Showing 135001 words to 138000 words out of 209154 words

Chapter 46 - GIDAN ARO COMPLETED HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3041

dake ba. Dan ma ana son tafiya dake.. Ba don Inne tace a kai mata ke ba Maiyasa ma zanyi tafiya dake bayan inada wata matar.. Kema Kinsan bake kad’ai gareni ba..”

Ta d’an juyar da fuskarta kad’an kafin tace “Maiyasa bazaka tafi da matar taka ba.. Tinda kanada ita..”

“Bakiji mai nace miki bane.. Badon Inne ba bazanje dake ba. Ita ke son ganinki kuma na mata alk’awari zan kai mata ke.. Nasan bazaki bari na sab’a wann alk’awarin da nai mata ba.”

Ta d’an dubesa kafin tace “Is this my new assignment..? Is this another mission..? Idan mun dawo mission d’in ya k’are..?.”

“Mai kike so ayi yanzu.?” Ya tambaya yana dubanta.


“Zanje sabida kace Inne.. Amma idan na dawo mission d’in ya k’are.. Kuma inada condition d’aya kafin na bika..”

Ya tsareta da idanu yana dubanta Wai sai ta gindaya masa sharud’a kafin Ta yarda Ta bisa.

“Meye condition d’in naki..?”

Muryarta ya sinkayo tana fad’in ”Sai ka rantse min da Allah zaka sakeni da zaran mun dawo kuma zaka fice daga rayuwata gaba d’aya.”

Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubanta Wai sai ya mata rantsuwa zai saketa kafin Ta yarda ta bisa.

Umma da Ta fito daga d’aki zata nufi kitchen Ta sinkayo tattaunawar nasu Sadiya na fad’in sai Mu’azzam ya rantse zai saketa kafin Ta amince ta bisa garinsu. Fasa shiga kitchen d’in tai Ta k’araso parlorn da sallama. Mu’azzam ya risina ya gaisheta.

Ta amsa tana aika ma Sadiya mugun kallo nan take tambayarsa jikin Mamynsa Ta kuma sanar dashi sunyi waya da Inne jiya da dare tace jikin Mamyn nasa da sauk’i. Mu’azzam yanata amsa mata cikin girmamawa yana fad’in aima yanaso yaje ya dubasu idan abubuwa suka d’an lafa.. Umma tace “Aikam ya kamata.. Allah dai ya bata lafiya yasa kaffara ne.”

Mu’azzam yanata amsawa da Ameen Umma yayinda Sadiya keta dubansu tana mamakin yaushe har sukai Sabo haka har Umma tasan ‘Yan gidansu suna gaisawa a waya. Bata ida tinanin ba Ta sinkayo muryar Umma na Ta taso suyi magana.

Jiki babu laka Sadiya tabi bayan Umma dan taga irin duban da Umman tai mata.


Tana shigowa d’akin taji sauk’an mari mai kyau a fuskarta.

Ta kame fuskarta tana kuka.

Umma na huci take nunata da yatsa “Ashe Bakida mutunci.. Ashe ke mahaukaciya ce ban Sani ba.. Mijin naki kike cewa yayi rantsuwa zai sakeki dan kawai yace yana so ya d’aukeki.. Ashe baki d’auki darasi kan abinda ya faru dani da mahaifinki ba.? Toh idan ya sakeki d’in sai muga ina zaki tafi dan nan ma alfarmarsa kikeci.. Yanzu Sadiya ashe duk karatun da duniya ta biya miki baki d’auki darasi ba.!”

Cikin kuka Sadiya ke fad’in “Umma fah baki San mai ya mun bane sanda ya d’aukeni. Yace mun ‘yar tasha ya kirani da sunaye masu muni har had’ani da Karnukansa yai yace ni Kariya ce.”

Umma ta kuma kai mata bugu tana fad’in “Sai mai dan yace miki haka.. Wa ya ja ma kansa.. Ke har kinada bakin magana bayan rufa miki asiri da yayi.. Mutumin da ya biya miki bashi ya tsare miki mutuncinki da na ahalinki ya kub’utar dake da ahalinki wannan mutumin kike k’ok’arin wulak’antawa.. Ashe idan baki gode masa ba har zaki wulak’antasa.. Ke bandama taimakon Ubangiji ina zaki samu miji irin Mu’azzam.. Har kina wani gindaya masa sharud’a shi bai miki haka ba.. Tun wuri ki wuce kije ki duk’a ki bawa mijinki hak’uri tun kafin Ubangiji baiyi fushi dake ba.”

