Showing 42001 words to 45000 words out of 209154 words

Chapter 15 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3092

Sabeera na biye dashi hannunsa nik’i nik’i da manya manyan ledodi shak’e da kaya.

Bakinsa har kunne ga malum malum d’insa dik sun sauk’e sun rufe ledar.. Tsaban takaici Sadiya mik’ewa tai Ta shige d’aki dan bazama ta iya duban fuskarsa.

Umma na nan zaune tsakar gidan saman tabarma Ashiru ya k’araso ya zauna gefenta sai lasar Ice cream d’in yake.

Shafa kansa Umma tai tace ya kan naka. Ya daina ciwo.?”
Ya jinjina mata kai yana bud’e ledar biscuit d’in dake d’aya hannunsa.

Umma ta Shafa kansa tace “Tashi ka shiga ciki koh ka bamu waje.”

Ya mik’e yana jinjina kai.. Yana shigewa Sadiya ta fuzge tarkacen da ya shigo dashi tai watsi dasu.

Kuka ya shigayi yana bori yana fad’in Maiyasa ta yar masa abinsa.. Ko takan kukan Ashir batabi ba ta shige d’aki zuciyarta na mata d’aci.

Umma da Alhaji Isyaku dik sunji abinda ya faru a kunnuwarsu..

Dikda jikin Alhaji Isyakun ya d’anyi sanyi bai fasa sanar da Umma buk’atarsa na son auren Sadiya ba..

Umma Ta murmusa cikeda takaici “Alhaji da ka daina wannan wahalan dan hukunci dai mun riga mun gama yankewa daga ni har Sadiya.. Kaje mun gode da niyyan taimako.”

Alhaji Isyaku yace “Baki fahimta ba Umma..”

“A’a ni dan Allah ka kirani da Uwani menene wani Umma.. Kaga Alhaji Takaba nake ba don tashin hankalin da muke ciki ba Ko barinka ka shigo gidan nan bazanyi ba.. Mun gode da kai Ashiru asibiti da kai dan Allah ina rok’onka ka tashi ka tattari kayyakinka ka tafi bamu buk’ata kuma kar ka sake dawo mana.”

Alhaji Isyaku ya murmusa kad’an yace “Umma kenan.. Barin fad’a miki kuna buk’ata na..”

Da mamaki Umma ke dubansa.

Alhaji Isyaku ya murmusa yana mai jinjina kai “ K’warai kuna buk’atana Umma.. Ya kamata ki sake tunani akan wannan al’amari.. Ki tuna makomar rayuwarku musamman yanzu da babu mahaifin yaranki.. Ki tuna halin rayuwa da zaku fuskanta.. Shin kina tunanin Sadiya zata samu miji ne bayan duk abubuwan da suka faru..? Kindai ji da kunnuwanki irin maganganun da mutanen unguwa keyi akan d’iyarki.. Kina tunanin akwai wanda zaizo ya aureta a haka..?” Ya kuma kannare idanu yana kuma duk’ar da kansa yace “Amma ni zan biya maku bashinku sannan zan auri d’iyarki na d’auketa daga garin nan, zan kaita can da nisa yanda babu wanda ya santa, gaba d’aynku ma zaku bar nan zaku koma sabon waje ku soma sabuwar rayuwa a can yanda babu tashin hankali babu komai..”

Umma da hawaye ke gangaro mata kafin takai ga furta wani kalma suka jiyo sallama daga waje.. Babu shiri Ta mik’e dan ba muryar kowa bane face Aminu dillalin da ya basu hayan gidan da suke ciki..

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai Umma ke nanatawa cikin zuciyarta.. Ta d’aga idanu tana duban glasses na window da Tabawa da ‘yandabanta suka fasa..

Umma murya na rawa take fad’i da Aminu “Malam Aminu Barka da Safiya..”

