Showing 192001 words to 195000 words out of 209154 words
shigo mata da farfesun kayan ciki da tace tana son ci.
Dubanta Safeenah tai tace “Iya nikam na tambayeki.”
Iya ta jinjina kai tace “Ina sauraronki.”
“Wai dan Allah meye alamomin mace mai ciki..?”
Iya ta zaro idanu waje tana tuna kashedin da Mommy ta masu. Ta kasa furta komai sai girgiza kai da take.
A kufule Safeenah tace “Bakiji tambayar da na miki bane..?!”
Daidai lokacin Mommy ta shigo.
Ta dubi Iya tace ta fice abinta.. Kana ta maidoda dubanta ga Safeenah “Mai kike son sani..?”
Safeenah ta kafe Mommy da idanu kafin ta girgiza kai tace “Kin sani Mommy.. Kinsan komai Kika zab’i ki b’oye mun.. Maiyasa Mommy..?” Ta k’arashe tana duban mahaifiyar tata.
Mommy Ta girgiza kai tace “Ban fahimci mai kike nufi ba..”
Safeenah ta mik’e zaune sosai tana kuma jinjina kai “Don’t play dump Mommy.. Kinsan komai.. Kinsan ina d’aukeda cikin Mu’azzam amma kika zab’i kiyi shiru kik’i sanar dani.. Mommy kina ganin yanda naketa faman shan wahala kan na karkato da akalar hankalinsa gareni.. Kina ganin yanda nake masifar son komawa gidan mijina amma duk kika zab’i kiyi biris sabida wani dalili naki.. Mommy shashanci nan ai bai kai yanda kike tunani ba.. Kina tunanin bana jin changes ne a jikina.. Kina tunanin bazan fahimci cewa inada ciki nan kusa bane.. Mommy abinda ban gane ba shine kan wane dalili zaki b’oye mun wann Babban makamin da zanyi amfani dashi wajen winning mijina back.. Haba Mommy Maiyasa zaki min haka.. Kinsan sarai Mu’azzam shine rayuwata shine cikar burina.. Maiyasa zaki hanani komawa gidansa..” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.
Mommy ta matso kusanta ta kamo hannayenta cikin nata, lallashinta ta somayi tana fad’in “Ba nak’i ki koma bane Safeenah.. Kuma ba nak’i sanar dake bane sabida wani manufa nawa.. Shin baki ganin yanda nake kulawa dake ne..? Irin tarairayar da ake wa mata masu ciki shi nake miki Safeenah..”
Cikin kuka Safeenah Ta fincike hannayenta daga cikin na Mommy tana fad’in “Ba ke kikeda alhakin kula dani da D’an ciki na ba Mommy.. Mijina shine zai tarairayeni ya kula dani.. Nayi imani da Mu’azzam yasan cewa inada ciki minti talatin bazan k’ara a gidan nan ba.. Haba Mommy wllhi ni kin cuceni.. Kinyi depriving mana right d’inmu nida d’ah na wajen kasancewa da mahaifinsa.”
Mommy ta girgiza kai “Safeenah ba haka bane.. Banda rashin wayo irin naki yanzu ai zai zaci k’Arya kawai kike masa babu wani ciki tattareda ke. Zaiyi tunanin so kike ya maidaki d’akinki sai kika b’ullo ta wann hanyar.. Kina tunanin zai yarda Kina da ciki ne.. Na bari cikin ya fito ne ya bayyana kowa ya shaida sai ki fi samun kulawar mijinki..”
Safeenah na hawaye take girgiza kai “Haba Mommy civilized world fah muke.. Kan wani dalili zaisa yak’i amincewa akwai gidan jininsa cikin jikina bayan ga prove na asibiti.. Mommy Mu’azzam needs to know.. He needs to know I’m carrying his child.. Kin fahimta..!” Ta k’arashe tana zaro idanunta dake jik’e da hawaye waje.
Ba tareda ta jira cewar Mommy ba ta janyo wayar salulanta ta soma dialing layin Mu’azzam..
Taita ruri ba’a d’aga ba. Ta soma k’ok’arin tura sak’o kenan Mommy ta kamo hannayenta tana fad’in “Mai kikeyi..?”
A d’an dak’ile take duban Mommyn “Text zan tura masa yasan da zaman D’ansa cikin jikina.”