Ta mik’e tana goge hawayenta. Tin kafin Ta zauna Umma Ta lek’o tana fad’in “Mu’azzam ka dena biye ma wann taurin kan nata, ta shirya maza ka d’auketa ku tafi bazata kuma kwana mana a nan ba..”

Ya murmusa kad’an yace “A’a Umma ba damuwa ai tafiyar ma zai kai zuwa thursday in sha Allah.. Ai hak’uri Umma..” Ya fad’i yana duban Sadiya dake goge fuskarta da mayafinta.


Umma Ta aika mata mugun kallo kafin tace “Kinci albarkacinsa.” Tai k’wafa kafin Ta janyo k’ofar parlorn ta basu waje.


Sai goge hawayenta take ba tareda Ta dubesa ba.

Ya k’araso ya kamo kafad’unta ya zaunarta saman kujera.

Hannunta ya cire ya shiga goge mata hawayen nata da yatsun hannunsa “I didn’t mean for this to happen.. I believe Umma bata San wasa kike ba.. Mission d’inmu bazai tab’a k’arewa ba har mu koma ga Ubangijinmu... Every day is another mission for us to accomplished..” Ya k’arashe yana mai mak’aleta gefen k’irjinsa na dama. Bata iya furta komai ba Sai lamo da tai cikin k’irjin nasa tana ajiyan zuciya.

Bashi ya bar gidan ba saida yaci Dinner, ko bayan da ya tafi ma Sabon fad’a Umma ta dingayi ma Sadiya. Ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Har saida Aunty Larai ta k’waci Sadiya hannun Umma.

Umma Ta mik’e tana furta “Wanda duk bai gode ma Allah ba zai gode ma azabarsa barikiji na fad’a miki..” Daga haka shigewa tai ta bar Sadiyar da Aunty Larai tana lallashinta “Haba Sadiya har yaushe zaki bud’I baki kice mijinki ya sakeki, kin kuwa San zunubin dake cikin yin hakan.. Mutumin da kullum rawar k’afa yake akanki yana sintiri a nan safe da dare bama muzguna miki yake ba balle ace eh ga dalili.. Kar fah ki mance Mu’azzam mata biyu ke garesa kuma wacce duk tafi kyautata masa cikinku itace zata zamto mai babban matsayi cikin zuciyarsa koda bai furta hakan ba dan zuciya tana san mai kyautata mata ne..”

Cikin kuka tace “Aunty wllhi fah ba sona yake ba kawai mission d’insa yake dani.. Umma bazata fahimci haka bane..”

Aunty Larai Ta murmusa kafin tace “Salon nasa soyayyar kenan Sadiya.. Kuma Kema na tabbata kina son mijinki kawai dai halin namu na mata ne kike d’an masa.. Hakan nada kyau dan mu mata saida aji koh.. Amma ai a hankali kar ya zarce kima.. Ki natsu ki karanci mijinki kisan wanene shi Ina nufin d’abi’unsa da halayyarsa.. Idan kika karanci wad’ann kika San yanda zakiyi mu’amala dashi ina mai tabbatar miki zaki samu mijinki zaki tafiyar da gidanki yanda kike so.. Ba Wai asiri bane ko tsafi yake sa a mallaki Zuciyar miji.. A’a babu boka babu Malam idan kinaso zaki zama sarauniya wajen mijinki.. Tsananin biyayya da iya kula da buk’atunsa shi ke sa mace ta samu wann d’aukaka a wajen miji.. Sannan kafin ki iya wann sai kin karanci wanene mijinki.. Shiyasa wasu lokutan sai kiji ana cewa wasu matansu sun asircesu.. Wlhi babu boka babu Malam kawai sanin makaman rayuwa ne. Quite alright akwai masu mallaka da asiri amma kuma akwai masuyi da dabaru irin namu na mata da Ubangiji ya hore mana.. Idan yace mission bishi a mission d’in, ki rikitashi da naki salon mission d’in kinji koh.. Yana jefo miki assignment capke ki solving masa tun kafin ya kuma jefo miki wani yanda zaki zamto kece wacce kike basa assignments d’in bashi ba.. Ko wane d’an adam akwai halinsa da yake nature ne, wad’ann natural d’in sai kiyi adopting nasu since we can’t change what’s natural. Mace ita take raya gidanta kuma ita take kashe gidanta.. Duk wasu makaman yak’in Allah ya mallaka miki kawai saidai idan baki San yanda zakiyi amfani dasu ba. Kina jina.. Ki saki jiki ki tarairayi mijinki Mu’azzam na matuk’ar k’aunarki koda wasa kar ki bari gidanki ya kufce miki a hannunki.. Kula da miji ba gajiyawa bane sannan yi masa biyayya ba kasawa bane. Wad’ann sune zasu d’aga martabarki da Kimarki a idanunsa kinji koh.. Idan nace haka ina nufin tsafta kwalliya kula da muhalli iya sarrafa kayan abinci da girkasu Duk suna cikin tattalin gida kinji koh.. Muhimmi kula da buk’atarsa, so goma idan zai nemeki kar ko gwada masa kin gajiya, ko a fuskarki kar ki bari ya gane haka, wnn ba k’aramin kima da martaba zai k’ara miki a idanunsa ba Sanna k’aunarki zai ninku cikin zuciyarsa.. Ki gyara masa kanki ciki da waje, idan nace ciki da waje Ina nufin jikinki da kuma matantakanki.. Gyara ko a musulunci nada kyau dik abinda kika san zaisa mijinki yaji dad’i ya kuma samu gamsuwa dake matuk’a bai kauce ma shari’a ba Sannan baya cutarwa kina iya amfani da abinki dan gyaran gidanki.. Abu na gaba ki girmama iyayensa mahaifiyarsa ‘yanuwansa ki nuna masa suma naki ne. Abokiyar zamanki ki zauna da ita zuciya d’aya da alkhairi..”