“Uwani ba wannan ya kawoni ba.. Zuwa nai dan na tabbata Kun fice daga gidan nan. Bazan d’auki asara irin haka ba.. Zamanku a gidan nan babu alkhairi dama baku biya kud’in hayan bara ba ga na bana.. Sabida mutuwar mijinki yasa na d’an d’aga maku k’afa. Nayi niyyan maku mutunci na barku ku zauna har ki ida takabanki kafin na sallameku amma Tunda abun ya zama haka gaskiya zaku tattara ku fice a gidan nan dan amana Alhaji ya bani.. Tinda nake masa dillancin gidajen hayansa a unguwar nan bamu tab’a samun matsala ba.. Bazan fara akanku ba, na kula masifa da tashin hankali bibiyarku suke Dan haka kawai ku biya kud’in hayanku ku k’ara gaba tin kafin Alhaji Sadi yaji wannan batu..”

Cikin rawar murya Umma ke fad’in “Malam Aminu dan Allah kai hak’uri ka taimakemu.. Ka rufa mana asiri yanda Allah ya rufa maka.. Idan muka tashi a nan bansan Ina zamuje ba.. Dan Allah kaji tausayinmu.. Ka bari Ko Takaban ne na gama.. Inada yara Malam Aminu bansan ina zan kaisu ba idan muka tashi a nan..”

Girgiza kai Malam Aminu yai yana duban wani gefen dan karma Ta basa tausayi “A’a Uwani.. Gaskiya bazan iya ba.. Gidan nan nima amana ce a hannuna, kawai ki daina rok’ona dan bazai yuwu kuci gaba da zama a nan ba.. Maganar gaskiya kenan..!” Ya k’arashe yana mai jaddada maganar tasa..

Alhaji Isyaku dake gefe gyaran murya yai yace “Aminu kayi hak’uri kar ka tashesu.. Ni zan baka kud’ed’en da ake binsu zan kuma biya damages d’in da Tabawa tayi ma gidan.. Mu k’arasa gidana ka amshi kud’ad’en..”

Umma baki sake take duban Alhaji Isyaku, Ta rasa wanne zatayi dan batada bakin maganar a halin yanzu.. Tana ganin Alhaji Isyaku da Aminu suka wuce Aminu yana fad’in “Wllhi ba don kai ba Alhaji saidai su bar gidan nan a yau dan na lura tsautsayi ke bin ahalin..”

Juyowan da Umma zatai taga Sadiya na tsaye bayanta hawaye na bin fuskarta.. Su duka biyun babu wanda ya iya cewa komai sai rungume juna da sukai had’i da sakin kuka mai ban tausayi..

**

Hindu ce taima Ajidde iso zuwa parlorn Aunty Nuratu. A nan suka tadda Inne harmada Aunty Shamau.
Ajidde ta risina ta gaishesu sai kalle kallen kayan alatu take wanda aka k’awata d’akin dasu. Tab lallai da ace zata iya kwashe wannan kaya takaima Kyallu da ta gama saye zuciyar Kyallu da imaninta..

Yanda take kalle kalle tana d’aga kai yasa Shemau zuba mata idanu fuska a yatsine “Ke.!! kiyi abinda ya kawoki ki tafi kin tsaya sai faman kalle kalle kike..”

Tsawan da Shemau ta daka mata saida ya sanyata zabura Ta k’ame waje guda.

Inna kaw a hasale Ta katse Shemau da fad’in “Haba Shemau ki bita a hankali mana.. Meye abun fad’a a nan inyi. Baki ganin yarinya ce..”

Shemau Ta d’an sassauta murya tace “Inne babu wani yarinta muguwar k’auyanci ne kawai..”

“K’auyanci.? Ked’in yaushe ne kika waye..! Koda wasa ni Kinsan bana d’aukan wulak’anta d’an Adam.. Ki k’yale yarinya tayi aikinta a natse, Zo ki fice ma bansan zaman mai kike a nan ba..”

Shemau ta d’an b’ata fuska ta fice ranta baiso ba Inne naci gaba da sababi..

