Showing 75001 words to 78000 words out of 209154 words
kan yaron murmushi saman fuskarsa. Da yawan yaran ko magana basu iya ba wasu kuma gwalamniya suke.. Duk yanda ka kai ga taurin zuciya idan kaga wad’ann bayin Allah dole kaji rauni ya ziyarci zuciyarka, ka kuma tina cewa kai d’an Adam ba komai bane, yanzu labarin rayuwarka zai iya canzawa.. Wad’ann mutane basuyi laifin komai ba ba wai kuma dan Allah yak’isu ba ya jarabcesu da irin wannan jarabawa. Sannan kaima ba wai dan yafi sonka bane ya baka cikakken lafiya.. Saidai dan ya jarabceka da lafiyar nan da ya baka yaga zaka gode masa ne ko zaka bijire ma rahamarsa.
Muryar Daddy ya sinkayo yana fad’in “Mu’azzam my Son, this is where I invited your inheritance.. Ban Sani ba ko na maka katsalandan amma tin lokacin da na fahimci bakada interest akan tara dukiya da abin duniya sai nayi tinanin bud’e wannan cibiya na taimaka ma nakasassu, da nusar dasu cewa nakasa ba gazawa bace.. Ana koyar da yaran karatu wasu ma ana koya masu san’a sannan wanda dik ya k’ware a sana’arsa ana tallafa masa da kayan sana’a sai a sallame sa a kuma d’iban wasu.. Wannan Cibiya taimakon masu jarabawar nakasa take domin a rage yawan barace barace da nakasassun mu keyi saman kwalta wanda zaka samu wasu ma a garin wannan barace baracen sun rasa rayukansu, wasu an sace su anyi tsafi dasu wasu idan sun fita shikenan ba’a sake ganinsu..”
Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Ko wani budget na Company Naka kason nan yake zuwa..A halin yanzu kayi aure .. And very soon zaka fara tara iyali so ban Sani ba ko zaka ci gaba da tallafa ma wad’annan yaran, amma daga wannan lokaci kasonka a company zai ci gaba da tafiya asusun ajiyarka ne.. Idan kanada interst d’in ci gaba da taimaka masu falillahil hamdu idan kuma kanada wani tunanin in mind shima Alhamdulillah..”
Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Kai hak’uri idan nayi maka katsalandan..”
Saurin girgiza kai Mu’azzam yai hawaye na ciko idanunsa.
“Haba Daddy.. Mutumin da ya nema maka Aljannah kana gadon baccinka irin haka har zai nemi yafiya wajenka.. Daddy ni ya kamata nai maka godiya bisa wannan sadaukarwa da kai min.. Allah ya saka maka da gidan Aljannah Daddy. And wad’annan mutane masu jarabawar nakasa zasuci gaba da samun kulawa daga wajena in sha Allah da duk mai niyyan taimak masu. Allah yasa manyanmu a k’asar nan suyi koyi da irin wannan tinani da kayi Daddy.”
Daddy ya murmusa yana mai kamo kafad’un Mu’azzam d’in suka nufi cikin building d’in yana saka ma Mu’azzam d’in Albarka.
Har kusan azahar suna foundation d’in. Basu bar wajen ba har saida suka amshi list d’in kayan amfani da nakasassun bayin Allahn nan ke buk’ata musamman na sana’ar hannu da ake koyar dasu.
A wannan ranan Mu’azzam ya kuma ganin girman Daddy da jin nauyinsa. Ya kuma yarda Daddy uba ne na K’warai a wajensa.
**
Koda Sadiya tai wanka bata yarda ta tab’a kayan dake jere cikin wardrobe d’in ba dan tasan bazai wuce na matarsa bace.
Tai tsuka a hankali tana furta “Yanzu ya zanyi..? What do I do now..!” Tai maganar cikeda shagwab’a kaman wani yana ganinta.
D’aura hijab d’inta tai a k’irjinta ta nufi toilet da rigar nata tana fad’in “Zaka gani kayana zan wanke.. I’m not wearing your wife’s cloth Mr Inspector.!”
Ta tab’e baki tana kwaikwayon maganarsa “You can use everything here free of charge.. Mtsww Mannerless.!” Ta k’arashe tana mai tura k’ofar bathroom d’in.
Ta shiga ta wanke rigar ta fito ta nufi balcony tana bibbige rigar.. Sam bataji ko alamun shigowarsa ba balle rufe gate.. Tana nan tsaye wajen tana aikin bige rigarta.