Sadiya kam sadda kanta k’asa tai tana d’aukan karatun Aunty Larai kaman D’alibi gaban Malami.

Aunty Larai da ta kula kunyarta take tace “Ki saki jikinki dani kinji koh.. Ki tambayeni dik abinda ya shige miki duhu kinji koh.. Ni da Allah ya bani d’iya haka zan zama very open da ita, kafin ta sani a wani waje ni zan koyar da ita ta hanyar da ya kamata.. Tinda Allah bai bani d’iya ba gaki nan ya bani.. Ki saki jiki dani kinji koh babu wani kunya yanda zaki inganta rayuwar gidanki da auratayyarki nake k’ok’arin fahimtar dake kinji koh.. Maza tashi kije ki wanke fuskarki anjima zamu ci gaba.” Ta jinjina kai a hankali kafin Ta mik’e ta nufi bathroom.


Aunty Larai ta bita da kallo fuskarta d’aukeda murmushi, ta d’au alwashin kafin Mu’azzam ya d’auki matarsa sai ta gyara masa ita tsaf, irin gyararrakin da suka cancanci Ta samu. Kama daga wanda idanu ka iya gani harma wanda idanu bai gani.

**

Washe gari aka sallami Assad sannan Mu’azzam ya karb’i takardan gwajin DNA da yai, result d’in bai matching da k’wayar halittar Musaddiq ba. Hakan na nufin hular bata Musaddiq bace.. Sosai hakan yasa zuciyar Mu’azzam yin sanyi.. Saidai ya rasa dalilin da yasa ya gaza samun cikakken natsuwa akan sakamakon gwajin. Baisan dalili ba amma can k’asar zuciyarsa yana jin bai yarda da sakamakon ba.

Sauk’e ajiyan zuciya yai a hankali yana mai fuzar da fuci lokaci guda ya saka abin goge allo ya goge dogon arrow da ya zana daga hoton Danger zuwa B.A.T da ya rubuta da question mark. Dai dai lokacin Yusuf da Maleeka suka shigo.




SameenaAleeyou📚
[9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO*




*44*






*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Marker ya kuma d’auka ya zana allon ya sake rubuta abinda ya goge. Maleeka tai masa K’uri tana dubansa, Toh ko bai yarda da sakamon gwajin bane.? Kodai shakku da kokonto ya fara..? Bata kai ga nemo amsar ba ta sinkayo muryar Yusuf yana fad’in “Sir menene B.A.T yake nufi if I may ask..?”


Mu’azzam na fuskantar allon yana karantar hotunan mutanen dake mak’ale jiki yake fad’i da Yusuf “Soon enough zamu gano wanene B.A.T.. But for now it’s classified..” Ya k’arashe yana mai juyowa had’ida tsaresu da idanu.

Yusuf ya d’anyi gyaran murya yace “Sir, is there any assignment da zaka bamu akan B.A.T..?”

Ya tsare Yusuf da idanu yana karantarsa kafin yace “For now akwai certain people a cikin Department d’in nan who are messing with our case.. And we need to find those people and make them pay..” Yana maganar yana duban Maleeka da tuni zuciyarta kaman bai wajen, kana ganinta zaka fahimci tana cikin tsananin tsoro.

Mu’azzam ya tako zuwa gabanta idanunsa tar akanta “You will be the one to take this part..” Ya fad’i yana dubanta.

