azzam d’in yai yana jin zuciyarsa na masa rauni shima “That’s enough Musaddiq.. Ikram bazata wuce lokacinta ba.. Amma wad’anda suka kasheta need to pay.. I promise you, I’ll make them pay for what they did to her. They’ll pay dearly.” Ya k’arashe yana mai janyo Musaddiq d’in suka zauna nan saman wasu kujeru dake gaban wajen.
A can interrogation kaw Safeenah dai kasa cewa komai tai sai ma duban Ameer da take da matuk’ar mamaki. Ya akai Ameer yasan anyi arresting d’inta.? Waye ya sanar dashi.? Yama akai har yaji komai ya taho in a very short time..?
“Did I surprise you.?” Ya fad’i yana dubanta murmushi saman fuskarsa.
Dubansa take har lokacin tana mamakin yanda akai yasan tana ofishin Yansanda. Lokaci guda ta jinjina kai tace “And you know I don’t like surprises..” Ta d’an dakata kafin tace “Ameer ya akai Kasan anyi arresting d’ina.. How did you find out about this in such a very short time.?”
Ameer ya murmusa yana mai d’aura k’afa d’aya saman d’aya “Let’s say I do my homework.”
Safeenah Ta girgiza kai tace “Ameer what kind of game are you playing..? Bayan threatening da kakeyi cewa Kasan wani abu game dani.. Now you appear as my lawyer. What is this Ameer..? Tell me mai ka sani gameda abinda ke faruwa dani.?”
Ameer ya rage girman idanunsa yana karantarta irin dai yanda lauyoyi keyi idan suna karantar mutum gaskiya yake fad’i ko k’arya. Lokaci guda yake furta “Na fad’a miki I do my homework Safeenah.. And idan zaki tsaya kina b’ata ma kanki lokaci da tambayoyin da bazasu amfaneki na zaki tafi jail ne a banza a wofi ba tareda kin aikata laifin da ake tuhumarki ba.. Safeenah even your family basu baki support ba. you are all alone in this battle, ya kamata ki taimaki kanki ki cire kanki a wannan mess d’in.. And ni kad’ai ne mutumin da zai cireki a mess d’in da kika tsinci kanki ciki Safeenah..” Ya gyara zama yana mai tsareta da idanu “Now you tell me everything.. I mean kar ki b’oye min komai.. Ki fad’a mun duk abinda ya faru.”
“What if I don’t.” Ta fad’i tana dubansa
“You’ll have to Safeenah.. Idan har kinaso ki fita daga wannan mess d’in.. Unless kuma kinaso ki tafi jail for the crime you did not commit.”
Safeenah daketa murza tafukan hannayenta kauda FUSKA gefe tai kafin a hankali ta soma furta “Mommy zata turo min lawyer, a very good one.. I don’t trust you, and I don’t want you to handle my case.. Ka gane..”
Murmusawa yai yana dubanta kafin yace “What if nace miki Mommy ce ta turo ni.?”
In a shock take kuma dubansa, ta girgiza kai kad’an tace “Pardon..”
Ameer ya d’an matso kad’an yana mai d’aura duka hannayensa saman table d’in “Feenah.. You need to cooperate with me idan har kina so ki ceci kanki.. Kema kin sani Mu’azzam zai komai Domin ya Turaki gidan yari.. Kuma ina mai tabbatar miki a halin yanzu zai wuya yaci gaba a zama dake matsayin mata da miji.. We are talking about his sister here Feenah.. Kina dai ganin yanda ya bada himma wajen ganin yayi nasara kan binciken da yake.. Kar ki bari bayan saye zuciyarki da soyayyarsa da yayi ya kuma saye miki freedom d’inki.. Ki tashi ma kanki kafin lokaci ya k’ure I’m sure baza’a d’auki lokaci ba za’a tafi kotu.. You don’t belong here Feenah.. You deserve a good life tareda mijin dake knaunarki.. Kar ki bari Mu’azzam ya d’auke miki wannan..!” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu.
Hawaye ne Safeenah taji na zuwa mata. Cikin muryar kuka take furta “Ban aikata ba.. I swear I didn’t do it.. But I don’t know.. Ban San ya zanyi bayani Mu’azzam ya fahimceni ba..”
Katseta yai da fad’in “Ba wa Mu’azzam zaki fad’i ba Safeenah.. Idan kuwa kikai gangancin fad’iwa Mu’azzam zaki k’ara kulle kanki cikin case d’in ne.. Kar ki mance cewa Mu’azzam shi yake gudanar da bincike kan case d’in nan.. Sannan Ikram ‘yaruwarsa ce.. So ko mai zaki ce bazai yarda ba Safeenah.. Kece kawai zakiyi duk yanda zakiyi ki zame kanki.. And don’t forget, You are well and fully entrapped in this case.. You’ve no way out domin kuwa Tabbas an tura miki sak’on address na location d’in da aka tsinci gawan Ikram.. And you received that text message.. But don’t you worry zan wanke ki a Kotu in sha Allah.. And I’ll do it to the best of my abilities.. I promise you.. Kawai abinda nike so dake shine ki bani had’in Kai Safeenah.. Hundred percent.. Kin fahimta..?” Ya k’arshe yana kuma tsareta da idanu.