Shiko Mu’azzam koda ya shigo bai ganta parlor ba, tab’e bakinsa yai kad’an kafin ya nufi upstairs yasan ba lallai dama ta zauna a parlorn ba. Kai tsaye upstairs ya haye.
Sautin buga abu da yake jiyowa daga d’akinta shi ya janyo hankalinsa. Yai tsaye yana duban k’ofan d’akin yana tinanin Toh meke faruwa da Ita. Lokaci guda ya yanke shawarin tura k’ofan d’akin.. Bai ganta cikin d’akin ba amma ga k’ofan balcony a bud’e. Lokaci guda ya nufi balcony d’in mamakin sautin k’aran buge abu da yake jiyowa bai bar saman fuskarsa ba.
Da tsananin mamaki Mu’azzam ya tsaya yana duban Sadiya dake d’aure da Hijab tana buge jik’akk’en rigarta.
“What.!” Ya furta da d’an k’arfi.
A wani irin birkice ta juyo tana mai sakin k’ara dan bataji shigowarsa ba sai muryarsa.
Ta shiga manna jik’akk’en rigar jikinta tana kare Jikinta dashi.. Cikin huci take furta “What are you doing here..?”
“This is my house, and I don’t remember asking for your permission idan Ina son shiga ko Ina a cikin gida na.. Get ready we are going out..!” Ya fad’i yana mai juyawa.
Kaman kuma wanda ya tina wani abu ya juyo yana dubanta k’asa k’asa musamman k’afafunta da take ta k’ok’arin d’ingilesu tana b’oyesu yace “And don’t think of wearing that thing you are holding.. wear something nice and decent..” Daga haka Sa kai ya fice ba tareda ya kuma cewa komai ba.
Rausayar da idanunta tai tana mai rakasa da mugun kallo.. “Tyrant.!” Ta fad’i tana jan gajeren tsaki.
SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO*
*26*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Rigar nata ta maida dikda cewa bai bushe ba, Allah ya gani bazata saka kayan da yace ta saka ba. Ta window take hangensa yana tsaye jikin motarsa waya mak’ale kunnensa. Tai tsuka a hankali tana tinanin ina zai kaita.. Allah yasa gajiya yai da zamanta a gidan, Allah yasa gida zai maidata wajen Ummanta. Wannan tinanin ne ya d’arsu a zuciyarta. Haka ta nufo waje sai rawan d’ari take dan harta hijab d’in ma da danshi jikinsa.
Da mugun mamaki yake kallonta, ya rasa wane irin taurin kunne take dashi, watau dai baza’a fad’a mata abu tai ba. Katse wayar yai yana dubanta yanda take k’ok’arin k’arasowa bakinta a ture tana kallon k’asa.
“Ke, Meye haka..?” Ya fad’i yana dubanta.
“Mene kenan..?” Ta tambaya tana d’an dubansa itama fuska a dame.
“Bance miki kar ki saka jik’akk’en kayan nan ba.. Do you want to fall sick.?”
Tab’e baki tai kad’an tace “Idan ma nayi rashin lafiyar ai jikina ne..”
Ya jinjina kai yana dubanta, a hankali ya furta “She’s so stubborn..” Ya d’ago yana dubanta kafin ya bud’e murya yace “And waye kike tinanin zai d’auki asaran saya miki magani.. Wuce kije ki canza kayan nan or else..”
“No I won’t change.. Kayana kenan..!” Ta fad’i tana mak’e kafad’a still tana rawar sanyi dan a lokacin ma hadari ne a garin iska na kad’awa.
Fuzar da huci yai kad’an kafin ya nufota, kafin ta ankara ya shiga janyo hannunta.. Tarjewa take tana fad’in “Malam ni ka sakeni.. Ni bazan saka wasu kaya ba bayan na jikina.. Bana so kuma bazan saka ba.”
Bakinta bai mutu ba haka nan shima Mu’azzam bai fasa janyota ba har suka shigo cikin d’akin. Tana gani ya bud’e wardrobe ya ciro wata Doguwar riga abaya kalan shud’i. Ta soma matsawa da baya ganin yana nufota.
Cikin rawar murya take furta “What are you doing.? Don’t come near me.. Dan Allah kayi hak’uri ka k’yaleni..” Ta k’arashe cikin rawar murya tana kuma matsawa baya.
Fuzgota yai ta fad’o cikin jikinsa fuskokinsu suka had’e waje guda.. Jikinta sosai ya soma rawa.. Ta shiga k’ok’arin turasa amma Ta kasa.. Kafin ta ankara taji hannunsa saman zip d’in rigarta yana k’ok’arin zugewa..