Saida ta d’an firgita kafin ta d’ago tana dubansa “Sir..?”

Mu’azzam ya d’an gyara tsayuwarsa kafin yace “Are you alright..?”

Saurin saita kanta tai kafin ta jinjina masa kai “I’m good, sir.”

Ya jinjina kai yana duban hannunta mai ciwo da aka harba “How is your wound.?”

Ta k’ak’aro murmushi cikeda jin dad’in ya tambayi ciwonta. Lokaci guda take duban hannun kafin tace “Na warke Sir, and I’m ready for another assignment..”

Ya jinjina kai kafin yace “Kinji abinda nace kenan..?”

Tai saurin dubansa sai kuma ta dubi Yusuf dake tsaye gefe yai Folding hannayensa yana dubansu. Saurin girgiza kai tai kafin tace “Pardon me sir, did you say something..?”

“About B.A.T..” Ya fad’i yana dubanta wanda ya kuma sanyata razana.

“Na zaci kace it’s classified, sir.” Ta fad’i a d’an daburce.

“I’ve changed my mind.. B.A.T is someone in our Department who is working hand in hand da criminals d’in da muke nema.. B.A.T is Danger’s Spy a cikin CID.. And If we want to catch Danger once and for all we must catch B.AT first dan shine zai leading namu to Danger..” Ya d’an soma takawa kad’an yana zagaye room d’in kafin ya tsaya jikin wani table da Maleeka ke tsaye gefe. Zuciyarta sai tsinkewa yake.. Lokaci guda Mu’azzam ke dubanta kafin yace “You will be the one to carry out this assignment.. ki nemo mana wanene B.A.T a cikin CID.” Daga haka d’aukan folder d’in dake wajen yai kafin ya fice daga office d’in.

Maleeka Ta fuzar da fuci tana duban Yusuf “Goddamn binciken cikin gida..? Ta ina zan fara.. Wa zan fara suspecting..? How am I going to carry out this assignment Yusuf..?” Ta k’arashe tana fuzar da fuci.

Yusuf ya d’an girgiza kai yana murmushi kafin yace “Tactics kawai zakiyi amfani da ki zak’ulo mana mai cin amanan K’asa da Al’umman cikinta.. Dan duk jami’in tsaron dake huld’a da ‘Yantadda maciyi amanan K’asa ne da Al’ummarta..” Yusuf ma ficewa yai ya barta nan tsaye a wajen gumi na tsartsafo mata.

Maleeka ta fuzar da fuci tana d’aura hannayenta saman table ko shakka babu ta fahimci Mu’azzam so yake ya kamata shiyasa kawai ya bata wann aikin.. Dan idan kana son kama mutum sai ka saka shi ya kamo kansa da kansa.. Yanzu mai zatayi..? Dole ta nemi taimakon Chief Dan idan ba haka ba tayi imani Mu’azzam Sai ya fahimci ita ce take masu zagon k’asa.. Da wann tunanin ta fice daga offishin tana sakin huci duk a dame take.

Kai tsaye Office d’in Chief Ta nufa tana yarfe gumi.

Chief ya tsareta da idanu yana girgiza kai alamun meke tafe da ita.

Fuzar da wani hucin ta kuma yi kafin tace “Ya fara zargina Chief..”

Chief ya girgiza kai yace “Waye kuma ya fara zargin ki..?”

“Waye kuwa idan ba Mu’azzam Gamji ba.. Can you imagine yayi assigning d’ina cikin team d’inmu na nemo masa wanene mai mana zagon k’asa a entire CID.. Idan ba zargina ya soma ba bazai tab’a assigning d’ina ba..” Ta k’arashe tana kuma shafe goshinta.

Chief ya murmusa kafin yace “Then give him what he’s asking for.. Ki kai masa mai yi maku zagon k’asan..”

Maleeka ta juyo tana dubansa shaye da mamaki kafin tace “Did you hear yourself..? Ni ce zan kai masa kaina ko kuma kai ne zan kai masa a matsayin wanda yake masa zagon k’asa.. Sanin kanka ne Chief binciken cikin gida yafi komai wahala a aikinmu..”