Ajidde taima Shemau gwalo cikeda jin dad’in bayanta da Inne tabi...

Mamaki ya cika Shemau dan taga sanda Ajidde ta mata gwalo harda kashe mata ido guda.. A ranta tace lallai wannan yarinya sai ta gyara mata zama.

Tana ficewa Ajidde ta saci kallon Inne saidai itama Inne ita take duba murmushi saman fuskarta.

“Taho muje.” Inne tace sanda ta mik’e ta nufi k’ofar d’akin da Aunty Nuratu ke kwance.

Ajidde tabi bayanta rungume da jakar maganinta still sai kalle kalle take tana k’are ma gidan kallo.



SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*



*16*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Suna ficewa daga lungun Alhaji Isyaku ya mik’a ma Aminu hannu saka tafa yana sakin muguwar dariya.

“Kai Aminu naji dad’in yanda ka masu barazana, na tabbata yanzu basuda yanda zasuyi face su amince dani.”

Aminu ya dafe kud’ad’ensa yana k’irgasu yake fad’in “Toh kai d’in ai bana wasa bane Alhaji. Na gode K’warai. Idan kanaso na koma gobe ma zan koma na kuma masu barazana.”

Alhaji Iskyaku ya kuma aza babbar riga yana sakin dariya “Aminu Aminu.. Ai bayan abinda ya faru yanzu dole zasu amince dani dan idan ba haka ba basuda mahalli, kaga basuda sauran zab’in da ya wuce su amince dani.”

Suka kuma k’ek’yata dariya Aminu na kuma godiya, nan yai sallama da Alhaji Isyaku ya wuce.

**

Tinda Inne ta tura k’ofar d’akin gaban Ajidde ke yankewa, batasan mai zata gani cikin d’akin ba amma kam zuciyarta ya tsananta bugawa. Bugun zuciyarta ya k’aru sanda Ta hango matar dake kwance saman gado idanunta a lumshe. Sumarta da yake tamkar na Indians ya rufe b’angaren fuskarta. Fuskar nata yayi fayau irinta marassa lafiya. Dan koda gani ba wata fara bace can tsananin Jinya ne ya sanya fuskar nata yin fari. Saidai ga dukkan alamu tanada Yalwan suma irin mai tsananin tsantsin nan.. Ajidde taci gaba da takowa a hankali tana jin zuciyarta na wani irin fuzga tana duban matar. Kyallu tasha kwantar da majinyata a gidanta tana masu magani da rawan Bori wanda akasari mutuwa suke amma ko kusa bata tab’a karo da matar da ganinta ya mugun raunana zuciyarta irin wannan matar ba. Taci gaba da takowa zuwa gadon da matar ke kwance bisa.

Inne na hankalce da ita har ta k’araso.
Ganin ta zubawa Aunty Nuratu idanu Ta kasa janye idanunta yasa Inne gyaran murya ta soma fad’in “Shekaru goma sha biyar kenan tana kwance haka. An gwada magunguna da dama, anje k’asashe da dama amma babu wani abinda yake canzawa haka za’a hak’ura a dawo da Ita.. Mun yanke shawarin dawowa gida ko Allah zaisa a dace.”

Ajidde tasa hannu Ta share hawayen da taji na ziraro mata.

Inne ta kuma dubanta tace “Ban tambayeki ba. Ya sunanki.?”

Ajidde ta d’ago tana duban Inne “Suanana Ajidde.”

“Ajidde.” Inne ta nanata, sai kuma ta saki murmushi tace “Ina fata maganinki ya mana aiki Ajidde.. Ina fata Ubangiji yasa mu dace da maganinki.. Allah ya nufa maganin Nuratu na cikin tafin hannunki.”

Ajidde Ta d’ago manyan idanunta da suke farare k’al masu gauraye da hawaye tana duban Inne dasu. Bata iya furta komai ba Sai duk’awa da tai gaban gadon tana k’ok’arin bud’e jakan maganinta.