Mommy Ta girgiza kai tace “Haba ke kaw Safeenah. Yanzu fah Mu’azzam a tafin hannnunki yake sai yanda kikaga damar juyasa. Yanzu lokaci ne da zaki d’aga darajarki a idanunsa ba wai kiyita lik’e masa kaman wata ‘yar anace ba. Ai idan kinaso ya yarda ya amince ciki gareki ba ke ya kamata ki kirasa ba. Ni ce nan zan kirasa na kuma sanar dashi halinda kike ciki.. Na tabbata idan yaga kirana bazai tsallake ba zai d’aga.”
Safeenah tai shiru tana duban Mommy kafin Mommyn ta jinjina kai a hankali, tai kiran mai aiki ta d’auko mata wayarta a uwar d’aki.
Ana kawo wayar Mommy Ta danna kiran Mu’azzam yayinda Safeenah Ta kafeta da idanu.
**
Mu’azzam kaw suna tafe saman kwalta shida Assad wayar Mommy ya kuma shigo masa bayan kiran Safeenah ya k’araci ruri bai d’aga ba.
Assad ya dubesa ya girgiza kai kad’an yace “Wai bazaka d’aga kiran nan ba.. Zai iya zama wani abu ne mai mahimmanci.”
Ba tareda ya dubi Assad d’in ba, idanunsa da hankalinsa naga tuk’in mota da yake yace “Mommy ce mai kira nasan duk bazai wuce kan fitinar Safeenah bane.”
“Haba Mu’azzam Mommy Ta wuce kaga kiranta kai biris da ita.. Ka daure ka d’aga kaji ko menene.. Tinda har kaga Safeenah ta kira sann ga Mommy na kira na tabbata it might be something serious.. Ko ba komai Mommy uwa ce ka d’aga wayarta dan Allah.”
Gajeren fuci ya fuzar kafin ya d’aga wayar ba tareda yace uffan ba tinda yasan shidai a idanun Mommy Sarkin laifi ne.
Daga d’aya b’angaren Mommy na jijjiga kaman wani Mu’azzam d’in na ganinta take fad’in “Ka rik’e gaisuwar ka dama bana so..” Saida tai fasali kafin tace “Mu’azzam, kazo ka d’auki matarka Safeenah ko dan ajiyan da kayi cikin cikinta.”
Out of the blue yaji maganar wanda har saida yasa ya kusan gwaran motar gabansa dan baima kula traffic light ya tsaida su ba.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*60*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
D’if yaji Mommy Ta katse kiran ba tareda Ta saurari abinda zaice ba.
Ya dinga nanata maganar Mommy a kwanyarsa yana ji kaman sautin maganar cikin kunnensa. Dik maganan da Assad ke masa yana fad’in an basu koren wuta baiji mai Assad d’in ke fad’i ba har saida ya soma jiyo horn daga motocin dake bayansa sahu sahu.
A hankali ya soma jan motar yana kuma jin maganar Mommy har wann lokacin.
“Are you alright..?” Assad ya tambaya daga yanda yake zaune gefensa.
Bai amsa Assad ba sai canza hanya da yai ya d’auki hanyar gidan Daddy dan dama kusan layin gidan suke. Assad ya zuba masa idanu dan yasan tinda Yai shiru bai amsa ba idan zai kwana a wajen yana tambayarsa ba lallai ya amsa d’in ba.
Suna isowa Assad ya dubesa kad’an yace “Daddy fah yana ciki ne..? Naga kusan duka motocinsa gasu nan a gida.”
Girgiza kai Mu’azzam d’in yai jikinsa duk ba kuzari “No yana Adamawa..”
Gyara zamansa cikin kujera Assad yai yana fad’in “Tinda baya nan no need na shiga ka shiga kai Bikon matarka kai kad’ai dama da Daddy na nan ne da Sai na shiga na tayaka biko.. A fito lafiya.” Ya fad’I yana mai tura kai cikin kujera cikeda zolaya.
Mu’azzam bai ce masa komai ba sai dubansa da yai kad’an kafin yasa kai ya nufi cikin gidan.
Zaune ya hango Safeenah a parlor fruit salad bowl ajiye gabanta. Aiko Safeenah tana jin alamun shigowarsa tai saurin ture kwanon fruit salad d’in ta soma yunk’urin amai kai kace da gaske aman ne ke taso mata.
Cikin sauri ya k’araso parlorn yana ambato sunanta “Feenah are you alright.? Do you need help..?” Yana maganan yana k’ok’arin duk’awa kanta.
Safeenah bata amsa sa ba sai k’ok’arin k’wak’ulo amai take tana rik’e cikinta tana kiran Mommy.
Babu shiri Mommy ta k’araso tana raba tsakanin Mu’azzam da Safeenah take fad’in “Safeenah sannu koh.. Cikin ne.. Tashi muje na rakaki bathroom.. K’ok’arta ki tashi..”