Kuka Ta soma tana girgiza masa kai “Please don’t.. Please..!” Tai maganar tana mai rintse idanunta jikinta bai daina rawa ba.
Mu’azzam kaw fuskarta yake duba musamman idanunta da ta rintse su da kuma bakinta da take motsawa a hankali tana rok’onsa ya k’yaleta.
A ransa yace ga tsoro ga tsaurin ido.
Jin ya tsaya Cak ya dena abinda yake ya sanyata tattaro sauran k’arfinta tai k’ok’arin turasa.. Aiko nan yai losing balance saidai bai yarda ya fad’a kan gadon shi kad’ai ba fuzgo hannunta yai suka fad’o gadon tare k’irajensu suka had’e waje guda.
Su duka biyun suna iya jin bugun zuciyar junansu.. Jikin Sadiya yaci gaba da rawa hawaye na gangaro mata. Tai azaman mik’ewa amma sai taji ya rik’eta ya hanata tashi.
Saitin kunnenta yake fad’i a hankali “Stop acting like you’re new in the system.. Like I told you everything here is free of charge.. Ba sai kin biya da jikinki ba.. I’m not interested.. Get dressed now.. And don’t make me wait..!” Daga haka mik’ewa yai ya fice ya nufo k’asa.
Tai saurin tattaro rigarta ta tak’ure waje guda wasu hawayen na zubo mata. Har lokacin bata dawo daidai ba.. Rintse idanunta tai sosai tanaji kaman har lokacin cikin jikinsa take.. A hankali ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka wanke mata fuska. Ta Ware Doguwar rigar tana gani.. Ya zama dole ta bar wannan gidan, bazata iya ci gaba da zama ba, ba Karnuka ba ko kuraye ne zai sake mata zata gudu.. Bathroom ta koma ta d’auraye fuskarta ta goge da towel.. Dama sumarta tupke yake cikin ribbon. Ba don taso ba Ta zira rigar wanda yake daidai ita kaman an auna. Ta rufa mayafin rigar akanta tana duban kanta cikin mirror a nan toilet d’in.. Dikda bata shafa komai a fuskarta ba Ta fito tas Sady pretty d’inta saidai fuskarta da yake kaman Ta maras lafiya. Ta sadda idanunta k’asa kafin ta nufo k’ofa, nan taga takalmi flats mai kyau a bakin k’ofar da alama shi ya aje mata. Ta zira k’afafunta ciki a hankali kafin Ta nufo motar tasa.
Tai tsaye kaman bazata shiga ba har lokaci idanunta na k’asa bata d’ago ta dubesa ba.
“Ke shige mu tafi we don’t have the whole day..” Ya fad’i yana key ma motar.
Bai tsaya biye mata ba ya mik’o hannunsa ya bud’e mata front seat.. Ta d’an d’ago ta saci dubansa amma sai taga idanunsa naga wayarsa ko kallon yanda take baiyi ba. Tai k’wafa cikin zuciyarta kafin Ta shige motar. Kaman wanda yake jira nan yaja motar suka fita daga gidan.. Ya sauk’o ya rufe gate d’in gidan kafin suka d’au hanya..
Suna tafe babu mai cewa komai. Addu’a kurum take cikin zuciyarta Allah yasa ya maidata gidansu.. Bata ida addu’an ba ta sinkayo muryarsa yana fad’in “A ina kuka had’u keda Sagir.. ? Allah yasa ba club bane ko Hotel dan ni banyi miki kama da mutumin da za’a gansa a irin wad’ann wajajen ba..”
Ta dubesa da mamakin tambayar sai kuma ta girgiza kai tace “Wannan ba matsalarka bace koma a Ina muka had’u..”
Jinjina kai yai yana duban kwalta “Baki so ki koma gidanku ashe..” Ya fad’i ba tareda ya dubeta ba.
Jin abinda ya fad’i ya sanyata saurin fad’in “A park muka had’u..”
Ya tambayeta sunan park d’in nan ta sanar dashi.
Jinjina kansa yai a hankali yana mai maimaita sunan park d’in..Lokaci guda ya d’auki direction d’in da zai kaisu Park d’in data fad’i masa.
Ta kuma sinkayo muryarsa yana fad’in “Kina jina.. We are on a mission.. If you mess everything up delay d’in komawarki gidanku zaki ci gaba da ja ma kanki.. We’ll go to the park, and we’ll act like a real couple.. Don’t mess up kinji abinda na fad’a miki koh.. Idan kika b’ata komai lokacin zama a GIDAN ARO kike k’ara ma kanki.. The sooner we are done with this mission, the sooner you get your freedom back. Did I make myself clear..?” Ya k’arashe yana dubanta da gefen ido.