“Amm Hajiya ko zan d’an sami k’aramar kwano.?” Ajidde ta tambaya tana duban Inne.

Murmushi Inne Ta sakar mata Tace “Ki kirani da Inne kinji koh..”

Ajidde ta maida mata martanin murmushin tana mai jinjina kai tace “Toh Inne..”

Inne ta kuma murmusawa kafin ta bud’e murya tana kiran Hindu.
Hindu ta shigo cikeda risinawa tana fad’in “Gani Inne.”

“Kije ki kawo mata kwano k’arama.”

“Toh Inne.” Hindu ta amsa tana mai ficewa.

Ajidde tai zuru tana jiran taga ko Inne zata fice amma bata fice ba, dik addu’an da take cikin zuciyarta matar ta fice daga d’akin domin ta gudanar da abinda Kyallu ta turota tayi amma tak’i ficewa. Har Hindu ta k’araso da k’aramar kwano ta mik’a ma Ajidde. Ajidde ta amsa tana mata godiya. Har lokacin dai Inne na zaune saman kujera mai kallon gadon Aunty Nuratun Ita kaw Ajidde tana zaune gaban gadon tana k’ok’ari ciro had’in maganin.. Wani ruwa cikin gora irin wanda ake fafewan nan ta ciro.. A hankali ta soma zuba ruwan cikin kwanon.. Saida ta ida zubawa kafin ta ciro had’in maganin tana tina bayanan yanda ake had’a maganin daki daki.. Tana ida had’a maganin ta rik’e cikin hannuwanta guda biyu tana duban matar dake kwance, hannayenta sai rawa suke, zuciyarta na wani irin tsinkewa.
‘Ke Ajidde kiyi k’ok’arin saita kanki idan ba so kike asirinki ya tonu ba.’ Ta fad’i haka cikin zuciyarta.
Ta d’an juyo ta dubi Inne wacce itama Ajidden take duba “Inn Inne nace Ko za’a d’an tallafa mun kanta zan bata magani."

Dai dai lokacin Mu’azzam yai sallama ya shigo, kayan training ne jikinsa, ga dukkan alamu daga morning jugging ya fito.

A tare Inne da Ajidde suka dubi mai sallaman. Zuciyar Ajidde yai wani irin yankewa, k’iris ya rage bata tintsirar da ruwan maganin dake rik’e cikin hannunta ba, dikda ba da wannan shigar ta gansa ba fuskarsa bai b’ace mata ba, tana tuno sanda ya nunata da bindiga daga yanda yake a saman bishiya.

Gaisawa Mu’azzam yake da Inne amma Ajidde bata janye idanunta daga dubansa ba. Har saida Inne tace “Yauwa Modibbo na tinda ka shigo sai ka taimaka mata ta bawa Nuratu maganinta dama zan kira Hindu ne tinda ni banida k’arfin d’agata amma tinda ka shigo sai ka taimaka mata.”

Mu’azzam ya juyo yana duban yarinyar da zata bawa mahaifiyarsa magani, K’uri yai mata yana so ya d’ago a ina yasan fuskar tata.. Taso ta masa kamanni da fuskar da ya sani amma ya kasa tuna ina yasan fuskar. Haka kurum yanayinta yai masa Zubi dana criminals abinka da wanda ya saba cin karo da masu laifi.. Shi bama wannan ba mamaki yake Wai wannan k’aramar yarinyar ce zata bawa Maminsa magani..? Jiyo muryar Inne da yai tana fad’in ya tallafo kan mahaifiyarsa a bata magani kar lokaci ya k’ure ya dawo dashi daga duniyar tinanin da ya tafi. A hankali yake takowa har ya iso kusan Ajidde.. Ajidde dai sai kauda fuskarta take alamun bataso mutumin nan ya ganeta.
Idanunsa naga Ajidde yake k’ok’arin tallafo kan mahaifiyarsa. Dik iya tinaninsa dan ya tina a ina yasan wannan fuskar ya kasa.