Kuka Safeenah ta fashe dashi tana kuma narkewa take fad’in “Mommy cikina it hurts.. Mommy bazan iya tashi ba.. Wayyo Mommy..”
Mu’azzam ya d’an kuma matsowa kaman mai son taimaka wa Safeenar.
“Kar ka kuskura ka tab’a mun ‘ya kauce ka bamu waje..” Mommy tace tana rik’o Safeenah, Mu’azzam ya d’an matsa gefe kad’an ya zuba masu idanu har suka nufi toilet.
Furzar da huci yai kad’an yana mai daidaita tsayuwarsa, nan idanunsa suka sauk’a kan takarda dake gefen Safeenah. Ya k’arasa ya d’auki takardan yana karantawa. Sakamakon gwajin cikin da aka mata ne wanda yai daidai da lokacin data sha poison har aka bata gado a asibiti.. Safeenah nada ciki har poison take sha duk a sabida shi.. What if wani abu yaje ya sami d’an.. Koma cikin ya fice gaba d’aya.. Baya fata rashin hankalin Safeenah yasa ya rasa D’ansa ko ‘yarsa dake cikinta.
Yaita juya takardan yana kuma nanatawa cikin zuciyarsa, Wai shi Mu’azzam zaiyi D’ah.. Allah mai iko.. Sai kuma yaji murmushi from no where na zuwa masa.
Yana nan zaune saman kujera har su Mommy da Safeenah suka fito, Mommy na tallafe da ita. Yanda Mommy ke riritata Kai kace kanta aka soma yin ciki.
“Sannu ko.. Kina buk’atan wani abu ne..?”
Idanunta a lumshe tace “No Mommy.. I just need to rest.” Ta fad’i daga nan yanda take kishingid’e.
Mommy ta dubi Mu’azzam da ya tsare Safeenar da idanu, har lokacin takardan na nan cikin hannunsa “Toh likita yace kar a dinga d’aga mata hankali.. High risk pregnancy ne da ita.. Matuk’a tana shiga damuwa komai ka iya faruwa..” Daga haka bata saurari mai zaice ba ta juya ta fice.
Mu’azzam baice komai ba, kansa na duk’e har Mommy ta gama maganganunta.
Tana ficewa ya taso daga kujeran da yake ya dawo kusan na Safeenah.
Safeenah tana jin alamun dawowarsa kusan kujeranta, tsaban kewarsa da tai sai taji kaman ta rungumosa ta sanar dashi irin missing d’insa da tai.. Amma sai Tai k’ok’arin rik’e kanta sabida ta d’auki shawarin Mommy na cewa Ta nuna masa itama mace ce kuma tanada aji da matsayi musamman yanzu da zata bashi abunda babu wata mace da Ta tab’a basa wato D’an cikinta. Muryarsa ta sinkayo Wanda Ta jima bataji ba, muryar da duk duniya babu muryar da take jin dad’in sauraro sama dashi.
“Why didn’t you tell me.. Maiyasa baki sanar dani tuntuni ba.?”
Idanunta a lumshe still tana nan kishingid’e take fad’in “Ka damu ka sani ne.. Yanzu ma ba don ina cikin mawuyacin hali ba da bazan bari Mommy ta kiraka ba..” Muryarta ya soma rawa irinta mai kuka “Kayi neglecting d’inmu nida abinda ke cikina.. Baka damu kasan wani hali nake ciki ba.. Yanzu idan aka haifo D’an nan yaji ga abinda Dad d’insa yaiwa Mom d’insa lokacin da nake d’aukeda cikinsa kana tunanin yaron zai tab’a yafe maka ne..?”
Ta bud’e idanunta masu zuban hawaye “Every single night cikin pain nake bacci sabida high risk pregnancy da nake d’auke dashi.. Dr ya bani bed rest ko toilet wasu lokutan bana iya zuwa sai Mommy ta taimaka mun.. Duk baka San wann wahalan da nake sha ba bayan cewa D’an nan ba nawa ni kad’ai bane harda kai.. And idan na haifesa har sai ka fini gadara dashi.. Sabida ku maza haka kuke.. Mace zata d’auki ciki na tsawon watanni tara.. Ta raini kayanta tayi enduring duk wani pain amma sabida son zuciya irin naku na maza ku amshe yaron nan ku rabasa da uwarsa yayi tashin maraici.” Ta gyara zamanta tana ci gaba da fad’in “Irin haka ne kake so ya faru da d’anmu..? Do you really want our child to grow up without a complete family... Do you really think your decision won’t affect our child..?!”