A hankali ta jinjina kanta har lokacin fuskarta a hard’e.. Suna tafe tana jinsa yana waya wanda dagaji da abokin aikinsa yake wayar.. Har suka isa Park d’in waya yake.. Saida sukazo yanda zai parking kafin taga yaja jikin Seat d’insa ya ciro bindiga.. Ganin bindiga da tai ya sanyata ta razana “Na shiga uku.. Mai zakayi da bindiga..?” Bai amsata ba yaci gaba da shirya bindigar kafin ya d’aga jacket d’insa ya mak’alata ciki..
Ya d’ago yana dubanta har lokacin a tsorace take “Don’t mess up na fad’a miki.. We will act like a real couple.. Kinji abinda na fad’a miki ko bakiji ba..?” Tai saurin jinjina kai alamun taji.
Sauk’owa yai ya zagayo yanda take zaune ya bud’e mata.. Hannu ya mik’a mata alamun ta kama hannunsa ta fito..
Ta dubesa ta kuma dubi hannun nasa. Tsareta da idanu yai alamun ta rik’e hannunsa ta fito. Zuciyarta sai tsinkewa yake, tai k’ok’arin saita kanta kafin ta mik’o masa hannun nata ya rik’o yana mai sakar mata murmushi..
“My lady..!” Ya fad’i yana sakale hannunta tsakankanin arms d’insa da k’irjinsa. Lokaci guda ya d’an janyota cikin jikinsa da k’arfin gaske yai k’asa da kansa saitin kunnenta yana fad’in “Remember this is all acting.. So you better cooperate.!”
Tai murmushin yak’e tana dubansa “Of course My Detective..!” Ta k’arashe tana d’aure fuska kaman ba itace mai fake smile d’in ba.
Sunata wuce mutane a haka sai ka rantse wasu masoya ne.. Saman grass carpet suka k’arasa suka zauna gefen wasu furanni.. Nan wayarsa ta soma ringing.. Assad ne mai kira..
Lokaci guda ya mik’e yana mai amsa wayar idanunsa akan Sadiya.
Daga d’aya b’angaren Assad yace “Kana nufin kaida Sadiya..? Toh mai kuke a park.?”
“We’re on a mission..” Ya basa amsa kai tsaye.
“Mission kuma.. Wane irin mission..?” Assad ya tambaya.
“Dama da nace maka aurenta da nayi mission ne baka yarda bane.. Well yanzu sai ka yarda.. Abun shine itada Sagir a nan suka had’u so kaga definitely ta iya yuwa shida accomplices d’insa suna zuwa nan.. Idan har suna hunting d’inta zasu making move”
Assad ya girgiza kai dan ya dena mamakin abokin nasa “You’ve got to be kidding me Mu’azzam.. What if she gets hurt.. What if suka mata wani abu bakada backup bakada komai..”
Katsesa Muazzma yai da fad’in “They’ll have to pass through me before they lay a finger on her..! Kaidai kawai stay alerted zan iya neman backup daga wajenka.”
Assad ya jinjina kai yace “Shieknan.. Be careful Mu’azzam.. Allah ya tsare.”
Mu’azzam ya amsa da Ameen kafin sukai sallama.. Yana dubanta yanda take ta wasa ma wani yaro shida mamansa sunzo sun zauna a wajen.
Yanata kallonta yanda take wasa ma yaron har dai suka mik’e zasu wuce shida mamansa yaron har waving yake mata itama tana masa kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Sosai Mu’azzam ya shagala da duban yanda take murmushi. Yana nan tsaye wayar Safeenah ya shigo masa..
Ya d’aga cikeda kulawa, saidai yana d’agawa da kuka Safeenah ta fara masa tana fad’in taji ciwo ya tafi ko sallama basuyi ba gashi nan taji ciwo kuma mai gyaran k’afan yace zata iya kaiwa sati guda kafin Ta fara taka k’afar.. Sai kukan shagwab’a Safeenah take masa.. Lallashinta ya soma idanunsa na kan Sadiya yana kuma matsowa kusan Sadiyar yanda zataji wayar da yake da matarsa.