Maidoda dubansa ga mahaifiyarsa yai yana k’ok’arin d’ago kanta. Ajidde sai rawa hannunta yake tana k’ok’arin kai kwanon kusan bakin Aunty Nuratu.

“Dakata.!” Ya fad’i yana duban ruwan maganin da yake bak’ik’irin.

Cak Ajidde ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa.

“Wannan ruwan za’a bata.?” Ya tambaya yana kuma duban ruwan.

Inne tai karaf tace “Maganin kenan za’a bata. Kasan had’e had’e ne.”

“But Inne wannan zai iya cutar da lafiyarta dan bamusan da mai da mai aka had’a ba.. Sannan wannan yarinyar itace mai maganin dama.?”

Inne ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Banda abinka Modibbo jinjiri ma ai sai ya baka magani kuma a dace idan Allah ya nufa. Karka damu da yanayin wanda zai baka magani kawai kai add’uan dacewa.. Mudai fatanmu shine Allah yasa a dace.”

Ya jinjina kai a hankali yana mai maidoda dubansa ga ruwan maganin.

Idanun Ajidde naga hannayen Mu’azzam da ya tallafi mahaifiyarsa wanda suke fresh dasu. Ta kasa janye idanu daga duban yatsun hannunsa da suke dogaye tamkar dai yanda yake da tsayi... Tsaban kallon yatsun hannayensa da take k’iris ya rage bata d’urawa Mamy magani a hanci ba. Mu’azzam yai caraf ya rik’e hannun nata wanda ke k’ok’arin Kai magani hancin mahaifiyarsa.. Jin hannunsa saman nata ya sanyata d’agowa a zabure tana dubansa zuciyarta na wani irin yankewa.

Shiko yasha mur sosai yake dubanta “Concentrate.. Ki kula..” Ya fad’i fuska babu walwala.

Ajidde ta jinjina masa kai amma jin bai sakar mata hannu ba ya sanyata kai idanunta ga hannayen nasu.. Sai sannan shima ya dubi yanda take kallo. A hankali ya sakar mata hanunta kafin ya kuma tallafe kan Mamy sosai..
Wane irin nannauyan ajiyan zuciya Ajidde ta sauk’e kafin ta soma k’ok’arin bawa Mamy maganin, a daidai sanda ta kawo maganin dai dai saitin bakinta tana jin sanda Mu’azzam ya furta Basmala a hankali. Batasan dalili ba amma taji wani irin natsuwa na sauk’o mata a lokacin da yake ambaton Allah.

A haka Ajidde ke bata maganin, rabi na shiga bakinta rabi na zubowa jikinta. Inne ta taso ta gyara mata napkin d’in dake d’aure wuyanta har saida Ajidde ta ida bata ruwan maganin kafin Mu’azzam ya maida kanta ya kwantar, ya dafa goshinta da gumi ke tsartsafowa tin sanda aka soma bata maganin. A hankali ya share mata zufan yana mai kuma gyara mata kwanciyar. Ya jima yana duban fuskar mahaifiyar tasa yayinda Ajidde ke k’ok’arin tattare kayyaykinta.

“Allah baki lafiya Maami.” Ya fad’i yana maida mata sumarta cikin hulan da aka rufa mata.

Ajidde samun kanta tai tana mai furta “Ameen.”

Yai saurin dubanta dan yaji Ameen d’in data ce, ya soma k’ok’arin tino yanda yasan irin muryar amma nan ma shiru bai iya tuna komai ba. Ganin zai bawa kansa wahala babu dalili ya sanyasa mik’ewa yana duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu.

“Abinci fah ko sai zuwa anjima.?” Inne ta tambayesa cikeda kulawa.

“No sai zuwa anjima Inne, zanyi wanka yanzu dai.” Yana ida fad’in haka ya nufi k’ofa.