Safeenah ta share hawayen da ya zubo mata. Daidai lokacin Mu’azzam ya turo k’ofan ya shigo domin kuwa lokacin da aka d’ibar mata na ganawa da lawyer d’inta ya cika.
Ya tsaresu da idanu musamman Safeenah dake matsan k’walla.
Lokaci guda Maleeka ta kawo kujera ta ajiye ma Mu’azzam nan jikin table d’in. D’akin binciken ya zamto su uku kenan ciki.. Safeenah sai Ameer Wanda take lawyer d’inta ne saiko Mu’azzam mai gudanar da bincike.
Ajiye wayar Sagir Mu’azzam yai saman table d’in kafin yace “An tura miki wannan sak’on da lambar ki a ranan 12 ga watan June.. You can’t deny it domin kuwa munada shaidan da zai tabbatar an tura sak’on zuwa layinki sannan Kinyi receiving.. Just admit it already..!”
Ameer ne ya katseta da fad’in “Excuse me Mr Inspector.. Are you suggesting that my client committed that crime.?”
Wani duban Mu’azzam ya aika masa kafin yace “I don’t remember asking you.. Safeenah nake tambaya kuma ita zata amsa min.!”
Safeenah dake sakin huci tana duban Mu’azzam d’in lokaci guda itama take furta “I have the right to be assistant by a Legal Counselor.. And Ameer here, is my Lawyer.!”
Ameer ya murmusa yana duban Mu’azzam d’in “Calm down Inspector.. Ina fata ka saurari matarka, I’m only her Lawyer. So don’t bring up your personal issues with me here.”
A wulak’ance Mu’azzam ke aika masa wani irin duba kafin yace “I don’t give a damn about you, Mr lawyer. Now you tell your client to answer my question.!”
Safeenah ta girgiza kai tace “Wannan layin tsohon layina ne.. Kuma ni banyi receiving sak’on ba.”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Amma bayan wannan ranan kika canza layin..? Haka ne.. So definitely wannan sak’on ya isa miki.”
Wannan karon Ameer ne Yai maganar “You heard my client Mr Officer, batai receiving sak’on ba. Gidan biki ne kar ka mance kuma ita d’in Amarya ce wacce aka sani da zafin kai, so za’a iya tura sak’on wayar nata na hannun wani.. So ba lallai ita tayi receiving wannan sak’on ba. And da kake maganar canza layi ansan most of Amare suna canza layi idan sukayi aure.. So ina shawartanka da ka daina d’aura wa client d’ina laifi kai tsaye.. Sannan sauran tanbayoyinka zaifi kyau ka ajiyesu ka sanar da lauyanka har dai zuwa ranan da zamu tafi Kotu.”
Ameer yana ida fad’in haka ya mik’e yana gyara zaman suit d’insa.
Mik’ewa Mu’azzam d’in ma yai yana aika masu wane irin kallo “You must talk Safeenah.. Sai Kinyi magana tun kafin aje Kotu na miki alk’awari.. Zaki fad’i komai..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga room d’in.
Koda aka fito da Safeenah za’a kaita cell d’inta a nan ta had’u da Musaddiq yayi tsaye yana aika mata wane irin duba. Safeenah ta rok’i sergeant d’in Ta barta tai magana da D’anuwanta.
Musaddiq ya k’araso yana mai zuba mata rinannun idanunsa “Tambaya d’aya nake so na miki. Maiyasa kika aikata..? Why did you do it Safeenah..? Maiyasa kika rabani da Ikram..?”
Girgiza kai Safeenah take tana duban Musaddiq “Wllhi ban aikata ba Musaddiq ka yarda dani.. And I know nothing about it..”
Jinjina kai yai yana dubanta kafin yace “Idan ya tabbata akwai saka hannunki a kisan Ikram ki mance kinada D’anuwa Musaddiq..!” Yana ida fad’in haka ya juya ya fice Safeenah na kiran sunansa ko tsaya baiba balle ya tankata. Haka sergeant d’in ta tasa kanta ta turata zuwa cell d’inta..