Abin ya mugun dad’i ma Safeenah ya kuma bata mamaki Wai Mu’azzam ne ke lallashinta irin haka ba tareda ya gwaleta ba ikon Allah.. Lallai ta yarda yanzu kam tana da matsayi mai girma cikin zuciyarsa.. Ta fara Mitan ita ta gaji Abuja take son dawowa su tattara su koma gidansu.
Mu’azzam yace “I had to attend to some urgent matters ne shiyasa na dawo cikin gaggawa but Kar ki damu soon zamu koma.. I promise you kina dawowa zamu koma gidanmu.. But for now kiyi abinda mai gyaran yace kar azo a sami matsala..”
Sadiya kaw d’auke kanta tai kaman bata a wajen.. Yanda kasan tafiyarsu ba d’aya bane haka tayi.. A ranta tana fad’in ita tausayin matar tasa ma take dan wllhi sam batai dacen miji ba.
Wasu samari ne guda biyu suka dosota d’ayan yana wani fad’ad’a murmushinsa ya k’araso yanda take zaune “Miss Beautiful are you alone..?” Ya fad’i yana mai k’ok’arin duk’awa. Ai kafin yakai k’asa Mu’azzam yai ma Safeenah sallama a gurguje yana sanar da ita zai koma bakin aiki.. Lokaci guda ya k’araso yanda Sadiya ke zaune.. Ya sakalota cikin jikinsa yana fad’in “Sorry Wife na barki ke kad’ai..”
Saurayin ya d’an sha jinin jikinsa ya mik’e yana basu hak’uri yana fad’in baisan matar aure bace.
Mu’azzam baice komai ba Sai aika ma Sadiya mugun kallo da yake.. Suna shigewa ta cire jikinta daga nasa su duka biyun suna sakin huci
“So abinda kika saba zuwa yi park kenan.. Dan kiyi new catch masu kud’i koh.. Kina wani zaune wancan d’aniskan yaron mai suma kaman na shed’an yana k’ok’arin zama kusa dake.. Kuma ko a jikinki koh.. Da kin bari ya zauna da na had’eku duka biyu na harbe..”
Rausayar da idanunta tai cikeda k’osawa take k’ok’arin mik’ewa “Mr Inspector da alama babu wani abinda zaka samu a nan.. Kaga ruwa zai iya sauk’owa any moment.. Dan Allah ka maidani wajen Ummata tinda nayi abinda ka umarceni..”
“Ank’i a maidake d’in..!” Ya fad’i yana tsareta da idanu dan zuciyarsa tafarfasa take tin lokacin da yaga samarin nan sun nufota.
Fuzar da fuci tai kad’an kafin tasa kai kaman zata shige.. Saidai tuni taji ya janyota ta dawo da baya.. Hakan yai daidai da soma zuban ruwan sama.. Mu’azzam ya mak’aleta cikin jikinsa yana mai kallon yanda ruwa ke zubowa.. Dubansa take da idanunta da sukai rau rau hawaye gauraye da ruwa cikinsu.. Drops d’in ruwa saman fuskokinsu su duka biyu.. Wani mutumi ne mai tallan lema ya k’araso yana fad’in “Rankaidad’e saura d’aya ce ta rage ya kamata ka siya.. Kar Amarya tayi mura..”
Mu’azzam ya dubi mutumi mai saida leman yace masa “Nawa ne..?”
Mutumin ya fad’i masa kud’in leman.. Zaro kud’ad’en yai cikin pocket d’insa ya mik’a wa mutumin yana fad’in “Keep the change.” Mutumin ya masa godiya had’ida mik’a masa lemar.. Saida ya bud’e masu ma kafin ya mik’awa Mu’azzam d’in..
Lokaci guda ya kuma janyota cikin jikinsa sannan ya rufa masu lemar akansu.. Ta dubi hannunsa yanda ya rungumota ya rik’eta, zafin kalamansa akanta kurum take tunawa da wulak’ancin Sa take tunawa.. Lokaci guda taji wani irin k’arfi yazo mata.. Tai k’ok’arin turasa dashi da lemar tasa.. Saidai sam bai saketa ba saima dad’a matseta da yai.. Saitin kunnenta yake fad’i a hankali “Don’t get wrong ideas dik cikin acting ne..!”
Lumshe idanunta tai hawaye na gangaro mata.
Ganin tana rawar d’ari ya sanyasa zame jacket d’insa ya rufa mata.. Still saida ya sake tina mata cewa a cikin acting ne.
Ruwan na k’aruwa dole suka nufi mota, ya bud’e ya shigar da ita.. Nan wani mutumi mai hoto ya tsallako a guje yana tare Mu’azzam d’in.. Envelope ya mik’o masa