Tinda Ta soma magana yake tattara naman goshinsa yana furzar da iska a hankali. D’agowa yai had’ida dakatar da ita da fad’in “Enough Safeenah.!”
Tai Burki tana dubansa da idanunta masu zuban hawaye.
Daga nan yanda yake zaune ya d’an rank’wafo hannayensa saman gwiwoyinsa yake jinjina kai yana fad’in “My child won’t grow up without a complete family in sha Allah.” Yana maganar yana jinjina kai alamun tabbatarwa.
Wani irin sanyi Safeenah taji ya ratsa zuciyarta tana jira taji yace ya maidata d’akinta sai sinkayo muryarsa tai yana fad’in “Have you forgotten.. Inada mata, and I’m hundred percent sure zata kular mun da d’ah na ina raye ko bana raye..” Yaci gaba da jinjina kai still yana duban Safeenah wacce ta daskare tana dubansa “I’ll be a parent to my child.. Koda ban zama miji ga mahaifiyarsa ba.”
Baikai aya ba ya hango Safeenah tana sauk’owa daga saman kujera cikin hawaye. Lokaci guda ta duk’a gabansa ta had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o..
Girgiza kai ya shigayi yana furta “What are you doing Safeenah.. Please get up..”
Bata tashin ba, taci gaba da hawaye tana fad’in “Nasan ni mai laifi ce.. Nasan nayi kurakurai da dama a baya.. But please kar ka bari kurakuraina ya shafi innocent soul d’in dake cikina... Ko banci darajan kasancewa ‘yaruwarta ba.. Naci darajan gudan jininka dake cikina.. Dan Allah kar ka bari D’anmu ya fito duniya ya tadda iyayensa basa tare.. Punish me all you want.. But please don’t punish our child..!” Ta k’arashe tana shafe cikinta still tana nan duk’e gabansa tana hawaye.
Tinda yake a rayuwarsa bai tab’a jin tausayin Safeenah irin na yau ba.. Allah ya gani baya sonta matsayin mace face ‘yaruwa.. Allah shine shaidar shi yana ma Sadiya soyayyar da bazai iya had’ata da wata mace ba.. Yana tsoron yai rashin adalci a tsakaninsu Ubangijinsa ya tuhumesa.. Amma yau yaji tausayin Safeenah.. Irin tausayinta da bai tab’a ji ba.. Shin yanzu idan Sadiya ta gujeshi zaiji irin ciwon da Safeenah ke ji cikin zuciyarsa..? Tambayar da ya kuma kashe masa gwiwa lak’was.
Cikin kwantar da murya yake fad’in “Safeenah.. Feenah.. Tashi ki zauna..”
Girgiza masa kai tai still tana duk’e gabansa tana hawaye “No.. Sai kace ka maidani..”
Ya furzar da huci kad’an yana shafe fuskarsa kafin ya duk’a nan gabanta suna fuskantar juna. Cikin yanayin kwantar da murya yake fad’in “Feenah ki nastu ki daina wann obsession d’in.. Ki tuna you are carrying a child in your womb now.. Abinda kikeyi can affect the child.. Look if you need a therapist zan nemo miki..”
Katsesa tai da fad’in “Aw bayan obsession da kake fad’i yanzu kuma mahaukaciya ka d’aukeni.. Well idan akan soyayyarka ne kana iya kirana komai.. Har abinda yafi mahaukaciya.”
Ya kuma furzar da huci kad’an yana mai duban wani b’angaren dan yanzu abin Safeenah ya daina basa mamaki, yafi danganta abin da rashin lafiya.. Idan bai bita a hankali ba za’a iya rasa abinda ke cikinta.
“Ba mahaukaciya na d’aukeki ba.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Idan na dawo zamuyi magana a natse. Kinga Dr yace high risk pregnancy kike d’auke dashi.. And shiga damuwa ko tashin hankali won’t do any good for the Baby.. Kuma kema Nasan baki son abinda zai samu Babyn right.?” Yanda yake maganar tamkar mai lallashin k’aramin yaro maras cikakken hankali haka yake mata.
Ta saki murmushi a hankali tana jinjina masa kai hannunta guda dafe da cikin nata.
Murmushi ya sakar mata shima kafin yace “Good.. Yanzu ki kwanta ki huta.. And idan kina son wani just tell me right away kinji koh..”
Ta jinjina masa kai a hankali kafin tace “Idan ka tafi zaka dawo ka dubamu..?I mean nida Babynmu..” Tana maganar tana shafa cikinta murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta.