Wai yau Safeenah Marwan Gamji ce a cikin cell, ‘yansanda na tsare da ita.. Abunda ko a mafarki bata tab’a hasasho kanta a irin wannan yanayi ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Tabbas idan Bawa bai mutu ba bai gama ganin jarabawar rayuwa ba.. Sai masifa Safeenah take tana fad’in azo a fiddata daga cikin cell d’in nan ita bazata iya ba. Sergeant ta darara mata tsawa “Ke Malama Ki mana shiru.. I know you live in a mansion, you better get used to staying jail.. Kin zaci a 5star hotel kike da zaki ishe mutane.. And don’t expect any VIP treatment Dan kina matar Inspector Gamji.. Yanda ake ma criminals d’in dake cikin cell d’in nan haka za’a miki.. Idan kina san samun rangwame shine ki bud’e bakinki ki fad’i Iyakacin abinda kika sani idan kuma ba haka ba. Yanzu kika fara zama behind bars har ki dangana ga Prison that is idan ba’a yanke miki hukuncin kisa ba.”
Safeenah ta zaro ido waje tana girgiza kai “No.. Bazai tab’a yuwa ba wllhi.. Nayi imani da Allah ban aikata ba babu kuma wanda ya isa ya hukuntani akan laifin da ban aikata ba ban kuma San wa ya aikata ba.. Ameer do everything you can to get me out of this place.” Ta k’arashe tana duban Barr Ameer kaman zatai kuka.
Ameer yace “Ki kwantar da hankalinki Safeenah. Zaki fita daga wajen nan.. I promise you.!” Ya k’arashe yana mai jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa.
**
A b’angaren Mu’azzam gaba d’aya zuciyarsa a jagule take. Ji yai kaman k’irjin ya masa mugun nauyi. Tamkar dai ya gaza d’aukan abubuwan dake cikin k’irjin nasa.. Gaba d’aya baisan meke masa dad’i ba daga jikinsa har duniyar Tasa ga kansa dake wani irin sara masa tamkar dai kan nasa zai rabe gida biyu.
Sun jima suna tareda Assad har dare, Assad na kuma shawartansa da ya d’auki abubuwa da sauk’i kafin daga bisani yai ma Assad d’in sallama. Bayan rabuwarsu da Assad Tsayawa yai a wani chemist ya sai maganin ciwon kai kafin ya nufo gida.
Yana shigowa gidan ya zube a nan parlor had’ida lumshe idanunsa yana tinanin abubuwan da suka faru a ranar. Rana ce data kasance mai tsawo a garesa.. Kiraye kirayen sallar isha da aka soma ya sanyasa mik’ewa ya nufi d’akinsa. Saida ya tsaya ya dubi k’ofar d’akin Sadiya na d’an lokaci kafin ya maidoda dubansa zuwaga katafaren hoton aurensu shida Safeenah dake aje wajen. Take yaji zuciyarsa na kuma masa zafi kansa naci gaba da sarawa. Lumshe idanunsa yai a hankali kafin ya nufi nasa d’akin.
Tana jin tab’a k’ofa ta mik’e daga zaunen da take tana aikin abu d’aya Wato kuka. Ba kukan abinda matar Mu’azzam da ‘yanuwanta sukai mata a ranan take ba. Kukan rashin sanin halinda ahalinta ke ciki take. Yinin ranan kuka take ga tsananin ciwon kai da ya addabeta itama. Ta fito da sauri tana lek’en ta ina zata gansa ta tambayesa ko an samu su Umma amma bata gansa ba. Baya kitchen sannan baya parlor.. Ta dubi k’ofan d’akin da take tinanin nasa ne. A hankali ta lumshe idanun nata wasu hawayen suka kuma gangarowa.. Bata shiga d’akin ba ta koma da baya ta nufi nata d’akin ta gudanar da sallar isha da tuni aka kira har wasu masallatan sun shiga.
Ta jima tana addu’o’inta tana sauraron ko zataji bud’e k’ofan d’akinsa amma shiru bataji ba.. Ta soma tinanin kodai ya fice daga gidan ne bataji fitarsa ba.? Ai kuwa bataci ta zama ba, bazata bari ya fice ba tareda ya sanar da ita komai gameda neman mahaifiyarta da ‘yanuwanta da yai mata alk’awarin zai ba.. Bazai yuwu ya kulleta a wannan kurkukun ba ya hanata fita neman ahalinta sannan shi ya gaza yin komai.. Ta mik’e da sauri ta fito tana dubasa cikin gidan. Bai ko ina sannan ga motarsa a haraban gidan. Definitely yana cikin gidan kenan. D’akinsa ne kawai yai saura bata duba ba, yau kam zata shiga domin tasan wani hali Umma dasu Habeeb suke ciki.. Ta isa jikin k’ofar d’akin ta murd’a handle d’in a hankali nan taga k’ofar ya bud’e.