Inne ta jinjina kai tace a fito lafiya.

Ajidde kaw alla alla take ta gama abinda take ta fice daga gidan kafin wannan mutumin ya kamata dan ta lura sam bai d’auko kamanninta ba. Ta murmusa cikin zuciyarta tana fad’in ta Ina zai d’auko kamanninta bayan yau d’in gaba d’aya ta canza yanayi, yau d’in jan powder ta shafa Wanda ya k’ara ma bak’in fuskarta haske sannan bata cika kwalliya ba kad’an tayi kuma harda hijabi Ta saka ba kaman wancan ranan ba, gaba d’aya dai ta sauya yanayi yanda ba lallai a ganeta ba. Canza yanayi da kamanni dik na cikin d’abi’ar Ajidde tinda dama damfaran mutane Kyallu ke sanyata yi, mai Sana’a irin nata dole yanada dabaru na b’adda yanayi daban daban.. Ta kuma murmusawa tana fad’i cikin zuciyarta Wo ni Ajidde gaskiya na iya shashashantar da mutane tinda na shashantar da wannan k’aton.. Muryar Inne ta sinkayo tana fad’in “Ajidde idan kin gama da maganin nata sai kici abinci ko.. Hindu zata baki abinci.”

Ajidde ta girgiza kai tace “A’a Inne na gode, sauri nake akwai yanda zanje na kai magani.”

Inne tace “A’a ai kuwa dole zakici abinci dan ba’a zuwa gidan nan a fita ba’aci komai ba kinji koh.. Jirani a nan Ina zuwa.”

Ajidde ta jinjina kai tana murmusawa. Inne tana fita Ajidde ta mik’e tana k’are ma d’akin kallo.. Ya zama dole ta nemi abinda zata d’auka takaima Kyallu.. Saidai sam idanunta basu gane mata wani abinda zata d’auka ba. Sannan bata jin zata iya satar ma Kyallu wani abu a d’akin majinyaciya irin wannan.. Yanzu ya zatayi.? Bata isa ta koma ma Kyallu hannu banza ba dan Ta tabbata muddin ta koma mata haka a d’akin awakai zata kwana. Tana tsaka da tinanin ta hangi k’ofar d’akin a bud’e a hankali cikin sand’a ta fito daga d’akin. Doguwar corridor ta hanga da ya mik’e zuwa b’angaren hagu, ga wasu k’ofofin kana iya hangowa. Cikin sand’a Ajidde ta soma bin wad’annan k’ofofin.. Tana tafe ta hangi wata kaman bata ida rufuwa kirif ba. Ta Washe baki tana fad’i a hankali “Sa’arki tazo Ajidde.” Cikin sand’a ta isa jikin k’ofar tana turata a hankali. D’akin tas tas Sai k’amshin ‘yan gayun da take shak’a kaman dai yanda tace a cikin zuciyarta. Ta lumshe idanu tana shak’an k’amshin. “Kaji k’amshin Turawa.” Ta fad’i tana gyad’a kai. Ga kuma zuban ruwa tana jiyo daga wani wajen amma batasan daga ina bane. Kar dai ma ana kallanta.? Ta tambayi kanta cikin zuciyarta. Kafin takai ga nemo amsar tambayarta ta hangi wannan bak’ar jakan Ta mutumin nan data so masa sata dan sam bazata mance jakan ba, sannan shine mutumin da ya taimaka mata suka bama matar nan magani. Ajidde ta Washe baki tana fad’in “Jaka jin nace sai na sata ma Inna Kyallu abinda ke cikinki.. Watau yauma saida kika biyoni. Toh Bari dai muga Meye a cikinki.” Tana ida fad’in haka ta k’araso kusan jakan tana mamakin yau a bud’e ta sami jakan. Saidai k’arasowarta jikin jakan kenan taji an turo k’ofar d’akin an shigo.

Cak Ajidde ta tsaya ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login