Jinjina mata kai yai yace “Of course zan dawo.. Just get some rest now kinji koh..” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye ya isa ya gyara mata pillow da tai matashi dashi yace “Zo ki kwanta ki huta..”
Ta mike tana murmushi ta iso ta zauna a kujeran. Ya sakar mata murmushi kad’an kafin yace “I’ll be goin now..”
Ta sakar masa murmushi tace “Ka sayo min roasted corn.”
Ya jinjina kai yace “Akwai wani abinda kike so kuma.?”
Ta girgiza kai kad’an “No gasashiyar masarar yayi.”
Ya jinjina kai kafin ya sakar mata murmushi kad’an ya fice zuciyarsa fal tausayinta.
Safeenah tabi bayansa da kallo tana murmushi “Sannu a hankali Mu’azzam.. Zaka mai dani gidana kafin na haife abinda ke cikina..” Ta k’arashe zancen zucin nata tana mai gyara kwanciyar ta.
Mommy dake lab’e taji dik yanda sukai. Murmushi ta saki kafin ta furta a fili “Greatest weakness d’inka shine wann cikin Mu’azzam.. Na maka alk’awari ni kuma sai nayi amfani da wann cikin na tarwatsa ka.. Ba’a cin bashi na a wanye lafiya ni Hajara.!” Tana ida fad’in haka ta juya ta bar wajen.
Tana shiga d’aki ta tadda wayarta na ruri. Lamba ce Babu suna.. Ta yatsina fuska kafin ta d’aga kiran tana fad’in “Hello hello wake magana.. Hello ba service.. Wrong number... Shuuuuuu..!” Mommy tace tana Yawo da wayar a iska.
Muryar Shemau ta sinkayo daga d’aya b’angaren tana fad’in “Kar ki kuskura Hajara..!”
Mommy tai tsaye tana sauraronta yayinda Shemau taci gaba da fad’in “Wllhi idan kika kashe mun waya yau kam sai na tona miki asiri. Na Sani sarai mijinki na nan Fufore yazo duba matarsa.. Yau kusan sati kenan Ina kiranki da different lines kina raina mun hankali, da kin d’aga ki wani fara hello hello ba network.. Toh ko uban Network ne Babu yau kam kika katse mun waya wllhi sai na kwance miki zani a kasuwa. Naji labarin Alhaji Marwan Gamji na gari tin shekaran jiya.. I can go straight to him na sanar dashi komai duk abinda kika aikata wa matarsa.”
Mommy tai ‘yar bazawarar dariya kafin tace “Shemau kenan.. Yo ce maki akai barazanarki zai bani tsoro.. Ince atata kice mun had’a baki nida ke mun d’auko wa Nuratu mai gani na bogi..” Ta mik’e tsaye tana zagaye d’akin, still waya manne kunnenta. Muguwar murmushi saman fuskarta take fad’in “Barin tambayeki Shemau, tsakanin ni da ke wacece Kyallu ta sani..?”
Shemau tai shiru batace komai ba jin Mommy zata juya teburin zuwa kanta.
Mommy tai murmushin cin nasara kafin taci gaba da fad’in “Ko nuna ni akaima Kyallu nayi imani bata sanni ba, bata tab’a gani na ba.. Wa ta sani..? Wacece Ta d’auko ta matsayin mai magani..? Kece Shemau.. Ke kikai kid’anki kuma kikai rawarki.. Ke da kanki zaki kama kanki.. Kuma na miki imani da Allah yanda yanzu baki tareda Salman Gamji tsaf Mu’azzam zai turaku kurkuku ne keda Kyallu..” Ta murmusa kad’an kafin tace “Kin zata bani da hankali ne..? Kin zata ni shahshasha ce.. Shemau nasan yanda nake buga wasanni na.. Ce miki akai bansan amfani kike so kiyi dani ba.? Nasan dole Kema akwai abinda kike nema wajena Watak’ila nan gaba kad’an ki bijiro min da abinda kike nema shisa kike taimakona.. Toh ni ba mahaukaciya bace Shemau.. Nasan sarai mai nakeyi.. Bakida wata dalili ko hujja akaina.. Idan kuwa kikai gangancin sanar da Marwan Gamji kin d’auko wa matarsa ‘Yar damfara matsayin mai magani ba ke kad’ai ba harta mijinki sai Mu’azzam ya bincika.. Kinga kuwa a banza Salman zai kuma tsananki..”
Shemau ta saki baki da hanci tana jin tuggun da Mommy ke fad’i, Wato ashe itace babban Shashahsha da tai komai ita kad’ai ba tareda tayi involving Mommy ba