D’ago idon da zatai ta hangesa kwance saman sallaya yana sanye da jallabiya mai ruwan sararin samaniya.. Take ta shiga sakin huci, Wato ma kwanciyarsa yazo yayi mahaifiyarta da ‘yanuwanta suna can ba’asan duniyar da suke ba. A zuciye ta shigo cikin d’akin tana fad’in “Mr Inspector ka tashi ka sanar dani Ina ahalina suke.. Bazai yuwu ka ajiyeni a wannan kurkukun da kake kira gida ba sannan kazo kai kwanciyar ka ba tareda sanin ina ahalina suke ba..!”
Shiru taji bai amsa ta ba sannan ko motsawa daga yanda yake kwance bai ba.. Nan Ta soma rau rau da idanu cikin rawar murya take fad’in “Nasan tsiwa bazai saka ka kai abu ba.. But please na rok’eka ka k’yaleni na fice na nemosu da kaina.. Please Mr Inspector.. Just put yourself in my place.. Dan Allah please..!” Ta k’arashe kuka na zuwa mata.
Har lokacin yana nan kwance bai ko motsa ba.. Abun ya soma k’ular da Sadiya ganin ya bata baya ko juyowa baiba balle ya amsata. Ta k’araso ta yanda fuskarsa ke kallo nan taga idanunsa a lumshe suke. Takaici ya kuma cikata.
“Mr Inspector..!” Ta fad’i daidai saitin fuskarsa.
Shiru bai amsata ba.. Ta shiga bubbuga gefen sallayar tana ambato sunansa, nan ma dai shiru bai amsata ba har lokacin idanunsa a lumshe suke.
Nan ne fah tsoro ya soma kamata, gani tai tamkar ma bai numfashi.. Taci gaba da buga gefensa tana ambaton sunansa.. Ganin da gaske dai k’ila numfashi ne baiyi ya sanyata matso da kunnenta guda saitin hancinsa taji kodai numfashin ne baiyi.. Aiko nan taji tamkar dai bai numfashi.. Girgiza kai ta soma tana fad’in “Oh no.. He’s not breathing..! What do I do now..? Na shiga uku ni Sadiya ya zanyi..? Who do I call..?” Ta soma girgiza kai cikin birkicewa da tinanin mai zata aiwatar.
“The gateman.. Shi zan kira.. Bara nai sauri na kirasa..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin mik’ewa saidai kafin ta ida mik’ewa taji Mu’azzam ya kamo hannunta ya janyota ta fad’o jikinsa.
Zaro ido tai tana duban fuskarsa wanda har lokacin idanunsa a lumshe suke yana sakin murmushi a hankali. Still idanun nasa a lumshe yana shak’an k’amshin jikinta yake furta “Your perfume is nice.!”
Takaici ya cika Sadiya, Wato dama duk yana jinta yai banza da ita, tana maganar neman ahalinta shi ta perfume ma yake, wai your perfume is nice.. Ita da ko turare bata saka ba bayan kayan wanka masu k’amshi da ya tara mata a toilet.. Inama taga wani nastuwan fesa perfume..Ta shiga kokawan cire jikinta daga nasa tana fad’in “You.. You scared me.. Let me go now.. Inspector.”
Bai sakenta ba har lokacin saima sakin murmushin da yake still idanunsa a lumshe. Saitin kunnenta yake furta “Did I scare you..? Kin zaci kin rasani kenan..? Kar ki damu bazan mutu ba until our mission is finally accomplished..!”
Turasa tai da k’arfi tana fad’in “Toh kama mutu mana. Who cares.. The only thing da na damu dashi shine kar ka mutu baka samo mun Ummata da k’annena ba.. I don’t care idan ka mutu..”
Ya bud’e lumsassun idanunsa wanda da gani zaka fahimci baijin dad’i yana dubanta dasu.
Still murmushin ne saman fuskarsa yana duban yanda take sakin huci “Don’t make the mistake of falling for me, because I’ll never love someone like you.” Ya fad’i idanunsa akanta.
A yatsine ta dubesa kafin tace “I’d rather die than to fall for someone like you. Mr Inspector.! Now you let me out and look for my family.”
Ya kuma murmusawa kafin yace “Kina son sanin ina ahalinki suke.?”
Tai saurin jinjina kai tana dubansa.
Ya jinjina kai kafin yace “I’m sick, and I need someone to take care of me.. Can you stay here in my room and look after me..?”
Galala take dubansa kafin tace “Allah ya sawak’e mun..!”
“Ashe baki son sanin ina suke.. Kin mance cewa yin hakan duk cikin mission d’inki ne..”
Sadiya tai rau rau da idanu tana dubansa, dik wani salon mugunta ya sani, dik abinda zai yi ya k’untata mata shi yakeyi da sunan mission. Tasa bayan hannunta ta goge hawayenta “But you’re not a baby. You can move your hands and legs.. Mai