Chief ya murmusa kafin yace “Ku duka yara ne a aikin.. Baku San yanda al’amara suke gudana a wajenmu ba.. Especially Inspector Gamji.. Yaro mai k’waza mai kuma so ya kawo sauyi a al’amran tsaro na k’asar nan.. Saidai kash da irin wann k’wazon nasa ina mai tabbatar miki baza’a barsa yaje ko Ina ba.. Ko ni Jaja banyi eliminating nasa ba akwai manyan k’wari a sama da zasu shafe shi musamman idan suka lura zai kawo ma business d’insu cikas.. Su Waye ‘Yantaddan Maleeka..? Suna nan a cikin mu kuma ana dama hark’an mulki da tsaro dasu.. Kawo gyara ba abu bane mai sauk’i a k’asa irin namu saidai talaka yayita add’ua yana neman d’auki a wajen Allah dan shine kawai zai iya saita al’amran k’asar nan..”

Maleeka ta fuzar da fuci tace “Ni duk ba wanna ba Chief.. Ya zanyi da Inspector Gamji..?”

Chief ya murmusa ya matso yana shafan fuskarta kafin yace “Abu ne mai sauk’i.. Idan ya gwada yana son kamaki ke kuma sai ki tura makusancinsa cikin ramin.. Abinda nake nufi wannan shine perfect opportunity naki da zaki gwara kansa da abokinsa..”

Maleeka tai shiru tana sauraron Chief kafin ta girgiza kai tace “Ban fahimceka ba Sir..”

Chief ya kuma murmusawa kafin ya saka makulli ya rufe ofishinsa ya janyo Maleeka yana fad’in barin na fahimtar dake.

Sai bayan tsawon d’an lokaci kafin Maleeka ta fito daga ofishin Chief tana kintsa kanta.

Mu’azzam da fitowarsa kenan daga wani dept d’in nan ya hangi Maleeka ta fito daga Office d’in Chief.. Sannan Ta fito dik a birkice sai waige waige take tana gyara zaman rigarta.

Jinjina kai yai a hankali kafin ya furta “Muje zuwa.. Sannu a hankali zamu kamaku..” Daga haka Sa kai yai ya fice daga ofishin gaba d’aya.

**

FUFORE


Yau ce Rana ta farko da ta soma shiga d’akin Inne, Inne ta aiketa ta d’auko mata k’aramar jakarta dake gefen bedside zasu fita zata raka Innen gaisuwan haihuwa jikar k’awarta ta haihu a cikin gari.. Nan Ajidde ta tsaya tana duban tsarin d’akin baki hangame tana fad’in “Kaga d’aki saikace ba na tsohuwa ba.. Masu shi dai suna abinda suka so.. An gaisheka d’aki kaci kud’in gidan gona gaskiya..” D’aga kan da zatai Ta hangi k’atoton hoto saman gadon.. Inne ce zaune a tsakiya sai Samaruka guda biyu Sun tsaya gefe da gefe sun sakata a tsakiya dukkansu sun dafa Innen murmushi saman fuskokinsu.

Ta gane d’ayan Mu’azzam ne wanda tasan jikan Inne ne saiko d’ayan da ko a mafarki bazatai kuskuren mance kamanninsa ba, Kuran tashe nata ne.. Toh ya akai sukai hoto irin haka kaman wasu ahali, a iyaka saninta Kuran tashe yace mata shi abokin jikan gidan ne.. Toh ma saida taga sunyi hoto haka taga kamanninsu ya fito.. Ikon Allah toh kodai ‘yanuwa ne..?

Bata kaiga samo amsar ba Mama Hinde ta shigo tana fad’in “Wai an aikeki Ajidde kaman an aiki Bawa garinsu.. Inne nata jiranki zaku fita..” Mama Hindu ta girgiza kai kurum ganin yanda Ajidde ta kafe tana kallon hoto..

“Ke Ajidde Wai bakiji bane..?”

Sai sannan Ajidde ta juyo tana duban Mama Hindu.. Sai kuma ta soma nuna mata hoton ba tareda tace komai ba..”

Girgiza kai Mama Hindu tai tace “Toh Sarkin shiririta wanene bak’o cikinsu a wajenki. Inne ce baki sani ba ko kuwa Mu’azzam da Musaddiq ne baki sani ba..?”

“Mana Hindu kika ce menene sunan wancan dake tsaye daga b’angaren hagu..?”


Mama Hindu Ta girgiza kai tace “Wai duk zuwanki gidan nan baki sansa ba.. Kwanakin baya ya koma can Abuja gidan Babansa amma ya jima a nan ai shi Musaddiq d’in..”

Ajidde tace “Kika ce sunansa Musaddiq.. Toh ai shine Kuran tashe.. Na rantse da Allah shine Kuran tashe.. Wllhi bazan tab’a mance kamanninsa ba.. Dama jikan Inne ne..?”

Mama Hindu ta girgiza kai tace “Adana tambayoyinki har ku dawo Inne na jiranki yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login